Chapter 11: Chapter 11
“Abba”
Ta kira shi a sanyaye, cak ya tsaya kafin ya jiyo yana kallonta, mamaki ne ya kama shi ya ce“Nana daga ina ki ke?” tana kallonsa ta ce“tare muka dawo da uncle” jin jina kansa ya yi dan sai sannan ya tuna ya ce masa sun fita da Zahra. Ya ce“to tawo mu tafi” ya yi maganar yana miƙo mata hannunsa na dama, ɗora nata tayi akai sannan suka ci gaba da tafiya. Babu wanda ya ce komai a cikinsu, sai dai kowa da abin da yake tunani cikin ransa, shi yana tunanin yanda zai hanata faɗa da mutane, ya yinda take tunanin maganganu da Zahra ta faɗa mata ɗazu. Ta ɗaga idanunta tana kallonsa ba tare da ya sani ba, tabbas ta yi gaskiya, Abba bai cancanci wulakantawa daga gareta ba, bayan duk irin so da ƙaunar da yake nuna mata, bai cancanci ta bijire masa ba, domin bai taɓa zaluntar ta ba. To amma me ya sa take jin zuciyarta kamar ba zata iya haƙura da Junaid ba? Ta sauke ajiyar zuciya tana kawar da tunanin daga ranta, domin ta bar shi har abada.
Koda suka shiga gidan basu sami kowa a parlon ba sai tv kawai dake kunne, bai saki hannunta ba ya nufi ɗakinsa, ita ma bata yi kokarin janye hannun ba ta bi shi ɗakin. Ɗakin was neat and organized, komai na ciki a tsaftace yake, ta kalli kan gadonsa wanda ya sha gyara farin bedsheet ɗin sai kyalli yake, sakin hannunta ya yi ya nufi wajen gadon, ta dinga kallon ɗakin tana tuna how long rabonta dashi, wajen study table ɗinsa ta ƙarasa ta dinga kallon tarin awards ɗinsa da kuma certificate as a MD of M-Shuwa group of companies, daga can be gefe ta hangi wasu sticky notes ta kai hannunta ta dinga tabawa kafin ta ce“laaa Abba kana da rubutuna har yanzu? Ni na rasa su” ajiye abin da ke hannunsa ya yi ya ƙaraso wajen ya tsaya a bayanta yana murmushi idanunsa ƙur akan note ɗin farko inda ta rubuta “Abba’s first born” ɗayan kuma ta saka “world best Daddy”
Lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe su akanta ya ce“lokacin kina ƙarama sosai, kamar kin fi yanzu hankali” juyowa ta yi tana kallonsa fuska a shagwaɓe ta ce“nafi hankali kuma? Ba an ce mutum yana girma yake ƙara hankali ba?” yanda ta yi maganar da zallar gaskiyar ta ya sanya shi murmusawa ya ja kumatunta sannan ya ce”eh wasu ba, amma ke da kin fi hankali” kallonsa ta dinga yi sai kuma ta ce“to me ya sa Abba?”
“saboda da kin fi son Abbanki, da baki ɓata min rai, u’re always been my favorite” rungume shi ta yi tana sauke numfashi a hankali ta ce“yanzu ma ina sonka Abba, ni ina sonka, na fi son ka yanzu” shafa kanta kawai ya dinga yi ba tare da ya ce komai, bai san me ya sa kullum yake ƙara jin yarinyar cikin ransa ba, ko dan ita kaɗai gare shi? Ya tambayi kansa. Jan hannunta ya yi har gaban gadon sannan ya miƙo mata katon ledar dake wajen, ta amsa tana murmushi ta ce“Abba me ka siya min? Ko…”
Wani irin ihu ta saki ta ƙanƙameshi tana dariya, dai dai lokacin Amma ta shigo tana kallon su a ɗan kiɗime ta ce“subhanallahi, lafiya dai?” ban da murmushi babu abin da Abba ke yi, ita kuwa sai faman ihu take tana tsalle, ya janyeta daga jikinsa still smiling ya ce“ya isa haka murnar” girgiza kanta ta yi sai kuma ta juya ta ɗauki system ɗin tana dariya ta ce“wow Abba, thank you so much, ashe baka manta ba?”
Jin jina kansa ya yi sannan ya ce“ya za’a yi na manta?”
Ta lumshe idanu tana murmushi ta ce “shiyasa nake sonka sosai” ta ƙare maganar tana kissing ɗinsa a kumatu, dariya kawai ya yi sannan ya bar wajen, ta ƙarasa inda Amma ke tsaye kamar an dasata ta ce“Amma kin kalla Abba ya siya min new system”
Murmushi kawai Amma ta yi dan ta san ƙaunarta da system ta ce“yar gatan Abba, congrats” ta ƙare maganar tana jan kumatunta, Dariya kawai Nana ta yi sannan ta ratsa ta gefenta ta fice daga ɗakin da sauri.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har tsawon sati uku, abubuwa suka dinga matsowa kusa, ban da shirye-shirye babu abin da ake ciki estate. Zuwa sannan duk sun haƙura akan zaɓin da aka musu, babu wanda ya sake tada zancen yana so ko baya so. Ranar Alhamis wajejen ƙarfe 12:00 na rana tana zaune cikin daƙinta wayarta ta fara ƙara, kallon screen ɗin wayar ta yi sai kuma ta ci gaba da danna system ɗinta. Kiran na katsewa wani ya sake shigowa, ta ɗan kalla sai kuma ta matse gefen wayar, ko kaɗan bata son ɗaga kiransa, bata son magana dashi, ta riga da ta haƙura dashi ta yarda da zaɓin da aka mata. Duk da ta san abu ne mawuyaci ta iya mantawa da Junaid cikin ranta, ƙarar da wayar ta yi ya sanya ta ɗan ɗago idanunta kamar zata yi kuka, ta kalli wayar kafin ta sanya hannunta na dama ta dauƙa ta kai kunne. Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya jin ta ɗaga wayar, muryarsa cike da damuwa ya ce
“Nana”
Shiru ta yi tana tura baki, ya sake faɗin “kina jina?”
Nan ma ta sake masa shiru tana jin kamar ta katse wayar,
“Nana ko dai…”
“ina ji”
Ta ce murya a ɗan kumbure. Jin jina kansa ya yi yana ɗan suɗe laɓɓansa ya ce“kin daina sona ko? Kin yar dani ko?”
Ciro wayar ta yi daga kunnenta ta dinga kallon screen ɗin kafin ta sake mayarwa, Junaid ya ce“Nana wane ya sauya miki tunani? Wane ya baki shawarar rabuwa dani? Ashe daman zaki iya barin a rabamu? Ashe zaki iya mantawa da alƙawarinmu? Kin bani mamaki Nana”
Sosai ta ji jikinta ya yi sanyi, nan da nan hawaye suka kawo idanunta, ta yi shiru ba tare da ta furta koda kalma ɗaya ba. Jan numfashi Junaid ya yi ya ce“shikenan Nana, tun da kin zaɓi rabuwa dani shikenan, zan haƙura dake, amma ina son ki sani ba zan taɓa iya daina sonki ba, ba zan iya mantawa da ke ba Nana, I’ll not! Kuma ina son ki sani bani na bar ki ba, ke ce ki ka bar ni”
Ya ƙare maganar hawaye na zubowa kan fuskarsa, shirun da taji ya yi ya sanya ta sauke wayar daga kunnenta, har sannan bai katse kiran ba, tana jin yanda yake sauke numfashi da sauri da sauri, kashe wayar ta yi gaba ɗaya ta yi wurgi da ita kan ƙarshen gadon sannan ta kwanta tana fashewa da wani raunataccen kuka. Tabbas tana son Junaid, kuma tana jin sa a ranta, amma ta riga da ta yi alƙawarin rabuwa dashi domin farin cikin iyayenta. Tana nan kwance har ƙarfe 1:00 tana faman kuka a hankali, agogon da ya buga ƙarfe ɗayan ne ya sanya ta tashi tana goge hawayenta, ta tashi daga wajen ta ƙarasa gaban mirror ɗinta. Kallon kanta ta dinga yi a jikin madubin, kamar ba ita ba, ta rame, idanunta sun yi jajur kuma sun kumbura. Haka ma fuskarta, ta sauke numfashi sannan ta nufi hanyar toilet tana haɗa hanya.
After 10mins ta fito tana goge fuskarta da towel, ta ƙarasa gaban gadonta ta ɗauki prayer mat da hijab ɗin da ta yi salla da asuba ta zura sannan ta shimfiɗa laddumar ta fara gabatar da salla, koda ta ida zama ta yi a wajen ta dinga addu’o’inta har wajen 1:30 na rana, kafin daga bisani ta tashi ta naɗe laddumar ta ajiye inda take sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin sanye da hijabin.
Kallonsu ta dinga yi kafin ta ƙarasa tana murmushi ta ce“laa aunty” ta ƙare maganar zama kusa da Ramlah. Murmushi ita ma Ramlah ta yi ta ce“Amarsu Nana” sunkuyar da kanta ta yi tana ɗan murmushi a hankali. Cikin zolaya Ramlah ta ce“wai sauran kwana nawa kenan?” kamar zata yi kuka ta ce“ni aunty ban so wallahi” dariya Ramlah ta yi ta ce“ƙaryar banza dai, muna nan zaki zo kina cewa Yaya Safwan kaza, wai ke ga me miji” tashi ta yi daga wajen da sauri tana satar kallon Amma da ke zaune gefe ɗaya, ta ɗan kalleta ta ce“Amma zan je wajen Aunty Zahra”
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“a dawo lafiya” to kawai Nana ta ce sannan ta yi waje da sauri, Ramlah ta bi bayanta da kallo tana murmushi ta ce“abun mamaki wai Nana ce zata yi aure” girgiza kai Amma ta yi ta ce“nima kullum da auren nan nake kwana nake tashi, Allah dai ya bada zaman lafiya” cikin fara’a Ramlah ta ce“to ya za’a yi? Amin ya rabbi”
****
Murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“to ya za’a yi?” Nana da ke tsaye jikin mota ta ce“bari dai naje na dawo sai mu yi maganar”
“okay zan faɗawa Amrah ma”
Wani irin banzan kallo ta watsa mata sai kuma ta ce“to ba zan je ba” murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“ai ko baki isa ba yarinya, wallahi kamar kin je kin gama” gaba Nana ta yi ba tare da ta sake bi ta kanta ba, Maimoon ta dinga kallonta har ta shige apartment ɗin sai kuma ta juya tana murmushi a hankali.
Tura ƙofar parlon ta yi bakinta ɗauke da sallama, Wata babbar mace ce zaune akan kujera ta ci ado da wani ubansu lace mai kyau da tsada, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya kitson attachment ya zubo ta ƙasan daurin sai taunar cew gum ta yi tana ƙas ƙas, Nana ta dinga kallonta sai kuma ta sake cewa“Salamu alaikum” ɗago kanta ta yi daga danna wayar da take ta ɗan kalleta babu yabo babu fallasa ta ce“wa’alaiki salamu” daga haka ta sake sauke kanta tana ci gaba da abin da take. Shiru Nana ta yi tana son ta tambayeta ina Zahra take tana kuma jin tsoron yi mata magana. Ganin mintuna biyu sun shuɗe ya sanya ta ce“dan Allah Aunty Zahra fa?”
“Tana ciki” matar ta ce a takaice tana taunar cew gum ɗinta, okay kawai Nana ta ce sannan ta nufi hanyar upstairs tana tafiya a nutse, matar ta ɗago ta bita da kallo sai kuma ta ɗan yi siririn tsaki. Kai tsaye ɗakin Zahra ta buɗe ta dinga kallon ko ina ganin bata ciki ya sanya ta mayar da ƙofar ta rufe, ta juyo tana ɗan kalle-kalle corridor ɗin. Ɗakin Noor ta buɗe nan ma taga babu kowa a ciki dan haka ta dawo downstairs tana tunanin inda Zahra ta yi,
Tsaye ta same su a parlon, Zahra na kallon matar tana faɗin “okay bari na faɗawa Safeena sai ta miki” toh kawai matar ta ce, Nana ta dinga kallonta kafin ta ce“Aunty Zahra” sai a sannan Zahra ta lura da ita, ta yi murmushi tana faɗin “au Nana ke ce?” gyaɗa mata kai ta yi ta ce“na shigo ban sameki ba, shi ne naje na duba daki naga bakya nan”
“Ayyah ina kitchen ne, girki muke, zo ki taya mu”
Zahra ta yi maganar tana murmushi, girgiza kai Nana ta yi ta ce“a’a bari naje gida an jima zan dawo, daman magana nake son muyi” ɗan harararta ta yi ta ce“to ki tsaya na ƙarasa mana sai muyi maganar” satar kallon matar dake zaune Nana ta yi daga yanda ta haɗe rai dan haka ta ɗan yi murmushi ta ce“a’a zan dawo ɗin” okay Zahra ta ce dan bata son ta takura mata, ta juya ta fice daga parlon da sauri. Sai a sannan matar ta ɗago kanta ta kalli Zahra ta ce“wace wannan?”
“Nana ce fa, yar ƙanin babansu doctor, zama ki ganeta wadda nake zuwa da ita gida fa da, kawai dai ta girma ne” taɓe baki ta yi sai kuma ta ce“shi ne har take shigar miki ɗaki kanta tsaye?” ɗan juya idanu Zahra ta yi sai kuma ta ce“kai Aunty Khadijah Nana fa, ai Nana yar ɗakina ce tun ina amarya” jinjina kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh i see” Zahra bata sake cewa komai ba ta koma kitchen ɗin, tsaye ta same su suna aiki suna hira, ta ƙarasa bayan Safeena tana duba carrots ɗin da take yankawa ta ce“wato bama aikin ku ke ba hirar ku kawai ku ke abin ku” Siyama da ke tsaye gaban tukunyar da aka ɗora ta ce“kai Aunty aikin fa muke, kawai hirar ce ta zo” taɓe baki ta yi ta ce“ku dai ku ka sani” daga haka ta juya ta fice.
****
Bayan sun gama cin abincin suka kwashe kaf kayan da suka ɓata suka koma kitchen suna wankewa, Zahra ta dinga kallon Aunty Khadijah jin abin da take faɗa, murmushi kawai ta yi ta ce“anan family ɗin? Ai ko abin da kamar wuya” ɗan haɗe rai ta yi ta ce“wuya kamar yaya? Kina cikin dangi sannan ki ce ba zaki samar mata wanda zata aura ba” girgiza kai Zahra tayi ta ce“a’a nifa ba wai ba zan samar mata bane, idan Siyama ta auri ɗaya daga cikin ya’yan gidan nan zan fi kowa murna dan nasan ta samu miji wanda kowace mace ke fatan samu, amma fa kin sani su basu auren bare, i junansu suke aure” wani kallon sheƙeke Aunty Khadijah ta yi mata sai kuma ta ce“eh mana ai shiyasa naga ke an auro ki, tun da kema yar dangin ce” kallonta Zahra ta dinga yi baki buɗe, can kuma ta ce“nifa Aunty ba maganar tashin hankali ba ce wannan ko kuma cin mutunci, na auri Doctor ne saboda Allah ya ƙaddara ni matarsa ce, babu kuma wanda ya isa ya goge wannan abun”
“Eh to yanda kema ki ka aure shi saboda Allah ya ƙaddara, haka ita ma zata auri ɗaya daga cikinsu, nifa tun da daman na shirya a gidan nan nakeson Siyama ta samu miji, dan haka aiki ya rage naki, ko dai ki taimaka mata wajen samun abin da muke so ko kuma ni nayi da kaina, ai kin san ba zai gagara ba, wato kina cikin daula da arziki shi ne baki son wasu su zo su ci to wallahi baki isa ba, Sai Siyama ta auri ɗan dangin nan!”
Tashi Zahra ta yi ta bar wajen ba tare da ta sake cewa komai ba, Aunty Khadijah ta bita da harara tana fadin “sai dai ki yi, amma wallahi babu wanda ya isa ya hanata! Idan bata auri ɗan dangin nan ba sai dai idan bana raye” .
****
Dafata Maimoon ta yi ganin yanda take hawaye yasa jikinta ya yi sanyi, ta ɗan numfashi kafin ta ce“ki yi haƙuri Nana, tun da har ki ka ce kin rabu dashi to kawai ki daina ɗaga wayarsa, ki yi blocking lambarsa ta inda ba zai sake samunki ba, ballantana kuma ya faɗa miki abin da zai karya miki zuciya” Girgiza kanta ta yi wasu hawayen na sake zubowa fuskarta ta ce“na kasa jurewa ne Maimoon, na kasa mantawa dashi, idan ya kirani ta zuciyata zafi take min, I feel like na koma na ci gaba da kula shi, amma da zarar na tuna da Abba sai naji na ƙara sarewa, shin ya zan yi ne ni? Me ya sa nake cikin ruɗani? Me ya kamata na kare? Soyyayata ko kuma iyayena?”
“iyayenki!”
Maimoon ta yi maganar muryarta a dake cike da kwarin gwuiwa, jin jina kai Nana ta yi ta sanya hannunta tana share hawayenta wasu na sake zubowa ta ce“alright, zan manta da sir Junaid, zan ci gaba da bawa zuciyata haƙuri har ta saba da rashin sa, amma wallahi wata tana zuciyata zata iya bugawa na mutu, zan iya mutuwa Maimoon” rungumeta Maimoon ta yi suka dinga rera kukan tare kamar waɗanda aka yiwa mutuwa.
****
Ƙarfe 5:34 na yamma suka fito daga gidan, sai da ta rako su har wajen motarsu sannan ta ce“to Aunty ku gaida gida, a gaida min da Umma da Abba” okay Aunty Khadijah ce, ta juya zata shiga motar sai kuma ta ce“au na manta, da kin kaimu wajen uwar mijin naki ai mun gaisa” to kawai Zahra ta ce duk da ba haka taso ba, ta ce“muje” daga nan suka nufi hanyar apartment ɗin Hajiya Babba. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga sannan suka biyo bayanta, Hajiya Babba na zaune kan kujera hannunta riƙe da azkar tana dubawa, ta amsa sallamar tana ɗago kanta, har ƙasa Zahra ta durƙusa sannan ta ce“Hajiya ina yini?” fuskarta a sake ta ce“lafiya kalau Fatima” tashi ta yi tana kallon su ta ce“to ku gaisa” cikin girmamawa Aunty Khadijah ta gaisheta haka ma su Safeena da Siyama, Zahra ta ce“Yayata ce Hajiya shi ne na ce bari na kawota ku gaisa” jin jina kai Hajiya Babba ta yi ta ce“Oh Masha Allahu, y yaran?” ta yi maganar tana kallon Aunty Khadijah,
“Suna nan kalau Alhamdulillah” ta ce da murmushi a fuskarta, masha Allah kawai Hajiya ta ce sannan kowa ya yi shiru, Siyama ta dinga kallon parlon kamar idanunta zasu fito, After 2mins Zahra ta ce“to Hajiya zamu tafi” Allah ya tsare ta musu sannan ta sanya aka ɗauko musu turamen atampa vilisco Holland wadda kimaninta ya kai 240k, suka dinga godiya kafin suka bar gidan. Apartment ɗin su Zahra suka koma ta sake musu sallama sannan suka shiga mota ita kuma ta juya ta koma ciki.
Basu yi nisa a cikin estate ɗin ba, Siyama ta dinga kallonsa sai kuma ta taɓo Aunty Khadijah tana fadin
“Mom! Mom! Kin ga wannan” ta ƙare maganar tana nuna shi da hannunta, ɗan tsayawa ta yi da tuƙin ta dinga kallonsa ita ma, fitowarsa kenan daga motar ya dauko briefcase ɗinsa sannan ya nufi hanyar apartment ɗin Hajiya Babba, sai da ya shige ta gaban motar su sannan ta kalleta ta ce“ya yi miki ne?” gyaɗa kanta ta dinga yi tana murmushi ta ce“sosai ma Mom, kalleshi fa, ga kyau ga kuɗi kuma saurayi” Ɗan murmushi Aunty Khadijah ta yi ta ce“shikenan” Safeena dake baya ta ɗan yi murmushi sannan ta ce“Hajiya Aunty Khadijah to ya za’a yi ta auri wannan?” ta madubi ta kalleta ta ce“ki jira ki gani” Safeena ta yi murmushi ta ce“to shikenan” daga haka ta ja motar suka ci gaba da tafiya.
****
Bayan magrib Aunty Ramlah ta fito hannunta riƙe dana … tana kallon Amma ta ce“to shikenan yanzu yaushe zata zo?” Amma ta miƙewa.. chocolate sannan ta ce“ko gobe ne, dan yanzu ma ban ganta bane da sai ku tafi tare”
“to goben sai ta zo, ina gida ai, idan ya so sai muje na rakata” okay Amma ta ce daidai lokacin da suka ƙaraso balcony suna hango Daddyn… da ya yi parking motarsa yana kallonsu ta ce“to ku gaida gida” zasu ji ta ce sannan ta juya ita kuma Amma ta koma gida. Bata fi 3mins da zama ba Nana ta shigo hannunta riƙe da bowl, Amma ta kalleta sai kuma ta ce“sai yanzu?” zama ta yi gefenta ta ajiye bowl ɗin farfesun kayan cikin ta ce“eh ina gidan su Maimoon ma fa”
“Zahran bata nan?”
Girgiza kai Nana ta yi ta ɗauki hanta ta kai bakinta sannan ta ce“tana nan, baƙi naga ta yi, wata mata kamar yar tiktok” Amma ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“ita Zahran?” Nana ta gyaɗa kanta tana ci gaba da cin namanta, shiru Amma ta yi bata sake cewa komai ba, ta ci gaba da danna wayarta.
Da daddare tana kwance around 10:20pm wayarta ta fara ƙara, ta tashi zaune ta janyota ganin numbern Junaid ya sanya ta yi tsaki sannan ta mayar ta ajiye ta koma ta yi kwanciyarta, kiran ne ya sake shigowa ta yi banza har ya katse sannan ta lumshe idanunta, ba’a fi seconds biyu ba taji ƙarar message dan haka ta ɗauki wayar, buɗe message ɗin ta yi taga an rubuta
“Ki ɗaga wayar akwai abin da za’a faɗa miki”
Nana ta dinga kallon message ɗin fuskarta ɗauke da mamaki, abun mene ne zai faɗa mata? Kuma za’a faɗa mata? To wane kenan?. Bata gama wannan tunanin ba wani sabon kiran ya sake shigowa, ta ɗan sauke numfashi kafin ta ɗaga ta kai kunne, daga can ɓangaren aka ce
“Salamu alaikum”
Sai da gabanta ya faɗi jin ba muryar Junaid ba, murya a sanyaye ta ce
“wa’alaika assalam, sir?”
Ta yi maganar da sigar tambaya, girgiza kansa ya yi yana rike da hannun Junaid da ke kwance ya ce“bashi bane”
Da mamaki sosai ta ce“bashi bane? To wane ne? Ina yake?” ta jera masa tambayoyin hankali a ɗan tashe, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce“ɗan uwansa ne, daman kira nayi na faɗa miki bashi da lafiya, yana kwance a asibiti, sai kiran sunanki yake shiyasa ma na ce bari na kira ki”
Dafe ƙirji Nana ta yi ta sauko daga kan gadon ba tare da ta sani ba, muryarta a raunace ta ce“innalil lahi wa ina ilayhi raji’un, me ya same shi?”
“har yanzu likita bai sanar damu ainihin abin da ya same shi ba, amma dai sun ce yana da bukatar kulawa” tuni hawaye suka fara zubowa kan fuskarta kamar an buɗe famfo, ta girgiza kanta cikin shessheƙar kuka ta ce“Allah sarki, Allah ya bashi lafiya, zan zo na duba shi da safe idan Allah ya kaimu” jinjina kai ya yi ya ce“to Allah ya kaimu” Amin ta ce sannan ya kashe wayar, ta silale ƙasan rug ta fashe da kuka, kenan bashi da lafiya saboda ya rasata? Me zai same shi?.
Daren ranar haka ta ƙarasa shi cike da damuwa, ta kasa bacci sai juye-juye ta dinga yi, har aka fara kiran sallar asuba ta tashi ta gabatar da sallah, addu’a ta zauna ta dinga yiwa Junaid tana nema masa sauƙi har gari ya fara haske sannan ta tashi ta koma ta kwanta. Ƙarfe 9:20 na safe ta farka, ta tashi zaune tana mitsitsika idanunta, wayarta ta ɗauka ta kalli screen ɗin taga missed calls har uku da numbern Junaid, ji ta yi gabanta ya yi wata irin faɗuwa, ta danna call back ƙirjinta na bugu da ƙarfi, ringing ɗaya ya ɗauka a sanyaye ya ce“Assalamu alaikum”
“ya jikin nasa? Yana iya magana? Me likitan ya ce”
Ta jera masa tambayoyin muryarta na rawa, numfasawa Al-ameen ya yi ya ce“da sauƙi Alhamdulillah, yanzu zan fita naje asibitin na gan shi”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta runtse idanunta hawaye ya dinga zirarowa ta gefen idanun, jin ta yi shiru ya sanya Al-ameen ya ce“Nana”
“shikenan nima zan zo asibitin, ka faɗa min address ɗin”
Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“bari zan turo miki da text message ɗin, private asibiti ne nan gefen Jalo” toh kawai ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar, ji ta yi jikinta ya ƙara yin sanyi, me zai faru idan wani abun ya samu Junaid ta dalilinta? Ya za’a yi ta yarda? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, ta dinga rerashi har bayan mintuna ashirin. Jiki babu kwari ta tashi ta shige toilet ta yi wanka ta fito, a gurguje ta shirya cikin wata umbrella pattern Abaya black colour, ko rolling mayafin ba ta yi kawai ta yafa shi loosely, har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta dawo ta ɗauki wayarta da atm card ɗinta sannan ta juya ta fita.
Koda ta fito parlon bata samu kowa ba, dan babu alamar ma sun fito daga ɗaki, dan haka kawai ta yi waje without second thought. Tafiya ta dinga yi da sauri da sauri har ta fice daga cikin estate ɗin, ta ƙarasa gefen titi, ta ɗauki a ƙalla 10mins a wajen kafin ta samu wani napep ya kawo mutane, ta tsaida shi ta shiga sannan suka bar wajen.



