⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 12: Chapter 12

Barraks road.

Siyama ce zaune kan sofa idanunta zube kan wayarta ƙirar iphone 13pro max tana dannawa a hankali, Aunty Khadijah ta fito daga bedroom tana gyara zaman mayafin jikinta ta kalleta ta ce“zan fita idan Umma ta dawo sai ki faɗa mata” sai da ta ajiye wayar sannan ta ɗago ta kalleta, sanye take da wata embroidery Atampa ja mai adon baki, ɗinkin t-boubou wadda ta sha stones sai kyalli take, wuyanta da hannunta sanye da kayan ado na ƙarfe sai wal-wal take, Siyama ta ɗan yi murmushi kafin ta ce“Mom kin yi kyau sosai wallahi” murmushi kawai Aunty Khadijah ta yi ta ce“nima nasani, kina ji idan na fita zan biya ta gidan Hajiya Baturiya sai muga yanda za’a yi” cikin farin ciki Siyama ta ce“yauwa Mom dan wallahi tun jiya hankalina ya kasa kwanciya, idan na rufe idona fuskarsa nake gani, ji nake kamar na shirya na koma gidan yau wallahi”

“A’a kar ki je, ba yanzu ba, ki bari na dawo sai mu ƙarasa maganar” to kawai ta ce sannan ta mata Allah ya tsare ta nufi hanyar fita daga parlon ta fice, ita kuma ta ci gaba da danna wayarta.

****
Misalin ƙarfe 10:30 na safe ta ƙaraso Jabo road, dan haka ta sauka daga napep ɗin ta tsaya tana tunanin yanda za’a yi ta bashi kudi dan babu ko biyar cash a hannunta, ganin yana jiranta ya sanya ta ce“yauwa ko zan maka transfer ne na manta ina sauri ban dauko cash ɗin kuɗi ba” kallonta mai napep ɗin ya dinga yi sai kuma ya ce“to shikenan yimin” numfasawa ta yi kafin ta buɗe wayarta ta shiga Opay ɗinta ya dinga karanto mata lambobin har ta gama ta tura masa sannan ya bar wajen, kalle-kalle ta dinga yi ganin titin babu wasu mutane sosai sai ɗaiɗaikun motoci dake shigewa, ta yi dialing numbern Junaid har ta katse ba’a ɗaga ba, ɗan tsaki ta yi ta sake dialing ta kai kunne, sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga da sauri ta ce

“yauwa gani a bakin titin”

“Nana!”

Junaid ya kirata muryarsa a ɗan shaƙe, dafe ƙirji ta yi nan da nan hawaye ya kawo idanunta ta ce“sir ya jikin naka? Kana lafiya dai?” jin jina kansa ya yi yana jingina da jikin gadon ya ce“da sauƙi Alhamdulillah Nana” ajiyar zuciya ta sauke ta ce“to gani a bakin titin ya sunan asibitin?” cikin sassanyar muryarsa ya ce“Al-ameen ya fito zai tawo dake kin ji, da baki wahalar da kan ki ba” Girgiza kanta ta shiga yi kafin ta ce“ba zan iya zama ban zo na ganka ba, ba zan iya ba!” ta ƙare maganar cike da rauni, Na hannunsa na dama ya sanya ya goge hawayen daya zubo masa ya ce“shikenan Nana sai kin zo” to kawai ta ce sannan ta kashe wayar, ta dinga tunanin halin da yake ciki, koda bata ganshi ba ta san jikinsa babu daɗi, domin ba haka ya saba maganarsa ba. Tana nan tsaye har wajen 11:00 na safen kafin su ƙaraso titin, kasancewar ana rana ya sanya ta ɗan ja mayafin Abayar jikinta ta rufe gefen fuskarta. A gabanta motar ta yi parking ya sauke glass ɗin yana kallonta ya ce“shigo muje” duk da bata san shi ba amma ta gane shi ne wanda ya zo ɗaukanta, dalilin muryarsa da taji, dan haka ta karasa ta buɗe passenger seat ɗin motar ta shiga sannan ta rufe, kallonta ya dinga yi a hankali kuma ya ce“sannu ko” yauwa kawai ta ce dan hankalinta gaba ɗaya yana wajen Junaid, shima bai sake cewa komai ba ya yi reverse ya bar wajen. Tafiya kusan 10mins ta kwo su bakin asibitin The Medicare, ya yi horn aka buɗe gate ɗin sannan ya zura hancin motar ciki, a parking space ɗin asibitin ya yi parking sannan ya sauka ita ma ta buɗe gefenta ta fito ta tsaya tana ƙarewa babban asibitin kallo,

“muje ko”

Maganar ta dawo da ita daga tunanin data tafi, ta jinjina kanta sannan ya yi gaba tana biye dashi, cikin vip suka shiga ita dai sai kallon wajen take har ya buɗe wani daki ya shiga, bin bayansa ta yi ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Junaid ne zaune tsakiyar gado ya jingina kansa da ƙarfen gadon idanunsa a lumshe, kallonsa ta dinga yi ganin yanda ya rame cikin kwanaki kaɗan, ya yi baƙi kamar ba shi ba, Alameen ya ƙarasa gabansa ya taɓa shi a hankali ya ce“Junaid gata” buɗe idanunsa ya yi a hankali kai tsaye kuma akanta ya sauke su, ya dinga kallonta ganin yanda ta yi kyau abin ta kamar babu abin da ke damunta, murmushin ƙarfin hali ya yi mata kafin a sanyaye ya ce“Nana”

Ƙarasowa wajen ta yi a hankali ta tsaya jikin gadon still looking at him ta ce“sir sannu, ya jikin naka?”

”Alhamdulilah Nana, naji sauƙi sosai” ya ce shima yana kallonta, shiru ta yi bata sake cewa komai ba, ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan fuskarta, girgiza kai Junaid ya yi ya ce“mene ne haka Nana? Stop crying mana” kamar jira take kawai ta fashe da kuka, ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, kasa hanata ya yi, ya dinga kallonta dakyar kuma ya iya cewa“Nana kina son wani ciwon na daban ya sameni?” girgiza masa kai ta yi ba tare da ta kalleshi ba, ya ce“to zauna ki daina kukan” Zama ta yi gefen gadon kamar babu laka a jikinta, ta kifa kanta bisa cinyarta ta ci gaba da kukanta a hankali. Juyawa Al-ameen ya yi ya bar dakin, Junaid ya numfasa sannan ya ce“Nana ɗago kan ki na ce” rage kukan ta fara yi a hankali sannan ta ɗago kan nata bayan ta goge hawayen ta kalleshi cikin shessheƙar kuka ta ce

“ka yi haƙuri sir, ka yi haƙuri, ban gaza ba wallahi, amma babu yanda zan yi ne, ba zan bijirewa iyayena ba, i can’t ruined my father’s image, ba zan iya ba!” ta ƙare maganar tana kecewa da wani sabon kukan, numfasawa ya yi sannan ya ce“Na sani Nana, na san ba laifinki bane, nima kuma ban riƙe ki ba, dan haka ki daina wannan kukan dan Allah kin ji” sake goge hawayen ta yi sannan ta ce“to me ya sa baka da lafiya? Mene ya sameka?” murmushi ya yi ya ce“bafa wani abun bane, zazzaɓi ne kawai nake, kin ji kar ki damu kan ki” kallonsa ta dinga yi kafin ta ce“ni nasan ba zazzaɓi bane, zazzaɓi ba zai saka ka dinga kiran sunana ba! Wani abun ne dai yake damunka ka ke son ka ɓoye min” girgiza kansa ya yi still smiling ya ce“kin san ai bana ɓoye miki abu, so ki yarda dani kin ji, na samu sauƙi Alhamdulillah” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce“shikenan, Allah ya ƙara sauki” sosai ya ji daɗi ganin ta haƙura ya ce“Amin Nanata, yanzu bari na akawo miki abu mai sanyi ki sha ya sauƙaƙa zuciyar” ya ƙare maganar yana kashe mata idanu, murmushi ta yi ta ce“babu abin da zai sauƙaka zuciyata face na ganka cikin farin ciki” waro idanunsa ya yi ya ce“da gaske?” gyaɗa kanta ta yi a hankali ya ce“tom shikenan, nima ina son naga kina farin ciki Nana Khadijatou” kafin ta yi magana ya buɗe kofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, amsawa suka yi sannan ya ƙaraso hannunsa riƙe da drinks da ruwa ya ce“kun gama kukan masoya?” sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, Junaid ya ce“kai zan maka rashin mutunci” harararsa ya yi ya ce“malam kaji da kanka kaji” ya ƙare maganar yana dariya, robar coke ya miƙawa Nana ya ce“Amarya ga drink ki sha ko kya samu sauƙi” Amsa ta yi tana murmushi ta ce“okay thanks alot” jinjina kansa yayi sannan ya miƙawa Junaid ɗin ya ce“bawan Allah kai ma gashi” karɓa shima ya yi ya ce“to Allah ya maka albarka yaron arziki” buɗe baki ya yi yana kallonsa sai kuma ya yi kwafa ya ce“zaka gane ne wallahi” daga haka ya juya ya fice daga ɗakin. Da idanu Nana ta bishi sai kuma ta mai da Idanunta kan Junaid ta ce“abokin ka ne?” gyaɗa mata kai ya yi yana bude robar hannunsa ya ce“childhood friend ɗina kenan, tare muka yi karatu a Paris” gyaɗa kanta ta yi ta ce“Allah sarki, yana da kirki”

“eh sosai kuma yana da barkwanci, let me help you” ya kare maganar yana miƙo mata hannu, robar ta miƙa masa ya buɗe mata sannan ya bata ta ɗan yi murmushi ta ce“thank you” taɓe baki ya yi ya ce“sannu to” she just smile sai kuma ta kai robar bakinta ta kurɓa, kallonta ya dinga yi sai kuma shima ya sha nasa sannan ya ce“ina Amma”

“tana nan kalau, ban ma faɗa mata ba fa na fito” ta yi maganar da iya gaskiyarta, zaro idanu ya yi sai kuma ya ce“but why Nana?” kwaɓe fuska ta yi ta ce“zan fito sai naga bata parlon maybe ma bacci take, that’s why yasa kawai nayi fitowa ta”

“yanzu idan ki ka koma sai ki ce mata kin je ina?” ya yi maganar da sigar tuhuma, shiru ta yi can kuma ta ce“kawai zan ce ina Apartment ɗin Hajiya Babba, ba zata ce komai ba” girgiza kansa ya yi sai kuma ya ce“kar ki sake irin haka Nana, babu kyau” toh ta ce a sanyaye, sai kuma shiru ya biyo baya, ta dinga sipping lemon hannunta a hankali har ta kusa shanyewa.

****
Da ɗan mamaki Abba ya ce“to ina taje?” Girgiza kai Amma ta yi ta ce“wallahi ban sani ba, amma maybe tana Apartment ɗin su Maimoon dan nan ne wajen zuwanta, ko kuma wajen Zahra” wayarsa ya zaro a aljihu ya ce“but it’s getting late fa, kusan ƙarfe 2pm bata dawo ba” zama ta yi kan sofa tana faɗin “haka take, sai ta yini a can fa, ko jiya bata dawo ba sai dare” Abba bai sake cewa komai ba ya juya ya fita, ta bi shi da kallo sai kuma ta ɗauki wayarta, lambar Ramlah ta yi dialing ringing ɗaya ta ɗauka daga ɗaya ɓangaren Aunty Ramlah ta ce“Yaya ina yini?” Amma ta ce”lafiya kalau Ramlah ya ku ka je gida?”

“Alhamdulilah”

Ta yi maganar tana ajiye plates ɗin data ɗebo, jinjina kai Amma ta yi bata ce komai ba, Aunty Ramlah ta ce“au Yaya naji Nana shiru bata zo ba” ɗan siririn tsaki ta yi sannan ta ce“yo bana manta ba, ita kuma ta tafi yawon magana tun safe har yanzu ban ganta ba” murmushi Aunty Ramlah ta yi ta ce“oh Nana sabga, to ko gobe sai ki turo ta” to kawai Amma ta ce sannan suka ci gaba da wata hirar.

****
Al-ameen ya dinga kallonta ganin yanda take bacci sai kuma ya kalli Junaid ya ce“yanzu mene ne abu na gaba?” murmushi kawai Junaid ya yi sannan ya ƙarasa kan gadon ya ɗan janye mayafin data rufe fuskarta dashi, kallon kyakkyawar fuskarta ya dinga yi yana murmushi kafin a fili ya ce“sai abin da na shirya” ya kare maganar yana dariya, dariyar shima Al-ameen ya yi ya ce“kaya ya zo hannu” ɗan haɗe rai Junaid ya yi kafin ya ce“kai wannan ba kaya ba ce, kadara ce malam!” tuntsirewa da dariya ya yi ya ce“to naji” janye mayafin kanta ya yi nan take lallausan gashinta ya bayyana akan gadon, ya ɗan suɗe down lip ɗinsa ya ce“ke tawa ce Nana, kuma babu wanda ya isa ya rabani da ke, ke ɗin mallakina ce, ni kaɗai, ni kaɗai NAANAH!”.

Amma ce tsaye tsakiyar parlon tana kallon Ummi ta mamaki ta ce“what? Bata zo nan ba? Nana bata zo nan ba tun safe?” girgiza kai Ummi ta yi tana kallonta cike da damuwa ta ce“bata zo ba, ni rabonda na ganta tun jiya da daddare” dafe ƙirji Amma ta yi, lokaci ɗaya wata matsananciyar faduwar gaba ta risketa, to ina Nana ta tafi?.

“ko dai taje wajen Zahra?”

Girgiza kai ta yi kafin ta ce“a’a bata je ba, dan ɗazu ma Zahra ta shigo take tambayar ina Nana take, shiyasa ma na fito” Ummi taja numfashi kafin ta ce“to ina yarinyar nan ta shiga dan Allah? Ko wani wajen ta tafi da taga yamma ta yi ba sai ta dawo ba?” Kwafa kawai Amma ta yi sannan ta juya ta bar parlon da sauri, da idanu Ummi ta bita sai kuma ta ce“kai Allah ya shirya mana yaran nan”

Koda ta koma gida zaune ta sami Abba kan sofa hannunsa riƙe da jarida yana dubawa a hankali, ganin yanda ta ɗan birkice yasa ya ce“lafiya da Rabi’a?” girgiza kanta ta yi jiki a sanyaye ta ce“babu komai” daga haka ta nufi daƙinta ba tare da ta sake kallonsa ba, shima bai damu ba ya ci gaba da abin da yake. Tana shiga ɗaki ta zauna gefen gado muryarta na rawa ta ce“Allah ka dawon da yarinyar nan lafiya koma ina ta tafi, Allah kada ka ɗora mana abin da ba zamu iya ba, Allah ka bata ikon dawowa gida cikin ƙoshin lafiya”

“Ina Nanan ta tafi? Bata wajensu Yaya?”

Abba ya yi maganar yana daga tsaye a gefen ƙofa, kallonsa ta yi da fuskarta wadda hawaye ya fara zubowa ta ce“bata can, sun ce bama taje ba kwata-kwata”

Da matuƙar mamaki yake kallonta sai kuma ya ce“and shi ne baki faɗa min ba? Kina cikin hankalinki kuwa? What idan wani abun ya samar min ƴa?” buɗe baki ta yi zata yi magana ya ɗaga mata hannu da sauri, ta dinga kallonsa ganin yanda ya haɗe rai, lokaci ɗaya kuma ya juya ya bar dakin a fusace.

****
A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda take jin sun yi mata nauyi, ta dinga kallon cealing ɗin ɗakin ba tare da ta gane inda take ba, da sauri kuma ta miƙe zaune tana ƙarewa ɗakin kallo, bacci ta yi anan? how and why? Ta tambayi kanta, kwayayen data gani a kunne shi ne ya tabbatar mata da cewa dare ya riga da yayi, lokaci ɗaya ta tuna da abin da ta zo yi dan haka ta ɗora hannunta aka cikin tashin hankali ta ce

“na shiga ukuna!”

Ta sauka daga kan gadon da sauri tana ɗaukan mayafinta dai dai nan ya buɗe ƙofar ya shigo, kallonsa ta dinga yi ganin kamar bashi ba, yana sanye da wata polo t-shirt red colour sai trouser black, murmushi ya yi ya ce“kin tashi?”

“ƙarfe nawa yanzu? Na shiga uku me zan ce a gida?” ta ƙare maganar hawaye na zirarowa kan kuncinta, numfasawa Junaid ya yi ya ce“yanzu kusan 7:20pm, naso na tashe ki sai kuma naga kamar bai dace ba, that’s why yasa na bar ki”

Wani irin kallo ta dinga yi masa sai kuma ta ce“daka tasheni ai, yanzu me zance a gida?”

Girgiza kai Junaid ya yi ya ce“ki bar wannan maganar ki tawo na mai da ki, kar daren ya sake yi”

Wayarta ta ɗauka sannan ta yi waje kamar zata tashi sama, wani kyakkyawan murmushi ya yi kafin ya bi bayanta. Tun da suka fara tafiya take kuka kamar ƙaramar yarinya, shi dai bai ce mata komai ba, kuma bai yi yunƙurin hanata kukan ba, ya dinga driving ɗinsa a hankali time to time yana ɗan murmushi.

****
Abdusammad ya dinga kallon Abba can kuma ya ce“to daman tana fita ba’a sani ba?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“nima ban sani ba wallahi, koma mene ne ai laifin uwarta ne da har zata bari ta fita bata sani ba, yarinya kamar Nana a ce ta kai har yanzu a waje, to ina ma ta sani ballantana taje?” Abba ya ƙare maganar yana sauke wani zazzafan numfashi, ko ba’a faɗa ba kasan ransa ya gama ɓaci, ɗan dafa shi Abdusammad ya yi ya ce“calm down dan Allah kada wani abun ya sameka, bari naje wajen Hajiya Babba ko taje can” saurin riƙe hannunsa Abba ya yi ya ce“a’a kar ka sanar mata, ban son hankalinta ya tashi, shiyasa ban bari an sanar da ita ba” shiru Abdusammad ya yi can kuma ya ce“alright ka koma gida, zan dawo da ita in sha Allah” jinjina masa kai kawai Abba ya yi sannan ya saki hannunsa ya nufi balcony ɗin gidansa, sai da yaga ya shige ciki sannan ya sauke numfashi ya juya shima ya bar wajen..

****
Zaune ya same su a parlon suna faman hira, yana shigowa kowacce ta yi shiru murya can ƙasa suka ce“sannu da zuwa Uncle” bai amsa ba, sai kallo daya dinga bin su dashi wanda ya sanya suka sunkuyar da kawunansu, harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana tawowa toward them ya ce“ina Nana take?”

Da sauri suka kalleshi sai kuma suka sake sunkuyar da kai, ya jinjina kansa sannan ya sake cewa“okay, ba zaku faɗi inda take ba ko? Then zan yi maganinku duka yanzun” ɗago kansu suka yi, kowacce ta dinga girgiza kanta dan ba ƙaramin tsoronsa suke ba, Maimoon da tafi kowa firgita ta ce“wallahi tallahi uncle ban sani ba, ni ban ma ganta ba yau, ban san ma bata gida ba” ta ƙare maganar tana girgiza hannunta, kallonta ya dinga yi rai a haɗe, lokaci ɗaya kuma ya mayar da idanunsa kan Hameeda, girgiza kanta tayi cikin sanyin muryarta ta ce“uncle ban ganta ba wallahi, rabon da naga Nana an fi kwana uku ma, bata fitowa yanzu” taɓe baki ya yi sannan ya kalli Amrah wadda taƙi ɗago kanta, ganin yanda take rawar jiki ya sanya ya daka mata tsawa wadda ta firgita su duka ya ce“ina Nana take?”

“wallahi ban sani ba, ban sani ba Uncle, bama magana da ita dan haka bata zuwa inda nake, ban san inda take ba wallahi” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Numfasawa ya yi dan ya tabbatar basu san inda take ban, ya juya ya fice daga parlon ba tare da ya sake ce musu komai ba, dafe ƙirji Maimoon ta yi a fili ta ce“wallahi Allah ya isana ba zan yafewa Nana ba data sanya aka ɗaga min hankali” girgiza kai Hameeda ta yi ta ce“mene haka? Ki ka sani ko wani uzurin ne ya fitar da ita?”

“Na rantse da a ce na san inda ta tafi sai na faɗa masa, to dan dai kawai ban sani bane” Amrah ta yi maganar cikin ɓacin rai, harararta Hameeda ta yi ta ce“saboda ba zaki iya rufawa yar uwarki asiri ba?”

“ai ita ba wadda za’a rufawa asiri ba ce, ke kina ganin da a ce kece ba zata faɗa ba?” Hameeda ta gyaɗa kanta ta ce“eh wallahi, ni nasan da ni ce Nana ba zata taɓa faɗa ba, ke koma ta san yawo na tafi ba zata faɗa ba, saboda bata da baƙin hali” daga haka ta tashi ta fice daga parlon. Da harara Amrah ta bita kafin ta ce“ai daman ni ce mai baƙin hali, naji ɗin to, wallahi sai na faɗa?” Ita dai Maimoon shiru ta yi tana tunane-tunane cikin ranta.

****
Ƙarfe 7:45pm ya yi parking a bakin estate ɗin, ganin bata ma san sun zo ba ya sanya ya juyo ya ɗan kalleta murya a sanyaye ya ce”Nana mun zo fa” janye mayafin data rufe fuskarta ta yi, ta ɗan kalleshi da kumburarrun Idanunta sai kuma ta buɗe motar ta sauka ba tare da ta ce komai ba ta nufi gate ɗin estate ɗin jiki a sanyaye. Ajiyar zuciya Junaid ya sauke sannan ya juya ya bar wajen lokacin da yaga ta shiga, koda ta shiga ciki bata samu kowa ba, dan daman i wannan lokacin ba’a fiye samun jama’a ba kasancewar akwai sanyi a garin, kowa yana cikin gidansu, ta dinga tafiya kamar wadda aka cirewa laka har ta ƙaraso bakin balcony ɗinsu, banda faɗuwa babu abin da gabanta ke yi, tunanin ɗaya abinda zata ce dasu Amma idan ta shiga ciki, dan haka ta ɗan tsaya tana sauke numfashi da sauri da sauri.

“Nana!”

Sai da taji sautin zuciyarta ya ɗan buga saboda tsoron da taji, ta juyo a hankali idanunta ya sauka akan Maimoon da ke tsaye sanye da hijabi, kallonta ta dinga yi sai kuma ta ce“ina ki ka je Nana?” kasa bata amsa ta yi sai kawai ta faɗa jikinta ta rungumeta tana kuka a hankali, tsoro da fargaba ne suka ziyarci Maimoon, ta ɗago fuskarta tana tattaba jikinta ta ce“kina lafiya dai?”

“Tsoro nake ji Moon, tsoro nake ji wallahi!”

Ta yi maganar cikin kuka, kallonta Maimoon ta dinga yi sai kuma taja hannunta suka fara tafiya, ita dai Nana sai bin ta take da kallo ba tare da ta san inda suka nufa ba. A bakin apartment ɗin Hajiya Babba ta tsaya ta kalleta murya can ƙasa ta ce“Hajiya ce kawai bata san bakya nan ba, dan haka ki shiga ki salallaɓa ki shige ko ɗakinta ne ki kwanta, ki cire wannan rigar ta jikin ki sannan kada ki nuna ba’a nan ki ka yini ba, ki ce baki da lafiya ne, ni kuma zan je na karbo abinci a wajen Ummi idan na shigo zan zo na taso ki kin ji” gyaɗa kanta kawai ta dinga yi still crying ta ce“to idan kuma Hajiyar tana ɗakin fa?” sai da ta kalli compound ɗin ta tabbatar babu kowa sannan ta ce“tana parlon, yanzu zan shiga na sanya ta shiga kitchen sai ki shigo kin ji” to kawai ta ce sannan Maimoon ta nufi ƙofar parlon ta murɗa handle ɗin a hankali, Hajiya Babba na zaune kan sofa tana cin abinci a hankali, Maimoon ta ƙarasa tana murmushi ta ce“hajiya Babbarmu” kallonta kawai ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“kin zo ki hana ni cin abinci ko?” kitchen Maimoon ta nufa tana faɗin“ni na isa na hanaki cin abinci, kawai nama zan ɗauka” zumbur Hajiya ta tashi tsaye tana kallonta ta ce“kar ki taɓa min abu a kitchen kin ji ko” ko saurarenta Maimoon bata yi ba ta shige kitchen ɗin tana dariya, ganin haka ya sanya itama Hajiyan ta bita da ɗan saurinta tana faɗin “yau naga tsiya da wasali!” Nana data kasa kunne tana saurarensu ta tura ƙofar a hankali ta shiga, ganin babu kowa a parlon ya sanya ta cire takalman ƙafarta ta kwasa da gudu ta yi sama. Hajiya Babba ta kwace robar dambun naman tana faɗin “fita ki bani waje” kwaɓe fuska Maimoon ta yi ta ce“kai Hajiya duk kin fi son Nanar nan haba!” daga haka ta fito daga kitchen ɗin tana leƙan parlon, ko tsayawa ba ta yi ba ta nufi hanyar fita daga parlon ta fice abin ta, ta dinga kallon balcony ɗin ganin babu Nana ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nufi hanyar gidansu da sauri.

Tana hawa saman ta shige ɗaya daga cikin bedrooms ɗin saman wanda ta tabbatar ba anan take kwana ba, ta ajiye wayar gefen madubi sannan ta nufi toilet da sauri, wanke fuskarta ta fara yi sannan ta ɗauro alwala ta fito, ta sake naɗa mayafin akan ta sannan ta fara gabatar da sallolin da ake bin ta. Bayan ta idar da sallar ta tashi ta fice daga ɗakin a hankali ta shiga ɗakin Hajiya Babba ta buɗe press ɗinta, kasancewar tana ajiye kayanta a ɗakin ya sanya ta ɗauko wasu riga da wando na bacci ta mayar ta rufe sannan ta fice da sauri. Ɗakin ta koma ta cire Abayar jikinta ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta sanya kayan, ta naɗe Abayar da mayafin ta tura ƙasan gadon sannan ta hau kan gadon ta kwanta har da jan duvet ta rufa..

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *