⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 8: Chapter 8

“Akan me? A saboda mu bamu isa mu zaɓa musu mazajen aure ba?”

Abba ya yi maganar a ɗan fusace. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya ce”a’a Abba, kun isa mana, amma kada a yi musu abin da zai ɓata farin cikinsu, ni nawa tunanin kenan”

“To an gode da shawara, amma ba za’a fasa wannan auren ba!”

Daga haka ya juya ya bar parlon kamar zai tashi sama, Girgiza kai Abdusammad ya yi yana tunanin ta inda zai ɓullowa al’amarin, yafi 3mins a tsaye kafin ya sauke numfashi ya fice daga parlon shima.

****
Hajiya ta dinga kallonta sai kuma ta ce”ban gane ba?” tura baki Nana ta yi ta ce”haka Mama ta ce wai Yaya Safwan zan aura, haka ne Hajiya?” Jinjina mata kai ta yi ba tare da ta yi magana ba, Nana ta ɗan kwaɓe fuska ta ce”amma Hajiya me ya sa sai shi zan aura? naga….”

“Bana son sake jin wannan maganar a bakinki kin ji Nana!”

Hajiya ta yi maganar fuska babu wata walwala, numfashi Nana ta sauke sannan ta gyaɗa mata kai. Ta ce”ki je kitchen wajen Rabi ki ce ta baki robar” Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen ɗin, After 2mins ta fito hannunta riƙe da wata farar roba mai ɗauke da dambun nama. Ta dinga kallonsa kafin ta ƙaraso a sanyaye ta ce”Hajiya sai da safe”

“Allah ya tashe mu lafiya”
Hajiya ta bata amsa idanunta na kan Abdusammad, Amin ta ce sannan ta ɗan kalleshi ganin ba ita yake kallo ba ya sa a sanyaye ta ce”uncle sai da safe” Jinjina kansa ya yi ba tare da ya ce komai ba, ita ma kuma bata tsaya jiran amsar tasa ba ta juya ta fice daga parlon. Hajiya Babba ta ɗan yi murmushi mai kama da na takaici kafin ta ce”Abdusammad! Abdusammad! Abdusammad!”

“Na’am Hajiya”

Ya amsa mata still looking at her. Fuskarta babu alamun fara’a ko annuri ta ce”kana son ka ɓata min rai ne daga zuwanka? ko kuma kana son tarwatsan iyali daga dawowarka?”

Numfasawa ya yi kafin ya ce”Allah ya huci zuciyarki Hajiya, amma ba haka nake nufi ba, kawai dai…”

Dakatar dashi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu, ya dinga kallonta bai ce komai ba. Tashi ta yi tana kallonsa ta ce”kai ka yi abin da ka ke ganin shi ne dai dai, ka auri wadda ka ke ganin ita ce dai dai da kai, duk da baka shawarceni ba a matsayina na mahaifiyarka. Amma na yi haƙuri na kau da idona daga kan ka, ba dan ban ji zafin abin da ka yi min ba, ba dan ba’a dinga ƙananun maganganu a cikin gidan nan ba, ba dan zuciyata bata min zafi kullum ba, sai dan nayi hakuri kuma ina jin wata rana zan sauya wannan al’amarin. Saboda haka kada ka zo ka bata min rai da zan ji daman baka dawo ba dan Allah Abdusammad!”

Sunkuyar da kansa ya yi yana jin ransa a dagule dan ko kaɗan baya son ɓacin ranta, ta sauke numfashi sannan ta juya ta shige ciki abinta. Da idanu ya dinga bin ta har ya daina hangota, ya mike jiki a saluɓe ya fice daga parlon shima.

Koda ya shiga gida zaune ya tadda Zahra a parlon tana jiransa, sanye take da wata sleeping dress doguwar riga mara nauyi wadda ta tsaya mata iya gwuiwarta, ta yi parking ɗan gashinta da bashi da yawa a ƙasan ƙeyarta. Sai tashin ƙamshi take gwanin sha’awa, tana ganinsa ta tashi tana murmushi ta ce”sannu da zuwa” jinjina mata kai kawai ya yi sannan ya nufi hanyar upstairs, Zahra ta bishi da kallo ganin har ya haye sai kuma tabi bayansa. Yana shiga ɗakin ta shigo, ta saki handle ɗin ƙofar har sai da ya yi ƙara wadda ta sanya ya juyo ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke idanunsa.

“Lafiya da Abu Noor?”

Bai juyo ba haka kuma bai bata amsa ba, ya zare rigar da ke jikinsa ya nufi toilet. Zama ta yi gefen gado tana tunanin wanda ya sake ɓata masa rai da daren nan, ta dinga jiransa har bayan 20mins sannan ya fito daga toilet ɗin sanye da bathrobe jikinsa sai ɗigar ruwa yake. Gaban dresser ya tsaya ya gyara kansa sannan ya ɗan shafa body lotion ɗin da yake sakawa ya feshe jikinsa da turare nan da nan ɗakin ya ɗauki wani ƙamshi na musamman. Press ya ƙarasa ya buɗe ya dauko pyjames maroon colour ya saka sannan ya juya yana shirin fita daga ɗakin, ganin haka ya sanya ta tashi tana kallonta muryarta na rawa ta ce

“Ina kuma zaka je? Idan wani abun aka yi maka ka sanar dani dan Allah”

Cak ya tsaya amma bai juyo ba, ta ƙarasa wajensa da sauri ta rungumeshi ta baya tana shessheƙar kuka, ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, ya janyo hannunta ya dawo da ita gabansa yana kallonta ganin yanda take kuka yasa ya ɗan juya gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta, dakyar ya iya laɓɓansa da juna kafin ya a sanyaye ya furta

“And what is this?”

Shigewa jikinsa ta yi tana kukan a hankali, ya girgiza kansa sannan ya ɗago fuskarta yana murmushi ya ce”tafi ki kwanta” a shagwaɓe ta ce”a’a ka faɗa min abin da aka yi maka dan Allah” jan kumatunta ta yi yana kallon wani wajen ya ce”idan na faɗa miki akwai abin da zaki iya ne? Uhm..”

Yanda ya yi maganar ya sanya ta yi murmushi ta shiga jan cute beard ɗinsa sannan ta ce”eh mana, I’ll, zan yi faɗa da duk wanda ya taɓa min mijina, I won’t take it likely with that person”

Faɗaɗa fuskarsa ya yi yana sake janta jikinsa ya ce”ko?”

Da sauri ta kalleshi fuska a ɗan kwaɓe ta ce”eh mana, just tell me wane ne”

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce

“Hajiya Babba ce!”

Saurin rufe bakinta ta yi tana girgiza kai, ta sake shi tana murmushi ƙasa-ƙasa, kamo hannunta ya yi ya ce”ina kuma zaki, ki ka ce za ki yi faɗa da koma wane?”

Zaro idanunta ta yi tana faɗin “Allah na tuba, ban san Hajiya Babba ba ce, Allah ka yafeni”

Ta yi maganar tana daga hannunta sama alamar roƙo. Dariyar da bai yi niyya ba ya yi kafin ya ce”ashe? Daman ba za ki iya tsayawa mijin naki ba ko?”

Jan kumatunsa ta yi tana murmushi ta ce”zan iya mana, amma ban da akan Hajiya, in dai akan Hajiya Babba ne to sai dai na kwanta maka”

Janye jikinsa ya yi yana dariya ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin “ina Noor?”

“Ta yi bacci”

Zahra ta bashi amsa tana bin bayansa.

****
Around 11pm tana kwance tsakiyar gadonta ta yi nisa cikin karatun littafin HASKEN CIKIN DUHU wanda Nanameera ta rubuta kira ya shigo wayarta, ɗan tsaki ta yi dan ji take kamar an katse mata jin daɗi, ta kalli numbern sai kuma ta ɗaga ta yi shiru. Daga ɗaya ɓangaren Junaid na zaune tsakiyar parlon da ke apartment ɗinsa idanunsa bisa tv yana kallon game ya ce

“Nana”

Murya can ƙasa ta ce

“Uhm”

“Kin yi bacci ce?”

Girgiza kanta ta yi kamar yana gabanta ta ce

“A’a ban yi, kawai I’m doing something ne”

Junaid ya rage sound ɗin tv jin ana ihu kafin ya ce

“Me ki ke yi da daren nan?”

Kamar ba zata ba shi amsa ba sai kuma ta ce

“Karatun novel nake”

Gyara zamansa ya yi yana faɗin

“Ashe? Wani novel ne haka da har ya hana ki bacci da wuri ke da ki ke kwanciya da wuri Nana?”

Ƙaramin yatsarta ta sanya a baki tana taune farcenta ta ce

“Karatun ne yake min daɗi”

Junaid ya jinjina kansa yana murmushi ya ce”lailai, kina jin daɗin ki, to ki bani labarin littafin”

Murmushi ta yi tana tashi zaune a kan gadon ta ce

“Toh kana ji”

Shiru ta ji ya yi, ta ɗan kwaɓe fuska a shagwaɓe ta ce”ba ka ji ne?”

Yana sake jingina da kujerar da yake kai ya ce”ina jin ki fa”

Murmushi ta yi ta ce”to sunan jarumar Salma, shi kuma jarumin sunansa Zayyad, Yaya Yad me paracetamol, ita ƴar talakawa ce shi kuma ɗan masu kuɗi, yana da girman kai kuma baya ji, sai yake zuwa garinsu a lokacin tana sai da lemo a bakin kasuwa suka fara haɗuwa ya mata rashin mutunci ta masa rashin kunya…”

Ta tsaya tana dariya a hankali. Dariyar shi ma ya yi ya ce”ina jin ki”

“To sai wata rana ya taimaketa wasu sun biyota, shikenan ya kai ta gidansu, ta fara zama yar gayu za’a sakata a makaranta kawai sai aka masa asiri ya haukace, kuma aka ce ita ta haukatashi dan haka tare zasu tafi duk in da zai je, abun tausayi, ta dinga wahala dashi ta samo masa abinci, ta basa kudi, ya daketa ya shaketa a haka har ya samu lafiya. Aka musu aure, kawai! Kawai sai iyayensa suka zo tafiya dashi ya ce wai ya saketa…”

Ta fashe da kuka tana jan numfashi, da sauri Junaid ya ce

“A’a Nana sorry kin ji, bar bada labarin haka kin ji”

Gyaɗa masa kai ta yi tana ci gaba da kukanta, ya kwantar da murya ya ce”nace ki yi shiru ko, ki kwanta sai da safe”

Toh kawai ta ce sannan ta kashe kiran, ta juya ta kwanta tana ci gaba da kukanta har bacci ɓarawo ya saceta.

**** Kusan sati biyu kenan, abubuwa sai kankama suke a cikin estate ɗin, ana ta shirye-shiryen biki wanda za’a yi nan da wata ɗaya da rabi. Duk yanda Abdusammad ya so ya sauya lamarin abun ya ci tura, dan Hajiya Babba ta hana shi magana a kai, dan haka dole ya saka ido kawai ba dan ya so ba. A ɓangaren Sultan kuwa kullum cikin damuwa yake, shi ma tun bayan da Ummi ta ce kar ya yi magana bai tada zancen ba, amma ko kaɗan bai ji wani abu ya ragu a zuciyarsa daga son da yake wa Nana, sai ma wani sabbin abubuwa dake son bijiro masa. Dan yanzu baya iya yini ɗaya bai sakata a idanunsa ba, ko dai su haɗu a Apartment ɗin Hajiya Babba, ko kuma ya je gidansu da sunan gaisar da Abba.

Tana zaune gefen famfon tana wanke inner ɗinta Amrah ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da ƙaramin bucket, zama ta yi gefenta ba tare da ta ce komai ba, ita ma kallonta kawai ta yi sai kuma ta ci gaba da abin da take, ba’a fi 2mins ba Maimoon ta ƙaraso wajen ita ma hannunta riƙe da nata bucket ɗin, ta zauna itama ta zuba uban tagumi, Nana ta ɗan kallesu ganin yanda suka yi sai kuma ta ce”ina Hamida?”

“Mama bata barta ba ina ga”

Cewar Maimoon hannunta tallafe da haɓarta, numfasawa ta yi sai kuma ta ce”to ko muje gidansu ne?” girgiza kai Amrah ta yi ta ce”idan muka je can ba zamu sake ba, that’s why yasa nace mu zo nan ɗin ma” Maimoon ce ta ce”eh nima haka nake tunani, wai yanzu da gaske auren nan za’a yi?” murmushin takaici Nana ta yi kafin ta ce”gashi kuwa, ni yanzu kullum hankalina a tashe yake, ji nake kamar wani abu mara kyau zai faru dani ɗin nan wallahi” tsaki Maimoon ta yi ta ce”ki ci gaba da ɗaukan haka, sai ki ga ya faru”

Kallon Amrah ta dinga yi ganin yanda ta ƙura masa idanu bata ko kiftawa, sam ba kula dasu ba dan haka ya yi shigewarsa. Nana ta janyo hannunta tana faɗin”keee wannan kallon….”

Maganar ta maƙale ganin yanda hawaye ki biyo kan fuskarta kamar an buɗe famfo, suka dinga kallonta da mamaki kafin Maimoon ta yi ƙarfin halin cewa” lafiya dai Amrah?”

Cikin shassheƙar kuka ta ce

“Kowa yana faɗar abin da ke ransa dan yaji daɗi, dan haka nima gara na faɗa ko zan samu sauƙi, wallahi tallahi ban taɓa son Yaya Sultan ba, ban taɓa masa kallon wanda nake so na aura ba, kullum zuciyata da tunanina suna wajensa, kullum fatana ya dawo ƙasar nan a haɗani aure dashi, kullum dashi nake kwana da shi nake tashi, ina sonsa! Ina son sa tun ina ƙarama wallahi!”

With so much confused suke kallonta, Nana ɗan girgiza kanta tana faɗin”ban gane ba? wane? Wa ki ke so?”

Ta jera mata tambayoyin a lokaci ɗaya tana mai da kallonta dan jiran amsar da zata bata. Amrah ta sauke nannauyan numfashi hawaye na sake zubowa fuskarta ta ce

“Uncle Abdusammad mana! Ina son shi, ina ƙaunarsa wallahi, ko mai ya yi birgeni yake, ko faɗa yake kyau yake, ina sonsa! Shi nake so na aura ni! Shi nake so Nana!”

Yan channel ɗina masu quality ❤️ This page na dedicated to guys, na bar muka kayanku, ku yi sama dashi abin ku, Nanameera heart u guys????.

Tuntsirewa da dariya Nana ta yi tana yin baya, ta yi zaman dirshan a wajen, Amrah ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan kuncinta, Maimoon ce ta kalleta ganin how serious she’s ta ɗan taɓa Nana a sanyaye ta ce”me ya sa ki ke dariya ne?” Ba ta ce komai ba sai ci gaba da dariyarta da tayi kama zararriya, suka dinga kallonta baki buɗe. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita tana ƙoƙarin saita nutsuwarta. Sai dai bata san sanda ta sake tuntsirewa da wata dariyar ba da suka haɗa idanu da Amrah, duka Maimoon ta kai mata tana tsaki ta ce”wai ke baki da hankali ne?” girgiza kanta ta dinga yi bayan ta rufe bakinta da hannunta ɗaya gudun kada ta sake dariyar.

“Wai me ki ke wa dariya to?”

Maimoon ta sake tambayarta a dame, gyaran murya ta yi fuskarta a sake ta ce”wai uncle take so, uncle fa, wannan tsohon, ya fa girmi duk ya’yan Hajiya, taɓ subhanallahi…”

Ta sake tuntsirewa da wata dariyar, a fusace Amrah ta mike tsaye tana kallonta rai ɓace ta ce”ke ki ke ganinsa a matsayin tsoho, amma ni bana masa wannan kallon, kuma kin san yafi kowane mutum a gidan nan daraja da martaba. Saboda ya fi kowa kyau, ya fi kowa kuɗi, ya fi kowa ilimi, sannan yafi kowa sanin abin da ya dace!. Ke bari ki ji ma ko Yaya Safwan ɗin da zaki aura a karkashinsa yake, daga jikinsa suke samun abin da suke yiwa kan su buƙata. Rabin arzikin wannan estate ɗin nasa ne, ke bama rabi ba, kusan duk arzikin nasa ne! Dan haka ki iya bakin ki wallahi tun kafin ran ki ya ɓaci!”

Wani irin kallo Nana ta dinga mata sai kuma ta yi shewa cike da ƙwarewa a masifa ta ce”banza kawai! Au she daman ba shi ki ke so ba, arzikinsa ki kewa. To sai me dan ya fi kowa kuɗi? Ke kudinsa ya dama, dan da alama abin da babanku yake baki baya isarki, domin da yana wadatarki da ba zaki taɓa zuwa kina faɗar irin waɗannan maganganun ba, da kin godewa Allah da ni’imar da ya yi miki. Amma da yake son zuciya ki ke sa a gaba har kin gano cewa yafi kowa arziki, to ina ruwana da arzikinsa? Mene abin da ya shafeni dashi, ni abin da ubana yake min shi ne abin tunƙawona ba wai wani can ba, banza kawai me son zuciya!…”

Cikin tsananin ɓacin rai Amrah ta jawota ta shiga faɗin”ke har kin isa ki zageni? Dan kin ga ina zama tare da ke? Ni sa’ar wasarki ce?”

Cikin azama Maimoon ta ƙarasa gabansu tana faɗin”mene haka? Sai wani ya zo shigewa ya gan ku, ke Amrah cikata mana”

Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin janye hannun Amrah daga jikin Nana, tureta Nana ta yi tana faɗin”Eh na faɗa ɗin, ko ba banzar bace? Ai duk wanda ya ga abin da ki ka yi zai tabbatar da cewa ke banza ce, irin banzar ma da bata san abin da take ba! Saboda haka…”

Cikin zafin nama Amrah ta sauke mata mari a kuncinta na dama, wanda ya sanya ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa maganar data fara ba, ta ɗora hannunta kan fuskarta tana faɗin “ni ki ka mara?”

Amrah ta ɗora hannunta a ƙugu tana faɗin “an mare kin ko zaki…”

Ko gama maganar bata yi ba Nana ta sauke mata wani lafiyayyen mari itama. Da sauri Maimoon ta rufe bakinta da hannunta tana kallon Nana da ke faman huci kamar ƴar damisa, Amrah ta dafe kumatunta tana gyaɗa kai, kwafa ta yi kafin ta yi wani kukan kura ta janyo Nanar ta shaƙeta tana faɗin

“Ni zaki mara? Ni sa’arki ce! Ko dan kin ga ina miki wasa?”

Ita dai Maimoon tsayawa ta yi a wajen tana kallonsu tana girgiza kai, ganin da gaske faɗa suke ya sanya ta ƙarasa tana ƙoƙarin janye Nana da ke kai mata duka ta ko ina ta ce”ke Nana sai na faɗawa Abbanki ba zaki bari ba!”

Hannayenta biyu ta sanya ta ingiza Maimoon tana faɗin “dallah can rabu dani!”

Daga haka ta mai da hankalinta kan faɗan da suke.

“Ke!! Kee!!”

Safwan ya yi maganar yana ƙarasowa wajen, da mamaki ya dinga kallonsu kafin ya janye Nana da sauri a ɗan tsawace ya ce”mene haka? Ba zaku bari ba!”

“Ni rabu dani, ba zan bari ba ɗin, wallahi ba zan bari ba!”

Nana ta yi maganar tana ƙoƙarin sake jawo Amrah, daka mata tsawa Safwan ya yi, kawai sai ta fashe da kuka ta juya ta bar wajen tana ihu kamar wadda aka daka. Da idanu ya dinga bin ta har ta sha kwana kafin ya dawo da idanunsa kan Amrah rai ɓace ya ce”mene ne haka Amrah? Da hankalinki?”

Cikin shassheƙar kuka ta ce”wallahi Yaya bata da kunya ne, marina fa tayi”

“Mari kuma?”

Safwan ya faɗa da matuƙar mamaki. Gyaɗa masa kai kawai ta yi tana ci gaba da shessheƙar kukanta, ajiyar zuciya ya sauke kafin y ce”to ki yi haƙuri kin ji, kar ki ɗaga maganar dan Allah” sake gyaɗa masa kai ta yi ya kalli Maimoon ya ce”ke kuma kina kallonsu ba zaki raba su ba?”

Marairaice fuska ta yi ta ce”Yaya nima fa tureni suka yi” taɓe baki ya yi sai kuma ya juya ya bar wajen ba tare da ya sake cewa komai. Ƙarasowa gabanta ta yi ta riƙe hannunta tana faɗin “ki yi haƙuri kin ji, zo mu tafi”

Fizge hannunta ta yi ta ce”rabu dani wallahi ba zan yarda ba na rantse da Allah!”

Da mamaki Maimoon ta ce”to sake kamata za ki yi da kokawar? Kina dai gani tafi ƙarfinki, ji yanda ta yakushe miki fuska”

Sai a sannan Amrah ta kai hannunta gefen fuskarta ta taɓa, jini ta gani a hannunta ta sake fashewa da kuka tana fadin”shegiya mayya, na rantse ba zan yarda ba sai naje na faɗawa Abba”

Girgiza kai Maimoon ta yi ta ce”ke kar ki yi haka, kin dai san halin Abba ko? Ki yi haƙuri kawai” tsaki Amrah zaka ta yi ta juya ta bar wajen kamar zata tashi sama. Numfashi Maimoon ta sauke sannan ta nufi hanyar gidansu da sauri dan daman ba’a san ta fito ba.

****
Amma ta kafeta da idanu ta ce”ba magana nake da ke ba?” shiru ta yi tana sake murza hannunta dake kan idanunta, a tsawace ta ce”ba zaki faɗa min da wanda ki ka yi faɗa ba Nana har ki ka yi squeezing da kayanki haka?” Cikin shessheƙar kuka ta ce”babu kowa fa” daga haka ta nufi daƙinta da sauri. Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta girgiza kanta dan tasan ƙarya take ta ce babu kowa dole faɗa ta yi da wani. Komawa ta yi ta zauna tana jiran ta fito ta sake tambayarta.

Ƙarfe 6:30 na yamma ta fito tana sanye da hijabi, ko gida bata shiga ba tun bayan abin da ya faru dan ta san Mami ba zata barta ta fito ba. Dan haka ta yi zamanta a Apartment ɗin Hajiya Babba har yammar ta yi. Ta kusa apartment ɗin su Nana ta gamu da Hamida tana tafe sanye da hijabi har ƙasa, ta dinga kallonta sai kuma ta ce”Amrah lafiya? Me ya sami fuskarki?”

“Babu komai”

Ta ce a takaice sai kuma ta yi gaba abin ta, Hamida ta sake juyawa tana kallonta kafin ta numfashi ta ce”Allah ya kyauta” daga haka ta juya ta ci gaba da tafiyarta. Cikin Sa’a ta tarar da motar Abba a compound ɗin gidan da alama dawowarsa kenan daga wajen aiki, Amrah ta ja ta tsaya a balcony jar ya fito ya nufo wajen, yana zuwa gabanta ta durƙusa har ƙasa murya a sanyaye ta ce”Abba sannu da zuwa” fuska a sake ya ce”Yauwa Mamana sannunki” daga haka ya juya zai ci gaba da tafiya, da sauri ta ce”Abba!” Cak ya tsaya ya juyo yana kallonta ya ce”lafiya dai?” sai a sannan ya lura da fuskarta ya sake cewa”subhanallahi, meya sami fuskarki haka?” madadin ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka tana murza idanunta, ya girgiza kansa yana faɗin”faɗi mene ne bana son kukan nan” cikin shessheƙar kuka ta ce”Abba Nana ce ta mareni” da wani irin mabayyanin mamaki ya dinga kallonta kafin ya ce”wace Nanar?”

“Nana dai, kawai dan nayi mata magana shi ne ta dinga zagina ta ce min banza mahaukaciya, wai bana son iyayena bana ganin girmansu, kuma Daddyna talaka ne bashi da komai, Abbanta yafi kuɗi, shi ne dan na mareta ta rama, kuma ta kama ni da kokawa ta dinga dukana har sai da ta yakushe min fuska”

Amrah ta ƙare maganar tana wani irin kuka, Kallonta kawai Abba ya dinga yi fuskarsa ta sauya kala daga fara zuwa ja, jijiyoyin kansa sun firfito ko ba’a faɗa maka ba kasan ransa ya yi masifar ɓaci.. Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi cikin gidan da sauri, Amrah tana ganin ya shiga ta sauke hijabinta tana murmushi a fili ta ce”yauwa! Yau na nasan sai kin gane kurenki yarinya!” Daga haka ta bar wajen ranta fes.

“Nana! Nana! Nana!”

Abba ya dinga kiran sunanta yana tsaye a tsakiyar parlon, Tashi Amma ta yi tana kallonsa ganin yanda fuskarsa take a ɓace ta ce”lafiya dai yallaɓai?”

“Ina Nana take?”

Ya tambayeta a fusace, da hannu ta nuna masa daƙinta ya yi gaba da sauri ya bar ta tsaye a wajen. Tana zaune a gefen gadonta hannunta riƙe da wayarta tana game ya turo ƙofar ya shigo, da sauri ta ɗaga idanunta tana kallonsa ganin yanda ya shigo a fusace yasa ta ce”sannu da zuwa Abba…”

Ko rufe bakinta bata yi ba ya sauke mata wani zazzafan mari har sai da ta tafi ta faɗi ƙasa, ihu ta saki wanda ya yi dai dai da shigowar Amma, ya ƙarasa ya fincikota yana mata wani irin kallo ya ce”wato kin dawo da halin ki ko? Wane sa’anki a cikinsu da har zaki dinga faɗa dasu? Har ki iya zaginta, sannan bayan ita ki iya haɗawa da babanta! Yaushe ki ka dawo da wannan mummunar ɗabi’ar taki?!”

Tafa hannaye Amma ta shiga yi tana salati kafin ta ce”ni daman na san tun da na gan ta ta shigo a birkice to magana ta dauko ashe kuwa haka ne, da wa ta yi faɗa kuma?”

Abba bai tsaya bata amsa ba ya zare belt ya dinga dukan Nana kamar Allah ya ai ko shi, ban da ihu babu abin da take, ta dinga kiran sunan Amma ta taimaketa amma ta mata banza. Sai da ya yi mata lilis sannan ya wurgar da belt ɗin yana kallonta ya ce”daga yau ko kallon banza ki ka sake wa wani wanda ya girmeki a cikin gidan nan zaki ga yanda zan yi dake!”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *