⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 4: Chapter 4

Sanda Safiyyah ta dawo hayyacinta ta kuma fahimci a inda take kwance asibiti ne, tana kuma jin ciwo ko’ina a jikin ta, ba karamin firgici ta shiga ba. Likita da Nas din dake duba ta suka dinga kwantar mata da hankali, har suka ce ta godewa Allah da babu karaya, shi kuma wanda ya buge ta ya dinga bata hakuri, da kyar suka samu ta nutsu, tace dashi babu komai ai tsautsayi ne. Nan suka tabbatar mata an gyara gocewar kashinta na kafa dana hannu. Kuma mutumin yayi settling bill din gabadaya, aka ce ta bada lambar wani nata a kira su a gaya musu halin data ke ciki suzo su kula da ita, don bazata iya tafiya gida a yau, kuma cikin wannan halin ba.
Sai a lokacin Safiyyah ta tafi ga tunanin ainahin abinda ya faru, da kuma sanadin afkuwar hakan, tabbas gagarumin laifi ta yiwa Zayyan. In fact, ta ci amanar aure, bayan ta fita babu iznin mijinta yanzu da bokannan ya samu nasara akanta fa, itada Zayyan shikenan ko! Aurensu ya lalace kenan! Yanzu gashi alhakin Zayyan da Allah yasan bashi da hakkinta, yasa mota tayi awon gaba da ita, don Allah ya nunawa Zayyan bata ji wa’azinsa da ban bakinsa ba, har gashi yanzu bata san ranar warkewarta ba, babu kafar yawon asibiti neman haihuwa data zuwa gidan Malaman tsubbu, balle ayi maganar kafar komawa gida.

Kawai sai Safiyyah tasa kuka, ta soma yinsa kadan kadan da sheshsheka. Sannan with a heavy heart ta fado/rattabo musu lambar wayar Zayyan, wadda ke kwance a kokon kanta tamkar karatun sallah.
‘Guilt’ ne dai gashinan duk ya lullubeta, don hakika taci amanarsa (tayi satar fita) abinda bata taba yi ba tun aurensu, har anyi kokarin yi mata fyade da aurenta.
Tunda sai da yace mata tayi tawakkali ta hakura da batun haihuwa in dai don shi take nemanta, amma kafiya da ci da zuci irinnata yasa taki ji.
Wani ikon Allah Zayyan yana shiga garin Kano inda daga nan zai dauki titin da zai kai shi Zaria, wajejen karfe takwas na dare wata bakuwar lamba ta kira shi.
Zayyan bai ko kalli wayar ba saboda halin da yake ciki, yana tuki yana azkar, da fari kamar bazai amsa kiran ba don baya cikin yanayi na iya amsar wayar mutane, amma ganin nacin mai kiran a karo na uku yasa ya daure ya dauka, murya a dashe.
Nan aka yi masa sallama, aka ce daga Asibitin gwabnati na garin Kura ne, suna tareda mai dakinsa wadda tace sunanta Safiyyah, mota ce ta bigeta akan titin garin Daka-Tsalle, taji raunuka amma da sauki.
Zayyan saura kadan sityarinsa ya kwace masa ya shiga fadin….. “Innalillahi…”. Allah ya taimake shi ya rike sityarin sosai. Yace musu yanzu ya shigo Kano, nan da ‘yan mintuna zai iso asibitin Kuran ya dauketa.
Cikin mintunan da basu gaza talatin ba, da taimakon kwatancen mutumin da ya buge Safiyyah ya isa asibitin kauyen.

Safiyyah kasa hada ido da Zayyan tayi, ta runtse ido tana hawaye lokacin da taji sallamarsa a dakin, cikin muryarsa mai ratsa zuciyarta yace “AsSalamu alaykum” sannan ya murdo kofar dakin ya shigo cikin nutsuwarsa, a nitsensa yake tsaf bai bari rudewar tasa ya gigice ba yanzun daya ganta kwance hajaran majaran a kan gadon asibiti, makale da allurar karin ruwa a hannunta, gadon da take kwance ya nufo kai tsaye gabadaya hankalinsa ya dauku gareta. A hakan kuma yake gaisawa da jama’ar dakin.
Tana ji suna gaisawa suna kuma jajantawa shida mutumin daya bugeta da kuma likitan da ya kula da ita da kuma Nas din.
Ya nemi alfarmarsu kan cewa a darennan zai wuce da ita Zaria bazasu kwana ba, tunda alhamdulillah ba karaya a jikinta. Amma Safiyyah taki yarda su hada ido sam.
Da taimakon ma’aikatan jinya mata aka sa Safiyyah a gaban motarsa. Zayyan yayiwa ma’aikatan da suka kula da ita alkhairi na kudi sosai. A daren wajejen karfe tara na dare suka kamo hanyar Zaria.
Tsakanin Kura da Zaria, bai fi tafiyar awa daya da rabi ba, tun basu yi nisa ba ya kira Anti Dije ya gaya mata ga inda ya tsinto Safiyyah.
Anti Dije ta dinga salati da sallallami, kannenta kuwa sai kuka, jin wai ta samu accident a wani kauye, ita kuwa tun hawansu titi ma tayi barcin gajiya da wahala a seat dint ana gefen damansa, sakamakon allurar barcin da aka yi mata.
Kai tsaye ABUTH ya nufa da Safiyyah don a kara bincikar lafiyarta da kyau, bai yarda da kwarewar asibitin kauyen ba, ta kuma samu kyakkyawar kulawar data dace, kai shi yana tantama ma yanzu akan lafiyar kwakwalwarta, in ba haka ba me ya kaita wani kauye Daka-Tsalle, wa ta sani a can? Ko dai son haihuwa ya soma motsa masa kwakwalwar Sophie ne?

Don a cikin handbag dinta da aka bashi wadda duk uban gudun da taci bata yarda ta yasar da ita ba, yaga takardun tasa-tasai (test-test) na wani asibiti a cikin jakar.
Sannan tun isowarsa Kura da suka hada ido uffan bata ce masa ba, bata ma kara yarda ta hada ido dashi ba, ignoring haduwar idonsu take, don gani take daya kalli idonta zai ga tamkar Tsimbirbira ya aikata abinda ya ambata da ita.
Daman dai iyalin Baba Zayyan in har ba asibitin koyarwa na Ahmadu Bello ba, basa gane kowanne asibiti, hatta daga Abuja suna tahowa suzo ABUTH idan lalura bata gaggawa bace, tun bayan rasuwar Baba Bello ya zama addicted da asibitin ABUTH.
A can asibitin Anti Dije ta samesu, tare dasu Sabah su duka ukun har ita hudu gabadayansu a rude suke.
Duk da ransa a mummunan bace yake da Safiyyah amma haka ya daure yayi ta hidimar lafiyarta, ya shiga nan ya fita can tare da likitocin dake dubata a A&E ko a fuskarsa bazaka ga fushin sa ko bacin ransa da Sophie ba.
Har saida ya tabbatar an bincike lafiyarta sosai ba wani mummunan rauni bayan gocewar kashin da kukkujewa da buguwa. Aka bata magungunan rage zogin ciwo ta sha. Tsakanin Anti Dije dasu Rayyah kadai ake tattauna wannan abu da ya daure musu kai, ko ina Safiyyah taje a Kura da Daka-Tsalle ba tareda ta bari dayansu ya sani ba? Don Zayyan ya tabbatar musu acan ya daukota. Har lokacin Safiyyah barcinta take sadidan, an bata maganin barci don ta huta daga azabar ciwon kashi, kuma alhamdulillah iyaka abinda likitan Kura ya fada suma shi kawai suka gani. Iyaka tsinkayensu sun kasa cankar inda taje, da kuma abinda ya fitar da ita ana tsaka da bikin ‘yar Antinta wato Ni’ima.

Da daddare bayan Anti ta kawo musu abincin dare tace “Zayyan kaje dakin bakin Babansu Ni’ima ka kwana ka huta mana, mu sai mu kwana da ita, akwai gajiya a tare da kai sosai”. Amma Zayyan yaki, yace da Anti Dije shi zai kwana su su tafi. Anti bata tafi ba saida ta tabbatar ta zuba mishi abincin data kawo da kanta ya ci, tuwon semo da miyar egusi, har lokacin Sophie bata farka ba, ya kai su Anti Dije gida ita dasu Rayha ya dawo asibitin, sai ya biya ya taho ma patient din tasa da Rufaidah Youghurt, don ya san tana sonta sosai, kuma ya samo mata wanda tafiso (thick and creamy) da fresh milk din Hollandia. Da duk abinda zasu dan bukata na kwana biyu a asibitin harda su brush da maclean da sabulun wanka, don an bata (bed rest) na kwana biyu.
Yana tafe yana waya da Anti Dike. Inda ya hana su Anti Dije gayawa Malam da Ammi komai akan fitar Safiyyah, yace shi zai iya tackling koma menene, tunda dai bata taba yin hakan ba. Kuma tunda alhamdulillah ba mummunan rauni sosai a jikin ta, to ba sai sun ji ba, don kada a daga musu hankali.

Daga shagon Rufaidah masallacin asibitin ya nufa yayi sallar magriba da isha da suka subuce masa, ya rokawa Safiyyah lafiya, a ransa yana addu’ar Allah yasa alkhairi ne ya fidda Safiyyah daga gida. Wanda ya bigeta ya tabbatar masa a Daka-Tsalle ya buge ta kuma da ganin ta ba cikin hayyacinta take ba, da gudun gaske ya ganta tsakiyar titi a gabansa. Sai ya soma karfafa tunaninsa na anya kwakwalwarta lau take? Hakan kuma bai danne fushinsa ba, amma ya danne fargabarsa.
Sanda ya dawo dakin wajejen karfe goma sha daya na dare ne Safiyyah ta farka. Yana shigowa suka hada ido, ba yadda zata yi tayi ignoring ya riga ya ga idonta biyu. Sai ta tsayar da idanunta suna kallon nasa cike fal da hawaye.
Ya dauke kai kamar bai kula ta farka din ba shima, kwarai yaga razana da rashin gaskiya a tattare cikin idanunta, sai ya ja kujerar dake gabanta can daga saitin kanta ya zauna, ya bude lemun da ya shigo dashi na gongoni na ‘Schweppes’ ya soma sha.
Sosai Zayyan ya share Safiyyah, a ransa yana kissima irin ‘silent punishment’ din da zai yi mata, har sai ta fallasa abinda take boye musu da bakinta, yayi kamar bai ankara da cewa ta soma sakin sassanyar kukanta cikin in’inarta na nuna nadama ba, ga firgicin tuno Tsimbirbira. Data rufe ido shi take hangowa ya biyota. Jikinta ya hau rawa da kyarma. Rashin ganin fuska daga Zayyan yau, da yadda yayi murtuk da ita ya hade giran sama da na kasa shi yafi komai tsoratata da kara sakata a damuwa.
Ga mamakinsa shi kansa, yau kukan Safiyyah ko kadan bai sosa ransa ba, don ya san na rashin gaskiya ne, duk da babu abinda ya tsana irin kukan Sophie, balle kuma bacin ranta akan komai, amma yau kwarai ta yi abinda bai taba zato ba, (satar fita) zai kira abun ko cin amanar yardar da yayi mata? Har shaidan na kimsa masa ko tun yaushe Sophie take yin hakan gareshi bai sani ba?

Kuma ina da ina Sophie take zuwa in tace masa zata je Zaria gun Anti Dije? Har sai yau da Allah yayi niyyar nuna masa, shine yasa mota ta kadeta, yadda bata da damar komawa gida bai ganewa idanunsa inda taje ba? Da yake shi Ubangiji ya san bashi da hakkinta, duk wata kyautatawa da trust dinsa ya mallaka mata su. Ransa ne kawai bai cire ya baima Sophie don soyayyah, kauna da yarda ba.
A irin yardar da yayiwa Sophie, da nagartattun halayenta daya riga ya shaida, da tarbiyyar da yake da tabbacin ta taso a cikin ta, baiyi zaton abinda zuciyarsa ke zargi yanzu a kanta ba gaskiya bane, amma fisabilillah bai taba kawowa a ransa Sophie zata iya ketare iyaka a cikin aurensu ko ta ha’ince shi ba. Tunda ta san ko me take so in ta nemi izninsa bazai hanata ba, gashi yanzu taje tana neman salwantar da rayuwarta a banza.
A zahiri Sophie bata taba bata masa rai ta bakanta masa, ta kuma sa masa zato da shakku akanta irin yau ba. Wani matsanancin kishi da bai san yana dashi a kan matar tashi ba sai yau yake fiddo kansa sarari, cikin fushin da yayi da Sophie.
Tun Safiyyah na kuka kadan kadan har kukan nata ya fito fili. Ta soma rera masa shi kamar ana busa sarewa ko yaji tausayinta ya saki fuskarsa. Sau tari ta san Zayyan baya bata bakinsa wajen cewa kayi masa ba dai-dai ba. Kuma baya son kayi masa laifi kayi ta bashi hakuri. Shiru yake yi ya dafa mutum da manyan idanunsa da shirunsa har sai ka gwammace ya bude baki yayi maka balbalin fada, ko ya zane ka da bulala fiyedawannan long silence din da zaiyi maka. Don zafin kallon data ke gani cikin idanunsa yafi na bulala radadi a jikinta da zuciyarta.

To irin abunda yayi mata yau ma kenan. Da kukan nata ya fara damunsa sai ya mike ya shiga toilet yana daura alwala don dare ya nausa yanaso yayi nafila, kasancewar a (amenity room) suke su biyu kacal, ya gama alwala ya wanko bakinsa da brush da maclean dinda ya sayo musu na ‘Longrich’ sannan ya fito ya fice daga dakin. Ya bar mata kamshin ultraviolet dinsa kadai a dakin asibitin.
Can anjima sai gashi ya dawo tare da nurse mace guda daya. A lokacin tana tsane hawayen idanunta tana harhada kalaman da zata yi masa bayani dasu a ranta, don kawar da zargi data lura ya samu muhalli a zuciyarsa da wanke laifinta. Suka shigo shi da nurse din, ganin ta farka kuma ruwan da aka saka mata ya kare sai Nurse din ta cire mata ruwan da allurar dake hannunta don ta huta.
Tace “to kukan na menene kuma Mrs. Safiyyah Rafindadi? Bayan gaki ga Oga a gefenki, tunda ya kawo ki ko sau daya bai zauna ba, yanata dawainiya dake. Likita yace ki maida hankalinki wajen shan magani cikin lokaci, in sha Allah sati daya yayi yawa za kiji dadin jikinki”.
Safiyyah ta gyada kai. Sai nurse din ta bata maganinta na dare. Sannan tayi musu sallama ta fita, bayan tace inda wani abu shi Zayyan ya kirata.
Dakin sai ya koma wani irin tsit, bayan fitar nurse din. Zayyan ya yada kansa bisa kafadarsa akan kujera yana zaune bisa kujera kwaya daya dake dakin, wadda ke fuskantar Safiyyah dake kwance.
Ko ya tambayeta ya akayi ya tsintota a Kura? Ko ina kika je a Daka tsalle? Kawai yaja bakinsa yayi shiru. Ita kadai ta gane cewa ‘silent anger’ ne a kwance kan fuskarsa ma’abociyar kwantaccen saje da gargasa, kuma ‘silent punishment’ dinsa na shiru dinnan da yafi komai kidimata yauma yake son yi mata.

Daga baya Zayyan sai ya lumshe idanunsa yana sauraron kukanta, har barci yayi awon gaba da ita.
A washegari ma haka ta wuni kuka, sikuma ya wuni zaune gabanta silently. Sallah kadai ke fiddashi masallacin asibitin. Su Anti Dije sai yamma suka zo musu ranar za’a kai amarya Ni’ima gidanta kenan, washegari su Sabah kuma zasu koma Dandume.
Har magriba suna tare dasu sai bayan isha suka tafi. Bayan sun tafi again zata cigaba da kuka ya bar mata dakin, bai dawo ba sai da ya tabbatar tayi barci.
Washegari aka sallamesu suka tattaro suka kamo hanyar Abuja, ko gidan Anti Dije basu koma ba, sai a waya ya gaya mata sun wuce. Tayi addu’ar su sauka lafiya.
Sun wuce Kaduna sosai amma ba umh ba umh umh tsakaninsu. Sai ta kukan a fili tana so ya kulata, at least ya tambayeta daga ina kike Sophie mana? Yadda zata samu gangara tayi masa bayani. Amma mutumin saima ya hade giran sama dana kasa yana tukinsa hankalinsa kwance, ransa a bace, hankalinsa ya dauku sosai ga tukin da yakeyi.

Data tabbatar Zayyan bazai kulata ba kuma bashi da niyyar hakan, sai ta soma magana cikin rishin kuka.
“Kayi hakuri, kayi hakuri Habiby, ka dubi halin da nake ciki ka gafarta min. Wanda ba komai ya janyomin ba sai rashin jin maganarka, da rashin daukar nasiharka, kace inyi tawakkali amma na kasa.
Ka yarda koma ina naje, kuma kowanne irin hadari na sanya kaina ciki, sannan na hadu da wannan tsautsayin duk ya faru dani a dalilin son mu rayu tare ne, da son samun ‘ya’ya daga gareka, da son cigaba da rayuwa da kai cikin kwanciyar hankali da soyayyar mahaifiyarka data ‘yan uwanka dana rasa, kwadayina kullum yana ga samun tsatso daga gareka Habiby!”.
Tayi shiru kadan tana kallon yadda yake sake hade girar sama data kasa, tana son gane ko bayaninta yayi wani tasiri? Sai bata gane komai ba.
Sophie ta gyara kwanciyarta a gefen damansa, jikinta duk ya mata tsami, ta fuskanceshi sosai cikin damuwa da zafin ciwo, fuskarta kan tafukan hannunta tace “wallahi Habiby…..” sai tayi shiru, ta kasa karasawa ta kuma saka kuka, ganin yau Habiby ko alamun gezau ya ki yi da damuwarta, balle yayi alamun zai karbi rauninta da tubanta.

Sai a lokacin zuciyar Zayyan ta dan fara russuna, yace “Umh? Ina jinki Sophie, kin shirya magana yanzun? Ko na kara miki lokaci ki kara deciding me zaki gayamin? Bana son ki takurawa kanki sai kin yimin wani bayani. Bana cikin damuwa kuma banida matsala akan hakan”.
Da sauri tace “na shirya zan gaya maka gaskiya tsakanina da Allah, amma don Allah kayi hakuri…” ai kawai sai in’inar ta taho mata gabadaya ta sarqe ta, dama in bata cikin nutsuwa sai ka nutsu sosai zaka gane me take cewa in tana magana in’inar bakidaya afkowa take yi.
Amma da yake Zayyan da Safiyya sai Allah duk abunda take fada ya gane tsab, bashi da matsala ko kadan da in’inarta, dadima take masa, nan ta fara bashi labarin zuwanta gurin Dr. Hadizah, da haduwarta da Ammara, da zuwansu gurin Tsimbirbira la’ananne.
Haka kawai yaji zuciyarshi na bugawa, gumi na karyo mishi, ya rasa ma zafi yake ji ko sanyi, daga inda tace ance sai ta kawo sperm dinsa.… baki daya jikinshi kyarma ya shiga yi har tukin ya soma kokarin gagararsa. Kafin ta kai aya daidai inda tace ance sai Tsimbirbira ya sadu da ita zata haihu, Zayyan bai tsaya yaji karshen ba ya daka mata tsawa jikinsa na zikiri, yace “bana son jin labarin, bana son ji, please ya isheni haka!!!”
Ya fada cikin tsawar data kada ‘yan hanjinta, kafin ya gangara motar gefen titi a hankali ya kasheta gabadaya, don tsoron kada ya kifar dasu.
Ya fara ambaton “Innalillahi wa inna ilaihi rajioun”.

Ya kura mata ido cikin mamaki da tsoro da tarin disappointment a cikin kallon dake fitowa daga idonsa. Yace.
“Safiyyah!” (Sunanda tun suna dating wato tun kafin aure rabon shi da kiranta da shi), kafin ta farfado daga wannan shock din na kiran asalin sunanta yace.
“Kinci amana Sophie, kinci amanar aure, me ya kaiki binta in the first place? Gaskiya kinci amanar tarbiyyar da Malam da Ammi suka yi miki yau.
Ya buga sityarin da karfi yana fadin “Ni Zayyan kika yiwa haka Safiyyah yau? I can’t believe it!”.
Ya ma rasa me zai ce da ita, saboda tsabar kaduwa. Sophien shi wani ya kusa ketawa rigar mutumci da aurensa saboda son zuciyarta. Ya sake maimaita “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”. Zayyan ya dade bai shiga tashin hankali irin wannan ba. Yace.
“Safiyyah why? Don me kika je? Ko saboda rashin godiyar Allah? In ba haka ba ni Zayyan na taba nuna miki wani abu da ya nuna na damu da haihuwa ko rashinta? Ko na taba matsanta miki akan inason haihuwa da har yasa kika kusa jefa kanki a fushin Allah saboda son wata haihuwa da ni bata gabana, wannan rashin tawakkali har ina?”

Sai taji kaman saukar aradu akanta. Tayi suman zaune ta kasa cewa komai, domin ya dauki al’amarin da girma har fiyeda yadda ta zaci zai dauka. Shi gani yake ma kamar Tsimbirbirar ya keta masa haddi sakayawa kawai tayi a gaban idonsa.
Wannan tashin hankalin da Safiyyah ta gani a tare dashi yasa ta kasa cigaba da kuka, don ta san duk abunda ya gaya mata ta cancanci ya gaya mata ko don ya huce bacin ransa.
Sai ya koma magana cikin rauni. Yace “Safiyyah Allah shaida na ne kan na soki da zuciya daya, rashin haihuwa bai taba sawa na rageki da komai ba, shi ne zaki saka mun da wannan butulcin, ki kai kanki ga wani zindiqi mushriki, kin butulcemin, kin butulcewa Allah, kaicon ki da rashin tawakkali Safiyyah”.
Ya ja motar a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki suka cigaba da tafiya. Har suka shiga Abuja bai kara ce mata ko uffan ba. Kuka Safiyyah ta yi shi har ta ji babu dadi. Kamar hawayenta zasu kare.
Taimakon Allah kadai yasa ya iya karasa tukinnan, ya kuma kawo su gida lafiya.

Yana fita daga motar ta biyoshi da sauri tana bashi hakuri, zata rike hannunsa yace “idan kika tabani wallahi zan bata miki rai, sai kinyi dana sanin zuwa kusa dani”. Ya shige ciki ya barta a wurin.
Nan Safiyyah ta zauna a kasa a harabar gidansu a salube, don kafarta ta kasa daukan nauyinta. Ba jimawa da shigarsa ya sake turo kofa ya fito ya fice, bata san ma inda ya nufa ba.
Zayyan dai tun daga ranar ya canzawa Safiyyah, wato ya dauke mata wuta, suka koma zaman marina ko zaman doya da manja shi da ita, baya shiga harkarta, baya kulata a shimfida, punishment sosai yake mata, amma in ta gaishe shi zai amsa yana cigaba da tafiya. A lokacin ya maida kanshi wani irin busy machine saboda aiki, dare da rana zane yakeyi, yana baiwa kanshi wahala yana ta zane-zane ba gajiyawa, in ya fita harkar neman kwangilarsa ma sai can dare yake dawowa.
Safiyya duk ta sha jinin jikinta cewa Zayyan yana zargin Tsimbirbira ya riga ya cika burinsa a kanta, ta dai boye masa ne, don haka gabadaya Sophie ta tsangwami kanta, ta tsani kanta, ta rame ta zuge cikin kwana uku, ta tsani haihuwar bakidaya ma.
Gashi ba halin ta kira kowa ta nemi shawara, don tamkar ta yi kirari ta dabawa kanta wuka ne a ciki. Musamman Ammi da Malam, da tsine mata ne kadai bazasu yi ba in suka ji abinda ta aikata saboda son haihuwa. Ta yi istigfar ta nemi gafarar Ubangiji yafi sau shurin masaki. Tace koda wannan punishment din na duniya Zayyan ya barta ya isheta kankarar zunubinta.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *