⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 12: Chapter 12

Fadin halin da Zayyan ya shiga na rashin Baba yayi kadan biro ya rubuta shi, a ranar aka wuce da gawar Baba Katsina, dimbin al’ummar ciki da wajen Rafindadi sukayi jana’idarsa a washegari.
In kaga Safiyyah da Zayyan lokacin amsar makokin Baba suna daka koyaushe, ko fitowa cikin jama’a basa yi, in ka gansu duka sai sun baka tausayi, sun yi laushi kamar an zare musu laka da bargo, musamman Safiyyah, da take ji a jikinta mai sonta kwalli daya cikin gidan Rafindadi ya tafi ya barta cikin fitinannun iyalinsa, wadanda ita da kanta ta shaida bata da farinjini a wurinsu.
Malam da Ammi tare dasu Sabah sun zo musu ta’aziyyah daga Dandume, sun wuni sur tare da ita a gidan makokin, Malam Usman ya girgiza kwarai da gushewar surukinsa na kwarai wanda suka zama tamkar abokai wato Baba Bello, saida aka yi sadaqar bakwai ne mutane suka fara watsewa Safiyyah da Zayyan ma suka koma Zaria.

Tunda suka dawo gida kuma sai Zayyan ya komawa Safiyyah tamkar yaron goye, ya jangabe a kwance ya kasa tsinana komai, komai sai ta kawo masa inda yake har Ruwan alwala ta kuma saka masa naci sannan zaiyi, abinci kuwa sai ta bashi a baki, kafin ta fahimci tamkar ciwon damuwa na wucin gadi ya kama shi (depression) don shikadai yasan halin rashin da yake ciki, shikadai yasan girman rashin Baba da yayi, da kuma irin kewarsa dake nukurkusar zuciyarsa da azabtar da ruhinsa bayan ya kaishi makwancinsa na gaskiya, don yasan rayuwa bazata kara koma masa yadda take a baya ba, tunda babu Baba.
Har ila yau, damuwarsa takan karu idan yana kintato girman burden din da ya hau kansa yanzu, na kula da mahaifiya da marayun kanne mata wadanda Baba Allah bai yi zai aurar dasu da hannunsa ba, wannan ma ya taka muhimmiyar rawa wajen jefa shi a halin da ya samu kansa na zama depressed, ga wani zazzabi-zazzabin damuwa da masassara dake sakadarsa cikin dare, alamun son shiga lalurar ‘anxiety’ sun gama bayyana kansu a tare dashi, sallah kadai yake iya tashi yayi in Safiyyah ta matsa masa, ko aiki Zayyan ya daina zuwa.
Safiyyah a kan haka saida ta dangana da dauko Malam wato mahaifinta, tun daga Dandume yazo har Zaria, tana kuka tace Malam yazo ya taimaketa Zayyan ya zama daddawar daka yafison ta barshi yayi ta kwanciya a gado kamar ruwa, ya daina fita aiki, karon Malam Usman na farko kenan da taka kafarsa gidan diyarsa ta farko da yake kira Nana Safiyyah.

Malam Usman ya samu Zayyan har kan gadon Safiyyah, ya rufeshi da wa’azi da nasiha mai shiga jiki da huda zuciyar musulmi, akan ya karbi rashin mahaifinsa da kyakkyawar zuciya da tawakkali cikin godiya ga mahaliccinsa, yace hakan shine cikar imanin bawa.
Har ila yau, Malam yace masa, ya tuna nauyin da yake rataye kansa yanzu, na uwa da ‘yan uwa, sai ya zama namijin duniya sosai zai iya saukewa musaman sha’ani na mata, yace ya tsaya akan zuciyarsa kada ya bari ta rinjayeshi yayi fushi da yin Allah.
Allah yafi shi son Baba Bello, shi yasa ya dauke abinshi, a sanda kowa ke tsaka da bukatarsa. Ko ya san cewa mafi yawan mutanen kirki basu cika jimawa a gidan duniya ba?
Malam Usman bai tafi ba saida yasa Zayyan ya shiga toilet yayi wanka, yayi askin fuska da yanke akaifarsa, ya canza kayan jikinsa daga jallabiyyar data jima a jikinsa, ya kuma umarceshi da ya daure yaje ya ga Mama don Safiyyah ta gaya masa tun baya sadakar bakwai bai kuma komawa Katsina ba, kuma baya kiran kowa a waya, yama kashe wayarsa tun da jimawa, Mama ko ta kira bata samunsa, fadin ranta kuma ya hana ta kira Safiyyah tace ta hadasu, Malam ya tuna masa cewa shine karfinta a yanzu don haka ya dinga zuwa ganinta akai-akai fiyeda baya.

Bayan tafiyar Malam Usman a daren ranar Safiyyah itama kwana tayi lallashin Zayyan, tana mai tunasar dashi muhimmancin karbar kaddara kyakkyawa ko mummuna. Tace.
“Shi kam Baba ai kowa ya san tasa tayi kyau, tunda ya rabu da kowa lafiya, ya mutu bai yi satar dukiyar al’umma ba, babu bashin kowa a kansa. Dubi yadda al’ummar musulmi suka yi dafifi don raka shi masaukinsa na gaskiya.
Hakika Baba ya samu kyakkyawar shaida ta kwarai, irin wadda kowa ke burin samu a karshen rayuwarsa Habiby.
Baba abin so ga Dalibansa, kada ka so ka ga yadda dalibansa suka dinga tuttudowa zuwa ta’aziyyarsa, da sauran al’ummar Katsina bakidaya”.
Safiyyah bata gushe ba cikin lallashin, tareda gaya masa kyawawan halayen mahaifinsa da kowa ke fadi, wadanda sukasa ake masa kyakkyawan zato.
Kawai sai ya mika hannnu ya janyota jikinsa, tabi umarninsa ta kwanta lumm a kirjinsa, su duka suna sauke ajiyar zuciyar tuna Baba Bello.
A karshe sai da ta dangana da inganta masa daren, yadda biro bazai iya bayyanawa ba sannan ya fara regaining consciousness, wani yanayine suka samu kansu na tsantsar soyayya mai shiga rai da farantawa juna rai, bayan nan haka suka kasance manne da juna cikin duvet a tsayin daren bakidayansa.

Fatan ta da burinta kadai Zayyan ya dawo hayyacinsa, ya karbi rashin Baba in good faith, so take ya koma Zayyan dinsa data sani, mai karancin far’a da rashin faram-faram, wato ya dawo normal Zayyan dinsa na baya, shikuma Zayyan bata sani ba, ya yanke tsammani da hakan, don ji yake a jikinsa bazai taba warwarewa daga rashin Baba har abada ba.
Baba ya tafi ya bar shi da wata irin kewarsa, ga nauyin mahaifiyarsa, kanne mata da ya yayye mata shi kadai namiji kwal a cikinsu da ya hau kansa yanzu.
Wannan kadai in ya tuna yana kara saka masa damuwa, don ya san yadda Baba ya rayu wajen sonsu da nuna musu kauna hadi da kyautatawa iyalin sa ba mai iya maye musu wannan gurbin.
Iyalin Baba basu san babu ba, basu san su nemi wani abu su rasa ba. Kome sukeso shi yake basu in dai baifi karfinsa ba.
Baba tsayayye ne akan bukatun gidansa da tarbiyyar su Hatoon, duk da ba koyaushe yake samun yadda yake so daga Mama akansu ba.
Shi kam har bai san ta ina za’a fara da maye musu wannan babban gibin ba.
Maye gurbin Baba babban maye gurbi ne mai wuyar samu. Ko yace wanda bazai samu ba. Bazai taba mantawa da watarana da Hatoon tace bata son abinda aka girka a gidan, haka Baba ya dauki mota ya fita cikin dare ya nemo mata abinda take so, haka da Zaitoon bata cin Biredi sa Gurasa Baba Gurasa yake saya mata kullum har rasuwarsa bai fasa ba.

Duk sanda yaji mai zuwa kano sai yayiwa Zaitoon sautun Gurasa. Ire-iren kulawar Baba Bello kenan akan iyalinsa, in dai akan farin cikinsu ne baida namba two, ko ta ina zai kwatanta zama shi a garesu???
Baba Bello daya ne cikin dubu, ko a cikin iyaye, ta fuskar kula da iyali, komai cewa yake “my family first”.
Kasancewarsa shikadai namiji a cikin su a ganinsa bazai isa hujjar da zai iya zamewa ahalin Baba makwafinshi ba, ko mayewa ‘yan uwansa da uwarsu wawakeken gurbin da Baba ya bari. Gabadaya wannan tunanin yasa ya raunana, babu sauran jarumta ko kankani a tare da shi, sabida tunanin halayen Baba masu wuyar imitating.
Ba rabo da gwani ba, aka ce maida kamarsa!
**** **** ****

Da wannan mutuwar jikin da raunin zuciyar yake kwana yake tashi tun rasuwar Baba Bello. Wanda shi ya kassara shi, ya kuma karar da duk wani karsashin da yake dashi, ya kusa sabbaba masa ‘anxiety disorder’.
Duk kuwa da kokarin Safiyyah na son (reviving mood) dinsa da yi masa addu’a a ruwa ta bashi ya sha, hadi da nau’ikan kulawa da soyayyarta na macen kwarai wadda ta damu da situation din mijinta, mijinta Zayyan da kusan suke sharing the same feelings itada shi a komai. Soyayya take gwada masa gangariya akan gadon barcinsu, but he hardly respond. Komai ya fita kansa fit, including soyayyar.

Shi kawai ya san bazai taba mayar da farin cikin da ya samu a rayuwar da yayi tare da mahaifinsa ba, tun daga haihuwarsa har girmansa a jikin Baba Zayyan ya rayu.
Kalamansa ne da support dinsa suka raineshi, har ya zama jarumin da ya zama. Yanzu kuwa da Baba ya tafi ya barshi, ya tabbata ya tafi harda jarumtarsa.
Sabida haka ba wani abu na farantawa ko wata soyayya da wani ko wata zai nuna masa yanzu da zata hana shi damuwa da rashin Baba da yayi. Saidai ya kalleka kawai. Har sai bayan zuwan Malam Usman ne ya dan samu canjin yanayi kadan.
Da safe suna karya kumallo, ya kalli Safiyyah, sai ya ga itama duk ta rame saboda damuwar da yake ciki, kamar ma ya fita kuzari yau, ya sa hannu a habarta yace “Sophie”, sai ta dago a hankali ta dube shi sai ga kwalla fal! A kwance cikin idonta.
Zayyan yasa yatsarshi manuni ya tabo kwallar ta idasa gangarowa, yayi mata murmushi yace “haba Sophie na, ban sanki da saurin karaya ba, in duk muka karaya wa zai cigaba da karfafa wani? Kiyi hakuri dani kinji, kici gaba da karfafani, ni nasan situation dina ba mai wucewa bane in har zan tuna Baba.

But I always pray that it will come to pass idan ina ganin ki a tare dani cikin walwala”.
Ya fadi hakan ne da ya yana tuno wasu kalaman Baba Zayyan akan Safiyyah, watarana suna hirarta yace dashi “Zayyan ina fada maka ka riketa da kyau, wannan matar kwarai ce, kada ka bari ta kubuce maka, ita kadai ta isheka rayuwar duniya kamar yadda Mamanku ta isheni, ni nasan ‘yar baiwa ce, tsatson albarka mai iya tattalin farin cikin mijinta, ko a fuskarta mutum zai karanci kaunarka, ka tattalata ka sata farin ciki kullum wallahi kadara ce ita babba gareka”. Sai yaji murmushi ya subuce masa. Yana shafa habar Sophie yana fadin “Sophie diyar Babanta, Baba Bello, I truly love you!”.
Murmushin da Safiyyah ta dade bata gani daga gareshi ba, watakila tun kafin rashin Baba rabon da taga murmushinsa. Yace.

“Zan wuce Katsina yanzu, amma bazan kwana ba in sha Allah, ki daina damuwa kinji Sophie na? Everything will be alright da karfin tawakkali.
My mood will be restored soon, idan wannan shine damuwarki. Zan yi kokari in dawo Habiby dinki da kika sani, kin ji Sophie?”
Safiyyah ta kusa shidewa don farin ciki, domin taji dadin kalamansa sosai, ta kasa boye jin dadin data yin ta hanyar fadawa jikinsa ta rungume shi, ta sumbace shi saman lips dinsa yayi maza ya kwaci kansa yana dariya yace “kada ki karya min alwalar walha” tace ba damuwa sai ka daura wata, nasan wannan ta riga ta kwance. I have no idea na yadda nayi missing my man anan wurin…”.
Ta fada tana rufe idon da ya bashi dariya, har yana tantama anya Sophien shi yau take masa wannan soyayyar? Safiyyah sarkin kunya sarauniyar ustazan Dandume? Inama ta dore da hakan, da ya zama dan sarki. Amma ya san mawuyaci ne ta dore din, kunya a jininta take. Da kyar ta bar shi ya tafi, don sai da aka yi alwala mai dalili, sannan ta bashi sakon gaisuwarta ga Mama dasu Zaitoon, ta rako shi har kofar gida.
Safiyyah bata koma gida ba sai da ya hau okada (babur) din da zata kai shi tashar da zai hau motar Katsina.

A farkon shiga unguwar Rafindadi ya sauka daga kan Achaban da ya dauko shi daga Tasha, ya taka a kafa, da dan nisa kadan kafin ya isa gidansu, sannu kan hankali yake takawa don isa zuwa kofar gidansu.
Ya sauka tun daga dan nesa da gidan ne don kawai ya motsa kafarsa, don ya dan dade bai taka ta sosai ba, hakan yasa ya samu damar da ya gaggaisa da jama’ar unguwarsu. Suna kara yi masa ta’aziyya. “hakika Baba Bello na kowa ne, Allah yabamu hakurin jure rashinsa” yadda ‘yan shiyyar Rafindadi da suka hadu a hanya suke yawan fada masa kenan.
Tun daga bakin kofar gidansu da ya sako kai ya shigo cikin harabar gidan, Zayyan ya kara gayawa kansa “lallai bangon gida ya fadi!” kamar yadda Mama tace. Wato Baba Bello ya barsu. Ya subhanallah! Meyasa yayi wannan dadewar bai zo gida ba ina tawakkalinsa da imaninsa suka je suka barshi?
Saboda da shigowarsa harabar gidansu yaga hatta fulawoyin gidan kansu, da grass carpet duk sun fara bushewa, kamar an shekara ba’a basu ruwa ba, alamu ne na rashin samun kulawa kamar da.

Abin mamaki ma’aikatan gidan sun fara watsewa wai ace daga rasuwar Baba, ko arba’in ba’a yi ba, ko a tunaninsu an daina biyansu ne yanzu, oho! Ko kuma don ya dade bai zo Katsina ba? Mama kuma ya san bata tasu take ba a wannan lokacin da take cikin alhini da Takaba. Maigadin Baba Malam Ilyasu ne kadai bai tafi ba. Ko dama can shi dan amanar Baba ne.
Busassun ganyaryaki duk sun cika harabar wajen ba’a share ba. Hakanan yake jin kararsu duk takun da yayi suna bada kara rakakas-rakakas na bushewa.
Wannan abu ya yiwa Zayyan ciwo. Yace yau gidansu ne za’a maida kango as early after the demise of Baba? Malam Ilyasu na gaisheshi bai ko amsa ba don bacin rai, kawai zuciya ta kawo shi wuya, ya fara fada ta inda yake shiga bata na yake fita ba akan Dattijon, har ya manta da shekarun Baba Ilya.
“Baba Ilya, yaya akayi aka bar gidan haka babu shara, sai kace bola?

Yaya aka yi shukoki suka mummutu haka ba kwa basu ruwa da taki ne? Motocin Baba ne sukayi irin wanan kura haka? Saboda babu Babana ko? Saboda ba’a biya ku kudin wannan watan ba? Ko babu mutane da suke rayuwa a cikin gidan ne?”
Nan Malam Ilya ya sadda kai, ba ciwon fadan da yaron ke masa yaji ba, a’a ya san feeling dinsa na yanzu, kamar baya cikin hayyacinsa yake maganar. Shima sai kewar Alhajinnasu ta zo masa har saida ya share kwalla, da kyar ya dafa kafadun Zayyan yana lallashinsa, yace masa “kayi hakuri Zayyanu, inna kira wayarka bana samunka, Hajiya kanta tace bata samunka a waya wai ta rasa lambar maidakinka cikin wayarta, naso in gaya maka Habu ya koma garin su tun bayan bakwai, wato mai kula da shukokin gidan, shikuma Umaru mai wankin motoci da share-share shima yace ya samu wani aikin don haka ya tafi, Bala direba kuwa ko sallama bai yimin ba na daina ganinsa”.
Zayyan yace a ransa “dan adam kenan! Babu komai, it is well. An gode”.

A fili kuma yace “kuma da babu Habu ba Umaru ba Bala a gidan, saboda su butulallun Allah ne, kai sai ka kasa share harabar gidannan ko sau daya?”
Shi bai san ba su Habu kadai ba, duk ma’aikatan cikin gida mata ma sun ware, don Mama tace bata bukatar kowa, Ankudi kawai tace ta zauna to itama tace zata ganin gida kafin sadaqar arba’in amma har yau bata dawo ba.
Daga cikin gida Mama ta jiyo tashin sautin Zayyan yana magana da Baba Ilya cikin fada-fada, take cema Hatoon “ke duba min ki gani naji kamar muryar Baffana yana fada a waje, jeki gano min shi da waye? Dama ashe Baffa ya iya fada haka?”
Hatoon ta leka ta taga ta ganshi, tace da Mama “ai kuwa shine. Baba Ilya ne maybe ya taka sawun barawo”.

Ya tako zuwa cikin gidansu yana gayawa kansa sai yayi da gaske, ya kuma tsaya tsayin daka don ganin gidansu bai mutu ba, a rashin Baba Bello.
Dole ya dinga zuwa akai kai, fiyeda baya don tabbatar da lafiyar gidansu, lafiyar kannensa data mahaifiyarsu, da bukatunsu na yau da kullum.
Yayi sallama a falon Mama Fatu, Maman ta amsa daga zaune akan sallayarta, bata dade da idar da sallahr azahar ba ya shigo, ta ce.
“maraba lale da Baffan Mama, kuma Baffa daga zuwa sai fada? Kai da waye halan? Waya taba min Baffana magajin gida haka?”
Zama Zayyan yayi, yana ajiyar zuciya, ransa yana sanyi da ganin Mama, da kalaman maraba da take yi masa cike da murnar ganinsa, bai ce komai ba, sai sauke ajiyar zuciya yake yana kallon Mama cikin tausayi, ganin yadda duk kibar nan tata ta jin dadi ta zaizaye rana daya yasa yaji zuciyarsa ta dada tsinkewa, gabadaya ta rame, alamu ne na har yanzu bata wartsake daga dukan da rashin Baba Bello yayi mata ba.

Idanuwanta duk sun yi ciki sun kankance don yawan kuka, Mama ta koma yellow kamar mai ciwon shawara daga fara, kuma jajazir din Barumiyarta.
Gidan da kullum zaka samu kowa cikin annuri ana raha da wasa da dariya, a shiga nan a fita can, walwalar gidan data mutanen gidan duk ta kaura yanzu, tabbas Uba shine jigon gida, don haka Mama Fatu kam ta ga mutuwa irin wadda bata taba gani ba, saboda Baba Zayyan dinnan shikadai ta sani ta kuma rika a duniya a matsayin komai nata, bata gajiya da fadawa ‘ya’yanta “Bello ne uwarta shine ubanta” tunda bata tashi tareda iyayenta ta san dadinsu ba sai nasa, shine kuma danginta don ba abinda dangi suka kulla mata a rayuwarta, tun tana karama iyayenta suka rasu, aka rasa mai daukarta sai wata kanwar mahaifiyarta a Rumah, ya kuma aureta ne da kananan shekarun da basu fice goma sha biyar ba.
Sun yi zama na kauna da soyayya abar buga misali ita dashi da ‘ya’yansu, na kusan shekaru arba’in da doriya.
Zayyan yasa farin hankacinsa yana share fuskarsa da tayi jajawur da gumi, hawaye ya digo masa.
Mama ta taba ce ma Zubaina.

“Wannan shine hawayen Zayyan na farko data yi witnessing a shekarun girmansa”.
Ko ranar da Baba ya rasu, Zayyan yafi kowa jarunta da nuna dakiya, amma a yau ganin yadda gidan mahaifin nasa ma neman mutuwa yake yi ya jefa shi cikin wani hali na jin mutuwar Baba Zayyan fiye da kullum.
Da kyar Mama ta samu ya saki ransa suka soma gaisawa, tace ina Safiyyah? Yace a ransa yau wace rana Mama ta tambayeshi Safiyyah? Ya gaya mata tana lafiya tana kuma gaisheta.
Yayi fatan Allah yasa Mama ta fara son Safiyyah ne saboda rashin Baba Zayyan, tunda ta san yadda shi Baban yake sonta kamar ‘yarsa, in ta cigaba da nuna rashin kauna ga Safiyyah abin zaiyi masa yawa.
Sunyi hirarraki masu dama ranar, Mama tace “dama inata jiran zuwanka tunda kaki ko waya ka kunna, in gaya maka sakon Babanku Alhaji Murtala.
Zuwansa har biyu kenan bai sameka ba, kan maganar dukiyoyin Babanku dake hannunsa da wadanda ya sani dake hannun Lauyansa dama wadanda ke Banki, yazo ne kan batun, don yanaso zai tattarosu a raba gado ranar sadaqar arba’in, a raba marigayin da wannan nauyin”.

Kamar yadda ya riga ya sani Arch. Murtala shine babban aminin Baba Bello, kuma kamar Ubangida yake a gareshi a harkar Real Estate, shi ya fara budawa Baba harkar ya shigeta sosai da taimakonsa, bayan ritayarsa daga aikin gwamnati, saboda Alh. Murtala yanada connections sosai da gwamnatin tarayya, da kuma gwamnatin jihar Lagos.
Arch. Murtala Babangida Masari, abokin Baba Bello ne tun na kuruciya (childhood friend) wanda tun zamanin makarantar sakandire suke tare, kuma sukayi karatun jami’a shima tare a fanni guda, don haka lokacin da Baba yayi ritaya sai ya jawoshi jikinsa ya tsundumashi a harkar da yakeyi ta kwangilar gine-gine da zanen gidaje.
Zayyan yace da Mama cikin raunin murya da karaya.

“Kamar ana jiran matsawar Baba har an soma zancen raba gadonsa? Hakan bai yi wuri ba saboda Allah Mama?”
Mama tace “umarnin Allah ne ai na raba gado cikin lokaci, ba umarni na bane, ba kuma na Babanku Murtala ba, don a raba mamaci da nauyinsa, ba don komai ake rabawa da wuri ba ai don amfanin mamaci ne, ba kuma ni nace dashi azo a raba din ba, balle kace na fiya kankanba”.
Kafin Zayyan ya samu abun cewa sai Hatoon ta fito daga daki, ta gaida shi, ta wuce kitchen ta zubo abincin da Mama tayi yau, ta dawo cikinsu ta zauna gefe tana ci, Mama tayi mata kallon takaici tace.
“Shi Yayanku da yayi sammako yayi doguwar tafiya tun daga Zaria baki ga ya kamata ki bashi abincin ba? Hatoon, na rasa irin hakalinki, yaushe zaki girma ne? Kullum sai kin nunawa mutane halinki na rashin da’a da sanin yakamata da zaisa aga laifina wajen baki tarbiyya kike jin dadi ko?
Cikinki kadai kika sani. amma na dan uwanki ko oho ko?”

Karo na farko da zai iya cewa yaga Mama tayiwa Hatoon dinta fada, kuma a kan abinda ya kamata. Kullum saidai tayi laifi in an yi yunkurin yi mata fada ko gyara ta tare mata.
Yau dai yanata ganin sauyi a tareda Mama yayi fatan Allah yasa ta dore. Yana matukar son ace halin uwarsa yafi na kowa kyau. Ganin yadda Hatoon ta zumburo baki, dama aka ce icce tun yana danye ake tankwara shi…..
Hatoon zatayi shagwabarta yadda ta saba sai suka hada ido da shi, irin kallon da ya sakar mata yasa ba shiri ta mayar da bakin data zumburo ya koma daidai, daga yadda taga yanayinsa zai iya marinta yau, don haka ba shiri ta tashi da sauri, ta koma kitchen din ta zubo masa Sinasir, Waina da miyar ganyen alayyahu da tantakwashin Sa, da Mama tayi. Ta kawo gabansa ta lallaba ta ajiye ta gudu dakinta bata kara fitowa ba.

To dai da yake yana jin yunwar da gasken gaske, shiyasa ya yarda da tayin Mama, ya mike ya wanko hannunsa a sink din falo, ya dawo ya zauna, ya yiwa Sinasir da wainar nan kyakkyawan ci, ko babu komai Mamansa ce tayi da kanta.
Yayi kewar girkinta sosai, don Mama ta iya girki na gargajiya, yana ci suna hira da Mama, hirar da suka jima basu yi irinta ba, yace zai je gidan Baba Murtala din cikin satinnan ya same shi har Lagos din.
Haka ya wuni sur tare dasu har la’asar yana Rafindadi, har su Zahra suka dawo daga makaranta suka sameshi a gidan suka sha hira shida su, abinda bai cika yi dasu ba a baya, amma yau ya zauna cikinsu ya saki jiki da fuska ya ji damuwar kowaccensu da sha’anin karatunta, ya basu abinda suke bukata don tausayinsu yake ji su duka in ya tuna yanzu sunansu marayu, musamman sanin yadda Baba ke kula dasu, kafin yamma tayi ya juyo Zaria. Sai dare can ya iso gida.
Ya koma Zaria da kyakkyawan kudurin ba zai sake nisa dasu Mama ba, hakika suna bukatarsa a kusa dasu, domin yaga yadda rashin Baba ya ragaita su.
Ya barwa ransa in sha Allah ba zai kuma jimawa bai zo garesu ba.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *