Chapter 9: Chapter 9
Maganganunta sun masa ciwo ya kuma yi niyyar ba ta amsa mai zafi, amma sai ya tuna cewa tana cikin watan haihuwarta, kada su yi fada yayi ‘inducing labour’ gara ya shanye duk rashin kunyarta in har za ta sauke masa dan sa ko ’yarsa lafiya.
Shi wannan duk ba shi ya fi bata masa rai ba kamar rashin godiyarta da kayan Mama, inda adalci Mama ba bakauyiya ba ce, kuma ta san kaya na yayi na ‘yan zamani tunda sana’arta kenan. Ta saka mata kananan atamfofi ne don tayi goyo da jego dasu.
Tsaki ya yi ya tashi zai bar mata dakin don ransa ya kai matuka wajen baci, ba tun yau ba ya san Azeezah ba ta da kunya, tunda ba ta shakkar gaya masa duk abin da ya zo bakinta.
Sai da ta ga fita zai yi, ta ce, “Baby! Wai nan fushi ka yi?”
Bai bata amsa ba, sai yasa kai zai fita a falonta, sai ta sake cewa,
“Yanzu ba za ka kai ni in sayo ‘Malaysian Fabrics’ ba sai sun kare? Wallahi tana kawowa basa sati a kasa sun kare saboda kyau da ingancinsu… ficewa ya yi kawai bai kula ta ba. A ransa ya ce, in na biye wa yarinyar nan sai na hada da cinye jarina, don dinka sutturun gayunta. Ba abinda Allah bai bata ba, amma kullum sabon yayi daya bullo jiya-jiya (latest) ta ke hangowa.
Ire-iren bambance-bambancen da yake ta gani kenan tsakanin Sophie da Azeezah, ko abin ya dame shi, ba ya zuwa ko ina zai manta saboda cikin Azeezah yasa ya manta kansa, Azeezah ta gama da shi da mahaifiyarsa da danginsa sakamakon cikin, komai ta yi daidai ne a wurinsu, ba mai iya cewa don me.
Baba Murtala kuma kullum kara jan Zayyan yake a jikinsa yana buda masa hanyoyin samu. Don haka kafin cikar shekara da zuwan Azeezah Safiyyah ta koma ‘yar kallo a gidanta.
Rashin adalci irin na kowanne Da namiji nata mijin is not exempted, musamman wanda ya samu kansa a kwatankwacin irin wannan situation din, ga haihuwa za’a masa ga ubanta ya baibayeshi da hanyoyin samu, yanayin rashin kulawar da Zayyan ke gwada mata yanzu, sai dai kawai ta kauda kai, ko ta yi masa uzurin da ba ta gajiya da yi masa shi, amma hakika Zayyan ya canza gabadayansa.
Desperation dinta kuwa a kan son haihuwa a yanzu babu shi. Tun samun cikin Azeezah Safiyyah ta yi addu’a ta kwantar da hankalinta. Normal ta ke harkokinta cikin gidanta, saidai bata da karsashi bata da wata power a gidan. Hatta ma’aikatan gidan basu damu da ita ba kamar yadda suke shakkar Azeezah da respecting dinta cikin gidan ba.
Yaushe rabon da su zauna su yi ZANEn gadaje dana Estates ita da Arch. Zayyan? Daya na tada daya akan idea? The two Architects, the unique lovers! His own alter ego Sophie….. yanzu ta nesanta daga zuciyarsa, sun komawa juna something different yanzu kamar Allah bai taba saka musu soyayyar juna ba sai girmama juna kadai. Babu irin hirarrakin nan nasu na baya masu kara ma soyayyahrsu danko.
Ita da Zayyan yanzu sai ‘yar agurguje. Wato in ya shigo sassanta kullum cikin sauri yake, in kuwa ranar girkinta ne ma watarana sai ta yi barci can dare ya kan shigo, idan Azeezah ta ga dama ta kyale shi ya zo dakin Sophie din ma kenan.
A haka rayuwar ke gangara musu har ranar wata lahadi da Azeezah ta haifo yaronta namiji mai kama da autar Mama sak (Hatoon).
Kasancewar cikin dare Azeezah ta haihu kuma a gida cikin gajeruwar nakuda, ko kafin ya fiddo mota daga ma’adaninta, haihuwar ta zo gadan-gadan lafiyayyen yaro ya sako kai.
Don haka dole Safiyyah ce zata iya taimaka masa on emergency. Ya kuma yi waya ya kira asibitin da take awo suka turo nurse ta kula da ita zuwa wayewar gari. Kukan jariri ya karade gidan gaba daya. Kukan ya tafi ya ratsa har zuciya da kwanyar Safiyyah…..yana mata amsa-kuwwa a kunne, daidai da karuwar bugun kirjinta.
Lokacin da ta ke karbar dan Zayyan (da wata matar ba ita ba) cikin cibin haihuwa da jinin haihuwa, wanda hakan ya kara tabbatar mata ta rasa Zayyan dinta kacokam! Yau forever!
Amma idanun Safiyyah ba su nuna hakan ba, ko kadan, sai tarin farin ciki da taya Zayyan murna.
Ta wanke jaririn nan sumul ta shafe shi da olive oil, sannan ta sunke shi cikin blue kayan sanyi masu matukar tsada cikin irin siyayyar da suka yi shi da Azeezah, sannan ne aka kira Mama aka gaya mata an sauka, sai Baba Murtala da Haj. Nanah!
Kafin wayewar gari Azeezah ta gyagije tayi wanka da ruwan zafi ta gasa jikinta tajikwari, ta karbi danta daga hannun Safiyyah, ta kura masa ido tana smiling, kaunarsa na ratsa ta nan da nan, tace, “Baby, da kai jaririn nan yake kama fa”. Ta fada tana murmushin jin dadi da alfaharin ita ta sunkumo wannan katon kyakkyawan yaron duniya, tana jan dan siririn karan hancin jaririn, wata irin soyayyar Da da mahaifi na dada mamaye ta.
Zayyan ya ce, yana manne su a jikinsa su biyun (ita da jaririn) ko kunyar idon Sophie ba su ji ba. Wadda ta sunkuyar da kai tana rokon Allah karfin zuciya na zahiri da badini, don gaba daya zuwa yanzu dakiyarta ta kai karshe. Zuciyarta ta karye da tausayin kanta.
Zayyan ya lura da hakan sai ya dan janye daga jikin Azeezah, ya dauko jaririn ya dora ma Sophie a kan hannayenta da cinyoyinta.
Ya ce, “Rike Babynki Sophie, ai na gaya miki dan ki ne, wanda muka haifa tare. Azeezah ta dade da yi min alkawarin da ya zo duniya ya koma hannunki”.
Sai a lokacin Azeezah ta tuno zancen da suka taba yi da shi kafin ya aure ta, da wanda suka yi ranar da aka yimata bushara da samun cikin, wanda a wancan lokacin ba ta dauki zancen wani abun ba.
Wani irin kallo ta yi musu shi da Safiyyah din, kafin ta mike zumbur ta sunkuce jaririnta daga hannun Safiyyah, ita kadai ta san wahalar da ta sha wajen rainon cikinsa da nakudar zuwansa duniya, sai kawai yanzu a zo ace an baiwa wata bakarariya kyautarsa don ta kasa yin nata cikin ta haihu?
Wani mikakken tsaki Azeezah ta saki ta ce, “Idan fitsari banza ne, Kaza ta yi mana. Ba wadda zan baiwa Dana, kana mafarki gaskiya, kowa ya yi zuciya ya haifo nashi in ya isa. Gaskiya Baby wannan expensive joke ne, na roke ka in wasa ka ke ka bari bana son irin wannan wasan mai daga hankali”.
Safiyyah na murmushin karfin hali, ta ce, “Ke ma kin san wasa yake yi. An taba raba uwa da jaririn da ta haifa yanzu-yanzu?”
Azeezah tace “ko na yayeshi din bazan bayar ba”.
Ganin ta dau huci sai Sophie ta mike tana gyara zaman hijab dinta a wuyanta, ta ce, “Bari in je zan gasa muku naman jego yanzun ina zuwa”.
Azeezah ta ce, “No. please, na hutar da ke, ba kowanne nama nake iya ci ba”.
Ba Safiyyah kadai ba, shi kansa sai da ya ji ba dadi a ransa, amma ko dagowa bai iya ya yi ba balle ya kwaba wa Azeezah ko ya ce ba ta kyauta ba abubuwan nan da take ma Sophie.
Wani a duniya bai taba cin fuskarta a kan rashin haihuwa irin yadda Azeezah ta yi yau ba…
Ko Mama bata taba gaya mata bakar data bakanta ranta irin wannan ba….
Kalmar idan fitsari banza ne kaza ma tayi ta saka ta tunanin shin ko ita ta yi wa Ubangiji wani laifi ne yake hukuntata a kan infertility? Ko kuma mai PCOS baida kwan haihuwa ajikinsa?
Hakika yau ta kara tausayawa duk macen da Allah bai baiwa haihuwa ba, kishiya ta zo ta haifa a madadinta.
Sophie ta ji wani irin emotion mara fassaruwa yana mamayarta, a lokacin da ta ga Zayyan dauke da dansa da ba nata ba yana sumbatarsa yana sunsunar wuyansa da fuskarsa. Ba ta ji haushi ba ko mamaki don Azeezah ta hana ta rikon danta, face bakar maganar data gaya mata, don dama ita tun lokacin da ya fadi hakan cewa zai auro Azeezah ne don ta haihu tabata dan bata wani yarda ba, ta sa a ranta wannan almara ce irin ta maza masu neman excuse na abarsu suyi aure.
Azeezah yau tace da ita idan fitsari banza ne, itama tayi, tabban haihuwa ba abun banza bace tunda tasan ita bazata iya ba, kalmar ta kusa zautar da zuciyar Safiyyah saboda tabo can kasan ranta, ta hada wani tarnaki kamar na dan sansanin yaki a kirjinta.
Har ta soma tunanin ko dai lokacin da zata bar Zayyan ya zo?
Don ko makaho ne ya shafa ya san Zayyan ba ya bukatarta cikin rayuwarsa ta yanzu, kawai yana kokarin yi mata kara ne da bata girman da yakasa daina bata. But he found his own family now.
Zuciyarta ba abinda bata saka mata a yau ba, a kan gara kawai ta hada yanata-yanata ta bar gidan Arch. Zayyan, tunda har aka gaya mata wannan maganar a gaban sa bai ce komai ba bai tsawatar ba haka bai biyo bayan ta ba don ganin halin da maganar ta jefata a ciki.
Wata zuciyar kuma ta ce, “daure Safiyyah, kin yi hakurin shekaru kusan goma sha uku for now, kina tafiya za’a ce bakin cikin haihuwar Azeezah ne ya kore ki.
Watakila ma asaki a waka a gidan Bello Rafindadi.
Besides, ta fanninsa yana kokarin faranta miki ko yaya ne, ko da kuwa adalci yake kokarin yi miki din, ba don so ba.
Amma ya dace Zayyan ya kyale Azeezah ta gaya mata irin wannan bakar maganar ko bakin gorin a gaban idonsa bai ce komai ba?
Hajiya Nana ce ta kira Zayyan ranar da ta zo ganin Baby, ta ke ce masa, ba ta yarda Azeezah ta je wanka gida ba, yadda ta tsara za ta taho bayan suna.
Ta ce, wannan jaririn ban yarda a hau jirgi ko mota da shi kwana bakwai da haihuwa ba, don haka ga Goggona Atika da na turo mata za ta ci gaba da zama da su har ta yi arba’in, ko me ya kamata za ta yi musu a nan, kai ma kuma sai ka saka ido a kansu sosai, don sanin kanka ne Azeezah nutsuwa ba ta ishe ta ba”.
Shi ma ai ya fi son hakan, don ba ya son nisa da su ko na minti daya. A rashin adalci irin na Da namiji sai ya zo ya samu Safiyyah a kan maganar, ya ce,
“Sophie, me kika tsara a kan sunan Baby?”
Tana juya miya a kan wuta ba tare da ta juyo ba, amma ta dan dakata. Ya jingina da cabinets din kitchen dinta ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallonta. Sai ya ga duk ta kara ramewa, ramar kuma ta kara fiddo dogon karan hancinta sarari da dara-daran idanunta. Safiyyah ta ce masa,
“Ban san tsarin Azeezah ba, don ka ga ba son yin magana ta ke yi da ni a kan haihuwarta ba.
Ni dai na gayyato su Sabah su zo suna tare da Anti Assafe matar Yayanmu da suka dawo daga Egypt last year. Sannan Anti Dije ma na gayyato ta amma ta ce ba za ta samu zuwa ba don Ni’ima ma ta haihu tana jego a hannunta”.
Ya ce, “Alright, na ji tana cewa za ta yi babban taron suna ne a nan gidan, duk mai son zuwa ki gayyato shi, sannan Sophie ina neman alfarmarki please, ki bar ma Azeezah kwanakin girkinki har su yi arba’in.
Mamansu ta ce tana tsoron abin da zai je ya zo in aka barta ita kadai cikin dare, duk da akwai wadda ke zama da su amma gara ina tare da su. Kin san Azeezah ba kan-gado ne da ita ba. Ki bar ni in koma wajensu don in dinga kula da su sosai in dinga ganin abin da suke ciki, Azeezah ba nutsuwa ce da ita ba sam, barcinta zatayi ta kyalemin yaro yayi ta kuka”.
A zuciyar Safiyyah ta ce a ranta, “A hakan dai ai ka ce ka ji ka gani. A rashin nutsuwar da rashin kan-gadon ka aure ta kake hutawa da ita ai har kuka haife”.
Amma a fili sai ta yi kokarin ba shi amsa da cewa,
“Ba wani abu, I will look for something that will keep me busy!”.
Sai bayan ta fadi hakan ne kuma ta ji wani irin rauni (weakness) din duniya ya rufto mata, taji kadaicin duniya ya lullubeta kamar ita kadai ta saura a duniya saboda rashin ‘ya’ya, yau Zayyan ne yake neman maraba da ita, yake neman ta ba shi izinin ya nisance ta kwana arba’in don ita ba ta haihu ba???
Ba tare da ya lura da halin da ya jefa ta ciki ba ya bar kitchen din sakamakon kiran wayar Azeezah, Safiyyah ta bi shi da kallo yana fita kitchen din yana kara ficewa a ranta, har ya fice.
Ranar suna ne Baba Murtala ya biyo jirgi ya zo ganin takwaransa da sassafe. Azeezah ta dage sunan Babanta za ta saka ba nasa ba. Haka shi da Mama suka hakura da saka sunan Baba Bello da suke so a yi, aka sa na Baba Murtala.
Ai kuwa da ya ji an masa takwara yau da ya zo ganinsa mukullin Estate guda ya bayar a Lagos ya ce a ajiye wa takwaransa, ya maida hakkin mallakar Estate din na yaron halak-malak.
Karon Baba Murtala na farko kenan da zuwa gidan tun auren Azeezah da Zayyan ya yi, shi da kansa ya lura babu matar Zayyan a cikinsu duk shagalin da akeyi, sai ya ce a kira masa uwargidan Zayyan ya hada su ya yi musu addu’a.
Safiyyah ya kira a waya ya ce ta zo falon Azeezah ga babanshi ya zo.
Da sallama ta shigo falon cikin nutsuwa da hijab dinta. Baba Murtala ya hada su ya yi musu nasiha ya kuma saka musu albarka. Bai jima ba ya tafi.
Sabah da Rayyah da farko cewa suka yi su fa ba za su je sunan gidan Yaya Safiyyah ba. Don ba sa son ganinta cikin wannan yanayin tausayi take basu wai gayyar sunan kishiya. Ammi ta karfafe su da su je, sune karfin gwiwarta a ranar, don ta tabbata dangin Zayyan bazasu kyale Sophie hakannan babu gori da habaici ba.
Sabah ce ta yi ma Assafe waya ta ce, ta san kishiyar Yaya Safiyyah ta haihu, to Ammi tace za su je Abuja suna. To shi ne Assafe ta gaya ma Yaya Sheikh. An yi sa’a ‘yan kirkin nasa na kusa, sai ya ce ta shirya ta bi su Sabah din kawai tunda da ma ta dade tana son zuwa.
Zai yankar mata tikiti daga Lagos zuwa Abuja. Saita hadu dasu Sabah acan. Amma Assafe ta yi ta nacin shima ya bi su ko na wuni guda ne Safiyyah ta ganshi, ta ce, tasan zata ji dadi tasan itama tanada gatan ‘yan uwa, ita ta kasa gane wannan abun tunda ya zo kasar Nigeria yake gudun haduwa da kanwar tasa, mafi soyuwa a gare shi.
Gudun kada Assafe ta yi masa wata fassara daban, don shima kansa ya kasa gane kansa din, ya sa ya yarda kawai su je tare Abujan watau gidan Safifi harda shi.
Don haka ranar suna wajejen la’asar suka shiga Abuja shi da Assafe.
Tuni su Sabah kuma suna gidan tun azahar daga Dandume.
Ita ta yi ta directing direban da ya dauko su daga filin jirgi shi da Assafe zuwa Sunset Estate, gidan da ya kere kowanne a Estate din watau gidan mamallakinsa Arch. Zayyan Bello Rafindadi.
Sune har cikin Rafindadi close, Ridhwan na kallon Estate din a sheleke, kafin suka iso gidan, Yaya Sheikh sai ya daga kai yana kallon gidan mijin Safiyyah, da irin dankareren Estate din da ya mallaka, watakila shi ya sa yake son haihuwa (a ganinsa kenan) yake aure-aure ko don wannan dukiyar daya tara, zai so dansa ko ‘ya’yansa su gada.
Tsaki ya yi kawai yayi zamansa a kofar gida, kuma bai shiga gidan ba, sai da Sabah tasa Zayyan ya aiko da kansa aka shiga da shi har sassan Safiyyah, bayan ta yi masa waya ta ce, Yaya Sheikh, ya zo da iyalinsa.
To ba ya gida ya yi nisa kadan, saboda yau ne Azeezah ta ke taron sunanta da yamma. Sai aiko Umaru mai wanki da guga ya yi masa jagora har falon Safiyyah.
Bangaren Azeezah ya cika makil da ‘yan suna. ‘yan uwanta dana Zayyan. Ko kare bai leka sassan Safiyyah ba a cikin danginsa. Bangaren Safiyyah kamar an share, ma’ana babu kowa sai kannenta Sabah da Rayyah. Sai ko Assafe da Yaya Sheikh da suka yi sallama yanzun a falon.
Safiyyah couldn’t control her tears… lokacin da ta yi arba da Yayanta Ridhwan, shi ma kuma kasa dauke ido ya yi a kanta yana cewa, “Safifi, ba ki da lafiya ne?” ganin yadda kasusuwa suka bulluko a wuyanta suka yi mata sarka.
Tana danne hawaye da hannayenta, tana danne kuka da halshenta, ta kama hannun Assafe tana kokarin furta mata sannu da zuwa ta kasa, Yaya Sheikh ya daka mata tsawa, ya ce, “Ke Safifi, na ce ba ki da lafiya ne? Ko ba kya cin abinci? Ko kuwa Depression kike fama dashi haka?”
Kukan da ta ke rikewa ne yanzu ya kece mata, wane bayani za ta yi masa ya fahimta?? Tana cikin damuwa wadda daga ita sai Ubangijinta suka santa.
Zayyan dinta ya subuce mata, tunda ta kasa haifa masa Da ko ‘ya? Ko kuwa tace masa itada Zayyan yanzu sun koma gasu nan ne dai sunan wai suna aure, amma babu soyayya, shakuwa babu wannan intimacy din namata da miji tsakaninsu kamar basu taba kaunar juna ba? A barta wulakancin da take kwankwada wajen danginsa da mahaifiyarsa da Azeezah kanta.
Dr. Ridhwan ya ce, “Safifi idan cutarki ake a auren nan ki bude baki ki gaya min in kwato miki hakkinki, in Malam bazai iya ba saboda kawaicinsa ni gani na dawo kuma bakida wanda ya fini, dukiya ba hauka bace kinji! Idan ma kwadayi ne ya zaunar da ke ake wulakanta ki kan rashin haihuwa ki dauko mayafinki mu tafi”.
Assafe ba ta taba ganin tashin hankalin Ridhwan irin wanda ta gani yau ba. Ko gutsurar naman Safiyyah Zayyan ke yi karshenta kenan. Kin zama ya yi a kujerar da Sophie ke nuna masa, ya ce, shi juyawa zai yi, a ransa ya ce, amma tabbas dole a zauna a yi magana da Zayyan din nan, in ya gaji da aurenta ne ya sallama mata, shi da ma ya riga ya san kansa a kan Safiyyah ba shi da hakuri, shi ya sa tuntuni ya ki zuwa, don ba ya son ya zo ya ganta cikin yanayin da zuciyarsa ba za ta jure ba.
Daga yadda Ammi ta ba shi labari ya san Safifi is in pain, true pain irinna mace akan ‘infertility’, ko ba ta furtawa kowa ba.
Da kyar Safiyyah ta iya magana a lokacin Ridhwan har ya kai bakin kofa.
Ta ce, “Yaya Sheikh, idan ka tafi ba ka sha ko ruwan gidana ba, ba zan ji dadi ba, ni babu abin da ya same ni fa. I’m, just moody!”.
Ta mika masa gorar ruwan da ta dauko masa a firji da tambulan.
Bai yi musu ba ya karba, sannan cikin wani yanayi wanda ya zarce na tausayi sai ko bacin rai, yace,
“kiyi hakuri da abinda zance miki Safifi, na san kina son mijinki ba tun yau ba, amma sau tari wani auren dashi gwara babu, baya zama dole idan babu farin ciki a cikinsa”. Duk yadda Safiyya taso ya zauna yaki, bai jima tare da su ba, ya ce musu tafiya zai yi Dandume. Ita Assafe ta zauna su taho tare da su Sabah washegari.
Safiyyah ta shiga ina taka saka ina taka aje da Assafe. Ta yi mata tarba ta musamman a sassan bakinta.
Assafe da su Sabah suka baje a sassan Sophie ranar sunan Azeezah, suka hana ta damuwa da komai sai hidimarsu kadai. Su Zubaida da duka kannen Zayyan sai shiga suke suna fita a gidan, ana karrama ‘yan uwan Azeezah da manyan bakin da suka gayyato, nata ‘yan uwan kuwa ko kallo ba su ishe su ba. Ko abincin suna da aka yi kala-kala na alfarma babu wanda ya damu da a ware a kawo sassan uwargida.
Mama ba ta zo ba don bata da lafiya, ta wayi gari ciwon suganta ya motsa ranar sunan.
Duk abubuwan da ake yi a gidan Assafe da ‘yan uwan Sophie na lura, amma sai suka ga ita Safiyyah din ko a jikinta. Ko a cikin dangin Zayyan babu wanda ya tako kafarsa a sassanta, balle a ba ta girmanta a dauko jaririn a kawo mata shi tayi masa addu’a. Itama kuma tun daga irin habaice-habaicen da Yaya Zubaida ke saki tunda safe, sai ta kama kanta, ta killace mutuncinta a sassanta bata shiga sabgarsu ba.
Yaya Zubaida har rawa ta ke a gaban kowa, tana fadin, “Magajin gida ya iso, Magajin Bello Rafindadi yazo, mai wuri ya zo mai tabarma sai ka nade kayarka”.
Ta ce, “Yanzu ne muka san Bello Rafindadi ya bar bayansa, yanzu ne muka san Baffan Mama ya yi auren da ya maida shi cikakken mutum!”
Har falon Sophie ta shigo ta yada wadannan maganganun, kafin zuwan su Assafe. Idan Sophie ta daga ido ta kalleta ma ta samu, don hakika ita bata ma san me ta ke ji a ranta a lokacin ba.
Ji ta yi tamkar ta zama hoto ko mutum-mutumi a gidan Arch. Zayyan Bello yanzu, wato ta zama tamkar ‘image’ a gidansa amma ba matar gida ba.
Haka nan Yaya Zubaida ta sake maimaita wadannan kalaman a gaban Hajiya Barmani Choge, mai kidan kwaryar da Azeezah ta dauko tun daga Katsina, Zubaina ba ta zo ba, don mijinta bai barta ba.
Aka yi kasaitaccen suna na gayya da huce shekarun da aka yi ba’a haihu gidan Arch. Zayyan ba. Aka watsar da doller kamar a bola ake debosu daga iyalin Baba Murtala dana Bello Rafindadi. Shi kuma tunda ya fita yau ba ya cikakken awa daya bai kira Azeezah a waya ya ji yadda abubuwan ke tafiya ba.
Ya ji kuma ko ta bai ma Baby nono, don yasan halinta sarai, kada ta shiga hidima ta bar masa yaro da tsotsan hannu.
Iyayen Azeezah sun yi rawar gani har fiye da burin Mama, an barar da dukiya a gidan Zayyan kai ka ce ba’a san zafinta ba, saboda takwara da aka yi wa Alhaji Murtala.
To bayan suna ne yake kiran yaron SHAHEED, ita kuma Azeezah ta ce masa Daddy.
Wannan jaririn masu aiki biyu aka ajiye masa mai raino da kula da shan madararsa da kuma mai kula da tsaftar kayansa, don Azeezah ba ta damu da breastfeeding ba, tana tsoron duk abin da zai canza halittar jikinta kota yankwane. Sai yanzu da Shaheed yake hana ta barci da kukan dare, da tumbudi most attimes, ya kuma hana ta holewa da mijinta ta soma tunanin dama Safiyyar ta bai wa rikonsa. Don kiri-kiri Zayyan ya fi bashi kulawa yanzu fiye da ita.
Kwana goma sha hudu kacal da haihuwa Azeezah ta ce ta gaji da jego, za ta yada wanka. Baba Atika ta yi kundumbala ta hana ta, ta ce ba ta isa ba. Saidai ta mutu amma bazata barta ta komawa miji da jaririn sati biyu ba. Don tsohuwar ta gane ba komai ke damun Azeezah ba tunda jinin biki ya dauke mata sai kulafucin mijinta yanayawan shiga sassan uwargida, ita kam haihuwar nan ta hana ta rawar gaban hantsi.
Yaron nan ko fitsari daya ya yi cikin pampers sai an canza ta a take. Haka zaka ga pampers anzubar fululu a rana kamar banza. Akwai wardrobe ta musamman da babu komai a cikinta sai madararsa da pampers dinsa. Kamar yadda ya roki Sophie alfarma gabadaya ya tare yanzu a wurinAzeezah da yaronta wai yana taya ta kula da Shaheed.



