⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 9: Chapter 9

Tana kallonsa ta Marairaice “Nuwaira ce tace muje mu ɗauko sa wlh ka yarda dani ba laifi na bane” cije lips ɗinsa yayi kaɗan ya ma rasa me zai ce mata, ta miƙe daga zaunen da take ta shige jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauƙe ajiyar zuciya “amma na maka alƙawarin bazan sake ba, daga yau duk abinda kace min zanyi kayi haƙuri pls Albi” shiru yayi bai ce komai ba ya sa hannu yana shafa kanta a hankali lost in thought cause Nuwaira itace problem ɗin Amira gabaɗayansa, for the past 5 years da suka yi aure duk wani matsala da suka samu wanda zuwa yanzu bazai iya lissafa su ba Nuwaira ce take janyo musu, it went as far as da ƙyar Amira ta yarda ta haifi Saif cause Nuwaira tace mata zata ɓata jikinta idan ta yarda ta haihu she wanted aborting cikin Saif ba don Allah ya taƙaita kuma ya ankara da wuri ba.

Ɗago ta yayi daga jikinsa ya maida iya gefen bed ɗin ya shafa fuskarta ya miƙe tsaye ya wuce closet dan shiryawa, wani murmushi Amira tayi tana binsa da kallo dan kwata kwata bata yi tunanin zai sauƙo da wuri haka ba, wannan ya sake tabbatar mata da irin son da Ahmad ke mata, miƙewa tayi tabi bayansa closet ɗin, ya saka dogon wando yana ƙoƙarin saka riga ta shigo ta tsaya daga bakin ƙofa tana masa wani naughty look, sau ɗaya ya kalleta ya cigaba da abinda yake yi, ta ƙaraso ta tsaya a gabansa tana kallonsa ɗage mata gira yayi ta girgiza masa kai ta kai hannunta duka biyu ta saƙala a wuyansa tana kallon cikin idanunsa kafin ta ɗan ɗage ƙafafunta ta haɗe bakinta da nasa, ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali ya sa hannunsa ya cire hannayenta daga wuyansa ya maidasu bayanta ya jingina ta da bangon wajen kafin ya zare bakinsa daga nata yana kallon cikin idanunta, murmushi ya mata ya sa hannunsa ya shafa fuskarta kafin ya sake ta ya koma ya ɗau rigarsa ya cigaba da sakawa, sai da ya gama sakawa kafin ya juya ya kalleta yanda ta jingina da bangon tana kallonsa jikinta duk a mace, ya juya ya fita daga closet ɗin, gaban dresser ya ƙarasa yana feshe jikinsa da turare ta fito daga cikin closet ɗin sai kuma ta nufi ƙofa fuuu ta fita, binta yayi da kallo sanda yayi murmushi ba yana shafa kansa. Satinta biyu kenan da dawowa Nigeria, zata iya cewa life has never been happier, sosai take jin ɗaɗin zamanta da Mami da big Daddy like dis is home, anan babu mummy da fuska biyunta, babu Suhaila babu Daddy though sometimes tana kewan Dad sosai, a yanzu ma makaranta ake ƙoƙarin nema mata cause big Daddy yace babu abinda za’a jira.

Yau ma suna zaune a palour da Fahad da tunda ya ƙyalla ido ya ganta sunje gidan uncle Aminu da Mami shikenan gidan Mami ya zama gurin zuwansa, kusan kullum sai ya zo har ta saba sosai da shi. Mami ta fito daga kitchen tana kallonsa tace “Fahad zaka ci abincin a dinning ko a kawo maka palour?” Girgiza kai yayi “No Mami wallahi am full daga gida fa nake” Mami ta hararesa tana ajiye warmer akan dining “ɗazu kuma kace daga wajen aiki kake, My friend zo kaci abinci” Na’ima tayi dariya tana kallonsa ya harareta ya miƙe zuwa dinning ɗin dan da gaske yunwa yake ji, yana kallon Mami ya zauna a kujerar dining ɗin ya langaɓe kai “kin dai yi insisting Mami amma ba wani yunwa fa nake ji ba” Mami bata kulashi ba ta dubi Na’ima da ta mayarda headphone ɗinta kunnenta tana gyara kwanciyarta akan kujera ta ɗaura mackbook ɗinta akan cikinta tana kallo

“Na’ima” pausing abinda take kallo tayi ta ɗago kanta “zo kici abinci” “Mami a ƙoshe nake nikam, besides bana son in ci anything heavy da dare” harararta Mami tayi bata sake ce mata komai ba tana kallon Fahad tace “jiya big Daddy ya maka maganan Makarantar Na’ima koh?” “Gyaɗa kai fahad yayi yana cin abincin gabansa “eh wai yace i should handle it, amma ke a ganinki base ko Nile wanne zaifi?” Ɗan kallon Na’ima tayi sai kuma ta maida kallonta kan Fahad “ina zan sani, ita wanne tafi so wai?” Sai da ya kurɓi lemon juice dake gabansa kafin ya dubi Mami “Faɗila ce take zugata wai taje Pan-atlantic tunda accounting take so” Mami tayi tsaki kaɗan “haka Faɗilar tace min, banda shirme tayaya Na’ima zata zauna a gidanta, itama duka duka yaushe tayi auren? Wata na biyar kenan fa har kuma ace ƙanwarta ta dawo wajenta da sunan karatu? Nikam ai nace mata bazai yiwu ba Big daddy ma ba yarda zaiyi ba” Fahad yana cin abincinsa yace “Ah toh, akan wani dalili ma kawai sai ta koma Lagos, ance mata ita kaɗai ke son Na’imar a dangi” Mami tayi murmushi bata ce komai ba tana kallon Na’ima da ta saka musu cartoon a laptop ita da su Aryan suka koma ƙasan carpet suka kwanta.

Wayarta da ya hau ringing ya sa ta dubi wayar ganin faɗila ke kiranta video call, ta matsa daga gefen su aryan tana dariya ta ɗauka, faɗila dake kwance a palornta tana kallon Na’ima ta cikin screen ɗin tace “Hiiiii” Na’ima tayi dariya “hellloooo” itama ta amsa Faɗila tace “ina Mami?” Juya mata camera ɗin tayi zuwa wajensu Mami kafin ta sake juyo da shi fuskarta, Faɗila ta kwaɓe fuska “yaya Fahad ne?” Na’ima na murmushi ta gyaɗa mata kai “shikenan yanxu zai zuga Mami a hanaki zuwa pan atlantic when am telling u its the best univerity Allah da gaske” Naima tace “its the best ko dai someone wants to be seeing me everyday, ni na haƙura ma yaya Fahad yace kawai zai nema min base” Fadila ta haɗe rai “Lallai ma Na’ima amma haka muka yi da ke?” Naima ta marairaice “ai dama ce miki nayi in Mami ta yarda to ta ƙi yarda ya zanyi?” Faɗila tayi shiru, Naima tana kallon yadda ta ɓata rai tace “kinga haka Mami tace Yaya Nasir ma ai bazai ji daɗi ba tunda baku daɗe da aure ba kuma kawai sai in dawo gidanki da sunan karatu” Nasir dake gefen Faɗila ya leƙo ta cikin wayar “haka muka yi da ke Na’ima? Ya kuna ma matata haka ne? Cant u see shes lonely here?” Ya faɗa yana taɓa kumatun faɗila, Naima tana dariya tace “good evening” “evening Na’ima ya gida?” Tace “lafiya ƙalau” Faɗila tayi wani murmushj tace “nasan wa zan ma magana, big Daddy zan kira anjima in faɗa masa ko kuma in kira daddyna shi ya faɗa ma big daddy, kuma ai bani da lafiya i need ɗan uwana kusa dani Nasan bazai hana ki ba, babe ull tell him too kaji?” Gyaɗa mata kai yayi “in sha Allah” shiru Na’ima tayi kafin a hankali tace “toh Allah ya sa ya yarda”

Washegari a wajen karyawa big Daddy ya dubi Na’ima dake juya tea yace “daughter da base da Nile Abuja da kuma pan atlantic Lagos wanne kike so?” Ɗan satan kallon Mami tayi ganin ba ita take kallo ba a hankali tace “ko wanne” yayi Murmushi “okay jiya uncle ɗinki Aminu ya kirani akan ʼyar uwarki ta damu tana so ki je wajenta ki zauna tare da ita kina so kije?” Sake kallon Mami tayi, ita dai Mami taƙi kallonta tana cin abincinta ba tare da ta kulasu ba, gyaɗa ma Big Daddy kai tayi alamar “eh” yayi Murmushi “okay then pan atlantic its, zan ma Fahad magana zuwa upper week sai ya kaiki Lagos ɗin yayi duk abinda ya kamata, ke kuma make sure kin mayarda hankali kinyi abinda ya kaiki, duk hutu sai ki dinga zuwa kina mana okay?” “Gyaɗa mishi kai tayi “yes Daddy” big Daddy ya kalli Mami “Madam babu abinda zaki ce?” Mami ta ɗan dube shi kaɗan “to me zan ce ? Allah ya bata ilimi mai albarka da anfani yasa can ɗin yafi alkhairi” duk suka amsa da Amin
Sai bayan da big Daddy ya fita kafin Mami ta dubi Na’ima tace “kun kyauta ai da ke da Faɗilar, saura kuje can kuyita shashanci tunda babu mai tsawatar muku, dan Allah Na’ima ki mayar da hankalinki kiyi abinda ya kaiki kinji” tashi tayi tazo ta bayan Mami ta saƙala hannunta a wuyanta “just say Ill miss u Na’ima “ Mami ta harareta “make sure duk hutu zaki zo nan” ta gyaɗa kai tana dariya “promise”

Amira na kwance a kan kujera daga cikin palourn tana danna wayarta ta ɗaga kanta ta saci kallon Ahmad dake kishingide a akan kujera opposite her reading through his tablet, Ga Saif kwance a gefensa yana kallon cartoon wanda Ahmad ɗin ya rage masa muryar har ƙarshe.

Maida kanta tayi kan wayarta tana karanta saƙon Nuwaira da ya shigo

“Ni dama ba nace miki na lokaci bane kika bi kika ɗaga hankalinki kamar wanda kika yi sata ko wani abu”

Sai da ta sake satan kallonsa kafin ta shiga typing mata reply “wallahi Nuwa ban taɓa sanin haka Ahmad ke so na ba sai jiyannan, kinsan ina cewa yayi haƙuri fa shikenan kawai ya bar maganar, kuma na ɗauka xuwa da mukayi muka ɗauko Saif ma zai yi bala’i amma kinga baiyi ba” immediately Nuwaira tayi viewing saƙon kamar dai tana cikin chat ɗin nata ne

“To dama me nace miki? Idan kina so ya dinga biye miki haka to dole sai kin zama kema jan wuya idan yace gabar kiyi kudu sai kiga ya biyo ki kudun”

Amira ta tura mata emoji ɗin dariya “aikam na tabbatar yanxu, ke har haƙuri fa ya bani kuma aka bani kulawa yadda ya kamata, ke nuwa ina son mijina”

“Mtsw kulawar me ya baki?”

“Kema ai kin sani, ba na faɗa miki yadda mukayi da shi ba jiya da dare, ke ashe yayi kewata sosai pretending kawai yake yi”

Nuwaira ta turo mata emoji ɗin dariya “haka kika ce min dai, to dama ai ke bata wasa bace Amii banda ma kin mayar da kanki wata bi ta can, yanzu dai shi yana ina ne?”

Sai da Amira ta ɗaga kai ta kalleshi kaɗan kafin ta gyara kwanciyarta akan kujera “ga shi nan kusa da ni, amma zuwa anjima zaije Abuja meeting, gobe zai dawo da safe, haka dai yace min”

“Ah lallai, meyasa bazai je da ke ba toh?”

“Gobe fa zai dawo Nuwa”

“tab ni dai ba ruwana, kinsan big babes ɗin dake Abuja kuwa ke dai kiyi a hankali”

Nan da nan mood ɗin Amira ya canza tayi shiru batayi reply ba tana kallon Ahmad, tun daga gashinsa dake nan so fyn har ƙafarsa ta bishi da kallo, ta dawo da idanunta face ɗinsa zuwa muscles ɗinsa kawai babu abinda take imagining sai what if da gaske abinda Nuwaira ke faɗa mata hakane kuma ai zai iya yiwuwa fa

Jin wayarta na ringing tayi saurin silencing kiran tun kafin wayarta yayi announcing sunan Nuwaira ta shiga uku, ya ɗago kanshi daga tablet ɗin ya kalleta, Murmushi ta masa ba tare da ya mayar mata ba ya mayarda kansa kan abinda yake yi.

Ta miƙe a hankali tana ɗaga wayar ta kai kunne “Hello Mummy..” ta faɗa tana nufar bedroom ɗinta, da gefen ido ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kai ya mayar da kansa abinda yake yi

“Ke ya zaki kirani bayan nace miki yana kusa da ni?”
Amira ta faɗa tana kulle ƙofar ɗakinta

“Shine zaki wani ce min mummy?”

“Okay so kike ya gane kece bayan ya ce min baya son mu’amalata da ke?”

Wani dogon tsaki Nuwaira ta ja “saboda gani ɓarauniya ko guba ai dole yace ki bar kulani, shi ya ma isa ya rabani da ke sai kace ba tare ya ganmu ba”

Amira ta ɗanyi dariya “bai isa ba kam”

Nuwaira tace “ah toh, yauwa kina faɗamin kika ce me ya faru jiya da daddare”

Amira ta tuntsire da dariya “akwai ki da son jin labarin other room”

Nuwaira na dariya tace “eh naji ni dai faɗamin dan Allah me ya miki kika ce…”

_______

Duk wani shiri da ya kamata Ammi da Big Daddy su mata sun mata na tafiya Lagos, wanda Faɗila tafi kowa zumuɗin zuwan Na’iman Lagos, lots of shopping sun sha shi da Fahad kusan kullum sai sun fita.

“Mami flats ɗinnan in tafi da black one ɗin ko nude?”

“Mami dake taya ta ninke kaya tace “ki tafi da duka” gyaɗa kai tayi ta ajiye takalman tana kallon Mami

“Im nervous” ta faɗa tana murza hannunta, Mami ta ajiye rigar da ta linke mata “meyasa? Ke da kika flying oceans ke kaɗai sai dan Fahad bazai samu kaiki ba sai ki ce ure nervous, ba komai lafiya zaki je abinki”

Gyaɗa kai tayi tana cigaba da haɗa kayan, amma deep down tana jinta daban kamar dai wanann tafiyar ba iya makaranta ce zata je ba kamar tafiya zatayi da yafi haka muhimmanci.

A ɗaya ɓangaren na zuciyarta kuma tunanin sadiq takeyi wanda sosai tayi mamakin rashin nemanta da yayi kuma itama ta gagara samunsa both a waya da social media handles ɗinsa abin ya fara damunta zuwa yanzu, tun da ta dawo Ninja baifi sau biyu suka yi magana da shi.

“Ki tabbatar kin saka wayarki dai a charge kuma u should park ur chargers kafin goben”

Muryar Mami ya dawo da ita daga tunanin da take, rigar hannunta da take ta juyawa ta naɗe ta saka acikin suitcase ɗinta tana gyaɗa ma Mami kai “toh Mami”

Mami na kallonta ganin kamar da abinda ke damunta tace “akwai wani abinne? Ko bakya son tafiyar ne?” Saurin girgiza kai tayi “Ah ah fa babu komai Mami”
“Okay bazaki iya faɗa min damuwarki ba kenan?” Mami ta faɗa tana jera mata jackets ɗinta “babu komai da gaske Mami, im just a litle bit worried ne na saba da ke da nan gidan yanzu xan koma sabon waje its not a big deal Allah” Shiru kawai Mami tayi ba dan ta yarda ba ta share maganar suka cigaba da abinda suke yi dan gobe jirginta na ƙarfe 11:30 ne zuwa Lagos, kasancewar ita kaɗai zata yi tafiyar yanzu banda fahad da abu ya taso masa mai muhimmanci yasa Mami take ganin kamar shine dalilin shiru shirun nata duk da ta saba da tafiya ita kaɗai, da har tace ta jira Fahad ɗin ya gama abinda yake yi sai suje amma faɗila sam taƙi, tace ai ita da Nasir zasu iya yin komai ba dole sai da Fahad ba.

Miƙewa Ammi tayi Na’ima ta ɗaga kai tana kallonta “ki tabbatar baki manta komai ba, idan kin gama haɗa kayan ki mayarda su aryan ɗakinsu tunda basu jima da baccin ba, nasan ba nisa sukayi ba ina taɓa su zasu ishe mu da darennan im not ready for that yanzunnan kaina ma ciwo yake yi” ta faɗa tana kallon su aryan dake bacci akan gadon Naiman, itama kallonsu tayi

“Ki barsu su kwana anan kawai tunda sun riga sunyi bacci, besides sai sunyi watanni yanzu basu ganni ba”

“Ai zasu sha rigima kam, hmm” Mami ta faɗa tana nufar ƙofa

“Kar dai ki Manta ki saka wayarki a charge ba sai gobe kiyita kame kame ba”

“In sha Allah Mami, kar ki manta ki sha magani” gyaɗa kai kawai Mami tayi ta ja mata ƙofar.

Mami na fita ta miƙe daga gaban kayan ta ɗauko wayarta, chats dinta da sadiq ta duba har yanzu bai hau online ba kusan sati ɗaya kenan ta sauƙe ajiyar zuciya ta ajiye wayar

Sauri sauri ta ƙarasa haɗa kayan da sun kusa gamawa dama da Mami, ta ƙarasa bakin gado ta zauna tana kallonsu aryan, takalman ƙafafunta masu taushi na bedroom ta cire ta haura saman gadon ta sa hannu ta gyara ma Aryan da Fauza kwanciyarsu kafin ta zare band ɗin da ta ɗaure gashinta ta riƙe da lips ɗinta ta saka hannayenta ta sake tattare uban gashin ta waje guda ta sa hannu ta cire band ɗin daga bakinta ta kame gashinnata duka kafin ta saka hula a kanta, sauƙa tayi daga gadon ta wuce toilet bata jima sosai ba ta fito tana gyara wandon bacci mai taushi na jikinta ta ƙarasa kan gadon ta hau ta kwanta tana karanto addu’ar bacci ta shafa a jikinta da jikinsu aryan har ta lumshe idanunta sai kuma ta buɗe da Sauri, wayarta dake gefen gadon ta ɗauka ta jona a charge ta juya kwanciyarta tana kallon ƙannen nata da sunyi nisa a baccinsu. Haka kawai ta samu kanta da kasa bacci abubuwa daban daban na yawo mata akai amma wanda yafi damunta shine rashin samun sadiq a waya kwata kwata.

Da ƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta, washegari tun da tayi asuba ta koma bacci jin kanta na ciwo, dama aryan da Fauza tun asuba suka gudu ɗakin Mami, ƙarfe 9 Mami ta tashe ta tayi wanka ta shirya sharp cikin clean white long sleeved shirt da sakakken jeans da ya mata kyau sosai, simple gold bracelet ta saka a wrist ɗinta da agogo da zobunansa kafin ta yane kanta da jersy veil tayi pinning ɗinsa da clips, fuskarta looking fresh sai glowing yake yi naturally, man baki kaɗai ta saka a lips ɗinta amma sai yayi kamar ta saka pink lipstick ne, da ƙyar Mami ta saka mata kwalli wanda ya sauya idanunta gabaɗaya ya saka haskensu sake fitowa, ta sunkuya ta saka snickers a ƙafafunta kafin ta sauƙo da suitcase ɗinta ƙasa tana rataye da designer tote bag a kafaɗarta, Mami dake bayanta tace “kici abinci kafinnnan” ɓata rai tayi zatayi magani Mami ta sa hannu tayi zipping bakinta alamun no buts, da ƙyar ta sha tea rabin cup da just 1 slice na bread, zuwa 10:30 Mami ta kaita Airport da kanta tare da su Aryan da ke ta hayaniyarsu a bayan motar.

Naima ta ƙarasa zuwa boarding lane ɗin business class ɗin da wayarta da ticket ɗinta a hannu ɗaya,tote bag ɗinta a rataye a kafaɗarta na ɗayan hannun, ta cire shades ɗin idanunta ta mayar saman kanta sassayen ƙamshinta da sai ka matso dab da ita zaka iya ji yana tashi a hankali.

Ko da ta shiga jirgin Seat 4A kusa da window shine nata, ta ƙarasa kujeran a hankali ta zauna tana tunanin sabon rayuwarta da zata fara a lagos

Jinginar da kanta tayi ta tana kallon window sai kuma ta lumshe idanun tana jin wani irin yanayi a tattare da ita, har ya zauna kujeran next to her 4B bata ma sani ba, sai da aka fara announcing saka seat belt kafin ta buɗe idanunta a hankalin ta gyaran zamanta da niyyar saka seatbelt ɗin, kallo ɗaya ya mata ya gane ta, ya ɗauke kansa yana ƙarasa saka seatbelt ɗinsa, like of all seats na cikin jirginnan he sat besides this girl? Meyasa yake ta haɗuwa da ita frequently? Ita dai ta gama saka seatbelt ɗinta ta koma ta jinginar da kanta, sake kallonta yayi is like bacci ma take ya jinginar da kansa ya lumshe idanunsa.

Har jirgin ya tashi idanunta na lumshe, basu jima sosai da tashi ba wata attendant ta ƙaraso wajensu da tray guda biyu sai da ta gaishe su kafin ta ajiye tray ɗaya a gaban Ahmad dake ɗauke da cup of black tea,fruit cup, da croissant, ta juya tana kallon Na’ima da ta buɗe idanunta tana kallonta jin tana magana, ta ƙarasa da niyyar ajiyewa Naima nata, murmushi Na’ima tayi ta miƙa hannu da niyyar karɓa tana furta “thank you” a hankali, bata san ya akayi ba hannunta yayi tripping ta ɗan buge cup na black tea ɗin cup ɗin yayi kamar zai faɗi amma sai bai faɗi ba sai dai shayin ciki ya ɗan splashing few drops a fari ƙal ɗin rigar jikinsa.
Shiru yayi yana kallonta Na’ima ta zaro idanunta ganin yanda ya ɗan ɓata masa rigarsa though its not too much amma its obvious, “oh my God, im so sorry” ta faɗa a hankali tana ƙoƙarin ɗaukan napkin daga tray ɗin, attendant ɗin ta miƙa mata ta amsa tana kallonsa ta kai napkin ɗin da niyyar goge masa, ɗauke hannunsa yayi tun kafin ma ta ɗaura napkin ɗin ”its okay” ya faɗa a dake da yasa ta tsaya da Napkin ɗin a hannunta tana kallonsa, yadda ya faɗa ɗin bai yi kama da its really okay ɗin ba, ta kasa daina kallonsa, kallo take masa irinna na sanka a wani waje amma na kasa tunawa, ɗayan hannunsa ya kai ya ɗau wani napkin ɗin a hankali ya hau goge inda ya ɓaci a shirt ɗin nasa.

A hankali ta mayar da na hannunta ta ajiye, bayan few seconds ta sake kallonsa ganin har sannan goge rigar yake yi yasa tace “dan Allah kayi hakuri, am really very sorry” ɗan kallonta yayi amma baice komai ba, itama sai kawai tayi shiru, ya ajiye napkin ɗin ya zare seat belt ɗinsa ya miƙe tsaye, zatayi magana ya kalleta a hankali yace “save it, kullum ne kike mistake sannan kice sorry? Its ur hubby kiyi abu sannan ki dawo ki bada hakuri, i can see that” daga haka ya juya ya nufi restroom da hannunsa ɗaya a aljihu, attendant ɗin ta matsa gefe da sauri har ya wuce, ita dai Na’ima ta mayarda kanta ta jinginar tana riƙe da tray ɗin, “kullum take laifi tace ayi haƙuri kamar ya?” Saurin buɗe idanunta tayi tuno inda ta san fuskarsa da tayi, tabbass shine wanda ta ture a Airport rannan ikon Allah, shi kuma kullum a filin jirgi suke haɗuwa kuma kullum suka haɗu sai ta masa laifi, bata san sanda ta ɗanyi murmushi ba tuno abinda yace mata rannan wai she should behave like shes in public, gashi yau ma kuma ta sake wani laifin, no wonder he couldnt talk for a moment.

Tana ganin yana dawowa ta rufe fuskarta da gyalenta, shima bai kulata ba ya zauna a kujerarsa kamar bai san da zamanta ba. Ko kallon direction ɗinta bai sake yi ba har jirginsu ya sauƙa a Lagos.

Tana kallonsa ta gefen ido har yayi unbuckling seatbelt ɗinsa ya miƙe ya ɗau briefcase ɗinsa yabi bayan ʼyan sauƙa a jirgin, itama miƙewa tayi tana shaqan ƙamshinsa da ya bar mata mai azabar daɗi ta rataya jakarta ta bi bayansa.

A arrival hall driver Nasir dake jiranta da sign mai rubuce da sunanta a jiki yana ganin ta nufosa ya ƙaraso da sauri yana amsar jakarta, “sannu da zuwa hajiaa, small madam, Madam faɗila dey wait for u for house”

“Thank you” ta faɗa a hankali tana murmushi

Ya buɗe mata bayan motar ta shiga ya rufe motar ya zaga ya shiga mazaunin driver ya tada motar suka bar Airport ɗin.

Hankalinta ta mayar window tana kallon the beautiful city of Lagos har suka iso gidan Faɗila dake lekki phase 1, Mai gadi ya buɗe musu makeken gate ɗin, driver ya shigar da motar zuwa parking space, yana gama parking kafin ya sauƙo ma ta buɗe ta sauƙo a motar tana ƙare ma gidan kallo, it seemed different dan lokacin da suka kawo ta kwata kwata bata yima gidan nutsattsen kallo irin wannan ba, ta ɗan sunkuya cikin motar ta ɗauko jakarta, dai dai lokacin ta jiyo muryar Faɗila

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved