Chapter 16: Chapter 16
Ai Aunty kawai ki bar komai a hannuna, ni zan kira Safwan nan muyi magana dashi, ba dai yana son Siyama ba?” Zahra ta ƙare maganar cikin sigar tambaya, gyaɗa maya kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh mana, har gida fa yake zuwa, ko jiya suna tare har wajen isha’i baki ga abun arzikin daya kawo mata ba”
Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta ce“to indai haka ne kar ki wani damu, Safwan ba zai taɓa bamu matsala ba, kin san me?” girgiza kai Aunty Khadijah ta yi, Zahra ta gyara zamanta sannan ta ce“Ba Safwan ne zai rabu da Nana ba, a’a ita da kanta ce zata ce bata sonsa, idan har ta ce haka to a sannan ne za’a saka ya fito da zaɓinsa, kin ga sai ya nuna Siyama” Murmushin jin daɗi Aunty Khadijah ta yi ta ce“gaskiya kuwa kin kawo shawara mai kyau Zahra, shiyasa nake son ki ƴar ƙanwata” murmushin kawai ita ma Zahra ta yi tana shirin magana suka ji ƙarar taku wanda ya sanya suka kalli wajen a tare, Nana ta ce take sakkowa daga benan a hankali tamkar wadda aka zarewa laka, fuskarta ta yi caɓa-caɓa da hawaye, bata kalli inda suke ba ta nufi hanyar fita daga parlon, Zahra ta taɓe baki sai kuma ta mai da Idanunta kan Aunty Khadijah ta ce“kin ga abin da na faɗa miki ko? Ba zata iya ja dani ba yanzu” gyaɗa kai kawai Aunty Khadijah ta yi, ƙasan zuciyarta tana jin wani irin farin ciki mara misaaltuwa, koda wasa bata yi tunanin Zahra zata amince nan kusa ba, ta yi zaton duk maganganun da malamin nan yake faɗa mata karya ne sai gashi yanzu ta tabbatar da hakan da kanta.
Nana na sakkowa daga balcony ɗin gidan suka ci karo dashi, ta ɗan ja baya a hankali idanunta a lumshe dan bata san ma ya tawo ba, kallonta Abdusammad ya dinga yi ganin yanda fuskarta ta yi jajur ga alamar hawaye a tattare da ita, ta sunkuyar da kanta muryarta na rawa ta ce“uncle ina yini?” shiru ya yi bai amsa mata ba, ya gyara tsaiwarsa kafin ya ce“mene ne?” girgiza kanta ta yi kuka na ƙoƙarin kwace mata ta ce“babb…babu komai!” taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“baki ji me nace ba?” kasa jurewa ta yi kawai ta faɗa ta jikinsa ta ƙanƙameshi tana sakin wani marayan kuka, Kallonta ya dinga yi da mamaki kafin a hankali ya sanya hannayensa duk biyun ya riƙeta sosai ta dinga rera kukanta kamar daman jira take a tambayeta, shiru ya yi mata ba tare da ya yi yunkurin hanata ba, Above 5mins kafin ta fara rage sautin kukan nata, ta dinga shessheƙar kuka tana sauke ajiyar zuciya, Sai a sannan ya ɗan kalleta dan gabaɗaya ta yi wata yar ƙarama a gabansa, a iya ƙirjinsa kanta ya tsaya, ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago fuskarta wadda ta gama lalacewa da hawaye da majina, hannunsa na hagu ya zura cikin aljihun trouser jikinsa ya zaro wani hanky coffee sai ƙamshi yake, da kansa ya goge mata hawayen sannan ya ce“now tell me mene ne?” janye jikinta ta yi daga nasa tana shessheƙar kuka ta ce“babu komai” Abdusammad ya haɗe ransa kamar ba shi ba ya ce“yaushe na fara wasa dake Nana?” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“babu komai wallahi kawai tsoro nake ji”
“tsoron me?”
Ya ce yana kafeta da idanunsa masu kaifi. Bakinta na ɗan rawa ta ce“ba..bana son auren nan uncle, tsoro nake ji sosai” dariya ce ta kusa kufce masa, amma ya maze ya sanya hannunsa ɗaya ya ja kumatunta sannan ya ce“silly girl, saboda za’a miki auren ki ke kuka? Ba kin girma uhm?” ya kare maganar yana murmushi, tura baki ta yi ta ce“ni ban girma ba uncle, I’m still a baby” jinjina kansa ya yi ya ce“yeh! U’re still a baby tun da har yanzu baki daina kukan banza ba, anyway zan faɗawa Safwan ya dinga siya maki chocolate kin ji, so don’t worry aure ba abin tsoro bane, daɗi fa zaki ji”
Waro idanunta ta yi dan har ta manta da ƙalubalen dake gabanta cike da yarinta ta ce“daɗi kuma uncle? Bayan ni zan dinga girki, sannan ba zan dinga fitowa kullum ba, ba zan dinga zuwa wajen Ammana kullum ba, sannan malamin mu ya ce sai an yi aure ake haihuwa, zan samu baby”
Murmushi sosai Abdusammad ya yi dan sai yau ya sake tabbatar da yarinyar ta, ya ɗauke kansa yana kallon compound ɗin gidan mai cike da shuke-shuke sannan ya ce“and u want a baby ba?” gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi ta ce“ina son Baby, tun da Amma bata haifa mani ba, ni zan haifa ai ko?” ta ƙare maganar tana kallonsa, gyaɗa mata kai ya yi yana ƙoƙarin barin wajen ya ce“toh tun da kina son Baby that’s means kina son aure” girgiza kanta ta yi tana tura baki gaba ta ce“ni bana son aure, baby kawai nake so” daga haka ta yi gaba ta bar wajen, da idanu kawai ya bita sai kuma ya yi dariya a fili ya ce
“ƙuruci dangin hauka”
Daga haka ya ci gaba da tafiya shima. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga parlon, Zahra ta yi saurin miƙewa daga zaune da take tana ƙirƙiro murmushi ta ce“welcome back doctor” jinjina kansa kawai yayi sannan ya nufi upstairs, Aunty Khadijah ta bi shi da kallo dan daman can ba shiri suke ba har ya haye sama. Sai a sannan Zahra ta kalleta ta ce“aunty why baki masa magana ba?” harararta ta yi ta ce“dani dashi wa ya kamata ya fara yiwa wani magana? Ni fa sirikarsa ce” Zama Zahra ta yi sannan ta ce“but he’s older than you, beside ma kowa a gidan nan ganin girmansa yake, kuma kema ya kamata ace yanzu kin ga girmansa kodan Siyama, saboda wallahi idan har ya ce a yi auren nan babu wanda ya isa ya hana, haka idan har ya ce baya so wallahi babu wanda ya isa ya yi shi” Aunty Khadijah ta jinjina kanta sai kuma ta ce“haka ne?” gyaɗa mata kai Zahra ta yi, Ta tashi tsaye tana faɗin “to idan haka ne shi ya kamata mu mallake ba Safwan ba, dashi ya kamata mu yi amfani ba Nana ba” da sauri itama Zahra ta mike sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a’a Aunty koda wasa kada ki ce zaki yi haka, wallahi ba zai mallaku ba, saboda ba’a zaune yake ba, sannan koma zai mallaku mijina ne fa, uban Yayana kin san irin yanda nakeson Doctor? Kin san irin yanda na damu dashi? Wallahi a’a ba zai yiwu ba” tsaki Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“to sannu me miji, ni dai abin da zai fisshemu shi zan yi” Zahra ta ce“eh you can do whatever you want, amma ban da taɓa min mijina!”
Kallonta kawai Aunty Khadijah ta yi ganin yanda ta haɗe rai kamar ba ita ba, ta dafata tana murmushi ta ce“to Shikenan” ajiyar zuciya Zahra ta sauke sannan ta kalli upstairs tana faɗin“bari naje gurinsa na dawo” tana ƙoƙarin barin wajen Aunty Khadijah ta ce“a’a nima tafiya zan yi mayi waya kawai” juyowa Zahra ta yi kamar zata yi kuka ta ce“aunty ba zaki jira na sakko ba?” girgiza kai ta yi ta ce“a’a akwai wanda muka yi alƙawarin haɗuwa dashi, Gara naje kawai” numfasawa Zahra ta yi ta ce“okay to ki gaida su Umma”
“Zasu ji” ta ce tana ɗaukan mayafinta, sai da ta fita daga parlon sannan Zahra ta nufi sama da sauri.
A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tana leƙen ɗakin, zaune yake gefen gado idanunsa zube kan system yana dannawa, ya rage kayan jikinsa daga shi sai wando 3-quater da kuma armless, farar fatarsa ta bayyana sai sheƙi take. Zahra ta ja ta tsaya tana ƙare masa kallo, sometimes tana tambayar kanta anya akwai mutum irin mijinta? babban mutum wanda ya san kansa, mai tarin dukiya da ilimi, mai kyau da nasaba, daɗin daɗawa hali nagari. Sai kawai ta lumshe idanunta a fili ta ce
“Alhamdulilah!”
Ɗago kansa ya yi ya kalleta dan bai san ma ta shigo ba, ta sakar masa kyakkyawan murmushi tana ƙarasowa, ta zauna gefensa ta ɗora hannunta kan nasa a sanyaye ta ce“sannu da dawowa” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce“yauwa, ina Noor?” murmushi ta yi ta ce“kai ma kasan tun da muka zo ƙasar nan ba zama take ba, kullum tana apartment ɗin Hajiya Babba” jinjina kansa ya yi hankalinsa na kan system ɗin ya ce“ai ta yi ta gama nan da 3weeks mun koma gida” da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce“tafiya zamu yi?” jin yanda ta yi tambaya da damuwa ya sanya ya ɗago kansa ya sake kallonta murya a sake ya ce“lafiya dai?” girgiza kanta ta yi tana kirkiro murmushi ta ce“kawai dai tambaya nayi” ɗauke kansa ya yi ya ce“to tafiya zamu yi, karatunta ya tsaya duk da ana yi mata anan, sannan nima abubuwa sun fara min yawa” a sanyaye ta ce“tom Allah ya kaimu, amma sai bayan biki ko?” gyaɗa mata kai ya yi ya ce“eh Abba ya ce na tsaya a yi, that’s why yasa na ce miki 3weeks da next week zamu tafi”
“ai next week ɗin ne bikin right?”
“eh haka ne”
Ya ce yana rufe system ɗin, Zahra ta dinga kallonsa har ya tashi ya ɗauke system ɗin ya mayar inda yake ajiyewa sannan ya nufi toilet.
****
Al-ameen ya kalleshi sai kuma ya ce“da gaske kana ganin wannan zai yi aiki?” Junaid ya ajiye wayar hannunsa ya zauna kan sofa sannan ya ce“eh mana zata yi bari kuma ka ga” dariyar mugunta Al-ameen ya dinga yi sannan ya ce“Allah sarki har ta bani tausayi wlh, yarinyar so calm da ita” harararsa Junaid ya yi dai dai nan aka buɗe ɗakin aka shigo. Wata babbar mata ce mai ƙiba sosai ta dinga kallonsu sai kuma ta ce“kuna nan kuna sana’ar taku ko?” sosa kai suka shiga yi, Al-ameen ya ɗan durƙusa ya ce“Mama ina yini?”
“lafiya kalau Al-ameen ya Mamanka?”
Murmushi ya yi ya ce“tana nan kalau wallahi, ta ce ma na gaisheki” jinjina kanta ta yi ta ce“ina amsawa, ku dai yiwa kan ku faɗa ku fito da matayen aure ku yi aure, wannan zaman babu inda zai kai muku” sunkuyar da kansa ya yi ya ce“tom Mama in sha Allah, Allah ya ƙara girma” Amin kawai ta ce sannan ta mayar da idanunta kan Junaid ta ce“daman Farhana ce ta zo take nemanka” ɗan tura baki ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce“Mama dan Allah ki ce bana nan” wani banzan kallo ta masa kafin ta ce“ka fito ina jiranka malam” daga haka ta juya ta rufe musu ƙofar. Kallonsa Al-ameen ya dinga yi sai kuma ya fashe da dariyar yana zamowa daga kan sofa, Junaid ya dinga kallon sa fuskarsa a haɗe sai kuma ya mike yana faɗin “banza mara hankali” ko ta kansa Alameen bai bi ba ya ci gaba da dariyarsa, Ya yi tsaki sannan ya fice daga ɗakin shima..
****
Ƙarfe 5:00 na yamma Amma ta buɗe ɗakin ta shigo, kwance ta sameta ta rufe jikinta da bargo sai numfashi take a hankali, ta ƙaraso ɗakin tana yaye duvet ɗin ta ce“ke Nana” a hankali ta buɗe idanunta wanda take jin sun yi mata wani irin nauyi. Muryarta a sanyaye ta ce“na’am Amma”
“ki taso Hajiya Babba na kiran ku” kamar zata yi kuka ta ce“Amma ki ce banida lafiya wallahi ba zan iya zuwa ƙauye ba” harararta Amma ta yi ta ce“ka da Allah yasa ki iya zuwa sai ki je ki faɗa mata hakan” daga haka ta saki bargon sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Dakyar ta tashi zaune ta jingina da fuskar gadon tana hawaye a hankali, wani irin nauyi ta yi ƙirjinta y yi mata, daga jiya zuwa yau ji take kamar zuciyarta zata tarwatse, ban da tunani babu abin da take, she wish ace mutuwa ta zo ta ɗauketa yafi wannan halin da take ciki, she wish ace duk abin da ke faruwa mafarkine ba gaskiya ba, da sai ta yi sallar godiya ga Allah idan ta farka, sai dai ganin lokaci na tafiya ya sanya ta tabbatar da ba mafarkin take ba. A hankali taja idanunta ta rufe wanda hakan ya bawa hawayen dake kurmin idon samun damar zubowa, ta taune down lip ɗinta tana shessheƙar kuka a hankali, kiran sunanta da taji Amma nayi ya sanya ta tashi jiki babu kwari ta nufi toilet, wanka ta yi sannan ta fito ta sanya wata doguwar rigar material sannan ta ɗauka wani gogaggen hijab ta saka wanda ya saukar mata har ƙasa, ko mai bata samu zarafin shafawa fatarta ba ta fice daga ɗakin, tsaye ta samu Maimoon da Hamida sai Amma dake zaune, ta kalleta rai ɓace ta ce
“da kin bari na dawo dakin sai ranki ya ɓaci wallahi”
Bata ce komai ba ita dai, Maimoon ta ce“mu je mu ake jira” har ta fara tafiya sai kuma ta ce“oh i forgot my phone” daga haka ta koma daƙinta da sauri, a gaban mirror ta ɗauki wayar bata tsayawa kunnawa ba ta nufi waje, a compound ɗin gidan Hajiya Babba suka tadda sauran wanda za’a yi tafiyar dasu, domin yana ɗaya daga al’adar gidan duk sanda zasu yi auren ya’ya sai an kai su can Yola ruga sun gaida kakkaninsu na can, Hajiya Babba ce tsaye sai Abdusammad a kusa da ita, sai Safwan, Sultan, Hamid da kuma Aliyu. Matan kuma akwai Zahra dake riƙe da Noor, Juwaira, Hamida, Maimoon, Amrah, sai kuma Nana. Papa da ke gefen Hajiya Babba na dama ya kallesu ya ce“a kula dan Allah, Abdusammad kai ne babba na san ba zaka bari su yi wani wajen ba amma dan Allah su kula sosai” jinjina kansa ya yi a sanyaye ya ce“okay Papa in sha Allah” daga haka ya nufi motarsa. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga shigewa mota, ita kuwa Nana taja ta tsaya dan sam bata ji zata iya zuwa ba, ganin kowa ya shige an barta ya sanya Hajiya Babba ta ce“a’a takwara lafiya dai?” kamar zata yi kuka ta ce“Hajiya banida lafiya fa” ƙarasowa inda take ta yi ta dafa jikinta jin babu zafi ya sanya ta ce“to meke damunki?” a sanyaye ta ce“kaina ciwo yake” Papa ne ya ce“to shiga mota idan kun tafi a hanya a siya maki magani” hawaye ne ya fara zubowa kan fuskarta ta ce“Papa ba zan iya zuwa ba wallahi, kaina ciwo yake sosai” haɗe rai ya yi a ɗan tsawace ya ce“kin shige mota ko sai ran ki ya ɓaci Nana!” yanda ya yi maganar cikin fargagi ya sanya ta dafe saitin zuciyarta tana wani irin numfashi, Hajiya Babba na ƙoƙarin magana Abdusammad ya fito daga motar yana kallonsu ya ce“mene ne?”
“wai ba zata je ba”
Papa ya yi maganar rai ɓace, kallonta ya yi sai kuma ya ja hannunta ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa motar Safwan ya buɗe front seat ɗin ya turata yana mata wani irin mugun kallo ya ce“kar na sake jin bakin ki kin ji” gyaɗa masa kai kawai ta dinga yi dan gaba ɗaya ba’a hayyacinnta take ba, Ya rufe motar sannan ya nufi tasa motar ya shige back seat dan shi da driver zasu tafi suka ja motar suka yi gaba, ɗaya bayan ɗaya motocin suka dinga fita har suka bar cikin estate ɗin sannan kowacce ta fara gudu akan titi.
Tun da suka fara tafiyar babu wanda ya ce da wani ƙala, kowa da abin da yake tunani cikin ransa, sai da suka ci rabin tafiyar sannan ya ɗan kalleta ta gefen ido, idanunta a lumshe suke sai dai babu tabbacin bacci take ko kuwa idanunta biyu, dan haka ya ɗan yi gyaran murya. Sarai Nana ta ji shi amma bata ko motsa ba ballantana ya saka ran da zata kalleshi, Safwan ya ɗan fara rage gudun da yake murya a sanyaye ya ce“Nana!”
Dakyar ta iya raba laɓɓanta da juna murya can ƙasa ta ce“na’am” sai da ya yi kwana sannan ya sake cewa“meke damun ki na gan ki so quiet kamar ba ke ba?” a hankali ta juyo da idanunta ta ɗan kalleshi sai kuma ta ɗauke ta maida su kan titi tana kallon yanda suke shige bishiyu da tsaunuka ta ce“babu komai” jin yanda ta yi maganar da wata irin muryar wadda bai santa da ita ba ya sanya ya juyo da kansa ya kalleta, ganin ba shi take kallo ba yasa ya mayar da hankalinsa kan tuƙin da yake kafin ya ce
“ko baki son auren nan?”
Kallonsa kawai ta yi amma bata ce komai ba, bai damu da rashin amsawar tata ba ya sake faɗin “ki sanar dani tun yanzu, cause naga yanda yan uwanki ke shirye-shirye ke bakya yi, gaba ɗaya kin zama wata so silent ba kamar yanda ki ke ba, ki faɗa min ba ki da sha’awar aurena or what?”
A hankali ta dinga kallonsa tana jin kamar ta ce masa eh bata so. Sai dai koda wasa ba zata iya furta hakan gare shi ba, dan haka ta yi shiru tana jin yanda bugun zuciyarta ke tsananta. Safwan bai sake cewa komai ba ganin ba amsa masa take ba, dan haka ya mai da hankalinsa gaba ɗaya kan tuƙin da yake, After 15mins ya ɗan saci kallonta ta gefen ido ganin idanunta a lumshe kamar ɗazu ya sanya ya ce
“tun da ba zaki yi magana ni bari na sanar dake abin da ke raina”
Buɗe idanunta ta yi ta ɗan kalleshi ba tare da ta ce komai ba, amma gaba ɗaya hankalinta yana kansa tana son taji shi mene ne nasa ra’ayin akan auren.
Numfasawa ya yi cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya fara cewa
“Nana tun da nake ban taɓa miki kallon wadda watarana zan iya aura ba, na yi tunanin za ki ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin ƙannena, sai dai babu wanda ya san abin da zai faru gaba, ban yi tunanin irin wannan lokacin zai zo ba, da har za’a haɗani aure dake, duk da yarintar ki.” ya ɗan numfasa sannan ya ci gaba da faɗin “sai dai a wannan yan kwanakin ina ganin komai kamar mafarki, tamkar ba gaskiya ba, har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa kece wadda zan aura, ta kasa aminta da hakan, gani nake kamar za’a fasa auren nan.” ya ƙare maganar yana kallonta to see her reactions. Nana da ke kallonsa tun ɗazu ta ɗan janye idanunta tana kallon fararen kyawawan faratanta muryarta a sanyaye kamar koda yaushe cikin kwanakin nan ta ce
“nima haka Yaya, kullum gani nake kamar ba gaske ba, ji nake kamar za’a ce an fasa aurena da kai, but u no what?”
Ta yi maganar tana kallonsa, girgiza kansa ya yi yana ɗan ƙara gudun da yake, ta sauke numfashi sannan ta ce“i wish a ce an fasa ɗin, cause am not ready to get married, ban shirya zama matar gida ba, I’m too young to carry that burden..” ta yi shiru jin kuka na neman kwace mata, Safwan ya dinga kallonta fuskarsa ɗauke da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, ya kasa tantance abin da yake ji game da ita a wannan lokacin, tausayi ne? Ko kuwa soyyaya ce?. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana ɗan faɗaɗa fuskarsa ya ce“kamar dai ni Nana, sai dai ni ba wai ina son a fasa aurena bane, a’a ina son nayi aure da wata ne bake ba?”
Da sauri ta kalleshi fuskarta ɗauke da mamaki gami da farin ciki, ta ɗan girgiza kanta ta ce“da gaske Yaya? Baka sona? Baka son ka aureni? Are ur sure?”
Girgiza kai Safwan ya yi yana kallon titi ya ce“that was not what i meant, ba wai bana sonki bane Nana, ina sonki, akan me zan ce bana son ki? Look at you, babu namijin da zai ce baya son yarinyar kamar ki, ga kyau ga hankali sannan ga nutsuwa, kina da qualities daya kamata ace an so ki saboda su, dan haka ba wai bana son ki bane, a’a kawai dai akwai wadda zuciyata ke ƙauna, wanda a yan kwanakin nan nake jin idan bada ita ba bazan iya rayuwa ba, ko bacci nake sai na farka na yi tunaninta, idan dare ya yi burina gari ya waye naje na ganta. And you know what?”
Ta girgiza kanta tana sake gyara zamanta, numfasawa ya yi ya ce“duk wannan son da nake mata bai kai rabin wanda take min ba, tana sona fiye da yanda nake sonta, but unfortunately we two can’t be together!” ya ƙare maganar jiki a sanyaye babu wani kwari.
Girgiza kanta ta yi a hankali tana kwaɓe fuskarta kafin ta ce“ayyah Yaya sorry kaji, to mene ya hanaka ka faɗawa kowa ita ka ke so?” ɗan murmushin ya yi ya ce“idan na faɗa ma ba zai wani amfani ba, babu wanda zai ɗauka maganata serious balle har a dubata, kawai na yanke shawara araina ne” Nana ta dinga kallonsa sai kuma ta ce“mene shawarar?”
“Idan na aureki daga baya saina aureta as a second wife” ya yi maganar da zallar gaskiyarsa dan shi sam ƙarya bata daga cikin layinsa.
Kallonsa kawai Nana ta dinga yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta koma ta jingina da bayan kujerar ta yi shiru tana tunani. Safwan ya ɗan kalleta sai kuma ya ci gaba da tuƙinsa jin bata ce komai ba.
Njomboli, Yola South.
Karfe 7:10 na magriba motocinsu suka fara parking a ƙofar babban gidan, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara fitowa suna sauke ajiyar zuciya wasu na hira ƙasa-ƙasa, Nana ta dinga kallon ƙaton gidan wanda ya kasance shine kaɗai kerarren gida kaf Njomboli da kallo, Babban gida ne wanda aka ƙawata shi tamkar a cikin gari yake, kasancewarsa shi ne asalin gidan su Late Alhaji Muhammad Shuwa, kuma nan ne inda sauran danginsu suke, Mutanen gidan suka firfito fuskarsu ɗauke da farin ciki mara misaaltuwa suna musu sannu da zuwa, kafin daga bisani suka musu jagora har cikin gidan.
A ɗakin Baba Atta suka sauka, wadda ta kasance yar uwa ga late Muhammad Shuwa wadda suke uba ɗaya, tsohuwa ce sosai amma Allah ya mata kyan jiki dan ba zaka taɓa cewa ta yi shekarunta ba idan tana wasu al’amuran, gaba ɗaya a ɗakin suka zauna dan ba ƙarami bane, ta dinga kallon su fuskarta ɗauke da fara’a cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce
“Sannunku da zuwa, sannu sannu!”
Wasu a ciki ne suka amsa, wasu kuma suka yi shiru dan duk a gajiye suke, Abdusammad ne ya tashi ya koma kusa da ita dan daman tafi saninsa a cikinsu kasancewar babba kuma da yana zuwar musu sosai sanda yana ƙarami, Ya ja kumatunta yana murmushi cikin harshen fulde ya ce
“Yar tsohuwa mai ran ƙarfe”
Doke hannunsa ta yi tana Harararsa ita ma cikin harshen da ya yi mata magana ta ce“rabu dani kai, ai nayi fushi da kai” murmushin da yake ƙara masa kyau ya yi kafin ya ce“fushi kuma ki rufa min asiri Atta, idan ki ka yi fushi dani ina na kama? Har yarinyata fa na kawo miki”
Washe bakinta wanda haƙora suka fara zubewa daga ciki ta yi ta ce“haba da gaske oh ni Atta ahe zan ga jikata?” dariya ya yi yana kiran Noor da ke hannun Zahra ya ce“gata nan kamar ku ɗaya da ita” ya ƙare maganar yana miƙa mata hannun Noor, riƙeta ta yi tana murmushi ta ce“masha Allahu wannan yarinyar ba da kai take kama ba kuwa?” Girgiza kansa ya yi ya ce“a’a ki kalleta da kyau ko sai na saka an miki tabarau?” duka ta kai masa tana cewa“kaji min ɗa? Idanuna sun fi naka kwari bari kaji” Sai da ta ɗora Noor kan cinyarta sannan ta ce“wai ina ma matar taka?” da hannu ya nuna mata Zahra dake zaune opposite ɗin su ta sunkuyar da kanta. Atta ta kalleta sai kuma ta kalli su Nana da ke zaune a ƙasa ta ce



