Chapter 10: Chapter 10
Zai wuni yana jinyar Sophie da tarairayarta, in dare yayi kuma ya karbe ladan jinyarsa in a loving and romantic manner.
Zuwa lokacin Safiyyah ta ware, ta karbi rayuwar aure ta reality. Ta daina tsoron shi, tana cooperating dashi dari bisa dari, tana kuma enjoying soyayyar kamar kowacce mace, ta rungumi rayuwar auren yadda ya kamata duk wata macen kwarai ta yi, a shekarun girman diya mace. Burinta kullum kasancewa tareda Habiby da farantawa Habiby rai, fatanta na yanzu shine samun ‘ya’ya masu irin halayensa da kamanninsa daga gareshi.
A duk sanda ya bukaceta yanzu a take amsar gayyatarsa. Don ta gane wuyar sha’anin ashe-ashe bata kisa, shu’umancin Aunty Dije ne.
Tafiyarsu zuwa Katsina sai a sati na gaba ta yiwu, ya zamanto cewa sati hudu cif kenan rabon Zayyan da gidansu, wato tun bayan tarewar Safiyyah. Saidai koyaushe basa rabo da waya shi da Baba da Mama da ‘yan uwansa mata.
Abinda bai sani ba ashe hakan da yayi wato kwashe sati hudu cur bai zo gida ba yayima Mama Fatu ciwo sosai, ya kuma fusatata, don sanin kowa ne Mama ta kallafa rai akan Zayyan, bata maraba da duk abinda zai canza mata shi ko ya canza tsarin rayuwarshi ta baya wajen kulawa dasu, kasancewarsa da namiji kwal data ke so fiyeda sauran yaranta, ta dai tsaya taga iya gudun ruwansu shi da matar tasa, na sai yaushe zai zo inda take saboda yayi aure. Mama ta kasa yin uzuri akan hakan. Har rannan take cema Yaya Zubaidah cikin damuwa, ranar Zubaidah tazo mata yini kamar yadda ta saba zuwa gida ta wuni duk sati.
“Zubaidah ko kin fahimci Baffana mace ta janye min shi tun ba’a je ko’ina ba?”.
Zubaidah tayi dariya kadan, tace “kai habawa Mama! Har yaushe aka yi daren da garin zai waye?
Ki barshi na dan lokaci ne, giyar amarci ke kwasarshi in kwannafi ya kwanta kanwa ta kar tsami zaki ganshi ne da kafafunsa.
Amarya kota buzuzu ce sai an yi dokinta Mama”.
Mama ta ce “umh” kawai.
Don bata so zancen yayi nisa ya kara janyo mata bacin zuciya.
Wannan itace haduwar farko tsakanin Sophie da surukuwarta Mama Fatu, haduwa ta zahiri. Saboda a hoto kawai Mama ta taba ganin Safiyyah sai ko yau data ganta a gabanta kuma a dakinta.
Nan Safiyyah taga inda Zayyan ya debo ruwan kyawunsa na Rumawa. Bai baro Mama a komai ba. Hatoon na makarantar kwana haka su Zahra suna jami’a.
Cikin sa’a daga Mama har Baba suka samu a gidan, dattijan suna shan hutun karshen mako yadda suka saba. Baba Bello da ‘yar lelensa Hajiya Fatimah (Mama shalelen Baba) inji ‘ya’yanta.
Kasancewar Asabar ce Baba yana gida bai fita ba. Zayyan ne a gaba, Safiyyah na biye dashi a baya, yayi sallama suka shiga kasaitaccen falon Mama.
Mama dake hakimce cikin kujerar falonta ta sha ado da (swiss lace) dan gaske, ruwan zuma, kwalliyar ta musamman ce yau ta karshen mako kasancewar Baba na gida yau yace ba inda zashi, kai in ka ganta a lokacin tamkar Hakimar Rafindadi, tana jiran Baba ya gama wayar da yake yi tayi masa korafin Zayyan, har yau bai zo ba tun tarewar amaryarsa.
Yanzu ita dashi sai dai waya, yana faman bata uzuri na zai zo, zai zo, sai kuma katsahan taji sallamarsa.
Mama ta amsa sallamarsa ciki-ciki don ta dau muryarsa tun daga waje, yana shigowa tace cikin nuna mamaki.
“Muryar wa nake ji mai kama data Baffana? Halan ka yi batan kai ne yau Baffa?”
Watakila saboda haushin Zayyan yayi sati hudu bai zo ba shiyasa Mama ta kasa yiwa Safiyyah kallon kirki. Duk wani dan canji yanzu ta cewa kanta sai tana kula, don kada diyar Alaramma ta janye mata shi da laqaninsu da tofinsu na ‘ya’yan Alarammomi. Shi daya jal din da Allah ya bata a matsayin namiji cikin ‘ya’yanta mata kenan bata wasa da al’amarinsa, bazata barwa wata mace kuma ‘yar talakawa da ta zo daga sama tayi yadda taga dama da rayuwarshi ba.
Idon Mama ya koma kan amarya Safiyyah. Duk inda Zayyan ya cire kafa nan take mayas da tata a falon, cikin yanayi na nuna bakunta da surukuta.
To da yake Mama bata zaci zuwanta a lokacin ba, yasata binta da kallo tana shigowa, da takunta na nutsuwa kanta a kasa. Ta lura wani kallon kurilla Maman Zayyan take mata.
Mama ta tsaida idonta a kanta tana kallon ‘Hijabhie’ din Zayyan dinta, wato Safiyyah Usman Dandume. Tun daga kallo na farko ta hango macen kwarai, amma son zuciya daya lullubeta da kyashin kasancewata diyar talakawa yasa taji kawai daga gani na farko Safiyyah bata yi mata ba. kamar yadda tun farkon fara zancen aurenta ma zancen bai mata ba.
Abun mamaki Mama ta kasa boye haka a kan fuskarta, don sai yamutsa fuska take yi kamar taga abun kyama. Kwarjinin Safiyyah irinna cikar tarbiyyah da riko da addini yaso ya dan rikita Mama, wadda a baya take mata kallon raini tun kafin ta ganta, just because an ce diyar Alaramma ce, sai ba haka ta tsammaci ganinta ba, wato dai ya zama cewa Safiyyah din ganinta yafi jinta!
Ta so ganinta typical bakauyiyar Dandume, yadda zata ji dadin raina mata wayau. Amma ina! Wane mutum! Safiyyah dai girman kauye ce amma bata da Ruwan kauyawa, sannan ta wuce ido ya kalla ya raina domin Safiyyah ta sha rubutun kwarjini a gidansu ta koshi. Ashe ba duka mazauna kauye keda appearace na kauyawa ba inji Mama.
Sai tafi mata kama da kalar matan manya ba yara ‘yan makaranta irin danta Zayyan ba; she is looking extremely classy, a cikin hijabin.
Yawanci mata masu tsayi da kyawun surar fuska dana kirar jiki irinna Safiyyah basu cika yawa a arewa ba, duk da za’a iya cewa Safiyyah bata da zubin kalar ‘yammatan da Mama ta saba gani tareda ‘ya’yanta, wato Safiyyah ba ‘yar gayu da son kwalisa bace, kwatankwacin ‘ya’yanta su Zaitoon da ire-iren kawayensu da ta sani, ma’abota kawar zamani irinna ‘ya’yan hutu, wadanda iyayensu wasu ne a Katsina, sun kuma daure musu gindin yin shiga mai tsada ta kece raini, ire-iren ‘yammatan da ta so ace Zayyan ya aura kenan, amma kuma ita Safiyyah nutsuwarta da kamewa, da innocent looks dinta da zubin halittarta na Alkyabbar mata yasa duk ta fisu kwarjini da kamala.
Ko makiyinta in ya ganta a lokacin, da irin shigar mutunci da tayi tazo gaban surukanta zai ce “Safiyyah is decent and classy”.
Duk da fatarta ba mai haske bace can, yatsun hannunta duk sun sha adon jan lalle na amarci har na kafarta, wanda bai gama fita ba har lokacin. Domin kumshi ne mai nagarta aka yi mata na aure. Kyakkyawar round face (zagayayyar fuskarta) kawai kake iya gani a jikinta da zara-zaran yatsun hannunta, bata shafawa fuskarta komai ba bayan ‘lip gloss’ data dan shafa kadan a fatar bakinta mai sulbi kamar yankan reza, zaka gane ita Safiyyah mai yalwar sumar kai ce (mai yawan gashin kai) ta hanyar tudun dankwalinta ta baya, nata tudun kallabin natural ne ba irin wanda ake kira a cuci samari bane.
Koko yace rashin haduwar jini na farat daya shi ya kara afkuwa physically a haduwar Sophie da Mama, tsakanin Mama da surukarta Safiyyah.
Don sam Mama har ranta bata yi farin ciki da zuwan Safiyyah gabanta ba, ta so ace shikadai ma ya zo, su sake su wuni hira abinsu.
Safiyyah tsugunne a gaban Mama Fatu, tana gaisheta da dan sassarfar halshenta na halitta, mai hade da in’ina (stammering) wadda bata zama (worse) din da za’a kasa gane me take cewa ba.
Mama data gane Safiyyah (stammerer) ce sai ta kama baki cikin kakabi tace.
“Allah Waahidun Ahadun! Yanzu Baffana, ka rasa wadda zaka auro duk fadin Katsina da wajenta sai mai tsamin baki da in’ina haka?”
Bashi Zayyan ne kadai yaji kunyar kalaman Mama ba, hatta Baba da ya ji abinda Mama Fatu ke furtawa saida ya kware da Ruwan da ya kurba a tambulan.
Yayi saurin kallon Safiyyah din, da addu’ar Allah yasa bata ji ba, duk da ya san addu’ar bata karbu ba, saboda Mama da karfi ta fada ba sakayawa, sosai Baba ya ji babu dadi hadi da kunya na wannan kalaman baran-barama na matarsa Mama Fatu akan surukarsu, a dai ranar haduwarta ta farko da surukar tata.
Wadanda are more of cin fuska. He felt embarrassed har fiye da Zayyan da Safiyyan.
Duk da Safiyyah taji ta muzanta da abinda Mama tace a kan yanayin maganarta, amma ko a fuskarta bazaka ga rashin jin dadin ba. Ta shanye hakan tsaf da kyakkyawan murmushi. Saidai ta kasa kara cewa komai bayan gaisuwar data yiwa Mama, wadda Mama Fatu bata ko kai ga amsawa ba har lokacin saboda takaicin ya dauko musu stammerer. Don da farko Safiyyah tayi niyyar tambayar Mama lafiyar ‘yammatanta wato kannen Zayyan su Hatoon, Zaitoon da Zahrah da bata gani ba, amma sai taji bakinta ya dinke, gwiwarta tayi sanyi kalau da yunkurin sake magana kuma, tunda yanayin halittar maganarta bata yiwa Mama dadin ji ba.…
Baba kam sai yayi funfurus dashi kamar bai ji Mama ba, ya zama kamar wani wanda baya jin yaren harshen Hausa, yayi kamar bai fahimci me Mama tace da Baffa din akan matarsa ba, sai ya fara,
“maraba lale da Nana Safiyyah, yau gidan namu nada manyan baki, tunda amarya Nana Safiyyah ce tazo da kanta ba sako ba!”.
Ko dama can Baba Bello mutum ne mai yawan raha ga iyalinsa. Mai saukin kai a cikinsu. Nan da nan yasa Safiyyah ta kara fadada murmushinta, ta duka ta gaisheshi shima, tanata kokarin adjusting in’inar, kada shima Baban Zayyan yace irin abinda Mama tace akan in’inarta.
Sai ta baiwa Baba Bello tausayi sosai. Yace yaya Zaria, bude baki Safiyyah muyi hira kinji? Yaya karatun naku da kuma wajensu Malam da Ammi a Dandume?
Ai kuwa Safiyyah taji dadi, ta saketana amsawa with ease. Baba ya tambayeta lafiyar sauran kannenta duka, Safiyyah na amsawa da lafiya kalau suke Baba. Baba Bello yayi duk yadda zaiyi cikin hikima yake janta da hira (just to make Safiyyah comfortable in his home) daga cin fuskar da Mama tayi mata.
Zayyan kuma sai ya zama dan kallo a hirar Baba da diyarsa Sophie, don Baba baya ko sako shi cikin hirarsu, musamman da yaji cewa Sophie ma dalibarsu ce wato Architect student ce. Sai hirarsu tayi tsayi, yana son sanin meye plans dinta bayan gama karatun? Aikin gwamnati ko private zane-zane?
Budar bakin Safiyyah sai cewa tayi, tafi so ta zauna agida ta kula da yara, in yaso ta dinga yin nata profession din daga gida tareda Zayyan, wato tanaso ta dinga yin nata Zanen a gida tana baiwa Zayyan, su hadu su tara idea akai, su kayata shi. Ta kuma dinga zama mataimakiyarsa ta cikin gida tunda duk abu guda suke karanta.
Wannan zabi na Safiyyah ya burge Baba Bello sosai, don da wuya ka samu mace mai zurfin ilmin da zata ce maka wai zata zauna a gida ta kula da yara, da taimakawa mijinta, hakan yasa ya jinjinawa integrity dinta cikin ransa.
Mama dai nata sauraren in’inar Safiyyah daga gefe tana dada harzuka, a kasan ranta tana ta maimaita mitar Zayyan ya rasa wadda zai kwaso musu sai mai fama da stammering, kamar ance kyawawan mata masu kyawun lafazi a Katsina da kewaye sun kare???
Saboda kokarin Baba na kyautatawa da farantawa ga Safiyyah, yasa har suka tashi tahowa gidansu a Zaria Safiyyah bata fito gidansu Zayyan da bacin rai ba sam, duk da Mama bata kara kula ta ba, ta dai sa mai aiki ta bata abinci, Safiyyah bata ko ci ba, don sai da shimfidar fuska kake iya cin abinci, Zayyan kuma yace tare zasu ci a gaban Mama, hakan yasa ta kasa ci don tana ganin Mama na satar harararta, saida Baffanta kadai take tadin hira. Shi kuma sai yayi ta jefo Safiyyah cikin hirar, ita kuma saidai tace eh ko a’ah.
Safiyyah bata kawo komai a ranta ba na basar da ita da Mama tayi, amma a ranta tace ga dukkan alamu bata samu karbuwa gun Maman Zayyan ba, ta fahimci halin Baba Bello Habibinta yabi ya dauke gabadaya, na karrama dan adam ko yaya yake bana Mamanshi mai fadin rai ba. Ba wata far’a da ta samu daga Mama, balle wata kulawa ta karbar bako.
Har suka bar gidan Mama bata maida hankali akan Safiyyah ba, bata jata a jikinta don ta sake da ita ba, bata nuna mata kowacce irin kulawa da kauna ta surukuwa ba. bata bata fuskar da zata ko iya ce mata sannu bayan gaisuwa ba. Wannan abu bai yiwa Zayyan dadi ba, ya kuma sosa ran Safiyyah daga bisani, ganin kirikiri Mama ta nuna Zayyan ne kawai nata, kuma dashi kadai take maraba. Ita Safiyyah bata san halin Mama bane rashin kara akan yaranta.
Amma ko a fuska bazaka gane bata ji dadin ba. kullum Ammi na nuna musu su zama masu shanye facial expression dinsu da hadiye rashin jin dadinsu akan duk wani unfavorable treatment da wani yayi musu wanda bai yi musu ba.
Ammi na yawan cewa ba kowa ne zai so ka a rayuwa ba. Tunda kuma ga Baba Bello da kansa yanata haba-haba da ita name zata damu kanta.
Sai yamma suka bar Rafindadi, suka kama hanyar komawa Zaria. Babu tsaraba kota tsinke da Mama tayi mata. Tsarabar da ita ta kawo mata kuwa Mama ba godi bare an gode, tace da Ankudi (mai aikinta) ta kai kitchen.
Ranar nan da Baba ya koma gida daga sallahr Isha’i ya samu Mama Fatu har dakin barcinta, Mama ta sha fada, wanda da wuya kaji Baba Zayyan nayi mata irin shi, akan abinda ta fada akan in’inar Safiyyah kuma a gabanta, daga bisani wa’azi da nasiha Baba ya maida fadan, yace “ba’a yiwa Allah izgili akan halittarsa, ta koyi iya rike magana a bakinta don rike girmanta, ba kowacce magana ce ta zo ranka akan halittar wani zaka furta masa ba, yace ta dinga tauna magana kafin ta furta don gujewa tozarta dan adam da ci masa fuska akan halittarsa, kalami mai dadi ma ga musulmi kawai sadaqah ne. Cin fuska akan nakasunsa kuwa zalinci ne ga zuciyarsa.
Yace yanzu ina amfanin abinda tace da Safiyyah a matsayinta na babba mai hankali kuma Uwa agaresu wadda ta san cewa in’ina halitta ce ta Allah?
Baba ya furzar da numfashi cikin bacin rai, ya dubi Mama yace “Annabin Allah ma yayi in’ina (Musa Alaihissalam) na tabbata kinsan hakan a tarihin Annabi Musa.
Tashin farko a haduwarku ta farko kin zubar da girmanki ga surukarki, matar tilon danki. Wannan cin fuska ne kikayima danki ba ita ba, tunda shi kika bari da ji miki kunyar”.
Mama zancen ya fara isarta, ta shuno baki gaba, tana son cewa wani abu sai ta fasa, ta daure bata ce komai ba dai, har Baba Bello ya gama fadansa da bambaminsa da wa’azinsa da nasiharsa ya gaji ya kyaleta.
Koda suka kama hanyar komawa gidansu a Zaria, shida ita duk suna bayan motar hayar data kawo su Katsina sunyi shiru, direban wanda shi yazo don ya maidasu gida yanata sharara gudu dasu bisa titi, a zaune suke dab da juna, hannunsa cikin na Safiyyah.
Zayyan sai ya samu bakinsa da baima Safiyyah hakuri kan abinda ya faru don ya zama restless da ganin shirunta, sai yake tunanin ko akan kalamin bakin Mama Fatu ne yasa ta rage magana, ya damu sosai har fiye da kima, ji yake kamar shi yayi mata gorin.
Safiyyah hakurin da Zayyan yake bata sai taji yafi abinda Mama tayi mata nauyi. Saboda Mama ai Mamansu ce su duka, ba abinda zata yi ko zata ce da zai bata mata rai.
Shi kuma wannan Zayyan mijinta ne, wanda Allah ya dora sama da ita, amma ya kwantar da kai irin haka yana bata hakuri akan laifin da bai aikata ba.
Sai tayi murmushin da zai kwantar da hankalinsa ta ce. Shirun daka ga nayi ba akan wannan maganar bane, tunanin su Ammi da kewar su Rayyah nake yi.
Yanzu Habibi me aka yi da zaka yi ta bani hakuri haka? Mama Mamana ce fa!
Ai gaskiyar Mama ne inada sassarfan harshen. Nima na sani, kowa ma ya sani, kuma ba so nake yi ba nima, nayi-nayi in bari tun ina karama na kasa, nima bana sonta ko kadan (in-inar), ina addu’a Allah yasa watarana in bari…”. Sai taji hawaye ya taho mata. Ta sunkuyar da kai ido fal kwallah don bata so ya gani, tace “this is nothing to worry about Habiby! Please stop it, hakurin da kake bani shi yafi komai karya min zuciya”.
Zayyan yayi maza ya rungumota jikinsa, (yama manta a motar haya suke), yasa hannu ya dago habarta, yayi kokarin saka idanunsa cikin na Safiyya, duk da tana kokarin kaucewa haduwar kwayan idanunsu saida yasan yadda yayi ya sarke idanunsa cikin nata, tuni ya zuba mata dafin dake cikin haduwar ‘eye contact’ dinsu, wanda ita kadai tasan irin tasirin da suke mata cikin ruhi da gangar jikinta, narka mata zuciya suke, su zuba mata dalmar soyayyarsa. Zayyan yace cikin shauki.
“My Dear Safiyyah, akwai abinda baki sani ba, something you don’t know ni kuma bazan gaji da gaya miki shi ba.
Tsamin bakin (as Mama called it) shine abu na biyu da ya fara inviting zuciyata zuwa gareki, I love your stammering! Kema kinsan haka. Ni son in’inar nake. Dadi take yi min.
Wani lokacin har imitating dinta nake yi nikadai kafin na mallake ki a gefena Sophie.
Idan shaukinki ya dameni cikin dare sai in yi ta kwaikwayon in’inar ina debewa kaina kewarki, kafin Allah ya dube ni da rahmarsa ya bani ke Safiyyahhh!”.
Safiyyah ta dago da mamaki tana kallonsa yace “yes, it’s the sweetest voice I ever heard. It sounds so special saboda zaki ga ba kowa Allah yake yiwa baiwa da irinta ba”.
Safiyyah tayi murmushi sosai har saida barin kumatunta na hagu ya lotsa sosai, feeling highly proud of her voice today, (cikin jin alfahari da muryar tata yau), tunda har muryar ta na yiwa masoyi Zayyan dadi, a hakan yadda take, to ta yarda don Allah kada ta yiwa kowa dadi.
Da wadannan kyawawan kalamai Zayyan ya lallashi Safiyyah, suka rufe chapter din in’inarta da Mama bata so, basu kara tada zancen nan ba har inda yau ke motsi.
**** **** ****



