⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 10: Chapter 10

Ya ce, “Eh Mama”. Ta ce, “To ka saurareni da kyau kaji abinda zan gaya maka yanzu, maza kayi gaggawar sanar da Baban naku, ina tabbatar maka yanzu ne za ka yi aure mai suna aure idan aka dace, aure na gata da mutunci, auren babban gida daya dace da kai.
Sauran al’amuran ka bar komai a hannuna, in dai ka gaya wa Alhajin naku ka gama naka, ko lefe ni zan hada maka komai kaji Baffa”.
Ya yi mamakin yadda daga ‘yar magana ta subutar baki Mama ta dauki zancen da matukar muhimmanci irin haka.
A daren da kyar Zayyan ya iya yayi barci saboda tunani, a karshe ya tabbatarwa kansa ya kuma gayawa kansa kara aure shi ne kadai solution na dukkan matsalolinsu shida Safiyyah ta kowanne bangare ya duba yaga hakan shine kadai maslaha.
Amma daga bangaren ita Safiyyah shin hakan zai zamo solution a gareta? Kuma ta wace hanya zai bi ya gaya mata yau shi Zayyan ya ga wata mace daban a duniya bayan ita ya kalla sai biyu, kuma yana so zai aura ya hada da ita? Duk da cewa ba haramun zai aikata ba, kuma bai taba yi wa Safiyyah alkawarin ba zai kara aure ba, amma Hausawa suka ce, wai ido da kunya!
Saboda nauyin idanun Safiyyah da ya fara ji tun yanzu, tun ma kafin ya sanar da Azeezah din ko mahaifinta, sai yayi maza ya kara kashe wayarsa, gani yake yana bude baki don yin magana da Safiyyah za ta ji abinda ke binne a zuciyarsa yau, wanda yake shirin aikata mata, wato sha’awarsa ta kara aure. Don haka kashe wayoyinsa shi yafi masa komai sauki.

Washegari tunda sassafe wayar Mama ce ta tashe shi daga baccin da ya samu bayan ya yi sallar asubah.
Kuma yana dagawa ko gama gaisawa ba su yi ba, ta ce, “Baffa mu gode wa Allah, mu kara gode maSa.
Yanzun nan na gama magana da uwar gidan Alh. Murtala wato Hajiya Nana Aisha, na tambaye ta ko an yi wa Azeezah miji, ta ce tukunna, amma akwai yaron da take tare da shi a Cyprus kafin ta dawo.
Saboda haka don Allah don Annabi Baffa kada ka yi da wasa cikin maganar nan, da zafi-zafi a kan bugi karfe”.
Shi dokin Mama a kan maganar ya fara ba shi mamaki, kamar dama a jirace ta ke da ya kyasa wata ya gaya mata?
Ya ce, “Mama ki bi a hankali, I haven’t decided yet”.

Mama ta ce, “Zancen banza da wofi kenan, ni har na saka Zubaida a fara hada lefe na alfarma, don ni wurina yanzu ne zaka yi aure na mutunci a inda ya dace Baffa, kuma aure daidai class dinka da matsayinka”.
Bai ce komai ba har Mama ta kashe wayarta. Ya ce, “Hummm! Mama kenan. Kowa in bai da kudi da reputation to ba mutum ba ne mai mutunci a idonta.
Ba wannan dalilin ne ya sa ya furta abinda yake ransa a kan Azeezah kenan ba, a’a shi ra’ayi ne da sha’awa suka zarge wuyanshi.
Daidai lokacin Baba Murtala ya kira shi a waya ya ce masa yana jiransa su karya kumallo.

A gurguje ya yi wanka ya shirya cikin ash colour yadin filtex mara kauri, ya sanya hula kalar kayan jikinsa data ciza sosai. Nan Zayyan ya fito a Zayyan dinsa, tamkar saurayi dan ashirin da bakwai ba mijin mace daya ba.
Ya gama feshe illahirin jikinsa da ultraviolet dinsa, sannan ya rufo dakinsa ya karanta addu’ar fita gida da neman sa’a sannan ya nufi cikin gidan.
Har addu’a Zayyan yake a ransa, Allah ya sa Azeezah ba ta falon, ko bata tashi barci ba, domin emotions dinsa a kanta suna kasa boyuwa in ya ganta har gashi Baba Murtala jiya ya kusa ramfo shi, watakila shiyasa ya shiga ba shi labarin rayuwarta.
Addu’arsa bata karbu ba, domin kuwa yana shiga falon Baban da ita ya fara yin tozali, tana zubawa Baba Murtala tea mai ganyen na’a-na’a.
Azeezah ta sha kwalliyar safe har ta gode Allah cikin wani ubansu combination na swiss lace da atamfar super orange and black.
Zuciyar Zayyan ta doka ta sake dokawa da wani sabon infatuation da sha’awar Azeezah, amma a hakan ya daure yasa tsahonsa ya shiga cikin falon da sallama dauke a bakinsa. Cikin dakewa da karfin halin kauda idanunsa daga gare ta.
Baba Murtala ya ce, “Zo daga nan gefena Zayyan mu sha tea. Ke Azeezah hada masa shayin na’a-na’a ya wartsake makoshinsa”.
Ya durkusa gefen Baba ya zauna yana gaisheshi da safiya.

Azeezah ta mike zata bar wajen, Baba Murtala ya ce, “Shin ke wace irin sakarya ce da kullum sai an ce ki gaida mutane sannan zaki gaishe su? Kuma shin baki ji nace ki hada masa tea irin nawa ba?”
A gaskiya Azeezah ta tsani yadda Baba ke dizga ta a gaban yaron nan, don ta lura wani matsayi yake da shi mai girma a gun Babansu, tunda dan Arch. Bello Rafindadi ne, wanda tun haihuwarta ta ke jinsa bakin Baba da girman abotarsu a bakin Babanta Arch. Murtala Babangida. To ya za ta yi? Haka ta juyo da zummar gaishe shi, yayin da idanunta suka fada a cikin nasa. Saura kadan zuciyar Azeezah ta narke kamar yadda kitse yake narkewa in ya shiga rana.
Hatta kalmar gaisuwar makalewa ta yi a makoshin Azeezah Murtala, domin sai yau ne tayi ma Zayyan Bello kallo na hakika don jiya ko kallon fuskarsa bata yi ba. Duk wata jijiyar da ke cikin jikinta sai da ta saki, ta karbi kwantaccen sakon da ke cikin idanunsa zuwa gare ta, kafafunta ma rawa suka hau yi, ta shiga gaishe shi da shakakkiyar murya da dimaucewa.
Baba Murtala ya kara bada ita da cewa,

“To shayin ma wato sai na sake cewa ki hada masa karo na uku ko Azeezah?”
Saura kadan Azeezah ta fashe da kuka, sabida bazata iya hada wannan shayin ba. Hannunta da jikinta duka rawa suke. Zayyan ya cece ta da cewa.
“Kyaleta ta je Baba, ni ko Safiyyah bata hada mun shayi, da kaina nake hadawa, kyaleta zan hada da kaina Baba”.
Tsaki Baba Murtala ya yi, yana ta korafi dai a kan halin sangartar diyar tasa, har yana cewa, yana jin tausayin duk mijin da zai kwashe ta. Domin kuwa ba haka uwarta take ba.
Murmushi Zayyan ya yi, beautiful serene smiles dinsa, wani tsadadden miskilin murmushi da ba koyaushe yake yin irinsa ba, ya ce.
“To Baba ni in rage maka dawainiya mana? Ni ina sonta a haka, ka ba ni ina so”.

Sakatoto da baki Baba Murtala ya yi yana kallon dan nasa, kafin ya ce, “Tau? Ubanka nake dai ba Kakanka ba, balle ka maida ni abokin wasan ka, ni ba sa’an wasanka ba ne Zayyan da za ka tsokane ni.
Barni in sha ‘tea’ dina cikin dadin rai, kada ka sa ya huce min da shiriritarku”. Ya daga kofin shayinsa ya kurba.
Zayyan ya dinga murmushi yana cewa, “In dai za ka ba ni Baba, ba zan yi maka wasa ko shiririta ba nima, ai babu irin wannan wasan tsakaninmu nida kai Baba. Uba ne da tilon Dan sa”.
Kawai sai ya ga Baba Murtala ya daddage ya fashe da kuka.

Jikin Zayyan ya yi sanyi, don ya dauka zafin maganarsa Baba Murtala ya ji, amma sai Baba ya kama hannunsa ya rike yana kallonsa da kauna ido fal hawaye.
Ya ce, “Bar ganin ina zubda hawaye, Bello na tuno. Ya taba cewa, ba don ka yi aure da wuri ba da zai fi so ka auri daya daga cikin ‘ya’yana mata don kara dankon zumuncinmu.
A lokacin sai na ce masa, kada ya kara irin wannan maganar kada mu taba tunanin yi muku auren hadi, wanda a karshe bata zumunci yake zama.
Yau da ka furta da bakinka cewa, kana son Azeezah, duk da yadda nake ta kushe ta a idanunka, tun zuwanka Zayyan ban yabi halin Azeezah ko daya a kunnenka ba, ko sau daya ban fadi alkhairi akanta ba, sai hakan ya tuna min da abinda Bello ya taba ce min a kanka.
Ya taba ce min, yana son baudaddiyar halayyarka, abin da kowa bai so ko ake ganin disadvantage dinsa, sau tari kai shi kake so. Abinda baya burge kowa kai shi yake burgeka.
Ya ce auren da ka yi shi kadai ya mara maka baya saboda daga Hajiya Fatu har ‘yan uwanka mata babu mai son auren saboda diyar Alaramma ce kuma stammerer.
Da wannan nake cewa, ni kuma na baka Azeezah, ka nemi yardarta, in Allah ya sa ta amince da zarar mun gama wannan project din, sai mu durfafi daurin aurenku”.
Shayin da basu sha ba kenan a yau, haka suka fita suka barshi a wurin ya huce.

Baba Murtala farin ciki ya hana shi sukuni, suna tafe a hanya direban Baban na sharara gudu da su a bayan Hyundai din Alhaji Murtala, sai ya ji Baba na waya da Azeezah din.
“Azeezah kina gida ne?”
“Mun fita ni da Mama Agege, amma muna hanyar komawa gida yanzu haka”.
Ya ce, “To ki shirya tarbar bako yau da daddare, wajen karfe takwas in na dawo gida”.
A dukunkune da fuska ta ajiye wayar don ta yi tsammanin ya dauko mata malamin da ya ce zai dauko ya dinga koya mata karatun addini a gida ne.
Ita a wurinta ta wuce zama gaban Malamin islamiyya yanzu. Baba Murtala kuma ya ce, ko izfi goma ya san bata hada ba.
Don haka ko da suka dawo gida ita da Mama, bata yi wani kyakkyawan minti goma a falo ba, ta gudu dakinta tasa sakata.
Zayyan sai goshin magriba suka dawo gidan shi da Baba, don haka masallaci suka wuce kai tsaye, wanda ke like da gidan Alhaji Murtala.
Can suka zauna suka bi jam’i har bayan da aka idar da sallar isha. Ko a masallacin Addu’a yake cikin ransa, idan nemansa da Azeezah alkhairi ne a gare su, shi da Safiyyah, Allah ya bashi kwarin gwiwar iya tsayawa a gaban wata macen da sunan neman soyayya ba Safiyyah Dandume ba.

Da suka fito daga masallaci Baba ya ce su wuce cikin gida su yi dinner, sai ya ce ma Baba yana zuwa.
Ya koma masaukinsa ya sake wanka, yau Zayyan kananun kaya ya saka, shirt da wandon jeans baki Tommy Hilfiger. Zai fesa turare kawai idanun Sophie suka fado cikin nashi idanun, sai ya fasa.
Don ji ya yi tamkar hakan ya zama cin fuska a gare ta.
“To na nawa kuma Malam Zayyan? Tunda gaka ka dauki wankan zuwa zance gun budurwa?”
Wata zuciyar ta tambaya ta kuma kara masa da ce masa, “You are no longer a trusted husband to Sophie, you are now a “man” like other men, who are guided by their heart desires and emotions”.
Ma’ana; kai yanzu ba dan amanar Safiyyah bane. Ba mijin da zata bugi kirji ta yarda dashi bane. A yanzun daya kake da sauran maza babu banbanci, wadanda ke tafiya akan muradin zuciyarsu da shaukin dake zukatansu”.
Wannan tunanin ne ya sa jikinsa yin sanyi kalau, ya maida turaren muhallinsa ya ajiye. Ya fasa fesawa.
Amma sai wata zuciyar ta tabbatar masa da cewa, kara aure ba cin amana bane ga maza, ba kuma cin fuska ne ga Sophie ba. Karewa ma, yana ganin zai nemi wannan auren ne don ya samar mata maslaha a zama da shi, sannan ya nemo mata nutsuwa da kwanciyar hankalin data rasa a cikin rayuwarsu.

Muhimmi shine zai yi auren nan ne ma don ta samu Da daga gareshi. Wanda ya yi alkawarin nata ne da duk macen da ya haifa, kuma hakan maslahar ta ce a rayuwa da Mama, duk wata tsangwama, duk wani zargi na ta mallake shi zai kau daga idanun Mama yanzu.
Da wannan tunanin ya dan samu karsashin nufar cikin gida. Wai shi Zayyan ne yau zai je zance gun budurwa ba Safiyyah ba. Yana taku a hankali kamar ya fasa zuwa zancen, musamman da yake jin tamkar idanun Safiyyah na kallonsa.
Amma da ya tuno surar Azeezah da iya kwalliyarta sai nan da nan wata zuciyar ta ce,
“Zayyan kada ka bada maza mana, polygamy ba kanka farau ba”.
Ya samu Baba yana waya, tuni an shirya musu abincin dare. Ya yafito shi da hannun damansa don ya zauna gefensa as usual.
Sai da ya gama wayar sannan suka fara cin abincin Baba na masa hira. Duk da Baba Murtala ya fahimci yau ya kasa sakin jikinsa da shi, shi ya sa ma yake kara jan hirar tasu don ba ya so surukuta ta shiga tsakaninsa da Dan nasa Zayyan tun yanzu. Yafiso su ci gabada gudanar da rayuwarsu normal ta uba da Da yadda suke yinta.

Sai da suka kammala Baba Murtala ya ce, ya shiga daga falon Hajiya Nana za ta turo masa Azeezah.
Bai jima da zama ba Hajiya Nana ta turo ta falon. Azeezah ta shigo fuska a turbune don ta dauka ko Malamin islamiyyar ne ya fara zuwa, don daga Mama har Alhajinsu ba wanda ya gaya mata cewa Zayyan ne. Don haka da ta ganshi a falon ta kusan sakin fitsari daga tsaye. Duk ta rude, domin kwarai Zayyan mijin Safiyyah ke da kwarjini a idanun ‘yammata.
Rasa me za ta ce ta yi, tunda dai ai ta san babu wata manufa da Baba zai turo mata shi in ba ta neman aure ko dalili makamancinsa ba.
“Zauna mana Azeezah”.
Zayyan ya fadi cikin tsare ta da idanunsa da suka kara ruda ta.
Haka ta dosana ta zauna a nesa da shi akan hannun kujera.
Ya gyara zama ya ce,
“Kun dawo kenan?”

Ta amsa da “Eh”. Tana wasa da ‘yan yatsunta.
Sai ya yi gyaran murya ya ce, “toh dai Azeezah, ba sai mun ja ta da nisa ba, tunda dukkanmu ba yau muka san juna ba. Kuma diyan Baba ne mu duka ba bakin juna bane.
Sannan ni ba yaro bane kamarki, na kusa shiga shekaru arba’in, kin ga kenan babu bukatar yin kwane-kwane ko bata wa junanmu lokaci.
Azeezah na ganki a gidanku, gaban iyayenki kuma na yaba, in short I admire you, zan so kara ki cikin iyalina idan kin amince.
Sunana Zayyan Bello, kamar yadda kika riga kika sani, ni dan marigayi aminin Baba ne. Ina da mace daya mai suna Safiyya, wadda tunda muka yi aure sama da shekaru goma ba mu taba samun matsalar da muka kasa warwarewa a tsakaninmu ba”.
Ya dan nisa kafin ya sassauta murya ya cigaba da cewa.
“Azeezah ni da matata muna da fahimtar juna, ina son kara aure ba don ta rage ni da komai ba, ina kuma barar shigowarki cikinmu, don kara dankon zumuncin gidanmu da gidanku. Idan har kin amince bana so abin ya dauki lokaci, don ni da ke babu bukatar sanin asalin juna, sai amincewarki kadai nake nema”.

Duk wata kalma guda daya da yake yi a kan matarshi kular da Azeezah ta ke yi, har ta ce a ranta, wai shi wannan a wurinsa haka ake zuwa neman soyayyar budurwa? Da alama farin shiga ne gun zuwa zance wajen budurwa ‘yar zamani kamarta.
Ba zai maida hankali wajen gaya mata irin kamun da soyayyarta ta yi masa ba, sai wani yan-yan-yan akan tsakaninsa da matarsa?
Kamar ta yi kuka saboda ba wannan take son ji ba, ta ce cikin gatse.
“Kuna da irin wannan fahimtar juna da soyayyar kai da matarka, to meye naka na son kara aure, kuma me ka zo nema a gare ni tunda ba so ba ne ya kawoka? In zumunci ne ai da abinku na ganku kaida Baba, so ko dani ko babu ni zaku cigaba da abinku yadda na riskeshi”.
Tana fadin hakan ta sha mur sosai, ta dora kafa daya kan daya, don ta tsani rainin hankali irinna maza.

Kwarai tambayar tata ta shammace shi, har ya rasa amsar da zai bata, hakan yasa ya baiwa kansa assignment na ‘yan sakanni. Don ya samu amsa kwakkwara da zai bata.
Yana ganinta yarinya, mai tarin wauta, ashe-ashe tasan abinda take yi? Meye dalilin son kara aurensa? In har yanada komai da yake bukata a gidansa? Shine assignment dinda shima ya baiwa kansa a yanzu.
Dalilai da yawa masu muhimmanci sun yi mujazar wannan son karin auren, domin yana ganin shine kadai maslaha a gare su shida Safiyyah, don yana sha’awar mace irin Azeezah a gidansa da rayuwarsa, yana son mace ‘yar gayu, mai wayewar kai, domin likely mace mai body shape dinta da irin dirarrun dugadugan kafar Azeezah itace daidai shi. Ustazancin Sophie yayi masa yawa, tsayin shekarun da sukayi tare da zata canza da tuni canza to ba’a sakewa mutum nature dinsa, wanda shi yake hana ta sakin jiki su yi irin soyayyar da shi yake so, for over a decade da aurenshi da Sophie yana ganin bai samu sakewarta da shi a gadon aurensu irin yadda yake so ya kai sau goma ba, saboda kunyarta da kawaicinta akan hakan, amma ba don bata sonshi ba.
Azeezah za ta yi bridging wannan gap din, ga dukkan alamu, duk da tarin negativities dinta da mahaifinta ke kuka dasu, shi ba zai zame masa matsala ba in dai zai samu yadda yake so da ita, yake kuma kwadayin samu a gidan aurensa, ko da kuwa Safiyyah ta haihu, hakan ba zai hana shi wannan auren ba.

Sannan idan Allah ya nufa ya samu haihuwa da Azeezah kafin Safiyyah dan ko ‘yar na farko da yardar ubangiji zai zamanto tukwicin kauna ta gaskiya ne da zai yiwa Safiyyah.
A takaice sexual dysfunction din Safiyyah da neman mata yaro daga gareshi, su ne dalili kuma silar son kara aurensa.
Azeezah ta kafe shi da idanunta tana jiran amsa, tana kuma ankare da yadda tambayarta ta jefa shi a gumi da tunani. Zayyan ya dago a hankali suka hada ido, sai ya yi mata murmushin da ya kara narka zuciyarta a kansa.
Ya ce, “kisa a ranki babu namijin da zai zo neman aure a inda babu burbushin soyayya a ransa. I like you Azeezah, amma don Allah kalmar SO dinnan ki yimin jinkirinta, har sai na tantance ta a raina, kada in fade ta a lokacin da bai dace ba.
Na yi miki alkawarin adalci da farin ciki a gidana, don ke kanwata ce da ba zan iya cutarwa ba, ina son aurenki bisa yarda da amincewarki”.
Maganganun nasa sun ki zauna mata daidai a kwanyarta, don jinsu ta ke tamkar rainin wayo. Amma me?
Zayyan din ya zo da karfin chemistry din da ya fizge zuciyarta nan da nan zuwa gare shi, har ta ke jin ba za ta iya ce masa dole sai ya takura kansa ya furta mata abin da ta ke son ji ba, tunda dai ya ce babu namijin da zai zo neman aure a inda babu burbushin soyayyar mace a ransa.

Zayyan ya katse mata tunanin da ya jefa ta da cewa,
“Can I go ahead Azeezah? Kin yarda iyaye su shigo cikin lamarinmu, in sanya ki cikin iyalina?”
Azeezah ta juyar da kai gefe, zuciyarta na bugawa da shigar SO farat daya, babu bata lokaci zuciyar tace itafa ta yi na’am da dan mutanen Rafindadi. Ko ma dai me yake nufi da cewa ta yi masa uzurin jinkirin kalmar soyayya zuwa wani lokaci za ta yi wannan uzurin, domin ta tabbata wuyarta a yi auren, tunda har ya kawo kansa ya yi confessing na neman amincewarta da bakinsa.
Tana wannan tunanin, ya sake maimaita tambayarsa na neman yardarta har ya ce,
“Kamar yadda ki ka gani ni ba yaro ba ne Azeezah, ba zan iya long dating dake ba, I truly admire you, ki ba ni yardarki”.
Sai ta samu kanta da gyada kai kawai, ta kuma tambaye shi ko yaransu nawa shi da maidakinsa Safiyyah?
Zayyan ya dan ciza lebensa cikin ‘yar damuwa kafin ya ce.

“Muna fatan Allah ya kawo su nan gaba. In kuma daga wajenki Allah ya bamu, ina neman alfarmar ki baiwa Safiyyah ko me ki ka haifa na farko. Na tabbatar miki za ta yi masa rikon da ko ke ba za ki yi masa ba tunda Da na ne. Za ta yi masa tarbiyyah irin wadda ko ke ba za ki yi masa ba. Za ki yi mana wannan alfarmar Azeezah?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *