⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 15: Chapter 15

Fitowarta kenan daga toilet taji ringing ɗin wayarta, ta ƙarasa kan drawer tana kallon mai kiran, sabuwar number ce dan haka ta goge ruwan hannunta sannan ta dauki wayar, Muryar wanda taji ya sanya ta runtse idanunta, lokaci ɗaya ta ji zuciyarta na wani bugawa da ƙarfi, cikin sanyin murya Junaid ya ce

“tun ɗazu ina ta kiran ki da lambata shi ne ba zaki ɗaga ba ko Nana?”

Shiru ta yi masa, bai damu da shirun nata ba ya ci gaba da faɗin

“shikenan faɗa min kin sauya shawara ko kuwa har yanzu kina nan akan waccan maganar ta ki?”

Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dake ta ce

“Eh ban sauya ba, ko da kana tunanin zan sauya ne? To ka sani har abada ba zan taɓa sauyawa ba! Ba zan dawo gareka ba! Na bar ka, bari irin na har abada”

Lumshe idanunsa ya yi nan take hawaye suka zubo daga cikinsu, ya jinjina kansa yana ƙoƙarin saita kansa ya ce“okay, shikenan Nana, Allah yasa haka ne mafi Alkhairi, sai dai ina neman wata alfarma a wajen ki koda zata zama alfarma ta karshe da zaki iya min”

Ban da hawaye babu abin da Nana take, ta jinjina kanta cikin shessheƙar kuka ta ce“ina ji”

“Akwai wani hanky da ki ka taɓa bani kin tuna? To ina son na dawo miki dashi ne, ina waje ko za ki iya fitowa ki karɓa?”

Shiru ta yi kamar me tunani can kuma ta ce

“okay”

Daga haka ta katse wayarta, hijabi ta ɗauka har ƙasa ta saka sannan ta fito daga dakin, koda ta zo parlon bata samu kowa ba dan haka kawai ta yi waje abin ta, da sauri ta dinga tafiya har ta ƙaraso wajen estate ɗin. Ta yiwa mai gadin wajen murmushi da yake mata magana sannan ta ce“bari na karbo sako” to ya ce sannan ta buɗe gate ɗin ta fita.

Tsaye ta hangi wata Camry blue colour ta yi parking sai sheƙi take, kamar me tsoron ƙasa haka ta dinga takawa har taje gaban motar, Junaid ya buɗe driver side ɗin ya fito ya zagayo inda take yana kallonta, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, ya jingina da motar yana murmushin ƙarfin hali ya ce“Nana kin rame” kallonsa ta sake yi a ranta ta ce

“har kura ce zata cewa kare maye?”

Dan shima ya ƙaramar rama ya yi ba, a fili kuma ta ce“bani zan tafi” ɗan murmushi ya sake yi ya ce“ba zamu gaisa ba?”

“idan babu abin da zaka bani zan koma ciki dan ina da abin yi”

Ta yi maganar a ɗan fusace, numfasawa ya yi sannan ya buɗe side ɗin da yake tsaye ya dauko yar ƙaramar jakar, juyowa ya yi ya miƙa mata yana kallonta, amsa ta yi itama tana kallonsa ta dinga kallon yar kit ɗin wadda aka yi cealing ɗinta da fari yanki da kuma wasu flowers jajaye, ta dinga kallon kit ɗin dan har ta manta da ita ma, Above 2mins kafin ta ce“sai an jima” jinjina kansa kawai ya yi sai kuma ya ce

“Allah ya haɗa kowa da Alkhairinsa, amma ni nasan ni ne alkharinki Nana” kallonsa ta yi sai kuma ta juya ta yi gaba ba tare da ta bashi amsa ba. Ya tsaya yana kallonta har ta shige ciki sannan ya sauke numfashi shima ya zagaya ya shige motarsa ya bar wajen.

Koda ta koma apartment ɗin Zahra bata samu kowa ba kamar ɗazu dan haka ta haye sama da sauri ta koma ɗakin da take, tana shiga taji wayarta ta yi ƙara alamar message ya shigo, sai da ta zare hijabin jikinta ta ajiye gefen gado haɗe da kit ɗin data karbo sannan ta ƙarasa ta dauki wayar, Junaid ta gani a jikin numbern dan haka ta buɗe sakon gaba ɗaya

_Nana kenan, kin ɗauka zan iya rabuwa da ke haka cikin sauƙi? Kin ɗauka ban san me nake ba, ban fara son ki dan na barwa wani ke ba, ina sonki ne dan na rayu da ke, ina son ki kalla saƙon dana baki da kyau kafin ki yankewa kan ki hukuncin, amma ki sani ba zan taɓa yarda ki bar ni ba, komai runtsi komai walaha ke tawa ce, tawa ni kaɗai NAANAH!_

Nana ta dinga kallon saƙon da wani irin mamaki, me yake nufi to? Wace magana yake? Girgiza kanta ta yi da sauri kuma ta kalli inda ta ajiye kit ɗin data shigo da ita, cikin hanzari ta ƙarasa gaban gadon ta zauna sannan za jawo kit ɗin ta fara buɗeta a hankali, har ta gama buɗewa gabanta faduwa yake, ta zaro hanky ɗin da yake magana sai ƙamshin turare yake, kallonsa ta dinga yi tana jujjuya shi, a fili ta ce“to me yake nufi?” sai kuma ta ajiye shi a gefe tana ƙoƙarin tashi idanunta ya sauka akan envelope ɗin da take cikin. Ƙura mata idanu Nana ta yi kafin ta sanya hannunta na dama ta ɗaukota, haka kawai ta ji gabanta yana wani irin faɗuwa, ta runtse idanunta a hankali ta ce

“Ya Allahu”

Ta sauke numfashi kafin ta fara ƙoƙarin buɗe envelope ɗin bugun zuciyarta na sake tsananta, hannunta ta sanya ciki tana taɓa takardun dake ciki, da mamaki ta janyo su duka tana sake ware idanunta dan ganin mene ne a ciki, wata irin zabura Nana ta yi ta miƙe tsaye jikinta ya fara wani irin rawa kamar ana kaɗa ganga, baki buɗe take kallon hoton wanda ya kasance hotonta ne kwance kan gado daga ita sai ƙaramar vest wadda bata kai ga rufe cibiyarta ba, sai ɗan ƙaramin underwear, kanta a buɗe babu dankwali.

Ta durƙushe a ƙasa tana wani irin numfashi dan tsabar tashin hankali kuka ya gagara zuwar mata, hannunta na rawa ta janye hoton inda na biyunsa ya bayyana kuma wanda ya fishi muni, hotonta ne da waccan shigar wannan karon ma a kwance sai dai a kusa da ita Junaid ne daga shi sai boxer, ta sanya hannunta ta rufe bakinta jin wani irin kuka yana neman tawo mata. Haka ta dinga buɗe hotunan ɗaya bayan ɗaya har ta kai ƙarshe, lokaci ɗaya ta yi jifa da hotunan tana sakin wata irin matsananciyar ƙara, dai dai lokacin Zahra ta shigo ɗakin da sauri tana kallon ta ta ce“Nana lafiya mene ne?”

Bata iya bata amsa ba sai wani irin numfarfashi take, ganin haka yasa Zahra ta ƙarasa inda take durƙushe da sauri ta dafata tana faɗin “mene ne Nana? Meke damunki? Baki da lafiya ne?” madadin ta bata amsa sai kawai taga ta faɗo jikinta a sume, Zahra ta dinga jijjigata cikin tashin hankali tana faɗin

“ke Nana! Mene ne? Me aka miki?”

Ganin bata san ma tana yi ba ya sanya Zahra ta kwantar da ita a ƙasa ta tashi da sauri ta fice daga ɗakin, ba’a jima ba ta dawo hannunta riƙe da rogar ruwa mai sanyi, ta ƙarasa inda take sannan ta buɗe robar ta ɗan yayyafa mata ruwan, ajiyar zuciya Nana ta sauke ba tare da ta buɗe idanunta, Zahra ta ajiye ruwan a gefe sannan ta ɗagota tana cewa“mene ne Nana? Meya faru? Ke da wa?” Bata ce komai ba, dan babu alamar ma tana fahimtar abin da Zahran ke cewa, Banda numfarfashi babu abin da take. Zahra ta rasa yadda zata yi da ita, dan haka ta tashi da niyyar ɗaukan wayarta ta kira Abdusammad, Sai dai takardar da taji ta taka a ƙasa ya sanya ta kalli wajen da sauri, da mamaki take kallon farar takardar dan hoton a kife yake, ta ɗan sunkuya ta ɗauko sannan ta juya shi, saurin ja da baya ta yi ta riƙe gefen dresser ta dinga kallon hoton baki buɗe, lokaci ɗaya kuma ta mai da Idanunta kan Nana da ke kwance gefe, girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa kan fuskarta, ta yi wurgi da hoton sai kuma ta sake kallon ƙasa sai a sannan taga tarin hotunan dake warwartse a wajen, ta bi kowanne ta ɗauko sannan ta ajiye gefen drawer ta koma kusa da Nana ta zauna tana kuka ta ce“Nana garin Ya ya? Me ya sa? Me yasa zaki yiwa kan ki haka? Me yasa?” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka, Kasa cewa komai Nana ta yi sai wani irin kuka daya kwace mata, ta ɗora kanta kan cinyar Zahra ta dinga rera kuka kamar ranta zai fita. Kasa hanata Zahra ta yi dan ta san akwai buƙatar ta yi kukan duk da ba shine mafitarta a yanzu ba, Kusan mintuna goma kafin ta fara rage sautin kukan nata, Zahra ta ɗago kumburarrun Idanunta ta kalleta cikin kuka ta ce“Akan me ki ka yi haka Nana? Yaushe haka ta faru? Meya sa?”

Ɗago kanta ta yi daga jikin Zahra, ta kasa kallonta dan har sannan hawaye basu bar zuba kan fuskarta ba, Zahra ce ta yi ƙarfin halin sanya hannunta ta fara goge mata hawayen, kafin ta ce“ki daina kuka dan ba shi ne mafita ba a yanzu ki faɗa min ya aka yi haka?”

Tana ƙoƙarin magana wayarta ta shiga ringing dan haka ta kalli wajen a tsorace sai kuma ta tashi da sauri ta ƙarasa inda ta yar da wayar ɗazu ta ɗauka, Sunan Junaid ne akan screen ɗin dan haka ta ɗaga wayar da sauri bakinta na rawa ta ce

“Sir…sir dan Allah… Allah dan girman Allah kada ka yimin haka kaji kada ka yi haka dan Allah”

Murmushi Junaid ya yi yana kallon titi ya ce

“Me nayi miki Nana? Kin ga saƙona ne?”

Fashewa ta yi da wani sabon kukan tana girgiza kanta ta ce

“Dan Allah kada ka bari wani ya ga hotunan nan, dan Allah kada ka tozarta min rayuwa, ka yi haƙuri dan Allah..”

Dariya sosai Junaid ya yi kafin lokaci ɗaya ya haɗe rai cikin kakkausar murya ya ce

“Ai daman babu wanda zai gani Nana, ya za’a yi na bari wani ya ga lalatattun hotunan ki? Ai ba zan bari ba daman, idan har kin bi abin da zan faɗa miki babu wanda zai ji kuma ya gani, amma idan har ki ka kasa yimin biyayya to ki sani ina da irinsu-irinsu copy biyar, zan sake su a duniya kowa ya gani, kin ga ba iya ke kaɗai ba shi kansa dangin da ki ke taƙama dashi saina lalata shi wallahi tallahi kin ji har na rantse Nana!”

Sakin wayar ta yi ta faɗi ƙasa, ita kuma ta silale a hankali ta yi zaman daɓaro akan tiles, Zahra ta dinga kallonta daga inda take zaune, ganin yanda take hawaye kamar an buɗe famfo ya sanya ta taso ta dawo kusa da ita ta riƙeta tana cewa“me ya ce miki Nana?”

Kasa cewa komai ta yi sai kawai ta tashi ta shige toilet da sauri, Zahra ta bita da kallo sai kuma ta tashi itama ta kwashe pics din ta mayar dasu cikin envelope ɗin sannan ta fice daga ɗakin.

****
Siyama ta dinga kallonsa tana murmushi kafin a hankali ta ce“ai na ɗauka ba zaka zo ba” Safwan da ke tsaye jikin motarsa ya girgiza kansa yana murmushin shima ya ce“haba dai naƙi zuwa, ai na ɗauka har yamma zaku kai a gidan namu” langwaɓar da kai ta yi ta ce“eh ai da yamman muka so kai wa amma sai aka ɓata mana rai” da ɗan mamaki ya ce“wane ya ɓata muku ran kuma?” taɓe baki ta yi ta ce“wata yarinya ce, ta ɗan zagemu to gudun mu ya hatsaniya da ita ya sanya kuma tawo kawai” Gyara tsaiwarsa ya yi sannan ya ce“yarinya kuma? Wace yarinya?”

Shiru ta yi tana kallonsa can kuma ta ce“wai ko Nana naji suna ce mata, yauwa ita ce ma yarinyar da zaka aura ko?”

Kallonta ya dinga yi bai ce komai ba, ta ɗan yi murmushi sai kuma ta ce“naga ka yi shiru” Girgiza kansa ya yi yana faɗaɗa fuskarsa ya ce“bakomai, ita Nanan ce ta zageku?” gyaɗa masa kai ta yi ya ce“okay I’ll talk to her, ki yi haƙuri kin ji” jinjina kanta ta yi ta ce”bakomai Yaya ai na haƙura tun da dai ƙanwar ka ce” Safwan ya ɗan yi dariya ya ce“to ya garin?” kamar jira take ta fara masa hira babu kama ƙafar yaro, y dinga murmushi yana saurarenta wani ya tanka ta wani kuma ya yi shiru.

****
Bayan sallahr magriba Zahra ta buɗe ɗakin ta shigo hannunta riƙe da tray, Nana na zaune ƙasan gado ta ɗora kanta gefen gadon sai hawaye take, karasowa ta yi ta ajiye tray ɗin gefe ɗaya sannan ta kalleta a sanyaye ta ce“Nana” shiru ta yi mata, dan haka ta sake kiran sunanta, nan ma bata amsa ba, Zahra ta dinga kallonta sai kuma ta kai hannunta ta taɓata ta ce“Nanaa!”

A ɗan firgice ta ɗago kanta, sai kuma ta goge hawayenta ta ce“Na’am Aunty”

“ki tashi ki ci abinci kin ji”

Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan kuncinta ta ce“naƙoshi aunty” Zahra ta dinga kallonta cike da tausayawa sai kuma ta ce“a’a Nana baki ƙoshi ba, zo ki ci abinci” sake girgiza kanta ta yi ta ce“wallahi bana jin yunwa, ba zan iya cin abinci ba Aunty” shiru Zahra ta yi can kuma ta numfasa ta ce“Nana faɗa min garin ya ya haka ya kasance tsakaninki da shi? A ina ya ganki har ya miki waɗannan ƙazaman hotunan?” madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinta tana faɗin

“wallahi aunty tsautsayi ne, ban yi tunanin haka daga gare shi ba, abokinsa ne ya ce min bashi da lafiya shi ne naje duba shi, ya bani lemo nasha sai bacci ya ɗaukeni, ina ga a sannan ya yi min haka, na yarda dashi but he deceive me, they trick me aunty, sun lalata min rayuwa, ya zan yi aunty? Ya xan yi dashi yanzu?”

Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, rungumeta Zahra ta yi itama tana kukan ta ce“kin yi kuskure Nana, ba’a bawa namiji yarda irin haka, kin yi kuskuren zuwa wajensa ba tare da shawara ba, amma yanzu aikin gama ya riga da ya gama, sai dai a yi addu’ar Allah ya kawo wa lamarin sauki”

“ya zan yi aunty? Ban san me zai buƙata daga gareni ba, kuma yace idan ban yi masa ba sai ya yaɗa hotuna na kowa ya gani, sai ya tabbatar ya ɓata sunan gidanmu, taya zan bari haka ta kasance aunty? Ba zan iya ba, tsoro nake ji aunty Zahra, wallahi zuciyata bugawa take yi da karfi aunty…”

Zahra ta dinga shafa bayanta tana jin yanda take kuka mai ban tausayi, tunda take da Nana bata taɓa bata tausayi irin na yau ba, yarinya ce ƙarama amma yanzu rayuwarta ta faɗa wani hali wanda Allah ne kawai zai iya fitar da ita, wace irin jarrabawa ce wannan?…

Sai ƙarfe 9:00 na dare sannan ta bar apartment ɗin Zahra, koda ta koma gida Amma ta samu zaune a parlon bayan ta haɗe kayan lefen can gefe guda, ta ƙarasa jiki a sanyaye ta zauna kusa da ita, Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce“Nana sai yanzu?” gyaɗa mata kai kawai ta yi, Amma ta sake cewa“kin ci abinci?” gyaɗa mata nan ma ta yi, ta yi shiru can kuma ta ce“ko zaki ga kayan auren naki?” tashi ta yi tana girgiza kanta ta ce“a’a Amma bacci nake ji” Amma ta dinga kallonta sai kuma ta taɓa jikinta, zafi taji amma ba can ba dan haka ta ce“kuka ki ka yi ko Nana? Ba zaki yi haƙuri ki yarda da ƙaddarar ki ba kenan? Kin fi so ki ɗaga hankalinki sannan ki ɗaga namu? Ba zaki haƙura ba ko?” kasa jurewa ta yi dan haka ta fashe da kuka tana rungume Amma ta ce“na haƙura Amma, wallahi na haƙura, ba wai ina kuka bane saboda ban sami wanda nake so ba, ina kuka ne kawai saboda ban san wace irin rayuwa zan yi ba bayan auren, amma na haƙura wallahi, tuntuni na cirewa raina wannan, dan Allah ki yi min addu’a Amma, ki dinga yi min addu’a wallahi tsoro nake ji”

Amma ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin tausayin tilon ƴar tata, ta shafa kanta a sanyaye ta ce“to Nana daman ina miki addu’a kullum sannan zan ci gaba da yi miki, kema ki dinga addu’a kin ji, kuma ki daina jin tsoro babu abin da zai faru sai Alkhairi”

Jinjina kanta ta yi sannan ta tashi ta bar wajen ba tare da ta sake cewa komai, Amma ta bita da kallo har ta shige daƙinta.

Washegari around 10:40 na safe ta fito daga ɗakinta bayan ta shirya cikin wata atampa tana kallon Amma ta ce“zan je wajen Aunty Zahra” to kawai Amma ta ce sannan ta fice daga gidan. Tafiya kawai take har ta kusa kaiwa apartment ɗin nasu ta hangoshi tsaye suna magana da Hamid, kallo ɗaya ta yi musu har ta ƙaraso inda suke ta ɗan rusuna a sanyaye ta ce“ina yini?” Hamid ne ya amsa, shi kuma ya dinga kallonta ganin zata shige ya ce“Nana zo” runtse idanunta ta yi sai kuma ta dawo ta tsaya kusa da su ta sunkuyar da kanta, Hamid y ce“to ni dai nayi gaba” okay kawai Safwan ya ce sannan ya mai da idanunsa kanta, above 5mins kafin ya ce“jiya wai kin yiwa su Siyama rashin kunya kin zage su?” da mamaki ta dinga kallonsa sai kuma ta ce“wace Siyama?” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce“je ki kawai” tura baki ta yi sannan ta juya ta bar wajen dan daman ba son magana take dashi ɗin ba.

Tana ƙoƙarin shiga parlon su Zahra wayarta ta yi ƙara alamar message ya shigo, ta kalli message ɗin tana kokarin buɗewa sai ga kiran waya ya shigo, tsayawa ta yi sannan ta ɗaga kiran ta kai wayar kunne, kafin ta yi magana ya ce

“Kin ga saƙona?”

Girgiza kanta tayi kamar yana gabanta ta ce

“A’a”

Junaid ya gyaɗa kansa sannan ya ce“okay to ba komai bane sai ina son sanar da ke cewa kisan duk yanda zaki yi kada a ɗaura miki aure da wannan mutumin, dole ne ki ƙi aurensa sannan dole ne ki gabatar dani a wajen iyayenki, ki ce musu ni ki ke so ba wanda suke shirin aura miki ba, idan ki ka yi haka to zan ƙona hotunanki da suke wajena, amma idan har ki ka saɓa abin da nace miki to wallahi sai na fitar dasu kowa ya gani, sannan har gida zan saka a kawowa mahaifinki ya gani, dan haka yanzu shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ko dai ki yi abin da nace ko kuma na lalata rayuwarki!”

Jingina ta yi da jikin bango tana sauke numfashi da sauri da sauri, nan da nan hawaye suka ciko idanunta, ya kashe wayarsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Kasa kukan ta yi sai ajiyar zuciya da take saukewa, above 5mins kafin ta ja ƙafafunta a hankali ta buɗe parlon ta shiga, Aunty Khadijah ce zaune sai Zahra a kusa da ita suna magana, ta kallesu muryarta na rawa ta ce“ina yini” babu wadda ta amsa a cikinsu dan haka ta haye sama abin ta, Zahra ta kalli Aunty Khadijah sai kuma ta ce“ina zuwa” okay kawai ta ce sannan ta tashi ta bi bayanta, tana shiga ɗakin Zahra ta buɗe ƙofa ta shigo, Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“aunty yanzu Junaid ya kirani” babu yabo babu fallasa ta ce“me ya ce miki?” jiki a sanyaye ta faɗa mata duk abin da ya ce mata, Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta ce“zo ki zauna zamu yi magana” ta ƙare maganar tana zama gefen gadon, to kawai Nana ta ce sannan ta ƙarasa ita ma ta zauna gefenta. Zahra ta dinga kallonta can kuma ta ce“kin san me nake so dake Nana?” girgiza kai Nana ta yi ba tare da ta ce komai, Zahra ta ci gaba da faɗin

“Ina son ki rabu da auren Safwan, ina son ki ce baki son shi da kanki, idan ta kama ki ɓata da kowa ma ki ɓata amma ina so ki bar maganar aurensa!”

Da wani irin mamaki Nana ta dinga kallon Zahra sai kuma a sanyaye ta ce“Aunty idan na ce haka kowa zai tsaneni, nima bana son auren Yaya Safwan amma babu yanda na iya, ba zan iya cewa a’a ba”

Zahra ta gyaɗa kanta sai kuma ta ce“ba zaki iya ba? To ai dole ki yi Nana, saboda Yar Yayata Siyama nakeson ta auri Safwan, ki cewa Abba bakya son sa ya zaɓa miki wani, amma ba dai Safwan ba!” a razane ta tashi tsaye tana kallonta, ta dinga kallonta tana hawaye kafin ta ce“a’a aunty ki daina min irin wannan wasan, zuciyata bugawa zata yi, ki bari dan Allah” tashi tsaye Zahra ta yi ita ma ta dafa kafaɗarta tana murmushi ta ce“ba zolayarki nake ba Nana, ina faɗa miki ne a matsayin shawara, bana son mu kai jallin da zamu ɓata dake akan wannan dan haka ki rabu da Safwan kin ji” ta ƙare maganar tana jan kumatunta. Janye hannunta Nana ta yi daga fuskarta sai kuma ta girgiza kanta ta ce

“a’a aunty, A’a! Wallahi ba zan iya ba, ba zan taɓa yi ba, zan auri Yaya Safwan muddin ba shi ne ya ce ya fasa aurena ba, ba zan ɗauki wannan shawarar taki ba!”

Zahra ta kalleta sai kuma ta ce“okay wait!” Daga haka ta fice daga ɗakin, Nana na tsaye tana tunanin abin da Zahra ta ce mata har ta dawo hannunta riƙe da envelope ɗin jiya, Nana ta dinga kallonta lokaci ɗaya gabanta ya shiga faɗuwa, zaro hotunan ta yi gaba ɗaya tana bubbuɗesu ta ce

“Idan baki ɗauki shawara ba na san zaki ji barazana, dan haka ki bar maganar auren Safwan muddin baki son waɗannan hotunan naki su fita” da wani irin mamaki Nana ke kallonta sai kuma ta kawo hannunta zata karɓe hotunan, Zahra ta janye hannunta tana murmushi ta ce

“so ki ke na baki hotunan ki? Zan baki Nana, da zarar kin yi abin da nace zan baki hotunanki, amma idan har baki yi yanda na ce ba to ki sani kai tsaye Abba zan kai wa wannan hoton, sannan kuma na bawa uncle ɗin ki wasu, na san ba zaki so hakan ba ko Nana?”

Shiru Nana ta yi dan ta kasa cewa komai banda hawaye babu abin da take, Zahra ta tako har gabanta ta sanya hannunta ta goge mata hawayen tana faɗin “stop crying lil sis, ki zama yarinyar kirki kin ji, babu abin da zai sameki, ni ba zan cutar da ke ba kin ji, kawai do as i said!” Zahra ta ƙare maganar tana murmushi sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin.

Mutuwar tsaye Nana ta yi a wajen, ta kasa koda ɗaga ƙafarta ballantana ta yi ƙwaƙwaran motsi, above 5mins kafin ta sulale ƙasa a hankali ta zauna kan tiles lokaci ɗaya ta fashewa da wani irin raunataccen kuka na zallar baƙin ciki da damuwa, gani take kamar a mafarki abin da ke faruwa, kenan bayan Junaid yanzu har da Zahra cikin masu son treating ɗinta? Me ya sa Zahra zata mata haka? Me ya sa mutanen data fi yarda dasu sune suke son cutar da zuciyarta, sai kawai ta sake rushewa da wani sabon kukan tana kifa kanta akan cinyoyinta. Can ƙasa kuwa Zahra ce ta kalli Aunty Khadijah sai kuma ta yi murmushi ta ce“ai kar ki wani damu wallahi kamar an yi auren nan ne, Nana ba zata taɓa bijirewa abin da nace mata ba, ni na sani” Aunty Khadijah ta jinjina kanta kafin ta ce“na yarda dake Zahra amma duk da haka akwai buƙatar mu sake kama yaron hannu biyu, saboda kin ga shi ne wanda zai je ya gabatar da Siyama a wajen iyayen nasa”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *