⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 11: Chapter 11

Cikin laifukan da ya tabbatar ya yi wa Safiyya, har da alkawarin da ya yi na bata danshi na farko, Azeezah ba ta bar shi ya cika mata wannan alkawarin ba, ta tozarta Safiyyah akan hakan a gaban sa bai ce komai ba, don daga baya har kararsa ta kai wajen Mama ta ce zai raba ta da danta….
Duk da tun a lokacin Sophie ta mayar da zancen wasa, ita Azeezah ba ta mayar ba, da gaske ta dauki fushi da tashin hankali a kai, sai da ta kira Mama a waya ta gaya mata ga Zayyan nan zai kyautar mata da jaririnta ga matarsa.
Ai kuwa Mama ta saka salatin gaske, ta kira shi ta yi masa tanadi irin wanda ba ta taba yi masa a kan Sophie ba, ta ce “da yake daukan cikin da haihuwar abun banza ne ko? Baffa to ka dauka ka ba ta din, sallamamme wanda aka gama shanyewa a minjaye. Sullutun wofi mai soyayyar da babu riba.

Ai sai ka dauka ka bata din mu gani tunda kai ka yi mata nakuda… Ni na rasa irin wannan So na masifa da jaraba. Yo na masifa da jaraba mana! Tunda babu ribar da ka ke samu a cikinsa sai tarin wahalar ciyarwa da tufatarwa da wahalar yawon asibiti. Idan don soyayya ake aure, Allah ya tsine ma soyayyar da ba za a haihu ba. Na kuma bi ta da gudu ni Fatu, na tattake ta ba takalmi a kafata!”.
Da haka da haka dai Mama da Azeezah suka kashe batun alkawarin da ya yi ma Sophie na bata rikon dansa Shaheed. Wannan bai isa ba, shi da kansa dokin haihuwar da ya dade bai samu ba ya sa ya gallaza wa zuciyar Safiyyah kwana arba’in ta hanyar hana ta girki, wanda hakkinta ne da Allah ya bata, ba fadar kowa ba ne, fadar Allah ne dole a bata kwanan aure tana haihuwa ko a’a.
Duk da haka Safiyyah ko a fuskarta bai ga wani abu mai kama da bacin rai ko canji ba. Duk ta dauke shi a matsayin gudunmawarta na taya Zayyan dinta murnar karuwar da ya samu. Amma shi da kansa yau din da ya gama dokin haihuwar ya dawo inda take, ya rike ta cikin jikinsa ya ga sauyi a tare da Safiyyah, ya kuma ji a ransa cewa hakika bai kyauta ba. Karshen rashin adalcin da namiji zai yi wa mace kenan, don an yi masa haihuwa yana dokin yaro ya hanata kwana.

Bayan madaukakin so da ya tabbatar yana yi wa Safiyyah irin wanda bai taba yi wa kowacce mace a duniya ba, a yau yana jin tausayinta, yana jin kunyarta a bisa jarrabawar Ubangiji a gare ta, ta rashin haihuwa wadda duk ita ce silar ma da ta kai shi ya kara aure, wanda a yanzu ya nesanta shi da Sophie.
Har rawa-rawa ya ji saman idonsa na yi ganin irin janyewar da Safiyyah ta yi daga gare shi, ta kara kawar da kanta daga inda yake cikin jin haushi da takaicin rungumar da ya yi mata.
Amma da yake Zayyan kunya ba ta ishe shi ba, sai ya basar kamar bai ga kallon haushin da ta yi masa ba, ya ce, “Sophie zan samu ruwan wanka mai zafi?”
Safiyyah bata dube shi ba, ta amsa da karsashi.
“Sosai kuwa Zayyan, yana nan a heater”.

Zayyan ya dan hadiyi miyau da kyar, ya ce, cikin raunin murya tare da harde hannuwansa saman kirjinsa, yana kallon Safiyyah daga tsakiyar idonsa, wadda ke kokarin canza kayan sallarta zuwa kayan barci.
Har yau har gobe tana nan a beautiful Safiyyarta, jikinta sumul-sumul kamar na budurwa ko mai shekaru ashirin. Komai nata cikakke danye sharaf! Duk da Safiyyah ba ta saka kayan da zai bayyana surar jikinta sosai, a hakan ma ba ta daina daukar hankalinsa a lokuta irin wadannan ba.
Yanzun ma wata sleepping dress ta dauko za ta saka mai kauri kadan, don ita bata saka lingeries, jikin rigar kuma mai santsi ne sosai. Tana kokarin saka rigar sai tawul din data daura daga kasa ya zame gabadaya duk a idon Zayyan da ya tsaya kallonta kamar tsohon maye.
Safiyyah ba ta yi aune ba ta ji Zayyan ya sure ta gabadaya, bai dire ta ko ina ba sai tsakiyar gadonsa, saman ruwan cikinsa, tana ta wutsil-wutsil din kwacewa yana mata magana cikin lallashi da hila…
“Wato yau da kaina zan dafa ruwan wankan ko Safiyyah? Tun daga ranar da na yi aure kin tsane ni gabadaya Sophie, duk abin da zan yi na daina burge ki.
Duk abinda kika san zai faranta min kin daina yinsa, kin maida mu wasu bakin juna. Your soft laughter, your caring smiles duk na manta kalarsu da launinsu.
Kin daina taya ni Zane Sophie. Kin daina hira da ni, kin daina taya ni creating ideas din Zane-zanenmu.
Hatta Profession dina ya fara ja baya, saboda komai nawa da ya canza yanzu a dalilin rashin saka hannunki, bana bai wa komai lokacina irin yadda nake bayarwa a baya. Sai Shaheed da Azeezah kadai. Ban sani ba ko laifi ne karin aure ga namiji, don cika sunnar ma’aikinsa, da kiyaye kai daga aikata zina?”

Safiyyah duk yadda ta ke jn tsanar Zayyan, hakan bai hana ta jin tausayinsa ba, a lokacin da ya furta hakan, a bisa wadannan maganganun nasa masu nuni da kaddararsa. Duk da haka ba ta ce komai ba, ba ta kuma taya shi sumbatar da yake mata hungrily har da hawaye ba.
Ganin ya yi nisa sosai yana son su hutar da zukatansu, su raya daren cikin soyayya, su bai wa sabaninsu baya kona dan lokaci ne, alhalin ita zuciyarta ta riga ta gama bushewa, babu komai a cikinta da ya saura na soyayyar Zayyan Bello, sai tawakkali da biyayyar aure. Don haka Sophie ta taka masa burki, ta ce,
“Zayyan, please don’t force yourself to make love with me wai don ka faranta min. mun wuce wannan matsayin.
Barmu mu ci gaba da irin zaman da ka zabar mana, kwanaki arba’’in!
Ni ba komai ba ce a gareka yanzu face mai gadin sassan uwargida, kuma matar ladan noma da Babana Baba Bello ya aura maka.
Na rantse da Allah ba na bukatar wannan rayuwar daga gare ka yanzu, ko ka yi tarayyar aure dani by force, ina tabbatar maka za ka yita ne da gangar jikina, amma ban da zuciyata…
Haihuwar ma bana bukatarta yanzu na yi rantsuwa da Allah ba ta raina, ko in ce, in dai don ita ake making love to ni na hakura da ita… na yafe…”.
Daga yadda ta ke furta kalaman kadai ka san suna fitowa ne daga kasan ruhinta, bitterly, kafin wani kakkarfan kuka ya ci karfinta ya kwace kansa.
Sai a lokacin Safiyyah ta lura cewa shi ma Zayyan kukan yake, amma sabanin nata, nashi na hawaye ne, zallah ba sauti, sannan maganganunta na raddi a gare shi ba su sa ya fasa abin da ya yi niyya da ita ba, yana yi yana istigfari a zuciyarsa. Ganin yadda jikin Sophie ke responding cikin kishirwar abun.

A fili kuma bayan ya samu gamsuwar da yake so, da kyar ya iya cewa,
“Ki yafe min Safiyyah, na cancanci kowacce kalma da za ta fito daga bakinki a yau, amma ki yarda haka Allah ya kaddara min zan rayu, wato kaddarar auran mata biyu! Wadda zuciyata ke matukar so, da wadda gangar jikina ke shaáwar kasancewa da.
Ki sani Safiyyah zan iya rayuwa da ke cikin kowanne hali ko babu haihuwa in dai za ki bar ni na rabe ki cikin ni’imar aure, ba zan iya rayuwa cikin horon da ki ke yi min na sexual denial ba, na yi aure ne domin kawo mana maslahar hakan, amma ba don rashin haihuwarki ba.
Na san na yi laifuffuka gare ki masu girma, har guda biyu. Na kasa cika alkawarin da na yi miki na ba ki yaron da Azeezah ta haifa, wanda ni ma an fi karfina ne a kan hakan. Sannan na yi kuskuren kaurace miki na koma gurinsu kacokam, amma ai sai da na nemi yardarki da amincewarki.
Ki yarda da gaske Azeezah ba ta da kula, ba za ta iya kula da jariri sabon haihuwa cikin dare ba. Bata kuma son shayarwa sai taga idona. Dalilina na kasancewa tare da su kenan, a kwanakinsa arba’in na farko na rayuwar duniya don in kula da shi”.
Safiyyah ta ce, “Zayyan ban ce ka yi min laifi ba. Ban ce ka yi ba daidai ba. a abinda ka yi, amma idan na ce maka ina sonka irin yadda nake sonka a baya na yi maka karya wallahi”.
Ta fashe da kuka, ta ce, “Ällah yana fushi da macen da ta ce mijinta ya sake ta, ban da haka da na ce ka sake ni, in koma gaban iyayena talakawa wadanda ba su da abin da za su baku ku kara a kan arzikinku.
Aurenka da ni an ce bai tsinana maka komai ba, faduwa ne da asara, tarin wahala da dawainiya…”.

Gabadaya kalamanta kara rura wutar sonta suke a zuciyarsa, suna kara zurfafa zafafan sakonnin ya ya yi wata daya da kwana goma bai mata su ba. Tun jikinta ba ya karba har hormones dinta na dan Adam suka soma responding.
Idan ta ce ita ba ta yi kewarsa a fatar bakinta ba zuciyarta da ke raurawa, da rawar da jikinta ke yi na karbarsa a daren ranar sun karyatata. Sosai suka goge wa juna duk wani burbushin tsatsar da ke cikin zukatansu, da ciwon son da ke addabar zuciyar kowannensu. Zayyan ya tashi kan Safiyya da soyayyah fiye da ranar farkonsu, wanda a cikin wannan daren daga Zayyan har Safiyyah.. sun yarjewa kansu bacin rai ko fushin zuciya ko KAWAR ZUCIYA irin nasa baida alaka da soyayyarsu ga junansu, sai dai rayuka su baci, kishi ya taka rawarsa, shaidan ya buga musu gangarsa, amma a karshen duk hakan Safiyyah-Safiyyah ce a gurinsa, wadda ita kadai ce nutsuwarshi.
In ka gansu a wayewar garin ranar kamar ba su ba. Sun manta komai Sophie na ta kai kawo a kitchen. Ta yi masa karin kumallo irin wanda ya dade bai samu daga wurinta ba suka karya tare can a dakin barcinsu, yana makale da Sophie duk motsin da ta yi sai ya ce, “Safiyyah yaya?””
Azeezah ta kira shi a waya har ba adadi kamar hauka, ya ki dagawa, daga karshe ma sai ya sa wayar a silent ya manta yana da waya a dakin.
Bayan sun yi wanka suka bige da kirkiran sabon zanen estate kasancewar ranar lahadi ce ba inda Zayyan ke zuwa.
Kwance suke a kan gado kafafunsu harde cikin na juna suka kirkiro sabon zanen wani gida mai ban sha’awa da kayatarwa.

Ba shi ya fita zuwa sassan Azeezah ba sai gefen azahar, sai a lokacin ne ma mai rainon Shaheed ta kaiwa Mama abincin ranarta. Yana shiga dakinta tana canza wa Daddy diaper, ta dube shi sama da kasa ta watsar don wani sabon annuri ta gani a tare da shi kamar sabon ango.
Ya ce, “Ya ya dai Maman Shaheed, good afternoon, ya Shaheed ya kwana?”
Ya fada yana daukar yaron zuwa kirjinsa.
Azeezah ta ce, “Mun kwana lafiya ba mu mutu ba, don ka tafi wajen tsohuwar zuma, mu ai kishi ba ya ramar da mu kullum mace kamar kudin guzuri.
Watakila yau tunda ta samu an kwana da ita sau daya a wata za ta fara murmurewa”.
Dariya da takaici maganarta ta bashi, ya ce, “Na yarda kishi ba ya ramar da ku, amma yana hana ku barci ai. Don na ga missed call 39 tsakar dare.

This is my last warning Zeezah, kada ki kara kirana cikin dare ranar girkin Safiyyah in ba rashin lafiya ce mai karfi ta faru ba”.
Wani banzan kallo Azeezah ta yi masa, ta ce, Äikin banza, to sai me don ban kira ka ba? Allah ya sa ma daga gidan ubana ka daukoni, ba daga sama ka dauko ni ba”.
Ta fashe da kuka tana cewa, “Idan ka haifu ka ce in koma gidanmu ka gani in zan kara kwana a akurkin gidanka, wanda bai fi dakin maigadin gidan ubana ba”.
Maganarta ta yi masa mugun ciwo, ya ga cewa in ya ci gaba da tsayuwa Azeezah neman rigima ta ke ji yau, za ta daga masa murya har Mama ta ji. Sai ya juya ya bar mata dakin zuwa guest wing, wato masaukin da suka sauki Mama.
Ya yi sallama Mama ta amsa daga kwance, abincin da mai aikin Azeezah ta ajiye mata yana daga gefe ko tabawa bata yi ba. Allah kuma bai ba shi ikon budewa ba don yana sauri zai fita. Suka gaisa da Mama, ta ce, “Miko min fresh milk a firjin can”.
Ya miko mata ya zubo a tambulan ya kawo har bakinta ya kafa mata ta sha sosai. Mama na son ta ce ba a kawo mata Shaheed ba tun safe, amma dai ta yi shiru don Azeezar ma kanta ba ta zo ta gaishe ta ba tun jiya da suka kawo ta masauki, ba ta kara ganinta ba, kuma ko a waya Azeezah bata kirata ta gaishe ta ba. Yanzun nan dai Sophie ta zo ta gaisheta ta fita, lokacin yana dakin Azeezah.

Duk da ba wai gwaninta gaisuwar tata ta zame wa Mama ba, amma akalla ita da ba a damu da ita din ba ita ce ta san da zamanta a gidan.
Ya ballo magani ya bai wa Mama ta sha da ruwa, ya yi mata sallama a gurguje, ya ce zai je sai dare kuma zai dawo yana da appointment har biyu ban da haka ba ya fita ranar lahadi. Mama ta yi masa addu’a ya wuce.
Sai bayan fitarsa ne can wajen karfe uku yunwa ta addabi Mama ta janyo warmers din da mai aikin Azeezah ta ajiye mata tun dazu. Tana budewa ta ga farar shinkafa da miya jawur da yankan nama uku batso batso dashi, ta tuna bayanin da likita ya yi ma Azeezah na cewa banda shinkafa a abincin Mama in ba diabetic rice din basmati ba. Wannan kuwa normal shinkafa ce suka dafa mata.
Da ta dandana miyar ma zafin attarugu ya sa ta yi saurin rufewa. Ita da kanta ta kira Azeezah a waya ta ce,
“Maman Shaheed kin duba abincin nan na yarinyar nan ta kawo min kuwa?”
Azeezah da Zayyan ya gama batawa rai yanzunnan, sai Mama ta taka sawun barawo, ta ce,

“Kamar yaya na duba? Ki tambaye shi ki ji ni ko kitchen ba sosai nake shiga ba. Sai na yi sati ban bi hanyar kitchen ba, Janet ce ta yi ba ni ba”.
Mama ta hadiye fushinta ta ce, “Azeezah, ni ce Hajiya Fatu, ko ba ki san da wa ki ke magana ba ne?”
Azeezah ta ce, “Ni kuwa na san Maman Rafindadi ce. Wallahi kuka ishe ni ke da shi zan bar muku gidanku, ni ba malamar jinya ba ce da zai dauko ki ya ce ki zo ki yi jinya a gidana in kula da cinki da shanki ba, ni ma gidan nan kula ake da ni, ba ni in kula da wani ba. Ko bai gaya miki na fi cin abincin Cilantro ko Blue cabana ba?”
Mama sai ta kashe wayarta tana jin gabanta na faduwa.
Da daddare ma haka Janet ta kawo mata dankalin turawa da miya, kai kamar da gayya ake kawo mata duk abin da suka san mai diabetic ba ya ci, madadin wadanda likita ya zayyano a dinga yi mata a gaban Azeezah. Gobe ma haka aka yi, aka kawo mata koko da sugar a ciki zambadadau!

Idan sun yi abincin wanda za su ci shi suke baiwa Mama, basa wani yi mata nata daban. Azeezah ba ta inspecting abincin kafin su kai, kawai ta ce da su su dinga yin abinci kullum sau uku da Maman mijinta suna kaimata visitors wing.
Bunmi da Janet ba sa ko yin abinci a kan lokaci sai sun gama ayyukan gidan Azeezah gabadaya.
Ba wanda ya ankara da halin da Mama ke ciki a gidan danta har sugar level dinta ya zama low da yawa saboda yunwa.
Kasancewar Zayyan kullum da safe yake shigowa ya gaida Mama, sai kuma da daddare in ya dawo ya lura Mama dai jiki ya ki yin kyau yadda ake fata, ga magani tana sha amma kamar ba ta sha, har gara sanda ta ke Rafindadi, ‘ya’yanta mata na tsaye a kanta kan jiki kan karfinsu.

Sai ya dauko likitanta har gida ya ce shi kam ya kasa ganin improvement a lafiyar Mama, likita ya duba Mama sosai, ya ce, weakness ta ke fama da shi, kamar yunwa ce ba ta cin abinci bisa ka’ida.
Allah ya so ma Zayyan din ba ya wasa da cika wa Mama firji da fresh milk da Locozode da sauran unsweetened abubuwan sha. Ashe su Mama ta mayar abincinta don ba za ta iya kai masa karar Azeezah ba, kamar ta yi kirari ta daba wa kanta wuka ne.
Likita ya yi fada yayi ta fada sosai kamar ya bugi Zayyan, ya ce, “Ba matanka biyu ba? Amma cikinsu a rasa wadda za ta kula da cikin mahaifiyarka at this critical moment? Me ye amfaninsu in ba za su kula da cimar mahaifiyarka na dan lokaci ba?”
Zayyan har da zufa a kan goshi, ya rasa abin da ke masa dadi.

To bayan fitar likitan ne ya matsa jikin Mama, ya ce, “To Mama ke kika dage Azeezah ce kadai za ta yi hidimarki.
Abin da ba ki sani ba Mama, ita kanta ba ta iya kula da nata cikin ba balle ta kula da naki, ko yaronta sai na ce ta ba shi nono, in ba haka ba har na je na dawo madara ta ke sawa kabilu suke bashi. Ki yi hakuri Sophie ta karbi ragamar abincinki”.
Mama ba ta da zabi ai yanzu, shi ya sa ta ce masa ta yarda Safiyyan ta dinga girka mata. Don haka Zayyan kacokam ya maida abincin Mama hannun Sophie bayan ya hada ta da likitan Mama ya gaya mata irin abin da za ta dinga bata, bakinsa da nata.

Janet ta gaya wa Azeezah baban Shaheed ya dakatar da su daga kaiwa Mamansa abinci. Ko a jikin Azeezah ta ce, “Ta fi nono fari, kuma kun huta, sai ku maida hankali kan aikinku na kula da Daddy, ni ba ‘yar aiki ba ce, matar gida ce ban saba irin wannan wahalar a gidan ubana ba, ya kai wa diyar Alaramma ita za ta iya”.

Sophie ta karbi abincin Mama da kyakkyawar zuciya, ta sa a ranta kamar Ammi ce mai jinyar sugar dinnan ba uwar miji ba, in ta yi mata abincin sai ta yi plating dinsa yadda ya kamata with enough veggies, da nama isasshe. Inda safe ne za ta mata kunun acca ko na tamba. Healthy options, har fiye da yadda likita ya umarce ta. Musamman ta je kasuwa ta yo cefanen girkin Mama daban, sannan duk sanda ta kai mata lunch ko dinner sai ta hada mata da fruits kala-kala. Wani zubin dinner din Mama gasasshen kifi ne Salmon ko Tilapia. Tana kuma yi mata su Oats haka lokaci-lokaci da zabo mata unsweetened yoghurts. Abincin Mama kullum lafiyayye mai kara lafiya da kuzari, su dafaffen kwai da Avocados.
Haka Mama za ta lashe komai tana santi don ko mai girkinta ta Katsina albarka. Amma da yake Sophie marainiyar wayonta ce koyaushe ta shigo kawo mata abinci ba ta rabo da kananan rashin mutunci na bakar magana da gori, kuma ba godi bare an gode. Balle sannu da kokari.

Rashin mutuncin Mama a kan Safiyyah tamkar a jininta ne, bata taba ganin farinta ko alkhairinta.
Yau da daddaren nan wani irin gashin kaza Sophie ta yi mata mai ruwa-ruwa a oven, a gefe ta yi mata salad da steamed veggies. Mama ta bude ta gani miyanta ya tsinke ta mayar ta rufe, sai cewa ta yi da Zayyan da ke shigowa a lokacin.
“Ni diyar Alaramma kadai ka ke yi wa cefane mai kyau a gidan nan ne?”
Ya zauna a gefen daman Mama ya ce, “Mama barka da dare, ya ya jikin, duk da dai alhamdu lillah da alama jiki ya yi kyau yanzu”.
Mama ta ce, “Ba ka amsa min ba, na ce Diyar Alaramma kadai ka ke ma cefane mai kyau a gidan nan ne da abincita ya banbanta da nasu?”
Da kanshi ya bude flask din daya bayan daya ya ga abin da Sophie ta shiryawa Mama na lunch. Cike da gamsuwa da jin dadi ya ce, “Kamar ya ya Mama? Ina fatan dai kin ci abincin ko? Kafin ki tsaya tambaya mara tushe?”
Mama ta hade rai don ita kanta ta ji kunya da yau da idonsa yaga irin abinda Sophie ke Bata, ta kuma ga jin dadin Hakan da alfaharin hakan kwarai a idanunsa. Amma kokari ta ke ta ce baya yi wa Azeezah cefane mai kyau, shi ya sa ba ta bata abinci irin haka.
Cikin mamakin Mama Zayyan ya ce, “To wallahi Mama ni ban ma yi wa Sophie cefane ba, ban bata kudi ba, ban aike ta ba, na dai sa likita ya gaya mata duk abin da ya dace ne. Mama Sophie ta san yakamata ai, ba kamar wannan hauragiyar taki ba”.
Duk korafin Mama na rashin gaskiya da rashin godiya dole ta hadiye shi cike da borin kunya.

Washegari Zayyan ya ce ma Azeezah, kullum ta dinga kai Shaheed gurin Mama in an shayar da shi ya koshi. Azeezah ta ce su yawon arba’’in ne a gabansu ba zaman gida ba.
Yau tun safe ta shirya Shaheed da mai rainonsa Bunmi suka fice, gidan aminiyar Mamanta Justice Rahmatu a Gwarimpha yawon arba’in, daga nan suka wuce gidan kawayenta har hudu, don haka yau Azeezah bata dawo gida ba sai goshin magriba.
Gidan ba kowa sai Sophie da Mama, Sophie ta yi mata dinner na sinasir da miyar ganye da ya ji wadatacciyar hanta da koda.
Azeezah tun randa suka kawo Mama dakinnan sai yau ne ta kara shigowa for the second time tun zuwan Mama gidansu, Bunmi biye da ita dauke da Shaheed da ke barci cikin shawul.
A kofar shiga dakin Mama ne suka yi karo itada Sophie da ke fitowa, ai kuwa Azeezah dayake tana wuya da Sophie kwana biyun nan, sai ta ce,
“Ke da Allah ba kya gani ne? kodayake idon naki a keyarki yake, ba abinda kika sani sai gidadanci da nunkufurci da son a ce kin iya. Shine Mama wajenki ta zo? Kozamanki ta ke yi da ki ke faman zarya a dakinta?”
Abun ya yi matukar bai wa Sophie mamaki, ta tsaya kawai a inda ta ke tana kallonta.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *