Chapter 11: Chapter 11
Safiyyah na level two a lokacin da sukayi aure. Kullum tare suke shiga makaranta in ta rigashi tashi ta jirashi har sai ya tashi ya goyota a bayan LIFAN dinsa su dawo gida tare.
Rayuwar sa da Safiyyah ta cigaba da tafiya a haka gwanin ban sha’awa ga duk wanda ke gefensu, zaka shaida cewa rayuwar aurensu cike take da so da kauna na hakika zallah, wanda babu karya ba kuma kwadayin duniya a cikinsa, suna masu yawan tausayawa juna, da taimakekeniya a tsakaninsu, ta fannin karatu da hidimar gida, har zuwa shigar Safiyyah level three. Zayyan shi ya cigaba da daukar nauyin karatunta bayan aurensu.
Da yawan abokan karatun Safiyyah basu san ma tana da aure ba, balle alaqar aure dake tsakaninta da Assistant Lecturer mai tashe a tsangayar zane-zane; Yaya Brainlliant Architect, Zayyan Bello Rafindadi.
Saboda babu wata alama da zata nuna maka cewa Sophie tayi aure yanzu, tunda dama kowa ya riga ya santa ne da shigarta ta kamala wato hijab ko jilbab da kowa ya santa cikinsu. Da wannan kalar ‘dressing’ din ta riga ta suffantu, tun shigarta jami’ar Ahmadu Bello. To da tayi aure ma ba abinda ta canza illa shi Zayyan dake koraffin Hijabin ya daina burgeshi yanzu, don har a cikin gida fama yake da ita akan ta saka masa suttura irin wadda yake sayo mata ya kawo mata, amma saidai ta boyesu a kasan akwati. In kayan kwalliya ya sayo ya kawo mata kuwa don tayi masa kwalliya a gida to su Rayyah da Sabah da Rayha take aikewa Dandume.
Har rannan wani coursemate dinta mai karambani da shishshigi mai suna Balarabe ya kasa shiru yake tambayarta, shin ko Zayyan Rafindadi biological Yayanta ne? Don yaga suna tafiya gida tare yanzu kullum, yana goyonta akan Lifan dinsa.
Ko kusa bai kawo aure a tsakaninsu ba, sabida Zayyan nada iya taku, baya bada wata kafa da zaka gane akwai alaqar aure tsakaninsa da Safiyyah Dandume, sai ta karatu a makaranta.
Ita kanta a makaranta “Malam” take kiransa, sai sun dawo gida zaka ji ya koma “Habiby”.
Safiyyah tayi murmushi tace da dan ajinsu Balarabe “eh, Mallam Zayyan Yayanta ne, kuma Malaminta ne”.
Bata kuma kara tofa komai akai bayan wannan ba, aka wuce wurin, wato aka bar zancen a haka. Amma shi dai Balarabe ya digawa abuna yar tambaya, don in ba Yayanta bane a kamala irin tata, bazata yarda ta dinga hawa bayan Lifan dinsa ba
Don haka take karatunta lafiya ba idon ‘yan ajinsu a kanta, musamman da Zayyan din baya daukar ‘yan level three. Level 1&2 yake dauka.
Library kuma bata fasa zuwa ba, ta wuni tana karatu acan da ‘Pink Travel Mug’ dinta na shan ‘hot coffee’. Allah ya sani she is addicted ga shan coffee, yana bude mata kwanya sosai. Musamman a lokacin da jarrabawa ta kusanto, ko in zata yi assignment, tana can library da pink travel mug dinta mai cike da hot coffee, to acan Zayyan yake samunta ya dauketa su wuce gida.
Har Kano Zayyan ya kaita sada zumunci wajen Yayarsa Zubaina, amma basu kwana ba, sun yi zumunci da ita da iyalanta suka dawo Zaria a ranar.
Sosai Safiyyah ta kwantawa Yaya Zubaina a rai, ta yaba da hankalinta da kamalarta, Zubaina ta kasa shiru har sanda zasu tafi ta kira Zayyan zaure kafin su wuce, ya dawo shikadai, sai ta rike hannunsa tana murmushi tace.
“Gaskiya Baffan Mama, ka gama yin dacen mata, ga kyau ga nutsuwa ga cikar addini, ka riketa da kyau, kaji Baffa?
Domin na hango maka mace tagari anan, wadda dukkan alamu sun gama nuna ta fito daga babban gida na tarbiyyah da addini, wadda zata baiwa ‘ya’yanka irin tarbiyyar da akeson ‘ya’yan musulmi su samu, a tareda Safiyyah”.
Zayyan ya gyada kai yana murmushi, ya kara jin son Yayarsa Zubaina, ita kadai ce ta yabi Safiyyah a danginsa, su sai dai suyi mockering dinta da diyar Alaramma ko ‘stammerer’. Sai kace fitowa daga tsatson Alaramman ba abun alfahari bane ko in-inar ita ta baiwa kanta. Yace.
“Nagode Yaya Zubaina. Na san you will always stand with me, akan duk abinda na kawo nace inaso.
Ko da kuwa ke abun bai yi miki ba zaki tayani son shi, da kula dashi. Ke kadai ce kika yaba da Safiyyah a cikinku. And I truly appreciate.
In sha Allah zanyi duk yadda kika ce akan Sophie, zan riketa amana, zamu rufawa juna asiri mu zauna lafiya”.
Da aka kwana biyu kuma ya kaita gidan Yaya Zubaidah a Batsari.
Tarbar ta sha banban tsakanin ta gidan Zubaina data ta gidan Zubaida, ko daga ruwan pure water biyu da aka ajiye mata akan plate aka shanyata a falo aka ce za’ayi magana da Baffa cikin daki, bayan daga nesa suka zo ko abinci bata basu ba, sai Baffa data janye uwardakinta tana masa korafin Baban su Amal ya hanata aikin da takeyi. Sabida yadda Mama ke yawan kiran Safiyyah diyar Alaramma yasa itama Yaya Zubaidah tuni tabi ta raina ajin Safiyyah tun kafin ta ganta.
Nan Safiyah ta gama gane ‘clear difference’ na halayen ‘ya’yan Mama, biyu sun biyo Baba Bello sak a komai (Zayyan da Zubaina), hudu sun kwashe Mama Fatu tsaf (Zubaidah, Zahra, Zaytoon da Hatoon).
Safiyyah a wannan dan tsakanin da take karatun digirinta na farko a Zaria, Zayyan na aikinsa na Lecturing, suna yawan zuwa Katsina gaida iyayensu, duk kuma sanda suka je Katsina sai sun shiga Dandume, sun shiga shekara ta biyu da aure yanzu, ta gama fahimtar halin dangin mijinta tsaf, don basa wata daya Zayyan bai kaita cikinsu ba. Musamman lokacin da Baba Bello ya kwanta wata ‘yar jinya.
Baba ya jima yana fama da larurar suga da hawan jini, amma basu taba kwantar da shi ba sai a wannan lokacin, kuma Zayyan ke kula da zarya da shi a asibiti, kullum yana hanyar asibiti dashi, don haka da aka baiwa Baba kwanciya don samun (bed rest) sai yayi tunanin maido Baba asibitin koyarwa na ABUTH kawai don dai yafi samun damar kula dashi da kansa, in yana kusa dashi saboda aikinsa, ya kuma ragewa kansa zirga-zirgar da yakeyi tsakanin Katsina da Zaria.
Sai hakan yasa takalihun abincin Baba da ake yi masa na musamman irin na masu ciwon suga a zaman asibitin ya dawo wuyan Safiyyah, ita ke kula da yi masa tsaftataccen abincin da ake masa na musamman, kullum ita keyi safe, rana da dare ta kai asibitin da kanta, to anan ne suka cakude da dangin Zayyan suke wuni tare har dare, wani lokacin Zahra da Zaitoon su kan biyota gidanta su kwana, da safe suyi wanka su koma asibiti tare, don autar Mama Hatoon na makarantar kwana har a lokacin.
A dan tsakaninnan kaf! Sophie ta gama banbance halin yayye da kannen Zayyan a kanta, dukkansu dinnan ra’ayinsu ya tafi daya dana mahaifiyarsu Mama Fatu akan rashin dacewar aurenta da Zayyan. A wurinsu ita ba tsarar aurensa bace, kamar wata alfarma aka yi mata da aka aureta, in ka cire mai saukin halin cikinsu Yaya Zubaina. Babu mai kallon kanta da gashi.
Abin mamaki ko a fuska Zubaina kadai ke kama da Baba Bello, dukkansu da kyakkyawa Mama Fatu suke kwasar kama har Zayyan din, kuma ita kadai take da halinsa na accommodating kowa ya rabeta, irrespect of social status. Safiyyah ta fahimci ‘yan uwan Zayyan da mahaifiyarsa sun raina ajawalinta, suna ganin bata isa ya aureta ba, kamar ajinta yayi kadan da auren Zayyan dinsu, matsayinta bai kai da auren dan uwansu/dan ta ba, balle ta samu matsayin shigowa cikin su ta hada kafada dasu a matsayin surukarsu/matarsa. Ta kan tambayi kanta to ko mai yasa ahalin Mama suka raina ajawalinta haka? Ita bawulakantacciya ba? Daga bisani ita da kanta ta gane sabida ita ba ‘yar masu kudi bace, kuma ba ‘yar gayu gangariya irinsu ba, ko daga yanayin sutturarta sun raina mata, wadda tasha bambam data ‘ya’yan Mama da abokan huldarsu.
Har ila yau, a wannan zaman ne ta fahimci tsakanin Zayyan da Zubaina akwai fahimtar juna mai kyau fiyeda tsakaninsa da babbar Yayarsu Zubaida.
Zubaina kamar ba sakuwarsa ba, tunda kowa ya san sako da sako ba’a shiri. Amma su shiri suke kamar aminai. Zubaina ita Zayyan ke bi a haihuwa, wato ita ta saki nono ya kama.
Ita kadai ke taya shi son Safiyyah bilhaqqi, take kuma girmama tushenta, asalinta da nasabarta, saidai kuma ita a nesa take, ko jinyar Baba da akeyi yanzu sau daya ta samu Malam Mahi mijinta ya barta tazo, kuma bata kwana ba a ranar ta koma.
Zubaina ce kadai bata samu ilmin zamani mai zurfi a cikinsu ba, kuma bata aikin gwamnati, don daga sakandire aka yi mata aure, mijinta kuma baya ra’ayin ta cigaba, sai ya bata jari take sana’ar poultry, amma hakika Zubaina tafi Zubaida kyakkyawar alaqa da kowa.
Zubaida kuwa babbar ma’aikaciyace a Batsari Local Government. Su kam su Zubaida, Safiyyah kan fada a ranta, duk an tsotso hali daga Mama, na raina mutanen da basu kaisu a status na rayuwa ba, halinta ba wanda suka bari sai ma wanda suka dara ta.
Abin nufi, ‘ya’yan Mama kullum suna kallon kansu da matsayin mahaifinsu da shaharar sunansu a Katsina, cewa su iyalin Bello Rafindadi ne, kamar diyan gwamna haka su Zahra ke jin kansu, in kai ba kowa bane a Katsina, iyayenka basu yi suna kamar nasu uban ba, kuma basu taka wani matsayi a boko ba, to ‘ya’yan Mama da ita kanta basa wata alaqa mai dadi da kai.
Ta gane wannan halinsu ne na cikin jini, akwai girmama abun duniya da daukaka sama da asali da nagarta.
Don haka Safiyyah ta zama kamar wata ‘yar karere a cikinsu, saboda yadda suke wareta gefe su manta da ita a wurin a zaman asibitinnan, kamar wata ‘yar aikin Mama haka suka dauketa. Don haka sosai Safiyyah ta kama kanta daga shiga sha’aninsu.
Bayan ritayar Baba Bello daga jami’ar Umaru Musa, kafin ciwon nan ya ci karfinsa, Arch. Bello ashe ya tara duniya a boye, domin ya koma ya kutsa sosai cikin sha’anin (Real Estate Business).
Baba Bello ya samu arziki ya kuma samu budi mai yawa akan harkar zanen Estate da ginasu da bada hayarsu cikin dan lokaci, ya samu alkhairi akan real estate nan da nan, har fiyeda lokacin da yake shugabantar jami’ar Katsina bakidaya.
Wannan budi da Baba ya samu rana daya sai girman kai da fahari (pride and arrogance) ya karu ga ‘ya’yansa mata, da mai dakinsa Haj. Fatu Rafindadi, mulki da zuba iko a cikin gida ya karu ga matarsa Mama Fatu, kai kace itace first lady ta lokacin watau “Turai ’Yar Aduwa”, don a lokacin nan da yake tunowa in har bai manta ba, kuma ya tuna daidai, marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar Aduwa ne yake mulkin kasar Najeriya.
Kodayake Mama ai first lady din ce, amma ta Baba Bello kadai.
Da wuya tayi laifi a gun Baba, don ko bata kyautatawa kowa ba, shi ya shaida tana kyautata masa.
Arzikin da Baba Bello yaketa samu farat daya akan harkar ‘real estate’ ya sa competition ya shigo cikin sha’aninsu, ya samu abokan hamayya na sana’a sosai, saboda cikin dan lokaci Baba Bello ya kudance yayi suna a harkar Real Estate, ya zamana yanzu harkokinsa da zaman sa yafi yawa a jihar Lagos.
Domin acan ne yafi karbar kwangilar zanawa da gina Estates har daga gwamnatin tarayya yana karba, daga baya daga masu private companies ma irinsu “Lange and Grant” da “Julius Berger Nigeria” Baba na samun kwangilar zane da gini daga hannunsu da aka gane shahararsa.
Rayuwa ta wani irin canzawa iyalin Baba Bello rana daya, fiyeda sanda yake aikin gwamnati a jami’ar Katsina.
Wani abu da zai burgeka ya kuma baka mamaki da Zayyan Bello Rafindadi shine, ko sau daya arzikin mahaifinsa na yanzu bai taba canza tsarin rayuwarsa daga wadda yakeyi a baya ba, kamar yadda ta kannensa mata ta canza. Yana nan a yadda yake. Zayyan mijin Nana Safiyyah. Don hatta Zahra da Zaitoon yanzu motar kansu suke ja mulmulalla, kalar da kowaccensu ta zaba Baba ya sai mata.
Shi kam har lokacin yana nan a yadda yake rayuwarsa tun fil azal, irinta malaman jami’a ba yabo ba kuma fallasa. Karamin Lecturer ne mai jini a jika da farin jini a wurin aikinsa, irin malaman jami’ar nan ne ‘yan zamani da suka san ciwon kansu matuka, suka san muhimmancin ilmi da amfanin neman na kai. Wadanda basa taba daukar samun wani a matsayin abin tinkahonsu ko dogaronsu.
Shi bai dauki rayuwar nan ta duniya da zafi ba, yana rayuwa within his own income, ya yarda komai na dan adam lokaci yake dashi, kuma arzikin Baba Bello ba nasa bane. Gumin Baban ne.
Arch. Zayyan Bello Rafindadi kenan. Wanda kowa ya san shi ya san shi da babur dinsa LIFAN mai lafiya guda daya da yake matukar kula dashi, tun wanda Baba ya bashi as gift din aure yau shekara uku kenan yana kula da lafiyar abinsa, da matarsa daya kamar ransa gimbiyar zuciyar Zayyan “Mrs. Safiyyah Rafindadi.
Ya kan yawan gayawa Safiyyah yadda yake matukar son ‘Bike’ din nasa da yake kira ‘Lifany’.
Yace in yana tukashi tana bayansa ta dafe masa suna tafiya wani irin nishadi yake tsintar kansa a ciki, wanda yafi gaban yadda zai iya fasaltashi. He feels himself on top of the world’s greatest happiness and excitedness. Safiyyah sai tayi ta dariya don itama tana son ‘Lifany’ din nasa. Tana wanke masa shi duk sati da kanta a harabar flat dinsu.
Don koda Baba yace zai canza masa da mota lokacin da Mama tayi korafin an sayawa su Zaitoon motocin kansu, yara dasu, an bar Baffanta da fama da tsohon Babur, shi da yake da nauyin iyali a kansa, Zayyan ki yayi sam, yace,
“Baba kyale Mama kawai ta tsani Lifany na rasa dalili, ni kuma wannan Lifan din na riga na saba da ita, ina sonta sosai fiyeda zatonta, jinta nake kamar jirgin sama, kuma ta isheni rayuwa a yanzu, ban san gobe ba. Koda zan sayi mota nafi son ya zama cewa da gumin aikina na sayeta. Baba kayimin komai a rayuwa tunda ka bani iyali to ka gama role dinka as a father, bai zama dole sai ka saya min mota ba.
Daga gidana zuwa cikin makaranta dai Allah na tuba babu wani nisa, in mun so ma a kafa muke takawa nida Sophie don motsa jiki da karin lafiya”.
A kullum Prof. Rafindadi yana matukar jin alfahari da godewa Allah da ya bashi Zayyan, Allah bai bashi wadatar ‘ya’ya maza ba sai Zayyan tilo a cikin mata, ya kuma zama jarumi a cikinsu, daya tamkar da goma.
Halinsa duk na dattako ne da ya banbanta dana sauran ‘yan uwansa mata, masu son jin dadi da rayuwar high taste anyhow, flamboyant life itace rayuwa a gun ‘ya’yan Mama.
Mama saida ta san yadda tayi ta kalallame Baba da lallami ya sayawa Zahra da Zaitoon motocin da suke hawa yanzu ba don ran Baba ya so ba, wadanda suke shekarar karshe a jami’ar Katsina a lokacin, don dai competition da kawayensu ‘ya’yan masu akwai.
Da wuya kuma Mama tayi umarni Baba ya tsallake ko baya so. Don yakan ce dasu komai ya samu a rayuwarsa tareda ita (Mama) suka sameshi. So baya iya yi mata iyaka da duk abinda ya mallaka.
Baba na matukar jin dadin yanayin rayuwar Zayyan dinsa, bai dauki rayuwar ‘ya’yan masu kudin Katsina ya dorawa kansa ba, wai don ganin budin da Babansa yake samu a yanzu, kamar wanda aka yiwa wahayin arziki ya sameshi a tsufansa.
A kullum Zayyan sakawa yake a ransa arzikin Baba ba nasa bane, gumin Baba ne, daya rayu yana fafutukarsa, Allah kuma ya rubuta bazai samu cin gajiyarsa ba sai a shekarun tsufansa bayan ritayarsa.
Irin manyan kwagilolin zanen Estates da gine-ginensu da Baba yake samu yanzu a Lagos, sanda yake aikin gwamnati bai samu ko kwatan-kwatansu ba, don haka shikam bashi da wani buri a kan dukiyar Baba, bai sakawa ransa fahari ko amfani da dukiyar Babanshi da ba guminshi ba.
Yafi maida hankali ga neman na kansa ta hanyar murza albarkar bironsa. Kullum yana gayawa kansa saida Baba ya sha irin wannan wahalar a kuruciyarsa, sannan ya samu nasibin da yake samu yanzu a shekarun girmansa.
Baba kuma nada yaqinin cewa, kyawun turbar rayuwar da Zayyan yake kai a yau, har da influence na auren macen kwarai, wadda ke taka rawa sosai wajen taya shi zama mutum nagari a cikin gida da waje, wato maidakinsa Safiyyah Usman Dandume, tana da hannu dumu-dumu wajen kara dora shi a kan turba sahihiya.
Rana daya ciwon Baba ya rikice, aka kuma rasa gane kan ciwon, tsakanin sugar dinsa da hawan jini likitoci sun kasa gane wanda ya kwantar dashi.
Baba Bello ya sha jinya mai tsayi a ABUTH. Safiyyah kuma tasha hidima da dawainiya da girke-girkensa da sauran hidimarsa a kullum, ta sha albarka kwando yafi dubu a gun Baba Bello, kullum ta kawo masa abinci tace ya tashi yaci da irin kalar addu’ar da zai yi mata mostly akan Allah ya bata ‘ya’ya nagari masu irin halayenta.
Bazai taba manta yadda a jinyar nan da Baba Bello yayi, kullum suka kebe shi da Baban a bayan idon Safiyyah, sai ya jaddada masa bukatarsa ta cewa ya kula da matarsa Safiyyah. Don Baba shikadai yasan wacece matarsa Mama Fatu? Macijin sari ka noke ce, akan duk abinda bata ra’ayi. Ko kuwa green snake under green grass idan bata son abu.
Duk da cewa Arch. Bello yafi karfin gidansa, kuma Mama na jin maganarsa, amma kowa da halinsa bai isa ya canza mata hali ba, shikadai yake iya tsawatar mata in tayi ba daidai ba, ya san wasu lokutan Mama sai a hankali, musamman in mutum bai yi mata ba, wato baiyi daidai da zabinta ba, yana sane da cewa tana ragawa Safiyyah wani wulakancin sau tari saboda ganin idonsa, don ta san bazai dauka ba, baya bari tayi mata wani abu da bazata ji dadi ba in dai yana wuri.
Baba yana iya kokarinsa wajen kulawa da Mama, wajen yi mata nasiha da karkato da hankalinta kan rayuwar duniya kalilan ce, hatta zumuncinta da danginta na Rumah sai ya tashi tsaye a kai take dan yi.
Lokacin da ya fahimci sam bata damu da alaqa da danginta ba, saboda basu da shi, sai kwashe-kwashen matan manya irinta, Baba bai kyale abin haka ba, haka kawai sai ya shirya kayan abinci ya cika bayan motarsa yace tazo su tafi Rumah su gaishesu.
Baba shine kamar uwarta kuma shine kadai ubanta mai sata a hanya, don iyayenta sun jima da kwantawa dama.
Baba Bello shikadai yake iya shaping din Mama Fatu ya tankwarata ta yi abu ko bata so, ya san halin Mama sarai bataso kowa ya rabeta sai ‘ya’yanta kawai, koda kuwa nata danginne, shikadai yake iyawa da halin Mama ya biyar da ita cikin lislama su zauna lafiya, kuma shikadai ya iya zama da ita, amma mutane da yawa musamman danginta na Rumah basa jin dadinta, yafi kowa sanin halinta ciki da bai dinsa, ya kan ce.
“Fatima zuma ce ga zaqi ga harbi”.
A zaman jinyar nan tasa da yayi a ABUTH yana ganin yanda Mama da ‘ya’yanta ke ware Safiyyah su mayar da ita bare a asibitin, sun mayar da ita kamar’yar aikinsu, saidai ka ganta ita kadai a can gefensu tana karatu a cikin wayar hannunta kamar basu san da kasancewarta a wurin tare dasu ba.
In har ba Zayyan yana nan ba, sai ya shigo wurin take dan sakewa don shikadai ke janta da zance, ko sakota cikin hirarsu.
Baba ya san shikadai yake iya yiwa Mama magana taji, baya taba saka kara Mama ta tsallake. To bai cika son yana mata gargadi akan Safiyyah ba, tun bayan wanda yayi mata na ranar haduwarsu ta farko, don kada ta tsaneta.
Ita Safiyyah din dai rannan yayiwa magana cikin sirri cewa “tayi hakuri da Mama, ta kasance mai hakuri da kowa zama ko alaqa ya hadata dashi”.
Saboda tun wancan fadan da ya taba yi mata akan Safiyyah din, lokacin da taci fuskarta a gabansa, da tace Zayyan ya rasa wadda zai dauko musu sai diyar Alarammomi mai tsamin baki (stammerer).
Baba da yayi mata fada batace komai ba, sai lokacin kwanciya barcinsu tayi masa martani, inda tace “ta lura yana son Safiyyah dinnan da yawa. Ita kuma bazata so su dinga samun matsala shi da ita akan suruka ba”. Tun daga lokacin yake kiyayewa da yi mata magana akan Safiyyah kada ya sayo mata tsana a wurinta.
Haka duk abubuwan dake faruwa a lokacin jinyarsa yana lura. Waretan da suke yi shi yafi komai saka shi a damuwa. Shi ya san Mama bata yin Safiyyah tun farko. In kuma Mama bata yin ka, ba wanda ya isa yasa ta yi ka.
Mafi a’ala gareka shine ka yi nesa da shiga sha’aninta.
Zayyan ya kara rintse idonsa a lokacin da tunaninsa yazo nan, ya ciza lebbansa na kasa cikin tuno rayuwar Baba Bello. It was a bitter past moment da baya ko son tunawa, amma dole ya tuna presence din Baba cikin rayuwarsu. Baba ya so Safiyyarsa, ya so zamar mata bango abin jingina a cikin iyalinsa.
Aka ce Allah baya barin wani don wani yaji dadi, shekarar Zayyan uku da auren Safiyyah Allah ya karbi ran mahaifinsa Arch. Prof. Bello Rafindadi.
A wannan shekarar da Baba Bello ya rasu, shugaban kasa ‘yar Aduwa shima ya rasu. Jihar Katsina bakidaya ta gigita ta girgiza. Katsinawan Dikko sun dimauta. Anyi rashin da za’a dade ba’a mayar a Katsina ba.
Safiyyah ta rasa mai kaunarta da gaskiya a family din Zayyan, wanda yake tamkar ‘shield’ ko ‘savior’ a gareta, Late Arch. Prof Bello Rafindadi.
Mutuwar data gigita iyalinsa, da daukacin al’ummar jihar baki daya.
A ranar lafiya kalau yayi sallar isha’I ya koma ya kishingida, kafin gari ya waye sai barci mai nauyi ya daukeshi. Ashe Baba tafiyar kenan, don ganin gari ya waye hantsi na neman ya dubi ludayi Baba bai juya ba bai motsa ba bai kuma tashi yayi sallahr asubah ba, hakan yasa Mama shan jinin jikinta, don ta san Baba ko ciwo baya saka shi jinkirta sallah balle barci.
Ilai kuwa tana dubawa ta tabbatar Baba anyi shahadar daren Juma’ah. Ta kira Zayyan a waya a lokacin yana kan hanyar isowa asibitin da abincin safensu. Yaji muryar Mama cikin rishin kuka tana fadin.
“Na rasa bango na Baffa, na rasa komai na. Bello ya tafi ya barni daku! Mazan duniya sunyi kaura, sun barni a duniya da tarin marayunsu, sun amsa kiran mahaliccinsu”.
**** **** ****



