Chapter 13: Chapter 13
“Ridhwan, zaman Nana Safiyyah a gidanku ya isa haka, ina son in bude ido in ganta a dakin miji kuma.
Na farko na gaji da zaryar Alhaji Murtala a gidannan, akan rokon a maida ma Zayyan da Nana Safiyyah aure, satin da ya wuce ita Hajiya Fatun ya sako a gaba suka zo nan gabanmu bada hakuri da neman gafara.
Ina ganin mutuncin Alhaji Murtala ina kuma ganin kimarsa.
Don haka na gaya musu ni tuni na yafe koma menene, amma ba ni da hurumi a kan al’amarin auren Safiyyah wannan karon, wuka da nama duk suna hannunta.
Ga kuma yaron nan Haroun, shi ma ba kashin yadawa bane a wurinmu. Don haka maaganar aiki da ka ce ka samar mata a Lagos ba mai dorewa bace, a ajiye ta a gefe a karbi reality.
Mutuncin mace shine dakin mijinta. Aayan ta shekara yanzu. Ya kamata a dauketa a bakin nono Nana Safiyyah ta shiga ibadar aure.
Ba zan yi furfurar banza ba a gurin Alhaji Murtala da Haroun, don duk nace su dakace ni sai ka zo.
Don haka ke Nana Safiyyah yau ga ni ga ki, ga Yayanki Sheikh, ga mahaifiyarki su zama shaida, ki fadamin me kika yanke? Me kika zaba?
Auren Haroun ko komawa dakinki ki raini Ayatullah a gaban mahaifinta?”
A wannan lokacin da Malam ya bata wannan zabin, Safiyyah ba abinda ya zo ranta sai sabon bacin rai, a bata zabin komawa Zayyan ma ai bata taso ba, ta gama sallama Zayyan ko wane irin repenting zasuyi shi da Mama, duk runtsi abinda za ta tarar a gidan Haroun ta tabbata bai kai na gidan Zayyan ba.
Ko babu komai bata da matsalar dangin miji da ta iyayen miji, don Haroun bai da wasu iyaye bayan nata.
Ba wai tsoron fuskantar kalubale take ba yanzu. Tanada karfin halin fuskantar kowacce irin rayuwa yanzu, daga kowacce irin uwar miji ko dangin miji.
Wato Safiyyar da ba ita ce yanzu ba, su Mama sun kangarar da zuciyarta, bata jin akwai wata kishiya da zata sake razanata ko ta hanata rawar gaban hantsi, ta yadda ita kanta in ta tuno irin tarin cin kashin data bari Azeezah tayi mata da kaskancin data jure a gidan Zayyan a dalilin kishiya haushin kanta ne yake kamata kamar tayi yaya.
Ammi fargabar amsar da Safiyyah zata bayar ya hanata ko motsin kirki, don Ammi ta riga ta gama tsanar auren Zayyan da Safiyyah a kasan zuciyarta ko bata furta ba, tun daga ranar da Safiyyah ta dawo gabanta an saketa, ta gama debe haso da tsammani da kaunar komawarta rayuwar Zayyan Bello.
Without a second thought kuma out of frustration Sophie ta ce ma mahaifinta,
“Malam! Gara mini auren Haroun din, da dai in komawa Zayyan. Na zabi Haroun, ku saka min albarka”.
Ammi har wata boyayyar ajiyar zuciyar jin dadi ta aje, jin finally, Nana Safiyyah da kanta tana kan nata zabin itama.
Babu wata nadamar Hajiya Fatu data taba dada Ammi Hafsatu da kasa, Haroun ne zabin Ammi a yanzu 100%.
Malam ya ce, “To shi ke nan Nana Safiyyah, kada Allah ya sa zabinki ya zama nadama, Nana Safiyyah yayi miki albarka, Allah ya ba ki ikon zama lafiya da mijin da kika zaba da sabuwar abokiyar zamanki.
Ni kuma zan kira Alhaji Murtala in bashi hakuri, in gaya masa ga abinda kika zaba, dama na ce ya bani kwana biyar komai ke nan kika zaba zan kira na sanar da shi, domin kwarai bawan Allahn nan ya damu da halin nadamar da dansa/surukinsa ke ciki”.
Su Safiyyah sun koma Lagos a washegari suka bar Malam da kiran Baba Murtala a waya cikin jin nauyi, bayan sun gaisa Malam ya kauda komai cikin alhini ya gaya masa ga abinda Safiyyah ta yanke, wato auren dan uwanta Haroun da ya tashi a hannunsu, kuma sun tsayar da lokacin daurin aure.
Baba Murtala ya ce,
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.
Daga kalbinsa har bakinsa damuwa ce tsantsa. Hajiya Nana na tambayarsa abinda ya faru shi kuma Baba Murtala yana kokarin kiran lambar Mama Fatu.
Mama na dagawa za ta fara gayar da Baba Murtala, cikin sanyi jikinta dana murya na koyaushe yanzu, wannan izzar ta Mama duk ta kau babu ita yanzu, Baba Murtala ya dakatar da ita ya ce.
“To Hajiya Fatu, sai ki zuba ruwa a kasa ki sha, finally, Safiyyah ta bar muku Zayyan keda Azeezah har abada, zata auri waninsa, dan uwanta from another mother, sati uku masu zuwa”.
Bai kuma bata damar cewa komai ba ya kashe wayarsa, Mama na faman bin kiran Baba ya ki dagawa. Daga nan Baba Murtala ya kira Zayyan.
Zayyan ya daga wayar Babansa cikin ladabi, suka gaisa da Baba Murtala. Nan yake gaya masa suna asibiti da Azeezah zata haihu.
Jin hakan da Baba Murtala ya yi sai bai ce masa komai ba, kada ya kara masa tension.
Baba ya yi addu’a ya ce, Allah ya raba su lafiya, waye tare da ita?”
Ya ce, “Anti Salma da mai rainonta dinnan, Azumi suna nan”.
Baba ya ce, “To zai gaya wa Hajiya Nana don ta san wa zata kara turowa daga Masari kafin ta samu jirgi ta taho da kanta a washegari.
Cikin gajeruwar nakuda Azeezah ta haifo yaronta namiji, bayan wasu awanni da haihuwar likitoci suka tabbatar yaron baida cikar lafiya, an haife shi ne da lalurar (Cerebral Palsy).
Azeezah ta firgita, tsoron daukar yaron ma take ji, amma Zayyan haka yaji son yaron ya kamashi a take yayi masa huduba da sunan Babansa Muhammad Bello.
Kwanan yaron biyar a duniya amma Azeezah saboda tsoronsa data ke ji bata bashi nono ko sau daya ba, ba tareda sanin Anti Salma ba, a daren na shida suka wayi gari jaririn ya koma ga mahaliccinsa.
** **
Malam ya saka daurin auren Safiyyah da Engr. Haroun Dalhatu sati uku masu zuwa.
Kwanansu biyu da dawowa daga Dandume bayan zuwansu Accra Haroun ya sake zuwa Lagos, wannan karon hatta da tsarabar Aayah daban ce.
Safiyyah ta fito ta sameshi a falon bakin Yaya Sheikh kamar wancan karon, saidai fuskar data fito masa da ita har gara ta zuwan farko, sunan an saka musu ranar daurin aure, ita kanta bata san meye matsalarta ba, batasan hakikanin meye zabinta ba, duk da cewa ita ta zabi Haroun din amma ta kasa jin contentment da hakan, gata nan ne dai kawai.
Sai dai yau bata zo masa da Aayah ba, ita kadai ta fito, ba wata kwalliya ta jan hankalin wanda ka ke shirin aura nan da ‘yan satittika, hirar ma duk Haroun ke yi mata sai dai ta yi murmushi ta ce eh, ko a’a. Amma ta kasa sakin jiki har fiye da zuwansa zance na farko. Abin ya dameshi, har ya rika tunanin kodai shine bai iya approaching mace ba?
Yanzu data tabbatar shi ne zabinta kuma sabon abokin rayuwarta sai taji batada kwarin gwiwa, da al’amuran Ubangiji masu juyawa, tsoron Allah kadai ya cika ranta tana kara tabbatar wa kanta ita ta yi wa kanta wannan hukuncin ba wani ne ya tursasata ba anya, ya zama dole ta bude zuciyarta ta karbi Haroun, ta kuma ba shi kyakkyawan muhallin zama a cikinta.
A can Kaduna kuma, yau Mama ta kira ‘ya’yanta mata bakidaya domin su yi closed-door meeting.
Mama ta shiga damuwa da firgici a kan maganar auren Sophie da dan uwanta da Baba Murtala ya gaya mata. Don haka ta kira su gabanta gabadaya ta sanar musu tana neman shawararsu.
Mama na magana cikin damuwar data yiwa zuciyarta katutu. Ta ce,
“Allah shi ne shaida a kan irin kokarin da na yi don na maida ma Baffa aurensa da nayi sanadinsa, amma iyayenta da ita kanta Saffiyyah basu bamu wannan damar ba a karo na biyu.
Ni dai na san na yi kyakkyawar nadama, na yi sahihin tuba a kan abin da na aikata musu irin wanda Ubangiji ya yi alkawarin karbarsa. Wato tuba da aka yi da niyyar ba za a sake komawa izuwa wannan abun da aka aikata ba. Amma na rasa me ya sa iyayen Safiyyah da ita kanta sun ki yarda da ni?
Mama tayi ajiyar zuciya kafin tacigaba da cewa.
“Babanku Murtala ya kira ni ya gaya min an saka ranar aurenta da dan uwanta da ya girma gidansu”.
Mama ta nisa cikin damuwa, ta ce, “Baffa nake tausayawa… ba shi da hakkina, ba shi da zuciyar dauka. Safiyyah kadai yake yiwa so na hakika”.
Mama ta soma share ido ta ce, “Ga baby ya rasa ko kwana uku ba a yi ba, na kasa gaya masa hukuncin iyayen Safiyya, na kuma tabbata babanku Murtala ma bai gaya masa ba”.
Zubainah ko a jikinta, ta ce, “Ällah ya sa hakan ne yafi ma Safiyyah alkhairi, iya abinda zan iya cewa kenan Mama, sai ya ji me ta ji itama da ya auri wata ya barta don bata haihuwa”.
Zubaida ta ce, “Habawa… haba, haba ke kuwa Zubainah wai ke abu ba ya taba wucewa a wurinki ne?
Ki tausayawa Mama da Baffa wace irin nadama kuma ki ke so su yi ne? akwai wanda yake sama da aikata kuskure in ya roki Allah afuwa ya gafarta masa?”
Zubainah ta ce, “Tunda haka ne, su iyayen nata sun ce sun yafe, amma ga hukuncinsu, abeg ku barsu su zauna lafiya, Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi.
In Aayah ta isa yaye ni zan karbe ta don ba zan ba Azeezah ita ba”.
Takaicin Zubainah ya ishe su gabadaya har Zahra na cewa,
“Lallai Ya Zubainah kin canza, na sanki da tausayi da karbar hanzari a baya, amma yanzu I wonder idan zuciyar da ke cikin kirjinki na aiki daidai kamar da”.
Zubainah ta ce, “Ai tunda dama likitar zuciya ce ke sai ki musanya min da mai aiki daidai”.
Duk yadda suka so Zubaina ta tsaya su samo wa Baffa mafita Zubainah ta ki shiga, ta ce, ita tafi so wa Sophie hakan. Tace.
“gara ta je inda za a so ta, a mutunta iyayenta, ta dandana rayuwar ‘yanci da soyayyar miji data Yan uwan sa a gidan mijinta.
Ba sai da dan uwanmu ne kadai Safiyyah za ta samu soyayya da haihuwar ‘ya’ya ba”.
Dole suka kyale Zubaina suka yanke mai fishsshe su, wato zuwa gun Yayan Safiyyah wanda aka ce ta koma hannunsa a yanzu, da kokon bararsu na karshe, ko zai dubi Allah ya tausayawa Mama da Baffa ya lallashi Safiyyah ta janye hukuncinta.
Zubaina kam ta san da wuya wai gurguwa da auren nesa. Iyayen Safiyyah dattijai ne basa magana biyu.
Bayan rasuwar yaron Azeezah da kwana bakwai, Mama da kanta ta sanar da Zayyan hukuncin da Safiyyah da iyayenta suka yanke kafin Baba Murtala ya gaya masa, kwana bakwai kenan da binne yaron da Azeezah ta haifa. A karshe Mama tace dashi ga shawarar da suka yanke ta zuwa gun Yayan Safiyyah a Lagos dukkansu, yayi kokari ya nemo musu adireshi.
Arch. Zayyan, a wannan daren ya kasa runtsawa, ya kwana cikin sabuwar nadama da despair, ya tuna abubuwa masu yawa da suka faru a zamansa da Sophie bayan ya auri Azeezah, ciki har da kin baima Sophie kwana da yayi na tsayin kwanaki arba’in cif, don shi ya samu haihuwa.
Ya tuno satar kwana da ya dinga yi mata yana zuwa yana rakashewa da amarya Azeezah.
Abin da yake ji a zuciyarsa yanzu, da Sophie ta zabi auren waninsa yake kwatantawa da wanda Sophie ta ji a wancan lokacin, da yake aikata hakan a gare ta.
Akace idan maye ya manta….
Zayyan ya rasa ina zai sa kansa, gani yake kamar garin Allah ba zai waye ba ya tadda Sophie a Lagos gobe, ya roke ta ta yafe masa, hakkinta dake kansa ko da ba za ta yarda ta dawo masa ba.
**
THE CONFIDENTIAL
(BEHIND THE SCENE)
Ba Zayyan kadai ne bai runtsa ba a wannan daren, daren yazo da wani al’amari mai girma a gareshi.
Dare ne na mazaje guda biyu, known and the unknown, wadanda soyayyar Safiyyah Usman Ladan ta dade da yi wa katutu a zuciya.
Ya kira tasa soyayyar da ‘confidential’.
He’s internally suffering a zuciya da gangar jikinsa, amma duk juyin da yayi sai ya kalli matarsa Assafe.
Wata irin mace mai halin ‘yan aljanna, wadda samun kamarta a wannan zamanin sai an tona.
Assafe is not only a good and confident wife to him, but also a good companion wadda zai iya sadaukar da komai ta zauna dashi.
Assafe ta rungumi danginsa da kowa nasa bai taba ji ko ganin mace mai kirki da sanin ya kamata kamarta ba.
Deep down inside him ya dade cikin wannan azabar, tsakanin soyayya da son rama halarci, watakila tun farkon balagarsa a haka ya rayu cikin uqubar soyayyar Safifi wadda kowa kewa kallon haduwar jini na ‘yan uwantaka, shi da kansa hakan ya dauka har sai bayan mutuwar aurenta ya soma gane shayi ruwa ne,
‘SAFIFI! Kanwarsa ce, amma wadda ya rayu tsayin shekarun girmansa cikin wani irin matsanancin so da kaunarta.
Amma a ture komai a dora al’amarin akan sikeli na hankali da adalci, ita zuciya sai ana sa mata linzami, ba komai data ke so dan adam zai biye mata a kai ba, yanzu idan ya fito da sirrin zuciyarsa ga iyayensu da ita kanta Safiyyah da me Assafe da sauran mata irinta zasu fassara shi idan ya fito da halin da yake ciki fili?
Anya hakan bazai kassara zuciyar mata irin Assafe su daina jan yan uwan mijinsu a jiki balle su taimaka musu cikin yanayi na zawarci da sukafi bukatar a kaunace su?
Bahaushe yace ana barin halas don kunya dole ya sadaukar wannan son don mutunta Assafe, aka ce sakamakon alkhairi halacci.
Zai bar Safifi ta auri waninsa don rama halacci ga Assafe, kuma har abada ba zai taba bari Safiyyah ta san wannan ‘hidden side’ din nasa a kanta ba, balle Assafe.
Yana addu’ar Ubangiji ya sa shi a jerin masu soyayya don Allah, da masu barin halas don halarci ba don kunya ba.
Karfe biyu daidai na sulusin dare a lokacin.
Safiyah idonta biyu tana kwance kawai, tunanin makomar sabuwar rayuwarta itama ya hanata runtsawa, kamar yadda tunanin rasata ya hana Sheikh da Zayyan runtsawa.
Wai tambayar kanta take da gaske ne zata auri wanin Zayyan sati mai zuwa?
Kuma Engr. Haroun ne mijin nata, wani kwayan mutum guda daya da bata taba jin komai da ya danganci kalmar SO a kansa ba bayan kallon dan uwa da take masa?
Wannan tunanin yau shi ya hana Safiyyah barci. Sai juyi take hagu da dama a gadon ta, don taji dadin kwanciyar amma ina! Ta kasa.
Safiyyah ta kurawa Aayah ido, wadda a karshen komai bata san makomarta ba, ta san dai Zayyan ko zata mutu ba zai bar ‘yarsa taje agola gidan Haroun ba yadda Haroun yake tunani, ita kuma yanzu ne ma take jin son Aayah da take hango musu lokacin rabuwarsu ya kusanto.
Daidai lokacin ta ji shigowar sakon (text) a wayarta, kamar yadda aka saba yi mata makamantan wadannan sakonnin a kwana ukun nan da suka gabata, da wata bakuwar lamba.
Sakon yau yafi na jiya sakata a duhu, na jiya dana shekaranjiya kuma sun kusan fasa mata kwanya saboda duhun da suke sakata.
“Safiyyah you will be in my heart till my dying days…”.
A karshen sakon ya saka kamar haka.
-First love (whose heart will die craving for you forever).
Sakon jiya wanda shi ma ya zo karfe biyun dare ne daidai da lokacin da na yau ya shigo, shi ya fi daga mata hankali.
‘some times we make hard sacrifices not because we will not succeed in achieving what we desire….. but only to repay back the kindness of others’.
Ma’ana, wani lokaci muna yin sadaukarwa mai matukar wahala ba don ba za mu yi nasara a kan abin da muke so din ba, (idan mun fito da shi fili) a’ah, sai don kawai mu ramawa wasu mutanen kirki kirkinsu garemu.
-First love.
Sakon shekaran jiya kuwa ga abin da ya kunsa duk dai daga wannan special number na wanda ya kira kansa da suna -first love.
Yace.
“Ni nasan na so ki kafin kowa, ina kuma sonki fiye da kowa, zan ci gaba da sonki fiye da komai, har zuwa karshen numfashina Safiyyah zan ci gaba da dakon son ki.
Ina addu’ar samunki a matsayin matata a gidan aljannah; one and only Hurul eeni na.
-First love.
“Yaa Rabbil Alameena waye wannan???”
Wannan tambaya Sophie ta yi wa kanta sau ba adadi, abin ya tsaye mata a rai, har a washegari Assafe ke cewa ta ganta cikin damuwa, mene ne?
Sai ta kasa gaya mata wani daya kira kansa boyayyen masoyi ne yake hanata barci da kalaman dake neman fasa kwanyarta, ta ce ma Assafe babu komai. Ba ta iya samun barci yadda ya kamata kwana biyunnan.
Assafe tasan tun daga ranar da aka sama Sophie ranar daurin aure ta canza, sai ta gyada kai kawai ta ce, ko asibiti za su je a auna jininta?
Ta ce, “Kada kisa ma kanki BP, hukunci ke kika yi shi da kanki ba wani ya saka ki ba, kuma har zuwa yanzu kina da damarmaki a kansa”.
Ta ce, “Anti, banida dana sani a kan hukunci na, da in komawa Zayyan, sau dubu gara min auren Haroun.
Zan zauna da Haroun don ni na zabe shi kuma zabin mahaifiyata ne, na tabbata ba zai taba wulakanta ni ba balle wani nasa”.
Assafe ta karyar da kai tana murmushi ta ce, “Kayyasa! Ba a nan take ba kinji? Love is real, da soyayya ne zaki jure komai, amma a inda babu soyayya???”
Sai Assafe ta girgiza kai tace “hummm! Amma dai a bar kaza cikin gashinta kawai, tunda kin riga kin yi making mind dinki”.
Da safe Zayyan ta hannun Sabah ya samu adireshin gidan Yaya Sheikh a Lagos, washegari suka wayi gari da bako a sassan bakinsu, Arch. Zayyan Bello Rafindadi yau a gidan Sheikh.
Sophie ta je wajen aikinta don mika takardar ajiye aiki, kasancewar saura sati daya kacal daurin aurenta da Haroun.
Zuwan Zayyan na farko kenan gidan Yaya Sheikh, an yi sa’a Sheikh din yana gida, aka kira daga gate aka ce masa yana da bako daga Katsina, ba tare da tambaya ba ya ce a kai shi ‘guest wing’ tunda daga Katsina yake ya huta.
Sai can jimawa Sheikh ya je dakin bakinsa. Ya sha mamaki da ganin Zayyan, don shi dai ya san bai bashi adireshi ba, kuma ya hana Malam da Ammi su ba shi tuntuni, tun farkon dawowar su Safifi gidansa.
Kwarjinin Zayyan, cikar zati dana mazantakarsa da ajinsa na kololuwa, duk ba su hana Dr. Ridhwan gurza masa rashin mutunci ba.
Ya zauna suka gaisa sosai ta hanyar baima juna hannu, Sheikh ya yi kamar bai gane shi bama, sai da Zayyan ya gabatar da kansa tukunna.
Yaya Sheikh ya ce masa, “oh! Ashe Baban Aayaah ne, marhaban, bari insa mai rainonta ta kawota”, yau Zayyan ya kauda komai yace ma Sheikh shi Sophie yau yazo gani kafin Aayah.
Yaya Sheikh ya gyara zamansa ya dube shi sosai, yaga yadda Zayyan duk ya birkice kamar ba shi ba, daga jiya zuwa yau kacal, da aka gaya masa hukuncin da Safiyyah ta yanke zaucewa ne kadai Zayyan Bello bai yi ba.
“Amma kana sane da cewa rana ita yau ne daurin auren Safifi da wani ko?
Arch. Zayyan, I am very sorry, kamata yayi ka fara neman iznin mijinta na yanzu, kafin ka nemi iznin ganinta daga gareni”.
Zayyan ya dago a hankali da rinannun idanu ya dubi Yaya Sheikh, tabbas Sheikh ya hada gobara a kirjin Zayyan, Sheikh ko a jikinsa shima ya dube shi cikin ido da nasa matsanancin kishin;
Arch. Zayyan shine silar da har gobe bai samu nasarar auren Safifi ba, sabida kutsen da yayi masa, ya kuma san shikadai Safifi ke yiwa so na soyayyah. Don haka a duniya Sheikh ya san yana kishin Zayyan Bello, fiye da yadda yake kishin Haroun ma.
Kafin ya sallami Zayyan sai ya tabbata ya dan wankeshi yau da soso da sabulu.
Yaya Sheikh yace “ban cika son mutane masu bin kawar zuciya ba ni, kai wani irin mutum ne da na kasa fahimtar inda ya dosa da soyayya, saboda a zahiri Zayyan baka ma san darajar abinda kake so ba, tunda har kayi wasarere dashi, har ya kubuce maka.
Kaima ka san wasa kake yi, idan ka ce min ka zo gabana ne bikon Safifi, bayan kai da kanka ka kore ta daga gidanka, to wannan binbinin da ke hana iyayenmu sakat na mene ne?
Avoid being selfish a komai, learn to care about the feelings of your wife and others. I don’t want to say you are a narcissist!”.
Haka Yaya Sheikh ya wanke Zayyan tas, ya kuma ce mutunci da alfarma daya zai yi masa shi ne a kawo masa ‘yarsa Aayah ya ganta.
Kan Zayyan a sadde, yana mai yarda da kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakin Sheikh, akan abinda suka yiwa Sophie shi da danginsa, duk da ya tabbata shi dai bai aikata haramci ba don ya kara aure, sunnah ya raya, amma wani zubin brave men like him a soyayyah, wadanda suka yarda suna son matansu fiyeda komai ai su kan hakura da jin dadinsu, don su kyautata ma matansu, wato suna barin halas wani lokacin don su ceci soyayyahr da sukema matansu.
Har Sheikh ya gama buga waya cikin gida, ya ce,
“Maman Ada ta kawo Aayah guest wing Zayyan baisan inda kansa yake ba”.
Aka kawo ma Zayyan Aayah, very cute and neat baby, sai kamshi take na turaren jikin uwarta cikin kyakkyawar suttura. Yana karbarta Yaya Sheikh ya tashi ya bar shi a falon.
Zayyan ya dade rungume da Aayah a jikinsa wadda ke barci sadidan, wani irin nauyi zuciyarsa tayi da kalaman da Yaya Sheikh ya yi masa, amma a kasan ransa ya san ainahin gaskiyar kenan. “He is a narcissist!”



