⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Nashiga Aljanna Book 2 Hausa Novels

Download Page: Go to Download Page
License: CC BY-NC-ND

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  1. NANA FIRDAUSI

    Bismillahi Rahmanir Rahim

    Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukaƙin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah da yabani baiwar rubututa littafai daban daban Ina ƙara godema Allah ????, Allah ka ƙaramin baiwa haƙuri dama juriya haɗida lafiya musamman ta idanuwana AMEEN YA ALLAH_

    *Ina godiya Kuma Ina ƙara godemuku MASOYANA Adik Inda kuke inajin daɗin nuna soyayyarku gareni dama littafaina Ina godiya Sosai ???? Allah ya ƙara Muna haƙuri da juna Ina sonku Adik indakuke Ni takuce SHA’AWANATU FARUK DIGGI ???? da bazarku nake rawa Akoda yaushe*

    BY
    SHA’AWANATU FARUK DIGGI✍️
    WhatsApp????

    01

    Wata yarinya ce zaune ta yi tagumi ta na tuninan ma fita saboda yunwa take ji sosai ta na nan ta na tunanin ta jiyo muryar wata matashiyar mata ta na bala’i .

    “Ke shegiya mayya mai baƙin hali ma za ki ta shi kije kiɗebo min ruwa wallahi ko na karyaki”, cewar matashiyar matar.

    “Inna wallahi yunwa nake ji sosai dan Allah kibani abinci na Sannan naje na ɗebo ruwan”, cewar yarinyar hawaye cike a idanuwan ta .

    “Wallahi ba za ki ci abincin nan ba, sai kin ɗebo ruwan idan kin iya ki mutu a can shegiya mayya mai baƙin hali duk sa annin ki son yi aure amma ke shiru.

    Haka yarinyar ta ta shi tana hawaye abin tausayi ta ɗauki bokitin ruwan..

    Tana tafiya tana rangaji har ta isa rafin, ta ɗeba ruwan har ta gama ji dan ruwan, amma abin tausayi tana gama ji dan ruwan aka saka ta wanki, ba yadda ta iya haka ta yi wankin har ta gama tana gamawa, wata yarinya ta fito da gudu ..

    “Laaaa Inna zoki ga Nana wankin bai yi fari ba”, cewar yarinyar yar shekara goma10 & 11..

    “Ki barta wallahi sai kin sake wankin nan shegiya da ta yi gadon maita a gun mahaifiyarta cewar Innar ta su.”

    “Inna wallahi idan kika kashe ta ke ƴan sanda zasu kama, kina jin tana Kiran yunwa take ji amma kin wani shareta, Allah ya sa ta mutu ƴan sanda sutafi da ke ko zamu huta”, cewar yarinyar ta zata kai sa’ar Nana din ..

    “Toh muna fuka ayer ɗin ki wallahi sai dai ƴan sandar sukama uban ki ..

    Ta ɗauki abincin tabbata ta ci Sannan ta sake wankin .

    Wani ma dai dai cin gida ne amma fa gidan ya haɗu sosai.

    “Nacewa Firdausi barana shiga gidan naga yanda yake sai na Baku labarin ..

    Wow gida ne ma sha allah gidan ya haɗu sosai komai na falon green ne kai komai na falon ya yi sosai mai karatu ka canka kyawon gidan .

    Toh mu je cikin bedroom ne toh shi ke nan mu je zuwa .

    Wow ɗakuna ne a cikin falon toh wane zamu shiga ne mu runtuba kawai ..

    Wow Ma sha allah wani bedroom ne ciki da falo da bathroom dakin brown ne amma ɗakin ya yi kyau sosai sai dai muce ma sha allah.

    Wani ƙyaƙƙyawan saurayi ne ɗaure da towel, da alama da ga wanka ya fito jikin shi sai fitar da ruwa yake, wani towel a hannun shi yana tsane gashin kansa ni kam ganin kyawun saurayin sai da na suma ..

    Mai ya sha fa ajikin shi Sannan ya je wardrob sai da narike bakina ganin kayan dake cikin ta ƙananan kaya yaɗauka ya saka wow ma sha allah, tsarki yatabbata ga Allah da ya yi wannan bawan nashi yanzun kyawun shi ya fito fili saurayin dogone sosai, fari ne sosai, jikin shi dai dai shi, shi ba mai ƙiba ba shi ba siriri ba fuskar nan na dauke da saje baƙi wulin, ga shin kan sa ya ji kyara sosai yakwanta kamar gashin turawa kai Shima kan shi kamar mahes babu dan andia ..

    Hummm wai ko dai ko dai amma saurayi na ya fi shi kyau ???????????? .

    Fita ya yi daga ɗakin bayan ya fe she turaruka ma su tsadar gaske ta fiya yake kamar ba ya son taka ƙasa wani ɗaki ya shiga wata mata ce a ciki itama ƙyaƙƙyawar gaske ce farace sasai.

    “Assalamualaikim yake Ammina.”

    “Waalaikamussalam my babana fatan katashi lafiya?” cewar Ammin tasa ..

    “Ammina ina kwana?.”

    “Lafiya qalau alhmdllh my son?.”

    “Babana wai ina maganar auran shi ke nan yanzun fa sa wa zaka yi?”.

    “Hummm Ammina kenan ni bazan auri mayaudariya azzaluma ba, zan fita a ƙauye nasami mace mai hankali da natsuwa gaskiya matan birnin nan basa son mutum tsakani da Allah sai yanada ƙudi saboda haka dan Allah Ammina kibari na je qauye.”

    “Tabdijam qauye fa ka ce bazai wuba, ƴar ƙauye zaka kawo min a cikin gida toh baka isa bah babana.”

    “Amma Ammi kin san wannan ba sona take ba ƙudi na take so.”

    “Duk da haka sai dai Ka ne mi mata a garin Nan.”

    “Ammi ki yi haƙuri zanyi miki biyayya kamar yanda kike so, amma ina son ki barni na je na nemi wacce nake so, ammi mace 3 kenan kina hadani da ita, amma daga karshe suci amanarki, saboda haka dan Allah kiduba girman Allah ammi kabari na je please ????.”

    “Hummm yanzun idan ka tafi wace sana’ar zaka yi.”

    “Ammi zanyi sana’ar tuka tuka yake ko mi?, mene ne sunan shi Ammi?.”

    “Me kake nufi kana nufin baro zaka yi ja”.

    “Yauwa shi ne ammi kinga aii gara tura baron ko..

    “Hummm baro zaka yi ja toh Allah ya bada sa’a Allah ya sa ayi a sa’a.”

    “Ameen ya Allah ???? yanzun Ammi zan wuce gobe dan wallahi na gaji da zama a garin nan.”

    “Toh badai gobe ba kam sai dai jibi, ina zuwa naga kamar fita za kayi.”

    “Eh Ammi zan je gidan su Sadiq ne, amma Ammi dan Allah ki yi hakuri kibari na je ƙauyen gobe idan Allah yakaimu please.”

    “Hummm ba dai gobe ba ta shi zuwa gidan su Sadiq din idan ka je ina gaida mamar ku.”

    “Tam zata ji in sha Allah amma dan Allah mama ki yi hakuri kibar ni na je goben please mana.”

    “Kai babana me ya sa idan kamaƙalewa a bu baka ji baka gani shi ke nan Allah yatsare hanya Allah yatashe mu lpy.”

    “Ta shi ya yi ya rungume Amminshi yana dariyar da yalotsar da dimple din shi sai yakara kyau kamar na sace shi na gudu.”

    “Toh ta shi ka je sai kadawo.”

    “Toh Ammina na gode sosai, sai na dawo zan je.”

    Ta shi ya yi yana tafiya tamkar dan sarki yakama hanyar gidan su Sadiq din…

    Dama mai gadi yasan da shi kawai gidan yabude ma sa dan yasan wankan mota sai faruq …

    Yana fakin yagaisa da mai gadin Sannan ya shiga gidan yana shiga ya ga wata matashiyar mata, da wata yarinya su na fira da alama ƙanwar sadiq din ce….

    “Assalamualaikum mama barka da safiya kintashi lafiya?.”

    “Waalaikamussalam lafiya qlau alhamdulillah Faruk fatan katashi lafiya?.”

    “Lafiya qalau alhamdulillah, Mama sadiq din fa?.”

    “Yana nan ciki matar ku ce ba lafiya shi ne yakecan.”

    “Yaya ina kwana antashi?.”

    “Lafiya kawai yace ma ta..

    “Kiramin Sadiq din.”

    “Wai ni kam Faruk ya zancen auran naka ne.”

    Sai da yanisa ya saukar da numfashi mai nauyi sannan ya ce .

    “hummm Mama babu shi, saboda ita ma bani take so ba ƙudi na take so, ni kam narasa me ya sa take son yimin aure saikace Wata mace.”

    “Ba haka ba ne Faruk duk uwa nason ta ga ɗan ta ya yi aure ya haihu ta ga jikokin ta, amma kuna ganin kamar muna takura maku ne, toh ba haka ba ne.”

    “Hummm toh shi ke nan Mama gobe ma zanje ƙauye neman matar aure in sha allah.”

    “Ƙauye fa Faruk anya kuwa zaka iya rayuwar qauye.”

    “Wallahi Mama tunanin dana yi na je ƙauyen a can zan sami mai sona tsakani da Allah, saboda su ba su sama da rayuwar ƙarya ba kamar ƴan birni.”

    “Toh yanzun idan kaje wace sana’ar zaka yi Faruk?.”

    “Mama cewa na yi zanyi jan baro ne…

    “Hhhhhhhhhhh chapp my friend kai ne zaka iya tuƙa baro hhhhhhh, amma dai fada kake yi kawai ko abokina?”, cewar Sadiq da duk abin da suke cewa yana ji…

    “Mtsss kai fa ɗan iska ne wallahi ya za ka min dariya banza kawai”, cewar Faruk saboda ya ji haushen dariyar da sadiq din ya yi mai…

    “Kai Sadiq bafana son wulakanci ya za kayi ma sa dariya.”

    “Abokina ka yi hakuri amma wallahi sai nake ganin kamar ba za ka iya ba, baro fa ka san yanda jan baro yake kuwa.”

    “Mtsss Mama zan wuce gobe idan Allah yakaimu, idan lokaci ya bari zan biyo mu yi ban kwana sai na wuce.”

    “Toh aii bamu ƙarasa maganar ba.”

    “Hummm Mama ki yi hakuri wallahi bana jin dadi ne.”

    “Ko dai dariyar Sadiq din ce taɓata maka rai Faruk?.”

    “Hummm a a Mama kawai bana jin daɗi yanzun.”

    “Toh yau ba za ka sha komai ba?.”

    “A a Mama na gode sai anjima.”

    “Abokina ka yi hakuri mana dan Allah na san na ɓata maka rai dan Allah ka yi hakuri muyi maganar fahimta.”

    “Toh idan ba shi ne ya ɓata maka rai ba ka yi ma sa sallama.”

    “Mama me ya sa sai na ma sa sallama ne?.”

    “Shine saidar baka fushi da shi.”

    “Ok toh shi ke nan sai anjima zan wuce gida.”

    “Toh mu je narika ka a motar.”

    “Hummm kai abokina Allah yabada sa’a Allah ya sa asami mai hankali.”

    “Yana shiga motar yafige ta da gudun tsiya yabar gidan saboda bakaramin ɓaci ran shi ya yi bah.”

    “Har ya tafi ne.”

    “Aii bai tsaya ba yafigi motar a tsiyace ya bar gidan nan.”

    “Wallahi naji figar motar ta sa Allah yatsare shi dai, ni wallahi haka nake ganin shi kamar mai aljanu wani lokacin.”

    “Hhhhhhhh kai Mama aljanu Kuma?, lafiya qalau yake.”

    “Toh yanzun wazai duba maka matar taka ne ?.”

    “Hummm zan je asibiti in sha allah zai duba ta.”

    “Amma ai gobe ba ya zuwa asibiti goben ne fa zai wuce.”

    “Bara na yi ma sa magana maybe zai duba min ita.”

    “Tana gama wanki taje ta yi wanke wanke ta yi sharan gida Sannan taje takwanta sai baccin wahala.”

    Marece na yi ta ta shi taje ta daura sanwan abinci, ga wutar tabata wahala sosai da haka har ta gama aikin.

    “Inna nifa yunwa nake ji ina abinci na ko shegiyar can bata gama ba ne?.”

    “Tagama mana ga shi nan kici idan ya yi raguwar sai kibata ragin naki…

    “Inna meki ke nufi ba ki bata abincin ta ba wallahi Allah ya sa idan kikaci hakkin ta yamaƙale miki a wuya tana maganar tana tam nar cingam kamar bakin ta zai cire…

    “Shegiyar banza ƴar iska nizaki yiwa addu’ar abinci yamaƙale min a wuya ahher ɗin ki wallahi shegiya mai kan ƙadan gare…

    “Eh naji dai Inna wallahi sai kin bata abincin ta ehhee…

    Ita dai Nana tana jin su batace masu komai ba…

    Ta shi yarinyar ta yi zata taje daukowa Nana abincin, kawai Innar tasu ta tureta ta fadi a ƙasa timm.

    “Ke Asama wallahi ki kiyayeni ni ba mahaifiyar ki bace za ki fifita wa ta a kai na.”

    Ta shi ta yi taje ta ɗauko abincin ga ba ki ɗaya ta kaiwa Nana…

    Karbi kici idan kika rage kimin magana idan du ka za ki cinye shi toh canye.

    “Kam bala’i ke mahaukaciyar inace wai ni ba mahaifiyar ki bace za ki riƙa yimin wulakancin, wallahi zan tsine miki kibi duniya.”

    “Humm ai Inna ko yanzun kika tsine min bazai daman ba dan ko yanzun wannan sana’ar da kika azani akai ba mai kyau bace, saboda haka ko tsine min kikayi wallahi bazai daman ba.”

    “Lallai Asama kin girma toh wallahi ni da kika raina gata nayi miki.”

    “Faruk ba abinda xai je da shi saboda ba wankan kaya masu kyau xai yi ba saboda haka gobe kawai yake jira ta yi.”

    “Ringing wayar shi tafara yi tana neman agaji sunan da ya bayyana a screen din wayar shine yasaka shi murmusawa MY LOVELY FRIEND nagani a screen din wayar tasa sai da kiran yakusa yankewa ya daga ..

    “Assalamualaikum my friend cewar Sadiq…

    “Hello my friend kana jina kuwa?” cewar Sadiq..

    Faruk najin shi ya yi ma sa banza sai da ya ga dama Sannan ya yi magana…

    “Waalaikamussalam?”cewae Faruk…

    “Yanzun dan Allah my man kana jina amma kamin banza.”

    “Anyi maka banza me za ka yi ni kafadi maganar ka ko na yanke Kiran.”

    “Alhamdulillahi tun da zaka tsaya ka ji mizan ce, dama madam ba lafiya shi ya sa nake son kazo kaduba min ita.”

    “Ok kana nufin ni zan je gidan ka naduba matarka ko toh kazauna har nazo.”

    NANA FIRDAUSI

    BY
    SHA’AWANATU FARUK DIGGI
    WhatsApp numbe ☎️

    02

    Ba yanda Sadiq ya iya haka ya dauki Fatima zuwa gidan su Faruk ɗin..

    Yana shiga gidan ya ci karo da Faruk a falo yana dannar laptop din shi…

    “Assalamualaikum my man gamu munzo sai ka duba min matata.”

    “Waalaikamussalam wallahi idan ka ishe ni tafiya ta zan yi, idan a kaƙi dubata ɗin mai zaka yi banza kawai.”

    “Eh na ji dai dan Allah kaduba min ita saboda naga taji jiki sosai.”

    “Mtsss meke damunta?.”

    “Tana zazzaɓi ne.”

    “Ok kai ne bakin ta kenan?.”

    “A a wallahi toh ke sai ki yi bayani mana…

    “Ina jin ta shin zuciya, da zazzaɓi, da kasala, sannan bana son cin abinci, saboda warin shi nake ji sosai.”

    “Shi ke nan ko da wani abun ne.”

    “A a shi ke nan ne.”

    “Congratulations nataya ki murnar samun ƙaruwa Allah yaraba lafiya.”

    “Da gaske abokina tana da ciki.”

    ” Ban sa ni ba banza kawai, idan son sa ni kake yi sai ka aunata ka ga meke damunta, ya faɗa cikin fushi

    “Yeeeee abokana Dr Faruk Allah ya saka da alkhairi na gode sosai.”

    Yana rungume da shi ne yana magana har da hawayen shi, dan ba ƙaramin daɗi ya ji ba.

    “Kai dan iska mene ne abun kuka anan?, aii abin murna ne ba kuka ba.”

    “Wai mene ne nake ji haka cewar Ammi tana leƙowa….

    “A a kune yau a gidan ba gaisuwa, yau ba ta ni a ke yi ba kenan, ai da nasami jika da ba haka ba idan uwayen sun gujeni shi kam bazai guje matar shi ba.” cewar Ammi…

    “Ammi kitaya mu murnar samon baby cewar Faruk…

    “To ma sha allah, Allah yaraba lapiya Fatima, amma na ji daɗi sosai wallahi, yanzun kam kun girma idan zaku je ku yi aure tun yaranku basu ci abinci aure ku ba toh, idan zama zaku yi ga shimfiɗa ku zauna.”

    “Ammi kin san aure lokaci ne idan lokaci ya yi ko bamu shirya ba sai anyi, dan haka dan Allah ki yi hakuri.”

    “Yanzun dai mekike so na dafa miki?, saboda na san mace mai ciki akwae kwaɗayi sosai…

    “Ammi kibari naje na ɗaura da kai na aii zan iya, saboda yanzun na ji sauƙi ba kamar da ba.”

    “A a ki zauna ki huta abin ki mai zan girka maki?.”

    “Ammi faten geru nake so Wanda ya ji man shanu da yaji.”

    “Ammi kada kibata yajin kawai kisaka ma ta man shanun.” cewar faruq….

    “Atam lallai kam mai danyen ciki baya cin yaji..

    Ammi ayinan da Fatima ayinan da ita su na nan har 9 na dare sannan suka tafi gidan, amma ba dan ta su ba.

    Shima faruq din kwanciya ya yi yana zumuɗin sapiya tawaye.

    Asuba ta gari faruq

    “A haka ne ake yiwa mutum gata Allah ya kiyaye wallahi, ni wannan gatan bata yi min ba.”

    “Shegiyar banza kawai ƴar iska niza ki wa rashin kunya.”

    Da haka dai har dare ya yi suka je suka kwanta…

    “NANA dai tanajin su ta yi shiru abin ta. ita ma kwanciyar ta yi…

    “Asuba tagari Nana

    Kiraye kirayen sallah ne ya tada Faruk da addu’a ɗauke a bakin shi, toilet ya shiga dan ɗauro alwala, masallaci ya nufa yana tafiya kamar wanda bacci bai sake shi ba.

    Ammi ta ji fitar shi dan haka ita ma alwala ta yi sannan ta gabatar da sallah, tana gama sallah addu’a ta yi sosai har Faruk ta yiwa addu’a sosai dan samun nasara.”

    Nana cikin bacci ta ji an watsa ma ta wani abu mai shegen sanyi a ruɗe ta ta shi dan ganin mene ne, ruwa ta gani, ɗaga kan da za ta yi sai ganin Inna ta yi fuskar nan kamar gwaggon biri.

    “Idan ba ki ta shi ba wallahi sai naci ubanki shegiya mayya mai mugun ga do, ni waɗan nan idanun naki sai na lallata su idan ba ki daina kallo da su ba, kuma ki ta shi zuwa tallah na tun kan mutane su watse, wallahi da bazan yi asara ba, sai kin biya ni kuɗi na.”

    “To Inna ban yi sallah dan Allah ki bari na yi wallahi idan nata fi sai in makara sosai.”

    “To ba za ki yi sallar ba a gidan nan sai kin yi tallar kin gama sannan ki yi sallar daga ba ya shegiya ke nake jira dan ubanki.”

    Haka ta shi ba dan taso ba sai dan tsoron duka, ta ɗauki tallar ta biya gidan wata ƙawarta dan su tafi tallah tare, can ta tsaya ta yi sallah sannan suka tafi.

    Kasuwa suka nufa suna tafiya suna fira idan Nana ta yi dariya ba zaka ce ita bace duk da wannan wahalar da take ciki, amma hauron ta farare ne tass abin su.

    “Nanata… Nanata…. Nanata tsaya ki ji dan Allah, tun ɗazun nake ina jiranki shine za ki biyo ki wuce ba ki kula ni ba.”

    “Ban kula ba ne yi hakuri kuma sauri nake yi yanzun haka na kusa makara idan kasuwar zaka je kazo mu je dan Allah bana son tsayawa kan hanya.”

    “To shi ke nan mu je ɗin.”

    Suna tafiya suna fira da shi har suka isa kasuwa bisa wani icce suka zauna su uku.

    “Nuratu kin san wai Nura ɗan sarki ya ce yana sona amma wallahi ni bana son shi, son nake naje birni na yi karatu sosai, idan naga ƴan birnin gidan Inna Hajju, Wallahi kamar kar su daina magana yanzun na idan na fita daga nan gidan zan je in leƙe sannan na yi gida.”

    “Mtsww ni kin san me nake so?.”

    “A a sai kin faɗa”.

    “So nake na auri miji ɗan birni mai kuɗi ko dukana yake yasin sai na zauna daram.”

    “Chapp ni dai wallahi a a doka fa kika ce?.”

    “Eh .”

    “Gaskiya ni kam bana son irin mijin nan gara mai sonka Inna ta ce yafi yi maka abin da kake so, amma idan baya son ka sai dukan ka yake.”

    “Ke ce Innar zata faɗawa haka?.”

    “Rufamin asiri na ji dai tana faɗawa Asama.”

    “Faruk ka riƙe imanin ka, ka riƙe sanin ya kamatar ka, ka riƙe tarbiyyar ka, ka riƙe tarbiyyar, ka riƙe tarbiyyar, ka riƙe kanka da ruɗin zuciya, Faruk matan ƙauye tabbas, basa ɗai da matan birnin, sai dai ko ina akwai na gari akwai ɓata gari, Allah ya haɗa ka da ta gari, abokiyar rayuwa, kuma uwar ƴaƴanka, Faruk Allah ya tsare min kai duniya da lahira, idan ka je dan Allah ka riƙa kirana saboda na ji yanda katashi da kwananka Faruk bana son na raka kamar yadda na rasa mahaifinka, ina son ka Faruk ina son ka Faruk…….” Kuka taci ƙarfin ta dan haka Faruk ya tsayar da ita dan ta sa mu nutsuwa.

    “Ammi kar ki damu ina tare dake rana ɗaya ba zan ƙi kiranki ba in sha Allah, ina son ki kawai tafiyar nan kamar ta zamamin dole haka nake nima kamar kar in je, saboda bana son kina shiga damuwa Ammi.”

    “Hummm kar ka ka tafi kawai Allah ya maka albarka Babana.”

    “Ameen ya Allah my Ammina.”

    “To yanzun tafiyar za ka yi ko sai anjima.”

    “A a sai na je gidan Mama sannan zan shirya sai in fuce.”

    Ok toh Babana Allah ya tsaremin kai

    “Ameen ya Allah Ammina.”

    NANA FIRDAUSI

    SHA’AWANATU FARUK DIGGI✍️
    whatpp number ☎️

    03

    Fira suka yi sosai tana tunatar da shi rayuwa da ruɗin zuciya, sun jima sosai sannan daga baya, ya ce zai je wajen Mama ya yi ma ta Sallama, ba dan Ammi ta so ba haka ta haƙura ta yi ma sa a dawo lafiya.

    Mota ya shiga yana tafiya a hankali kamar ba ya son yin driving, yana cikin driving ne ya hangi mai sai da apple, tsayawa ya yi dan ya siyawa Maman Sadiq, siya ya yi da yawa dan shima zai je da ragowar, sannan ya kai gidan hon ya yi a ka buɗe ma sa gidan ya cilla hancin motar shi, parking ya yi sannan ya fito ya shiga gidan.

    A zaune ya samu Sadiq da Fatima da ƙanwar Sadiq .

    “Assalamu alaikum.”

    “Waalaikamus salam.”

    “Yaya sannu da zuwa.”

    “Yauwa sannu da gida Farha?.”

    “Yauwa Yaya.”

    “Ina wuni Yaya Faruk.”

    “Lafiya ƙalau ya jikinki?.”

    “Da sauƙi sosai, sai dai ina jin ciwon ciki kuma yanzun.”

    “Ayya da sannu da zai daina in sha Allah.”

    “To na gode sosai.”

    “Ba komai.”

    “Ikon Allah wai babu faɗa meya kawo gaba kuma.”

    “Mtsww Farha ina Mama?.”

    “Yaya tana cikin kitchen.”

    Tafiya ya yi niyar yi amma Fatima ta tsaida shi da faɗin.

    “Yaya dan Allah ka yi hakuri komai ya yi maka, amma gaskiya ba ya da gaskiya dan Allah ka yi hakuri, ya min bayanin abin da ya haɗa ku Please Yaya dan Allah.”

    “Fatima bana son kina shiga tsakani na da shi ki bar shi, abin da ya min ya ɓata min rai sosai fa.”

    “Eh Yaya na sa ni amma dan Allah ka yi hakuri.”

    “Shi ke nan na haƙura, amma idan ya sa ke gaya min wannan maganar sai mun fi shekara bamu yi magana.”

    Hahaha ???? dariya Fatima da Farha suka yi dan maganarsa dariya ta ba su.

    “Hakan ba zata ƙara faruwa ba in sha Allah.”

    “Kiran Mama ke.”

    “To Yaya”, da sauri ta tashi dan ta san halin shi sai ya maketa ba ruwan shi.

    Tare suka fito da Mama.

    “A a to ba dai tafiyar ba ce tun yanzun?.”

    “Eh tafiyar ce Mama, ina kwana?.”

    “Lafiya ƙalau.”

    “Amma gaskiya Baban Amminsa ka yi sauri ai na yi tunanin ko ka bari sai zuwa azahar.”

    Murmushi ya yi dan ya san zolayar shi ne take yi wai Baban Ammin shi.

    “Au shiru kake min ko?.”

    “A a Mama yanzun zan tafi, kawai na zo mu gaisa ne kuma naga ya jikinta.”

    Sadiq ta shi ya yi da in da yake zaune ya koma in da Faruk ya zauna.

    “Haba abokina dan Allah ka bari zuwa anjima da azahar sannan ka yi tafiyarka nima zan raka ka har ƙauyen da zaka je, amma ka bari anjima.”

    “Idan kaga na bar tafiyar nan zuwa azahar yasin ba ni ba ne.”

    “To shi ke nan abokina Allah ya tsare hanya amma zamu riƙa yin waya ko? Dan na san da ita zaka je.”

    “Eh dan gaskiya bana iya tsama da ƙaramar waya, amma zan bar saura a gida, sai na je da ɗaya.”

    “To shi ke nan Allah ya tsare hanya.”

    “Ameen.”

    “Kun gama ne?.”

    Hahaha ???? “eh Mama mun gama”, Faruk ya bata amsa cikin dariya.

    “To shi ke nan ka saurareni da kunnen basira Faruk, ka riƙe mutuncin ka, ka riƙe tarbiyyar da mahaifiyarka ta baka tun kana shan nono, Faruk Amminka bata son rabuwa da kai ko karatun da ta turaka ba yanda ta iya ne, dole ka sami ilimin boko da na islamiyya, Faruk ka riƙe addu’a, ka riƙa addu’a, ka riƙa addu’a, da yin sallah ta farillah,da na fila, kar matan ƙauye su ruɗeka har ka kauce hanyar Allah, Faruk Allah ya kare ka da maƙiyanka masu sun ganin bayanka, Allah ya baka mata ta gari, Allah ya haɗa ka da alkairi ya kare da sharri a duk in da yake.”

    “In sha Allah Mama na gode sosai zan kiyaye in sha Allah ba zan bar wani gurbi da zasu yi amfani da shi dan cutar da ni ba.”

    “To shi ke nan Allah ya muku albarka.”

    “Ameen ya Allah Mama mun gode sosai.”

    “Yaya Allah ya baka mata kamar ni.”

    “Hahaha ameen Ya Allah.”

    “Laaaa Yaya kana son irina.”

    “Eh mana ai kin fi ɗan iskan nan hankali.”

    “Yeee kin ji aunty ai dama na faɗa miki wallahi nafi Yaya hankali, amma kika ce wai a a .”

    Dariya kuwa ya yi dan yarantar Farha abin birgewa ne.

    “Mama zan wuce yanzun.”

    “To Faruk Allah ya tsare hanya.”

    “Ameen ya Allah.”

    “Allah ya kai ka lafiya Yaya.”

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum.”

    Ta shi ya yi dan wucewa zai yi, Sadiq ya raka shi har mota sannan suka yi ban kwana idanun Sadiq jawur shi ma Faruk ɗin bai ji daɗi ba, amma shi ai ya sa ba da tafiya.

    Shiga mota ya yi da gudun tsiya ya bar gidan, shi dai idan na fuskanta yanayin tukin shine a haka.

    Mantawa ya yi da apple ɗin da ya siyawa Mama, dan haka da abin shi ya koma gida.

    Shiga gidan ya yi sannan ya yi parking bai ɗauki apple ɗin ba kuma ya shige cikin gidan.

    Falo ya tarar da Amminshi zaune duk jikinta ba daɗi.

    “Ammina mai ya faruwa ne naganki haka kamar ba kya jin daɗi.”

    “A a Babana lafiyata ƙalau kawai ina tunanin tafiyar nan taka ce, kuma ba zaka daina ta ba ko?.”

    “Ammi dan Allah ki sa ke ranki ba abin da zai faru fa kawai addu’ar ku nake so, in sha Allah ba zan bar tarbiyyar da kika bani ta yi kuka ba in dai ina raye.”

    “To shi ke nan babana je ka shirya kazo ka tafi, Allah ya maka albarka.”

    “Ameen ya Allah Ammina na gode da addu’ar da kuke min ke da Mama Allah ya saka da alkairi.”

    “Ba komai ai kai ɗan mune dan haka dole zamu yi maka addu’a, kuma na ji su Falmata sun ce za su dawo gidan nan da zama, saboda Yarinyarta take son ta yi karatu a garin nan.”

    “Ba komai sai sun zo fatan alkairi zamanki da su Ammina.”

    “Ameen ya Allah.”

    “Bara na je na shirya kar lokaci ya ƙure min.”

    “To”, kawai ta ce dan ba abin da za ta yi da zai hana ma sa wannan tafiyar.

    Tafiya ya fa ra yi cikin ƙasaita kamar wani ɗan sarki ya shiga part ɗin shi, ita dai Ammi kawai ido ta bi shi da shi, dan ba ƙaramin kama ya ke da mahaifinshi ba.

    Zama ya yi kan kujerar ɗakin shi dafe kanshi ya yi dan ba ya son ran mahaifiyar shi ya ɓaci akan tafiyar shi amma ba yanda ya iya, tunanin shi wai mai zai sa su Aunty Falmata zuwa gidan su bayan sun raba gida, to mai zai kawo su nasu gidan, da dai tunanin nan har ya haɗa tufafin shi da zai je da su.

    Tunanin tafiyar ta shi, shima yake yi dan yana son Ammin shi amma ba yanda zai yi tun da ta matsa ma sa cewa ita aure ta ke son ya yi, shi ma kullum maganar shi ɗaya wai shi yaro ne bai isa aure, sai yanzun da ya ga ba sarki sai Allah, sannan ya ce zai yi auran.

    Cikin wata jika ya saka kayan shi mai ɗaukan kala takwas, ya saka kayan nashi sannan ya fito dan ban kwana da Ammin shi.

    “Ammina na shirya zan tafi.”

    Gaban ta ya yi mummunar faɗuwa, gani take kamar idan ya tafi ba zai dawo ba.

    “To babana sai ka dawo dan Allah ka riƙa barin wayar ka a kunne, idan mutane suka kiraka su ji ta a kunne ka ji ɗan albarka.”

    “To Ammi in sha Allah ba zan bari ta mutu ba zan siya Powa bank in sha Allah.”

    “To Allah ya tsare hanya.” hawaye ne suka saukowa Ammi ta yi sauri ta share su kamin ya gani.

    shi kuma ya ri ga ya gani kawai ya kawar da kai ne tun da bata son ya gani.

    NANA FIRDAUSI

    Sha’awanatu Faruk diggi ✍️
    Wtspp☎️☎️

    NANA FIRDAUSI

    04

    “Ammi sai mun yi waya.”, ya kama hanyar fita dan ya san idan ya biyewa Ammi sai ya kwana bai fita ba.

    Da “to”, kawai ta iya amsa ma sa

    Bai je da mota ba da ƙafa ya fita bakin titin gidansu, wani ne ya gan shi a tsaye ya zo in da yake ya ce.

    “Ranka ya daɗe ina zuwa haka ga abu a hannunka, kamar me shirin barin gari?.”

    “Eh tafiya zan yi”, ya ba shi amsa cikin ƙosawa da tambaya.

    “Amma…..” Hunnu Faruk ya ɗaga mai hakan ya sa ya yi shiru.

    “Yi hakuri ranka ya daɗe mu je na rage maka hanya.”

    “Ok”, haka kawai ya faɗa.

    Shiga motar ya yi ya zauna, amma bai yi magana saboda shi ma bai san ina zai je ba.

    “Ranka ya daɗe ina muka nufa ne?, naga sai tafiya muke yi amma baka ce ga in da zaka je ba.”

    “Ban sani ba nima, kawai ka samu wuri ka ajiye ni zan ƙarasa da kaina.”

    “Ranka ya daɗe ka faɗa min nima zan taimaka maka in sha Allah.”

    “Nura nima ban san in da na nufa ba kawai na san ina son zuwa ƙauye ne.”

    “Ƙauye kuma ranka ya daɗe?.”

    “Eh.”

    “To shi ke nan barana kai ka wani ƙauye na nan kusa da mu, amma da nisa gaskiya.”

    “Ok nawa zan biya ka.”

    “Haba ranka ya daɗe kuɗi kake tunanin ka bani, ai abin da ka min ya fi wanda zan maka.”

    “To na gode mu je kawai.”

    Tafiya suka ci gaba da yi, sun yi tafiya mai nisan gaske sannan suka ƙarasa in da ƙauyen, amma mota bata shiga cikin ƙauye sai an yi tafiya zuwa cikin sa, dan haka Nura ya ce.

    “Ranka ya daɗe sai mun shiga da ƙafa saboda ba hanyar mota.”

    “Da ƙafa kuma wannan wane irin ƙauye ne kuma?.”

    “Hahaha ranka ya daɗe ka yi hakuri ai haka ƙauye yake wani ƙauyen sai a hankali amma wani kam gaskiya lafiya ƙalau yake, saboda akwai hanya amma wannan shi ne na kusa damu.”

    “Ok to ka yi tafiyar ka kawai ni zan shiga da kaina, amma ina fatan wannan wajen ne zan bi kar na je na ɓace.”

    Hahaha ????”Haba ranka ya daɗe ɓacewa kuma a yankin nan kam ai duk in da ka shiga ba zaka ɓace ba.”

    “To shi ke nan godiya nake Nura.”

    “Ba komai.”

    “Sai anjima Nura na gode fa sosai.”

    “Ba komai ranka ya daɗe nine da godiya.”

    Tafiya ya yi mai nisan gaske har ya gaji da tafiya, ƙafafunsa duk ciwo suke ma sa sosai ba halin kwanciya, cikin kasuwa ya fa ra shiga sannan ya samu wani wajen ya zauna yana hutawa, wani ya zo wajensa ya zauna ya ce ma wata yarinya mai fura dake nisa da su amma ba sosai ba.

    “Nana dan Allah ki dama min fura kuma wallahi bana da kuɗi yanzu idan na samu gobe zan ba ki.”

    “Gaskiya Basiru ka yi hakuri idan na baka ban kaiwa Inna kuɗi ba, wallahi duka na zata yi dan haka kawai ka kawo kuɗin ka.”

    “Haba Nana dan Allah ki ba shi mana taimaka ma sa za ki yi fa.”

    “Amma kin san irin dukan da Inna za ta min dai ko?.”

    “Eh na sa ni kawai ki ce ma ta sha kika yi.”

    Kallo ya ke dan ganin wacece Nana ɗin murya mai daɗi ya faɗa a cikin ranshi.”

    Da yake ba su suke kalla ba suna daga baya su kuma suna da gaban su ne dan haka ne bai ga fuskar ta ba.

    “Gaskiya ba zan yi ma ta ƙarya ba, kawai zan ba shi amma ba zan yi ƙarya ba.”

    “To Nana gimbiyar mata na gode.”

    Wani mahaukaci ne ya zo wajen Nana ya zauna yana kallonta ai ganin haka jikinta ya ɗau makarkata ganin haka Nuratu ta fa ra dariya.

    “Nuratu dan Allah ki yi ma sa magana wallahi zan iya suma anan dan Allah ki taimaka min.”

    “Kai mahaukaci kana shan fura ne?.”

    “Kai kawai ya jijjiga alamar a a .”

    “Mai kake so to?.”

    Ya nuna Nana sannan ya tashi ya zo in da take daff ya tsaya.

    Ai ganin haka Nana ta kurma ihu ta ruga a guje tana ihu mutane sai dariya suke yi, shi ma Faruk ɗin dariya ya yi sosai dan ta ba shi dariya sosai.

    “Nuratu ta waigo “Dan Allah Basiru ka kula mana da kayan mu bara na je na dawo da ita.”

    “To kuna rakaki ne?.”

    “A’a fa ka kula mana da kayanmu kawai.”

    Da gudu ta tabi bayan Nana ita ko Nana tana gudu ta ci karu da karen kasuwa aiko suma kawai ta yi a wajen, haka Nuratu ta tarar da ita kuka ta saka wani tsoho ne zai wuce sai ya ganta tana kuka ya ce

    “Mai ke faruwa ne a nan?.”

    “Baba dan Allah ka taimaka min ta mutu wallahi ta mutu.”

    Ta ɓa ƙarjin ta ya yi sai ya ji tana sauƙe numfashi kaɗan kaɗan, dan haka ya ce ta kawo ruwa, da gudu ta shiga wani gida ta ɗebu ruwa ta kawo wa tsohon zuba ta ruwan ya yi a fuska, a gigice ta farfaɗo tana salatin Annabi, sannan da ta ce.

    “Nuratu ina ƙaren nan?, ina mahaukacin ya ke.”

    “Haba Nana dan Allah ki kwantar da hankalin ba abin da zai maki kawai yana wasa ne fa.”

    “Dan Allah ki ɗauko min kaya na zan koma gida wallahi bana iya komawa can.”

    “Kina nufin kare ne da mahaukaci kike tsoro har kika suma?.”

    “Eh malam.”

    “To ki daina tsoron su saboda sun san mai tsoron su sun san wanda ba ya tsoron su dan haka ki rage tsoron nan kin ji.”

    “To malam.”

    Koma wa suka yi amma ta sa ɗan kwalinta ta rufe fuskarta da shi, hakan ya sa Faruk bai ga fuskarta ba.

    “Haba Nana ai sai ki hallaka kanki da kan ki, mene ne idan ya nuna ki ai mahaukaci ne bai san mai take nufi ba kawai ya nuna ki ne kika san ko firar yake so.”

    “Eh haka ne kuma fa wallahi na tsorata ne.”

    “Kee matsoraciya kawo min fura zan sha.”

    Muryarsa suka ji kamar daga sama, dan haka suka yi muryar kamar ina busa algaita, hakan ya sa Nuratu wai gowa ai san darewa ta yi saboda ko a mafarki bata taɓa tunanin ganin kyakkyawa kamar shi ba.

    “Ke Nuratu mai kike kallo haka ne ji dan Allah bakinki har kunnen ki basa jikinki.”

    “Nana juyo ki gani karna gani ni kadai, wallahi aljani a kusa damu, dan wallahi wannan ba mutum ba ne, sai dai aljani.”

    “Amma dai Nuratu ke kin yi hauka ai tun ɗazun yana nan dan nima nan nan natarar da shi a zaune.”

    “Capp gaskiya ban yarda ba.”

    “Nace a kawo min fura zan sha yunwa nake ji sosai.”

    “Amma malam kai baƙo ne ko?.”

    “Eh yau ne shigowa ta a garin nan ko masauƙi bana da shi.”

    “Allah sarki ko zaka zo mu je ɗakina sai ka ci gaba da zama can idan babu damuwa.”

    “Wow, thank you so much my friend.”

    Wannan maganar da ya yi har Nana sai da ta juyo suna kallon ikon Allah, dariya suka girkewa Basiru da ke saken ido kamar ɓarawo.

    Shiko ido ya zubawa Nana amma ba halin ganin fuskar ta dan haka idanunta kawai yake kalla.

    “Haba bawan Allah ya zaka zage ni?, bayan taimaka maka nace zan yi.”

    “Ayya ba fa zagin ka na yi ba cewa na yi na gode sosai abokina.”

    Dariya ya yi sosai, sannan ya ce

    “Kun ji Nana ashe ba ba zagi na ne ya yi ai na yi tunanin ko zagi na ne ya yi.”

    Da haka dai har suka sai da kayan su suka ta shi zuwa gidan, dukan uku gabanta ya fa ra yi dan ta san abin da zata tarar a gida.

    “Haba Nana mai ya sa kike sarewa ne, ki zan ka hakuri kawai idan kika fito zuwa jidan ruwa sai mu je mu leƙa ƴan birnin gidan Inna Hajju.”

    “To haka zamu yi kam, sai na fito.”

    Tana shiga ta tarar da Inna na bala’i wai ta daɗe ko ta zubar ma ta da kuɗi ne.

    Gaban ta ne ya faɗi da ta tuna shi ma baƙo bai bata kuɗi ba “lallai na shaga uku na.”

    Haka nan dai tabawa Inna kuɗin ta karɓa tana bala’i.

    “Kambu ina sauran murtalla 10?.”

    “Wallahi Inna Basirun gidan Inna Asabe ya amsa har gobe.”

    “To ki bari ai na san zai shigo gidan nan kuma zan tambaye shi.”

    “Eh Inna na yarda.”

    “Ta shi ki je ki ɗebo min ruwa dan Ubanki.”

    “To Inna.”

    “Ke zonan?.”

    Tana zuwa Inna ta ɗauke da mari, kuka ta saka saboda ta ji zafin marin kuma bata yi tunan hakan ba.

    “Inna dan Allah ki yi hakuri, naga ɗan abokiyarki ne shi ya sa na ba shi, amma dan Allah ki yi hakuri.”

    “Dallah matsa can ki bani waje mahaukaciyar banza.”

    Da gudu ta ɗauki bokiti ta fita tana kuka dan ta ji zafin dukan.

    Shi ko yana bakin kofar ɗakin Basiru ya ga wulgawar mutum kamar matsoraciya, kuma kamar ba ita ba.

    Dan haka fitowa ya yi amma ba kowa dan haka dole ya koma dakin.

    Ita ko gidansu Nuratu ta je suka fito zuwa jido ruwan suna tafiya suna fira amma rabin firar tasu duk akan zaluncin Inna ne, har suka isa in da zasu ɗebi ruwa.

    NANA FIRDAUSI

    Sha’awanatu Faruk diggi ✍️
    Wtspp ☎️☎️

    NANA FIRDAUSI

    05

    “Nana kin san ɗan birnin nan na ɗazun ya burgeni sosai, da zaice yana sona wallahi da gudu zan ƙarɓa, amma ko anya zai iya zama ɗakin Basiru kuwa?.”

    “Hahaha to ni ina ruwana da zaman shi ko rashin zaman shi, ni dai bana son shi kin ga daga zuwan shi ya saka Inna ta dake ni akan shi, saboda bai bani kuɗin fura da yasha ba, Inna har marina ta yi sannan ga kuɗin Basiru shi ma bai biya ni ba.”

    “Yi hakuri wata rana sai labari kika san ko ki auri ɗan birnin da zai saka ki makarantar boko, ka yi karatu sosai.”

    “Humm Nuratu dan Allah ki daina min maganar ƴan birnin nan, wallahi sai nake jin kamar Inna bazata bari na auri ɗan birnin ba, kuma kin ga sai abin da ta ce Baba ke yi, bana da mai tsaya min bale na samu sauƙi a rayuwata, kullum rayuwata ƙara shiga ƙonci take yi, idan naga mutum da mahaifiyarsa har daɗi nake, naji ina ma tawa Mamar na nan dana fi kowa farin ciki.”

    “Ka yi hakuri Allah yana tare da mai gaskiya in sha Allah sai kin auri ɗan birni.”

    “Ke dai ɗauki ruwanki mu je kin san sai na dawo fa.”

    “Eh nima zan dawo ai saboda yau ina da jidan ruwa da yawa.”

    “To shi ke nan.”

    Da haka dai har suka gama ɗaukan ruwan, Nana ta shi wahala tana gamawa ta ɗaura sanwar abinci, ga wutar ba sauƙi duk ta wahalar da ita.

    “Abokina mu je masallaci, saboda naga kamar tun zuwan ka baka fita ba, dan haka mu je masallaci idan muka gama sallar sai mu je cikin gari na nuna maka.”

    “To shi ke nan, amma dan Allah a ina zan samu baro ne a garin nan.”

    “Baro kuma abokina?.”

    “Eh ko bazan iya jan shi bane?.”

    “A a zaka iya in sha Allah amma nifa ɗan ƙauye ne amma wallahi ban iya jan baro.”

    “Nima ɗan ƙauye ne fa, kuna maku gama da ɗan birni?.”

    “Ah kai ba gaskiya bane wallahi abokina wazai ganka ya ce wai kai ɗan ƙauye ne gaskiya ban yarda ba.”

    “Me zan yi dan ka yarda?.”

    “Kawai mu je masallaci sai muyi maganar akan hanya.”

    “Nana mu yi sauri kan Inna ta ganki ta ce bazaki je ba.”

    “Bara na rufe fuskata saboda kar Baba ya ganni.”

    “Shi ke nan to.”

    Da gudu suka fito suna fitowa Nana ta yi karo ta mutum ta ji zafi sosai,amma bata tsaya ba bale ta ba shi hakuri, shi ko Faruk Nuratu kawai ya gane, saboda Nana ta rufe fuskarta da mayafi.

    Gudu suke yi sai gidan Inna Hajju, suka tarar da mutane ƴan birni suna zaune.

    “Laaaa kin ga waccan tafi so kyau, ga fari sai dai tana da ƙaton hanci” suka saka dariya, sai da suka yi dariya mai isar su sannan suka tafi.

    Suna tafiya sai Nuratu ta ce .

    “Gaskiya Nana mu yi sauri Ibrahim zai zo taɗi dan haka ki yi sauri gaskiya.”

    “To ke taɗi za ki je nifa taɗin doka zan karɓa” ta faɗi maganar tana hararan Nuratu.

    Da haka dai har suka isa gida Nana ta shiga gidan sai taja ba ya da sauri.

    “Ke lafiya kuwa?.”

    “Lafiya ƙalau amma kuma idan na shiga mai zan cewa Inna?.”

    “Aifa kuwa gaskiya ki yi tunanin abin yi kamin ki shiga.”

    “Ke Nana mene ne kuke yi a ƙufar gida?.”

    Bata jiyo ba ta ce.

    “Basiru ka bani kuɗi na kai da ɗan rainin hankalin abokinka wallahi ku bani kuɗi, ga shi Inna har faɗa ta yi min akan na yarda kuɗinta.”

    “Ga kuɗin naki jiyo ki karɓa dan Allah.”

    “Wallahi ba zan juyo ba kuma ka bani kuɗi na tun kan na yi maka rashin mutunci.”

    “Eh juyo ɗin sai ki min rashin mutunci na yarda.”

    “Wai muryar wa nake ji kamar shegiyar yarinyar can, zo ki duba min ita.”

    Da sauri ta shiga gidan ta ɓuya bayan ƙofar gidan, tana zuwa ta ga Basiru da wani kyakkyawan saurayi, da sauri taƙarasa in da yake tana zubar da yawu.

    “Basiru bako ku ka yi ne amma dai Wallahi akwai kyau ma sha Allah.”

    “A a abokina ne ɗazun yazo garin nan.”

    “Mtsww aikin banza kawai” cewar Faruk yana tafiya.

    Kiran Ammi ya yi bugu ɗaya ta ɗaga.

    “My son kana lafiya, tun ɗazun kiran ka nake jira amma shiru lafiya ƙalau kake kuwa?” Duk lokaci ɗaya ta jero ma sa waɗan nan tambayoyin.

    “Ammi lafiya ƙalau nake na sauka tun ɗazun na bari na huta ne kamin na kira ki amma ki yi hakuri ba zan sake ba.”

    “Amma ka bar ni hankali a tashe ka kyauta Babana.”

    “Yi hakuri Ammi ba zan sake ba in sha Allah amma yanzun kaina bisa wuyana.”

    “Shi ke nan to Babana na haƙura amma kar ka sake yin haka.”

    “To Ammi ba zan ƙara ba in sha Allah, ya maganar zuwan su Aunty Falmata ne Ammi sun sake yin magana ne?.”

    “Eh amma ta ce wai na tura ma ta numberka.”

    “No no no Ammi dan Allah kar ki bata number na Please Ammi.”

    “Wai me ya sa ka tsani matar nan ne? Babana bana son wulakanci fa.”

    “Ammi ka yi haƙuri amma gaskiya ni kawai mu bar maganar Ammina.”

    “To shi ke nan.”

    “Kambura’uban can na rantse da Allah sai anbiya ni kuɗi na, ni za a yiwa sata a gidan nan wallahi wallahi wallahi sai an fitar min da kuɗina.”

    “Babana me nake ji haka wannan ashar ɗin fa.”

    “Ammi gidan da nake zaune ne wallahi, ni ina tunanin barin gidan ne ma.”

    “A a bana goyon bayan hakan kawai ka yi zaman ka, amma ka kula sosai dan gidan daga ji ba gidan masu hankali bane.”

    “Hahaha kai Ammi da hankali kawai yanayin su ne a hakan.”

    “To shi ke nan.”

    “Sai anjima zan kira kamin na kwanta.”

    “To shi ke nan.”

    “Laaa abokina da budurwarka kake waya?.”

    “A a mahaifiya ta ce .”

    “Allah sarki.”

    “Ga abincin ka.”

    “A ina yake?.”

    “Ga shi nan.”

    “Capp gaskiya ba zanci ba, idan akwai wajen sayarwa a nan mu je ka nuna min, amma ba zan iya cin wannan abin ba.”

    “Eh akwai abincin talatuwa.”

    “Ok mu je can muci to, amma gaskiya ba zanci wannan ƙatsantar ba.”

    “Hahaha aiko dai a gidan nan wallahi Innata tafi kowa iya abinci.”

    “A hakan ne tafi kowa iya abincin?.”

    “Kai dai yanzun mu je na nuna maka.”

    “Ok to.”

    BAYAN SATI UKU

    Faruk tun ranar da suka yi karo da Nana tun lokacin bai sake ganinta, ko gibtawarta baya gani, ga tunanin shi duk ita ce yana son ya bata kuɗin ta kuma ga shi baya ganinta.

    “Allah ya sa dai lafiya” ya faɗa a ranshi.

    Wata murya ya ji mai daɗin gaske tana magana cikin gidan.

    “Inna ki ba da kuɗin shinkafa.”

    “Wace Uwarce ta aiko ki ƙarɓan kuɗin shinkafa, to ki je kice ma ta ba zan bada kuɗi ba, duk abin da zata yi tazo ta yi.”

    “Amma Inna ai yau kika ce na zo na karɓa, dan Allah ki bani kuɗi na wallahi Innata ta ce idan na koma ba da kuɗin ba sai ta ci mutuncina.”

    “Allah ya sa ta kashe ki wallahi ba zan bada ba sai na siyar gyaɗata.”

    “To shi ke nan.”

    Tafiyar ta yi tana kawowa ƙofar gida taci karo da shi a ƙofar gidan saurin ja baya ta yi sannan ta ce.

    “Wani irin abune wannan kazo ka wani tarema mutane hanya, dan Allah ka bani waje zan wuce.”

    Ido ya zuba ma ta bai taɓa ganin kyakkyawar yarinya irin ta ba, dan haka duk faɗan da take yi ba wanda ya ji sai dai yana ganin bakinta na mutsi amma bai san mai take cewa ba.

    “Malam da kai nake dan Allah ka bani hanya zan wuce.”

    Ganin alamar ba hanya zai bata ba hakan ya sa tabi gefen shi ta wuce abinta.

    Yana nan tsaye yana tunanin kyau irin nata har yanzun ita yake gani kamar tana kusa da shi, Basiru ne ya taɓa shi yana faɗan.

    “Kai lafiya kazo ka wani tsaya kan hanya idan mutum zai wuce fa?.”

    “Ayya wai ta tafi? Wace hanya tabi ta wuce ne?.”

    “Wace ce?.”

    “Kash ba kowa ina tunanin gida ne.”

    “Allah sarki to ka je ka yi sati mana sai ka dawo.”

    “A a duka duka yaushe nazo ba zan koma yanzun gaskiya, a ina ake siyar da katifa ne?.”

    “Me zaka yi da katifa kuma? ai garin nan sai masu kuɗi ke kwanciya a saman katifa.”

    “Me ake yi da katifar jifar da ita zan yi hankalin ya kwanta.”

    “Allah ya ba ka haƙuri, ni ba haka nake nufi ba.”

    “Me kake nufi to?” Ya tambaye shi cikin rainen hankali.

    “Ina nufin a ina zaka samu kuɗin siyan katifa, bayan ko aikin baka yi, katifa na da tsada sosai.”

    “To mu je kawai zan siya ai zan fa ra yin aikin ne, amma baka faɗa min in da ake siyar da baron ba.”

    Abokina da kana bin shawarata da kabar maganar baron, kawai ka yi siyar da kayan zaƙi irin wanda yara zasu yi siya.”

    “Yes hakan ma ya yi gaskiya nima ina nan ina tunanin yanda zan yi jan baron.”

    “Gaskiya dai gara wannan kawai kana zaune ne.”

    “Hakan ya yi amma gaskiya naji daɗin wannan shawarata ka.”

    “Mu je ka siya katifar .”

    “Yauwa mu je.”

    “Basiru…. Basiru …. Basiru tsaya ka ji dan Allah.”

    “To” kawai ya ce .

    “Basiru dan Allah magana nake son ka yi min a gun Nana, Wallahi ina son yarinyar sosai, naga kuna da alaƙa tsakanin ku.”

    “Wallahi ba wata Nana da zan yiwa magana, ka je da kanka amma ni ba zan yi.”

    “Shi ke nan zata zo wajen wasar ne?.”

    “Ka je gidan su ka tambaya, dan nima ban sani ba.”

    “To shi ke nan wannan fa?.”

    “Dan uwana ne.”

    “Dan uwan ka kuma, amma bai saba zuwa ba ko?.”

    “Dan Allah ka tambaye shi, ga shi nan, haba ka cika ni da tambaya.”

    “Yi hakuri sai mun haɗu anjima.”

    “To sai mun haɗu.”

    NANA FIRDAUSI

    Sha’awanatu Faruk diggi ✍️
    W ????

    06

    “To.”

    “Wai wane ne wannan ne?.”

    “Abokina ne shi, kuma son Nana yake yi nima na sani, saboda wani hauka da yake yi.”

    “Ita tana son na shi ne?.”

    “A a wallahi, ita fa karatu take sun yi, saboda yana burge ta.”

    “Shi karatun?.”

    “Eh, yanzun ka yi mata maganar karatu to ka gama da ita wallahi, ga in da ake siyar da kati fa.”

    “Ok toh mu shaga ci ko.”

    “A a ka bari har suzo, idan suka tambaye ka wace iri kake so, sai mu shiga.”

    “Wai anya zan iya zama garin nan, komai na shi bai yi min ba wallahi, wai wannan wajen siyar da katifa ake yi hummmm” duk wannan zan cen shi ka ɗai ke yin abin shi a ransa.

    “Abokina ka yi shiru lafiya dai?.”

    “Eh lafiya ƙalau, kawai ina dubin gurin ne.”

    “To, amma abokina na manta ban tambaye sunanka ba.”

    “Ok sunana Faruk?.”

    “Allah sarki, to shi ke nan zan dinga kiran ka da Faruk ɗin.”

    “Okay, that’s it” (Ok toh shi ke nan)

    “Dan Allah ka daina ɓaci na, wallahi bana jin abin da kake cewa.”

    “To na daina.”

    “Basiru yakike ya gida.”

    “Lafiya lau wallahi Nasiru, katifa muke so, sabuwa cikin laidar ta.”

    “Ah tabɗijam, ta kwancin mutum biyu, ko ta mutum hudu.?”

    “Babba muke so.”

    Wata katifa aka kawo masa, har da jiruwayen fitsari ai da sauri ya matsa gefe yana faɗan.

    “Wannan ce sabuwar dana ce, dan wulaƙanci ya zan ce sabuwa, sannan ku haɗa ni wannan abin.”

    “Yi hakuri yallaɓai wannan ita ce sabuwar katifar mu.”

    “Wannan abin?.”

    “Eh.”

    “Bana so ka mayar da abin ka, bana bukata” ya faɗa rai ɓace saboda ranshi ya ɓaci sosai,

    “ya zasu raina masa da hankali wai sabuwar ce wannan mtsww aikin banza kawai.”

    Haka ya bar wajen ranshi a ɓace.

    Basiru da gudu yabi bayanshi dan ya tafi ya bar Basirun.

    “Haba Faruku yi hakuri wallahi wannan katifar sabuwa sosai.”

    Ranshi ƙara ɓaci ya yi, da sunan da Basiru ya ce masa “wai Faruku.”

    “Faruku da kai nake magana fa.”

    “Dallah yi min shiru, sha-sha-shun banza kawai, ni zaka kawo wannan wajen dan iskanci da wulaƙanci, ka rasa ina zaka kawo ni sai wannan wajen, to yau sai naci ubanka idan muka je gidan ku.”

    Tsoro ne da farga ba suka ciki cikin Basiru anya Faruku ne, lafiya lau suke fa, kuma ba abin da ya yi masa anya ba shi da Aljanu.

    “Amma Faruku mene ne na yi maka da zaka ce haka eh, ban yi maka komai ba, dan Allah idan aljanun ka ne suka tashi kabasu hakuri, wallahi ban yi komai ba, kuma aradun Allah tsoron su nake yi.”

    Faruk ji ya yi kamar ya ɗauke shi da mari, sannan kuma ya ci ubanshi, ranshi ya kai matuƙar ɓaci, ran da yake ba wanda ya taɓa ɓata masa rai, irin wannan sha-sha-shun Basirun nan, akan takaici Faruk hanya ya raba da Basiru, kuma ya ce.

    “If you follow me, I swear I will deal with you severely there, you useless fool.” {Idan ka bi ni, wallahi sai na yi maka mugun hukunci a can, wawan banza.}

    Akan tsoro Basiru da gudu ya bar wajen, saboda wallahi da gaske Faruk tsoro yake ba shi.

    Shi ma Faruk ɗin tafiyar shi ya yi, bai san in da ya nufa ba, kawai tafiya yake, sai da ya kai bakin rafi shiga ciki ya yi, wanka ya yi, sannan ya fito ya zauna a wajen, yana kallon yadda ruwa ke wucewa da gudu gwanin birgewa.

    “Kai…. Kai… Kai…. Baƙo lafiya ƙalau kake kuwa? naga kazo a rafi ka zauna kamar wani zararre, ko da yake ai zararren ne” ta bawa kanta amsa.

    Ɗago kain da zai yi wa zai gani Nana da Nuratu suna kallon shi.

    “Lafiya nake.”

    “Amma baƙon me yasa kazo nan ka zauna?, kamar baka jin daɗi fa?.”

    “Lafiya nake nace.”

    “To me ya jiƙe maka kayan ka ga su nan sai fitar da ruwa suke yi?.”

    “Nace lafiya nake kun cika ni da tambaya.”

    Nana kam tun tambayar shi da ta yi, bata sake yin magana ba.

    “Mtsww dallah mu tafi, dan an tambaye shi matsalar shi zai yiwa mutane wulaƙanci, za ki zo mu tafi ko sai kin gama zama ana wulakanta ki.”

    “Nima dai ban ji daɗi ba gaskiya, saboda duk wanda ya damu da damuwar ka, kamata ya yi kai ma ka damu da shi, amma ba komai sai anjima.”

    Mamaki ya ishe Faruk wai, wannan yarinyar ce mai bakin da zata faɗa masa haka.

    Tafiya suke ba maima wani magana daga cikin su har suka isa gida.

    “Ke munafukar yarinya, yau narantsa da Allah sai kin ci ubanki, shegiya mayya, wa zai soki da wannan baƙin gadon naki, kuma ki ajiye ruwan kizo ki yi min shara, ki gama ki ɗaura sanwar abinci.”

    “Inna ki bari gobe sai na yi yanzun dare nayi fa, kuma wallahi kaina ke ciwo, dan Allah ki bari har gobe, yanzun zan yi ɗeban ruwan idan yaso gobe kawai aikin zan yi ba sai na je ɗeban ruwa ba.”

    “Ina magana kina magana, wallahi sai kin yi sharar da abinci dan ubanki, shegiya ƴar isaka kawai wacce ta yi lali kowa baya so.”

    Hawaye ne suka cika idon Nana, saboda taso ta je dandali, amma yanzun ba damar zuwa, kuma ance har baƙin gidan Inna Hajju zasuje, amma ba ita, kuma taso ta je ko dan ta gansu, amma Inna ta hana ta, hawayen da suka cikin idonta ne suka faɗu a fuskar ta abin tausayi, zuwa ta yi dan ta yi aikin, ko zata gama kamin lokacin.

    Da sauri ta yi shara, sannan ta je ta ɗaura sanwar abinci, da sauri har ta gama lokaci bai yi ba, daɗi ta ji kamar mi, wanka ta yi ta saka wasu jemammin kaya da suka ruwa, ba abin da ta shafa, tana gamawa ana kiran isha’i, dan haka da gudu ta bar gidan, ƙofar gidan taci karo da Faruk gaba ɗaya ta faɗa a jikin shi, kuka ta saka, sannan ta kauce da ga jikin shi tana faɗin.

    “Allah ya isa na, ban yafe ba, tun da ka faɗa min a jiki, kuma wallahi sai na faɗawa Basiru cewa kai ɗan isk…..” Bai bari ta ƙarasa maganar ba sakamakon, bakinta da ya buge da hannun shi.

    “Ke ni kikewa rashin kunya? ki faɗa kaina sannan kizo kina kiran, wai ni nafaɗa kan ki, mene ne a jikin da har zan faɗa miki” ya ƙarashe maganar da hararanta.”

    Kuka ta saka masa wai wallahi sharri yake ya mata a ina ta ganshi da har zata faɗa masa.

    Ni…..Ni….Ni…. wallahi….. wallahi… wallahi…. sharri kake min, kawai dan kana son na kulaka ne shi yasa ka biyo ta wannan hanyar, kuma wallahi sai Allah yasak….” Sake buge bikinta ya yi.

    Jin muryarta ne a waje da Inna ta yi yasa ta taleƙawa, ai randa ta ga Inna ta wurga a guje tana gudu kamar tsuntsuwa.

    Dariya Faruk ya sosai, sannan ya shiga ɗakinsu, shiryawa ya yi cikin ƙananan kaya, amma ba sabin kaya bane, aiko ya fito tamkar ɗan ƙauye, madubi ya kalla, dariya ya yi ganin yanda ya koma, kamar ɗan ƙauyen gaske.

    Basiru ne ya shigo da wasu kaya, duk wando a yage kamar wanda ya yi faɗa da kura.

    Faruk ne ya kalle shi yana faɗin.

    “Basiru wannan kayan fa, ko kura ta biyo ka ne?” ya faɗi maganar yana leƙa ƙofa.

    “Faruku wannan ai wulaƙanci ne, ya zan yi kwalliya sannan ka ce min kura ta biyo ni, kuma fa sune kayan da nake sakawa idan zan fita.”

    “Nifa na faɗa maka, ka daina kira na da wani Faruku bana son wannan sunan.”

    “Shi ke nan na manta ne ya sunan yake ne?.”

    “Faruk ko ka ce Umar kawai.”

    “To shi ke nan Faruk.”

    “Yauwa ko kai fa, yanzun baka ji sunan yafi daɗi ba?.”

    “Eh yafi daɗi kam.”

    “Yanzun ka kayana ka saka mu je.”

    “A a kabar shi kawai zan je da nawa.”

    “Kai baka fa nayi saboda kai ne ɗan uwana a garin nan.”

    “Da gaske kake faɗar wannan maganar abokina?.”

    “Eh da gaske nake faɗar maganar.”

    “Na gode sosai Allah yasa ka da alkairi.”

    “Ameen ya Allah.”

    Amsar kayan ya yi yasaka, kayan sun yi masa kyau sosai.

    Fita suka yi sai Basiru ya ce yana zuwa, shiga gidan ya yi yana faɗan.

    “Ƴan bakin ciki sai dai ku mutu wallahi kun ganni da sababbin kaya ko? To abokina ya bani su, amma kunzo kuna kiran shi da maya ne, tun da kun ganshi kyakkyawa.”

    “Kai dallah yiwa mutane shiru, sai ka zauna ana baka kaya kana sakawa, wa ma yasan ko asiri ya yi kayan, sannan ya ɗauka ya baka, sannan zaka zo kana yiwa mutane hauka” cewar wata mata a haife zata haife shi.

    “Eh asirin ne ya yi min sai mi, ni ga zan iya zama da shi, baku ba saboda haka kowa ya yi min shiru, kuma zamu je dandali sai mun dawo.”

    Tafiyar shi ya yi, yana kai wajen Faruk sai wayar Faruk ɗin ta yi ringing, tsayawa ya yi da ga baya.

    “Hello My Ammina barka da dare?.”

    “Yauwa barka dai Babana.”

    “Yakike kina lafiya.”

    “Lafiya ƙalau nake Babana.”

    “To ma sha Allah, yana ji muryar ki kamar mara lafiya ne Ammina.”

    “Lafiya ƙalau nake, ba abin da ke damuna ga Mamar ku.”

    “Mama kuma Ammina?.”

    “Eh ko baka da gaskiya ne Babana?.”

    “A a da gaskiya na ni kam Ammi, ki bata wayar to.”

    “To shi ke nan.”

    “Mama ina wuni?.”

    “Ya gida yasu Farha.”

    “Lafiya ƙalau ai ka manta da Farhar ko?.”

    “A a Mama ba haka ba ne, kawai abubuwa ne suka min yawa, amma in sha Allah zan riƙa kiranki muna gaisawa.”

    “To shi ke nan, amma Sadiq ya ce yana kiranka bata zuwa lafiya dai?.”

    “Lafiya ƙalau wallahi maybe laifin network ne, saboda suna da ƙarancin network.”

    “Ok to shi ke nan, ka kira shi, dan Allah ka ji yaron kirki.”

    “To Mama zan kira idan na dawo yanzun zan je wani wajen ne.”

    “A ina ne zaka je, har an zama ƴan gari kenan.”

    “Eh wallahi, wani wajen ne zan je, tare da wanda na sauka ɗakin shi.”

    “Ok to kaba shi mu gaisa mana.”

    “A a Mama ba yanzun ba zan haɗaku wani lokacin, amma ba yanzun ba.”

    “To shi ke nan Allah ya kaimu lokacin.”

    “Ameen sai anjima.”

    “To sai anjima.”

    Yanke wayar ya yi, waigawar da zai yi sai ganin Basiru bayan shi ya yi, cikin rashin gaskiya ya ce .

    “Har ka fito mu je to?.”

    “Eh ai na jima da fitowa, tun wayarka na ƙara na fito.”

    “Ayya to mu je ko?.”

    “Eh mu je.”