Chapter 18: Chapter 18
Da safe ya zagayo ta bayanta ya kara mata wata ‘yar takarda a idonta mai dauke da list na wurare goma mafiya kyau da shahara da zuwa honeymoon in Nigeria, list din ya hada wuraren ziyarar masoya a kasar Nigeria tun daga kan
Sencillo, ta jihar Lagos,
La Manga Luxury Villa,
Epe Resort and SPA,
Inagbe Grand Resort and Leisure, Obudu Mountain Calabar,
Yankari Game Reserve, Bauchi, The Whisphering palms, Badagry, La Compagne, Tropicana.
Ya ce Sophie ta zabi waje biyu suje don tun aurensu basu taba zuwa ‘shahr al asal’ ba (honeymoon), yana so yanzu su je kona sati hudu ne su huta.
Safiyyah ta ce ita duk cikin wadannan top wuraren da ya kawo a kasar Nigeria, ba inda ta ke son zuwa sai “Gembun su Siyama VOA, wato “Mambilla Plateu”.
Don haka a ranar suka yi kyakkyawan shiri suka dauki hanyar jihar Taraba a mota.
Tafiyar da Sophie ba ta dawo ba, sai da tsarabar dan bafullacen “Gembu”. Wanda tun cikinsa yana wata uku sun amince takwaran Arch. Bello Rafindadi ne zai iso, in sha Allahu.
Kafin dawowar Zayyan da Sophie daga Mambillah Azeezah ta sha horo iri-iri a wurin iyayenta, Baba Murtala kuma ya daina barci bai fuskanci gabas ya roki Allah akan ya shiryi Azeezah ba, ya baiwa mijinta hakurin zama da ita. Addu’ar iyaye tabbas bata faduwa kasa banza Azeezah kafin ta dawo gidan Zayyan ta yi lakwas sosai, don boyi-boyin gida Haj. Nana ta maida ita duk ayyukan gidansu ita ake dorawa ta sallami duka masu aikinta tana sani.
Daga Manbilla suka wuce Lagos suka ga Aayah da a gun su Yaya Sheikh. Aayah ta girma tayi wayau tayi bulbul da ita, kulawa take samu a gun Assafe irin wadda ko uwarta bata yi mata. Shi da kansa Zayyan yaji bazai iya dddauko Aaayah ba sabida tausayin Sheikh da Assafe, yana iya hango damuwarsu da tashin hakalinsu cikin idonsu don sun dauka sun zo ne tafiya da Aayah.
A daren ranar Zayyan da kansa yace ma Sophie a dakin bakin Yaya Sheikh da aka saukesu, bazai tafi da Aayah ba, ya barta har illa masha Allah a gaban Sheikh da Assafe. Yana add’ar Allah ya raya ta, ya basu wasu masu albarka.
RUFEWA
Zaman Sophie da Azeezah wani irin zama ne na ba ruwan wani da wani, amma suna gida daya, karkashin inuwar miji daya.
Amma in sun hadu misali a parking lot in kowacce zata fita suna gaisawa da juna.
Ita kam Azeezah ta san rayuwa ta yi gwatson mage da ita, tun daga lokacin da tayi wancan kuskuren na cire mahaifa, kimarta ta karasa zubewa a idanun Zayyan da yan uwansa.
Yana zaune da Azeezah ne har gobe kuma har gaban abada zaman alfarma, wato alfarmar Baba Murtala. Ya kuma gyara nashi kuskuren duk hakkin ta da ya rataya a wuyansa yanzu yana saukewa albarkacin mahaifinta.
‘Yan uwan Zayyan yayye da kanne sun rungume Safiyyah da sahihiyar kauna, Azeezah kam tana gidan ne, amma tamkar babu ita, don sai ka zo ka wuni ka tafi ba ka san Safiyyah na da kishiya ba.
Safiyyah ta mamaye komai na gidanta da mijinta.
Ta zama tauraruwa a gun danginsa sai abinda ba’a rasa ba irin na harshe da hakori da ‘yan adamtaka. Yayinda Azeezah ta zama koma baya a komai, daga Zayyan har ‘yan uwansa kallon alfarmar Baba Murtala suke yi wa zaman Azeezah a gidansa.
Duniya kenan, rawar ‘yammata, mu taka ta a sannu babu wani abu cikinta da yake tabbatacce. Yau tana hannun ka gobe zata koma hannun wanda ka raina.
Duniya da lahira Zayyan da Sophie sun bar wa Yaya Sheikh da Assafe ‘yarsu ta fari watau “Aayah”, wadanda har zuwa lokacin su Allah bai basu ba. Assafe ta bai wa Sheikh damar kara aure da kanta, amma Sheikh ya ki, ya ce in dai a kan haihuwa ne ba zai yi ba, Aayah ta ishe su.
Don haka Aayatullah ta tashi cikin matsanancin gata da tattali daga kowanne bangare. Ta san Sophie ce Mamanta amma bata damu ba sosai tafi son zama dasu Assafe.
Shekara na zagayowa Sophie ta dire ma Zayyan photocopy din Baba Bello. Babu ja in ja yaro da marigayi Baba Bello yake kama, don haka ranar suna ya ci suna Muhammad Bello Zayyan Rafindadi.
Kafin haihuwar Safiyyah Zayyan ya cika kudirinsa, sun je sun kai Mama an yi mata (artificial leg) shida Sophie a kasar Jamus, wadda da taimakonta Mama ke dingisawa da kafa biyu yanzu. Mama ta koma gidanta wato gidan marigayi Arch. Bello a Rafindadi, ta debo wasu daga ‘yan uwanta biyu daga Rumah suna zaune tare, karkashin kyakkyawar kulawar ‘ya’yanta bakidayansu da mai aikinta Ankudi.
Tun daga kan Muhammad Bello haihuwa ta zame wa Sophie kwanika, wato kafin ta yaye za ka ga ciki ya billo. Akufi-akufi haka take haihuwarsu.
Allah kenan da ba a sa mai wa’adi a kan komai. Har gobe Azeezah na nadamar cire mahaifarta data yi da kuruciyarta, in ta duba yadda Sophie ta cikama Zayyan gida ya yara kyawawa son kowa, gasunan maza da mata ‘yan dugui-dugui gwanin sha’awa, wannan na bin wannan da gudu, hatta dan ta Shaheed nai cika nemanta cikin gidan ba, ita ta koma takashin baya a gidan Arch. Zayyan Bello Rafindadi wanda ala dole yasa ta rage karsashi.
Tsakanin Sophie da yayye da kannen Zayyan bakidaya yanzu sai sam-barka, sai abinda ba’a rasa ba na yan adamtaka, a halin yanzu business ma sukeyi tare itada Yayyen Zayyan wato Zubaidah da Zubaina, Mama kuwa tana nesa, amma basa gajiya da zuwa gaishe ta akai akai, da kai mata duk abinda take bukata, sam Mama bata shiga sabgar Sophie da Zayyan balle kuma wata karan kada miya Azeezah.
Azeezah ta yi sanyi sosai da wasu daga halayenta ganin yadda rayuwa ta sauya mata, miji baya ta tata, ‘yan uwansa basa ta tata, iyayenta basa bayan halinta, ta duba ta ga hatta da Shaheed ya fi son zama cikin kannensa wato ‘ya’yan Sophie bai damu da ita ba sam. Wannan ya sata yin hankali kadan.
A halin da ake ciki yanzu yara shidda Sophie ta haifewa Zayyan. Kafin cikarsu shekaru 20 da aure. Hudu maza biyu mata Aayah da Hafsat mai sunan Ammi.
Zayyan ke nemo wa Sophie projects na zanen gidaje da Estate tana yi daga gida ana biyanta, ba karamin budi rayuwarsu take samu ba, ta ke kuma cigaba da samu. Domin sun fahimci juna sun baiwa manyan matsalolinsu baya, sai ‘yan wadanda ba a rasa ba, wadanda kusan dole ne ko tsakanin harshe da hakori.
A yau da suke bikin cikarsu shekaru ashirin da aure (20th wedding anniversary), a nan falon Sophie aka hada zungureren farin ‘Candle Lit Cake’, yaransu shidda har Shaheed na bakwai zagaye da su don taya su yanka koton cake din mai harafin Z&S. tareda taimakaon hannayen yaran duka aka hure candles din aka yanka cake dinnan mai tsohon tarihi.
Zayyan da ya tashi kawo gift dinsa na ranar, rungumo Sophie yayi a barin damansa yana gaya mata cikin rada a kunnenta.
“I brought to you an XP-Pen Artist 12 pro Drawing Tablet, as our 20th wedding anniversary gift, for your digital drawings My co-architect”. Ina fatan da shi za ki karasa zana mana zanen ‘Ultra-Modern Market’ da zamu yi a cikin Sunset Estate a nan gaba kadan, in sha Allah”.
Cike da farin ciki Safiyyah ta amshi XP-Pen Artist 12 Pro Drawing Tablet din daga Zayyan, data yanko wani katon cake ta danna masa a baki yayi dumu dumu da bakinsa, yaran abin ya basu dariya da nishadi, suka dau tafi da dariya gabadayansu, suna cewa “Mummy kara masa…” shima ya gutsuro katon gaske ya danna mata a nata bakin. Shaheed da Aayah data zo hutu yadda ta saba duk term daga Lagos ke daukarsu hotuna da digital camera din Aayah don tarihi. Safiyyah tace,
“Baban Aayah ka gama min komai da wannan gift din, na dade ina mafarkin mallakarta, and with it, the two ARCHITECTS will keep the ball rolling… in their drawings”.
** **
Recently, Nana Safiyyah ta wallafa littafin labarin soyayyarsu da harshen hausa, wanda ta sakawa suna “KAWAR ZUCIYA” don amfanin matan da suka samu kansu cikin jarrabawar jinkirin samun haihuwa. Ko wadanda basu sameta ba har gobe, Safiyyah na yawan ce da ‘yan uwanta mata masu irin wannan jarrabawar data samu kanta cewa ita haihuwa lokaci ce, idan da rabonta a duniya za’a samu komai daren dadewa.
Idan babu rabonta a duniya akwai kyakkyawan fata na cimma babban rabo a dalilin rashin samunta a lahira, tunda Ubangiji da kansa yace “Yana jin kunyarku (Matan da Allah bai baiwa haihuwa ba)”.
Allah ya kara muku imani.
Sadaukarwa ne ga duk mata masu lalurar rashin haihuwa ko jinkirinta.
Karshen littafin KAWAR ZUCIYA kenan.
Abinda na yi kuskure a ciki Allah ya yafe min shi, alkhairin da ke ciki Allah ya raba mana ladanshi nida ku makaranta bakidaya.
Sumayyah Abdulkadir
Takori
10/03/2025.



