Chapter 7: Chapter 7
Don haka Zubaina ta je bakin kofar dakin Ammi, tana rokon Safiyya ta bude kofa su fahimci juna, amma Safiyyah ta ki, don ko ganin fuskar Mama Safiyyah ba ta son sake yi a rayuwarta.
Ammi ta ce da Zubaina “da dai kin kyale ta zuwa wani lokacin, in ta nutsu, amma ban da yanzu”.
Don haka Mama da ‘ya’yanta haka suka baro Dandume wutsiya a zage, ba tare da tabbacin samun yafiyar Safiyyah ba. Amma dai iyayenta sun nuna dattaku irin nasu na koyaushe.
Bayan tafiyar jama’ar Rafindadi da kamar awa daya, sannan Ammi ta kammala girkinta, ta zuboma Safiyyah nata, dashishin alkama ne tayi da miyar taushe da taji tantakwashi, ta samu ta lallashi Safiyyah ta bude kofar dakin.
Ammi ta shiga dakin ta zauna daga gefen gadonta, tana kallon Safiyyah wadda da alama ta ci kuka ta koshi. Ammi tace “to kukan kuma na menene? Ai sun jima da tafiya”.
Safiyyah tace “Ammi ni tunda dai wannan cikin ne yasa Mama da ahalinta sake waiwayar inda nake da sunan sulhu, to ni Ammi gara in haifi dan babu rai, da dai ya zame min silar sake kulla alaka tsakanina da Mama da ahalinta”.
Ammi ta ce, “subhanallah! Nana Safiyyah meke damunki ne haka? Ki yi maza ki yi istigfari akan kalamannan, ina hana ki yin mummunan fata kowanne iri a kan cikin nan, ba tun yau ba.
Allah na son ki da rahma yana kuma sonki da zama uwa kamar kowa, shi yasa ya amsa addu’armu ya baki. Don haka ki ajiye batun Hajiya Fatu da iyalinta a gefe ki yi fatan Allah ya sauke ki lafiya, Ya kuma bamu mai albarka, walau mace walau namiji”.
Amma ina! Duk wadannan nasihohin da Ammi ke faman yi kullum, a gefe Malam ma yana nasa kullum, amma Safiyyah ta kasa son cikinta idan ta tuna jikan Mama Fatu ne, bata wani farin cikin haife dan Zayyan yanzu.
** **
A wannan satin Azeezah take son shirya 25th birthday dinta, duk yadda ta yi kokarin Zayyan ya bata kudi isassu gogan nata ya ki, shirin tafiya Saudiyyah Umrah yake yi, data takura masa da rokon kudi yace, shi fa a saninsa birthday ba fadar Allah ko na Annabi bane, saboda haka shi baya ciki. Bai taba yi ba, wani cikin ahalinsa ko iyalinsa bai taba yi ba.
Zayyan ya kammala duk shirinsa na tashi zuwa Umrah a yau, jirginsu zai tashi karfe takwas na dare daga Nnmadi Azikiwe, Abuja.
Tun karfe shidda ya fita zuwa filin jirgi, fitarsa ba jimawa Azeezah ta yanke shawarar abinda zai fishssheta. Don ta tambayi Baba Murtala shima ya ce ina mijinta? Ko me ta ke so mijinta ne a hakku da yayi mata yanzu ba shi ba. Shi kuma Baba Murtala baya son sakarwa Azeezah kudi ne kamar sanda take gabansa sabida kada Zayyan yaga ko ya raina kulawarsa gareta, ko an raina arzikinsa.
Azeezah in ta sakawa ranta tana son yin abu ruwa ko iska ko iyayenta ba wanda ya isa ya hanata.
Ta riga ta saka ma ranta son yin (Grand Pool Party) na murnar cikarta shekaru ashirin da biyar da haihuwa. Ta dade da sanin cewa Zayyan kan ajiye kudade a gida a cikin safe dinsa da password din shekarun haihuwar Sophie, don bukatu na cikin gida da na yau da gobe da ba sai yaje banki ko ATM cire kudi ba.
Ba tun yau ba Azeezah ta san inda kudaden suke cikin safe dinsa, kawai zuciyarta ta raya mata ta kwashe su, in yaso kome zai yi yayi, ai ta tambaya ya hanata, bayan kuma duk abinda ya kama na bukatun gidan ya bar mata. Ba ta ga abin da zai hana ta yin birthday din nan ba ko kome za’ayi.
Ai kuwa tana saka pin din safe din ya bude, ta samu har abinda bata yi tsammani ba domin tsabar kudin Amurka ta gani a shirye wrapper-wrapper na US Dollars.
Ko da Zayyan yake ajiye kudinsa a gida (local currency) yake ajiyewa a kadai a gida, wadannan yayi canjinsu ne don biyan kudin asibitin Mama sunyi magana da Habibu Nahuce da taimakon matarsa Dr. Rahinah Nahuce akan zai fidda Mama Germany dasu ayi mata kafar roba, tun lokacin da wayar Zubaina ta same shi akan cikin Safiyyah, bai kara tunawa da zancensu ba sai ya watsa su a safe kawai ya rufe da zummar sai ya samu nutsuwa sannan a cigaba da zancen asibuitin Mama.
Zuciyar Azeezah ta shiga gaya mata ta kwashe su duka gabadaya, ai ko a ina Zayyan ya samesu ubanta ne silar samo masa su, ita bata son kankamo, kuma bata son rayuwar matsi, a gidansu ba’a mata iyaka da duk abinda take so, to why a gidan aure???
Zayyan yana can yana ibada a Raudha a kasar Saudiyyah, yana mai godewa Allah bisa kyautar da yayi musu shida Sophie, a lokacin da suka riga suka fidda rai, cikin kuka da hawayensa na godiya ga Ubangiji, Azeezah da kawayenta na rakashewa a gidansa da facaka da makudan kudadensa da shi kadai ya san adadinsu.
Satinsa biyu a Saudi yayi shirin dawowa, kada kaso kaga wata uwar tsaraba da Zayyan ya narkoma Safiyyah, duk da bashi da tabbacin ma yadda zaiyi ya ganta balle ya bata, da babyn da bai ko zo duniya ba akwati-akwati haka ya ciko musu, abun sai ya baka tsoro kayi tsammanin ko ya karar da dukiyarsa ne.
Abayoyi ne masu karshen tsada har dozen daya, da bangles masu kauri na zinare guda uku.
Duk wata addu’a da Zayyan yayi a Maqama Ibraheem akan Sophie ce, yana rokon Allah ya sa akwai sauran zama tsakaninsa da Sophie. Ya san sauran rayuwarsa bazata kara bada ma’ana ba, ba tareda Sophie ba.
Ya kuma roki Allah akan ya bashi rinjaye akan iyayenta, da karfin zuciyar iya tunkararsu ita da iyayenta da zarar ya koma gida Katsina.
Safiyyah da Zayyan basu da contact da juna kwata-kwata, tun fitowar Safiyyah daga Sunset Estate rabonta da sake rike waya, amma yanzu da ya kammala Umrah, ya kamo hanyar dawowa jin kansa yake cikin wani irin confidence da matsanancin karfin gwiwa, sannan da wani sabon dokin ganinta, yaji zuciyarsa tayi dakewar da har yake jin zai iya tunkarar Safiyyah yanzu.
Engnr. Haroun, yana kwance rigingine a gadon dakinsa yana tuna maganarsu a waya ta daren jiya shi da Amminsa. Yace.
“Ammi na so in same ki fuska da fuska, amma wallahi nauyinki da kunyarki sunsa na kasa. Ban sani ba ko don ban taba yin zance makamancin irin wannan da ke akan Safiyyah a lokacin da ya dace ba?”.
Ammi ta ce, “Haroun, to in baka yi kowanne irin zance da ni ba, da wa zaka yi? Ni fa na raine ka Haroun, jinin haihuwa ne kawai ban diga maka ba. Ka zama a sake, ka gaya min ko mene ne akan Nana Safiyyah din”.
Haroun yayi ajiyar zuciya cikin kankanuwar murya da jin nauyin Amminsu yau, ya ce.
“Ammi wallahi tun ban san kaina ba, tun ban san matsayina a gunku ba nake jin raina na matukar son kanwata (Safiyyah). To amma Ammi na yi kwauron baki, ko ince ina tunanin matsayina bai kai na in auri diya mafi soyuwa ga Malam ba, a matsayina na almajirinsa tun a wancan lokacin.
Har gobe kuma ina kan wannan matsayin, na kasancewa almajiri a gare ku, wanda ya koyi karatun sallah daga bakinku.
Na sha fama da kaina na shiga wani yanayi da bazai misaltu ba Ammi, bayan na samu labarin kun bayar da auren Safiyyah ba zato, ga wanda yayi dacen auren ta. Na dade ban koma daidai ba daga dukan da auren Safiyyah yayi min.
To amma Ammi bayan ji daga bakinki da na yi cewa auren Safiyyah ya mutu, wallahi Ammi tun daga ranar na kasa sukuni. Matata Ambashayr ta kasa gane kaina tun lokacin, har sai da ta kai ga na gaya mata gaskiyar halin da nake ciki.
Wallahi Ammi Ambashyr da kanta tace in gaya miki, idanma shakkar tunkarar Safiyyah da zancen nake ji.
Ammi ni da Ambashyr muna da fahimtar juna, domin tun aurenmu na sama da shekaru goma Ammi ke shaida ce akan irin zaman da muke yi nida ita.
Ammi Safiyyah ba ta taba kallona da wata fuska daban koda zuciyar soyayya ba, banda irin kallon da take yi ma sauran wadanda Malam ya kawo ya ajiye a gabansa, tun kafin a haife ta.
Da wannan, nake rokon arzikinku Ammi, na san ban isa ba, amma ayimin alfarma, idan Safiyyah ta amince, ko zan samu alfarmar auren Safiyyah a wannan karon, wadda ko a mafarki ban taba zaton wannan damar zata zo min ba?”.
Ammi ji ta yi hawayen tausayi na son tsinke mata. Haroun komai nasa mai sanyi da sanyaya rai. Hatta maganar Haroun sanyi gareta. Ko daga yadda yake maganar wato yadda haruffan ke fita daga bakinsa cikin salama, mutum ne shi mai sanyin hali kwarai ba tun yau ba.
Ita ta san Haroun farin sani, ko tace tafi kowa saninsa, da wuya ka ji cikinsa, mutum ne mai zurfin ciki na gani kasheni. Tunda har yau ya furta abinda ita ta dade da sani to abun ya kai makura ne ya kasa cigaba da dannewa. Domin ko babu komai Haroun yana da matsayin Da a wurinta,
ita ta raine shi, kuma ta fi kowa sanin nagartaccen halinsa, sannan da Safiyyah ta komawa Zayyan a wurin Ammi sau dubu gara mata auren Haroun.
Don haka sai Ammi ta yi murmushi ta ce,
“Na ji batunka Haroun, kuma ni dama na san dashi a ranka ko baka furta ba.
Hakika bawa bai hada sani da Allah ba, amma tun farko ni da kaina na gaya wa Malam da kai ya aura ma Nana Safiyyah da hankalina yafi kwanciya.
Bazan manta amsar da Malam ya bani a lokacin ba, cewa baka furta masa ba, kuma in ka auri Safiyya itace zata koma mijin kai ka koma matar don da fuskarsa shi mahaifinta zaka dinga kallonta. Kuma da yake ance matar mutum kabarinsa Allah ya rubuta aure tsakaninta da Zayyan.
Hakika mijin Safiyyah mutumin kirki ne, ban taba nadamar aurenta dashi ba, ko hada zuri’a dashi, don ko bayan kara aurensa yana kwatanta mata adalci. Nana Safiyyah ta gaya min koda wasa koda subutar baki bai taba yi mata gorin haihuwa ba! Sai ko sauran ajizanci irin na dan adam.
Kawai dai bai yi sa’ar uwa da ‘yan uwa mata ba. Dukkansu mutane ne masu son zuciya da bin KAWARta.
Sannan a halin yanzu ita Safiyyah da ciki ta fito daga gidanta, wanda mu duka ba mu san dashi ba sai daga baya, don haka babu wata magana a yanzu, har sai Allah ya sauke ta lafiya, wato a sannan ta gama iddarta”.
Da wannan suka kawo karshen maganarsu shi da Ammi. Yana fatan Allah ya sauki Safiyyah lafiya, yana fatan rikema Sophie danta ko ‘yarta tare da nashi ‘ya’yan, yana fatan baiwa Safiyyah dama ta raini dan ta da kanta a gidansa in har Allah ya qaddara masa samun aurenta, aurensa da ita ba zai taba rabata da abinda ta haifa ba.
Yana fatan bai ma Sophie soyayya, da farin cikin da shi kansa bai taba baiwa kansa ba. Yana musu fatan karasa rayuwa tare, don ya san Ambashyr za ta taimaka masa a kan wannan kudirin nasa, duk da bashi da burin hada su gari daya ma balle gida daya, shi kadai yake ta wannan sake-saken, kamar ma an ce gashi an ba shi auren Safiyyah da zarar ta haihu zata tare.
A wannan halin Ambashyr ta riske shi sai murmushi yake rungume da waya, hannunta ta kai ta wulga a gaban idonsa ganin yayi nisa cikin imaginations, ta ce.
“Someone is in love! Dadina da su Hubby ba’a iya kankanuwar soyayya ba sai zazzafa.
Allah dai ya kai damo ga harawa”.
Engr. Haroun yayi mata wani kallo, sannan ya yunkura ya tashi zaune, bai ce komi ba dai sai murmushin yake mata, Ambashyr tace “su Tasnim sun gama shiryawa kai kawai suke jira ka sauke su school”.
Engr. Haroun ya mika hannu ya janyo ta jikinsa ya ce, “Ambashyr, ki min addu’a kin ji? Na yi magana da Ammi a kan Safiyyah jiya da daddare”.
Ambashyr ta hadiye wani miyau da kyar, tace, “Hubby, ai addu’ata gareka akan Safiyyah ka sani kullum ce, ina yi mana kan cewa idan Safiyyah alkhairi ce a garemu Allah ya kawo ta gidan nan cikin ikonsa. Idan babu alkhairi Allah ya mantar da kai zancenta”.
Engr. Haroun Dalhatu Babagana kenan. Haroun baki ne irin kalar mutanen Yobe. Amma hakika kyakkyawa ne shi na gaske mai dogon hanci, kuma mai suffar da kowacce mace zata yiwa kanta fatan samunsa.
A satin ya shirya zai shiga Katsina haka ya jibgi provision na abubuwan ci dana sha, masu karama mai ciki lafiya da kuzari, komai katon na garari ya wuce da su zuwa Dandume.
Haroun bai jima da isowa gidansu Safiyyah ba al’amarin ya faru.
Yana zaune falon Malam yana cin abincin rana suna hira shida Malam, hirar tasu a kan transfer na aiki da aka yi masa zuwa jihar Benue, Malam yace yanzu haka zaka kwashi kananan yarannan ku koma kasar Inyamurannan da aka ce cin mutane suke yi?”
Dariya Haroun yayi, ya ce ma Malam.
“Ai Malam ba zan tafi Benue da su Ambashyr ba, na gama ginin gidana na Yobe, zan dawo dasu Yobe, saboda karatun su Tasnim inason ya dawo Arewa, yaran ko hausa basa ji yanzu….ga inyamuranci a bakinsu kamar me”.
Sai jin dirin wata sullubebiyar mota mai numfashi suka yi ta faka a kofar gidan Malam, rurin motar kadai ya sha bambam dana sauran motocin dake wucewa, horn din motar wani irin ‘cool’ babu hargagi.
A lokacin almajiran Malam sun fara isowa don daukar karatun yamma.
Don haka Haroun ya ce ma Malam zai shiga daga ciki su gaisa da Ammi, daganan ya fito ya wuce masaukinsa don sai gobe zai wuce gaida Baffansa a Geidam.
A lokacin Arch. Zayyan Bello ya fito da jikinsa gabadayansa, daga santaleliyar motarsa kirar G-Wagon baka wuluk, sai numfashi take tana sheki, yana sanye da farin yadin nan nashi na koyaushe, watau tsadadden farin filtex da aka yiwa dinkin Kaftan mai aji matuka. Kamshin sassanyar turarensa ya surnano hancin jama’ar da suka cika soron Malam, duk suka bi shi da kallo saboda kwarjinin sa abun a daga ido a dubeshi ne, suna amsa sallamarsa cikin karramawa da girmamawa. Haka ya shiga basu hannu daya bayan daya suna gaisawa cikin girmamawa, a yau ba kamshin Ultraviolet kadai ke tashi jikin dan Rafindadi ba har dana turaren Baccarat Rouge (Francis Kurkdjian) da ya sawo a Saudiyyah musamman don wannan ranar da zai zo bikon Sophie.
Yana sako kai kofar shiga falon Malam Haroun na kokarin fitowa don shiga cikin gida sai da suka dan gogi kafadar juna.
A lokaci guda suka daga ido suka dubi juna. Kowannensu sai da zuciyarsa ta doka, ta sake dokawa da ganin dan uwansa yau, ko me yasa? Haroun ya san Zayyan a fuska ba tun yau ba, tunda ya taba taka har gidansa ya raka Malam har dakin Safiyyah, shi ma kuma Zayyan ya san Haroun a bakin Sophie, a matsayin Almajirin cikin gida ga Malam, amma wanda Ammi ke matukar so, ta gaya masa almajirci aka kawoshi ga Malam wanda suka dauka a gabansu tun yana karami kamar su suka haifa, sanda aka kawo shi hanci duk majina baki duk busashshen koko tace amma kuma ya kasance yanada sa’a a rayuwarsa, ta taba gaya masa yayi karatu har matsayin degree na biyu a gabansu Malam, wadanda suka kula da rayuwarsa da ilminsa har ya girma bai san iyayensa ba.
Bai san me ya sa ganin Haroun yau ya tayar da hankalinsa ba, shi ma Haroun ganin Zayyan ba karamin faduwar gaba ya haifar masa ba. Ba ance sun rabu ba? Haroun ya samu kansa da tambayar kansa me Zayyan kuma ya zo yi yau? Shima Zayyan ya tambayi kansa Me Haroun ya zo yi? Bayan yanada masaniyar cewa dan gida ne amma shi a wurinsa Haroun bare ne.
Amma da yake maza ne na gaske dukkansu sai kowanne ya waske. Haroun shi ya fara baiwa Zayyan hannu, yayi kamar bazai karba ba sai suka hada ido da Malam, sannan Zayyan yaji kunya ya mika masa nasa nasa hannun, Malam na kallonsu suka gaisa a gajarce, Haroun ya wuce cikin gidan yadda yayi niyya.
Zayyan ji ya yi kamar ya bi shi cikin gidan ya finciko shi, tunda dai ai shi ba jinin gidan bane kuma yanzu ya girma ya zama babban magidanci, ta yaya zai shiga gidan Malam haka kai tsaye, alhalin akwai matan mutane a cikin gidan.
“Matan mutane?” Wani dan sako daga can kasan zuciyarsa ya kalubalanta, har yace da shi ai yanzu baka da right akan wannan, Sophie allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka, baka da hujjar cewa matar ka ce, duk da tana cikin zimmar aurenka, besides, Haroun dan gidan ne da wane dalili zaiji haushin shigar mutum gidansu?
Kuma abinda ya kara kular dashi Malam yana kallon shigar Haroun cikin gidan amma sai cewa yayi dashi “in ka shiga kace da Ammin taku a miko mun fura mai sanyi ko farau-farau”. Tsabar a nuna masa Haroun na gida ne.
Zuwan Arch. Zayyan na farko gaban Malam Usman kenan tun bayan rabuwarsa da diyarsa Nana Safiyyah…
Don haka ba karamin nauyi Zayyan ke ji a ransa da zuciyarsa ba, lokacin da suka hada ido da Alaramma Usman.
Malam ya amsa daga zaune, fuska ba yabo ba fallasa. Ya daga kai yana kallon Zayyan yana shigowa cikin nutsuwarsa ta halitta, Zayyan ya tsugunna gaban Malam yana mika gaisuwa, Malam ya saki fuskarsa suka gaisa kamar yadda suka saba, bai nuna ma Zayyan komai ba, musamman daya ga Zayyan ya yi haske, amma ya rame sosai.
Wani kwayan mutum guda daya da ya tabbatar Safiyyah ta so a duniyarta da rayuwarta, ko har yanzun tana son abinta ma wa ya sani? Ta yaya zai daina kaunar yaronnan?
Mutum ne mai yawan alkhairi da matukar kyautatawa ga surukansa, dama al’ummar dake zagaye dashi gabadaya.
Bayan gaisawarsu Zayyan sai ya koma gefe yayi shiru, don ya rasa ta ina zai fara, wai ido da kunya ya ce da Malam sai yanzu Mama taga dama ta sako shi ya zo. Ai ko bai zo don Safiyyah ba ya cancanci su ya zo gaishesu. Ba sai yanzu daya tabbata Safiyyah nada cikinsa ba.
Kunyar duniya ya ma rasa ina zaisa kansa a gaban Malam. Sai mutsu-mutsu Zayyan yake. Da kyar ya iya buda baki, halshe na rawa yace.
“Malam!!!



