⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 20: Chapter 20

Karfe 4:00 na yamma aka fara henna’s party ɗin, gaba dayansu suna apartment ɗin Hajiya Babba dan duk yafi ko ina girma. A compound ɗin gidan aka kira masu decorations suka tsara wajen, kai ka ɗauka wani event ɗin aka je. Gaba ɗaya dangi na kusa dana nesa sun zo gidan, dan haka wajen ya cika da jama’a. Amaren suna sanye da dogayen riguna na saki maroon colour, kasancewar su farare yasa ya yi musu kyau sosai. Fuskarsu fresh dan basu yi kwalliya ba, sai powder da lip gloss da suka shafa. Kowacce sai harkokinta take da ƙawayenta dan duk an gama masu ƙunshin, Nana kuwa na gefe ɗaya ta zauna kusa da Aunty Mariya da suka zo daga Abuja. Ta yi shiru tana kallon fararen hannunta wanda suka yi kyau da lallen da aka yi musu, sai dai zuciyarta a dagule take da tunane-tunane kala-kala. Sai kusan magriba sannan aka tashi, Kai tsaye apartment ɗinsu ta nufa tana zuwa ta shige ɗakinta tun kafin mutanen gidan su taru.

A gefen gadonta ta zauna tana wani irin numfarfashi dan tun ɗazu take jin ƙirjinta na mata wani irin zafi, Ta kwanta a hankali tana lumshe idanunta, a hankali kuma ta fara jin azabar na ƙaruwa, numfashinta ya fara ɗaukewa dakyar take iya jawo shi. Tana nan kwance har bayan mintuna ashirin sannan wani wahalallen bacci ya ɗauketa, Cikin baccinta taji kamar a mafarki ana kiran sunanta, dan haka ta buɗe idanunta a hankali tana ware su a ɗakin. Babu kowa a ciki dan haka ta tashi zaune tana dafe saitin zuciyarta wanda ya ci gaba da bugawa da sauri, Ta lumshe idanunta sannan ta tashi ta shige toilet. Wanke fuskarta ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito, ta zura hijabinta ta gabatar da sallar magriba sannan ta zare hijabin, tana ƙoƙarin tashi daga wajen Amma ta turo ƙofar tana kallonta ta ce

“Nana ki zo inji Abbanki”

Toh kawai ta ce ta juya ta fita. Ta karasa zare hijabin jikinta sannan ta ɗauki mayafin abayar dake kan gadonta ta rufe kanta dan tuni ta cire ɗaurin sego ɗin ta fito. Bata gan shi a parlon ba, sai taron mutanen gidansu Amma da suka zo. Ta ƙarasa tsakar parlon ta ɗan gaishesu sama-sama sannan ta kalli Amma a sanyaye ta ce“Ina Abban yake?”

“Yana balcony da Abdusammad”

To kawai ta ce sannan ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsaye ta same su da uncle suna magana, ta ƙaraso a hankali tana wasa da fingers ɗinta, sai da ta gaishe da uncle ya amsa yana kallonta sannan ta kalli Abba muryarta na fita a hankali ta ce“Abba gani” envelope ɗin da ke hannunsa na hagu ya miƙo mata yana faɗin

“Yanzu na haɗu da malamin nan naku, shi ne ya ce na kawo miki”

Nana ta sanya Hannunta duk biyun ta karɓa sannan ta ce“Abba wane malamin?”

“I can’t recall his name, but ina yawan ganinsa idan naje Aun”

Nana ta yi shiru sai kuma ta juya a hankali ta koma ciki. Abba ya bita da idanu sai kuma ya kalli Abdusammad ganin shi ma itan yake kallo yasa ya ce“gaba ɗaya ta zama wata so silent da ita. Ban taɓa tunanin akwai lokacin da Nana zata nutsu irin haka ba” murmushi kawai ya yi sannan ya ce“ai fa. Kamar ba ƴar rigimar nan ba”

Abba ya ɗan yi dariya sannan ya kawar da zancen ya koma kan maganar da suke ya ce“Ni ina ga kawai ka yi haƙuri. Tun da kaga Atta ta riga da ta dage, and sanin kanka ne ba zamu iya ja da ita ba. Idan har muka ce a’a zata ga kamar dan babu ran Yaya ne ya sanya” Abdusammad ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce“amma Abba ni bani da niyyar ƙara aure, beside ma koma zan ƙara aure sai na rasa wadda zan aurar sai wannan yarinyar? She’s too young wallahi gaba ɗaya fa da kaɗan ta girmi Nana. Ni bana son auren yarinya ƙarama wallahi”

Abba ya ɗan murmusa kafin ya ce“To ya zaka yi? Tun da dai har kana da matarka wadda kake so to ka bari ayi auren nan kawai. Bayan Atta kana ganin Hajiya ma ta dage, kuma dai ka san ba zata bari a fasa ba, bayan haka ma yau an saka ma yara lalle ai kaga aure ya tabbata” Abdusammad ya yi shiru can kuma ya ce“ai shikenan. Amma ni gaskiya bana jin zan iya tafiya da ita can, sai dai ta zauna anan kawai a samar mata schl ta shiga” Abba ya jinjina kansa ya ce“a’a da dai ka tafi da ita. Cause school ɗin can yafi nan”

Numfasawa ya yi kawai sannan ya ce“tom bari naje dare nayi” jinjina kai Abba ya yi sannan suka yi sallama ya tafi.

****
Nana na shiga daƙinta ta ajiye envelope ɗin gefen gado sannan ta sake ficewa daga ɗakin. Apartment ɗin su Maimoon ta je, ta samu basu nan wai suna gidan Mama. Babu yanda ta iya haka ta dawo gida dan ita ba wani son zuwa Apartment ɗin su Hamida take ba saboda faɗan Mama. Kai tsaye daƙinta ta shige, ta kalli envelope ɗin data ajiye saman gado sai kuma ta nufi kan drawer in da ta ajiye wayarta, missed call ɗin Khadijah ta gani. Dan haka ta ɗauki wayar ta koma ta zauna kan gadon tana dialing numbern nata, ringing biyu ta ɗauka, Nana ta sauke numfashi bata ce komai ba. Khadijah da ke zaune kan sofa ta gyara zamanta tana faɗin

“Ina ki ka shiga ina ta kiranki?”

A sanyaye Nana ta ce“na ɗan fita ne”

Khadijah ta jin jina kanta kafin ta ce

“To ya shirye-shiryen?”

“Yaushe za ki taso?”

Nana ta mayar mata da tambayar ba tare da ta amsa tatan ba. Murmushi kawai ta yi ta ce“Da gobe nake saka rai. Ina jiran Daddy ya dawo ne”

Ɗan haɗe rai Nana ta yi kamar tana gabanta ta ce

“Har sai gobe?”

Khadijah ta waro idanu tana murmushi ta ce“to yanzu da daren nan ki ke son na biyo Flight or what?”

Nana ta yi shiru can kuma ta ce“amma da sassafe zaki tawo?”

Khadijah ta girgiza kanta still smiling ta ce

“a’a zuwa azahar dai, zan biyo flight ɗin 9 kin ga idan na zo zan fara zuwa gidan Ammi”

To kawai Nana ta ce jin kira na shigowa wayarta ta ce“alright sai goben” okay Khadijah ta ce sannan ta katse kiran. Nana ta dinga kallon numbern Junaid da ke ruri akan screen ɗinta, sai kawai ta yi jifa da wayar kan gado ta yi kwanciyarta a gefe. Ganin bai tsaya da kiran nata ba ya sanya ta tashi ta kalli wayar sai kuma tayi tsaki. Ta sanya hannunta ta janyota ta dinga kallon screen ɗin sai kuma ta yi rejecting call ɗin ta kifa wayar kan cinyarta. Ta dafe kanta tana sauke numfashi, Above 5mins kafin ta ɗago fuskarta idanunta sun sake yin jajur kamar me shirin kuka. Ta ajiye wayar tana shirin tashi idanunta ya sauka akan envelope ɗin, Hannunta na dama ta kai ta ɗaukota ta dinga juyawa tana tuna maganar da Abba ya faɗa mata.

“Malaminmu? A Aun?”

Ta tambayi kanta. Sai kuma ta shiga ɓare envelope ɗin ta leƙa, tun da taga tarin takardu taji gabanta ya faɗi. Ta ƙarasa zaro su hannunta na rawa, A firgice ta miƙe tsaye hannunta riƙe da hotunan jikinta sai wani irin rawa yake kamar ana kaɗa ganga, Nana ta dinga girgiza kanta hawaye na biyo kuncinta. Ta ɗauki wayarta da sauri ta shiga dialing numbernsa tana hawaye, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. Bata jira ya yi magana ba ta fara faɗin

“Dan Allah dan Annabi kada ka sake turo min da hotunan nan, wallahi zuciyata na gab da tarwatsewa. Idan har da gaske ka ke sona, so kuma na tsakani da Allah to ka taimaka min ka rufa min asiri” ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Junaid da ke tsaye a balcony ya saki kyakkyawan murmushi muryarsa wasai babu alamar damuwa ya ce

“Da dana ke kiran ki shi ne ba zaki ɗaga ba ko?. Sai yanzu saƙona ya iso gare ki kenan, fatan dai ke kaɗai ki ka gani?”

Nana ta haɗiye wani miyau mai ɗaci ba tare da ta ce komai ba. Junaid ya ci gaba da faɗin

“Ki ɗauka wannan shi ne karo na ƙarshe da zan gargaɗeki akan maganar auren nan. Wallahi idan har aka kai gobe ban ji labarin fasa aurenki ba to ba saƙo zan bawa mahaifinki ya kawo miki ba. A’a shi da kansa zan bawa a matsayin kyautar auren ki”

Runtse idanu Nana ta yi saboda yanda zuciyarta ta yi wata irin bugawa, ta zauna gefen gadon hawaye na zubowa kan fuskarta. Cikin sabon yanayin daya risketa ta buɗe bakinta a sanyaye ta ce

“Shikenan zan fasa auren!”

Nana ta sauke numfashi tana jiran abin da zai ce. Ɓoyyayiyar ajiyar zuciya Junaid ya sauke sai kuma ya ce“Taya zan tabbatar da haka?”

Runtse idanunta ta yi wanda ya bawa hawayen dake cikin idanun damar gangarowa kan fuskarta. Ta ɗan suɗe laɓɓanta na ƙasa kafin ta ce“zan faɗawa Abba bana son auren” jinjina kai Junaid ya yi sai kuma ya ce

“Ok. Na baki daga yau zuwa gobe, idan har ban ji an fasa auren ba to ki sani zan kawo ƙarshen wannan wasan namu”

Nana ta yi shiru tana shessheƙar kuka a hankali. Jin bata ce komai ba yasa ya ce “Zan katse wayar”

“A’a dan Allah… Ina son na tambayeka”

Junaid ya gyara zaman wayar da ke kunnensa yana saurarenta da kyau ya ce“ina ji”

“Da gaske kana sona kuwa?”

Nana ta yi maganar cikin wani irin sanyi daya zarce misali. Junaid ya ɗan murmusa ya ce

“Tambaya ki ke Nana?. Duk abin da nake bakya gani kenan?”

Ta girgiza kanta kamar yana gabanta ta ce“ance masoyin gaskiya baya son yaga masoyiyarsa cikin matsala. Amma me ya sa kai ka ke kokarin yin abin da zai zame mini matsala?”

Junaid ya yi shiru kamar me tunani. Jin haka yasa Nana ta ɗan yi wani murmushi mai haɗe da hawaye ta ce

“shikenan sai da safe”

Daga haka ta katse wayar ta ajiye gefenta. Rasa abin yi ta yi sai kawai ta fashe da wani irin raunataccen kuka, Dai dai nan aka buɗe ƙofar ɗakin. Aunty Ramlah ta dinga kallonta sai kuma ta ƙaraso ciki tana faɗin

“Nana kukan me ki ke?”

Girgiza kai Nana ta yi cikin kuka ta ce“Aunty ki kira min Ammana. Dan Allah ki kirata mutuwa zan yi”

Aunty Ramlah ta dinga kallonta sai kuma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Nana ta yunƙura da kyar ta mike ta haɗe hotunan ta tusa ƙasan katifar gadonta dai dai nan Amma ta shigo ɗakin Aunty Ramlah na biye da ita. Amma ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, Ta zauna gefen gadon ta dafata cikin rauni ta ce

“Nana mene ne kuma?”

Kasa bata amsa ta yi sai kawai ta shige jikinta tana sake rushewa da wani sabon kukan, Amma ta ɗora hannunta akan bayanta ta dinga shafawa a hankali. Gaba ɗaya bata jin daɗin yanda Nanar ta koma, ta rasa dalilin daya sanya taƙi kwantar da hankalinta. Suna nan zaune har bayan mintuna biyar sannan ta fara rage sautin kukan nata, dan haka Amma ta ɗagota tana kallonta ta ce“kukan me ki ke Nana?” cikin shessheƙar kuka Nana ta ce

“Amma dan Allah ina son magana da Abba. Dan Allah Amma, zuciyata zafi take min”

Ganin yanda take numfashi da kyar ya sanya Amma ta ce“to tashi muje na raka ki yana ɗakinsa” dakyar Nana ta miƙe Aunty Ramlah na kallonsu ta ce“ku je bari na jira anan” okay kawai Amma ta ce sannan ta riƙe hannun Nana suka fita daga ɗakin a hankali. Aunty Ramlah ta girgiza kai tana kokarin zama gefen gadon ta ce

“oh Allah ya yi mana maganin masifa”

Zaune suka tadda Abba kan kujerar da ke ɗakin, yana waya da wasu abokansa da zasu zo daga Paris. Ganin hawaye a fuskar Nana ya sanya ya katse wayar ba tare da ya gama ba. Ya dinga kallonsu sai kuma ya ce

“lafiya dai?”

Ya yi tambayar yana miƙewa tsaye. Amma bata ce komai ba, sai sakin hannun Nana da ta yi. Ta ƙarasa gabansa a hankali tana kuka ƙasa-ƙasa, Ba ƙaramin rikicewa Abba ya yi ba, dan duk wani abu daya shafi Nana baya ɗaukansa da sauƙi. Ya riƙe hannayenta duk biyun muryarsa cike da damuwa ya ce

“Nana mene ne?”

Sunkuyar da kanta ta yi wasu zafafan hawaye suka shiga sakkowa kan fuskarta. Ta kasa cewa komai sai murɗa yatsun hannunta take, Abba ya yi shiru sai kuma ya kalli Amma ya ce“what’s going on?” girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce“wallahi nima ban sani ba. Ramlah ta zo ta ce min wai gata nan tana kuka, da naje shi ne ta ce na kawo ta wajenka”

Abba ya mai da idanunsa kan Nana wadda har sannan bata ce komai ba. Ya zaunar da ita sannan ya zauna gefenta yana kallonta sosai ya ce“Nana tell me meya faru? Why are you crying?”

Ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleshi, bakinta ya fara rawa kamar zata yi magana sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tana sakin wani sabon kukan. Abba da ransa ya fara ɓaci ya ce

“Kin faɗa min mene ne ko sai na bugeki?”

A hankali ta sake ɗago kanta tana kallonsa, sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli Amma dake tsaye kusa da su. Ganin duk ita suke kallo yasa ta saukar da idanunta ƙirjinta na wani irin bugawa da ƙarfi, ta buɗe bakinta da take jin kamar ba nata ba. In a very polite tongue ta ce

“Abba daman akwai abin da nake son faɗa maka, but…but I can’t, saboda ban san ya zaku ɗauki al’amarin ba”

Abba ya yi shiru yana saurarenta. Jin babu wanda ya ce komai a cikinsu yasa ta ɗago kanta hawaye na biyo fuskarta ta ce

“wallahi bana son Yaya Safwan. Bana son aurensa, dan Allah dan Annabi Abba a fasa auren nan. Wallahi ba zan iya zama dashi ba, dan girman Allah kawai…”

Bata samu zarafin faɗin ƙarashen abin da ke bakinta ba, sakamakon zazzafan marin da Abba ya sauke mata akan both checks ɗinta. Ta sanya hannunta ta dafe kuncinta tana jin wata irin raɗaɗin azaba. Dakyar ta iya buɗe idanunta wanda take jin kamar sun fashe ta ɗago kanta. Tsaye taga Abba a gabanta yana wani irin huci kamar yunwataccen Zaki. Yanda yake kallonta zai tabbatar maka da tsananin ɓacin ransa da yake ciki, gumi sai tsatsafo masa yake duk da ac dake ɗakin.

Amma ta ƙaraso wajen da sauri ta jawo hannun Nana itama ta sauke mata wani zazzafan mari a kuncinta na dama, Nana ta rasa yanda zata yi saboda azabar data mata yawa. Cikin tsananin ɓacin rai Amma ke faɗin

“Wato duk irin abin da na faɗa miki baki ji ba kenan ko Nana? Duk nasihar da nayi miki ta tashi a banza kenan ko? Baki ji abubuwan da nace miki ba ko?”

Ban da girgiza kai babu abin da Nana ke yi dan gaba ɗaya magana ta gagareta. Ta zube a ƙasa ta riƙe ƙafafun Abba da duka hannayenta biyu cikin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fara magana

“Na sani Abba ban kyauta ba, ban kuma yi dai dai ba idan har naƙi bin umarninka a matsayinka na mahaifina. Ka cancanci nayi maka kowace irin alfarma Abba, amma wallahi ba zan iya wannan ba, ba zan iya auren Yaya Safwan ba. Zuciyata ba zata jure zama dashi ba, na so na danne na kuma yi haƙuri akan haka, amma ina gudun abin da hakan zai haifar daga baya. Dan haka dan girman Allah, dan soyyayar ka da Annabinsa. Ka raba auren nan dan Allah, kada ka bari na aure shi Abbana, ka rufa min asiri!”

Ta ƙare maganar tana sakin wani irin marayan kuka. Dakyar Abba ya janye ƙafafunsa daga gurin, ya shiga zagaye ɗakin ba tare da ya ce komai ba. Amma ta tsaya a wajen kamar statue, sai ta kalleshi sai kuma ta kalli Nana. Above 5mins kafin yaja ya tsaya a tsakiyar ɗakin hannayensa naɗe a ƙirjinsa yana kallonta. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajur dasu, har wani ruwa-ruwa ne ya kwanta a cikinsu na zallar baƙin ciki. Ya furzar da zazzafan numfashi daga bakinsa sai kuma ya shiga girgiza kansa yana faɗin

“Wai Ƴata! Wai ƴar dana haifa ce zata faɗi irin wannan maganar. Ƴar da nake saka ran zata yimin biyayya koda ace bata son abu, Yar dana ɗauki dukkan yarda na ɗora mata ita ce take shirin watsa min ƙasa a idanu!. Yar da nake tunanin ba zata taɓa bani kunya ba, ita ce ke shirin tona min asiri a cikin dubban jama’a.” Ya tsaya da maganar yana sauke numfashi, Sai kuma ya sake mai da idanunsa kanta a zafafe ya ce

“Wallahi tallahi baki isa ba Nana! Ban haifi Yar da zata juyani ba. Duk abin da ki ke so zan iya miki shi, amma ba zan taɓa yarda ki zubar da mutuncin gidanmu ba! Baki isa ba Nana!”

Kasa ɗago kanta ta yi sai hawaye take dan yanzu ko sautin kukan nata ma ba’a ji. Amma ta yi shiru tana kallonsa duk da bata ji daɗin abin da Nana ta yi ba, hakan bai hanata jin tausayinta ba a matsayinta na mahaifiyarta. Sai dai ganin yanda ran Abba ya ɓaci ya hanata cewa komai. Da kansa ya tako har gabanta ya sanya hannunsa ya ɗagota yana kallonta ya ce

“Koda auren Safwan na nufin rasa rayuwarki wallahi Nana sai dai ki mutu. Na kuma yarda na rasa ki, akan ki zubar da martaba da kuma ƙimar da muka ɗauki shekaru masu yawa muna tattalinta. Dan haka ki shirya zama matar aure daga yau zuwa jibi.” yana gama faɗin hakan ya saketa ya juya ya fice daga ɗakin yana bugo ƙofar. Amma ta sulale a ƙasa tana jin ranta na mata wani irin suya, ita kuwa Nana kasa motsi ta yi sai numfarfashi take. Har bayan mintuna sha biyar suna zaune a wajen zuciyoyinsu babu daɗi, Nana ta yunƙura da kyar ta tashi ta fice daga ɗakin tana riƙe da kanta, Amma ta bita da idanu har ta fice. Lokaci ɗaya ta fashe da wani irin kuka, wanda rabonta da ta yi kuka tun rasuwar mahaifiyarta sai gashi yau tana sake kuka akan auren NAANAH..

****
Ƙarfe 9:30 na dare ta buɗe ɗakin ta shigo. Zaune ta hangeshi tsakiyar gado ya tankwashe ƙafafunsa yana sipping coffee a hankali, hannunsa ɗaya akan system yana operating ɗinta. Zahra ta dinga kallonsa can kuma ta sauke numfashi ta ƙaraso ciki, A gefen gadon ta zauna tana kallonsa har sannan ba tare da ta ce komai ba. Idanun da yaji suna yawo akan sa ya sanya shi ɗago kansa, suka yi ido biyu da Ita, a hankali ta sauke nata idanun. Ya dinga kallonta sai kuma ya rufe system ɗin ya sakko daga kan gadon, a gefen drawer ya ajiye system ɗin ya kuma ajiye mug ɗin hannunsa. Sannan y koma ya zauna yana kallonta yace

“Zahra”

Yanda ya yi maganar a sanyaye ya sanyata ɗago kanta, hawaye ya gani kan farar fuskarta. Ya yi shiru can kuma ya ce“zo mana” jiki a sanyaye ta tashi ta ƙarasa inda yake sannan ta zauna, ya jawo hannunta yana shafawa a hankali ya ce

“Mene ne?”

Muryarta na rawa ta ce“doctor da gaske aure zaka yi?”

Ta ƙare maganar tana ɗago idanunta wanda hawaye ke zuba daga cikinsu. Abdusammad bai iya ɓoye-ɓoye ba dan haka ya gyaɗa mata kai ba tare da ya ce komai ba. Ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali, girgiza kansa y yi sai kuma ya ɗago fuskarta da hannunsa na hagu yana kallonta ya ce

”but you promised cewa ba zaki tada hankalin ki ba right?”

Zahra ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta shiga goge hawayen idanunta ta ce“i’ll not. Allah ya bamu zaman lafiya”

Amin kawai ya ce sai kuma ya yi shiru yana nazarinta. Tabbas bata ji daɗi ba, kawai dai bata son ta nuna tashin hankalinta har ya ɓata masa rai, dan haka shima bai sake maganar ba suka shiga wata hirar ta daban.

Daren ranar babu wanda ya runtsa tsakanin Abba, Amma da kuma Nana. Kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa, Amma na tunanin yanda zata saka Abba ya yarda a fasa auren Nana, yayinda Abba ke tunanin yanda zai ɓoye al’amarin kada kowa ya samu labari. A ɓangaren Nana kuma ta kwana tana kukan rashin sanin abin yi, ya zata yi da Junaid da kuma Zahra? Junaid ya yi alkawarin idan har bai ji maganar fasa aurenta gobe ba zai turowa Abba hotunanta. Haka ma Zahra, dan haka abin duniya ya isheta ta kasa koda runtsawa sai juyi take akan gadonta, ana fara kiraye-kirayen sallar asuba ta mike daga kwancen, ta shiga toilet ta ɗauro alwala sannan ta fito ta fara gabatar da sallolin nafila har aka yi assalatu. Koda ta idar da sallah zama ta yi nan kan ladduma ta ci gaba da saƙa da warwara har gari ya fara haske. Ringing ɗin wayarta ne ya sanya ta tashi daga wajen, ta ƙarasa gaban mirror ta ɗauki wayarta, ganin kiran Junaid ya sanya gabanta ya yanke ya faɗi, hannunta na rawa ta ɗaga kiran ta kai kunne. Junaid na fitowa daga masallaci ya ce

“Ya dai Nana?”

Shiru ta yi tana tunanin ta hanyar da zata fara faɗa masa. Jin bata ce komai yasa ya sake cewa

“are you there?”

Ta gyaɗa kanta kamar yana gabanta. Sai kuma ta numfasa ta ce

“eh.”

“Ya ku ka yi dasu?”

Girgiza kanta ta yi ta ce

“basu yarda ba, Abbana ya ce dole sai na aure shi. Dan Allah dan Annabi sir ka yi haƙuri, ka barni na yi auren nan. Ni na haƙura da soyyayar, Allah ya baka wadda ta fini”

Junaid ya yi wani murmushi sai kuma ya ce

“shikenan Nana. Allah ya baku zaman lafiya, zuwa an jima kuma saƙona zai iso ga mahaifinki.”

Daga haka ya katse kiran, girgiza kai Nana ta yi sai kuma ta sake dialing number amma sai aka ce mata a kashe. Ta koma gefen gado ta zauna lokaci ɗaya ta fashe da kuka, kifa kanta ta yi akan cinyarta ta fara rera kukanta, ta dinga jin zuciyarta na mata wani irin zafi da suka, tana nan zaune har bayan mintuna biyar wayarta ta fara ruri dan haka ta ɗago kanta da sauri ta ɗauki wayar da tunanin Junaid ne. Sai dai ganin lambar babu suna yasa ta kawar da wannan tunanin, ta yi kamar ba zata daga kiran ba sai kuma wata zuciyar ta ce mata

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *