Chapter 17: Chapter 17
THE SECOND MIGHTY NIGHT
A wannan daren abubuwa masu dimbin yawa sun kasance tareda masoyan. Shi Zayyan ya san rayuwarsa tana zama mai ma’ana ne kadai idan akwai Sophie a gefensa. Contentment na zuciyarsa yana samuwa ne kadai idan ya bude ido ya ga Sophie a kwance a gefensa, tana masa magana cikin in’inarta, wadda ta fi komai dadin sauraro a kunnensa, da saka shi ishadi, sannan tana saka wani irin sanyi da sa’idah a zuciyarsa.
“Farin ciki yana dauwama a gidannan, kwanciyar hankali da ci gaban rayuwata duk suna da kyakkyawar alaka da rayuwa tare dake Sophie, kinsan cewa you are my Alter ego ko?!”
Zancen zuci ya ke bai san cewa a fili yake yi ba, kuma sambatun nasa duka yana shiga kunnen Safiyyah da ke kwance lummm! A saman kirjinsa a lokacin. Idanunta a rufe ruf, sai ka rantse barci take yi, amma a zahiri ba barcin take ba, amsar bulalar da kalaman soyayyahr Zayyan keyi mata take yi a cikin duukan ilahirin jikinta.
Wannan yana faruwa ne bayan shigarsu gidansu na Sunset Estate, No. 1 RafinDadi Close. A daren ranar dawowar Sophie gidanta.
Estate din data yiwa kanta zanen bangarenta da kanta, ta kuma zana ‘terrace’ dinta na cikinsa da kanta, yau gashi duk sun dawo gare ta, bayan haye jarrabawar rayuwa kala-kala. Zayyan ya maida komai na gidanta sabo, babban abinda yafi burgeta shine bangaren wasan Aayah dakinta.
Zayyan ya ga sauyi sosai a tare da Sophie, duk da ba wai ta bar kunyarta din bane gaba daya, amma hakika Sophie ta samu ilmin zamantakewar aure fiye da baya adalilin zama dasu Assafe.
Ta samu karin wayewar kai dai-dai misali, ta tsaya ta ingantawa Zayyan daren yau fiye da kintacen mai karatu.
Har ta kai ta kawo Zayyan na tambayar kansa ko dai kwas (course) ya kai Sophie na shekaru biyu yanzu ta gama ta dawo gidansa?
Duk da haka, shi ya san Safiyyah har abada za ta ci gaba da zama decent dinta, wannan tarbiyyarta ce kuma nature dinta ne, amma ta basu dama sun yi hijira yau na dan wani lokaci saboda son ta faranta masa, a daren yau ta bashi dukkan soyayyarta da kulawarta da agajinta 100% yadda ya dade yana so, har sai da hakan ya sa shi kwallar farin ciki, ya kuma gode wa Yaya Sheikh da Assafe sau ba adadi don ya tabbata sun gane matsalarshi da Sophie, sun kuma yi aiki tukuru a kan maganceta.
Fatan dai Allah ya yi musu sakayya da babban rabo a duniya da lahira, ya basu ‘ya’ya masu albarka suma, sune ‘real defination’ na zumunci da ‘yan uwantaka. Ita kuma Assafe ita ce mace tagari da kowanne miji zai so samu, wato matar da za ta rungume kowa nasa da zuciya daya babu kissar munafunci, ba keta ba mugunta ba zagon kasa ko ganin ido.
Daren bakidayansa daren farin ciki ne a gare su, suna fatan dauwama a cikin irinsa har karshen rayuwarsu da yardar Ubangiji.
** **
Da safe Azumi mai aikin Azeezah ta yi wa Azeezah waya wadda har lokacin take gidan Anti Salma, ta ce, “Anti, matar gidan nan fa ta dawo jiya, a gidannan ta kwana. Baban Shaheed din ma ya dawo, tare suka shigo”.
Azeezah ta ce cikin faduwar gaba.
“Wace matar gidan?”
Ta ce, “Hajiya Uwargidan nan”.
Duk da Azeezah bata da case da zaman Safiyyah a gidan Zayyan, kusan ma tana ganin dawowarta ya fiye mata amfani, amma hakika taji kishi mai tsanani, kishi gaskiya ne a zuciyar kowacce diya mace.
Nan take wani tunani ya zo mata, wato sai ta karasa cika kudirinta na cire mahaifa, musamman tunda ya dawo da rabin ransa, tunda an ce ita yanzu tana haihuwa, in ya so ita tayi ta haifa masa.
Dama a rashin tata haihuwar ne ai ya aureta ya takura mata haihuwa.
Abinda zata yi shi ne canza asibiti, tunda wancan dan iskan likitan ya zubar mata da mutunci a idon Zayyan, tun lokacin ya ce ta je gida sai ya neme ta.
Tunda Azeezah ta san ba ta isa ta tunkari gidansu gaban iyayenta ba, tace musu Zayyan ya koro ta, karshenta Baba kiransa zai yi yabi diddigin korar allura ta zo ta tono garma.
Sai kawai ta taho gidan Anti Salma, ta ce mata za ta yi sati biyu ne, Zayyan yayi tafiya tana jin tsoron zaman gidan daga ita sai Azumi, don ita kanta Anti Salma ta fara ganewa halin Azeezah sai ita, bata so ta dinga bata mafaka yanzu a gidanta, don in ta zo ba zama take waje daya ba, sai yawo da mota a cikin gari da hanging-out da kawaye kamar wadda taci kafar kare don yawo.
Azeezah ta yi wa Anti Salma sallama ta ce za ta je asibiti, ta tambaye ta ciwon me ta ke? Ta ce check up za ta je a sabon asibitin data bude file.
Azeezah ta figi motarta ta fice tun safe har yamma shiru, Anti Salma bata ganta ba, duk ta shiga damuwa. Ta gaya wa kanta ko me Azeezah ta rakito a kanta zai kare, don Baba Murtala baya da wasa a kan lamarin iyalinsa. In the first place cewa zai yi don me zata bari ta dinga kwana a gidanta? Idan mijinta tafiya yayi wannan ba hujjabace ta baro gidan aurenta. Ba zaman aure ta ke yi irin na sauran mata ba?
Kuma dai ta san Azeezah sarai ba ta jin magana, don ma dai ubanta tsayayye ne a kanta da sai tafi haka giggiwa da kangarewa.
To an yi sa’a uban na taka mata birki a lokuta da yawa, yana daidaita mata sahu. Kuma dari bisa dari tana shakkarsa.
Anti Salma ta ce, bari dai ta kira Zayyan din, ta tabbatar in ba karya ma Azeezah ta ke ba, don yau ta doshi sati biyu a gidanta ko sau daya ba ta ji su suna waya da juna ita da Zayyan din ba, kuma wane irin check-up ne tun safe har yamma, duk da ta saba fita, amma ta rasa me ya sa dadewarta na yau ya dame ta, musamman data ce, asibiti za ta je.
Ga Shaheed ta bari a gida sai kuka yake yana kiran Abbansa zai je, don tun jiya Azumi ta je can gidansu dauko musu wasu kaya bata dawo ba kuma, shikuma ba wai ya saba da Anti Salma bane.
Kawai sai Anti Salma ta dau waya, ta doka wa Zayyan, da kyar ya iya daga wayar don a lokacin yana makale da Sophie yana mata matsar jiki bayan kare lafiyayyiyar soyayya. Yana dauka suka gaisa da Anti Salma, ta ce.
“Zayyan ka dawo ne?”
Ya ce, “Daga ina Anti?”
Ta ce, “Azeezah ta ce min baka Nigeria”.
Ya ce, “Ni din? To ina wace kasa?”
Tayi ajiyar zuciya itama tana jin faduwar gaba ta ce, “Haka dai ta ce min, yau satinsu biyu a gidana”.
Ya ce, “Umh! Ba ta je Lagos din dana ce ta je ba kenan, ta fake a gidanki? Anti Allah ya shiryi Azeezah kawai…”.
Anti Salma ta shiga damuwa, ta ce, “Lagos ka ce ta je? To me ya faru?”
Ya ce, “Tsakaninmu ne wannan Anti”.
Anti Salma ta nisa kafin ta ce, “Zayyan, na san kana hakuri da diyata, ina rokonka ka kara a kan naka.
Yanzu ma abinda yasa na kira ka shi ne, saboda yau hankalina ya ki kwanciya da fitarta asibiti tun safe… ta ce min check up zata, amma har yanzu shiru, kuma in na kira wayarta bata shiga sam, I’m afraid ko wani abu ne ya faru da ita a asibitin ko a hanya, ga Shaheed data bari tun safe yake kuka ya ki cin komai dana bashi.
Ita kuma Azumin tun jiya ban ganta ba, daga cewa ta je can gidanku ta dauko mata wasu kaya taje tayi zamanta nikuma bai saba dani ba”.
Al’amarin Azeezah yanzu ya daina dagawa Zayyan hankali, don ya san komai ma ya same ta ita take kai kanta, amma iyalinsa ce, uwar yaronsa, kuma bai kyauta wa Baba Murtala ba idan ya yi biris da al’amarinta, ashe bata je ma Lagos din ba da ya ce ta tafi sai ya neme ta ba, nufinsa da ma in ta je ya san dole Baba zai kira shi, a yi mata fada a kan halakar da ta kusa jefa
kanta. Amma daga baya ya baiwa kansa laifin hakan, tunda ya san ga yadda Azeezah take amma bashi da nutsuwar bata hakkinta har ya kure hakurinta ta kusa aikata haramci.
To ashe ba ta je bama, tana cikin Abuja tun lokacin.
Yanzu ma in ya kyale ta bai kyautawa iyayenta ba. Ya ce a ransa bari ya je ya dawo da ita dakinta, ko alfarmar gyara rayuwarsa da samar masa da farin ciki da Baba Murtala ya yi, amma ba don yana da bukatar Azeezah yanzu a rayuwarsa ba.
Ya nisa kafin ya tambayi Anti Salma wane asibiti ta tafi? Ta gaya masa sabon asibitin data bude file. Wai check up zata je ayi mata”.
Sai da gabansa ya fadi da ya tuno abinda ya faru zuwanta asibiti na karshe da wancan arnen, wanda shi ya sa Azeezah karasa ficewa fit! Daga zuciyarsa.
Dole ya yi excusing Sophie, ransa a bace, yasa kaya a jikinsa ya dau mukullin mota ya fita.
Kai tsaye asibitin ya nufa, kuma bangaren mata, don jikinsa ya gama bashi, a kan wancan kudirin nata ta dawo bata hakura ba, duk da tsallake rijiya da bayan data yi, zuwansa ya cece ta daga aikata zina.
Ya kara sarewa da lamarin Azeezah ne da aka tabbatar masa yanzu aka fito da ita daga dakin tiyata. Tana dakin hutu.
Wannan bayanin ya fito daga bakin Azumi da ya tarar tare da ita a gynaec ward, don haka ya nemi ganin likitan da ya yi mata aikin, ya ce a matsayinsa na mijinta yana son sanin aikin me aka yi wa matarsa babu saka hannunsa?
Likita ya ce an gaya mata duka implications na cire mahaifa, kuma duk da haka ta yarda ta sa hannu ta ce a cire mata. Su kuma yanzu likitaci sunyi sharadin cewa mahaifa ta mace ce, suna cire ta ne bisa bukatar mace ba lallai sai da izinin mijinta ba. Amma suna fada mata implications din hakan kafin a cire, kuma tace taji ta gani.
Don haka an cire mata mahaifa bisa bukatar radin kanta, tunda tata ce.
Zayyan ya zauna jabar! A gaban gadon da Azeezah ke kwance yana jiran farfadowarta, ihu ne kawai bai yi ba don bacin rai. Ya tabbata Azeezah tafi karfinsa, idan kamun da yayi mata a wancan asibitin ana neman keta mata haddi, bai sa taji tsoro ta yi hankali ta hakura da batun cire mahaifa ba, baya jin akwai sauran mutuncinsa a idon Azeezah da in yasa kara yace kada ta tsallaka zata saurareshi.
Ya yi ma Sophie waya ya ce mata kada ta jira shi, yana attending wani emergency case na Azeezah a asibiti.
Safiyyah ta ce,
“Hope lafiya dai ko?”
Ya ce, “Da sauki dai, amma komai dare zan dawo gida insha Allahu”.
Sai wajejen magriba allurar tafi da ranka ta saki Azeezah. Tana bude ido a hankali har idonta ya washe ta yi tozali da mijinta Arch. Zayyan Bello a gefenta. Kafin ta dawo hayyacinta ta tuno abinda ta aikata, sannan likitoci suka zo suka duba ta suka tabbatar ba wata matsala bayan an cire din.
Ya ce suna iya tafiya yanzu? Suka ce a’a sai bayan kwana uku.
Azeezah duk ta gama tsoracewa don bata so ya sani ba, ko daga yadda kalar idanun Zayyan suka koma ta san ya san komai.
Haka ya koma wurin Sophie cikin dare. Ba tareda yacewa Azeezah komai ba.
Safiyyah ta ga Zayyan cikin matsananciyar damuwa, ba ta tambaye shi ba, shima kuma bai bude baki ya gaya mata ba, ya gama yankewa zuciyarsa shawarar da yake ganin tafi masa amfani wato sakin Azeezah da an sallamota, Safiyyah ta fahimci shi da Azeezah ne, amma Zayyan haka ya zubar dakomai dake ransa, ya nemi Sophie ta tallafe shi, ko ya samu sauki daga tension da bakin cikin da bacin ran da yake ciki akan abinda Azeezah tayi.
Haka Safiyyah ta dage ta zage ta cire kailula, ta inganta masa daren kamar ba gobe. Har ma fiye da zatonsa, don yau komai a hannunta yake, itace wuka ita ce nama, ma’ana sai yadda ta ga dama take kuma so haka take juya ragamar Zayyan da zuciyarsa.
Kwanan Azeezah uku da cire mata mahaifa, sannan aka sallame ta.
Tun daren jiya ya dauke Shaheed ya kaima Safiyyah. Daga asibitin ya duko Azeezah a gaban motarsa kamar gaske, Azeezah ta dauka gida zasu wuce, iyakaci yayi masifarsa ya gaji ya kyale ta, amma dai ta yi abinda ya fi mata kwanciyar hankali, kuma wanda zai fishsheta, da dai ta dinga haifo abnormal yara masu Cerebral Palsy tana jin tsoron daukarsu. Tun can asali kuma ita din ba mai son tara yara bace, kuma ai ta gaya masa tun farkon fari, yabi ya kalallameta, ai ya san hakan tun kafin ya aure ta wannan ba sabon magana bane a wurinta.
Amma sai kawai ta Zayyan yayi kwana ya nufi filin jirgi da ita, kuma ya ki magantuwa tun tahowarsu sai tuki yake cikin nutsuwa da hailala a zuciyarsa don rage bacin rai. Har suka shiga filin jirgin saman Nnmadi Azikiwe International Airport. Ya yankar musu tikitin tafiya Lagos tare.
Ta so ya saka ta a jirgi ita kadai, amma bai yi hakan ba kamar ya san niyyarta kuma haka yasa ta a gaba hannunsa cikin nata har gaban Baba Murtala.
“Baba na kawo Azeezah yau ne gabanka don ka shaida tafi karfina Baba. Azeezah ta je ta cire mahaifarta, bada sani da yardata ba. Saboda kawai ba ta son haihuwa dani, kamar jinina ne ya bata haihuwar da mara lafiya.
Yaronta Shaheed ku shaida na kaiwa Sophie rikonshi daga yau, na san ita bata kyamar hada zuri’a da ni Baba, ko da kuturu zata haifar min, I’m sure Baba zata shayar dashi da nononta ba za ta bari yunwa ta kashe shi ba, ba ‘cerebral palsy’ ba ko menene.
Ka shaida Baba Azeezah ta fi karfina daga yau, kuma wallahi bata so na. Ta aure ni ne kawai don in zama injin biyan bukatar gangar jikinta…”.
Tsabar bacin rai Zayyan yama manta ko dawa yake magana, abinda ke binne a kasan ransa kawai yake amayowa Baban cikin haki da huci na bacin rai.
Baba Murtala ya ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, cire mahaifa fa ka ce?”
Azeezah sai barin jiki ta ke. Tana mazari, jikinta na zikiri.
Baba Murtala ya ce, Zayyan tashi ka je gida ka nutsu ka ji? Na baka sati daya ka yanke wa kanka shawara a kan zama da Azeezah ko rabuwa da ita.
Kada ka yi la’akari da ni, kada ka danganta rayuwarka da ni. Na sani Azeezah ‘yata ce amma wallahi na haife ta ne amma ban haifi halinta ba, ko wani Da cikin ‘ya’yana mai irin halinta babu. Ka tashi ka je, ka yi shawara da zuciyarka ni babanku ne ku duka, ba Azeezah kadai na haifa ba har da kai. Kuma ban taba yi maka wani abu saboda Azeezah ba sai saboda dan uwana marigayi Bello Rafindadi.
Don haka kada ka yi amfani da ni ka tauyi farin cikinka, da kwanciyar hankalinka… Yarinyar nan iblishiya ce”.
Duk da ya baro Azeezah a Lagos tareda iyayenta Baba ya zaneta ciki da bai da wayar cajarsa, ya dawo Abuja, amma ya kasa yankewa kansa hukuncin komai a kanta, a kan zabin da Baba Murtala ya bashi na cigaba da zama da ita ko a’ah?
A kasan ransa yafi son ya sahale mata.
Sosai Safiyyah ke kula da Shaheed ba ta barshi a hannun Azumi ba, tun tafiyar Zayyan da Azeezah Lagos har bayan dawowarsa. Bai gaya mata komai da ke faruwa tsakaninsa da Azeezah ba, amma tana ji rannan yana waya da Habibu Nahuce.
A cikin hirarsu yake ce masa Safiyyah ta dawo, kuma yana jin zamansa da Azeezah yazo karshe, don Baba Murtala da kansa ya bashi zabi, na ci gaba da zama da ita ko a’ah, ba tareda hakan ya shafi alaqar su ba, nan da kwana uku zai koma ya gaya masa abinda ya yanke. Shi gaskiya sahale mata zai yi.
Safiyyah ba ta dai ji me Habibun Nahuce ya ce masa ba, wanda shi kadai ta sani a matsayin aboki na jiki ga mijinta Zayyan Bello.
Don haka Safiyyah ta shiga tunanin ta yaya zata taimaka gabanin Zayyan ya yanke hukunci a kan Azeezah?
Ta dandana rayuwar saki, data zawarci wato ta zaman gida, banda ita Allah ya bata iyaye nagari bata yiwa kowacce mace fatanta.
Amma bai kamata a duba halin Azeezah ba, duk da haka bata kyautawa kanta ba kuma kanta kadai ta cuta ba wani ba, Sophie na ganin a komai a duba dattijon Babannan nata, jarabta ce Allah yayi masa da Azeezah a matsayin ‘yarsa ba gadon gidansu tayi ba, shi kansa Zayyan din ta san abinda yake dubawar kenan da yasa ya zauna cikin damuwa kwana da kwanaki bai kaiwa Baba takardar sakin Azeezah ba.
Ba ta yi masa magana ba, tunda shi ma bai ce mata komai a kan laifin da Azeezah ta yi masa ba. Malam ta kira cikin sirri, ta gaishe shi, farin cikinsa da jin muryarta ya ki boyuwa, ya ce ai dazun nan muka yi waya da amaryata (Aayah) tana can tana tsalle-tsallenta ta manta da ke”.
Ta yi murmushi ta ce, “A gaya mata ni ma ai na yi sabon Da kyakkyawa, Yayanta (Shaheed) tuni na manta da ita”.
Malam ya yi dariya. Sannan ta kwashe abinda ta fahimta a kan Azeezah da Zayyan, cewa suna cikin matsala, wai har yana tunanin sakinta cikin kwana uku masu zuwa, ta ce ita bai gaya mata me ya hada su ba, amma ya kawo mata Shaheed, ya ce dama can danta ne da ya yi mata alkawari, to gashi ya cika ya ba ta.
Ta ce, “Malam kada ka barshi ya yi sakin nan, kada ya zama dawowata ce ta kashe nata auren, duk da matsalarsu bata shafeni ba”.
Malam ya ce, “Subhanallah! Bar ni da shi. Zan kira shi yanzunnan”.
Kwanan Azeezah biyar a gidan iyayenta suna gasa mata gyada a hannu, don wannan karon har Hajiya Nana bata bi bayan Azeezah ba, ta dinga loda mata wanke wanke da shara da duka ayyukan gidan tace in ta kashe aurenta haka zata maida ita ‘yar aikin gida, ta ce, kanki kika cuta wallahi da kikayi tunanin cire mahaifarki daga haihuwa daya.
Shi namiji ne zai auri hudunki ya haifi yara dari in yana so, ni dai Azeezah na rasa irinki, ba ki yi halina ba, bakiyi na Babanki ba, baki yi na ‘yan uwanki ba, halinki naki ne ke kadai.
Ko ina hauka ba zan cire mahaifata ba, saboda rudin duniya. To gaki ga duniyar nan ki ci ta da tsinke. Ba baki nake miki ba.
Shashasha kawai, Allah ya dube ki ya ba ki miji dan albarka mai sanin darajar iyayenki, ya aureki duk da halinki da aka gaya masa ya zauna dake ba don halinki ba, wanda tun farko an gaya masa tun asali baki da hali mai kyau, amma ya ce ya ji ya gani yana sonki haka.
Yana ta hakuri da ke, amma sai da kika kawo shi bango, ya tattaro ki ya dawo mana dake gida duk girman mahaifinki dake idonsa.
Shikenan ai sai kiyi ta zama ga kafadata ga taki, tunda haka ki ke so”.
Baba Murtala ya ce,
“A ina? Ai muddin Zayyan ya yanke shawarar hakura da auren Azeezah, Hajiya Nana ki zama shaida ba ni ba ita, na sallama wa duniya ita, kuma sai ta bar min gidana”.
Azeezah ta rushe da kuka tana cewa, “Baba na tuba na tuba, na bi Allah na bi ka!”.
Baba Murtala ya wuce bai tsaya ba, karo na farko da zai iya cewa Azeezah ta yi laifi, an mata fada, kuma ta ce wai ta tuba. A baya sai dai ta yi fumfurus, ko ta bada amsar duk da ta zo bakinta.
A daren Malam ya kira Zayyan suka gaisa a mutunce, gaisuwar uba da Da, Malam yace da shi, “a matsayina na uba gareka Zayyan, in har ka yarda ni din uba nake a gareka, to ko me Azeezah ta yi maka, in dai ba shirka bane, ba kuma auren ya haramta bane kwatakwata, ka je gobe-goben nan inda ka kaita ka dawo da ita bisa umarnina.
Haba Zayyan! Ai ana barin halas don kunya, mu rama alkhairi da alkhairi, ka yi hakuri ta ci darajar karimin mahaifinta har abada ka ji? Ko me ta yi bi ta kansa ka wuce, ka yafe mata ka dawo da ita dakinta, darajar Alhaji Murtala”.
Zayyan ya bi maganar Malam, ba don ransa na so ba, a rana ta bakwai da Baba Murtala ya deba masa ya kira Baba Murtala a waya tun da safe, shikansa Zayyan muryar Baba Murtala yau ta bashi tausayi, da alama cike yake da fargaba, in Zayyan ya gaji ya saki Azeezah wa zai iya? Wa zai likawa wannan fitinanniyar? Yace “Zayyan me ka yanke? Na roke ka Allah da manzonsa kada ka kwari kanka a kaina” Zayyan ya rintse ido cikin tausayin dattijon, yace “ai Baba na yafe laifin da Azeezah ta yi min, saidai wanda ke tsakaninta da ubangijinta, zan yi tafiya yanzun wadda zata dauke ni wata guda, amma idan Allah yayimin dawowa lafiya zan zo in dawo da ita”.
Ya ce, “komai ya wuce in sha Allah Baba, Azeezah kanta tayiwa bata yiwa kowa asara cikinmu ba”.
Baba Murtala ya ce, “Are you sure, har zuciyarka duk da halayenta zaka iya ci gaba da zama da ita?”
Zayyan ya ce, “Insha Allah Baba, amma a ja mata kunne sosai kafin dawowata, bazan kara daukar yawon da take a gari da asibitoci da ‘hang out’ da kawaye ba”.
Yau da wuri Zayyan ya dawo gida, kawai ya tattara Shaheed da kayansa ya kaiwa Azumi sassan Azeezah, ya ce ta kula da shi sosai, za su yi dan balaguro mara nisa.
Sophie ta fito daga wanka kenan a daren ranar ta tarar Zayyan na shirya musu kaya a trollies biyu, ta ce, “Habiby sai ka daukemin yaro ba ka gaya min ba? Ina ka kaishi?”
Ya ce, “can inda ya budi ido, shida uwarsa sun hana ni cin amarci yadda ya kamata, matsalar yau daban ta gobe daban Allah na gaji, hutu kawai nake bukata da Habibiyata”, ya kanne mata ido daya yana cewa “ko ya kika gani my co-architect? My alter ego, my everlasting sweetheart”.
Yace “Ki shirya gobe da safe za mu yi balaguro”.
Ya fada yana rungumo ta jikinsa daga tsayen da take, bayan ta zauna a cinyarsa tana sharce kanta, wata matsiyaciyar sumba ya kai mata a kasan wuyanta har saida ya bata kunya ya kuma tada tsigar jikinta.
Sophie na son tambayarsa ina za su je? Ya ce, “ai sai inda mai ya kare. A kudu da yamma gabas da arewacin Najeriya”.
Daga nan kuma labari ya sauya, ya shiga sukurkutata da lafiyayyar soyayyah……



