⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 15: Chapter 15

“Zayyan alhamdulillah, finally, ga ni ga Safiyya ga Mamanku a gaban Yayanta Sheikh….”.

Numfashin Zayyan har turiri yake, kirjinsa kuwa neman rabewa gida biyu yake. Watakila matan nan guda biyu su ne ajalinsa! Domin Baba Murtala ya ci gaba da gaya masa cewa.
“Finally, Safiyyah ta yafewa Hajiya Fatu, duniya da lahira, amma kai ta ce har abada ba zata dawo maka ba. Sannan ta ce tana so kabar mata rikon ‘yarta har zuwa isa aurenta.
Zancen da nake maka yanzu ga katin daurin aurenta a hannunmu ni da Hajiya Fatu, saura kwana uku a daura mata aure da wani dan gidansu mai suna Haroun”.
Baba Murtala ya rufe zancensa cikin tausasa murya da cewa.
“Ka yi hakuri ka ji ko Zayyan, ka fauwalawa Allah tunda ya riga ya rubuta iyakar zamanka da Safiyyah kenan. Ni kuma ko ‘yar wa ka ke son kara aure, ko mata uku ne a rana daya Zayyan kaje ka nemo aurensu, nayi alkawarin yi maka walicci da biya maka sadakin aurensu!”.

Baba Murtala bai jira cewarsa ba, amma yana iya jin saukar numfashin Zayyan ta cikin wayar. Wanda ke safka da sauri-da sauri kamar na mai ciwon asthma. Sai kawai Baban ya kashe wayarsa saboda tausayin Zayyan yaji ya ratsa har kokon ransa, musamman yau da ya samu yin arangama ‘face to face’ shima da Safiyyah diyar Alaramma Usman Ladan Dandume ya san cewa Zayyan yayi rashin mata daya da daya a duniya.

Hakika wannan ita ce matar da kowanne uba zai so dansa ya aura, ga nutsuwa ga ilimi da hankali da sanin ciwon kai. Uwa-uba ta fito daga tsatso na gari, ta samu tarbiyyar addinin musulunci data dattijan iyaye gwargwado. Wadanda babu duniya a ransu sam. Sai bai ga laifin marigayi Bello Rafindadi ba, da ya so wa dansa rayuwa da ita, shi kuma ya biyewa fitinanniyar uwarsa suka tasata a gaba, har suka kai ta bango.
Yayi iya abinda zai iya don ganin Safiyyah ta dawoma Zayyan, amma a wannan gabar ya fidda hannunsa, ba zai yi jayayya da hukuncin Ubangiji ba, kuma ba zai takura wa iyayenta ba, sun ba ta hakkinta wanda addini yace su bata.
Ita kuma Safiyyar a cikin halayen kwarai nata na kashin kanta tayi hukuncin yafewa Mama, kome ta yi mata, har tace wanda ta sani da wanda bata sani ba, amma ba za ta komawa auren Zayyan ba.

Sai kuma ga wayar Mama bayan ta Baba Murtala, ita kam Mama a nata kalaman ta kasa daukan kaddara kamar yadda Baba Murtala ya dauka, cewa ta ke,
“Baffa ka yi wani abu, kafin Safiyyah ta kubuce maka har abada… Baffa aure zata yi, kwana uku masu zuwa… na cuce ka Baffana, don Allah ka yafe mini…
Baffa ka yi kokari ka dawomin da Safiyyah da Aayah, ba zan kara shiga rayuwarku ba idan ba alkhairi zan shuka muku ba.
Na yi wannan alkawarin tsakanina da mahaliccina Baffa!”.

A salube Zayyan ya ajiye wayarsa a kan cinyarsa, ya rasa kalar hukunci ko tunanin da zai yiwa rayuwarsa…..

A karshe ya bige da daukan biro da zungureriyar takarda, ya kwanta rub da ciki akan kilishin falonsa, ya hau rubutu kamar sabon marubucin littafi.
Rubutu yake amma shikansa bai san me yake rubutawa ba.

“Dearest Safiyyah, my co-architect, my alter-ego, now and forever!

A cikin wannan wasika da zan rubuta zuwa gare ki, zan fara da cewa, bani kadai ne final decision dinki zai cutar ba, har dake kan ki, da kuma ‘yarmu, da bata da hakkinmu, wadda Allah ya bamu don ta zama ‘izna’ a garemu watau AAYAH!

Wadda Allah bai ga damar bamu ba sai a lokacin rabuwarmu.

Ina tabbatar miki kin dai yi hukuncin sake aure ne out of frustration amma har abada wannan hukuncin zai ci gaba da farautarmu nida ke da Aayah, kamar yadda nawa kuskuren yake ta farautata har yau.

Dearest Safiyyah, kin yi gaggawa, ko ince, kin yi hukunci na ramuwar gayya, wanda addini ma bai yarda dashi ba.
Gaggawa daga shaidan ne, listen to your heart first and think of our future. Dearest Sophie, na so ace kin tsaya kin saurari zuciyarki ne, kamar yadda nake sauraron tawa a halin yanzu. Ki ji irin nata hukuncin bana fatar bakinki ba.
Amma albishirinki Sophie, I am forever your alter-ego, a saboda haka ina tabbatar miki bazaki taba farin ciki a gidan wanina ba.
Kamar yadda nima tun barinki rayuwata ban kara farin ciki da komai ba, ban kara zama Zayyan ba sai Zaynu.

Ramuwar gayya ba taki bace Sophie, a wannan lokacin da muke gab da cin jarrabawarmu, you better look for your eternal happiness wanda ba kowa bane, sai Architect Zayyan, and his beautiful daughter, Aayah.
Allah da Ya halicce mu Shi Yaga damar halittar soyayyar juna a zukatanmu, ya dunkule zuciyarmu cikin ta juna, soyayyarmu bata da alaka da duk wai nau’in physical or materialistic attachement. Sophie Please come back to your humble abode.
Na yi miki alkawarin canzawa daga mai bin KAWAR ZUCIYA, zuwa na zama mutum mai godiya da duk yanayin da na same ki. Inyaso, I will be open to you, seek redress and adjustment daga gareki ba tare da jin nauyi ba.
Akwai muhimmin abinda muka rasa a cikin tarayyarmu, wanda yafi komai muhimmanci a mu’amala ta aure, shine “openness” ga junanmu akan mu’amalar auratayya, and communication gap dana samar a tsakaninmu, a gudun kada in ci miki fuska, wanda ya zo ne sanadin kawaicinki da alkunyarki da kuma girmanki da nake gani cikin idanuna, ina jin nauyin fito da su baro-baro in nusarsheki a kansu, maimakon hakan, sai kawai na bige da bin KAWAR ZUCIYA a matsayin samo maslaha.

A cikin tafiyata zuwa ga birnin KAWAR ZUCIYA ban samu guzurin komai a ciki ba sai na buhun bacin rai da dana sani da yaki karewa, pleasure din da na samu cikin kawar zuciya ba’a taba comparing dinsa da soyayyar nan taki ta ainahi ba. Truly na samu pleasure a cikinsa; amma transient, ephemeral pleasure.

A yau Safiyyah na gane kuskurena, domin na girbi duk abin da na shuka miki a tafin hannuna.

Safiyyah tun bayan tafiyarki nake nadama, har gobe gan gama ba, kuma batada niyyar karemin tun bayan fitarki daga rayuwata. Safiyyah ki karbi nadamata don Ubangiji Yana son masu afuwa da yafiya.

Kada ki yaudari bawan Allah Haroun, he’s innocent, kada kiyi wasa da emotion dinsa da innocence dinsa ki cutar dashi ta hanyar yin auren huce haushi dashi, he didn’t deserve this from you and from every woman because he’s innocent. And it will eventually backfire on him.
Domin na tabbata ba kuma zan yi kaffara ba in na rantse cewa ba za ki iya bashi farin ciki ba, za dai ki yi auren ramuwar gayya da huce haushin Zayyan da shi.
Believe me or not, I’m the only love of your life. Kuma ni ma haka, domin ke kadai ce macen da na aura don ina yi wa so na hakika. My dear Safiyyah, you are forever… “my alter-ego”.
A karshe ni Zayyan dinki ga ni on my knees, ga ni na dira a kan gwiwoyina ina neman rangwamenki Safiyyah.
Na tuba na bi Allah, na yi nadamar lalata mana rayuwa ta hanyar bin kawar zuciyata, ki yi hakuri ki dawo mu koma rayuwarmu da ‘yar mu in between a tsakaninmu. Come back to your humble abode.
Sa Hannun
Arch. Zayyan Bello.

Bayan ya gama rubutun da biro, Ya sake bin dogon rubutun yayi masa punctuations, sai kawai ya samu yatsun hannunsa suna typerwa a cikin wayar hannunsa, daya gama, ya yi masa ‘yan gyare-gyare, sannan ya aika shi lambar wayar Safiyya ta hanyar manhajar aika sako (text message).
Da jimawa Sabah ta gaya masa akwai waya a hannunta yanzu, kuma tsohon layinta tayiwa welcome back.

Ya yi wannan rubutun ne don fidda tsatsar da ke zuciyarsa kadai, ba don tunanin aikawa Safiyyah ba da farko, don haka koda yatsunsa suka tura rubutun zuwa gareta bai yi burin samun amsa daga Safiyyah ba, amma at least duk sanda ta ci karo da shi, ta kuma karanta, za ta fahimci illar da ta yi musu bakidayansu, kuma zai rage masa nauyin kirji idan Safiyyah ta san cewa bin kawar zuciyarsa na auren Azeezah bai kai shi ko’ina ba sai ga tafkin nadama.

Yana tura mata sakon aka tabbatar masa sakon nasa ya je, sai ya sulale a kan kilishi ya kwanta. Biron yayi nasa waje, iskar fanka ta dauke takardar wani gefen daban. Babu abinda yake hangowa a wannan dakikar sai Sophie tare da Haroun a rayuwa ta ma’aurata, yana kuma hango taswirar Azeezah cikin gizo na zuciya wani katon arnen banza yana lalata da ita da igiyar aurensa….

Kenan wadannan mata guda biyu, da khashi’ah mai kishi da kharija-iblishiya sune ajalinsa….. Numfashi ya soma yi wa Zayyan wuyar shiga da fita…..

A karshe ya soma samun congestion a huhunsa wajen fitar numfashi. Ga shi ya kulle kansa a sassanshi babu wanda ya san halin da yake ciki.

Washegari da Haroun zai wuce Geidam daga Lagos don shirin daurin aure, kafin ya wuce filin jirgi sai da ya fara biyowa gidan Yaya Sheikh, don yin sallama da amaryarsa Safiyyah. Don daga yau ba za su kuma haduwa ba, sai ko a gidansa, ko kuma bayan daurin aure in sun isa Dandume ita dasu Assafe.

Safiyyah ba ta kunna wayarta ba tun daren jiya sabida ta kwana cikin ciwon kai da takurar kirji, wanda ba komai ya sababba mata shi ba sai yawan tunani har zuwa wayewar garin ranar, da ta fito wanka tana shiryawa cikin wani material mai taushi yellow. Aunty Assafe ta leko tana gaya mata Haroun na falo, yace kuma sauri yake kada jirgi ya tashi ya barshi.
Ta karasa daura kallabinta, sannan ta dauki turare zata fesa… kome ta tuna a lokacin? Sai kurum ta mayar ta fasa.
Ta dauki wayarta da mayafinta da ya dace da launin kayan jikinta masu tsari, ta yafa, ta fice zuwa gurin Haroun.
Haroun na ganin isowarta ya saki wani murmushi na musamman mai tafe da ajiyar zuciya na godiya ga Allah. Hakika mahakurci shine mawadaci. Ba tun yau ba Safiyyah na masa kama da ‘yammatan kasar Ethiopia (duba bangon littafin). Tafi shekara goma sha a gidan auren wani, amma dubeta yanzu, tana nan ‘yar cas da ita kamar budurwa mai shekaru ashirin da hudu ba wanda zai ce ta dau ciki ta kuma haifa ta shayar.
A lokacin bata jima da kunna wayarta ba, Haroun kuma yace ba jimawa zai yi ba, saboda kada yayi missing flight dinsa, wanda nan da awanni uku zai tashi. Ta dage sai ya tsaya ta hado masa breakfast ko yayane, don tana da tabbacin bai karya a masaukinsa na hotel ba.
Murmushi ya yi, ya ce,
“Wa zai yi jayayya da amarya ne wai? Je ki kawo!”.

Nan inda ta tashi ta bar wayarta, bisa centre table din dake tsakaninsu. Ta tafi kitchen don hado masa abin karin kumallo.
Haroun na latse-latse cikin wayarsa ya ga wayar Safiyyah na ta haske tana daukewa, ga vibration tana tayi na shigowar sakonni akai-akai. Yawan shigowar sakonnin ne yaja hakalinsa wane irin sakonni ne haka ake turo mata haka a jejjere?
One after the other?

Kawai ya ji sha’awar kallon wayar hannun Safiyyah, don ya san irin wacce ya kamata ya canza mata da ita.
Ya daga wayar yana juya ta a hannunsa, Yaya Sheikh ne ya saya mata. Hoton Aayah ne a screen saver din wayar ta maqale a wuyanta hakoransu duk a waje cikin nishadi mai yawa suke, setting din wayarta mai fallasa shigowar sako ne daga sama, don haka daga sama sunan ‘sender’ din sakonnin yana ta bayyana,

‘HABIBY……’

sunan da ya dauki nutsuwarsa kenan har ya ji sha’awar son sanin waye Habiby din? Kuma sakon me yake turo mata haka sama da guda talatin? Tunda shi ko a waya ya kira ta Safiyyah zillewa hirar take yi.
A garin curiosity irin na Da namiji, da ba ya son rivalry, Haroun ya bude sakon farko dake ta shigowa daga Habeeby.
Kuma bai ko yi nisa cikin karanta sakon ba ya fahimci daga inda yake babu dogon nazari ko bincike.
Statement din farko kuma shi ya fi komai jan hankalinsa.. ga karance sakon daga farkonsa har karshensa. Zufa na barko masa, zuciyarsa na raurawa……
Bai ko kai ga kaiwa karshe ba yaji bazai iya ba….
Yana kokarin dire wayar a kan centre table din da ya raba tsakaninsu, wato inda ya dauke ta, Safiyya ta shigo falon niki-niki da ‘tray’ a hannu. Fuskarta fal fara’a ta ce,
“I’m sorry Baban Safiyya, for keeping you waiting. Bayan ka gaya min sauri kake yi. Kawai ina so ka ci girkin hannuna ne shi ya sa na tsaya na hada da kaina”.
Ta aje tray din a gabansa kan center table. Ba tareda ta lura da yanayinsa da ya koma kamar yana hadiyar kunama ba. Haroun, wanda tun daga cikin gashin kansa har zuwa yatsar kafarsa gumi yake, kamar yana tauna rikakkiyar kunama sai ya bi ta da kallo kawai, ya kasa cewa ko sannu, balle na gode. Saboda hatta fara’ar da yake gani a kan kyakkyawar fuskartar daga jiya zuwa yau zuciyarsa na gaya masa fake ne, wato na bogi ne.

Allah sarki. Safiyyah bata san me ke faruwa ba, bata san bomb din da Zayyan ya dana mata ya tashi da ita ba. Ta dai kasa gane kan Haroun daga wannan lokacin, hira ta ki yiwuwa kuma yaki cin ko loma daya na hadadden breakfast din da ta shirya masa.
A karshe ya mike yana duba agogo, ya ce mata zai wuce. Cikin damuwa da rashin jin dadin yanayinsa, Safiyyah ta ce.
“Amma ko kadan ba za ka ci ba, Yaya Haroun? I cooked it myself, my hand cooked just because of you”.

Haroun ya yi mata wani irin kallo, yana kissima abubuwa daban-daban a ransa, kafin ya ce,
“Don’t worry, next time insha Allah”.
Kawai sai ya sa kai ya fice yana cewa, “See you soon…..”.

Ya yarda kishi zai iya kashe maza, har dai in suka gane su ta bangarensu za su auri macen da suke matukar so, amma ita a bangarenta zatayi amfani dasu ne don biyan bukatar kanta.
Ya tafi ya bar Safiyyah a falon da himilin kayan abincinta cikin dumbin takaicinsa, da mamakin wannan abu, kamar wani mai fama da shafar jinnu, lokaci daya duk ya hautsine mata ya canza kala kamar hawainiya.
** **

A cikin jirgin ‘Max Air’ da zai kai Haroun Maiduguri inda daga nan zai wuce Yobe a mota, ba abinda Haroun yakeyi sai sake rereading da comprehending sakon Zayyan ga Safiyyah yake a zuciyarsa, ya yarda dari bisa dari babu karya ko daya cikin kalaman Zayyan Bello, cewa Safiyyah na son yin amfani da shi don ta yi auren ramuwar gayya ta huce haushinsa shi tsohon mijinta.
Matsayinsa kuma na dan Adam mai daraja, wanda ya san ciwon kansa da kimar kansa, duk da yake alamajirin gidansu, to darajarsa ta wuce haka. Zuciyarsa is pure akan kowa, don haka matsayin ta ya wuce mace tayi masa wasa da ita don biyan bukatarta.
Zayyan ba zai yi karya ba, ai tun farko ya kamata ya gane cewa Safiyyah ta fi karfinsa, bazata taba sonshi ba. Ta inama zai kwatanta kansa da mijinta a komai banda ya yardarwa kansa cewa shima namiji ne kamarsa? Kowa ma ya shaida Zayyan kadai Safiyyah take yiwa so na hakika, bacin rai ne ya kaita ga zabensa.
Shi kam ai a rashin uwa ne za a yi uwar daki da shi. Hakika SO yaso ya rufe masa ido da farko, ta yadda ya yaudari kansa kan Safiyyah zata iya aurensa, gara da Allah ya sa Zayyan ya farkar da shi daga mafarkinsa.
Self-esteem dinsa na ce dashi ya barsu yadda ya gansu su koma aurensu wato, better he maintains the status quo. In ya yi hakan, ba jihadi kadai ya yi ba, ya ceci kansa daga nadamar da ba za ta yi amfani ba, ya gama yarda da kalaman Zayyan da yace,
“Safiyyah ba za ta iya taba bashi farin ciki ba”.
Canzawarta dinnan na daga jiya zuwa yau pretending ne kawai irin na munafurcin mata. Shi kuma ya san shi mutum ne mai tsananin kishi da ya wuce ka’ida. Don haka bai san me zai faru ba idan ya auri Safiyyah Zayyan ya ci gaba da turo mata sakonni irin wadannan, yana kiranta ‘alter-ego’ dinsa.
Zai iya kisa a kan kishi, shi ya sa tunda ta auri Zayyan bai ko kara daga ido ya kalleta ba, bai kara kulata ba, koda da kalaman fatar baki ne.
Duk da cewa ita ba ta san ma halin da yake ciki ba, maganin kada a yi kawai kada a soma. Domin da muguwar rawa hausawa suka ce gwamma kin tashi (in ji Haroun).

Da wannan tunanin Haroun ya canza niyyarsa ta shiga Geidam, bayan ya isa Maiduguri kawai sai ya juya ya kamo hanyar Dandume.
** **
Tun isowar Haroun Dandume suka kule a dakin soro shida Malam.
Allah kadai ya san me Haroun ya gaya wa Malam, ko Ammi bai bari ta ji komai ba.
Malam ya ce, “Haroun, Haroun, Haroun, sau nawa na ambaci sunanka?” Haroun yace “sau uku Allah Gafarta Malam” Malam din yace to Allah ya yi maka albarka sau uku, ya baka hajji da umara sau uku, ya raya maka ‘ya’yanka guda uku.
Domin ka zo gabana ne da wani abin dake raina, sabida wallahi nima kaina na san akwai fushi da son huce haushi cikin hukuncin Nana Safiyyah, da na mahaifiyarta. Kuma ni ma zan fi so a ce Ayatullah ta tashi a tsakaninsu su biyu. Tunda farkon rayuwarta basu yi shi tare ba. Allah ya yi maka albarka Haroun, ka ji? Ina rokon ka bar wannan maganar a tsakaninmu ko Amminta kada ka bari ta ji ta.
A take Malam ya kira Baba Murtala, me suka ce? Me suka ce, oho! Sai kawai naga Baba Murtala ya daga hannu ya hau jero hamdala da godiya ga Ubangiji, ya ce insha Allahu yana tafe gobe, lokacin da aka sa na daurin auren da Haroun ba za a canza ba, in sha Allahu.

“Shekara biyu da bana nan wani abu ya ragu a jikinka?
Ko ka kasa rayuwa da matarka da danka? Ina ruwanka dani da Aayah ai ‘ya ta ce”
Zayyan yayi maza yace, “Say it loudlyin dai hakn zai sa ranki yayi dadi, Aayah inda adalci taki ce, amma fa ba ke kadai kika haifeta ba, banida guts din yi miki gadara a kanta, amma in reality ‘ya ta ce da bazaki taba canza mata uba ba sai uban daki.
Yes, you are right, Safiyyah na yarda na rayu da wasu iyalin daban bayan wucewarki da kafin wucewarki, amma ki sani a kan komai akwai exceptionality, extraordinariness, exquisiteness and perfection a gun namiji mai soyayyah ta gaskiya irina ni Zayyan.
Idan na ce miki ban kara sha’awar jima’i ba daga ranar da kika sa kafa kika bar gidana nasan bazaki taba yarda ba, har na soma tunanin koma kin tafi tare da mazantakata ne? Sai ko idan na shafo na ji ta tana nan”

Maganar ta baiwa Safiyyah matukar kunya sosai, saida ta runtse idonta ta kalmashe wuyanta tana sunne kai. Zayyan bai damu ba ai halin Safiyyah ne kunya bazai taba barinta ba, shima fa yana son kunyar nan kawai akwai inda baya bukatarta ne, ya cigaba da maganarsa.
“ban ji ni a Zayyan dina ba sai a daren jiya, da aka yi min albishir mafi girma da sanya kwanciyar rai a zuciya”.
Ya kama yatsun hannun Sophie ya kai bakinsa ya wani irin sumbata, deep, cool, calm kiss, da sauri Sophie ta janye hannunta, amma ba karamin dafi sumbar ta zuba a gangar jikinta ba, ta soma kokarin mikewa don ta canza kujera saboda Zayyan ya fara zarce ka’ida, amma da hanzari Zayyan ya mayar da ita inda ta mike ya kwantar da kai a masangalin wuyanta, ya rufe idanunsa yana sumbatar kasan wuyanta in a soothing manner, a cikin dabara ba tareda Safiyyah ta ankara ba bakidaya Zayyan ya kanainaye ta ya janyota ya kalmasheta cikin jikinsa. Suka koma shaqar turaren juna cikin susucewa da tsren numfashi.

“Sophie you know you are my alter ego ko?!”
Ba ta amsa ba, sai ajiyar zuciya take yi, domin jikinta ya fara daukar sakon gaggawa da Zayyan yake ta faman aika mata ta hanyar sumba a tsanake, sumba irin mai tsayi da zurfi a kasan dogon wuyanta, cikin kalamansa na soyayyar da ya saba wadanda bata iya escaping tasirinsu, domin kullum sababbi yake shirya mata cikin kunnenta ita kadai ranta kamar wanda ake yiwa wahayinsu, hannayensa biyu baibaye da jikinta suna shafar duk inda yake son shafowa a tsanake, with passion and emotion, kewa kamar ta kashe shi, shekara biyu ba kwana biyu ba gabadaya Zayyan ya kunna Safiyyarsa, ya tado mata nata soyayyar, by mistake ta ruko hannunsa cike da jin tsoron al’amarin dake faruwa dasu yau tamkar magic, ta ce, “Z-Zayyaaan”. Tana kokarin janye jikinta amma ta kasa, yaki bata damar hakan sannan bata da karfin tureshi, girman da kwarin kashin ba daya ba.
Dalilin da yasa kenan har Zayyan yayi nasarar kwantar da ita akan doguwar three seater, ya lullubeta da fadin kirjinsa ya rungumeta tsaf, fuskarshi da lallausar gargasar nan ta sajen gefen fuskarsa suna shafar kasan gashin kanta mai yalwa, santsi da cika, jikinsa na vibrating, muryarsa na trembling yake cewa.
“Sophie I missed you…..!”.
Sai bata iya ture shi ba ko kadan, ta saki jikinta gabadaya cikin nasa, yau jinsa yake at the zenith of his thirties! Kamar yau ya taba kai hannu da zuciyarsa jikin Safiyyah! Kalaman soyayya gangariya haka Zayyan ya yi ta zubawa Sophie cikin kunnenta yana kara wanke kansa ta hanyar narkar da duk wani burbushin bacin ranta da unavoidable soyayyarsa. Sai ga hawaye na gangarowa ta gefen idon Safiyyah…..
Tana iya kokarinta na ture shi, don ta tashi zaune, Zayyan na sake mannewa a jikinta kamar tsohon tuzuru, ita kam Safiyyah kokari take ta samu ya cikata saboda gabadaya ya hautsine ya birkice mata kamar ranar first night dinsu a Zaria. Fatanta su rabu lafiya, kada ayi abun kunya karo na biyu a turakar Malam, Malam baya mantuwa, ganin yaki sakinta sai kawai ta saka masa kuka mai sauti tana cewa.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *