⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 10: Chapter 10

Barraks road,
Gibson jalo.

A babban compound ɗin gidan motar ta yi parking, Zahra ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito daga motar, ita ma Nana ta fito tana ƙarewa babban compound ɗin gidan kallo, bishiyu da flowers sun cika ko ina, Zahra ta zagayo tana riƙe da hannun Noor ta ce“muje Nana” okay kawai ta ce sannan suka nufi hanyar balcony ɗin gidan. Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga, Ta ajiye wayar gefenta ta tashi tana murmushi ta ce“laaa aunty sannu da zuwa” Zahra ta yi murmushi tana kallon budurwar mai matukar kama da ita ta ce“Safeena kina zaune, yauwa” daga haka ta nufi kan kujera ta zauna. Safeena ta ɗan kalli Nana ta ce“welcome sis” murmushi Nana ta yi ta ce“thank ya ki ke?”

“Alhamdulilah”

Ta ce tana komawa ta zauna, ita ma Nana tafiya ta yi ta zauna kan ɗaya daga royal cushion ɗin dake zagaye da ƙaton parlon, Safeena ta kama hannun Noor tana faɗin “wow aunty ashe Noor ta girma” ta ƙare maganar tana ɗorata kan cinya. Murmushi Zahra ta yi ta ce“eh yar taku ta girma mana, Ina Aunty Khadijah da Umma?”

“Umma tana sama fa, ita kuma Aunty bata nan sun fita da Siyama”

Okay Zahra ta ce sannan ta miƙe ta nufi saman da sauri, Nana ta bita da kallo sai kuma ta ɗan jingina da kujerar tana sauke numfashi. Zahra ta tura kofar bedroom bakinta ɗauke da sallama, Umma dake zaune ƙasan gado tana jan carbi ta ce“wa’alaiki salam, Fatima” ta ƙare maganar tana gyara zamanta, fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa ta zauna gefenta ta ce”Ummata”

“ya mai gidan naki?”

Sai da ta kwanta kan cinyarta sannan ta ce“lafiya kalau, ya ce an jima zai bi yo ya gaisheku”

Jinjina kai Ummar ta yi sannan ta ce“Ina Noor ɗin?”

Murmushi Zahra ta yi ta ce“tana ƙasa wajen Safeena”

Okay Umma ta ce. Shiru ne ya biyo baya kowa da abin da yake tunani can kuma Zahra ta ce“laa Umma wai ina Aunty Khadijah?”

“ta fita kin san halinta dai ba son zama take ba, tuni ta fice”

Murmushi Zahra ta yi ta ce“hajiya Aunty Khadijah kenan, Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta dai”

“to san auren take Zahra? Ai bai dameta ba, tafi son ta yi ta yawo daga nan sai nan” girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a’a Umma tana so mana, ai kowa ce mace na son ta yi aure duk da ta taɓa yi amma zawarci ai bashi da daɗi” taɓe baki Umma ta yi ta miƙe sannan ta ce“ai duk kun fita hankali, ita ce babba amma babu abin da ta iya sai shirme” daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin, jim Zahra ta yi a wajen tana tunani kafin ta miƙe ta fito ita ma.

Umma ta dinga kallon Nana fuskarta ɗauke da fara’a har ta ƙaraso wajen ta ce“wa nake gani kamar Nana?” zamowa ta yi daga kan kujerar ta gaisheta, Umma ta zauna kusa da Safeena tana faɗin “lafiya kalau Khadijah, haka ki ka girma?” sunkuyar da kai ta yi a hankali, Umma ta sake cewa“ina mamanki?”

“tana gida”

Ta yi maganar a sanyaye, jinjina kai Umma ta yi ta ce“Allah sarki na kwana biyu rabon da na ganta” ɗan murmushi Nana ta yi bata ce komai ba dai dai nan Zahra ta sakko daga saman, ta ƙaraso wajen Nana tana faɗin “umma kin ga yanda Nana ta girma ko?”

Jin jina kai Umma ta yi ta ce“yanzu nake faɗa nima, kamar ba ita ba ce ki ke zuwa da ita ba lokacin tana ƴar ƙarama, bata fi girman Noor ba” Zama Zahra ta yi sannan ta ce“wallahi amma yanzu ta zama ƙatuwa ta kamoni a jiki” langwaɓar da kai Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kai Aunty”

“ƙarya nayi? Yanzu fa kin yi girmana wallahi sai dai a ce idona ya fi naki buɗewa, kin ga Umma aurensu fa za’a yi nan da 6weeks”

Riƙe haɓa Umma ta yi ta ce“Allah alhakamu, har lokaci ya zo? Daɗina dasu auren wuri na huta kafin yaro ya fanɗare, to wa zata aura a cikin samarin gidan? Ko sun daina auren Zumuncin?”

Ummar ta jera mata tambayoyin a tare. Murmushi Zahra ta yi idanunta zube kan Nana ta ce“Safwan zata aura, ina zasu daina auren zumunci Umma?”

Waro idanu Umma ta yi ta ce“Ikon Allah wane Safwan ɗin? Ban san shi ba” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a’a dai baki gane shi ba, Safwan fa ɗan autan su Daddyn Noor” jinjina kai Umma ta yi ta ce“eh na gane shi kuma, wani mai kama da Abdusammad ko?”

“eh shi fa kin gane shi ma” cewar Zahra tana murmushi. Kallon Nana Umma ta yi ta ce“Allah ya sanya Alkhairi Khadijah ya baku zaman lafiya, amma ki yi ta haƙuri, aure sai da haƙuri”

Jiki a sanyaye Nana ta ce“to Umma in sha Allah”

“Ni kam suna burgeni wallahi Aunty, ko nima zaki sama min miji a cikin estate ɗin ne?” Safeena ta yi maganar cike da zolaya, riƙe baki Zahra ta yi tana faɗin “kee rufa min asiri, su basu auren haɗi” ta ƙare maganar cike da raha, Safeena ta ce“assha da dai kin duba, a yan samarin nan nasu a sama min ɗaya na aura, wallahi suna mugun burgeni bama ni kaɗai ba, ko a cikin jama’a zaki ji ana maganar dangin. Haka rannan wata course mate ɗina wai zata min ƙarya ai tana dating da ɗaya daga cikin ya’yan gidan na ce to wallahi ƙarya take dan Yayata babban ɗan gidan take aure” tuntsirewa da dariya Zahra ta yi ta ce“wato ke ga gwana ko?” murmushi Safeena ta yi ta ce“ai gaskiya ce, ke fa Allah ne ya baki shi wallahi, daman ance matar mutum ƙabarinsa amma idan ba dan haka ba ya za’a yi ki aure shi” ɗan haɗe rai Zahra ta yi ta ce“to kar ki faɗa min magana kuma”

Zazzaro idanu Safeena ta yi tana murmushi ta ce“nii to Allah ya baki haƙuri Hajiya” ta ƙare maganar tana gyarawa Noor gashin kanta.

****
Junaid ya girgiza kansa idanunsa zube kan wayar hannunsa ya ce“ni fa ba zan yi ba, kai wai kana ma da hankali ne? Ce maka nayi fa ina son na aureta, idan ba zaka iya bani shawarar arziki ba ka rabu dani dan Allah” ya ƙare maganar yana ɗago kansa, Taɓe baki Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“Baba ka ji fa, ana bashi shawara yana gwale mutane, to kaje ka ci gaba da bin ta tana jan ka a ƙasa” ya yi maganar cikin ɓacin rai, Harararsa Junaid ya yi ya ce“eh naji mene ne dan ta jani a ƙasa? Ai daman ita mace an santa da haka, kuma kaf cikinku babu wanda yake dating yar babban gida irin yanda nake, sai dai idan baƙin ciki ku ke min”

“kai ka isa mu maka baƙin ciki akan waccan kwailar yarinyar? Mu da muke da mata waɗanda suka san kansu” cewar Habib a ɗan zafafe. Kallonsu ya yi sai kuma ya taɓe baki ya ci gaba da danna wayarsa ba tare da ya sake bi ta kansu ba.

****

“Sultan! Sultan! Sultan…”

“na’am Ummi”

Ya amsa mata yana kokarin tashi zaune, kallonsa ta dinga yi daga tsayen da take kafin ta ce“mene haka? Kwanciyar me ka ke a ɗaki har wannan lokacin?” Ummi ta yi tambayar tana kallon fuskarsa wadda ta rame sosai, girgiza kansa ya yi ya ce“babu komai Ummi, kawai ina ɗan ciwon kai ne shi ne ya hana ni tashi, amma yanzu zan tashi”

“ciwon kai ne ya hana ka tashi daga kwance har la’asar ko? Sultan ko dai kana son ka zaja min masifar da ba zan iya da ita bane? Akan maganar aure ka bi ka ɗaga hankalinka, ita matar mutum ai ƙabarinsa mene ne abun wannan damuwar?”

Lumshe shanyayyun idanunsa ya yi kafin ya ce“na haƙura fa Ummi, na bar wa Allah komai, idan Nana ce Alkhairina Allah ya sani kuma zai bar min ita a duk yanda take, amma idan ba ita ba ce ba na san ba zan sameta ba, so ki bar damun kan ki” ya ƙare maganar a sanyaye, girgiza kai Ummi ta yi sannan ta zauna gefen gadon ta dafa kafaɗar sa cike da kulawa irin ta uwa ta ce

“na sani akwai ciwo ka rabu da wanda ka ke so, na sani kana son Nana, ita kuma tana sonka, amma ka sani baka isa ka bawa kan ka abin da Allah bai baka ba, idan ba ita Allah ya ƙaddara maka ba, ba zaka taɓa samunta ba, sai dai ka yi ta damun kan ka kana shiga wani hali, mata su aka sani da irin wannan ba maza ba, ka zama mai ɗaukan ƙaddara a duk yanda ta zo maka, ka daina wannan ƙuncin da damuwar. Ka fawallawa Allah komai dan Allah Sultan”

Faɗawa jikinta ya yi yana sakin wani marayan kuka mai ban tausayi, kuka yake ko ya samu sauƙin abin da yake ji a zuciyarsa, ya sani ba lallai bane ya samu Nana tun da aka yi haka, amma zuciyarsa ta kasa haƙura ta daina tunaninta. Ummi ta shiga shafa kansa a hankali tana jin babu daɗi a ranta, tabbas da tana da dama da sai ta bawa Sultan matar da yake so, sai dai ko kaɗan bata da wannan damar, ba zata iya cewa koda ƙala ba akan maganar auren, dan haka dole ta ci gaba da rarrashinsa da kuma yi masa addu’a har ya manta da Nana.

****
Around 5:20 na yamma ta sakko ƙasan hannunta riƙe da wayar Zahra, babu kowa a parlon dan haka ta yi waje da sauri kafin wani ya zo. Tafiya ta dinga yi tana waiwaye har ta fice daga gidan, ta tsaya a jikin gate ta fara dialing numbern tasa, sai dai kafin ta kai ga kira taji ana yin horn daga gefenta na dama, dan haka ta juya tana kallon wanda yake horn ɗin, kamar yanda ta zata haka ce ta faru, Junaid ne zaune gaban motar hannunsa maƙale kan steering motar yana kallonta, ta sauke numfashi sannan ta ƙarasa wajen. Buɗe motar ta yi ta shiga tana kallonsa, ya dinga kallonta shima yana murmushi, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta ta ce

“ina yini?”

Yanda ta yi maganar ya sanya shi murmushin da bai yi niyya ba, ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tana murmushin itama.

“kin yi kyau abin ki”

Ya yi maganar cikin nishadi, ɗago kanta ta yi ta kalleshi ta ce“kai ma haka sir, ka yi kyau kamar ango”

“ango ranar bikinsa ko?”

Gyaɗa masa kai ta yi ya ce“to yaushe ne bikin namu?” ɗan zaro idanu ta yi sai kuma ta ɗauke kanta bata ce komai ba, ya dinga kallonta can kuma ya ce“kin san me yasa na zo wajenki?” Girgiza kanta ta yi ya ce“daman ina son na sake tambayar ki ne akan maganar aurenku, shin da gaske nan da 6weeks ɗin ne?”

She just nodded her head fuskarta babu walwala, ya sauke numfashi sannan ya ce”and har yanzu Abbanki bai karbeni ba?”

Kamar zata yi kuka ta ce

“ban fa faɗawa Abba komai ba, da Amma kawai muka yi maganar saboda nasan ta fi shi sauƙin kai, but unfortunately sai naga ita ma bata yarda ba, ta ce idan na yiwa Abba maganar sai ta ɓata min rai, and nima na san koda na yi masa ba zan taɓa samun abin da nake so ba, ba zasu barni ba, in dai ina cikin estate ɗin M-Shuwa ba zan taɓa kasancewa da kai ba, sai dai…”

Ta ɗan yi shiru tana kallonsa idanunta cike taf da hawaye

“Sai dai me?”

Junaid ya yi maganar yana ci gaba da kallon kyakkyawar fuskarta. Furzar da numfashi ta yi sannan ta ce

“Sai dai idan barin gidan zan yi, sai dai idan na bika mu gudu, sai muje wani wajen muyi aure”

Da wani irin matsanancin mamaki Junaid ke kallonta, ya girgiza kansa kafin ya ce

“mu gudu kuma Nana? Kin san me ki ke faɗa kuwa?”

Jinjina masa kai ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce

“eh mu gudu, ka gudu dani dan Allah, muje mu yi aurenmu muyi rayuwarmu mu kaɗai”

Junaid ya dinga kallonta baki buɗe, ta goge hawayenta tana fadin“saboda idan har ina cikin gidan to sai dai mu haƙura da juna, amma idan muka yi aure basu sani ba, koda na dawo zasu haƙura kuma…”

“Nana!”

Ya daka mata tsawa wadda ta sanya ta yi shiru, cikin ɓacin rai ya ce“baki san me ki ke faɗa ba! Baki da hankali ne shiyasa, har yau yarinta ke damunki, kin san irin yanda iyayenki ke son ki da har zaki yi yunƙurin rabuwa dasu? Kin san halin da zasu shiga? Do you have any idea about how much they care about you? Kin san irin soyyayar dake tsakanin iyaye da ɗan su kuwa? Kin bani mamaki. Ko zan rasa ki ba zan taɓa yarda da wannan gurguwar shawarar taki ba, ba zan taɓa aminta da ita ba! Ki sake magana!”

Kallonsa ta dinga yi hawaye na zirarowa kan kuncinta sai kuma ta ce“Ai shikenan tun da ka ce haka, daman ba sona ka ke ba, a baki ka ke faɗar son amma babu shi cikin zuciyarka, har ka ke iƙirarin ka rasani, to kaje ɗin, nima na rabu da kai, ba zan sake kula ka ba! Ba zan sake kiran ka a waya ba! Ba zan kuma ba wallahi!” ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka dake ƙaryata kalaman bakinta, ta buɗe motar a fusace ta fita. Junaid ya dinga kallonta har ta buɗe gate ɗin gidan ta shige, ya sauke numfashi yana jin babu daɗi a cikin ransa ganin yanda ta yi fushi. Sanin saurin fushinta da kuma saurin saukarta ya sanya bai damu ba ya yiwa motar key ya juya ya yi reverse ya bar unguwar.

Wata irin faduwar gaba ce ta risketa saboda ido biyu da suka yi da Zahra tana tsaye ta naɗe hannayenta a ƙirji, ta dinga kallonta ba tare da ta ce komai ba. Sunkuyar da kai Nana ta yi tana goge hawayenta da gefen mayafinta, Zahra ta fizgi hannunta ta fara janta. Bin ta Nana ta dinga yi tana jin zuciyarta na wani irin bugawa, tsoro da fargabar abin da Zahra zata ce mata suka shigeta. A gaban wasu fararen kujeru ta tsaya, ta dangwarar da ita akan ɗaya sannan ta zauna a wadda take facing ɗinta.

Ganin irin kallon tuhumar da take mata ya sanya jikin Nana ya sake sanyi, ta ɗago kanta cikin shassheƙar kuka ta ce

“wallahi Aunty…”

Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu, ta yi shiru a dole ba dan ta fadi abin da ta yi niyya ba. Shiru wajen ya ɗauka na wasu mintuna kafin Zahra ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce

“Nana wane wannan? A ina ki ka san shi? Mene ne alaƙar da ke tsakaninki dashi? And why you dey called him here!”

Zahra ta jera mata tambayoyin tana kafeta da idanu, shiru Nana ta yi tana matsar kwalla, hakan kuma ya ɓatawa Zahra rai matuƙa dan haka a fusace ta ce

“okay kar ki yi magana, wallahi idan baki faɗa min wane shi ba sai na faɗawa uncle ɗin ki, idan ya so ya sanar da Abba!”

Da sauri ta ɗago kanta, ta dinga girgiza kan tana hawaye a kiɗime kuma ta ce“a’a aunty zan faɗa miki, dan Allah kar ki faɗawa Abbana!”

Haɗe rai Zahra ta yi ta ce“oya faɗa min wane ne shi?”

Sai da goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta buɗe bakinta a hankali ta fara faɗin

“saurayina ne, malamin mu ne a Aun, tun ina jss muke tare, at first na ɗauka kyautatawa ce kawai tsakaninmu, dan tun da ya zo school ɗin ban sake rasa wani abu ba, shi ne yake koya min karatu idan ban iya ba, shi ne yake sakani na gyara kuma ya hanani ba dai-dai ba. Sai da muka zo senior sannan ya faɗa min abin da ke ransa, to nima daman ina son shi a sannan ɗin, duk da ban san mene ne son ba, amma naji yana burgeni, kuma naji ina son na aureshi. Dan haka muka fara soyyaya dashi sosai, kullum sai mun haɗu a Aun, saboda ni yaƙi barin makarantar duk da iyayensa sun yi kokarin saka shi yin haka, a kwana a tashi naji son shi na ƙaruwa a zuciyata, duk da a lokacin nasan mataki da kuma tsarin gidanmu, amma a duk lokacin da naji ina son na bar shi sai naji zuciyata tana yimin zafi, sai naji numfashina na ƙoƙarin barin ƙirjina. To a sannan na gane ba zan iya rabuwa da sir Junaid ba, ba zan iya barinsa ba, dan haka na ɗauki aniyar sai na aure shi koda hakan na nufin zan ɓata da kowa, ma ɗauki aniyar sauya al’adar danginmu, yanda za’a dinga bawa kowace yarinya yancin auren wanda take so. Za’a daina mana auren haɗi, domin yawanci ba wanda ka ke so ake baka ba, dan haka ni sir Junaid nake son aure, kuma sai na aureshi!”

Ta ƙare maganar tana shessheƙar kuka, Zahra ta dinga kallonta tana nazarin kalamanta, she just can’t believe a ce Nana ke faɗar irin wannan maganar, magana irin ta manya cike da nutsuwa. Ta numfasa kafin ta ce

“kenan kina shirin tarwatsa dangin ku? Kin yarda ki zama almakashin da zai datse zumuncin da ke cikin dangin ku? Kin yarda ki zama wadda iyayenta zasu yi Allah wadai da haihuwarta? Kin yarda ko Nana?”

Girgiza kanta ta yi still crying ta ce“a’a Aunty, bana son na tarwatsa zumunci kawai ina so…”

“kawai me Nana? Shirin ki na auren bare dai dai yake da tarwatsa dangin da iyayenki suka sha wahala wajen samar dashi, kin san mene ne zumunci kuwa Nana? Kin san girman da yake dashi? Kin san falalar da take cikinsa? Kin san yanda ubangiji ke kallon duk wanda ya sadar dashi? Mene ne yake damunki Nana? Yarinta? Ko kuma wannan ba yarinta ba ce son zuciya ce, tun da har ki ka gane ki lalata zumuncin Allah to tabbas son zuciya ce a cikin lamarin ki.”

Ban da kuka babu abin da Nana ke yi, ta ɗago runannun idanunta tana kallonta ta ce“to aunty ya zan yi? Na bari na auri wanda bana sonsa? Na bari a lalata min farin ciki? Na yi shiru ina gani”

Jinjina kai Zahra ta yi ta ce“eh ki yi shiru, domin babu wanda ya taɓa bin iyaye kuma ya taɓe, Nana kin san wani abu?” girgiza kai ta yi, Zahra ta gyara zama sannan ta ci gaba da faɗin

“idan har ki ka ƙi wannan auren tamkar kin raba tsakanin ki da Abba ne, saboda Abba ma ɗaya daga cikin ƙashin bayan wannan zumuncin, su ne suka assasa shi, suka sanya ake auratayya a tsakani saboda a samar da tsaftacen dangi da babu bare a cikinsa. To i dan har ƴar sa zata bijire me hakan ke nufi? Kina son tozarta mahaifinki ne, kina son lalata farin cikin wanda ya fifitaki fiye da komai, wanda yake ɓata lokacinsa da ƙarfinsa domin samar miki da abin da ki ke buƙata, wanda yake baki komai ba tare da ya miki gori ba, idan ki ka raunata zuciyarsa kina nan kin yi dai dai kenan? Kina ganin zai yi alfahari da ke? Ke kaɗai ce yarsa dan haka duk wata taƙama da uba ke yi akan yayansa ke dake kaɗai yake da wannan damar, idan har ki ka ƙi wannan auren tamkar kin wulaƙanta shi ne a idon duniya, kin nuna ce shi bai isa da ke ba, ballantana har wasu su ga girmansa su girmama hukucinsa. Idan har kina ganin wannan shi ne abin da ki ka zaɓa shikenan Nana, ba zan takura ki, ba kuma zan miki dole ba, amma idan da ni ce a matsayin ki…”

“za ki haƙura da Junaid domin kare martabar mahaifin ki da kuma dangin ki”

Zahra ta gyaɗa mata kai, ta runtse idanunta tana hawaye ta ce

“to nima zan yi hakan aunty, zan bar wanda nake so domin kare martabar Abbana, ba zan taɓa yin abin da zai sanya shi a damuwa ba, nayi alƙawarin zan zame masa farin ciki, ba zan saka shi takaici ba, ba zan bari a daina ganin girmansa ba, na haƙura da Junaid aunty, na haƙura dashi na haƙura Aunty…”

Zahra ta dinga kallonta cike da farin ciki, ta tashi ta ƙarasa gabanta ta tsuguna sannan ta kama hannayenta ta riƙe cikin nata ta ce“da gaske Nana? Kin haƙura dashi? Ba zaki sake kula shi ba? Ba zaki sake shiga harkarsa ba?”

Jinjina mata kai Nana ta yi ta ce“eh aunty, na bar shi wallahi na haƙura, ba zan sake ɗaga maganar ba”

Zahra rasa abin yi ta yi sai kawai ta tashi ta rungumeta tana murmushi ta ce“Allah ya yi miki albarka Nana, ya baki zaman lafiya a gidan mijinki, ya haɗa ki da mai ƙaunar ki wanda ba zai ɓata miki ba, wanda zaki so shi fiye da tunanin ki”

Ƙanƙameta Nana ta yi sannan ta ce“amin aunty, Nagode, Amma dan Allah kada ki faɗawa uncle ko Abbana”

Ɗagota ta yi daga jikinta tana murmushi ta ce“har abada ba zan taɓa faɗawa kowa ba Nana, ki ɗauka mun rufe wannan maganar a nan”

Jinjina kai ta yi cike da farin ciki ta sake rungumeta tana fadin “nagode auntyna, Allah ya bar mana ke” Zahra ta yi dariya ta ce“amin tare da ke Nanarmu”.

****
Wani irin banza kallo ya dinga masa kafin ya ce“amma dai an yi banza wallahi tallahi, yarinyar ta baka dama sannan ka yi wasa da ita? Ashe ba sonta ka ke ba daman, ba ƙaunarta ka ke ba, a baki ne son wallahi” taɓe baki Junaid ya yi ya ƙarasa kan sofa ya zauna hannunsa riƙe da coffee ya ce“kai dai baka san abin da ka ke ba, yarinyar da nake son na aureta mu samu zuri’a mai kyau da tsafta ita ce zan gudu da ita? Na aureta bada yardar iyayenta ba? Kidding!”

Zama shima Al-ameen ɗin ya yi ya ce“to mene ne shirin ka? Taya zaka sameta bayan kasan babu wata hanya?”

Ɗan murmushin baka san me ka ke ba ya yi masa kafin ya ce“ba dole ba ne na faɗa maka shirina, but when it goes well zaka ji” murmushi Al-ameen ya yi ya ce“daɗina da kai kwanya, dan Allah ka faɗa min mene ne plan ɗin”

Sai da ya yi sipping coffee ɗinsa sannan ya ja gajiyayyun idanunsa ya rufe yana sauke numfashi a hankali, Al-ameen ya ce“ka faɗa min mana dan Allah”

“ba fa zaka ji ba yauwa!” cewar Junaid yana kallonsa, taɓe baki Al-ameen ya yi ya ce“to ka ci kanka”

****
Ana idar da sallar isha’i suka shigo cikin estate ɗin, Nana ta dinga kallon jama’ar da ke fitowa daga cikin masallacin har idanunta ya sauka akan Abbanta dake tsaye suna gaisawa da Abbansu Hamida, ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“Uncle a sauke ni anan” yana ƙoƙarin parking ya ce“akan me?”

“Abba na hango zan bi shi”

Ta ce a sanyaye. Gyaɗa kansa ya yi sai kuma ya ce“to sauka” ya yi maganar bayan ya ƙarasa parking ɗin. Buɗe handle ɗin motar ta yi ta sauka, babu wanda ya ce komai a cikinsu ta juya ta nufi inda ta hango Abban. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya ci gaba da driving ɗinsa.

Sai da taga ya baro cikin mutane ya nufi hanyar gida sannan tabi bayansa a hankali har ta iske masa dan ba sauri yake ba

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *