⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 17: Chapter 17

“Oh lalashewa ta sameka Arɗo”

Da ɗan mamaki ya ce“lalacewa kuma Atta?”

Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta sake kallon Zahra tana taɓe baki ta ce“saboda baka jin magana, ka je ka haɗu da arnakun banza ya sanya ka auri wadda ba jininka ba, ko kunyar Ubangiji baka ji, to wallahi da sake sam ba zan yarda ba, sai ka auri jininka wallahi, dan Yaya ba zai taɓa alfari da kai ba idan ka mutu akan wannan turbar”

Ta ƙare maganar tana lakuce masa hanci, murmushi kawai ya yi yana satar kallon Zahra wadda ta sunkuyar da kanta ya ce“haba Atta, mene ne haka? Daga zuwanmu sai ki fara faɗa?” wani kallon tara saura kwata ta masa sannan da ƙarfi ta ce

“Kaltume! Salame!”

Shigowa suka yi a tare suna faɗin “gamu Atta” kallonsu ta yi sai kuma ta kalli su Nana ta ce“a kai su ɗaki su huta sai a kawo musu abinci”

“Ni dai fura nake so Atta”

Abdusammad ya ce da sauri, murmushi ta yi ta ce“to jikin Ahmadu ai daman nasani shiyasa tun da Kabiru ya ce min kuna hanya na sa aka tatso nono” jinjina kansa ya yi ya ce“Allah Atta? To nima na zo miki da tsaraba” washe baki ta yi ta ce“me ka kawon?” maƙe kafaɗa ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce“sai kin fara bani fura sannan zan baki nima” taɓe baki ta yi ta ce“to ai sai ka yi ta yi” ta mai da Idanunta kan su Salame da suke tsaye har sannan ta ce“wai baku ji bane ku ke kallona kamar wasu gumakan farko?” ta ƙare maganar a ɗan fusace, murmushi kawai Abdusammad ke yi dan daman ya san halin jarabarta. Jiki na rawa suka kalli su Maimoon cikin gurɓatacciyar hausar su suka ce“mu je kun ji”

Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe ban da Nana data ko motsi bata yi ba, Atta ta kalli Aliyu wanda tun shigowarsa bai ce komai ba ta ce“wannan ba Ali bane?” a sanyaye Aliyu ya ce“ni ne Atta” harararsa ta yi ta ce“aa to kaje da mugun halin ka, tashi ku je a buɗe muku sabon sashin can na yan jimeta” to kawai ya ce dan shi ba wani hira suke da ita saboda jarabarta ya kalli su Sultan ya ce“mu je ko” okay kawai suka ce sannan suka tashi suma suka fice, wajen ya rage daga Abdusammad sai Zahra da kuma Nana, wani kallo Atta ta yiwa Zahra sannan ta ce“ke ba zaki tashi bane?” jiki a sanyaye Zahra ta mike ta fice daga ɗakin dan ita bata taɓa haɗuwa da Atta ba tun da ta auri Abdusammad, duk yanda yake bata labarinta yau ta tabbatar da tafi gaban nan, ta mai da idanunta kansa dan sam bata lura da Nana ba ta ce“daman na ajiye maka gilishi so nake su hita na sa a ɗauko maka” murmushi kawai ya yi sannan ya ce“yauwa shiyasa nake sonki ai”

“bari kaji amma wallahi sai ka sake aure dan ba zaka zauna da jinin da ba naka ba, idan mata sun ƙare a jimeta sai ka ɗauki ɗaya anan ka shige da ita”

Kallonta kawai Abdusammad ya yi sai dai ban tanka ta ba, dan yana sake magana zata iya rantsewa, Kaltume ce ta dawo ɗakin tana kallonta cike da girmamawa ta ce“Atta ita wannan ba tafiya zata yi bane?” ta ƙare maganar tana nuna Nana dan tun ɗazu take jiran taga ta fito kuma ta ji shiru. Mitsi-mitsi Atta ta yi da idanu tana kallon Nana ta ce“wace wannan?”

Abdusammad ne ya juya yana kallonta ganin yanda ta sunkuyar da kanta, babu yabo babu fallasa ya ce“Nana” a hankali ta ɗago kanta ta kalleshi da kumburarrun Idanunta wanda hawaye ya cika su,Baki buɗe Atta ke kallonsu sai kuma ta ce“wace Nana?”

“Nana da ki ka sani ya gidan Abba”

Atta ta dinga kallon Nana da bayyanin mamaki kafin ta ce“iko sai mai sama! Yanzu wannan yar jaririyar ce ta girma haka, yarinyar wajen Ahmadu dai?” gyaɗa mata kai Abdusammad ya yi ta sake jinjina kanta sannan ta kalleta ta ce“ke zo nan” dakyar ta iya miƙewa tsaye dan zazzaɓi ne a jikinta ta ƙarasa gaban Atta sannan ta tsuguna. Taɓa ta ta yi tana ɗago fuskarta sosai ta ce“gata kuma kamarta ɗaya da babanta” murmushi kawai Abdusammad ya yi ya ce“eh suna kama da Abba” sakinta ta yi tana cewa“amma girmanta ya bani mamaki, rabon dana ganta tun sanda naje Jimeta kafin mutuwar Yaya” Abdusammad ya ce“ai kin daɗe rabon ki da Jimeta gaskiya” sake kallon Nana ta yi ta ce

“To ai kuwa ka samu mata, wannan zankaɗeɗiyar yarinyar ba’a bari ta auri wani ba, daga ganinta za’a yi mace! Dan haka na maka mata ta biyu!”

Kallonta ya dinga yi, sai kuma ya ɗan haɗe ransa yana kallon Nana ya ce“ke tashi ki tafi” kafin ta yi magana Atta ta yi saurin faɗin “a’a ba zata tafi ba wallahi, ban gama ganin jikata ba” ɗauke kansa ya yi bai sake magana ba, Atta ta tashi ta shige kitchen ɗinta. Bata jima ba ta fito hannunta da wani madaidaicin bowl mai tsafta, ta miƙa masa tana cewa“gashi nan na dama maka” amsa bowl ɗin ya yi yana murmushi idanunsa zube kan tsaftacciyar damammiyar furar wadda aka zubawa zuma akai, Nana ta ɗan leƙa bowl ɗin tana murmushi, ganin bai ce komai ba yasa Atta ta ce“idan ka gama sai kaje sashen Baba ka kwana” toh kawai ya ce yana ɗaukan ludayin da ke ciki furar ya fara juyawa a hankali.

Atta ta ja hannun Noor ta ce“muje ciki yar nan” daga haka ta fice daga parlon gaba ɗaya, Bismillah ya yi sannan ya kai ludayin furar bakinsa, daɗi da garɗin nonon ya sanya shi lumshe idanu. Nana da ke kallonsa ta lashe baki kamar ita ce ke shan furar, ganin yana ta shan furarsa ba tare da ya kalleta ba ya sanya ta tashi ta zauna gefensa tana murmushi ta ce

“uncle”

Yanda ta yi maganar a ɗan shagwaɓe ya sanya ya ɗago kansa ya kalleta, washe masa baki ta yi ta ce“nima zan sha furar” sai da ya ajiye ludayin cikin furar sannan ya ce“mene?” yanda ya yi maganar babu alamun wasa a tattare dashi ya sanya ta ɗan kama kanta. Murya a shagwaɓe kuma ta ce“to ni ba zan sha ba?” dungure mata kai ya yi ya ce“ni abokin wasanki ne? Tashi anan” rau-rau ta yi da idanu kamar za ta yi kuka, ya taɓe baki sai kuma ya ci gaba da shan furarsa. Tana nan zaune har ya kusa shanyewa ta ɗan leƙa bowl ɗin taga sauran kaɗan sai kawai ta fashe da kuka tana murza idanunta, ɗago gajiyayyun idanunsa ya yi ya ɗan kalleta sai kuma ya ce“mene kuma?”

“Sai ka shanye baka bani ba”

Ta yi maganar cikin kuka, girgiza kansa ya yi sannan ya ɗebo furar ya kai mata ludayin baki, kallonsa kawai ta yi sai kuma ta kalli ludayin. A hankali ta buɗe bakinta ya zuba mata furar, lumshe idanunta ta yi tana tauna furar, ya kalleta yana murmushi sai kuma ya dungure mata kai ya ce“kwaɗayayyiya kawai” turo bakinta ta yi a hankali ta ce“ni ɗin uncle” sai da ya sake kai furar bakinsa sannan ya ce“eh ɗin ke” daga haka ya ɗebo ya kai mata baki, haka suka dinga shan furar tare har suka shanye, ya miƙa mata bowl ɗin yana gyatsa a fili ya ce

“Alhamdulillah”

Sannan ya miƙe yana kallonta ya ce“tashi ki tafi wajen su Maimoon” Toh kawai ta ce sannan ita ma ta miƙe ta fara kai bowl ɗin kitchen sannan suka fito a tare. Kalle-kalle ta dinga yi a babban tsakar gidan, ganin yanda mutane ke ta shige da fice yasa ta rasa in da zata yi, ganin yana shirin barin wajen yasa ta ɗan ƙara sauri har ta cimmasa sannan ta ce“uncle to ina zan je?” juyowa ya yi yana kallonta fuskarsa a haɗe ya ce“Nana ba zaki kyaleni na huta ba kenan?” sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, ya ɗan kalli tsakar gidan sai kuma ya ja hannunta suka bar wajen.

****
Washegari da sassafe suka yi wanka suka shirya dan zuwa gaisar da sauran dangi da yan uwa, Nana na ƙoƙarin rufe ƙaramar trolley ɗin Maimoon bayan ta ɗauki mayafin Zahra ta shigo ɗakin, Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta, lokaci ɗaya ƙirjinta ya dinga wani irin bugu. Zahra ta zauna gefen gadon tana kallonta fuska a sake ta ce“Nana!” ɗago fuskarta ta yi ta ɗan kalleta a sanyaye ta ce

“Na’am”

Sai kuma ta mayar da kanta kan abin da take, Murmushi ta yi ta ce“ya muke ciki ne da ke akan maganar mu?” ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleta amma bata ce komai ba. Zahra ta girgiza kanta ta ce“naga kina shirin kuka? Mene ne abun kuka anan?”

“Dan Allah dan annabi aunty ki yi hakuri, dan girman Allah…” ta ƙarasa maganar cikin shessheƙar kuka, haɗe rai Zahra ta yi ta mike tana kallonta ta ce“da kin yi min wani abu ne Nana? Ni na ce ba zan haƙura ba? Ai bani za ki bawa haƙuri ba, zuciyarki ita zaki bawa haƙuri akan Safwan, ki san yanda zaki yi ki ce baki sonsa”

Cikin kuka Nana ta ce“wallahi ba zan iya ba Aunty, ke da kanki ki ka ce kada nayi abin da zai ɓata sunan Abbana, to idan har zan ce ba zan auri Yaya Safwan dai dai yake da ɓata sunansa ai”

“To ki ɓata ɗin. Sai me dan kin ɓata sunansa Nana?. Look ni bai dameni ba ko ki ɓata sunansa ko kar ki ɓata, kawai abin da na sani shi ne ki fasa aurensa!”

Zahra ta yi maganar cikin ɓacin rai. Ganin bata ce komai ya sanya ta yi kwafa ta sake cewa“kuma ki sani idan har baki yi abin da nace ba nan da kwana uku wallahi tallahi sai na tona miki asiri Nana! Sai na tabbatar da hotunan ki sun shiga in da bakya tsammani”

Cikin kuka ta rarrafa gabanta ta rike ƙafafunta ta ce“dan Allah Aunty kada kimin haka, dan girman Allah ki rufa min asiri, wallahi idan Abbana ya gani zai iya mutuwa” hankaɗeta Zahra ta yi tana mata wani shegen kallo ta ce“to sai me. Idan ya mutu ni ce na mutu? Ai gara ma ya mutu domin yana ɗaya daga cikin waɗanda suke haddasa wannan fitinar ta auren zumunci, wallahi Nana kin ji har na rantse idan har baki yi abin da nace ba sai na bata miki”

Ta janye jikinta ta fice daga ɗakin fuuu.. Ban da kuka babu abin da Nana take, ta dafe saitin zuciyarta dake mata wani irin zafi. Sannan ta tashi ta koma gefen gadon ta zauna tana ci gaba da rera kukanta.

Ƙarfe 1:20 na rana Maimoon ta shigo ɗakin hannunta riƙe da ƙaramin kofi, sai da ta zauna gefen gadon sannan ta taɓa Nana tana cewa“ke Nana! Ke!” a hankali ta buɗe idanunta wanda suka kumbura saboda kukan da taci, ta tashi zaune tana kallon Maimoon fuskarta a haɗe ta ce“mene ne?”

“kina ta faman bacci tun ɗazu har mun je gidajen wasu”

Taɓe baki Nana ta yi sai kuma ta ce“to ni daman bana son naje ko ina ai” Maimoon ta tashi tana harararta ta ce“to kar ki so kuma ki je Atta na kiranki” sauka tayi daga kan gadon tana gyara zaman hular kanta ta nufi toilet, da idanu kawai Maimoon ta bita sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin.

Ƙarfe 2:30 na rana suka haɗu dukkansu a parlon Atta, sai hira ake gwanin ban sha’awa, Atta ta kalli su Maimoon ganin babu Nana a ciki ya sanya ta ce“wai ina yarinyar nan naga tun da safe ban ganta ba”

Maimoon na kokarin magana Nana ta yi sallama ta shigo dakin, Atta ta washe baki tana cewa “yauwa yarinyar kirki shigo kin ji” jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa inda take zaune ta zauna gefenta, Atta ta riƙe hannunta ta ce“baki da lafiya ne?” girgiza mata kai ta yi a sanyaye ta ce“a’a lafiyata kalau” jinjina kai Atta ta yi sannan ta ci gaba da musu hira tana basu tarihin rayuwarsu a da, Nana ta ɗan zame jikinta ta ɗora kanta bisa cinyar Atta tana lumshe ido. Suna nan zaune har aka fara kiraye-kirayen sallar la’asar sannan mazan suka tashi dan tafiya masallaci, Matan kuma ta ce su shiga cikin ɗakinta su yi sallar acan, Zahra ta miƙe ganin Abdusammad yana ƙoƙarin fita, Da idanu Atta ta dinga binta ganin tana shirin bin bayansa yasa ta ce

“Ke ina zuwa ne?”

Cak Zahra ta tsaya kafin ta juyo a hankali tana kallon Atta data tsareta da idanu..

“Naga kina wani kokarin bin sa lafiyarki dai?”

Murya a sanyaye ta ce“a’a Hajiya daman zan masa magana ne”

Cike da faɗa Atta ta ce“lalashewa ta same ki ƴar nan, sabidda baki da kunya irin ta fulani yasa zaki iya bin miji a gabana? To mu ba haka muke ba.Sam wannan ba ɗabi’ar mu ba ce, kuma ba zamu lamunci wannan abun ba!”

Ita dai Zahra shiru ta yi tana kallon Atta, ganin bata sake cewa komai ba ya sa ta koma ta zauna dan ita tana fashin sallah. A hankali Atta ta tashi Nana da bacci ya fara ɗauketa ta ce“tashi muje ki yi sallah” to kawai ta ce a sanyaye sannan ta tashi tana murza idanunta ta nufi cikin ɗakin Atta. Sai da taga Nana ta bar wajen Sannan ta kalli Zahra da tayi shiru ta ce“kin ga wannan yarinyar. Ita ce wadda mijinki zai aura nan kusa, dan ba zai yiwu ya zauna da ke ɗaya bare ba! Dole ya auri jininsa”

Da sauri Zahra ta kalleta fuskarta da wani irin mamaki, Atta ta jinjina kanta tana watsa mata wani kallo ta ce“eh!. Haka na ce, kuma dole ya bi umarnina. Dan babu wanda ya isa ya bijirewa abin da nake so kaf dangin Shuwa wallahi, Saboda haka ba zai yiwu ya ci gaba da zama da wadda bata danganci danginsa ba, dan ni ban ji daɗin haihuwar da ku ka yi dashi ba! So nayi ya haihu da jininsa wadda zamu yi alfahari da ita!”

Zahra ta dinga kallon Atta ganin yanda take gasa mata magana hankali kwance, ta mike tana shirin barin ɗakin Abdusammad ya shigo, faɗawa ta yi jikinsa tana fashewa da kuka, Ya ɗora hannunsa ɗaya a bayanta yana kallonta da mamaki ya ce

“Mene ne?”

Kasa cewa komai ta yi sai sake ɗora kanta da ita a ƙirjinsa tana ƙara sautin kukan nata.

Atta ta miƙe tana harararta ta ce“to da ki ke kukan dukana zai yi? Kuma aurene babu fashi muddin ina raye sai ya yi wani aure wallahi kuma sai ya auri Nana?”

Da sauri Abdusammad ya kalleta rai ɓace ya ce“Atta!”

Wani mugun kallo ta yi masa kafin ta ce“zaka dakeni ne? Na ce zaka dakeni ne? Wallahi sai ka auri Nana muddin ina numfashi a duniyar nan”

Janye Zahra ya yi daga jikinsa yana kallonta cikin ɓacin rai ya ce

“Atta wai maganar me ki ke yi haka ne? Wace Nana? Ko zan auri kowa a duniya me zan yi da Nana? Yarinyar dana raina da hannuna kuma ita ki ke son na aura?. And beside ma Nanar da ki ke magana har da ita a wanda za’a ma auren next week, Safwan zata aura, dan haka dan Allah ki daina wannan maganar kina zubar min da mutuncin gaban mutane. Sannan Zahra matata ce, na aureta saboda ina sonta ki daina zaginta dan Allah! Dan Allah Atta”

Atta ta yi mitsi-mitsi da idanunta cike da masifa ta ce

“To ina ruwana da matarka ce? Kai ta dama bamu ba, abin da muka sani shi ne sai ka ƙara aure. Sannan da ke maganar wai za’a yiwa Nana aure, ai ba auren aka yi ba, to wallahi bari kaji ko auren aka yi sai ya saketa ka aureta! Kai nake so ka aureta ba wani ba, kuma babu wanda ya isa ya hanani zartar da wannan hukunci!”

Zahra dake tsaye tana kallon Atta ta fashe da kuka ta juya ta gudu ta bar ɗakin tana rufe bakinta da hannunta, Bai kalleta ba haka kuma bai yi yunƙurin bin bayanta ba. Sai ma takowa daya fara yi ya zo gaban Atta, ganin yanda ta haɗe ranta sai huci take ya sanya ya ɗan sassauta nasa fushin babu yabo babu fallasa ya ce“Atta dan Allah abar wannan maganar, ki daina sako Nana cikin maganar nan, aure fa za’a mata” wani irin kallon sheƙeke Atta ta yi masa a zafafe ta ce“to ba zan barta ba. Idan ka ji na bar maganar nan to an yi abin da nake so ne” Abdusammad ya dinga kallonta dan ya rasa abin da zai ce mata kuma, Ya girgiza kansa sai kuma ya juya ya bar ɗakin. Da harara ta bishi sannan ta ce“to zan ji tsoronka ne? Wallahi sai an yi abin da nake so idan ba haka ba hankalin kowa ba zai kwanta ba!” Atta ta ƙare maganar tana nufar ɗakinta..

Yana tura ƙofar ɗakin ya fara jin shessheƙar kukanta, Ya ƙarasa shiga ciki yana kallonta tana haɗe yan kayan da ta zo dasu a ƙaramar trolley ɗin gabanta, Sakin ƙofar ya yi sai kuma ya ja ya tsaya a wajen ya naɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu. Zahra ta kammala haɗe kayan nata tana kuka ta zura hijabi har ƙasa sannan ta juyo da shirin fita ta ganshi tsaye jikin ƙofa. Kallonsa ta ɗan yi sai kuma ta ɗauke kanta tana sake nufo ƙofar da shirin fita, murya a sanyaye kamar babu abin da ke damunsa ya ce

“Fateemarh!”

Yanda ya yi maganar cike da nutsuwa ya sanyata dakatawa, ta tsaya cak inda take har sannan tana shessheƙar kuka. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya baro jikin ƙofar ya shiga takowa har gabanta, ƙamshin turarensa daya cika mata hanci da kuma kaifin idanunsa ya sanya ta sunkuyar da kanta lokaci ɗaya taji tsigar jikinta na tashi. Kallonta ya dinga yi kafin a hankali ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago haɓarta yana kallon kyakkyawar fuskarta ya ce

“Mene ne?”

Kamar jira take ta faɗa jikinsa tana sakin wani irin kuka, ta ƙanƙameshi kamar zata ɓara ƙirjinsa gida biyu. Abdusammad ya ɗan yi murmushi sai kuma ya saka hannayensa duk biyun ya zagayeta a jikinsa, a hankali kuma cike da nutsuwa ya dinga shafa bayanta ba tare da ya ce komai ba. Bayan mintunan da basu shige biyar ba ta fara rage sautin kukan nata. Ya yi shiru yana lumshe idanunsa har ta yi tsit gaba ɗaya sai shessheƙar kukan da bata daina ba. Sai a sannan ya ɗago kansa daga bayanta yana kallonta ya ce“kukan na mene?”

Girgiza kanta ta yi tana shirin fashewa da wani sabon kukan ya ɗora hannunsa a baki cikin wata irin murya ya ce

“shiiiii!”

Haɗiye kukan nata ta yi, Ya ja kumatunta sannan ya ce“ just tell me kukan me ki ke?” Zahra ta dinga kallonsa da runannun idanunta, kenan bai ma san kukan me take ba? Bai san abin da aka yi mata ba? Sai kawai ta sake jin wani sabon kukan na kwace mata.

Abdusammad kallonta ya dinga yi sai kuma ya girgiza kansa wannan karan fuskarsa a haɗe ya ce“Idan baki min shiru ba zan ɓata miki rai kuma!”

Sanin babu wasa acikin lamarinsa ya sanya ta yi shiru tana murza idanunta, ya taɓe baki yana ƙarewa trolley ɗin hannunta kallo ya ce“get ready nan da 1hr zamu tafi”

Tamkar ta zuba ruwa a ƙasa tasha haka taji saboda daɗi da farin ciki, dan kwata-kwata bata ji daɗin garin ba, kuma ba kowane sanadi ba illa Atta, wadda tun zuwansu bata barta ta huta da jarabarta ba. Sai da ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce“Doctor tafiya zamu yi?” gyaɗa mata kai kawai ya yi yana nufar toilet. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zare hijabin jikinta ta koma ta zauna gefen gadon.

****
Sultan ya dinga kallon Safwan rai ɓace ya ce“amma baka cikin hayyacin ka ko? Baka san me ka ke cewa ba ko?” Safwan dake tsaye yana rufe agogon hannunsa ya ɗan yi gajeran murmushi sai kuma ya ce“Ya Sultan na san me nake mana, kaga maganata ta yi maka kama da ta wanda bai san me yake ba?” a fusace Sultan ya mike tsaye yana masa wani irin kallo ya ce“amma idan haka ne baka da hankali wallahi! Wace irin rayuwa ce wannan Safwan?”

“Me nayi kuma? Dan na sanar da ita gaskiya?. Wallahi Yaya ban taɓa jin son wata yarinya cikin raina sama da Siyama ba, Ni ita zuciyata ke so, amma nasan banida ikon aurenta a yanzu. Dan haka ba zan zafafa na ce dole sai ita ba, zan karbi Nana hannu bibbiyu. Amma dole ne na sanar da ita cewa ina da wadda nake so, kuma nake da burin aure. Saboda haka kar ta saki jikinta tayi tunanin da ita ɗaya zan zauna”.

Jinjina kai Sultan ya yi yana kallonsa sai kuma ya ce“okay kayi duk yanda ka ke ganin shi ne dai dai, ba zan hanaka ba, amma ina son ka sani idan har ka cutar da yarinyar nan wallahi tallahi Allah ba zai bar ka ba, idan har ka yi amfani da aurenka wajen zaluntarta Allah sai ya saka mata!” Yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin fuu ba tare da ya jira ta bakin Safwan ba. Taɓe baki Safwan ya yi ya bi shi da idanu sai kuma ya ci gaba da abin da yake.

****
Ƙarfe 5:10 na yamma suka fito ƙofar gidan, Atta dake riƙe da hannun Nana ta kalli Abdusammad daya haɗe ransa kamar ba shi ba ta ce“to da ka ke haɗe rai shi ne zai hanani abin da naga dama?” kallonta kawai ya yi amma bai ce mata komai ba, ta taɓe baki ta ce“aaa to kaje da baƙin halinka, Ni kada ka tafi dani a baki, baƙonka Annabinka” duk yanda ta bashi dariya dakewa ya yi babu yabo babu fallasa ya ce“Sai kun zo Atta”

To kawai ta ce masa dan sam bai bata fuskar da zata sake wata maganar ba, ya shige motarsa dan daman tuni Zahra ta shiga. Da kyar su Maimoon suka rabu da Atta dan magiya suka dinga mata akan ta zo su tafi tare amma sam taƙi yarda ta ce sai ana i gobe ɗaurin aure zata zo. Babu yanda suka iya da ita haka suka haƙura suka shiga mota, ta sake sallama dasu Aliyu sannan ta kalli Nana fuskarta ɗauke da damuwa ta ce

“Ai da bake za’a yi aure ba ai zaman ki zaki yi anan ma tafi tare” murmushi kawai Nana ta yi dan ita ma taji daɗin zama da ita, Muryarta a sanyaye ta ce“to Atta ki zo mu tafi tare mana” girgiza kai ta yi ta ce“a’a ku dai je ina nan tawowa”

Langwaɓar da kai Nana ta yi ta ce“to sai kin zo” daga haka ta nufi motar Safwan tana daga mata hannu. Sai da motocinsu suka bar ƙofar gidan sannan Atta da sauran jama’ar suka koma ciki cike da begensu.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *