Chapter 3: Chapter 3
Dariya ta yi, ta ce, “Ka ji da turancinka kai kadai, ga kanwarka Safiyyah ta zo ita ma, gashi ba ta jin dadi daga asibiti muke balle ince ta zo ku gaisa”.
Da sanyin murya Haroun ya ce, “A’ah ba komai Ammi, kyaleta ta huta, allah ya kara lafiya, ko zuwa gobe ne in bata koma ba in taji sauki sai mu gaisa”.
Ammi ta ce, “Wane komawa? Auren ya mutu ai, mijin ya sake ta, ni ma yanzun nan kafin mu shigo ta ke tabbatar min”.
A firgice Haroun da Malam suka dubi Ammi. Malam ji ya yi tamkar yanzu ne ya ji zancen cewa an saki Safiyya da ya tabbatar daga majiya mai tushe.
Duk suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Kafin Haroun cikin rawar murya ya ce,
“Ammi ban ji dadi ba. Allah ya halatta saki amma baya son sa.
Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ta da mu bakidaya”.
Ammi ta ce Rayha ta shiryo abinci ta kawo ma Haroun, amma sai ya ce ma Ammi shi a koshe yake.
Tun daga nan ya takaita magana don ya lura Malam ya fada cikin wani hali, idanunsa sun kada sunyi ja, sun canza launi. Don haka shi ma Haroun jiki a mace ya ce ma Malam zai shiga cikin gari ya dawo, yana so zai ga abokinsa Danlami Dandume.
Bayan fitar Haroun ya sa almajirai suka sassauke katon-katon na kayan abincin Dangote suka shiga da su cikin gida kamar yadda ya saba koyaushe zai zo da irin wannan hidimar ta kayan abinci da buhunnan shinkafa da jarkokin mai yake zuwa daga jihar Rivers.
Fitar Haroun daga sitting room din ke da wuya Malam ya tashi ya bi bayan Ammi dakinta, har yana hardewa da babbar rigarsa.
Nan ya tadda su, Ammi ta sa ta a gaba tana fama da ita da lallashi a kan ta ci abinci, kamar yadda ake saka yaro karami a gaba a ce sai ya ci abinci, amma Safiyyah ta ki. Kuka ta ke haikan kawai tana fadin.
“Ammi ki yi min alfarmar nan da na roka?”.
Ammi ta ce, “Har abada ba za a hada kai da ni a yi kisan kai ba, ko da kuwa shege ne balle da Ubansa… haife shi ni ki bani, ni ina so tunda ba kya so!”.
Malam daga bakin kofa jin abin da Ammi ke fadi ya kusa faduwa, ya kama marikin kofa yana fadin.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, ni’imal maula wa ni’iman naseer”.
Ammi ta ce, “Gara dai da ka zo Malam! Nana Safiyyah na neman rasa imaninta. So ta ke in barta ta zubar da cikin da Allah bai ga damar bata ba sai yanzu.
Wannan butulci ga Ubangiji har ina? To ba dai da ni Hafsatu za’a yi shi ba”.
Malam ya zauna sosai a kujera jikinsa yana kyarma da abinda yake ji. Ya na hamdala a zuciyarsa, ya ce,
“ita Nana Safiyyan ce ta ce miki tana so ta zubda ciki? Wace Safiyyar? Ba dai wannan tawan ba dai ko, wadda nake yi wa fatan samun rahmar ‘ya’yan da za su ji kanta su bi ta irin yadda ta ke jin kanmu ta ke binmu?
Kullum cikin dare sai na tashi na roki Allah ya baiwa Nana Safiyyahta ‘ya’ya masu albarka, wadanda za su yi mata fin abin da ta ke yi mana!”.
Zuciyar Safiyyah ta idasa karyewa, hawayenta yau ya kusa karewa, kukan da kansa neman gagararta yake yi, sai dai shessheka da ajiyar zuciya.
Malam ya ce, “Maza ki yi istigfari a kan wannan sabon kin ji Safiyyah! Ni na san ko da yardarmu in kina cikin hankalinki ba za ki aikata shi ba, to in hankali ya bata sanadin bacin rai, hankali ake sa wa ya nemo shi kin ji ko Nana Safiyyahta?
Maza nemi tsari daga shaidan la’ananne wanda kullum burinsa shi ne ya samu abokan tafiya wuta”.
Haka Malam ya zauna ya yi ta tausar diyarsa da wa’azi da nasiha mai shiga jiki da ratsa bargo, har ya samu ta yi masa alkawarin ta bar zancen zubar da cikin Zayyan.
Malam ya shi mata albarka yafi cikin kwando, ya kuma ce, tunda yana raye kuma da sauran karfinsa, zai kula da ita da abin da ke cikinta.
Zai yi musu komai daidai karfinsa ko ba da tallafin Zayyan ba.
Zasu tsaya su ga cewa rabuwa da Zayyan bai zama karshen farin cikinta ba.
(Hakika idan Allah ya barka da iyaye na kwarai a raye, har zuwa shekarun girmanka, Yayi maka babbar suttura da rufin asirin da babu mai iya ba ka sai Shi).
Daga wannan lokacin ba ta kara cewa sai ta zubar da ciki ba. Da ta ki cin abincin Ammi madarar shanu mai dumi ta sa aka je gonar Malam aka tatso mata.
Har zuwa washegari da Haroun zai koma Rivers bai ga Safiyyah ba, don sosai zazzabin ya sake rufe ta, ta sha magani bayan ta sha madarar sai barci.
Sai da ya fito zai tafi ne washegari da yamma Ammi ta kawo shi har kofar dakinta. Ya yi ma Safiyyah sannu da jiki, ba tareda ya shigo dakin ba, itama ta amsa ba tare da ta dago ta dube shi ba. Ya ce zai wuce Portharcourt, kanta a sadde ta ce a gaida iyali.
Ya tsugunna ya ajiye rafar kudi masu tudu a gabanta, ya wuce ba tare da ta lura ba, sai bayan tafiyarsa ne Ammi ta nuna mata.
** **
Su Ammi basu gayawa Yaya Shaikh batun Safiyyah ba, wanda yana wani gajeren course na watanni shidda a lokacin a birnin Arkansas.
Akai-akai Ammi ke raka Safiyya asibiti har zuwa lokacin da cikin ya isa awo, ta fara zuwa ante-natal clinic, daga shigar cikin watanni na hudu ta fara awo sosai.
A cikin zuciyarta Safiyyah tana kiran cikin nan ‘unwanted pregnancy’ wanda ya zo a sanda bata bukatarsa.
Don haka ma duk wasu magunguna da ake bata a sibiti don kula da rainon ciki irinsu folic acid da vitamin c bata shan ko daya. Fatan ta ma cikin ya zo (as stillbirth).
Malam da Ammi wataran suna hira, Ammi ta ce, “Malam, ina ganin ikon Allah Buwayi gagara misali, an sako Nana Safiyyah saboda rashin haihuwa, ashe dai kuma Allah na son Ya nuna ayarSa ne, tunda da cikinta ta fito.
An yanka ta tashi a gidan Haj. Fatu, duk da har yau ban san saki nawa ya yi mata ba. Yanzu ya ka ke ganin za’a yi?”
Malam ya ce, “Ya kuwa za’a yi? Banda a barwa Allah ikonsa da iyawarsa? Ai ba a ma Allah shisshigi. Nana Safiyyah ta yi rainon cikinta a gabanmu, har Allah ya sauke ta lafiya, sannan a san abin yi”.
Cikin na girma, kuncin da ke zuciyar Safiyyah a kan cikin shi ma yana karuwa, don duk abin da zai hada ta da zuri’ar Mama har yanzu Safiyyah ba ta sonshi, neman tsari ta ke da shi.
Amma ya za ta yi ban da zubawa sarautar Allah ido, cikin dan/ ‘yar Zayyan har ya fara kutufonta a cibinta cikin dare.
Haka za ta zuba wa kazarniyar cikin ido yana ta mutsu-mutsu da zulliya. Cikin da tuni ta yanke tsammani ta fidda rai da samunsa.
Tunda ta baro gidan Zayyan ba ta fito da wayoyinta ba, a can gidan ta baro su akan gadonta, don haka yau watanni hudu kenan da zuwanta gida kuma rabonta da communicating da kowa a waya, har kuwa da Aunty Assafe, ta kan ji su suna waya da Ammi da Rayha, bata taba cewa su bata su gaisa ba, suma basu taba yi mata zancen dawowar Safiyyah gida ba.
Haka Allah yake al’amarinSa, Safiyyah kan ce “ga bikin zuwa, amma babu zanin daurawa….”.
Wato ga cikin ta samu amma a lokacin da bata so ba.
Ga dai ciki na haihuwa a tare da ita, amma babu Zayyan din da zai tayata tattalinsa da rainonsa.
Ba wai kewar Zayyan ta ke ba, saboda yadda zuciyarta ta riga ta bushe a kansa, kawai tana zama tayi imagining in ya sani ko ya ya zai yi reacting?
In da suna tare ko wane irin tattali zai yi wa cikin nan?
Tsakanin Zayyan da Mama Fatu, bata san wanne ne cikinsu ya fi zaluntar rayuwarta ba. Shi da ya saketa ya maidata bazawara take rainon ciki a katifar uwarta, ko kuka Maman data saka shi aikata sakin sabida son zuciyarta???
Yau wata biyu kenan da yi wa Mama aiki, an cire kafarta ta hagu daga gwiwar kafa zuwa kasa. Mama ta yi jinya mai tsawo a asibitin koyarwa na Shika, Zaria.
Duk wata kulawa da kauna da Da zai yi wa uwarsa, Mama ta gani daga gun yaranta a wannan lokacin. Har zuwa yau sun kasa sabawa da ganin Mama da kafa guda daya. Duk sanda suka kalla sai hawaye ya balle wa kowaccensu.
Maman ita ta koma rarrashinsu, tana cewa su yi tawakkali su kuma gode Allah da ya dauke Baba Bello gabanin faruwar wannan iftila’in a gare ta.
A hankali Mama na samun sauki, ciwon yana warkewa kuma.
Abubuwa goma da ashirin ne kusan suka hadewa Baffan Mama, wadanda suka haifar masa da ‘shock’ na lokaci mai tsawo, ya zama tamkar mai fama da lalurar ‘emotional disorder’. Ranar da aka yanke kafar Mama daya, bai iya ya kwana a asibitin ba, domin zuciyarsa ta kusan bugawa. A dakin hotel ya kwana a tsaye shi kadai a ‘congo conference’.
Mama gabadaya ta zube, ta zabge ta koma rabi. Duk da haka lafiya na ci gaba da samuwa gare ta a hankali.
Sai da Mama ta kwashe watanni biyu da rabi a asibitin sannan aka ba su sallama.
‘Ya’yan Mama ke shawarar wa zai zauna da Mama a cikinsu tunda yanzu Mama sai da mataimaki a gefenta, tunda Mama yanzu sai ta hada da crutches wajen tafiya, ko a saya mata wheelchair.
Cikin duka zabin da likita ya bayar, Zayyan ya kasa zaben ko guda daya, har aka sallami Mama dukkansu suka ce ba su yarda Mama ta koma gidan Zayyan ba.
Sai Zahra ce ta karbi Mama ita da ba ta aikin gwamnati, don dukkansu sun tsaya a kan ba za su bar Mama ita kadai a gidanta Rafindadi ba.
Ita kanta Mama ba son komawa gidan Zahra take yi ba don dai babu yadda za ta yi ne da juyin rayuwa.
Mama bayan ta tabbata ta nakasa physically, sai ta koma yawan ibada daga zaune, tunda kullum tana zaune wuri daya ba inda take zuwa. Yaran Zahra guda biyu na wurinta kullum suna tayata hira don suna son ta sosai, haka maigidanta Ubaid shima kullum zai dawo sai ya shigo mata da wani abun na ci, amma duk da haka har gobe Mama so ta ke ta koma Rafindadi, ‘ya’yanta na tausarta da cewa ta bari ta kara jin karfin jikinta, ta warke sosai tukunna yadda zata iya kula da kanta a cikin gida da waje kafin su yarda su maidata gidanta.
** **
Duk yadda Azeezah ta kai da hakuri da yi wa Zayyan uzuri a zamansu na yanzu, yau ya kai ta makura. Duk wani hakuri da ta ke tunanin tana da shi ya zo karshe yau. In har za ta iya tunawa yau ana neman wata biyu da yi wa Mama aikin kafa, kuma rabonta da shi a shimfidar aurensu bazata iya tunawa ba. Ta yi hakuri ta yi hakuri har ya tuke hakurinta yau.
Wani abu guda daya da Azeezah Murtala take da tabbacinsa shi ne, za ta iya rayuwa babu Zayyan, amma ba za ta iya rayuwa babu sex ba, she loves him because shi kadai ne yake iya gamsar da zalamarta. To tun tafiyar Sophie daga rayuwarsu komai ya cakalkale ma kowa, kowa na jin consequences din a jikinsa, ba Zayyan kadai ba.
Wanda sai yanzu da babu Safiyyah a tare da shi ya kara tabbatar da maganganun Baba Bello cewa;
“Ita Safiyyah matar da za ta rufa masa asiri ce, kuma wadda za ta jure kowanne yanayi ta riske shi a ciki”.
Ya kara gane hakan ne daga yadda zamanshi da Azeezah ya koma yanzu.
Wato tunda ya rage walwala da ita da bata abinda ta ke so daga gare shi, ita ma ta canza gaba daya daga Azeezar da ya sani uwar soyayya da lobayya zuwa mara damuwa dashi da al’amarinsa.
Duk wani abu da ta ke yi masa in dai ba zai kwanta da ita a rana sau biyu ko uku ba, to ita ma saita daina yi masa. Abun nata ya koma ‘yimin in maka’. Sai kashe kudi na fitar hankali a shopping. Ko ya bata ko bai bata ba Azeezah zata bude ‘safe’ dinshi ta dauka bai sani ba. Sabida yanada dabi’ar ajiye kudi a ‘safe’ yasa code (pin) ya rufe, kuma tunda jimawa Azeezah ta dade da gane pin dinshi wato lambobin shekarun haihuwa Safiyyah sune ‘pin’ dinsa. Kullum tana satar kudin amma tana jin takaicin pin din kamar me.
Ta san ba ta da hujjar da za ta dinga karbar kudi irin wadanda take so a gun Baba Murtala shi kuma Zayyan komai nasa yanzu ya canza, ya daina yin komai with pleasure, kaman a dole yake yin komai nasa, not like before, da gidan ke cike da walwalarsa da nishadinsa ga matansa, sabida rashin nutsuwa da walwalar da ke tattare da shi yasa ko
kudi baya baiwa Azeezah irin da, ita kuma tana jin girman kan tayi ta rokonsa yana shareta, ya zama yanzu Zayyan ba ya enjoying komai tun tafiyar Safiyyah.
Ga dai Azeezah da yake dulmiyewa cikin sha’awarta, ga gayun nata ga seduction, ga enough stylish sex din da yake kwadayi kullum, ga haihuwa akufi-akufi ya samu (don Azeeza ciki na biyu gare ta yanzu ba tare da ita da kanta ta sani ba), amma duka ya kasa jin dadinsu ya kasa amfana daga ni’imomin su. Shaheed ne kadai ya ke saka shi murmushi, a duk sanda ya dane wuyansa in ya shigo gidan yana,
“Oyoyo Papa!”
Azeezah bayan Zayyan ya sallami su Janet, dole sai Masari ta aika aka kawo mata yara ‘yammata hausawa guda biyu, su kam ya barsu tunda suna sallah, kuma ya yarda a irin upbringing din da Azeezah ta taso a cikinsa ba za ta iya daukan responsibilities na ayyukan gida da raino ba, dole ya kyale ta da su Azumi da Asbi da ta dauko.
To ba a jima da zuwansu ba ma ta ce, Asbi ta cika yi ma Zayyan kallon kurillah, don haka ta kore ta, saura Azumi. Shiyasa Azumi ta shiga taitayinta ta kuma iya takunta akan mijin uwar dakinta, in Zayyan ya shigo gida ba ta kara giftawa ta gaban Azeezah sai washegari da safe in ya fita aiki.
Mayatar Azeezah a kan gadon aurensu da yawan sex da ta ke saka shi kullum, ga damuwa ya sa kullum Zayyan kara ramewa yake yi. Shi da kansa yanzu ya san Azeezah nympho ce, ba irin halittarsu daya ba, shi ba khariji bane ba kuma dakhili ba, yana tsakiya dai. Tunda yayi na marmari da na doki ya gama satisfying abinda zuciyarsa ke kawata masa, duk ya gaji yanzu. Ko kuma fitar Sophie daga rayuwarsa ne ya sa komai ma ya fita daga zuciyarsa oho?
Fitowarsa daga wanka kenan a daren yau, dawowarsa gidan kenan daga Kaduna gidan Zahra inda ya je duba Mama, yau ya sayi crutches da hannunsa ya kai wa Mama, wanda zai taimaka mata ta dinga tafiya da kanta. Kafin ya san abinda ya kamata ayi akan kafarta.
Yana cikin damuwar irin rabuwar da suka yi da Zubaina a waya dazu don Zubaina har lokacin fushi ta ke da shi mai tsanani.



