Chapter 11: Chapter 11
Bata tsaya jin amsarta ba ta bace a wurin don bata saba karya ba, in ta tsaya suka yi ido hudu da Sophie tsaf zata gano karya take yi.
Safiyyah bata san da zuwan Zayyan gidan ba. Don haka ta ja sabon gyalenta ruwan goro mahadin kayan jikinta ta yafa a saman kafadunta, ta fita don amsa kiran Malam, don ita bata ma san sanda yazo aka kai masa Aayah ba, sanda aka zo aka fita da Aayah wurinsa tana bayan gida tana wankan jego.
Safiyyah da zuciyarta daya ta yi sallama a falon Mahaifinta, dakin da suka sha yin hirar saurayi da budurwa itada Zayyan, daki mai tsohon tarihi a rayuwar soyayyarsu, a dakinnan Zayyan ya fara kama hannunta ya saka ta cikin jikinsa karo na farko da zamowarta matarsa, kasancewar Zayyan daga kujerar kusa da kofa yake zaune bata ankara da mutum a dakin ba, har sai bayan data shigo har cikin tsakiyar dakin sosai. Jikinta ya bata akwai mutum, jin saukar numfashinsa.
Da sauri Safiyyah ta juya bayanta.
Arch. Zayyan Bello Rafindadi ke zaune a daya daga cikin kujerun falon, kansa sunkuye a kan kyakkyawar fuskar diyarsa da baya gajiya da kallo. Jin shigowarta da sallamarta baisa ya dago daga sunkuyon ba, duk da ya ga shigowarta ta kasan idanunsa. Yana sanye da wani farin lallausan yadin voile, kamar koyaushe dinkinsa bai cika ado ba, amma dinki ne na ‘class’ wato mai aji na karshe na kasaitattun maza, wanda tsadadden ‘links’ din dake hannun rigar mai ruwan zaiba, da maballayen silver na wuyan rigar kadai sun fiddo darajar suturar dana dinkin jikinsa bakidaya.
Daga zaune ya dago kansa a hankali, ya daidaita idanunsa a kanta yake kallonta da wani irin ‘mixed feelings and inexpressible emotions’ cikin idanunsa.
Aayah na kwance kan kafafuwansa, tanata mutsu-mutsu irin na lafiyayyun jarirai. Safiyyah bata lura da cewa babu Malam a dakin ba, kuma bata ankara da bako a zaune daga kujerar hanyar fita ba, har sai bayan data juyo.
Safiyyah na juyowa tayi arba da dan Bello Rafindadi, kawai sai ta kama taku zata fice daga dakin, Zayyan na mikewa tsaye, bayan ya kwantar da Aayah a cikin kujerar da ya tashi, da azama ya tare mata hanya, wato ya sha gabanta.
Babu ko shakkah Zayyan dinta ne yau a gabanta, her co-architect, her alter ego, wanda cikin kowanne hali kamanninsa ba sa canza mata, kuma a duk lokacin data ganshi ko ta ji muryarsa sai zuciyarta ta doka, ta sake dokawa, idan ta tuno shi zai zuciyarta ta motsu, ruhinta ya motsa. Rabonta da jin hakan kuma watanni kusan takwas kenan, wato tun barowarta gidansa dake Sunset Estate, data tattara komai daya shafeshi dashi kansa ta saka a tsohon kundi ta rufe, ta ture shi can karshen zuciyarta.
Ganinsa a yanzu a dakin mahaifinta ya tuna mata abubuwa da dama, daga ciki ya tuna mata wanna Zayyan ne, kuma they are still apart, Zayyan din da ya yi shattering zuciyarta daga yarda da soyayya da duk abin da ya shafi Da namiji.
Lokacin da suka hada ido, Sophie da Zayyan, bayan gushewar watanni takwas basu ga juna ba, komai na ranar rabuwarsu dawowa Safiyyah ya yi, shima komai na ranar ne ya dawo masa tamkar scenario, nan da nan zuciya tazo wa Safiyyah iya wuya, tunda har Zayyan ya iya ya sake ta, to babu sauran alaqa tsakaninta dashi, banda wannan alaqaqan haihuwar da Allah ya rubuta mata, daga kansa ta rufe yarda da soyayyahr maza kowacce iri ce, ba tasa soyayyar kadai ba, a’a ta kowanne DA namiji.
Sai kawai ta zagaye shi zata bar dakin, Zayyan yayi maza ya sake shan gabanta, suka tsaya a gaban juna cirko-cirko, kirjin Zayyan na hawa da sauka, na Safiyyah kamar ana luguden sakwara sabida irin zabalbalar da yake yi da bacin rai. A wannan lokacin Arch. Zayyan ji yake kamar ya kama Safiyyah ta karfi ya rike cikin kirjinsa, taji irin bugun da zuciyarsa ke yi da nadama, ya tuna babu wannan damar yanzu, wato ta kama Safiyyah ya saka a jikinsa, a halin yanzu ma babu iddarsa a kanta, tunda ta haihu.
Kamar yayi ihu ya dubeta cikin rikicewa da rawar murya ya mika hannu kamar zai rike nata yayi maza ya fasa, yace, “Sophie, Sophie kece? Ko dai mafarki nake yi irin wanda na saba tun bayan tafiyarki? Sophie ashe zan sake ganin ki a duniya?
Inata addu’a a kan Allah ya ara min dama irin wannan, ko yaya take, kafin ya dau raina da tarin hakkokinki, ba kuma don komai ba sai domin in yi amfani da damar ganinki ido da ido in baki hakuri, I know I hurt you, and I can never reverse the beautiful moment we spent together… bazan iya dawo da bara bana ba, ba zan iya maida hannun agogo baya ba, balle in gyara barnar da nayi saboda abinda zuciyata ta kawata min, amma ina amfani da damar yau ina baki hakuri Safiyyah! Safiyyah Allah ya baki hakuri, Ya huci zuciyarki”.
Safiyyah dai ba ta ce komai ba, babu alamun kuma kalamansa ko daya sun huda zuciyarta, don dai ya tare mata hanya ne, cikin shaking din da muryarsa ke yi ya ci gaba da cewa.
“Once again, ina yi mana barka da samun Ayatullah, ki bar ni in yi miki barka ko yaya yau Safiyyah da samun Aayah. Ko malam bai ce ba, na yarda da sunan da ya saka mata.
Safiyyah in na ce ina baki hakuri ya yi kadan, ko da yawun bakina zai kare waje cewa ki yi hakuri, ban gama baki hakuri ba”.
Ya mika hannu ya kamo nata ya dora a saitin kirjinsa. Baka jin komai a saitin zuciyarsa sai dukan sakwarar da zuciyar ke yi. Da hanzari Safiyyah ta janye hannunta daga kan kirjinsa data tuna waye ne Zayyan yanzu a gare ta, ta yi azamar janye hannunta daga kirjinsa tana harararsa, ta bi gefensa za ta wuce, Zayyan ya sakalo hannunta cikin nasa. Kamar ace ya sarko yatsunsa tsakiyar nata. Cikin karkarwar jiki da ta murya ya ce.
“Allah ya raya mana Aayah!”.
Sai wannan lokacin Sophie ta daure ta ce,
“Ameen!”.
Ta zare hannunta a hankali, tana kokarin ratse shi ta wuce bayan ta zare hannunta daga nasa sai kawai Zayyan ya kasa daurewa, yayi maza ya yi hugging Safiyyah, a very tight hug, tayi – tayi ta kasa kwatar kanta sabida rungumar Zayyan ya yi mata kamar har abada ba zai sake ta ba. Safiyyah is more than bewildered, da abinda ke faruwa dasu, ta soma mutsu-mutsu na son kwace kanta, sai kawai zayyan ya nemo bakinta ya huce zabalbalar da zuciyarsa ke yi na rashin Sophie for quite a long tima da wani zazzafar kisss! Tun daga bakinta har kasan wuyanta sumbata yake abruptly. Hakan yasa Safiyyah hawaye na wannan haddi da Zayyan ke keta mata, domin karfi sosai ya riketa a cikin jikinsa, duk da hawayenta dake sauka da gunjin kukanta amma Zayyan ya ki sakinta ya like a jikinta tamkar da glue aka like shi, tamkar kaska ta manne a fatar dan adam.
A haka Malam ya sako kai falon zai dauki littafi da sauri ya koma da baya yana a’uziyyah. Safiyyah ji ta ke tamkar Zayyan ya lika mata wuta da haduwar fatar jikinsu. Allah ya taimaketa Aayah ta motsa ta soma kuka, abinda bazai iya jura ba wato jin kukan Aaayah, dole ya shika Safiyyah ta samu ya sassauta rikon da yayi mata ya koma kan baby, ai yana sakinta da gudu ta barsu a dakin ta fice, tana kissima yadda za ta ci uban Sabah yau la’ada ciki da waje da yaudarar da ta yi mata.
Sabah kuwa da ta hango tahowarta tuni ta bi ta kofar kitchen ta fice zuwa soro. Ta bille ta kofar soro ta fice dakin Malam. Ita ta karbo Aayah a hannunshi. Ya dinga yima Sabah godiya kamar zai goyeta, duk abinda ke aljihunshi ya tattaro ya baima Sabah amma taki karba. Tana dariya tana tsokanarsa tana cewa “haba Baban Aayah nida kai ai akwai amana, barni inga kwanciyar hankalinka”.
Safiyyah na shiga gida ta fashe da kuka tana ce ma Ammi sai ta karairaya Sabah yau.
Ammi ta ce, “Me ta yi miki? In aka kyale ki sai ki daki mace da tsohon ciki haka?”
Ta ce, “Ammi, Sabah munafuka ce, ta yaudare ni!”.
Kuma ta kasa fadar yaudarar data ke ikirarin Sabah din ta yi mata, har Sabah ta shigo dakin dauke da Aayah tana dariya Safiyyah tayi kanta. Sabah ta gudu bayan Ammi tana cewa “Ammi boyeni zata dake ni”. Ammi ta ce “mai dukar min Sabah kuwa sai ruwan sama, shima sai in ban ga sanda hadarinsa ya taso ba”. Kowa adakin yayi dariya. Nan Sabah ta ke gaya musu Zayyan ne ya zo yi mata barka. Me ye laifi a cikin yin barka???
Washegari aka yi radin suna, Safiyyah ta hana a tara mata mutane, amma sai da makwabtansu duka suka shigowa Ammi barka, su isu iya family dinsu suka yi yinin sunansu mai armashi da kayatarwa.
Da yamma, can misalin karfe biyar na yamma sai ga ‘yan Rafindadi kwansu da kwarkwatarsu, sun zo da kabakin abinci a manyan kuloli na alfarma. Ba abinda basu dafo sun kawo ba na nau’in abincin suna na al’ada, pepper chicken kawai manyan kuloli uku suka ciko da ita, sinasir, waina, alkubus da farfesun kan Sa, farfesun kayan ciki da soyayyayyen rago guda. Su Anti Dije da Anti Assafe da Ammi kanta kallon ikon Allah suke, don sun kawo sakon ‘bangles’ din Aayah na farin ‘gold’ guda shida, suka ce sako ne in ji Mama, a sakawa Aayah a hannunta, Zubaina ta dauki Aayah ta zura mata bangles din da kanta, ‘yan sirara dasu. Ba karamin kyau suka yi a hannun yarinyar ba musamman da yake bulbul take masha Allah.
Mama ba ta iya ta zo suna ba, amma duk abin da ake bukata na abinci da abin sha ta sa ‘ya’yanta sun yi sun kawo.
Kwanan Safiyyah takwas da haihuwa wato a washegarin suna Assafe ta hada mata dalleliyar wayarta da Yaya Sheikh ya aiko mata da ita, ta yi mata ‘welcome back’ na tsohon layinta sannan ta yi sallama dasu ta wuce Lagos.
Anti Dije ma a washegarin tafiyar Assafe itama ta koma Zaria.
Su Sabah ma duk rana daya mazansu suka zo suka wuce da su gidajensu.
Gidan ya saura daga Ammi sai Sophie da Rayha, sai baby Ayatullah. Ammi ta cigaba da kula da Aayah Sophie sai shan nono ne tsakanisu. Daga wannan lokacin Zayyan ya balle musu da zuwa ganin Aayah kusan duk bayan kwana biyu, kamar bashi da wani aiki a gabansa sai kallon Aayah. Malam abun har ya soma damunshi don Safiyyah ba bari take ya ganta ba ma, iyaka dai a kai masa Aayah din.
Malam ma yayiwa Ammi gargadin kada Safiyyah ta kara fita inda Zayyan yake don shikadai yaga abinda ya gani, kada a maida shi dattijon banza.
Malam ya taka masa burki da cewa, ya dinga bari sai bayan sati bibbiyu tunda tafiyar mota yake yi zuwa Dandume, akwai tsoro sosai a bin hanyar Katsina a wannan lokacin.
Tun daga waccan nasihar da Malam ya yi mata Safiyyah ta yi wa kanta fada ta ci gaba da shayar da Baby Aayah. Amma ba ruwanta da hidimarta.
A hankali kuma kaunar yarinyar ta soma huda ranta sabida hakurinta, ko koke-koken dare irin na jarirai bata cika yi ba, saidai tayi ta tsotson hannunta, sai dai har lokacin ba ta yarda ta yi eye-contact da Aayah, saboda idanunta ma sak irin na Mama Fatu ne, irin na Rumawa.
Yaya Sheikh bai zo Dandume ba sai ranar da Safiyyah ta yi kwana arba’in da haihuwa. Ko a jiyan ranar kuma Zayyan ya zo ya ga Aayah, kamar koyaushe, bai ga Safiyyah ba.
Malam suna cin abinci shi da Yaya Sheikh a ranar da ya iso, bayan an kawo masa Aayah ya ganta yayi mata addu’a, malam ya ce da Sheikh.
“Nifa gara daka zo Ridhwan. Abunnan ya tsaye min a rai yana damuna. Sintirin uban yarinyar nan ya ishe ni, kamar a kansa aka fara haihuwa?
Na fahimci yana son yayi amfani da damar ganin ‘yarsa ne ya nemi su daidaita, nikadai na san abinda na gani rannan a tsakaninsu, to wallahi bada ni za’a yi wannan kuskuren a sabawa Allah ba.
Ni na rasa irin wannan abu, ka sake mace da kanka, ta dawo gidansu, to sintirin da kulafucin haihuwa kuma na menene?”
Tsaki sosai Yaya Sheikh ya yi, ya ce, “Malam fuskarku fa Zayyan ya gani yake kokarin kawo rainin hankali. Don inda baiga fuska ba, ko kusa bai isa ba ya zo gidannan. Don haka ni zan wuce da Safifi Lagos bisa umarninka.
Idan ya isa yazo gidana yace zai ga Safifi. Diyarshi kuma in an yaye kawai ya zo ya dauki abarsa.
Safifi aiki za ta fara, zan samar mata aikin koyarwa a UNILAG in sha Allah don ta samu abun debe kewa da dogaro da kanta”.
Cikin shakka da abun Malam ya ce, “A yi haka Ridhwan? Matarka fa? Baka ganin zasu takura mata?”
Sheikh ya ce, “Malam kun fi ni shaidar Assafe. Ba ta da irin wannan matsalar insha Allah, ga shi kuma Allah ya hada jininsu da Safifi, hasali ma ita ta kawo wannan shawarar ta in dauko su su dawo Lagos, don Safifi ta samu canjin environment, ta yi moving on da rayuwarta ta manta da wannan dan rainin wayon.
A lokacin da mace ta dandana bala’in bacin ran dake cikin sakin aure, Malam abinda tafi bukata shine canjin muhalli, da na fuskokin mutanen da ke zagaye da ita, sannan da soyayyar iyaye da kowanne makusancinta.
Da wannan nake rokonku Malam! Akan ku ba ni Safifi in canza mata muhalli, ta samu ta yi adjusting.
Kuma ku samu ku huta da sintirin wannan dan rainin hankalin, ni mutum in ya isa ya zo nawa gidan kullum, ya ce ya zo ganin ‘ya, ya gani in zan dauka.
Bazan hana shi ganin ‘yarsa ba, amma ayi komai na hankali da ka’ida”.
Da wadannan kalaman Yaya Sheikh, ya samu ya kalallame Malam, ya yarda da tafiyarsu Sophie jihar Lagos.
Safiyyah da Aayah sun isa birnin Ikko lafiya ta jirgin sama. Inda suka samu tarba ta musamman da kulawa ta musamman daga Antinsu Assafe. Fadar cewa Safiyyah ta ji dadin komawa Lagos gidan Yayanta Sheikh, wani abu ne da ba ya bukatar dogon sharhi.
Domin Assafe mutum ce guda har da rabi, wadda ta dauki dangin mijinta matsayi daya da nata dangin, saboda son da ta ke yi ma dan uwansu Ridhwan.
Kwana biyu da tafiyarsu Safiyyah Lagos, sai ga Arch. Zayyan ya zo Dandume kamar yadda ya saba, bayan motarsa shakare da sayayyar Aayah da Mamanta, harda wadanda bazasu yiwa Aayah amfani ba a wadannnan kananan watannin nata na haihuwa ba.
“Ayya, ka daki gurbi Zayyan, ai yau kwanan su Aayah biyu da komawa Ikko. Maman nata za ta fara aikin koyarwa a can”.
Malam ya ce da Zayyan, wanda ya zo ya tadda wayam babu Aayah a Dandume.
Allah Ubangiji ya jarrabe shi da wata irin matsanciyar kaunar Aayah, kamar a kanta ya fara haihuwa. Ta zame masa ‘favorite’ a zuciyarsa, sanyin idaniyar da yake gani kadai ya ji ta dauke masa kewar Sophie.
Abu goma da ashirin kenan sun hade ma Arch. Zayyan Bello Rafindadi, domin tun tafiyar Azeezah gida, Baba Murtala ya koro ta, to ba ta dawo gidan Zayyan ba, gidan kanwar mahaifiyarta Anti Salma ta koma anan Abuja.
Anti Salma kuma ta daure mata gindin cewa tunda har Zayyan yayi kuskuren kai hannunshi fuskarta da sunan duka, kuma Baba Murtala ya ki yin komai a kai, to ta yi zamanta a gidanta sai Zayyan ya zo da kansa. Shi kuma sam a wannan lokacin baima da nutsuwar komai, tun haihuwar Aayah ya koma kamar wani susutacce, musamman in ya tuna cewa daga wannan lokacin Sophie ta fita daga iddarsa.
Ya san da cewa, Azeezah na gidan Anti Salma don tun ranar da Baba ya rarako ta Azumi mai aikinta ta kira shi a waya ta fada masa suna can. Amma ko a jikinsa bai ma yi tunanin zuwa ba. Saboda Aayah ta dauke dukkan attention dinsa da affection dinsa. Yanzu kuma gashi ya zo ganin Aayah yau an bi shi da wani zance marar dadi, wai ita da Mamanta sun bar Dandume bakidaya.
Don haka yau jikinsa ba lakka ya bar gaban Malam Usman. Malam yaga yadda kamanninsa suka birkice, ya rikice gabadaya. Saboda ya san Sheikh tuntuni baya wani son shi, ya san babu fuskar ma da za ya je gidan Sheikh. Asalima bai san a ina gidannasa yake a Lagos din ba.
Ko da ya dawo gida yau, Zayyan ya kusa zaucewa, ya husa yin dan karamin hauka a masterbedroom dinsa, two zero babu Sophie babu Zeezah.
Zama ya yi dabas! A dakin barcinsa ya hada kai da gwiwoyinsa, maraicin Babansa yake ji yau har ruhinsa, yasan da yana nan, da abubuwa da yawa da suka faru yau da basu faru ba, yana kara ce ma Ubangiji Ya yafewa Mama Fatu har zuciyarsa, yadda ta yi shattering rayuwar gidansa da farin cikinsa dana iyalinsa…., yace Ya Allah kada Allah ka kama Mama da wannan laifin na zama azzalumar uwa agareni, saboda KAWAR ZUCIYARTA da rashin tawakkalinta da insatiable nature irinna dan adam.
Zubainah ta muskuta cikin kujerar da take zaune, tace cikin tausasawa.
“Komai ya faru da rayuwar bawa Baffa da sanin Allah fa, kuma idan ya tsorace shi zai bashi mafita, Ya azurta shi ta inda bai zata ba.
(WA MAN YATTAQILLAHA YAJ’ALLAHU MAKHRAJA. WA YARZUQHU MIN HAITHU LA YA YAHATASIB). Kai dai ka tabbata baka sake maimaita kuskuren sakin mace a rayuwarka ba, domin Allah da ya halatta saki; ba Ya sonsa.
Sannan Ya yi alkawarin jarabtar bayinsa da soyayyar matan da suka saka babu dalili.
Balle Safiyyah da kuka hadu kaida Mama kuka yi wa saki bisa zalunci.
Yanzu dai kokari za ka yi, ka yi hakuri ka dawo da Azeezah first, ita ce tabbas din dake hannunka.
A komai Azeezah ta ci gaba da cin arzikin Baba Murtala a gurinka, domin shi ma ya rike mu a lokacin da muka rasa mahaifinmu. Ya tallafemu da rayuwarmu bakidaya, ya tsaya maka, ya gina ka. Kuma har abada yana kaunarka. Hakuri da Azeezah ya zame maka farillah ma ba Sunnah ba. Don haka Baffa ka ci gaba da hakuri da ita da halayenta, irin hakurin da za ka yi da kanwarta Hatoon idan ta kuskure, don gudun maimaita irin kuskuren da aka yi a baya.
Besides, ku kuka saya Azeezah ta siyar muku kaida Mama, kowa ya sayi rariya kuwa ya san za ta zubda ruwa.
Amma a lokacin da zuciya ke bisa kan dokin ‘kawa’ (adornment) mawuyaci ne a gane hakan, har sai an hau dokin, an dandana gudunsa an sauko a hankali.
Dole ka yi hakuri da Azeezah ka kuma je ka dawo da ita, don ita ce reality din da kake da shi a hannunka yanzu. Sophie gaibu ce, ko daga take-taken iyayenta da ‘yan uwanta bana jin za su kara yarda su dawo mana da ita.
Duk da haka keep your hope alive! Allah shine masanin gaibu, ni nasan kai kadai ne Safiyyah ta so a rayuwarta. Da wuya wannan soyayyar taka da Safiyyah ta koma kiyayya sai dai bacin rai kam, wanda ya riga ya gama samun muhalli, fatanmu Allah ya huci zuciyarsu”.
Zubainah ta dade tana kwantarwa da kanin nata wato Baffa (Zayyan) hankali, ta wayar da suke yi, har ya yarda gobe zai je gidan Anti Salma ya dauko su Azeezah, alfarmar mahaifinta karimin uba a gare su, Alhaji Murtala Babangida Masari.
** **



