⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 29: Chapter 29

“Amma”

Kallonta Amma ta yi kafin ta ce“na’am mene ne?”

Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“Allah Maimoon tausayi take bani, ɗazu fa da naje sai kuka take.”

Da ɗan mamaki Amma ta kalleta ta ce“ita Maimoon ɗin? To meya ke damunta?”

Langwaɓar da kai ta yi ta ce“akan wannan cikin ne fa. Gaba ɗaya ta zama abar tausayi, ni kuwa nace ta cewa Yaya Aliyu yasa a zubar da cikin ko dan Allah?” ta ƙare maganar tana kallon Amma dan ta ji me zata ce. Wata uwar harara ta maka mata kafin ta ce“saboda ke ce gwana uwar iya ko? Ina ruwanki?” tura baki ta yi ta sunkuyar da kanta daman ƙaikaiyin bakinta yasa ta fadawa Ammar. Amma taja tsaki tana janyeta daga jikinta ta ce“ni tashi ki bani waje. Na sake jin irin wannan maganar a bakinki” tashi tayi ta ɗauki wayarta ta bar parlon jiki a saluɓe. Tana shiga daƙinta ta mayar da ƙofa ta rufe ta sake zumɓura baki a fili ta ce

“To daga na faɗa mata gaskiya?. Taɓ”

Ta ƙare maganar tana zame hular kanta, kyakkyawan gashinta wanda ya sha gyara ya sakko har gadon bayanta dan ba’a kitse yake ba. Ta ƙarasa wajen gado ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

****
Bakinsa ɗauke da sallama ya murɗa handle ɗin ƙofar parlon, Turus yayi ganinsu zaune dan bai yi tunanin kiran na meeting bane. Ganin yaja ya tsaya yasa Atta ta ce

“To kai kuma tun da ba soja bane ai ka ƙaraso ciki ko?”

Kallonta kawai ya yi sai kuma ya saki ƙofar ya ƙaraso ciki. Kujerar da Abba ke kai ya ƙarasa ya zauna sannan ya gaida Hajiya Babba da kuma Mama dan su ne yau bai gani ba. Bayan sun amsa Papa y yi gyaran murya kafin ya ce

“Ba wani abu ya saka muka taru anan ba sai don maganar zumuncinmu…”

Bayan sun gama tattaunawa Abdusammad ya tashi zai wuce dan Allah Allah yake ya bar parlon, Sai dai cikin rashin sa’a Hajiya Babba ta kira sunansa. A dole ya koma ya zauna yana kallonta fuskarsa babu annuri, Kallonta duk suka yi dan basu san me zata ce ba, ta gyara zamanta tana kallon Papa ta ce

“Kabeeru ai ina ga ba’a gama ba”

Da ɗan mamaki ya ce“To muna ji Hajiya”

Ta numfasa sannan ta ce“ba wani abun bane daman maganar aurensa ne. Ina ga ya kamata ace Nana ta tare a ɗakin mijinta tunda dai komai ya riga da ya saisaita”

Atta ta cafke maganar kamar daman jira take ta ce

“Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba.. wallahi kullum dashi nake kwana dashi nake tashi, to yarinya sai zama take da aure aka. Ita ba’a danganata da ɗakin aurenta ba. Gashi sa’annin auren duk kusan Allah ya bada rabo, to dan Allah itama ba ƙara ta tafi nata ɗakin ba, ko mun sake samun jikoki?.”

Murmushi suka yi, Ban da Abdusammad wanda ya sake haɗe rai kamar yaga mala’ikan mutuwa. Hajiya Babba ta ce“In sha Allah Atta nan bada jimawa ba zata tare”

Yatsine fuska ta yi ta ce“ban gane nan bada jimawa ba?. Ai ina, dole ta tare gobe, bana son wani neman magana, an riga da an gama komai na al’adar auren budurwa da ita, dan haka gobe a sadata da dakin mijinta. Dan so nake na koma Njomboli kuma ban tafiya sai naga yanda zaman nasu zai kasance aradu!”

Shiru Hajiya Babba ta yi dan bata son musu da ita. Abba ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce“kul kul Ahmadi, ina ganin girmanka dan haka kar ka ce zaka saka baki anan. Ko ka manta batun yarka ake?” shiru Abba ya yi bai yi maganar ba, ta kalli Mama wadda ke faman murmushi tun ɗazu ta ce“Ke Fatime ki shiryata gobe ki kaita ɗakin mijinta. Nima zan biyo bayanku”

Da fara’a sosai Mama ta amsa. Abdusammad ya ɗan kalleta ganin yadda ta zaƙalkale tana magana, ji yayi kamar ya maƙureta saboda haushi, sai dai sanin babu yanda ya iya da ita ya sanya shi yin kwafa yana sake maida hannunsa ga fuskarsa. Duk abin nan da yake Papa na lura dashi, ya girgiza kansa a hankali. Kasa ci gaba da zama ya yi, ya miƙe yana gyara zaman rigar jikinsa ya ce

“excuse me pls”

Daga haka ya yi waje da sauri, da harara ta bi shi sai kuma ta ce“kaga shashashan ɗa? Ina magana ya yi wani fitarsa. To idan ma yarinyar ce baya son a kai masa wallahi sai dai ya ƙarata, dan gobe sai ta tare a gidansa.” Murmushi kawai suka yi sanin halin faɗanta yasa babu wanda ya tanka, ta gama barbaɗin jarabarta ta tashi ta bar wajen, Sai a sannan Abba ya sauke numfashi ya ce

“Allah ya kyauta.”

Da Amin suka amsa sannan ya yi musu sallama ya tashi ya bar parlon dan dare ya fara. Da idanu Papa ya bi shi sannan shima ya fice daga parlon.

****
Kai tsaye gidansa ya nufa, yana jin wani irin ɗaci a ransa. Zaune ya sameta a parlon Noor na kan cinyarta tana bacci, ya haye sama ba tare da ya amsa sannu da zuwan da take masa ba. Ɗakinsa ya shige ya zame duk kayan jikinsa ya nufi toilet, ruwan sanyi ya sakarwa kansa, ya dafa bango yana sauke ajiyar zuciya jin yanda ruwan ke ratsa fatarsa. Abu ne ke neman haɗe masa goma da ashirin, idan ya tuna Nana matsayin matarsa take sai yaji duk hankalinsa ya tashi, he just can’t believe a ce wannan yar yarinyar sunan matarsa take amsawa. Babu abin da ya sake ƙona masa rai sai maganganu da Atta ta yi ɗazu, kenan har wani tunanin samun wani abu take daga gare shi? Da wannan yar yarinyar, yaja wani dogon tsaki wanda bai san sanda ya kubuce masa ba. Ya ɗauki mintuna masu tsawo a haka kafin ya rage gudun showern ya yi wanka sannan ya ɗauro alwala ya fito yana sanye da bathrobe. Zaune ya sameta kan gadonsa ta yi jigum da alama jiransa take, Ya ɗauke kansa daga gareta ya nufi mirror ɗinsa, mai ya shafa sannan ya gyara kansa. Yana gamawa ya buɗe press ya dauko wasu riga da wando na bacci masu taushi ya saka, sannan ya feshe jikinsa da turare. Duk wannan abun ya dake akan idanun Zahra yake yin su, dan koda na sakan ɗaya ta kasa ɗauke idanunta daga kallonsa, wata sabuwar soyyayarsa take ji na yawo a cikin zuciyarta, ji take inama ta tashi ta rungumeshi ta yi bacci a jikinsa kamar da. Sai dai ta san yanzu hakan ba mai yiwuwa bane, dan sharadin daya kafa mata ba zata iya dashi ba, Nana ba zata taɓa yafe mata ba. Wannan tunanin ya sanya zuciyarta tsinkewa, ta sunkuyar da kanta hawaye na biyo fuskarta. Sam bata san sanda ya zo gabanta ba, bata san sanda ya zauna a gefenta ba. Sai kawai tattausan hannunsa da taji akan nata, ta yi saurin kallon hannun nata sai kuma ta kalli gefenta na dama. Gani ta yi yana mata murmushi, ai kuwa kamar jira take ta faɗa jikinsa tana fashewa da wani raunataccen kuka. Hannunsa ɗaya ya ɗora a bayanta yana shafawa a hankali, ta dinga kuka kamar ba zata daina ba. Sai da ta fara jin abin da ke damunta ya fara raguwa sannan ta ɗago kanta daga jikinsa har sannan tana shessheƙar kuka. Hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen fuskarsa a sake kamar ba shi ba ya ce“Ya isa haka to” jinjina masa kai ta yi tana murmushi mai haɗe da kuka ta ce“Doctor tam.” Ya ɗan yi shiru yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame kamar ba ita ba, har wasu kasusuwa ne suka mata ƙawanya a wuya. Duk wanda ya ganta sanda suka zo ƙasar nan ya kalleta yanzu ba lallai bane ya ganeta. Ya riƙe fuskarsa da duk hannayensa biyu yana murmushi ya ce

“naga kin ƙara kyau?”

Murmushi ta yi a sanyaye ta ce“doctor ka yafe mini yanzu?” shiru ya yi kamar ba zai bata amsa sai kuma ya ce“shikenan ya shige. But kada ki sake irin haka kin ji, na san ba halinki bane, ƙoƙarin ɓata ki ake but karki biye musu Zahra. Na yarda dake fiye da yanda ki ke tunani, bana son ace daga gareki aka samu matsala..dan hakan zai haifar da maganganu acikin gidan nan, ni kuma duk wanda ya zageki ko ya aibata ki ba zan ji daɗi ba. Dan haka dan Allah Zahra kar ki sake.”

Ya ƙare maganar in a very polite tone. Kasa cewa komai ta yi kawai ta sake rungumeshi tana jin wani sabon so da ƙaunar mijin nata na shigarta. Ya yi shiru yana sauke numfashi, ba komai ya sanya ya yi hakan ba sai dan zuwan da Nana za ta yi. Idan har ya nuna mata baya shiri da Zahra ba zasu taɓa zaman lafiya ba kuma hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba, dan ya san halin Nana kamar yunwar cikinsa. Janye jikinta ta yi daga nasa tana lumshe idanu, ya sake jawota jikinsa yana ƙoƙarin kunce zaren sleeping dress ɗin dake jikinta. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi ya manna mata kiss a goshi, ta sake maƙalewa a jikinsa tana rufe idanunta, tana jin sa har ya sauke rigar ƙasa, Jin hannunsa akan fatar jikinta ya sanyata sauke wata ajiyar zuciya tana ɗan ƙanƙameshi. Cikin yan sakkani kuma wasan nasu ya fara neman sauyawa..

****
Amma ta dinga kallonsa ganin kamar bai san abin da take cewa ba, Ta ajiye cup ɗin akan table sannan ta zauna gefensa a hankali ta dafashi, Ya juyo a ɗan firgice yana kallonta, a sanyaye ta ce

“tunanin me kake ne? Ina ta maka magana baka saurarena”

Girgiza kansa ya yi yana furzar da iska daga bakinsa ya ce“Abun ne, hankalina ne sam yaƙi kwanciya.” da mamaki ta ce“dame fa?”

“Akan auren Nana da Abdusammad. Gobe zata tare inji Atta, kuma kin san babu wanda ya isa yaja da maganarta, tsoro nake kada wata fitinar ta ɓullo tsakaninsu dalilin zuwan Nana.”

Shiru Amma ta yi, lokaci ɗaya taji jikinta ya yi wani irin sanyi. Can dai ta numfasa ta ce“gobe kuma? Me yasa ba’a faɗa mana da wuri ba amma?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“ai babu wani abu da za’a yi shiyasa, kawai Fatima ce zata rakata.”

“But at least ya kamata a sanar dani ko da abin da zan shirya mata.”

Abba ya kalleta wanda ya sanyata yin shiru, Ya ɗauke kansa yana kallon tv ya ce“kira min ita.” Toh kawai ta ce sannan ta mike jiki a saluɓe ta nufi ɗakin Nanar.

Kwance ta sameta har ta yi shirin bacci. Ta taso ta sannan ta dawo parlon ta zauna, after 2mins Nana ta fito tana jan ƙafa a hankali, hannunta ɗaya akan idanunta tana murzasu saboda baccin data fara yi. A gefen Abba ta zauna ta jingina da jikinsa, Ya gyara mata zama dan so yake ta fahimceshi ya ce

“Tashi zaune ki ji Nana.”

Toh kawai ta ce sannan ta gyara zamanta, dan tun bayan abin da ya faru bata sake masa musu ba. Ya dinga kallonta dan har ga Allah tausayinta yake, Ita ma kallon nasa take. Ganin damuwa akan fuskarsa ya sanyata wartsakewa gaba ɗaya, Ta yi shiru tana jiran abin da zai ce. Sauke nannauyan numfashi ya yi kafin ya fara magana cikin nutsuwa.

“Nana ina son ki buɗe kunnawanki ki ji abin da zan faɗa miki. Ba’a fasa aurenki ba saboda bakya nan, an ɗaura miki aure a ranar kamar yanda aka ɗaurawa yan uwanki!”

Sai da taji gabanta ya fadi, Ta zaro idanu tana kallonsa, Lokaci ɗaya hawaye ya fara zuba daga idanunta, bakinta na rawa ta ce“Abb…Abba nima an yi min aure? Wa aka aura min?”

Kallonta ya yi ganin yanda take kuka a hankali yasa ya ce“banason wannan kukan kin ji. Duk abin da na faɗa miki kuma ki yarda” gyaɗa masa kai kawai ta yi, dan ita daman bata ji zata musa masa ba ko me yace kuwa. Ta shirya karɓar duk abin da Allah ya bata. Ganin ta kwantar da hankalinta yasa ya ce

“An ɗaura aurenki da uncle ɗinki Abdusammad!”

A tsaye suka ganta ta dinga kallonsa bakinta na rawa ta shiga girgiza kanta, can kuma ta yi luuu ta faɗi ƙasa a sume..

Murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta yi bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta hangeta tsakiyar gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take a hankali. Amma ta sauke numfashi sai kuma ta saki ƙofar ta ƙarasa ciki hannunta riƙe da mug ɗin, A kan drawer ta ajiye mug ɗin sannan ta zauna tana kallonta a sanyaye, kasa ce mata komai ta yi, ta yi shiru tana sauraren sautin kukanta dake tashi a sanyaye. Sun ɗauki mintuna a haka kafin daga bisani Amma ta sauke ajiyar zuciya ta dafata cikin tattausar murya ta ce

“Nana!”

A hankali ta ɗago kanta. Amma ta ƙura mata idanu ganin yanda hawaye da majina suka cika mata fuska, Amma ta girgiza kanta tana kai hannunta fuskarta ta ce“ya isa haka kin ji. Ki daina kuka”

“Amma uncle fa? Uncle fa Amma. Ya ma za’a yi ace uncle ne mijina? Ya za’a yi na aureshi?”

Nana ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, Ta kifa kanta kan cinyar Amma tana jan numfashi. Shafa bayanta Amma ta dinga yi a hankali cike da tausayinta ta ce“to mene ne Nana? Ba uncle ɗin ki bane. Kuma ai kin san ba zai taɓa cutar dake ba ko?”

Sake ɗago kanta ta yi tana kuka ta ce“Amma ya za’a yi na zauna dashi a matsayin miji? Uncle ne fa. Ya za’a yi na aureshi? Ni wallahi ba zan iya baaa!”

Ta sake faɗawa jikinta tana kuka har da birgima. Shiru Amma ta yi bata sake cewa komai ba dan ta san ba saurarenta zata yi ba, Ta ɗauke kanta tana kallon ƙofa, ita kanta ba son auren nan take ba. Saboda Abdusammad ya yi wa Nana girma. Ta sauke zazzafan numfashi tana maida idanunta kanta jin har sannan bata daina kukan ba yasa ta ce

“Ni ɗagani idan ba zaki yi shiru ba. Mene ne dan kin aureshi? Ina ruwanki da kasancewarsa uncle ɗinki? Ke ba matsayin miji zaki ɗaukeshi ba.”

Tashi zaune ta yi cikin gunjin kuka ta ce“to me yasa za’a ce na aureshi? Ita Maimoon ta auri Yaya Aliyu, ita Amrah ta auri Yaya Sultan, ita kuma Hamida ta auri Yaya Hamid. To sai ni kuma a aura min uncle? Bayan kuma tsoho ne!”

Ta faɗa tsakiyar gado tana kuka kamar ranta zai fita. Murmushi Amma ta yi dan cikin kukan nata har da na banza, ta tashi dan ba zata iya da halin Nanar ba ta ce

“Abdusammad ɗin ne tsoho?”

“wallahi tsoho ne Amma. Kalli fa babu mai aure sai shi, kuma har ƴa ce dashi. To ni ya za’a yi na zauna dashi a haka?”

Amma ta ɗan waro idanunta tana kallonta ta ce“au dan yana da aure shi ne ya tsufa? To shi Aliyun ba kusan sa’ansa bane. Daga shi naga sai shi”

Ɗago kanta ta yi tana murza idanunta cikin kuka ta ce“to ai dai ya girme shi, duk fa ya girmi kowa.”

Amma ta ɗan ja tsaki ta ce“to tun da ba zaki haƙura ba bari zan je na faɗawa Abban naki shi sai ya san yanda zai yi dake.”

Daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin. Nana ta sakko ƙasan gadon ta zube a wajen ta sake fashe da wani sabon kukan mai cin rai, a fili kuma ta dinga cewa

“na shiga ukuna, wayyo Allahna. Wallahi bana sonsa.”

Ta dinga maimata maganar can kuma ta baje a wajen tana birgima.

Amma na fita ɗakin Abba ta shiga, zaune ta same shi gefen gado ya gama shirin kwanciya. Ta ƙaraso ciki ta tsaya jikin mirror ta yi shiru, kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa yana gyara zama pillow ɗin gabansa ya ce

“Madam lafiya dai?”

Sauke numfashi ta yi tana kallonsa ta ce“Ni ko baka ganin auren nan akwai matsala?. Nana yarinya ce ƙarama, shekarunta 17 fa kawai. Abdusammad kuma ya girme mata, girma bana wasa ba. Sai nake ganin kamar zamansu ba zai yi dai-dai ba.”

Abba ya dinga kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, Can kuma ya yi mata alama da ta zo da hannunsa. A sanyaye ta ƙaraso wajen ta zauna gefensa, Abba ya kama hannunta na dama yana murzawa a hankali ya ce

“Rabi’a kenan. Ya kamata a ce kin kwantar da hankalinki, na san kin san wane Abdusammad, kin san abin da zai iya da kuma wanda ba zai iya ba. Bana da damuwa akansa na san zai kula da Nana, kulawa irin wadda ba kowane namiji ne zai yiwa mace ba. Ba zai taɓa bari ta yi kuka ba, saboda ba tun yau ba na san yana sonta, kawai ba zai iya faɗa bane saboda yana ganin kamar hakan bai kamata ba. Yanzu kuma da ya samu dama kina ganin zai bari ta yi kuka a gidansa? Kina ganin zai gaza wajen kulawa da ita?.”

Numfasawa Amma ta yi ta girgiza kanta kana ta ce“nima na san ba zai bari ta yi kuka ba, amma fa ka sani ba shi kaɗai bane. Yana da mata har da ƴa, sannan matarsa babba ce wadda ta mallaki hankalin kanta, kuma tana da wayo. Sannan ita ce ta yi yunƙurin cutar da Nana, yanzu kana ganin idan ta shiga gidan a matsayin kishiyarta zata barta ta zauna lafiya? Nana yarinya ce. Duk da rashin jinta da kuma neman faɗanta bata da wayo, cikin ruwan sanyi za’a iya cutarta ba tare da ta gane ba. Tana da saurin yarda da mutum. Shi ne abin da nake tsoro wallahi”

Abba ya yi shiru yana nazarin maganarta, tabbas tana da gaskiya, Nana bata da wayo ko kaɗan. Ya sauke numfashi sannan ya ce“Duk wannan ba zai zama damuwa ba in sha Allah. Babu abin da zai faru, mu yi musu fatan zaman lafiya” jiki a sanyaye Amma ta ce“tam shikenan, Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka cikin auren.” murmushin jin daɗi ya yi kafin ya ce“Amin ya rabbi.”

Ta mike tsaye tana fadin“sai kuka take yi na yi nayi da ita taƙi shiru.”

Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“Allah sarki, tausayi take bani, zata shiga cikin wata rayuwa wadda bata san da ita ba. Ki barta ta yi kukan, ba koda yaushe ake hana mutum kuka ba, tana buƙatar ta yi, so just leave her.”

Jinjina masa kai Amma ta yi ta ce“daman na rabu da ita in sha Allah. Gobe da safe zan kira Ramlah ta zo” okay ya ce mata sannan ya zare glasses ɗin idanunsa ya kwanta dan dare ya yi sosai, Amma ta ɗan kalleshi sai kuma ta nufi ƙofa ta fita dan bata gama abin da take ba.

Daren ranar kasa bacci Nana ta yi, ta dinga kuka har sai da muryarta ta dashe, ganin dare ya yi sosai ya sanya ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala sannan ta fito ta zura hijabi ta fara gabatar da sallolin nafila, bayan ta gama ta zauna a wajen ta dinga addu’o’i neman yafiyar ubangiji sannan kuma da samun zaman lafiya. Daga bisani kuma ta ci gaba da kukanta har asubahi, Gari ya fara haske wajejen 6 na safe aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, bata iya ɗaga kanta ba, hasalima bata san an shigo ɗin ba saboda tunanin da ta yi zurfi a cikinsa. Abba ya ƙaraso gaban gado ya zauna yana kallonta ganin yanda ta kifa kanta kan cinyoyinta. Ya dade yana kallonta kafin ya yi gyaran murya ya taɓata, a firgice ta buɗe idanunta, ganin shi ne ya sanya ta sunkuyar da kanta jiki a sanyaye ta ce

“Abba ina kwana”

Duk da muryarta da bata fita hakan bai hana shi jin abin da ta ce ba. Sai dai bai amsa ta ba, Madadin hakan ma sai ya sakar mata murmushi, ya yi mata alamar ta zo ta hannunsa. A danya ta mike ta dawo kusa da shi ta zauna Abba ya ware mata hannayensa duk biyun, kamar jira take kuwa ta shige jikinsa tana sakin wani marayan kuka, Kuka take mai tsuma zuciya, kuka ne wanda ke nuna irin rauninta gaban mahaifin nata. Shi kansa Abba sai da jikinsa ya yi sanyi, Ya dinga dukan bayanta a hankali ba tare da ya yi yunkurin hanata kukan ba, Madadin hakan ma sai ya dinga cewa

“Cry! Cry Nana, cry as much as you can. Cry Nana.”

Kamar kuwa turatan yake haka ta dinga ƙara sautin kukan nata tana ƙanƙameshi. Shima ya sanye duk hannunsa biyun ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya, Allah ya sani yana mugun sonta, yana son gudaliyar ƴar tasa fiye da tunanin mai tunani. Koda wasa baya son abin da zai ɓata ranta, ballantana har yaji kukanta, shiyasa a tsawon rayuwarsu tare zai iya ƙirga sanda ranta ya ɓaci a dalilinsa. Sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka har sai da ta fara rage sautin kukan nata don kanta. Ya ɗagota daga jikin nasa ya fara goge mata hawayen nata da hannunsa, ita kuwa sai ƙara narkewa take dan ta samu abin da ta ke so. Kuma sosai taji zuciyarta ta mata sanyi sakamakon kukan da ta yi, Sai da yaga ta yi shiru gaba ɗaya sai shessheƙar kuka kawai take sannan ya ce

“Yanzu kin haƙura?”

Gyaɗa masa kai ta yi a hankali, Ya yi murmushi sannan ya ce“Yauwa Allah ya yi miki albarka, Ya baki zaman lafiya a gidan mijinki. Ya…”

“Abba da gaske uncle zan aura? Da gaske ni matarsa ce?”

Ta katse shi da sauri jin ya yi maganar gidan mijin. Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce

“Eh Nana, da gaske ne, Abdusammad shi ne mijinki. Kuma ina fatan ki yi masa biyayya, ki rufe sirrin mijinki, ki zauna dashi lafiya. Ki kula da dukiyarsa, ki zama mata tagari a cikin gidansa. Koda wasa kada ki bari mijinki ya yi kuka dake, kada ki bari ya kawo ƙararki. Ki zama yarinyar kirki kin ji Khadijatou.”

Samun kanta ta yi da sake fashewa da wani sabon kukan, ta sake rungumeshi tana kukan ta ce“Abba uncle fa? Uncle ɗina ne, daman ana auran uncle? Ustaz ɗin mu ya ce mana ba’a aure da uncle. Me yasa ni zai aureni?”

Murmushi irin na manya uncle ya yi sannan ya ɗago kanta ya gyara mata zama yanda zata fahimce shi sosai ya ce“Haka ne, ba’a aure da uncle. Amma ba irin naki uncle ɗin ba”

Da ɗan mamaki ta kalleshi, ya jinjina mata kai ya ce“Abdusammad ɗan Yayana ne, hakan na nufin shi ɗin cousin ɗinki ne. Kuna ce masa uncle ne dalilin kallon mahaifin da ku ke masa, ba wai dan shi ɗin ƙanina bane. Abdusammad ɗana ne kamar yanda ki ke ƴata, dan haka aure a tsakaninku halattaccan abu ne, aure ne na raya sunnar ma’aiki, dan haka idan kina kallon babu aure tsakaninku ina son ki daina daga yau kin ji.”

Sunkuyar da kai ta yi tana gyaɗa masa kai, Daman ta san da wannan bayanin tun tuni. Amma ita sam bata masa kallon wanda zata iya aura, a koda yaushe kallon mahaifi take masa. Ɗaukansa take kamar Abbanta, ashe watarana zai iya zuwa ya aureta?.

Miƙewa Abba ya yi yana ɗaukan cazbaharsa ya ce“Idan Allah ya kaimu an jima za’a sadaki da ɗakin mijinki, don haka ina mai miki nasiha da kiji tsoron Allah, ki kasance haske mai haska zuciyar mijinki. Ki zame masa ƙawa kuma abokiyar arziki, dan Allah Nana kada ki bamu kunya.”

Yanda ya yi maganar a tausashe ya sanyata kallonsa, Hawaye na biyo kuncinta ta ce“Tam Abba in sha Allah ba zan baku kunya ba, ba zan bari ku sake kuka dani ba.”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *