⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 28: Chapter 28

Ban da dariya babu abin da Aliyu ke yi, Ya dafe cikinsa sannan ya ce“daga faɗar gaskiya? Allah ya nuna mana to” wani dogon tsaki yaja ya yi gaba dan ba zai ma iya zama a wajensa ba ya ce“Allah ya baka sauƙi” Aliyu ya amsa da Amin yana dariya har sannan. Ganin ya yi gaba abin sa yasa shima ya juya ya nufi cikin gidansa. Ya yi nisa yaja ya tsaya maganar Aliyun na masa yawo a ƙwaƙwalwa, yaja wani sabon tsakin yana ayyana ta inda zai iya wata mu’amala da Nana, yarinyar da yake ma kallon yarsa. Saurin kawar da tunanin ya yi a fili ya ce

“Astgfirullah”

Sannan ya yi gaba yana sake girgiza kansa.

****
Washegari da sassafe around 7:00am suka gama shiri cikin wata atampa glitter da Mami ta ɗinka musu. Ko powder babu wadda ta shafa a cikinsu dan duk jikinsu a sanyaye yake, suka fito parlon suna jiran Daddy. After 5mins ya fito yana gyara zaman babbar rigar jikinsa Mami na biye dashi da kuma Adeel, Tsaye ya samesu suka gaisheshi ya amsa cike da fara’a sannan ya maida idanunsa kan Mami ya ce“to sai mun dawo ko” murmusawa ta yi ta ce“Allah ya dawo daku lafiya.” sannan ta ƙarasa inda suke tsaye ta dafa Nana ta ce“daughter sai yaushe?” rungumeta Nana ta yi ta fara kuka ƙasa-ƙasa. Mami ta ɗagota tana goge mata hawayen ta ce“haba dai kuka, shikenan kuje Allah ya tsare.”

Cikin shassheƙar kuka ta ce“Mami yaushe zaki zo?” murmushi Mami ta yi kafin ta ce“nan kusa in sha Allah kinji.” Toh kawai Nana ta ce sannan Daddy ya ce“to idan kun gama muje kun san jirgi baya jira” sakinta Mami ta yi tana musu Allah ya tsare, Khadijah ta rungumeta ta ce“sai mun dawo Mami” Allah ya tsare ta ce sannan tabi bayansu Daddy da suka yi waje. Adeel ne yaja motar kai tsaye kuma filin tashin jirage na Malam Aminu Kano suka nufa, basu daɗe ba kuma jirginsu ya tashi zuwa Yola.

Tafiyar awa ɗaya ce ta kawo su Adamawa, jirginsu ya sauka a filin tashin jirage na Yola international airport. Bayan sun fito daga airport suka shiga mota dan already Daddy ya yiwa wani friend ɗinsa magana akan zuwansu, kai tsaye kuma M-Shuwa Estate suka nufa. Tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai, Nana ta yi nisa cikin tunani, gabanta sai faɗuwa yake. Tsoronta ɗaya abin da zai faru idan ta koma gidan, Khadijah dake danna wayarta a hankali ta dinga kallonta time to time a haka har suka ƙarasa estate ɗin. Sai da suka tsaya a bakin gate ɗin wajen securities kafin suka basu damar shiga da motar ciki. A compound ɗin su Nana suka yi parking, saboda mutanen da suka hango tsaye, Nana ta ɗan waro idanunta tana son ganin su wane a tsaye, sai dai kai tsaye ba zata ce gasu ba saboda sun juya baya. Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya buɗe motar ya fito, Sai a sannan Khadijah ta kalleta ganin bata da shirin sauka ta ce“Nana mun zo fa” numfasawa ta yi sai kuma ta gyaɗa mata kai. Khadijah ta buɗe side ɗinta ta fito tana gyara zaman mayafin jikinta, A sanyaye Nana ta buɗe motar ta fito tana riƙe da wayarta. Ganin Daddy ya yi gaba ya sanya ta kalli Khadijah kamar zata yi magana sai kuma ta yi shiru, Daddy kuwa wajensu Abba ya ƙarasa da suke tsaye shi da Papa da Abdusammad. Sallama ya yi musu suka amsa sannan suka gaisa fuskarsa a sake ya ce

“Yallabai wajenka nazo” ya yi maganar yana kallon Abba dan ya riga da ya san shi. Murmusawa shima Abba ya yi ya ce“Tom Alhaji muje ciki” jinjina kansa ya yi sannan ya juya ganin yanda suka cake ya ce

“Ku tawo mana”

Maganar ta sanya hankalinsu kai wa inda su Nana ke tsaye, cikin rashin sa’a idanunta ya sauka cikin na Abba. Wani irin abu taji ya zo mata wuya, ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. Abba ya haɗiye wani miyau mai ɗaci sannan ya kalli Daddyn Khadijah murya a shaƙe ya ce

“lafiya dai Alhaji?”

Dafa shi Daddy ya yi ya ce“idan mun shiga ciki zaka ji” shiru kawai Abba ya yi yana kallonsa, Jiki a sanyaye suka ƙaraso wajen, barin Nana data sunkuyar da kanta bakinta na rawa ta kalli Papa ta gaishe shi. Da murmushi a fuskarsa ya amsa, dan har ga Allah yaji daɗin ganinta, Ta saci kallon Abdusammad wanda ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, a hankali ta sunkuyar da idanunta sannan ta gaishe shi. Ba zaka taɓa cewa dashi take ba, dan ko motsi bai yi ba ballantana ta saka ran yaji abin da tace. Ta ɗan yi shiru tana jin hawaye na neman zubowa kan fuskarta, ta kalli Abba wanda ke kallonta sai kawai ta tafi zata shige jikinsa. Ɗaga mata hannu ya yi wanda ya sanyata dakatawa, cikin kakkausar murya ya ce

“Kar ki kuskura!”

Ya faɗi maganar yana nufar cikin gida kamr zai tashi sama. Daddy ya sauke numfashi sai kuma ya kalli Papa da Abdusammad ya ce“muje ciki kuma dan Allah” toh Papa ya ce masa, Abdusammad kuwa girgiza kansa ya yi ya ce“sorry ku je kawai” Daddy ya ɗan murmusa kafin ya ce“Da ka yi haƙuri mun shiga cikin” ya buɗe baki zai yi magana Papa ya riƙe hannunsa ya ce“muje” daga haka suka nufi cikin gidan. Daddy ya juyo yana kallonsu ganin Nana sai kuka take ya dafata cikin son kwantar mata da hankali ya ce“kar ki damu komai zai shige kin ji.” Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta daina kukan ba, Ya kalli Khadijah ya ce“ku samu guri ku zauna ko ku koma mota kafin mu gama” toh kawai ta ce masa sannan ta riƙe hannun Nana. Ya juya ya nufi gidan shima. Kalle-kalle ta fara yi can ta hango wata bukka ta zamani nesa dasu kaɗan, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ja hannun Nana suka ƙarasa wajen. Zama ta yi sannan ta saki hannunta, Nana ta ja kujera ta zauna ta ɗora kanta kan table ɗin wajen ta ci gaba da kukanta a hankali.

****
A parlourn kuwa Abba ne zaune kan sofa sai Abdusammad a kusa da shi, ɗaya kujerar kuma Papa ne zaune. Daddy kuma na zaune kujerar dake facing ta Abba idanunsa maƙale a kansa ya ci gaba da fad’in

“Kamar yanda na faɗa dole sai mun yi haƙuri. Saboda mu iyayene, babu alfanu cikin fushi da yara. Yanzu idan ka yi fushi da ita Alhaji hakan ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba, ba zata shiryu ba, sai dai ma ta sake lalacewa. Domin fushin iyaye akan ya’ya masifa ce babba, kome suka aikata dole ne mu yi haƙuri. Kuma ba’a cewa an sallama ɗa, idan ka sallamata ka nunawa Allah ka zaga akan amanar daya baka, ka butulce masa. Na san kuma ba zaka so kayi hakan ba, Laifi ne ta riga da ta aikata shi, wanda idan aka biyo abun tun daga farko ma bata da wani laifi, ƙaddara ce, duk abin da ta yi yarinta ce. Laifin na yaron daya ɗauketa hotunan ne”

Daddy ya yi shiru yana kallon Abba wanda ya yi ƙasa da kansa yana jin zuciyarsa na tafasa. Ganin halin da yake ciki ya sanya Daddy numfasawa kafin ya ci gaba da faɗin

“Dan Allah Alhaji Ahmad kayi haƙuri. Ka yafe mata, ka ɗauki komai a matsayin ƙaddara, kada ka ce zaka riƙeta a ranka. Yarinya ce ƙarama, har yanzu bata kai munzalin hankali ba. Ballantana ace tana sane ta aikata abin da tayi. Maganar aure kuma ka aura mata kowane, tun da daman ita ba ƙi ta yi ba, tana gudun abin da zai je ya dawo ne, kuma har yanzu bata san kun ga hotunan ba. Da nasan ba zata taɓa biyoni ba, bana gari sanda ta zo, da wallahi a ranar zan dawo muku da ita.”

Ya ƙare maganar a tausashe. Girgiza kai Papa ya yi cikin mutuntawa ya ce“haka ne Alhaji, wannan haka yake. Haƙuri shi ne ribar zaman duniya, kuma dole mu yi hakuri da wawtar ya’yanmu. Kamar yanda mu ma iyayenmu suka yi haƙuri da tamu, Babu wnada ya shige ƙaddara ta faɗa masa, komai girmansa komai ƙanƙantarsa. Ni wallahi tausayi ma yarinyar ke bani, Allah ya jarrabeta da ƙananun shekaru, sauran ƴan uwanta duk suna zaune hankali kwance.”

Daddy ya ce“Allah sarki. Daman haka Allah ke ikonsa, wani bawan sai ya yi ta jarrabashi daga wannan sai wannan, wani kuma kamar bai zo duniya dan wahala ba. Amma ubangiji da kansa yake faɗa gwargwadon jarrabawarka, gwargwadon kusancinka gareshi. Kaga ashe jarrabawa na tafiya da imanin mutum ne”

Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Allah mai girma, Allah ya bamu ikon cinye jarrabobinmu” da Amin suka amsa a tare sai kuma parlon ya dauki shiru. Abdusammad hankalinsa na ka Abba wanda har sannan bai ce komai ba, ganin kamar jiransa ake ya sanya ya ce“Abba dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba laifinta bane, idan ma tana da laifi to bai shige na kula yaron data san ba ɗan danginta bane. Kuma nayi magana dashi yaron kansa, ya tabbatar min da cewa shi ne ya sanya aka ɗaukesu hotunan saboda ya dinga mata barazana ta yarda ta aureshi, amma bai ce mata ta gudu ba. Batun guduwarta nada alaƙa da Safwan ne da Zahra. They’re behind it”

Ya yi shiru yana jin ɗaci a kasan ransa. Da mamaki suka dinga kallonsa, Har Abba sai da ya kalleshi. Papa ya ce“ka yi mana bayani yanda zamu fahimta Abdusammad” numfasawa ya yi sannan ya basu labarin duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. Papa ya dinga girgiza kansa cike da mamaki da al’ajabi, Shi kansa Daddy sai da abun ya taɓa shi. Ya kalli Abba wanda ya yi shiru har sannan ya ce

“Ka gani Alhaji. Gaba ɗaya ma ba laifinta bane, yaudararta aka yi. Dan haka dan Allah ka yafe mata”

Ɗago kansa ya yi ya kalleshi. Sai kuma a hankali ya zare glasses ɗin dake idanunsa, ya sanya hanky ya goge hawayen dake maƙale cikin kurmin idonsa. Ya yi gyara murya kafin ya ce

“Ni daman ban riƙeta ba. Ban kuma taɓa tunanin aibatata ba, kawai tana bani tausayi ne, yanda rabuwarta ta lalace da ƙananun shekaru. Amma tun da an yi haka babu komai, Allah ya yafe mana gaba ɗaya, ya rabamu da mummunar ƙaddara.”

Da Amin suka amsa masa sannan Abdusammad ya ce“Abba babu abin da ya sameta fa. Ba wai ya lalata bane ko wani abu, kawai dai ya ɗauketa hotunan ne, ka daina damun kan ka dan Allah.”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleshi a sanyaye ya ce“da gaske?” gyaɗa masa kai Abdusammad ya yi. Ya zame jikinsa daga kan sofar ya durƙusa ya yi sudujusshukur ya godewa Allah sannan ya tashi ya koma ya zauna. Daddy ya yi murmushi ya ce“mun gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara girma” girgiza kai Abba ya yi ya ce“a’a kai ne ka cancanci mu yiwa godiya. Ka tunasar dani abin da na manta, sannan ka tawo tun daga wani gari dan kazo ka gyara ɓarna. Allah ya biya ka da gidan aljanna” Da Amin suka amsa sannan ya sake cewa“To yanzu ya maganar auren nata? Za’a bari ta huta ne ko kuwa akwai wanda zai aureta yanzu?” murmushi Abba ya yi ya girgiza kansa ya ce“ai an ɗaura mata auren tun ranar” washe baki Daddy ya yi ya ce“masha Allahu. Wane mijin?” da hannu Abba ya nuna masa Abdusammad wanda ya yi shiru ya ce“shi ne ya aureta tun a ranar” murmushin jin daɗi Daddy ya yi yana kallonsa ya ce“naji daɗi sosai wallahi, Allah ya sanya albarka ya bada zaman lafiya.” Suka amsa da Amin sannan ya miƙe yana gyara rigar jikinsa ya ce”to Alhaji ni zan shige a ƙara haƙuri” miƙewa duk suka yi Abba ya ce“da sauri haka? Ba zaka yini ba?” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“da wuri nake so na koma ne. Jiya na dawo ƙasar” Papa ya ce“Allah sarki. To Allah ya bada lada, mun gode sosai” ya amsa da Amin sannan suka fito daga parlon a tare. Ganin bai gansu ba ya sanya ya kira wayar Khadijah, bayan ta ɗaga ya ce ta fito dan haka ta taso tana riƙe da hannu Nana suka dawo wajen. Daddy ya dafa Nana ganin yanda idanunta suka kumbura ya ce“Mamana ya isa haka kukan. Komai ya shige kinji.” da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta kalli Abbanta, ganin ita yake kallo yana murmushi ya sanya ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana ƙanƙameshi. Abba ya rungumeta tsaf a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Ita kuwa sai faman kuka take, Murmushi duka suka yi ban da Abdusammad wanda har sannan fuskarsa babu yabo babu fallasa. Daddy na murmushi ya ce“to ba zaki zo muyi sallama ba?” sakin Abba ta yi ta dawo wajensa kanta a ƙasa. Ya ce“Allah ya yi albarka ya kiyaye gaba kin ji.” a sanyaye ta amsa da Amin. Ya sake musu sallama sannan ya kalli Khadijah ya ce“muje ko” da sauri Nana ta kalleshi sai kuma ta ce“Daddy ba zata zauna anan ba?” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“a’a Nana. Idan an kwana biyu sai ta zo” bata ji daɗi ba, kuma ba dan taso ba suka yi sallama da Khadijahn ta rakasu har mota sannan ta dawo gurin Abbanta. Sam taƙi yarda da bar jikinsa, Papa ne ya kalleta yana murmushi ya ce“to ni bari na shige office, kije Apartment ɗin Hajiya Babba kin ji” to kawai ta ce ya juya ya bar wajen sannan suka nufi gida ita da Abba..

Amma na zaune gefen gadonta ta rufe fuskarta da hannunta tana tunani wanda ya zamar mata dabi’a taji an bude ƙofar ɗakin. Da sauri ta ɗago kanta, sai dai wadda ta gani ya sanya ta miƙe tsaye zumbur bakinta na rawa ta shiga nunata da yatsa tana cewa

“Naaana. Nana?! Ke ce?”

Da gudu ta tafi ta rungumeta. A tare suka fashe da kuka, Amma ta dinga taɓa ta kamar zata zare ta ce

“Nana. Nana ke ce? Ina ki ka tafi ki ka bar mu? Me yasa Nana?”

Kasa bata amsa ta yi sai sake ƙanƙameta da take. Abba ya shigo ɗakin yana kallonsu, bai ƙoƙarin hana su ba ya ɗauki abin da ya zo ɗauka sannan ya fice daga ɗakin ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba dan sanar da ita..

****

Is been a days da dawowar Nana gida, lokacin kowa na estate ɗin ya san ta dawo, Safwan har sannan bai iya zuwa ya sameta ba duk da ya ji sauƙi, Zahra kuwa idan hankalinta ya yi dubu to ya tashi, dan tsoronta ɗaya ranar da za’a ce Nana ta shigo gidan a matsayin matar Abdusammad. Bangaren Nana kuwa babu abin da ke damunta, sai dai koda yaushe tana ɗakinta dan tun bayan sanar da ita da aka yi cewa Safwan ya fitar da hotunanta bata sake samun sakewa ba. Kunyar kowa take ji, Idan har ka ganta a waje to sai dai apartment ɗin Hajiya Babba idan Atta ta kirata dan har sannan taƙi komawa Njomboli. Yau ma kamar kullum tana zaune a daƙinta tana game aka buɗe ƙofar ɗakin, bata ɗago kanta ba amma ta katse game ɗin tana jiran abin da Ammar zata ce. Jin an yi shiru ya sanya ta ɗago kanta a hankali, idanunta ya sauka akan Zahra dake tsaye bakin ƙofar ɗakin. Sauke idanu ta yi ƙasa, Zahra ta numfasa sannan ta shigo ɗakin ta mayar da kofar da rufe. Ƙarasowa ciki ta yi ta zauna gefen gadon tana kallon Nana. Ita kuwa ɗauke kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta a hankali, Sun ɗauki mintuna a haka kafin Zahra ta yi ƙarfin halin cewa

“Nana”

Kamar ba zata amsa ba. Sai kuma ta tuna da abin da Amma ta ce mata, dan haka ta amsa ciki-ciki, hakan bai damu Zahra ba dan bama ta yi tunanin zata amsa ba ɗin. Ta numfasa sannan ta ce“na san ba lallai bane abin da zan nema amma ya zama dole na faɗa miki koda ba zaki yarda ba. Dan Allah Nana…”

“Babu komai Aunty, Ni ban riƙe ki ba. Allah yaga zuciyata”

Nana ta katseta da sauri. Kallonta kawai Zahra ta yi ta kasa cewa komai, Nana ta sauka daga kan gadon ta ɗauki Jersey veil ɗin dake kan gado ta ɗora kan riga da wando jikinta, kasancewar jeans ne a jikinta blue sai yar ƙaramar riga me bottles itama blue, ta gama yafa mayafin sannan ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake kallonta ba.

Da idanu kawai Zahra ta bita sai kuma ta sunkuyar da kanta, daman ta san ba lallai bane ta saurareta, sai dai ta yi hakan ne a bisa umarnin da Umma ta bata. Zaune ta samu Amma a parlon tana cin abincin rana, ta dinga kallonta sai kuma ta ce“har kun gama?” gyaɗa mata kai ta yi tana shirin fita waje ta ce“eh.”

“Nana!”

Cak ta tsaya jin yanda Ammar ta kira sunanta, ganin irin kallon da take mata ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“A haka zaki fita?”

Amma ta yi tambayar tana kafeta da idanu. Kallon jikinta ta yi ba ƙarya jeans ɗin ya matseta sosai, dan duk surar jikinta ta bayyana. Amma ta ajiye spoon ɗin hannunta still looking at her ta ce“bana son shashanci fa”

Sum-sum ta koma daƙinta, bata ko kalli Zahra dake zaune tana kuka ƙasa-ƙasa ba ta ƙarasa press ɗinta ta ɗauki wata After dress baƙa ta ɗora akai sannan ta fito parlon. Kallo Ɗaya Amma ta yi mata ta ɗauke kai, ta fice daga parlon da sauri kai tsaye kuma apartment ɗin Maimoon ta nufa.

Koda ta shiga bata sameta a parlon ba, ƙamshin girkin da taji ya sanya ta nufi kitchen ɗin, tsaye ta sameta tana juya stew, ta jingina da jikin cabinet tana murmushi ta ce

“Amaryar Yaya Aliyu”

Kallonta kawai Maimoon ta yi sai kuma ta ɗauke kai ta rufe tukunyar sannan ta dawo gabanta ta ce“uwar gida” daga haka ta fice daga kitchen ɗin. Bin bayanta Nana ta yi suka dawo parlon, ta zauna kan kujera ta ɗauki remote ta ƙaro gudun ac dan zafi take ji, Nana ta zauna gefenta ta ɗora kanta a cinyarta ta ce“ke yanzu dan Allah duk sanyin da ake bakya ji?” gyaɗa mata kai Maimoon ta yi. Nana ta taɓe baki ta tashi zaune kamar wadda aka tsikara ta ce tashi zaune tana kallonta ta ce“kin san me?” girgiza mata kai Maimoon ta yi, Nana ta hankaɗeta ta ce“ke ji banza. Ina miki magana kina wani shareni wai ke matar aure” murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“to ke me ce ce?” tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce“matar gida mana. Wai abun mamaki duk kun yi aure” ta sake tuntsirewa da dariya. Kallonta kawai Maimoon ke yi ba tare da ta kanta ta ba. Nana ta ce“wai Zahra ce ta zo apartment ɗin mu yanzu wai na yafe mata” gyara zama Maimoon ta yi ta ce“sai ki ka ce mata me?” ɗan juya Idanunta ta yi kafin ta ce“na ce mata ai na yafe mata” wani mugun kallo Maimoon ta watsa mata ta ce“amma ke banza ce wlh” murmushi kawai Nana ta yi ta ce“to me zance mata? Ai idan ta yimin da kyau ta sani, idan kuma ta cutar da shima ta sani.”

Tashi tsaye Maimoon ta yi tana kallonta cike da masifa ta ce“Ada kenan da baki da damar ramawa, yanzu kuwa kina da damar da zaki rama ki nuna mata ke ba yarinyar da zata rainawa hankali ba ce.”

Kallonta kawai Nana ta dinga yi, Maimoon ta ci gaba da faɗin“koda wasa kada ki bari ta huta, ki nuna mata cewa ke ki ke da gida kuma ke ce yar uwarsa” Ita dai Nana kallonta kawai take dan ba fahimtar abin da take cewa ta yi ba. Ta taɓe baki ta ce“to wai akan wa zan rama?”

“Akan uncle Abdusammad mana!”

Shiru Nana ta yi sai kuma ta ce“to a matsayina nawa?”

Harararta Maimoon ta yi ta ce“a matsayinki na matarsa mana! Kuma kishiyarta.”

Wani kallon sheƙeke Nana ta yi mata sai kuma ta ce“ke me ki ka ce?” sai a sannan Maimoon ta tuna abin da ta faɗa. Lokaci ɗaya ta sanya tafin hannunta na dama ta rufe bakinta a fili ta ce

“Ya ilahi”

Leƙa fuskarta Nana ta yi. Ta ɗago tana kallonta, da hannu ta yi mata alama da mene ne, ta girgiza kanta tana murmushi ta ce“ke babu komai. Zauna ki ji” taɓe baki Nana ta yi sai kuma ta koma ta zauna tana kallonta, Maimoon ta furzar da iska daga bakinta sannan ta zauna ita ma tana kallonta ta ce“kin je wajen Hamida kuwa?” girgiza mata kai ta yi ta ce“to kawai sai na dinga yi muku yawo a gida mazajenku na nan” tsaki Maimoon ta yi tana kai mata duka ta ce“kin ji banza. Dallah can ki je bata da lafiya”

Ƙasa-ƙasa Nana ta yi da murya, ta ɗan matso kusa da ita sosai ta kara hannunta a gefen kunnen Maimoon ta ce“ko dai itama irin abin da ya same ki ne ya sameta?” ta ɗago tana kallon fuskar Maimoon ɗin to see her reaction. Haɗe rai Maimoon ta yi ta turata tana cewa“ke daɗina dake hauka wallahi. Bata da lafiya ne kawai” kamar jira Nana take ta fara sheƙa dariya kamar zararriya, Maimoon ta dinga kallonta cike da takaici, ji ta yi kamar ta shaƙeta saboda haushi, dan gaba ɗaya cikin ya mayar da ita masifaffiyar ƙarfi da yaji. Sai da Nana ta yi mai isarta sannan ta tashi ta gyara zamanta tana kallon yanda Maimoon ɗin ta haɗe rai. Ta tsuke bakinta kamar gaske ta ce“Tam na daina muku dariya. Allah ya sauke ku lafiya, in sha Allah mace zaki haifa a saka mata sunana”

Banza ta yi mata, ta yi murmushi sai kuma ta dafata ta ce“to bana baki haƙuri ba?” madadin ta bata amsa sai kawai taga ta fashe da kuka. Nan da nan hankalin Nana ya tashi, ta dinga taɓa ta cike da damuwa ta ce

“mene ne? Ko baki da lafiya? Ina ne ke miki ciwo? Ko na kira miki Ummi?”

Shiru Maimoon ta yi mata, sai kukanta take.. Nana ta sake matsawa kusa da ita ta riƙe hannunta cikin nata a sanyaye ta ce“to bana ce ba zan ƙara ba? Wallahi ba zan sake miki dariya ba.”

Janye hannunta ta yi daga nata, ta shiga goge hawayenta cikin shessheƙar kuka ta ce“to nima ance miki son cikin nake? Gaba ɗaya tsoro nake ji. Wallahi bana so na haihu yanzu, shikenan kowa ya yi ta kallona” ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Girgiza kai Nana ta yi tana kallonta cike da tausayawa ta ce“Allah sarki to ki yi haƙuri. Idan Yaya Aliyu ya shigo sai ki faɗa masa ke bakya son cikin nan a zubar” ko saurareta Maimoon bata yi ba ta ci gaba da kukanta a hankali.

****
Da daddare bayan sallar isha’i tana zaune kan cinyar Amma tana danna wayarta a hankali. Ita kuma Amma tana kallon dramar da ake a tv, kamar wadda aka tsikara haka ta tashi zaune ta juya tana kallonta sosai ta ce

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *