Chapter 33: Chapter 33
Ta yi maganar a shagwaɓe, Jinjina kansa ya yi babu yabo babu fallasa ya ce“ai daman baki yi kama da wadda ta iya girkin ba.” Tura baki ta yi kafin ta ce“To bayan boarding school nayi, dan Allah a ina zan iya girkin?” sai da ya gama maƙale agogonsa ya mike sannan ya ce“haka ne.” ganin yana shirin fita yasa ta ce“uncle cewa nayi fa yunwa nake ji.”
“To Nana cinyeni”
Ya yi maganar yana kallon ta, Murmushi ta yi ta ce“to ai bana cin mutun, ni muje ka siya min abincin dan Allah.” harararta ya yi ya ce“ki je apartment ɗin Hajiya Babba a baki.”
“To Atta ce zata yimin faɗa fa.”
Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Bai sake bi ta kanta ba ya fice daga ɗakin. Nana ta yi shiru tana kallon sa, kafin daga bisani ta koma ta kwanta akan gadon tana hawaye, dan har ga Allah yunwa take ji bata wasa ba.
Ba’a fi 10mins ba aka sake buɗe ɗakin, Bata ɗago kanta ba sai kukanta da take a hankali, ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce
“taso mu tafi”
Jikinta har rawa yake ta tashi daga kwancen ta sauka daga kan gadon ta nufosa. Wani mugun kallo da taga ya watsa mata ya sanyata tsayawa, Ya kalleta frm head to toe sannan ya ce
“Kin koma kin rufe jikin ki ko sai na makeki anan?”
Jiki a sanyaye ta koma ciki, ta buɗe press ɗinta ta zaro wani hijabi har ƙasa baby pink ta saka. Ya yi kamar riga dan mai babban hannu ne, Yana kallon ta har ta gama sakawa sannan ta ɗauki wayarta dake gaban mirror. Ya ɗauke idanun sa daga kanta ya juya ya fice daga ɗakin, ta tura baki gaba sannan tabi bayansa. Babu kowa a parlourn ya yi waje abin sa tana biye dashi. Cikin wata Lexus jeep ya shiga, Nan da nan guards ɗin dake wajen suka taso, ya girgiza musu kai alamar shi kadai yake son fitar. Har ya gama warming motar tana tsaye tana bin sa da kallo, Ya ɗan kalli side ɗin da take fuska a haɗe ya ce“sai na bi ta kan ki ne?” sai a sannan ta sauke idanunta ta buɗe motar ta shiga passenger seat ɗin, Ya taɓe baki sannan ya juya ya bar wajen.
Sun yi nisa ta kalleshi kamar wadda aka tsikara ta ce“uncle ina zamu je?”
“siyar dake zan yi.” Ya ce ba tare da ya kalleta ba, Tuntsirewa ta yi da dariya, Ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana murmushin shima. Har suka ƙarasa gaban gidan babu wanda ya sake cewa wani abu, Ya yi horn aka buɗe gate ɗin sannan ya tura hancin motar cikin babban compound ɗin gidan. Yana gama parking ya sauke ba tare da ya kalleta ba, Itama ta buɗe side dinta ta sakko tana ƙarewa gidan kallo, Babbar gida ne wanda aka yishi cikin tsari na turawa, Daga gani ka san guest house ne, Zagayowa ya yi side ɗinta ya riƙe hannunta suka yi gaba. Nana ta dinga bin sa tana mamakin dalilin zuwan su gidan.
A babban parlourn gidan suka tsaya, parlourn an ƙawata shi da kujeru na zamani masu kyau da kuma tsada, Ko ina tsaf dashi sai ƙamshi mai daɗi dake tashi wanda ya gauraye da sanyin ac ya bada wani yanayi mai daɗi. Nana ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta jingina kanta da kujerar tana lumshe idanu, Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya buɗe wata ƙofa ya shige, Ta ɗauki a ƙalla 15mins a wajen kafin aka buɗe wata ƙofa, tabi wadda ta shigo da kallo, wata maid ce hannunta riƙe da ƙaton tray, ta ajiye a gaban Nana sannan ta koma ciki. Nana ta dinga kallon tray ɗin wanda aka cika shi da kayan shayi, tana nan zaune maid ɗin ta ƙara dawowa hannunta riƙe da warmers guda biyu. Ta sake ajiyewa gaban Nana tana murmushi ta ce
“Can i serve you ma?”.
Girgiza mata kai Nana ta yi, Ta sunkuya sannan ta juya ya bar parlour. Sai a sannan Nana ta zamo ƙasa a hankali tana sauke numfashi, Ta ɗauki tea flask ɗin sannan ta janyo wani mug ta tsiyaya shayin, bayan ta zuba wanda take ganin zai isheta ta mayar ta rufe sannan ta saka madara da kuma bounvita da yake wajen, ta saka sugar kaɗan dan bata son zaƙi. Juyawa ta yi sannan ta ajiye, Ta buɗe warmer taga soyayyen dankalin turawa a ciki sai kuma wainar kwai masu kauri, murmushi ta yi sannan ta ɗauki plate ta zuba dankalin sannan ta saka wainar guda biyu, ta tankwashe ƙafafunta sannan ta fara shan tea ɗin. Da fari sai da ta kusan amai sakamakon dadewar da ta yi bata ci abincin ba, Ta ajiye mug ɗin tana sauke numfashi a hankali. Can kuma ta fara cin dankalin tana haɗawa da kwan, idan ta ci sai ta sha tea ɗin a haka har ta cinye na gabanta tas. Ta yi gyatsa dan ta ƙoshi, amma ta gyara zamanta sannan ta buɗe ɗayar warmers, farfesun catfish ne sai tiriri yake, Ta washe baki tana dariya sannan ta saka yatsanta ta dangwali romon, lumshe idanu ta yi a fili ta ce
“woww!”
Ta ajiye murfin a gefe sannan ta janyo wani sabon plate ɗin da spoon, yanda zai isheta ta saka sannan ta zuba uban romo akai. Ta tura warmer gefe sannan ta fara ci a hankali, Sam bata lura da sanda ya shigo parlourn ba, har ya zo kusa da ita ya zauna a kujera. Ya yi Shiru yana kallon yanda take ta cin kifin tana tsince ƙaya tana tarawa a gefe. Sai da ta cinye shi shima tas sannan ta ɗago kanta tana shirin ɗaukan ruwa suka haɗa ido dashi, Ta yi saurin ɗauke nata tana tura baki. Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“har kin ƙoshi?” sai da ta ɓalle murfin robar ta sha ruwan kusan rabi sannan ta ajiye tana kallon sa ta ce“na ƙoshi sosai uncle.” jinjina kansa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Ta tashi ta kwashe kayan ta nufi hanyar da taga maid ɗin tayi, dan ita a rayuwarta bata son taga an bar waje da datti. Bayan ta kai kayan na farko ta dawo parlourn da niyyar ɗaukan sauran, sai dai abin da ta gani ya sanyata tsayawa cak, ta sake ware idanunta tana son tabbatar da abin da take gani. Da gudu kuma ta nufi inda Abdusammad yake ta faɗa jikinsa ta ƙanƙameshi tana wani irin kuka, Abdusammad ya riƙeta gam yana shafa kanta a hankali. Junaid dake zaune kan kujera ya dinga kallon ta idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, Sun ɗauki mintina a haka kafin ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen ya ce
“mene ne to?”
Sake rungume shi tayi tana kuka ta ce“uncle dan Allah, dan Allah uncle, bana so. Wallahi ba zan ƙara ba, kace ya tafi, ka ce ya yi tafiyarsa dan Allah uncle…” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka. Shiru Abdusammad ya yi yana jin yanda hawayenta ke zuba a jikinsa. Ya ɗago kansa ya kalli Junaid babu yabo babu fallasa ya ce
“I think kaje kawai. Komai ya shige”
Jiki a sanyaye Junaid ya ce“dan Allah Yallaɓai ka barni na nemi yafiyarta, ka barni na nemi afuwarta, ko na samu sauƙin abin da nake ji a zuciyata. Dan Allah…”
Abdusammad ya ɗan yi shiru can kuma ya sake ɗago kanta da kyar ya ce“Nana nace ki tsaya ko, ki bar kukan”
Girgiza kanta ta yi ta ce“bana son na ganshi uncle. Ya cuceni, shi ne fa ya cuceni, kace masa ya tafi uncle. Wallahi ba zan sauraresa ba, ba zan amsa maganarsa ba!”
Junaid ya yi shiru, can kuma ya sakko daga kan kujerar da yake, ya durƙusa akan ƙafafunsa, ya haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Bai damu da juya masa bayan da ta yi ba, Cikin wata irin murya mai fito da asalin raunin mutum ya fara cewa
“Na sani Nana, ban cancanci ki yafe min ba. Ban cancanci ki kalleni ba, ban kuma dace daki tausaya min ba. Na aikata kuskure wanda na san ba zan taɓa iya gyarasa ba, amma ki sani Nana wallahi duk abin da nayi soyyarki ce ta janyo min, duk abin da ki ka ga na yi ƙaunar da nake miki ce sanadi. Nana ina son ki, ina son ki, ina son ki fiye da yanda ki ke tunani, wallahi ban yi tunanin cutar dake ba, na yi haka ne saboda tunanin zaki hana ayi aurenku da ɗan uwanki ni kuma na samu na aureki. Ban taɓa tunanin turawa wani hotunan ba, kuma ban da wadanda na bada aka sake kawo miki wallahi tallahi bani da su Nana! Gurguwar shawarar abokina ce tayi tasiri akaina, na ɗauka hakan zai yi aiki ashe ba haka bane, madadin na sameki sai ki ka min nisan da har abada ba zan iya kamo ki ba.”
Junaid ya yi shiru yana jan numfashi saboda kukan daya tawo masa, Ya dinga shessheƙar kuka a hankali. Nana dake jikin Abdusammad ta sake riƙe shi ƙam tana kuka itama, Junaid ya ci gaba da faɗin
“Zan tafi Nana, ba zan nemi afuwarki ba, na san koda nayi hakan haƙƙin cutarwa da nayi miki ba zai barni ba. Amma ina son ki sani, ina sonki Nana. Kuma har abada ba zan daina sonki ba!.”
Janyeta Abdusammad ya yi daga jikinsa, ya miƙe tsaye ya ƙarasa inda Junaid yake, Hannunsa ya sanya ya ɗago shi, Junaid dake kuka ya girgiza kansa ya ce“nagode sosai daka bani damar magana da ita. Dan Allah yallaɓai ka fahimtar da Nana ban da niyyar cutar da ita, idan har zan ga wani ya cutar da ita to wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare. Ƙaddara ita ta kaini ga aikata hakan, ƙaddarar data ka aureta.”
Murmushi Abdusammad ya yi kafin ya ce“ba komai ta yafe maka. Allah ya kiyaye gaba.”
Junaid ya jinjina kansa sai kuma ya ce“Ina yi muku fatan Alkhairi a cikin aurenku, Allah ya baku zaman lafiya, da zuri’a ta gari.” Jiki a sanyaye Abdusammad ya amsa, sannan Junaid ya yi gaba yana biye dashi. Duk wani taku da suke yi tafiya yake da bugun zuciyarta, Ƙirjinta har ɗagawa yake, Ban da kuka babu abin da take. Ji tayi kamar suna tafiya da duk wani kwarin gwuiwarta, nutsuwarta, farin cikinta. Ita kanta ta san tana son Junaid, so mai tsanani, son da bata yi tunanin zata iya yiwa wani ɗa namiji shi ba. Amma me yasa ta ji zuciyarta ta kasa yafe masa? Me yasa ta ji bata son ganinsa, Bata son jin muryarsa. Tana nan zaune tana kuka har Abdusammad ya dawo, Ya dinga kallonta kafin ya ƙaraso wajen, Bai ce komai ba ya kamo hannunta ya niƙar da ita tsaye. Har sannan bata yi shiru ba, Ya goge hawayen duk da sabbin dake sake zubowa. Waje ya nufa yana riƙe da hannunta cikin nasa, Ya buɗe passenger seat ya sakata sannan ya rufe ya koma driver seat ya shiga. Kifa kanta ta yi akan cinyarta ta ci gaba da kukanta, Bai yi yunƙurin hanata ba ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata, kafin daga bisani ya yiwa motar key su bar gidan.
Sun kusa zuwa gida ya ɗan saci kallon ta, ganin har sannan bata daina kukan ba yasa ya yi gyaran murya kafin ya ce“Ko na siya miki ice-cream?” girgiza masa kai ta yi a hankali. Ya gangara gefen titi ya yi parking, Bai kalleta ba ya sauka daga motar, ta bi shi da idanu tana goge hawayenta. Jingina ta yi da kujerar motar ta lumshe idanunta, gaba ɗaya ji tayi jikinta ya yi wani sanyi, ga ƙirjinta dake mata wani irin zafi she wish bata bishi ba, da bata haɗu da Junaid ba. Taja numfashi ta sauke hawaye na zubowa kan kuncinta, Bai wani jima ba ya dawo ya buɗe motar ya shigo, ajiye mata ledar ya yi akan cinyarta sannan ya yiwa motar key suka bar wajen. Har suka ƙarasa gida bata yi magana ba, shima kuma bai yi mata ba. A tsakiyar compound ɗin gidan ya yi parking sannan ya juyo yana kallonta ya ce“Ki ke gida I’ll be back.”
Bata ce komai ba ta sauke ledar daga cinyarta sannan ta buɗe motar ta sauka, Ya bita da kallo har ta shige gidan sannan ya yi reverse ya bar compound ɗin. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga parlourn, Zahra na zaune kan sofa tana gyarawa Noor kanta. Ta amsa ba tare da ta ɗago kanta ba, itama Nanar bata bi ta kanta ba ta haye sama da sauri. Daƙinta ta buɗe ta shiga, ta ajiye ledar ice-cream ɗin a ƙasan carpet sannan ta haye kan gado, ta ƙanƙame pillow tana fashewa da wani sabon kukan.
****
Anty Khadijah ta dinga kallon Kaddu da rashin fahimta. Can kuma ta ce“kin ga ni wlh ban gane abin da ki ke nufi ba. Kamar ya Zahra?” wani murmushi Kaddu ta yi tana gyara zamanta ta ce“bari na fahimtar dake. Idan har kina son ki samu kuɗaɗen daga hannunsa to ai dole sai dai ki yi amfani da Zahra, saboda ita kaɗai ce wadda zata iya wannan aikin.” Shiru Anty Khadijah ta yi tana tunanin maganar Kaddun, Kaddu ta miƙe tana ɗaukan wayarta ta ce“Kin ga idan baki yarda dani ba, muje wajen Malam ya faɗa miki.” Tashi Anty Khadijah ta yi ta ce“bari na fara sallah sai muje.”
****
Murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ya yi ya shigo, Ya ƙaraso ciki ya tsaya gaban gadon yana ƙare mata kallo. Agogon hannunsa ya kalla yaga kusan 1 na rana, ya kalli ledar ice-cream ɗin dake ajiye a ƙasan wanda ke nuna bata sha ba. Durƙusa ya yi ya taɓa ta ya ce“Nana!”
Ɗago kanta ta yi a hankali, ta goge hawayenta sannan ta gyara zamanta, zama ya yi gefen gadon idanunsa akan ta ya ce
“Har yanzu baki daina kukan ba?”
Sunkuyar da kanta ta yi bata bashi amsa ba, Ya ɗan matso kusa da ita sannan ya ce“zo nan.” kamar jira take ta shige jikinsa tana sakin wani sabon kukan, Ya shafa kanta a hankali ya ce“Ya isa haka. Ki yi shiru kin ji, ai ya tafi”
“Uncle ƙirjina ciwo yake min, zafi nake ji.”
Ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, Ya sake rungumeta ya ce“sannu kin ji, ki daina kukan zai daina.”
Cikin kuka ta ce
“uncle shikenan kowa ya ga hotuna na? Shi kenan kowa yana ganin ina bin maza? Ba zan iya ba, mutuwa zan yi uncle…” ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, Girgiza kansa ya yi cikin son kwantar mata da hankali ya ce“wane ya ce miki haka? Kowa ya san ba ki da laifi, baki ga babu wanda yake jin haushin ki ba?” Ɗago fuskarta ta yi tana kallon sa ta ce“to uncle shikenan ai kowa ya ganni amma. Kuma da baka aureni ba ai babu wanda zai aureni a haka..”
Shiru ya yi yana kallon fuskarta wadda ta gama kwaɓewa saboda kuka da kuma shagwaɓar da suka haɗe mata. Abdusammad ya ɗan yi murmushi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce
“To bana aurekin ba?”
Gyaɗa masa kai ta yi hawaye na sakkowa kan fuskarta. Ya jinjina kansa sannan ya ce“oyaa stop crying” ganin tana shirin sake fashewa da wani sabon kukan ya sanya ya shiga jijjigata kamar ƙaramar yarinya kafin ya ɗora kanta akan hannunsa ya ɗan durƙusa kansa kusa da fuskarta ya ce“Haa.”
Kallon idanunsa ta yi sai kuma ta buɗe bakin nata a hankali, Bata yi aune ba kawai sai jin warm lips ɗinsa ta yi cikin nata. Nana ta ja wani irin dogon numfashi tana jin wani abu na mata yawo a jiki, Kokawar kwace bakinta ta fara yi, sai dai sam bai bata wannan damar ba, ya sake zura bakin nasa cikin nata yana sauke mata wasu hot kisses yana kuma tsotsar harsheta, Tuni ta nemi ficewa daga hayyacinta, Ta rufe idanunta ruf jikinta na wani irin rawa. Abdusammad daya fara kasa gane inda yake ya fara ƙoƙarin kai hannunsa kan ƙirjinta, Sai dai sulɓin hijabin da yaji ya sanya shi dakatawa. Ya zare bakin nasa daga nata a hankali yana sauke wani zazzafan numfashi, Hannunsa ya sanya ya yaye hijabin jikinta. Nan take ƴar ƙaramar t-shirt ɗin dake jikinta ta bayyana, Gaba ɗaya ana ganin shatin breast ɗinta sakamakon kamanta da rigar ta yi. Ya ja idanunsa ya lumshe sannan yake buɗe su a kan ƙirjin nata. Sam ya manta da wadda take hannunsa, Ita kuwa Nana ban da kuka babu abin da take, Hannunsa na rawa ya fara ƙoƙarin ya ye rigar jikinta, tuni numfashinta ya fara ƙoƙarin barin jikinta, Ganin rigar na neman ɓata masa lokaci ya sanya ya jata da wani irin ƙarfi nan take ta yage, Idanunsa ya sauka kan ƙirjinta wanda yake fari ƙaƙal dashi, sai numfashi take saukewa. Kamar wanda ake tura shi haka ya kai hannunsa kan ƙirjin, Nana ta saki wani irin ihu lokaci ɗaya fitsari ya fara zubowa daga jikinta, hannunsa ya kai bayanta yana ƙoƙarin ɓalle bra dake jikinta, Ta sanya hannayenta duk biyun ta rike rigarsa gam tana wani irin kuka mai haɗe da numfashinta. Cikin wani irin yanayi ta buɗe bakinta wanda ke rawa ta ce
“uncleee..!”
Yanda ta faɗi sunan nasa in a romantic style ya sanya shi mai da idanunsa kan bakinta, A hankali kuma ya sake ɗora bakin nasa kan nata ya fara tsotsa kamar ya samu alawa, yayinda hannunsa ɗaya ke bayanta yana ɓalle bra ɗinta.
Wani irin jan numfashi ta dinga yi, idanunta a rufe sai hawaye ne ke zubowa ta gefensu, Ta kasa koda motsi gaba ɗaya jikinta ya yi sanyin. Shi kuwa kamar ana ƙarar wutar abin da yake yi, Ya gyara zamanta akan cinyarsa tasa bayan ya zare bakinsa, Yana ƙoƙarin kwantar da ita kan gadon aka fara knocking ƙofar. Dakyar ya iya buɗe idanunsa, Ya janye jikinsa ya miƙe tsaye, Sai a sannan Nana ta samu damar tashi zaune ta koma can ƙarshen gadon ta cure jikinta waje ɗaya. Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi ya tsaya a jiki yana kallon ta da lumsassun idanunsa. Zahra dake tsaye ta ɗan sunkuyar da kanta kafin ta ce
“Daman Aliyu ke nemanka.”
Gyaɗa mata kai ya yi kawai sannan ya mai da ƙofar ya rufe. Wata irin zabura Nana ta yi tana sake ja da baya, Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, Ya juya ya fice daga ɗakin. Ɗakinsa ya shige kai tsaye kuma toilet ya nufa, Wanka ya yi sannan ya fito ya shirya cikin wata jallabiya maroon colour mai taushi, Ya gyara gashin kansa sai sheƙi yake. Turaren oud ya fesa mai daɗin ƙamshi. Gaba ɗaya a sanyaye yake komai, Ya dafa dressing mirror yana karewa kansa kallo, lokaci ɗaya scene ɗin ɗazun ya dawo masa. Wani dogon tsaki yaja, Sam bai san garin ya ya haka ta faru ba. Hannunsa ya kai kan lips ɗinsa ya shafa sannan ya ce
“Astagfirullah!”
Ya faɗa yana barin wajen, Wayarsa ya ɗauka gefen gado ganin missed calls ɗin Aliyun ya sanya shi yin waje.
Kallon ƙofar dakin nata ya yi sai kuma ya nufi upstairs da sauri, Zaune ya samu Zahra tana cin abinci ta kalleshi amma bata ce komai ba. Kamar zai wuce sai kuma ya tsaya idanunsa a lumshe har sannan ya ce
“Ina Noor?.”
“Juwaira tazo ta tafi da ita.”
Zahra ta bashi amsa jiki a sanyaye. Bai sake cewa komai ya juya ya fice daga parlourn.
Tsaye ya samu Aliyun a balcony ya harɗe hannayensa a ƙirji idanunsa maƙale da sun glasses. A hankali ya ƙarasa cikin takunsa na isa da taƙama, Aliyu ya zare glasses ɗinsa yana kallon sa, Shi kuwa ɗauke kansa ya yi yana kallon wani wajen daban. Aliyu ya yi murmushi ya ƙaraso gabansa ya ce
“Buddy na ganka haka?”
Haɗe rai ya yi sosai ya ce“mene? Me ka gani?”
Tuntsirewa da dariya Aliyu ya yi ganin yanda ya wani cure gira, Ya ce“Gani nayi ka yi fresh da kai kamar ango, ko dai?.”
Wani banzan kallo daya watsa masa ya sanya shi tsuke bakinsa. Abdusammad ya zabga masa harara sannan ya ce“idan kaga dama ka zauna anan.” Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin yin gaba, Murmushi Aliyu ya yi ya biyo bayansa yana cewa“To mene abun fusata anan?” shi dai ko kallon sa bai yi ba ballantana ya saka ran zai amsa masa, deep down nasa kuwa baya son Aliyun ya gane abin da ya faru tsakaninsa da Nana ne. Back seat suka shiga, driving ya shiga gaba suka bar gidan tare da excort ɗinsa.
****
Tafi awa kwance a wajen, Ita kanta bata san abin da ke damunta ba. Ji take yi kamar ba ita ba, Idan ta tuna abin da uncle ɗin ya yi mata sai taji kuka ya sake tawo mata, Tana nan kwance har wajen ƙarfe 3:00 na rana, Wayarta ta fara ringing. Dakyar ta tashi zaune sai a sannan ta tuna da rigarta da take a rabe, Ta ɗan kalli ƙirjin nata sai kuma ta sake fashewa da kuka, Taya ma za’a ce uncle ya yi mata haka? Akan me zai ga jikinta, ringing ɗin da wayar ta sake ne ya sanyata tsagaita kukan, Ta jawo wayartata ta kai kunne. Khadijah dake cikin mota ta ce
“Na kusa fa.”
Gyaɗa mata kai ta yi kamar tana gabanta, Khadijah ta sake cewa“Nana ko bakya jina?”
Jan numfashi ta yi kafin ta ce“Ina ji. Sai kin zo”
“Kuka kuma? Me aka yi miki?”
“Babu komai fa sai kin zo.”
Nana ta bata amsa a hankali, ok kawai Khadijah ta ce sannan ta kashe wayar ba dan ta yarda da abin da ta ce ɗin ba. Nana ta miƙe tsaye a sanyaye ta nufi toilet hannunta dafe da ƙirjinta. Wanka ta yi ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga ta material mai sulɓi, Ta ɗaure kanta da ɗankwalin yadin sannan ta saka hijabi ta gabatar da sallar azahar. Bayan ta idar ta jingina da jikin gadonta ta yi shiru tana tunane-tunane, hawaye ya ci gaba da zuba daga idanunta. Bayan mintuna sha biyar wayarta ta sake ringing ta ɗaga bata ce komai ba, Khadijah ta ce
“Na sauka fa, ina Apartment ɗin ku.”
“To bari na zo mu tafi tare”
Nana ta yi maganar a sanyaye. Kafin Khadijahn ta yi magana Amma dake jin su ta ce“kin tambayeshi ne da zaki fito?”
Wata irin faɗuwar gaba ce ta risketa, ta yi saurin girgiza kanta dan ba son maganarsa take ba ta ce“A’a. Khadijah ki ƙaraso”
Toh kawai Khadijahn ta ce sannan ta kashe wayar. Amma ta mike tana cewa“bari na baki saƙo ki tafar mata dashi.” to Khadijah ta ce tana gyara zamanta.
Bayan wasu mintina aka fara knocking ƙofar daƙinta, Nana ta kalli ƙofar da sauri hankalinta a ɗan tashe ta ce“wa…wane?”
“Ke ni ce.”
Khadijah ta bata amsa. Sauke numfashi ta yi sannan ta miƙe ta zare hijabin dake jikinta ta ƙarasa ta cire key ɗin data sakawa ƙofar, Tsaye ta ganta hannunta riƙe da wata warmer tana mata murmushi. Rungumeta Nana ta yi tana sauke ajiyar zuciya, Khadijah ta ce“Ke sai kin karyani?”
Ko saurarenta Nana bata yi ba, Ta karɓi warmern hannunta sannan suka shiga ciki, Tana ganinta mayar da key ɗin ƙofar ta rufe. Khadijah ta ƙarasa ta zauna gefen gadonta tana cewa



