⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 30: Chapter 30

Ta ƙare maganar kuka na kwace mata, Murmushi kawai Abba ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Nana ta bi bayansa da kallo sai kuma ta sake fashewa da kuka, ta faɗa kan gadonta ta shiga rera shi kamar waƙa.

****
Zahra ta dinga kallonsa ganin yanda yake cin abincin hankali kwance, idanun da yaji na yawo a kansa ya sanya ya ɗago kansa, cikin rashin sa’a idanunsu suka sarƙafe da juna. Ta yi saurin janye nata tana ɗaukan mug ɗin tea ɗinta, Ɗan murmushi ya yi sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannunsa still looking at her ya ce

“why are you staring at me?”

Yi ta yi kamar bata san me yake nufi ba, ta kalleshi ta ce“magana ka yi doctor?”

Ɗauke kansa ya yi yana murmushi ganin tana shirin raina masa hankali, Zahra ta saci kallonsa ta gefen ido ganin yanda yake murmushi ya sanyata yin murmushin itama. Bai sake bi ta kanta ba har ya kammala breakfast ɗinsa, Ya tashi yana goge bakinsa da tissue ya ce

“To zan fita sai na dawo.”

Tashi itama ta yi tana murmushi ta ce“Tom a dawo lafiya Allah ya tsare hanya.”

Da Amin ya amsa sannan ya juya zai bar wajen, kamar wanda ya tuna wani abun kuma sai ya tsaya cak. Ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“doctor lafiya dai?” juyowa ya yi yana kallonta ya ce“wallahi na kusa mantawa ne. Idan Allah ya kaimu an jima za’a kawo Nana, so get ready please.”

Ji tayi kamar an zare mata lakar jikinta, taji ƙafafunta na neman gagarar ɗaukan gangar jikinta. Numfashinta ya tsaya na wasu sakwanni, Ganin haka yasa Abdusammad cewa

“Lafiya dai?”

Girgiza masa kai ta yi a sanyaye. Ya dinga kallonta ganin yanda ta sunkuyar da kanta, Taku ɗaya ya yi ya koma gabanta, Ya sanya hannunsa ya ɗago kanta. Hawaye ya gani na zuba daga cikin idanunta, Ya ɗan ware idanunsa da mamaki ya ce“Zahra mene haka?”

Saurin goge hawayen ta yi da hannunta tana shessheƙar kuka ta ce“babu komai. Ban sani ba ne”

Ta ƙare maganar tana kirkiro murmushi. Wani irin kallo ya dinga yi mata sai kuma ya ce“Saboda nace miki Nana zata zo ki ke kuka?”

Saurin girgiza masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce“A’a doctor, babu komai fa.”

Taɓe baki ya yi dan ya san ƙarya take ya ce“na miki kama da wanda zaki ma karya Zahra?.”

Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta sake sunkuyar da kanta kuka na sake tawo mata, ya kalli agogon Rolex ɗin dake maƙale a hannun hagunsa sai kuma ya mai da idanunsa kanta ya ce“But you promised me cewa komai ya shige? Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh doctor babu komai Allah ya kawo su.”

“Amin”

Ya amsa a takaice. Sai kuma ya sake cewa“make sure kin shirya kinji. Ki yi kyau abin ki”

Ya ƙare maganar yana jan kumatunta. Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce“In sha Allah I’ll” ya yi murmushi sannan ya juya ya bar wajen. Sai da taga ya fice daga parlon sannan ta sulale a ƙasa a hankali, kamar jira take ta fashe da wani raunataccen kuka..

Yana ƙoƙarin shiga mota yaga kiran Papa, Ya tsaya hannunsa ɗaya riƙe da handle ɗin motar ɗayan kuma riƙe da wayarsa ya ɗaga kiran, gaishe shi ya yi amsa sannan ya ce

“Abdusammad ka zo ina nemanka”

Shiru ya yi sai kuma ya ce

“Papa lafiya dai?”

“Lafiya fa. Idan ka zo kaji”

Papa ya bashi amsa kai tsaye, To kawai ya ce sannan ya kashe wayar, Abdusammad ya sauke wayarsa yana mamakin kiran, can kuma ya sauke numfashi ya shige motar.

****
Abdusammad ya girgiza kansa da rashin fahimta ya ce“Papa ban gane abin da ka ke nufi ba.” Gyara zama Papa ya yi kan sofar yana kallonsa ya ce“abin da nake nufi shi ne idan ka san ba zaka iya zama da yarinyar nan ba gara tun yanzu ka saketa!”

Da wani irin mamaki yake kallon Papa can kuma ya ce“But why?” cike da nutsuwa Papa ya ce“saboda baka sonta. Bayan haka ban ga alamun zaka kula da ita ba.”

“Wani abun nayi mata Papa.?”

Girgiza kai Papa ya yi kafin ya ce“ko kaɗan zuwa yanzu babu abin da ka yi mata. Amma alamunka sun nuna nan gaba zaka iya yi mata, Jiya duk ina kallonka kuma naga yanda ka yi, baka shirya zama da yarinyar nan ba. Ko kaɗan baka ji daɗin cewar da aka yi ta tare ba!”. Papa ya ƙare maganar yana jingina da kujerar da yake kai. Numfasawa Abdusammad ya yi dan sai a sannan ya gane inda ya dosa, har ga Allah shi kansa ya sanya bai shirya da karɓar tata ba, amma ya zai yi?. Jin bai ce komai ba ya sanya Papa gyaran murya kafin ya ci gaba da cewa

“Ina son ka dinga tuna abu guda ɗaya, ba yarinyar nan ta ce ka aureta ba. Ba mahaifinta bane, ba tilastaka aka yi ba, kaine ka yi hakan saboda raɗin kan ka. Idan har ka ce zaka cutar da ita a zaman da zaku yi tare to ka sani Allah ba zai bar ka ba, Dan haka da azo ana ɓacin rai daga baya gara kawai ka saketa tun yanzu.”

Papa ya yi shiru yana kallon sa. Ajiyar zuciya Abdusammad ya sauke kafin ya fara magana

“Ni fa ba wai ina jin haushin yarinyar nan bane Papa, na san bata da laifi. Kuma koma tana da shi ai abin da ya wuce ya riga da ya wuce, dan haka babu amfani tado shi. Kawai na kasa yarda ne a ce wai Nana matata ce, na kasa yarda zata shigo gidana ta yi rayuwa dani irin rayuwar miji da mata, bayan yanda na ɗauketa yar ƙaramar ƴata a wancan lokacin.”

Murmushi irin na manya Papa ya yi kafin ya ce“Na gane abin da ka ke nufi, amma ba hujja ba ce. Babu yanda za’a yi ka ce dan kana yi mata kallon ƴa ba zata zama matarka ba watarana, baya da haka ma kasan akwai aure a tsakanin ku. Dan haka ina ganin ka bar wannan tunanin zai fi, sannan kuma kada ka kuskura ka ce zaka yi treating ɗinta a kar yarinya ko ƙarama da ka ke ganinta. Dole ne ka sauke duk wani haƙƙinta da yake kan ka, dole ka bata kulawa irin wadda miji ke bawa matarsa, dole ka saurari matsalarta sannan ka yi mata maganinta.”

Numfasawa ya yi jiki a sanyaye ya ce“Tom Papa in sha Allah.”

“Allah ya yarda ya sanya albarka cikin auren, ya baku zaman lafiya.”

Da Amin ya amsa sannan ya tashi ya masa sallama ya fito.

****
Ƙarfe 9:00 na safe Aunty Ramlah ta sauka a gidan, ta ajiye jakarta tana kallon Amma da ke haɗa wasu turaren wuta ta ce“To amma dan Allah sai a ce yau zata tare? Ina ma laifin a ce gobe fisabilillahi.” ɗan murmushi Amma ta yi ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce“to basu ce haka ba Ramlah. Ni yanzu ki tashi ki je idan da abin da zaku yi ku yi, saboda na san tunda aka haɗa sabgar nan da Atta to wallahi ba zata jira ba, tana iya zuwa ta ce dole sai ta tafi da ita.” Tashi Aunty Ramlah ta yi tana murmushi ta ce“Atta ko jaraba” daga haka ta yi dakin Nana da sauri. Bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, Sai dai turus ta yi a bakin ƙofar saboda Nanar data hango tana kuka a ƙasa ta yi baje-baje sai birgima take. Aunty Ramlah ta saki ƙofar da sauri ta ƙarasa ciki tana faɗin

“Subhanallahi. Nana mene ne haka?”

Ko kallonta bata yi ba sai ma sake ƙara sautin kukan nata da ta yi, Aunty Ramlah ta ɗagota tana kallonta hankali tashe ta ce“baki ji ina miki magana ne? Sai ran ki ya ɓaci tukun”

Ganin yanda ta yi maganar babu wasa a kan fuskarta ya sanya Nana tsagaitawa da kukan. Ta fara sauke numfashi tana shessheƙa a hankali, Zama Aunty Ramlah ta yi a ƙasan tana kallon ta ta ce“Yanzu faɗa min kukan me ki ke?”

“Anty wai uncle zan aura. Uncle fa, Ya za’a yi a ce shi ne mijina…”

Ta ƙare maganar tana sake rushewa da kuka. Girgiza kai Aunty Ramlah ta yi ta ce“a’a ban gane ba Nana, mene ne da uncle ɗin?” ɗauke Hannunta ta yi daga fuskarta cikin son yi mata bayani ko Allah zai sa ita ta fahimceta ta ce

“Anty uncle Abdusammad fa. Kina ganinsa ai kin san Babba ne ko? Kuma fa har mata ce dashi, ni kuma ai yarinya ce, duk su sauran sun yi aurensu da Yara sai ni a aura min tsoho? To dan Allah ba babba bane shi. Ni kuma kalleni fa, Sai a dinga cewa ni ce matarsa?..”

Ta sake fashewa da kuka tana faɗawa jikin Aunty Ramlah. Murmushi Ramlah ta yi sannan ta ce“ke kuma kin fi son ki auri yaro ko? Kin fi son wanda zai nuna miki soyyaya? Wanda ba zai dinga miki faɗa ba ko?.”

Jin ta faɗi abin da take so yasa ta ɗago kanta cikin shessheƙar kukan ta ce

“Eh mana Anty. Yanzu dan Allah kamar Yaya Sultan, ai kin ga bai min girma ba sosai, to amma ji fa uncle, ƙato ne shi fa. Kawai sai a dinga yimin dariya, Kuma har ƴa ce dashi, wallahi tsoho ne, ni saurayi nake so na aura”

Ta sake komawa kan cinyar Ramlah tana kukanta. Girgiza kai Aunty Ramlah ta yi dariya na son kwace mata ta ce

“To ai duk wannan abun dana lissafo shi uncle ɗin naki zai dinga miki. Ba zai bari ki dinga kuka ba, zai kula dake sosai kin ji”

Ɗago kanta ta yi ta ce“To bayan ma har mata ce dashi, kuma ni wallahi bana son kishiya.”

Haɗe rai Aunty Ramlah ta yi ta ce“to ke ina ruwanki da matarsa? Babu abin da ya shafeki da rayuwarta.”

Tura baki ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce“ni Allah bana son zama da kishiya, wallahi sai dai ya saketa!”

Kallon kin zama mahaukaciya Ramlah ta yi mata kafin ta ce“to don’t ever, kar ki sake koda wasa ki fadi wannan maganar a gaban wani kin ji abin da nace.?”

Gyaɗa mata kai ta yi, Aunty Ramlah ta sauke numfashi ta ce“ki daina wannan shirmen ki saurari abin da zan faɗa miki kin ji.”

Shiru ta yi kamar gaske, Aunty Ramlah ta kama hannunta na dama cike da kulawa ta ce

“Nana ki daina wannan kukan haka. Kin san dai tun da an riga da an ɗaura auren na babu wanda ya isa ya sa a kwance shi, saboda haka ki kwantar da hankalinki. Babu wata matsala dan ance Abdusammad ne mijin ki, me ake buƙata ne a aure ba zaman lafiya ba? Da soyyayar juna. Na tabbata Abdusammad ba zai ce baya son ki ba, saboda ke ɗin mace ce irin wadda kowane banki ke fatan samu, kina da kyau kina da tarbiyya. Sannan bugu da ƙari kina da ɗabi’u irin wanda maza ke so, Idan har kin kwantar da hankalin ki, to babu yanda za’a yi ya zama na wata. Dole ke zaki kwace shi, musamman daya kasance ke ɗin ƴar uwarsa ce, saɓanin waccan da kawai a wani wajen ya ganta ya aureta. Dole kina da alfarma a wajensa, Sannan idan har bai ji zai iya zama dake ba ba zai taɓa yarda ya aureki ba, kina dai gani babu irin macen da ba’a nuna masa ba a cikin gidan nan a lokacin da zai aure amma sam ya ce babu wadda ta yi masa, babu yanda ba’a yi dashi ba. Amma ke babu wanda ya yi masa dole, shi da kansa ya ce a ɗaura muku aure, ya biya sadaki mai yawa kina ganin ba zaki iya kwace shi daga hannunta ba.?”

Aunty Ramlah ta yi shiru tana kallonta, ganin yanda ta ƙura mata idanu wanda ke nuna tana fahimtar abin da take cewa yasa ta ci gaba da faɗin“Idan har zaki bi abin da zan faɗa miki to tabbas uncle ɗin zai zama naki. Zaki mulki gidan fiye da yanda ki ke tunani, duk da kasancewarsa tsayayyen namiji zaki iya cin galaba a kansa, dan haka ki buɗe kunnunwanki ki ji abin da zan ce miki.”

Ganin bata ce komai ba ya sa Anty Ramlah ta haɗe ranta ta ce“ba magana nake miki ba.?”

A sanyaye ta ce“Ina ji”

Anty Ramlah ta gyara zamanta sannan ta ce“Yauwa kina ji…”

Around 11am Amma ta shigo ɗakin, zaune ta sameta, Nana na kan cinyarta ta yi shiru. Amma ta ce“Ramlah babu abin da zaku yi lokaci fa na tafiya?”

Girgiza kai Anty Ramlah ta yi ta ce“a’a zamu yi, Nana tashi muje.”

Tura baki ta yi sannan ta tashi zaune tana haɗe-haɗen rai. Anty Ramlah ta sauka daga kan gadon tana kallonta ta ce“taso nace.” kamar zata yi kuka ta ce“to bari nayi wanka.”

Girgiza kai Anty Ramlah ta yi tana jan hannunta ta ce“a’a idan mun je can kya yi” da ɗan mamaki ta ce“Anty to ina zamu je?”

Harararta Anty Ramlah ta yi ta ce“kin tashi ko isata zaki yi da magana?”

Zumɓura baki ta yi sannan ta tashi a hankali, Hijabin dake ajiye kan drawer ɗinta ta ɗauka ko gama zurawa bata yi ba Anty Ramlah taja hannunta suka yi waje. A parlon suka tsaya Amma ta ce“dan Allah Ramlah kar ku dade a zo a isheni.”

Murmushi Ta yi ta ce“To idan ba’a gama ba ai ba zamu dawo ba Yaya.”

Shiru Amma ta yi, can kuma ta sauke numfashi ta ce“to Allah ya tsare hanya.” da Amin ta amsa sannan suka yi waje, suna ƙoƙarin shiga mota, suka ƙaraso compound ɗin, Da idanu Nana ta dinga bin su ganin sun zo inda take yasa ta ɗaga mata hannu. Ita ma Amrahn daga mata hannu tayi tana murmushin, ganin ya kalli inda take yasa ta ɗan sunkuya a sanyaye ta ce

“Ina kwana Yaya.”

Fuska a sake ya amsa mata sannan ya gaisar da aunty Ramlah ta amsa ta ce“Sultan ya gida ya iyalin?” murmushi ya yi ya ce“Alhamdulilah Anty ya kids?”

“Suna nan kalau” ta ce a sake. Jinjina kansa ya yi ya ce“Tam a gaishe min dasu pls” zasu ji ta ce sannan suka yi gaba ita kuma ta buɗe motar ta shiga, a sanyaye Nana ta shiga motar lokaci ɗaya taji ranta ya sake ɓaci. Aunty Ramlah bata ko kalleta ba ta yiwa motar key suka bar Estate.

****
Wajejen ƙarfe 3:00 na rana Maimoon ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama. Bata samu kowa a ciki ba, kamar ta juya ta fita sai kuma taja ta tsaya tana jiran taga ta inda zata fito, bayan mintinan da basu shige biyar ba Zahra ta fito daga kitchen Saboda kiran wayarta da taji, sai dai ganin Maimoon ya sanyata tsayawa ta ce“Laaa Maimoon ke ce a gidan yau?” babu yabo babu fallasa ta ce“Eh ina yini?”

“Lafiya kalau ya gida?”

Zahra ta amsa mata da fara’arta. Taɓe baki Maimoon ta yi dan ba abin da ya kawota ba kenan ta ce“Daman Atta ke kiranki.” shiru Zahra ta yi da mamaki ta ce“Atta kuma? Meya faru” girgiza kai Maimoon ta yi cike da rainin hankali ta ce“A’a ni ban sani ba gaskiya sai dai idan kin je kya ji. amma kuma kamar akan maganar tariyar amaryar da za’a yi an jima ne.” Maimoon ta ƙare maganar tana sakin wani kyakkyawan murmushi na zallar rainin hankali, Kallonta kawai Zahra ke yi can kuma ta danne zuciyarta ta ce“Tom gani nan in sha Allah.”

“Yauwa da yafi dai.”

Ta ce tana juyawa, sai da taga ta fice daga ɗakin sannan ta zauna kan sofa hawayen da take ta maƙalewa suka gangaro kan fuskarta. Wani irin zafi take ji a zuciyarta, kenan tun kafin ta shigo sun fara nuna mata irin abin da zasu yi, kenan zata zama shara a cikin gidan, Ta ɗora kanta bisa cinyarta tana fashewa da kuka. Ta dade a wajen tana kukan ganin ba zai kai mata ba ya sanya ta ɗago kanta ta ɗauki wayarta da ke kan table ta danna numbern Aunty Khadijah. Sai da kusa katsewa sannan ta ɗaga. Zahra ta kasa cewa komai sai kuka da take a hankali, Aunty Khadijah da ke zaune gaban motar wani Alhaji ta ce

“Lafiya dai Zahra?”

Cikin kuka ta ce“Aunty basa sona. Mutuwa zan yi wallahi, ƙirjina zafi yake min” cike da rashin fahimta ta ce“ban gane ba Zahra, me ya faru? Su wane basa sonki”

“Yan gidan nan mana, basa son zama dani. Wai an jima zata tare, ya zan yi Anty?”

Girgiza kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“ba dai bakya jin shawara ba Zahra? Yanzu kin ga Siyama na samun matsala dasu tun da taje? To ya ma za’a yi ta samu matsala bayan mun yi maganin matsalar, amma ke sam kin ƙi yarda, kin biyewa Umma da bata san me duniya ke ciki ba. Dan haka kuka yanzu ki ka fara shi wallahi, nan gaba ma sai sun koro ki daga cikin gidan baki ɗaya.”

Zahra ta girgiza kanta tana kuka ta ce“A’a wallahi, in sha Allah ba zan bar gidan nan ba. Ba zan rabu da mijina ba, ki faɗa min me zan yi Anty? Wallahi zan yi koma mene ne muddin zan zauna lafiya a cikin gidan nan, dan Allah ki faɗa min me zan yi.?”

Jinjina kai Aunty Khadijah ta yi sannan ta ce“alright we should talk later.” daga haka ta katse wayar saboda mutumin da yake gabanta. Zahra ta sauke numfashi ta sanya hannunta ta goge idanunta sannan ta tashi ta haye sama, Mayafi kawai ta dauko sannan ta dawo ƙasan, ta fito daga parlon jiki a sanyaye ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba.

****
Anty Ramlah ce tsaye gabanta. Ta kai mata duka tana cewa“ke Nana tashi mu tafi!” a ɗan firgice ta buɗe idanunta sai kuma ta tura baki, Ta sanya hannunta wanda yaji red henna gaba da baya. Ya yi wani irin kyau kamar a fatar hannun aka halicce shi. Ta murza idanunta a shagwaɓe ta ce“To Anty yanzu zamu tafi?” Gyaɗa mata kai ta yi ta ce“to ba an gama komai ba?” Sai a sannan ta kai hannunta kanta, jin yanda ya yi wani irin santsi ya sanya ta miƙe tsaye tana kallon console mirror ɗin da ke wajen. Juyowa ta yi tana washe baki ta ce“Anty ji kaina ya yi kyau.” murmushi Anty Ramlah ta yi kafin ta ce“Eh mana gashinan kinyi kyau abin ki, da an ganki an ga amarya.” sunkuyar da kanta ta yi tana sosa kai, Anty Ramlah ta sake murmushi sannan ta ce“oyaa zo mu tafi Amma ta fara kira.”

To kawai ta ce sannan ta ɗauki hijabinta ta zura, Anty Ramlah ta ƙarasa cashier ɗin wajen ta biya kudaden sannan suka fita daga shagon. Bayan sun shiga mota sun fara tafiya Anty Ramlah ta ce“Nana zamu je na amso saƙo nan Jalo”

Kallonta Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Kuma dai Anty? Ni fa na gaji” harararta ta yi tana shan kwana ta ce“to ai sai ki yi ta gajiyar.” Tura baki Nana ta yi kafin ta koma ta jingina da kujerar motar idanunta ƙur akan titi tana kallon motocin da ke shigewa, Time to time take tuna maganganun Anty Ramlah, wani ta yi dariya wani kuma ta tura baki, murya can ƙasa ta ce

“Wai uncle ɗin tab!”

“Magana ki ka yi?”

Anty Ramlah ta tambayeta ba tare da ta kalleta ba, girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“A’a.” Bata sake ce mata komai ba har suka ƙarasa Gibson Jalo ɗin, Ta buɗe motar ta sauka tana kallonta ta ce“ki jirani ina zuwa” gyaɗa mata kai ta yi, Ta juya ta nufi gidan da yake kallon su. Tun Nana na jure zaman motar har sai da ta gaji, ga yunwa da take ji, ga kuma gajiya. Kanta har wani ciwo yake mata, sai bayan kusan mintuna talatin sannan Anty Ramlah ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da wata jaka mai ɗan fadi, Ta buɗe back seat ta ajiye sannan ta dawo driver seat ɗin ta tada motar suka bar wajen. Har suka ƙarasa gida babu wanda ya ce komai a cikin su, Tana gama parking Nana ta fito ta nufi balcony ɗinsu da sauri, Sai dai kafin ta kai ga ƙarasawa taji an kira sunanta. Cak ta tsaya tana zumɓura baki a fili ta ce“Na shiga uku!”

Ta juya tana kallon Maimoon dake ƙarasowa wajen, Kamar zata yi kuka ta ce“mene ne dan wallahi nagaji” hararara ta zabga mata sannan ta ce“To Atta ke kiranki” haɗe rai ta sake yi sannan ta ce“to ni wallahi ba zan je ba!” daga haka ta juya ta nufi cikin gidan su da sauri. Da idanu kawai Maimoon ta bita dai-dai nan Anty Ramlah ta ƙaraso wajen, Ta gaisar da ita cike da girmamawa, Amsawa ta yi kana ta ce

“Maimoon ya jikin?”

Sunkuyar da kai ta yi sannan ta ce“Alhamdulilah Anty”

“Sannu Allah ya raba lafiya.”

Anty Ramlah ta yi maganar tana kallonta, Da amin ta amsa sannan ta ce“Anty kawo na riƙe miki kayan” waro idanu ta yi lokaci ɗaya kuma ta girgiza kanta ta ce“haba dai rufa min asiri, na wahalar da ke. Shiga ciki kawai”

Ɗan murmushi ta yi dan daman ba wani daɗin jikinta take ji ba kawai dan Atta ta takura mata ne ya sanya ta fito. Ganin tana ƙoƙarin yin gaba yasa ta ce“Aaa Anty dan Allah idan kin shiga ki saka Nana ta zo, Atta ke kiranta kuma ta ce wai ba zata je ba.” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi ta ce“Allah ya shiryi Nana, tam zan turota” okay kawai ta ce sannan ta juya ta bar wajen, ita kuma ta nufi cikin gidan.

Kwance ta sameta a parlon kan cinyar Amma, ta ajiye jakar hannunta ta zauna ta ce“wash!”

“Sannu sai yanzu?”

Amma ta tambaya tana kallonta. Jinjina mata kai ta yi kafin ta ce“wallahi Yaya, kin san sai da suka mata gyaran jiki sannan aka mata Henna da saloon. Kuma na biya gidan matar can na amso magungunan da turaren”

Amma ta ce“Shiyasa ku ka daɗe, Yanzu ku fara cin abinci sai ki ƙarasa.” zare mayafin jikinta ta yi sannan ta ce“a’a ni a ƙoshe nake wlh, Nana tashi muje” kamar zata yi kuka ta ce“Ina kuma? Ni Allah fa nagaji sosai, kaina ciwo yake.”

Harararta Amma ta yi ta ce“ɗagani ni. So ki ke kakarki ta zo ta fara azazzalata ko me? Tashi mana.” dakyar ta miƙe zaune har da yan hawayenta ta ɗauki hijabinta ta shige ciki, Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta ɗauke kanta ta ce“Allah ya shiryeki.” Miƙewa Anty Ramlah ta yi ta ɗauki jakar da ta shigo da ita sannan ta bi bayanta.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *