⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 43: Chapter 43

Shiru ba’a yi magana ba, Ta sake cewa waye amma ba’a bata amsa ba. Shiru Nana ta yi tana kallon wajen ta cikin duhun, Lokaci ɗaya ta ga haske ya mamaye parlourn, Sai a sannan ta fara ƙarewa parlon kallo. An ƙawata shi da baloons gwanin ban sha’awa, Kafin ta yi magana taji spray na zubowa kanta, ta ɗaga idanunta tana kallon saman amma bata ga kowa ba. Murmushi ta fara yi tana kallon yanda baloons ɗin ke fashewa, Ta sauke idanun ta tana kallon jikin bangon parlourn. Wani ƙaton enlargement ɗin hoton ta ne na ranar da aka haifeta a kafe, Sai kuma wasu hotunan na sanda tana ƴar ƙarama Abdusammad ya ɗauketa, wasu tana kuka, wasu kuma tana masa dariya, Daga saman su kuma an saka “Happy birthday Naanah!”ƙasa kuma an ajiye number 1&8 wanda ya yi making 18yrs. Nana ta dinga kallon su tana jin wani irin farin ciki a cikin ranta, Lokaci ɗaya ta kalli inda yake tsaye yana kallon ta sai murmushi yake, Sanye yake da suit black colour wanda suka amshi jikinsa kai ba ka ce ya taɓa raɓar ƙasar Hausa ba. Fuskarsa a sake sai murmushi yake, Da gudu ta ƙarasa inda yake tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungumeshi tana sakin wani irin kuka. Ya dinga dariya yana shafa kanta jin yanda take kuka tana sake ƙanƙameshi, Ɗago fuskarta ya yi yana murmushi ya ce

“Happy birthday ƴar rigimar uncle!”

Ta kalle shi sai kuma ta sake mai da kanta ƙirjinsa tana ci gaba da kuka. Sake ɗago kan nata ya yi ya ce“Mene kuma abin kuka? Or are you not happy? Uncle ya shirya miki birthday party”

Girgiza kanta ta yi tana kuka mai haɗe da dariya, ta ce“No uncle. Kawai…kawai…” ta kasa ci gaba saboda kukan daya sake kwace mata, Mai data ƙirjinsa ya yi ya rungume ya ce“Shikenan ya isa haka.”

Ta dinga gyaɗa masa kai ba tare da ta daina kukan ba, Noor ce ta sakko daga sama ta ƙaraso wajen ta rungumeta ta ce

“Happy birthday Anty Nana!”

Sai a sannan Nana ta sake shi ta durƙusa ta ɗauketa tana murmushi ta ce“thank you Noorie.”

Murmushi duka suka yi, Ya kalle su ya ce“to a yanka cake ɗin ko? Dare nayi” Sauka daga jikinta Noor ta yi ta ce“Abbie bari na kira Ummi” Girgiza mata kai ya yi ya ce“na kirata yanzu zaki ganta.” Ko rufe baki bai yi ba Zahra ta ƙaraso wajen tana sanye cikin wata Abaya green dark ta ɗaura veil ɗin akanta. Noor ta tafi wajenta da sauri ta rungumeta ta ce“Ummi daman kiran ki zan yi, Ki zo mu yanka cake.” Murmushi Zahra ta yi ta ja kumatunta ta ce“to gani nan.” Noor ta bar wajen ta koma wajen Nana ta tsaya, Inda aka ajiye manyan cakes ɗin suka ƙarasa, Cake ne yafi kala biyar manya wasu da hotunanta a jiki wasu kuma da stickers. Abdusammad ne ya miƙa mata wuƙar yana murmushi ya ce“oyaaa” ta amsa tana kallon sa, A hankali waƙar Birthday ta fara tashi sauran maids ɗin gidan suna ta tafi, a haka Nana ta yanka cake ɗin. Koda ta ciro Abdusammad ɗin ta miƙowa, Ya ɗan ware idanunsa sai kuma ya buɗe bakin. A hankali ta saka masa, Suka sake tafi Noor sai dariya take tana tafi abin ta, Zahra kuwa kasa tafin ta yi dan ji take kamar ƙafafunta na neman kasa ɗaukanta, Danne zuciyarta kawai take yi. Shima ya yanko cake ɗin ya bata ta amsa tana murmushi sannan ta bawa Noor, Da kansa ya ƙarasa inda Zahra ke tsaye hannunsa riƙe da cake ɗin ya ce

“Haaa.”

Babu musu ta buɗe bakin ya saka mata, Ta fara taunawa tana murmushin da bai kai zuci ba. Bayan sun gama yanke-yanke cake ɗin aka fara bata gift, Noor ce ta fara bata wasu manyan chocolate a cikin kwali tana murmushi, Nana ta amsa sannan ta rungumeta ta ce“Thank you Noor, Allah ya miki albarka.” Dariya ta dinga yi, Zahra ma ta ƙaraso wajen ta miƙo mata wata ƙatuwar jaka mai rubutun Happy birthday a jiki, amsa Nana ta yi tana murmushi ta ce“Thank you Anty zahra.” Karo na farko data kira sunanta da girmamawa tun bayan abin da ya faru, Zahra ta ɗan yi murmushi without saying anything. Juyawa ta yi tana kallon Abdusammad dake tsaye ganin bashi da niyyar bata waya gift yasa ta taɓo shi, Yana murmushi ya ce

“mene ne?”

“Gift ɗina”

Ta ce a shagwaɓe.

“au nima sai na bayar?” ya yi tambayar yana nuna kansa, Tura baki ta yi tana shirin barin wajen taji ya riƙo hannunta, Ya ƙarasa da ita har gaban wata sofa wannan aka rufe da farin veil. Da kansa ya janye veil ɗin yana murmushi ya ce

“Happy birthday once again Nana.”

Kallon sa ta yi sai kuma ta kalli tarin kayan dake kan kujerar, Ta durƙusa a wajen da sauri ta shiga ɗaga su. Teddies ne irin wanda take so manya, Sai kayan zaƙi da yawa, Ta dinga bubbuɗawa tana murmushi. Wata ƙatuwar teddy red colour ta ɗauka ta miƙe tsaye tana kallon sa fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce

“Thank you Unclena… Ina sonka!”

Ta ƙare maganar tana faɗawa jikinsa, Murmushi ya yi kawai ya ce“da gaske kina sona Nana?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ɗagota ya ce“tsohon?” wata irin matsananciyar kunya ce ta rufeta. Ta sunkuyar da kanta ba tare da ta ce komai ba, ganin yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya shi jan kumatunta ya ce

“Kee relax, I’m just kidding.!”

Hannunta ta sanya ta share hawayenta, Ya taɓe baki sannan ya kama hannunta yana cewa“Allah ya miki sauki.” Bata ce komai ba suka koma inda su Zahra ke tsaye, Ya kalle su ya ce“muje.” To kawai suka ce sannan ya yi gaba yana rike da hannun Nana suka bi bayansa, A babban compound ɗin gidan suka tsaya, Nana ta dinga kallon motar dake gabansu wadda aka rufe da baƙin yadi. Da idanu ya yi musu alama da su buɗe, Wasu maids guda biyu suka ƙaraso wajen suka janye yadin daya rufe motar. Wata Lamborghini Aventador ce White colour, an yi mata ado da red bow wanda suka sake haskata. Nana ta dinga kallon motar babu ko kiftawa, bata san sanda ya zagaya hannunsa a jikinta ba, Kawai kallon Hannunsa ta dinga yi wanda ke riƙe da car key. Ya miƙo mata yana murmushi can gefen kunnenta ya ce

“And this na virgin gift. Allah ya miki albarka Nanata. Kin sani farin ciki mara misaltuwa, naji daɗi. Na samu nutsuwa, Thank you, na gode da ki ka kare mutuncinki har zuwa ɗakin mijin ki. Allah ya miki albarka kin ji!”

Wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji, ta kasa koda motsi sai hawaye shar dake zubowa kan kyakkyawar fuskarta. Above 2mins kafin ta saki wani irin raunataccen kuka ta juya ta shige jikinsa tana kuka kamar ranta zai fita, Shiru Abdusammad ya yi ya ɗora hannunsa a bayanta yana ɗan bubbugawa a hankali, ganin bata da niyyar yin shiru yasa ya kai bakinsa kunnenta ya ce

“Ko baki so ne?”

Saurin girgiza masa kai ta yi, Ta ɗago tana kuka ta kalle shi ta ce

“Thank You… Thank you Uncle, Na gode sosai, na gode uncle. Ina sonka Uncle, ina son ka sosai, na fi kowa sonka wallahi. Ina son ka uncle ɗina…”

Caraf taji ya kame bakin maganar, ya fara kissing ɗinta a hankali in a different romantic ways. Karo na farko data fara mai da masa da martanin abin da yake mata, Hakan ya sanya shi sake chopping face ɗin su yana ci gaba da abin da yake… Ƙarar fashewar abin da suka ji shi ne ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi, Ya janye bakinsa daga nata a hankali yana sakin numfashinta. A tare suka kalli inda suke jin ƙarar, Abdusammad ya ware idanunsa yana kallon ta da mugun mamaki…

Zahra ce tsaye gaban motar ta tawarwatsa glass ɗinta, Hannunta duk jini sai kuka take. Sakin Nana ya yi da sauri ya ƙarasa wajen ya finciko hannunta ganin tana ƙoƙarin sake buga flower base ɗin, Fizge hannunta ta yi cikin kuka kamar wata zararriya ta ce

“Ni ka rabu dani! Ka kyaleni, na rantse da Allah ba zan yarda ba!.”

Abdusammad ya dinga kallonta da mamaki, Nana ta ƙaraso wajen tana kallon yanda Zahra ta ci mutuncin sabuwar motar tata, Wani ihu ta saki ta yi kanta ta shaƙe mata wuya. Zahra ta fara ƙoƙarin dukanta, Kasancewar ba ƙarfin su ɗaya ba ya sanya ta murɗe mata hannu ta kifa mata mari. Bata ɗauke hannunta ba taji an sauke mata wasu tagwayen maruka akan fuskar, Ya fizge Nana yana kallon ta rai ɓace. Ɗago kanta ta yi tana kallon sa hannunta dafe akan kuncinta. Ta dinga gyaɗa kai kafin ta ce

“Doctor saboda wannan yarinyar ka mareni? Saboda wannan ƴar iskar ka mareni? Akan ta?”

Wani banzan kallo ya dinga watsa mata, Ya juya ya kalli Nana dake tsaye kusa da shi tana kuka a hankali, Bai ce komai ba ya ja hannunta suka nufi cikin gidan. Zahra ta bisu da kallo ganin ya mayar ta mahaukaciya ya yi tafiyarsa, Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan ta sake ɗaukan flower base ɗin ta ci gaba da dukan glass ɗin motar yana fashewa. Dan kanta ta gaji ta sulale a ƙasa tana ci gaba da kuka kamar ranta zai fita. Sai da ya kai ta har Apartment ɗinta sannan ya kulle ya dawo ƙasan. Noor dake tsaye tana kuka ya ɗauka, ta yi saurin rungumeshi tana faɗin

“Abbie Ummina”

Shafa kanta ya yi ya ce“Don’t worry kin ji.” Sun daɗe a haka kafin ya miƙawa wata maid ita ya nufi wajen, Zaune ya tarar da Zahra gefen motar tana kuka har sannan. Ya ɗan yi jim sai kuma ya ƙarasa yana kallon ta ya ce

“Tashi daga nan”

“Ba zan tashin ba! Ina ruwan ka dani ma? Mene ruwanka da zamana?”

Zahra ta yi maganar a fusace. Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya dauke kansa yana kallon fountain ɗin dake zubar da ruwa as usual ya ce

“Kada ki ɓata min rai. Ki tashi ki koma ciki nace!”

Miƙewa ta yi tana kallon sa rai ɓace ta ce“au tunanin ka zan yi abin da ka ke so ne? Bayan ka mayar dani banza shara a gidanka? Bayan kana nuna rashin adalci a fili? To wallahi ba zan yi ba! Kuma ka sani wannan abun da ka yi tamkar ka buɗe wani sabon shafi ne na bala’i da tashin hankali a cikin gidan nan, ba zan taɓa bari a zauna lafiya ba! Ita kuma yarinyar za tayi dana sanin shigowa cikin gidan nan!”

Zahra na gama faɗin hakan ta nufi cikin gidan kamar zata tashi sama, hannunta sai ɗigar jini yake amma ko damuwa bata yi ba, da idanu kawai Abdusammad ya bita sai kuma ya sauke numfashi. Ya dinga kallon yanda ta wulaƙanta tsaddajiyar motar, gaba ɗaya ta farfashe glasses ɗin ta. Girgiza kansa ya yi yana sake jin jina al’amarin mata, Kafin daga bisani ya yiwa wasu securities umarni dasu gyara wajen a ɗauke motar. Shi kuma ya koma cikin gidan.

Nana na zaune gefen gadonta sai kuka take, idan ta tuna yanda Zahra ta farfashe mata glass ɗin sabuwar motarta sai taji ranta na ɓaci. Kasa jurewa ta yi ta janyo wayarta dake can ƙarshen gadon ta yi dialing numbern Hajiya Babba. Sai da ta kusa katsewa sannan Hajiya ta ɗauka, Daga ɓangarenta ta ce

“Nana yau kuma kin tuna dani?”

Fashewa da wani sabon kukan Nana ta yi, Hankalin Hajiya Babba ya tashi ta ce

“Mene ne? Kukan me ki ke takwara?”

Cikin shessheƙar kuka ta ce

“Hajiya Anty Zahra ce!”

Da mamaki Hajiya Babba ta ce

“Me ta yi miki ita Zahra?”

Nana na goge hawayenta ta ce

“Dukana ta yi Hajiya, saboda kawai nayi magana shi ne ta mareni. Kuma ta fasa min motar da uncle ya siya min…”

Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Hajiya Babba da ranta ya gama ɓaci sakamakon maganar dukan da taji ta ce

“Shi Abdusammad ɗin yana gani ta mareki?” gyaɗa mata kai Nana ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce

“Eh mana. Kuma Hajiya ta fasa min motar da ya bani…”

Shiru Hajiya Babba ta yi can ta ce“shikenan yi shiru bari zan kira shi ya kai mata wayar naji dalilin da zata dake ki.”

Nana ta gyaɗa kanta ta ce“To Hajiya na gode.”

“Ki daina kuka”

Hajiya Babba ta yi maganar a tausashe, To Nana ta ce sannan ta kashe wayar, Ta kwanta gefen gadon ta yi shiru tana tunani.

Zahra na zaune tsakiyar gadonta tana waya da Anty Khadijah ya shigo ɗakin, Tana ganinsa ta sauke wayar daga kunnenta ba tare da ta kashe ba, Ya ƙaraso gaban gadon ya zauna yana kallon ta fuska a ɗaure ya mika mata wayar dake hannunsa. Kallon wayar ta yi sai kuma ta kalle shi, Ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta amsa ta saka wayar a kunne. Hajiya Babba dake zaune kan sofa ta ce

“Zahra’u”

Cike da girmamawa ta ce

“Barka da rana Hajiya, Ina yini?”

“Alhamdulillah. Daman naji wani batu ne wanda bai min daɗi ba, na ce bari na miki magana. Akan me kina da hankalin ki zaki dinga biye wa yarinya ƙarama? Akan me zaki daketa? Kin san yanda muka ɗauketa? Kin san matsayinta a wajen mijin ki shi kansa? Akan me haka?”

Hajiya Babba ta yi maganar a faɗace, Shi dai Abdusammad shiru ya yi dan duk abin da take faɗa yana ji saboda a handsfree wayar take. Zahra da hawaye ya sake cika idanunta ta girgiza kanta ta ce

“Wallahi Hajiya ba laifina bane. Yarinyar ce bata da kunya, Har ni Nana zata dinga yiwa kallon kishiya tana faɗawa magana? Kasa jurewa nake wallahi!”

“Shi ne ki ke dukanta? Idan mahaifinta yaji zai ji daɗi ne? Kin san son da yake wa ƴarsa? Bana son sake jin irin haka ta faru. Kada ki sake cewa zaki kai hannu ki daketa, idan ta yi miki laifi ai ga mijinku nan ki sanar masa, amma kada ki sake cewa zaki ɗauki hukunci da kan ki.”

Zahra ta haɗiye wani miyau mai ɗaci kafin ta gyaɗa kanta ta ce“In sha Allah Hajiya ba zan sake ba.”

Hajiya Babba ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce“Yauwa to, Allah ya yi albarka.” Da Amin ta amsa sannan ta miƙa masa wayar, Ya karɓa ya tashi ya fice bayan ya saka wayar a kunnensa. Zahra ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga sakkowa kan fuskarta, Anty Khadijah da ke kan layi har sannan ta taɓe baki ta ce

“Zahra! Zahra! Zahra! Kina zaune a inda ba’a ganin darajarki? Kina zaune a inda ba’a ganin ki da ƙima? Ya ma za’a yi uwar mijin ki ta dinga faɗa miki irin wadannan maganganun? Taɓ!”

Zahra da taji kamar ta fama inda ke mata kaikayi ta fashe da kuka tana cewa“Anty kin gani ko? Basa sona! Ba sa ƙaunata, basu damu dani ba. Kamar ba sirikar gidan ba, Daman Hajiya Babba ba son auren mu take ba kawai ta yi shiru ne. Yanzu kuma ya auri wadda take so dole ta nuna mana banbanci, wallahi ji nake kamar na gudu na bar gidan nan, kamar na yi tafiyata na bar su!…”

Ta sake fashewa da wani kukan. Girgiza kai Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“ba za’a yi haka ba, dole a san abin yi. Babu yanda za’a yi na bar ki cikin wannan masifar Zahra! Yanzu ni babu kudi a hannuna. Duk na bawa Garba, idan kina da wasu kuɗaɗe ki samu ki turo ko ki karɓa a hannun mijin ki, na san abin da zan yi miki. Wallahi babu wadda ta isa ta fitar dake daga cikin gidan nan, Kuma ko kallon banza babu wadda ta isa ta yi miki har da uwar tasa.” Shiru Zahra ta yi kamar me tunani sai kuma ta ce“Ina da kuɗi zan turo miki Anty.” Anty Khadijah ta gyada kanta ta ce“Toh shikenan. Ki daina kuka amma” Share hawayenta ta yi ta ce“In sha Allah Anty.”

“Ki saki ran ki, kada ki nuna ran ki ya ɓaci, Ku tashi ki je ɗakinsa. Kada ki ce zaki yi fushi yanzu, ki kwantar da kan ki” Toh kawai Zahra ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar. Ta tashi kamar yanda Anty Khadijah ta ce mata ta shige toilet, wanka ta yi ta fito ta ɗauki kayan baccinta ta saka sannan ta fito daga nata apartment ɗin ta nufi nasa.

Koda ta shiga zaune ta same shi tsakiyar gado ya yi shiru da alama wani abun yake tunani, ta ƙarasa ciki ta zauna gefen gadon tana kallon sa ta ce

“Doctor!”

Tamkar a mafarki haka yaji muryar tata, Ya ɗago ya kalleta. Sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, Ya ɗan yi jim kafin ya ce

“Zahra lafiya? Ko nan ɗin ma zuwa ki ka yi ki tadan hankali?”

Saurin girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“A’a wallahi, dama zuwa nayi na baka haƙuri. Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, ba zan sake ba, wallahi kasa jurewa nake doctor, kai kan ka ka san ina sonka. A duk sanda naga Nana ta raɓeka ji nake kamar zuciyata zata fito, sai naji ba zan iya barinta ba. Dan Allah dan Annabi doctor ka fahimceni, koda zaka nuna mata soyyaya kada ka yi a gabana. Wallahi ba zan jure ba, Ita tana da kowa, tana da danginta wanda suke sonta. Tana da dangin miji wanda suke goya mata baya, sannan kuma tana da kai. Ni kuma bani da su, kai kaɗai nake da! Da kai na dogara. Idan ka gujeni bani da kowa….” Zahra ta ƙare maganar tana kallon sa hawaye na zubowa kan fuskarta. Ban da kallonta babu abin da Abdusammad ke yi, Ya sani Nana ta fita gata. Nana na da gatan iyaye, tana da na yayye sannan kuma ga gatan miji. Saɓanin ita da shi kaɗai ne gatanta sai kuma Allah, Tashi ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna gefenta ya kama hannunta murya a sanyaye ya ce

“Na sani Zahra, kuma kema kin san bani da niyyar wulaƙanta ki, ban aure ki saboda na cutar dake ba. Na aure ki ne saboda ina son ki, saboda na shirya zama dake, kuma zan kare mutuncin ki da martabarki. But why ki ke son ɓata kan ki? Akan me ki ka sauya? Ba haka ki ke ba da Zahra. Wannan ba ɗabi’un ki bane, Kin zama mara haƙuri, kin zama mara kunya, kin koyi rashin mutunci kala-kala. Faɗa min wane yake son gurɓata tunanin ki?”

Ya yi maganar cikin tausasa harshe, Zahra dake kuka ƙasa-ƙasa ta ɗago kanta ta kalle shi sai kuma ta girgiza kanta ta ce

“Dan Allah ka yi haƙuri, ba zan ƙara ba.”

Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce“Ba komai ni ban riƙe ki ba. Kuma idan sabon mota ki ke so ba sai kin fasa nata ba, sai ki faɗa min na sauya miki. Naga kina da cars har biyu kuma ba hawa ki ke ba, that’s why yasa ban sa an kawo dake ba. But za’a kawo miki kema” Girgiza kanta ta yi ta ce“a’a wallahi, ka bar shi.” Bai ce komai ba ya jawota jikinsa ya rungumeta, Zahra ta saki ajiyar zuciya tana jin duk wata damuwar na narkewa.

Washegari da safe ya shiga apartment ɗin Nana, tana kwance akan gado tana kallo, Ya ƙarasa ciki ya zauna kan drawer yana kallon ta ya ce

“Madam ko gaisheni ba zaki yi ba?”

Ko kallon sa bata yi ba ballantana ya saka ran zata kula shi. Ya ɗan yi murmushi yana shafa kansa kafin ya ce

“Yau kuma me nayi?” .

Tashi ta yi ta rufe system ɗin dan ba son jin muryarsa take ba, ta sauka daga kan gadon tana shirin barin wajen taji ya jawota. Ƙoƙarin kwance kanta ta dinga yi amma ta kasa, Ya matseta sosai a jikinsa ya ce

“Ke me yasa baki son hutawa da rigima?”

Rufe idanunta ta yi ba ta ce komai ba, Ya sanya hannunsa ya janye nata yana Murmushi ya ce“Ko kallo ban ishe ki ba kenan?”

“Ni ka rabu dani…”

Ta ce kamr zata yi kuka, harararta ya yi yana jan kumatunta ya ce“naƙi ɗin, ba zan rabu dake ɗin ba.” Nana ta buɗe idanunta tana kallon sa, murmushi kawai yake, Kasa ɗauke idanunta ta yi ganin yanda murmushin ke ƙara masa kyau. Ganin tana kallon sa ko kiftawa babu ya sanya shi ɗago fuskarta ya yi chopping face ɗinsu suna jin saukar numfashin juna ya ce

“Me yasa ki ka faɗawa Hajiya Babba jiya? Bana ce miki ban da surutu ba.”

Saurin janye fuskarta ta yi ta sauka daga jikinsa ta koma gefen gadon tana kallonta. Tasowa ya yi ya dawo kusa da ita ya jawota yana fadin

“Ina magana kina share ni ko? Kin raina ni”

Turo baki ta yi tana kallon sa ta ce“Ni wallahi ba zan yarda ba. Sai ta biyani motata, kuma sai na rama marin da ta yi min” waro idanunsa yayi yana kallon ta jin abin da take cewa. Lokaci ɗaya kuma ya yi kwanciyarsa kan gadon yana murmushi, Kallon sa ta dinga yi sai kuma ta kwanta ta ɗora kanta a ƙirjinsa ta ce

”Kaji uncle. Ka rama min”

Murmushi kawai ya yi ya janye hular dake kanta yana shafa sumar kanta ya ce

“To naji zan rama miki.”

Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, ganin yana dariya ya sanya ta tashi zaune tana kallon sa ta ce

“wallahi ba rama min zaka yi ba. Ni bari naje na rama da kaina” Ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon, Ji ta yi ya jawota ya kwantar da ita gefensa ya ɗago yana kallon ta ya ce

“Bana son rigimar banza. Ki bar ni na huta”

Turo ɗan ƙaramin bakinta ta yi ta ce“To ba kace kana sona ba? Ai sai ka rama min duka. Kuma kana gani fa ta dakeni” Murmushi kawai ya yi, ta sake buɗe bakinta zata yi magana taji ya kame bakin, Zaro idanunta ta yi tana kallon sa. Ya lumshe idanunsa yana kissing ɗinta a nutse, Shiru Nana ta yi tana karɓar saƙon nasa. Ganin yana yawo da hannunsa a jikinsa ya sanyata zabura zata tashi, Ya sake maidata ya kwantar ya sakar mata nauyinsa….

Tun daga wannan ranar bata sake samun sukuni ba a wajen uncle ɗin nata, Baya taɓa barinta ta huta, kullum yana maƙale da ita. Idan ba ranar kwananta bane da rana sai ya kirata apartment ɗinsa, Sai dai idan baya gidan. Tun tana kin zuwa tana masa kuka har Itama ta saki jikinta ta saba dashi, A ɓangaren Zahra kuwa bata wani shiga sabgar su. Idan ba Noor ce ta dawo daga school ba bata sakkowa ƙasa, Ta zama so silent abin ta. A haka har kusan sati huɗu suka shuɗe, Ranar wata Alhamis da daddare Nana na zaune ɗakinta suna video call da Maimoon take faɗa mata Haule ma ciki ne da ita, Nana ta dinga dariyar keta. Maimoon kuwa murmushi ta yi ta ce

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *