⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 47: Chapter 47

“Sorry mana”

“Ni ka cikani, na daina kula ka!”

Ta yi maganar tana tura baki, Gyara zaman sa ya yi ya ɗago fuskarta yana kallon ta sosai ya ce“Shikenan zan faɗa”

Tsayawa ta yi da kokawar tana kallon sa ta ce“To faɗa min.”

Ɗan murmurshi ya yi sannan ya ce

“To rufe idanun ki”

Ɗan juya idanunta ta yi ta ce

“Ni kawai ka faɗa min wallahi.”

Girgiza kansa ya yi ya ce“Ai sai kin rufe”

Ta tura baki gaba sannan ta sanya hannunta ta rufe fuskarta gaba daya, Numfasawa ya yi, Bata yi aune ba taji ya rungumeta tsam a jikinsa, Ya ɗora kansa a gefen wuyanta, Ajiyar zuciya Nana ta sauke. Ta sanya hannayenta duk biyun ta riƙe shi ita ma, Bata yi aune ba sai jin zubar hawaye ta yi a bayanta, Ta ɗago dan ganin abin da ke faruwa amma ya sake riketa gam, Yanda ba zata iya ganinsa ba. Lokaci ɗaya kuma yana ci gaba da kukansa.

“Uncle.”

Ta ce a sanyaye, Bai bata amsa ba sai sake rufe fuskarsa da ya yi a jikinta. Shiru Nana ta yi tana sauraren sautin kukansa, Gaba ɗaya jikinta ya yi wani irin sanyi,Tun da take bata taɓa jin kukansa ba. Bata taɓa gani ba, Duk yanda abu ya dameshi ba lallai ya zubar da hawaye ba. Koda zai zubar Hajiya Babba da Abba ne kawai suke iya ganin hawayensa, amma yau gashi yana kuka a gabanta. Sun ɗauki mintina a haka har sai da ya yi shiru dan kansa, Abdusammad ya janye fuskarsa daga jikinta yana ƙoƙarin goge ragowar hawayen da ke kan fuskarsa.

“Uncle..”

Ta kira sunansa a sanyaye, Ɗan tsuke fuskarsa ya yi hannunsa riƙe da ƙaramin hanky yana goge hawayensa. Shiru ta yi tana kallon sa har sai da ya gama, Sannan ya buɗe bakinta tana shirin yin magana taji ya ce

“Nana!”

Yanda ya kira sunanta in a serious tone ya sanyata nutsuwa, Ta kalleshi ta ce“Na’am uncle.”

“Kar naji maganar kuka a bakin wani, Understood?”

Shiru ta yi bata ce komai ba, Ya sanya hannunsa yaja hancinta sannan ya ce

“Ina wasa da ke?”

Girgiza masa kai ta yi, Ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya shige toilet. Tana nan zaune har ya fito, Ta dinga kallon sa ganin yana shirin fita yasa ta ce

“Uncle ina zaka je kuma?”

Sai da ya ɗauki wayarsa saman kujerar sannan ya ce

“Sallah zan yi, Kema ki yi”

Tashi ta yi tana ƙoƙarin gyara mayafinta ta ce“To bari na tafi”

Wani irin kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sunkuyar da kanta, Fuskarsa a tsuke ya ce

“Idan ki ka bar nan sai na ɓata miki”

Turo baki ta yi ta koma ta zauna, Ya juya ya fice daga ɗakin.

****
Umma ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, Zahra na zaune gefen gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take a hankali. Umma ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tana kallon ta, Tun bayan da ta dawo ɗazu da safe bata yi shiru ba, Dakyar ta yiwa Ummar bayanin abin da ya faru da kuma dalilin sakin nata. Duk irin yanda Umma ta dinga bata haƙuri kin ji ta yi, Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, Dan kanta kuma ta gaji ta yi shiru da yamma, Bayan sallahr magriba kuma ta ci gaba da kukan. Umma ta sauke numfashi tana kallon ta ta ce

“Zahra’u”

“Na’am Umma”

Ta amsa cikin kuka, Shiru Umma ta yi zuciyarta a dagule, Ba ƙaramin tausayi ta bata ba, Gefe guda kuma ga takaicin biyewa Khadijah da tayi. Can dai ta ce

“Kenan ba ki san ƙaddara ba? Baki yi imani da ita ba? Ba zaki haƙurcewa zuciyar ki ba?”

Dakyar Zahra ta ɗago kanta tana kallon ta cikin kuka ta shiga girgiza kanta ta ce

“Wallahi Umma ina son Doctor, Ina son Abban Noor. Bana son rabuwa dashi, Zuciyata zafi take min Umma. Ji nake kamar zan mutu, Na kasa yarda ya sakeni, Na kasa Umma!”

Ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Shiru Umma ta yi tana kallon ta, Can dai ta dafata cikin sanyin murya ta ce

“Na sani, Na sani Zahra’u, Amma ina so ki sani duk abin da ubangiji ya hukunta babu makawa sai ya faru. Allah ne ya hukunta zaki aure shi, Wannan shi ne dalilin daya sanya ku ka haɗu tun farko, Har ku ka haifi ƴa tare. Sannan sakin ki da ya yi shi ma Abu ne wanda ubangiji ya hukunta ba mutum ba, Shi aure rai ne dashi, Duk ranar daya ƙare to dole sai an rabu. Dan haka ki ɗauki sakin nan matsayin ƙaddara, Kada ki ce zaki damu kan ki dan Allah Zahra’u. Kada ki sakani cikin wata damuwar bayan wadda nake ciki, Ki taimaka”

Sosai Ummar ta bata tausayi, Dan ta san duk abin da faru ita ce sila, Sun kasa barinta ta samu nutsuwa, kullum cikin ɗawainiya take dasu tun bayan rasuwar mahaifin su. Ta gyaɗa mata kai duk da yanda take jin abu ne mai wahala ta manta dashi ɗin ta ce

“To Umma….”

Ta ƙare maganar cikin kuka, Numfasawa Umma ta yi ta ce

“Allah ya shige mana gaba, Ki daure ki ci abinci.”

“To Umma”

Shi ne kawai abin da ta iya furtawa, Umma ta tashi ta fice daga ɗakin a sanyaye. Zahra na ganin ta fita ta sake rushewa da wani sabon kukan, Ta sani ba zata mance da Abdusammad nan kusa ba, Ba zata manta rayuwar su tare ba. Abu ne mai wahalar gaske ta iya cire shi daga ranta, Ta sake kan numfashi tana ci gaba da kukanta. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, Ta ɗaga kanta tana kallon ta, Anty Khadijah ce ta shigo tana kallon ta, Zahra ta yi saurin tashi tsaye tana girgiza mata kai cikin kuka ta fara magana

“Kar ki matso kusa dani, Kin cuceni Anty! Kin cuceni, Wallahi ba zan taɓa yafe miki ba.”

Zahra ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Kallon ta Anty Khadijah ta dinga yi, Ta taɓe baki tana girgiza ƙugu ta ce

“Na cuce ki fa ki ka ce Zahra? Na cuce ki a ina? Ni na saka ki? Dole nayi miki?”

Zahra bata iya cewa komai ba sai kuka kawai take, Anty Khadijah ta ɗan yi murmushi ta ce“Ai ni ba cuce ki ba, Duk abin da nayi saboda ke na yi sa, Saboda ina son na taimake ki ne, Dan haka mutuwar aurenki ba laifina bane. Sakacin ki ne ya janyo miki”

Ta ƙare maganar tana zabga mata wata uwar harara, Can kuma ta juya ta fice daga ɗakin rai ɓace. Silalewa a ƙasa Zahra ta yi tana ci gaba da kukanta, ta yi dana sanin yarda da maganganun Anty Khadijah, Ta yi dana sanin biye mata, Da duk hakan bata faru da ita ba. Da Noor bata mutu ba, Da Abdusammad bai saketa ba, da ace ta ɗauki duk maganganun da Umma take faɗa mata da yanzu tana zaune gidan mijinta cikin kwanciyar hankali, Ta sake fashewa da wani sabon kukan tana ɗora kanta gefen gado.

****
Bayan sallar isha’i ne suna zaune a parlon wanda suka haɗa da Abba, Papa, Sultan, Hamid, Aliyu, Daddy, Mama, Hajiya Babba, Atta da kuma Abdusammad. Papa ya kalli Abdusammad jin bai ce komai ba ya ce

“Abdusammad muna jin ka.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, Can kuma ya ɗan numfasa kafin ya fara magana cikin nutsuwa.

“Na rasa ta ina zan fara, Na rasa me zan yi? Na rasa da wane ido zan kalle ku duka”

Da ɗan mamaki Papa ya ce

“Me ya faru Abdusammad? Wani abun aka yi?”

Shiru ya ɗan yi kamar me tunani, Can kuma ya girgiza kansa muryarsa a sanyaye ya ce

“Komai ma ya faru Papa, Nayi laifi, Laifin da ban gane girmansa ba sai daga baya. Laifin da ya zama sanadiyyar saka dangina cikin matsala, Na yi kuskure, Na rasa ta ina zan fara gyara shi”

Ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi, Su dai babu wanda ya ce komai a cikin su sai kallon sa suke,

“Na san ba lallai ku gane abin da nake nufi ba, Ina magana ne akan auren da nayi. Duk abin da faru ya faru ne ta dalilin auren da nayi, Tabbas duk abin da babba ya hango yaro ko ya hau saman dutse ba zai hango shi ba. Ban kyauta ba, Na ƙarya doka da tunanin cewa auren dangi tamkar take haƙƙi ne. Ban nemi shawarar kowa ba, Ban yi tunanin abin da hakan zai jawo ba, Ban yi aiki irin na masu hankalina ba. Kawai na yi abu dai-dai da son zuciyata, Na auri wadda nake ganin ita nake so, Ita ce zan iya rayuwa da ita. Ita ce zata haifa min ya’ya mu yi rayuwa irin wadda na shirya, amma abin da na kasa ganewa shi ne aibun dake cikin bijirewa iyaye.”

Tsayawa ya yi da magana, Ya ɗan gyara zamansa yana mai da idanun sa kan Hajiya Babba sosai ya ci gaba da cewa

“Hajiya ban kyauta ba, Na bijire miki, na yi ba dai-dai ba. Ban ɗauki shawarar ki, Ban ma baki wannan damar ba, Na sani duk abin da faru ya faru ne dalilin bijire miki da nayi, Dan Allah dan Annabi ki yafe min…”

Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa, Idanun sa suka circiko kamar me shirin yin kuka, Dafa shi Abba ya yi a sanyaye ya ce

“Abdul me ya faru ne? Mene ne haɗin auren ka da abubuwan da suka faru?”

Kallon Abba ya yi da jajayen idanun sa, Sai kuma ya girgiza kansa muryarsa a sarƙafe ya ce

“Abba komai ma ya faru ne sanadiyyar aurena. Zahra ita ce wadda ta fitar da hotunan Nana, Daman kowa ya san da wannan, Ita ce wadda ta fara tarwatsa rayuwar yarinyar har ta kai ga ta samu ciwon zuciya. Sannan da ban auri Zahra ba da ƴar uwarta ba taga Safwan ba, Kuma da Safwan bai auri Siyama ba da bai rasu ba Abba. Domin Siyama ita ce wadda ta shafa masa cutar Hiv ɗin da ta yi ajalin sa!”

A firgice duk suka dinga kallon sa, Hajiya Babba da tun da ya fara magana bata ce komai ba ta gyara zamanta muryarta a dake ta ce

“Siyama kuma?”

Kallon ta Abdusammad ya yi kafin ya gyaɗa mata kai ya ci gaba da cewa

“Eh Hajiya, Ita ce, Safwan ya faɗa min komai. Ya kuma nuna min komai, Siyama ita ce take ɗauke da cutar, sannan ita ta shafa masa, wannan dalilin ya sanya ya saki Haule gudun ta kamu da cutar ita ma. Hajiya na yi kuskure, Duk abin da Safwan ya yi ba shi da laifi, domin da bai ga nayi ba shima ba zai yi ba, Da bai ga na auri Zahra ba ba zai taɓa cewa zai auri Siyama ba. Da bama zai ganta ba, Sun asirce shi ne ita da mahaifiyarta domin kawai ya bijire muku, Duk abin da Safwan ya yi ba shi da laifi.”

Babu wanda ya iya cewa komai a cikin su, Atta kuwa tuni ta fara kuka tana girgiza kanta. Ajiyar zuciya Abba ya sauke jikinsa duk a sanyaye ya ce

“Ka daina faɗin haka Abdul, Duk abin da ya faru ba laifin ka bane. Ƙaddara ce! Ita kuma ƙaddara ba’a iya guje mata, Haka Allah ya tsara babu yanda zamu iya”

Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce

“A’a Abba wannan ganganci, Sakaci na ne, Wannan shi ne dalilin daya sanya Allah ya jarrabeni. Abba na muku ba dai-dai ba, Na rusa muku dangi da abin da ku ka daɗe kuna ginawa, amma duk da haka baku ce min komai ba. Baku yi fushi dani ba, Kun ci gaba da zama dani kamar ma babu abin da ya faru, Me ya sa Abba?”

“Saboda mun san wata rana dole zaka gane gaskiya kamar dai yau ɗin nan!”

Papa ya bashi amsa kai tsaye idanunsa zube akan sa. Juyawa Abdusammad ya yi ya kalle shi sai kuma ya jinjina kansa ya ce

“Haka ne, Cikin ikon Allah gashi na gane gaskiya, Dan haka zan yi duk mai yiwuwa wajen ganin na gyara abin da na ɓata. Zan karɓi abin da yake nawa, zan ɗauki girman da Allah ya bani. Ba zan sake aikata irin abin da na aikata ba har abada”

Murmushin jin daɗi Abba ya yi, Zuciyarsa wa sai dan daman ya san dole wata rana sai Abdusammad ya gane abin da ya yi, kuma ya karɓi laifinsa. Duk da bai yi tunanin abun nan kusa ba, Ita kanta Hajiya Babba zuciyarta ta fara sanyaya, Takaicin ta ya fara raguwa. Duk da daman ita bata taɓa rike shi a ranta ba. Ganin babu wanda ya ce wani abu ya sanya ya ci gaba da cewa

“Na rabu da Zahra, Ba dan na tozarta ta ba, sai dan ba zan iya ci gaba da zama da ita a haka ba. Zan zauna da Nana, zan kula da rayuwarta, Ba zan taɓa bari wani abun ya sameta ba in sha Allah.”

Da mugun mamaki duk suke kallon sa,

“Akan me ka saketa?”

Ya tsinkayi muryar Hajiya Babba tana tambayarsa, Sosai yaji san yi a ransa jin yanda ta yi masa maganar. Ya numfasa kafin ya ce

“Saboda ba zan iya ci gaba da zama da ita ba Hajiya, Zahra ta kashe min Noor, ita ce wadda ta saka guba a cikin abincin da sunan ke zata kawowa. Sai kuma Nooriya ta fara cin abincin wanda ya yi sanadiyar rasa rayuwarta, Dan haka ba zan zauna da ita ba. Ba zan iya ci gaba da kallonta da igiyar aurena ba, dole na rabu da ita!”

Salati da sallalami aka fara a parlourn, Kowa na fadar abin da ke ransa. Shi dai bai iya cewa komai ba ya sunkuyar da kansa, Cikin kuka Atta ta ce

“Amma wannan yarinya ba zamu yafe mata ba, Saboda mugunta shi ne har zata iya zuba guba a abinci? Na shiga ukuna! Wace irin rayuwa ce muke ciki ne? Me yasa mutane basu ɗaukan ran mutum a bakin komai?”

Babu wanda ya ce wani abu, Ta ci gaba da kukanta tana maganganunta. Can dai Hajiya Babba ta ce

“Ya isa haka, Ku bar aibata ta, Ni na yafe mata. Idan tana sane ta yi Allah ya shiryeta, Idan kuma cikin rashin sani ta aikata to ubangiji ya yafe mana baki ɗaya, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu.”

Da Amin Abdusammad ya amsa. Papa ya ce

“Amin. Dan Allah abar wannan maganar a nan, duk abin da ya wuce a bar shi a ya wuce ɗin. Tun da har ya saketa to kar a sake tada maganar, ita kuma wacce da zarar ta gama takabarta za’a sallameta ta tafi gida, Dama ba wani abu ya sanya muke kin auren bare ba, muna ƙi ne saboda irin haka. Baka san wa zaka je ka auro ba, Idan ma ka yaba da halayenta to baka san su wane danginta ba, Dole shi kuma kowane tsuntsu kukan gidan su yake. Duk halin kirkinta za’a iya jan ra’ayin ta, Dan haka ya sanya muke zaba muku mata a cikin dangi inda ka san su wane iyayenta da kuma ahalinta, Ba wai muna yi bane saboda mu cutar da ku, Mu a ganin mu gata ne muke muku a matsayin ku na ya’yan mu, Dan haka dan Allah dan Annabi ku zama masu biyayya, Su iyaye ba’a ja dasu. Koda abin da suka ce bai maka ba to ka yi musu biyayya tabbas zaka ga ribar hakan, Bijire musu babu abin da zai jawo sai dana sani, Dan haka ku kiyaye.”

Jinjina kai kawai suka yi kafin suka amsa da in sha Allah, Abba ya gyaɗa kansa cike da gamsuwa ya ce

“Wannan haka yake. Allah ya ci gaba da haɗa kan mu, Ya bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya, Ya jiƙan magabatan mu, da kuma yaran mu, Allah ya jiƙan Yaya, Allah ya jiƙan Safwan, Allah ya jiƙan Fatima. Ya gafarta musu, Ya sanya Annabi ya san da zuwansu. Mu kuma Allah ya sanya mu cika da imani, Da mu da sauran al’ummar musulmai, Allah ya sanya mu mutu muna masu ambaton sunan Allah!”

Da Amin duk suka amsa, Suka ɗan yi shiru kafin kowa ya fara tashi yana tafiya ɗaya bayan ɗaya, Sai da ya rage kowa ya fita sannan ya tashi ya koma kusa da Hajiya Babba ya zauna a ƙasan kujerar da take, Cikin sanyin murya ya ce

“Mamaa…”

Yanda ya faɗi sunan nata ya sanyata kallon sa, Bai ce komai ya ɗora kansa akan cinyarta lokaci ɗaya ya saki wani kuka mara sauti, Shiru Hajiya Babba ta yi tana sauraren sa, Koda wasa bata son abin da zai ɓata ransa, Tun yana ƙarami Allah ya dora mata ƙaunar sa, Kaf cikin ƴaƴanta ta fi son sa, Daga shi sai Safwan. Bata son abin da zai saka su a damuwa, yanzun nan itama hankalinta zai tashi, Ta ɗan sauke numfashi muryarta a nutse ta ce

“Mene haka?”

Ci gaba ya yi da kukansa, Ya girgiza kanta ta ce

“Arɗo!”

Da sauri ya ɗago kansa, Rabon da yaji ta kira shi da sunan har ya manta. Hannunta ta buɗe yayi saurin tashi daga ƙasan ya koma kan kujerar ya zauna yana shigewa jikinta, Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Hajiya Babba ta sauke, Ta sanya hannunta na dama tana shafa sumar kansa a hankali. Tun yana kuka har sai da ya yi shiru dan kansa ya komai sauke ajiyar zuciya, Gaba ɗaya sai yaji damuwarsa ta kau, Yaji ya daina jin abin da ya tokare masa a ƙirji, Yaji nutsuwar daya rasa tana dawowa a hankali. Sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka har sai da taji ya yi shiru sannan ta ɗago kansa tana kallon sa ta ce

“Kai yaushe zaka girma?”

Sake mai da kansa ya yi jikinta yana murmushi, ta girgiza kanta kafin ta ce

“Allah ya shirye ka”

A zuciya ya amsa da Amin, A fili kuma ya ɗan yi murmushi. Bai bar apartment ɗin Hajiya Babba sai wajen karfe 10 na dare, Shima ita ta kore shi ta ce masa bacci zata yi, Bayan ya gama yi mata hira. Kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya nufa, Koda ya shiga bai samu kowa a ƙasan ba dan haka ya haye sama kai tsaye, Ɗakinsa ya murɗa ya shiga, Ya ajiye wayarsa akan gado sannan ya nufi toilet. Wanka ya yi ya shirya cikin kayan baccin sa na campanyn Gucci sai zuba ƙamshi yake, Ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin. Daƙinta ya murɗa ya shiga, Zaune ya hangeta can tsakiyar gado sai danna wayarta take a hankali, Ya ɗan saki murmushi sannan ya ƙarasa ciki. A gefen gadon ya zauna yana kallon ta, Ta ƙi yarda ta kalli inda yake fuskarta a ɗaure, Girgiza kansa ya yi sannan ya hau kan gadon ya zauna gefenta ya zare wayar daga hannun ta yana cewa

“wa ne ya taɓa min Nanata?”

Wani irin kallo ta yi masa sai kuma ta ɗauke kanta tana tura baki, Ya jawota jikinsa yana murmushi ya ce

“Am sorry kin ji, me nayi?”

“Ni ka sakeni wallahi.”

Ta yi maganar kamar zata fashe da kuka, Bai saurarenta ba ya sake matseta a jikinsa yana shafa dogon gashin kanta a hankali. Ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi muryarta a sanyaye ta ce

“Ni ka barni na ce, bana so!”

Bai tsaya saurarenta ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya yana sauke mata wasu zafafan kisses masu tsayawa a rai, Sam bata san sanda ta sakar masa jikinta ba, Ta fara ƙoƙarin taya shi. Cikin yan mintunan da basu shige ashirin ba ta fara ƙoƙarin kwace jikinta jin abin da yake shirin yi, Sai dai sam bai bata wannan damar ba, Cikin kuka ta ce

“Uncle ka sakeni, Ni bana so wallahi. Zan je gida kada Amma ta dinga nemana”

Ko amsa bata samu ya bata ba, Dan babu tabbacin ma yaji abin da ta ce ɗin, Haka ta ƙaraci koke-kokenta ta rabu dashi. Around 2:00am ta buɗe idanun ta, Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune tana ƙarewa dakin kallo, gaba ɗaya jikinta ciwo yake ga wani irin zazzaɓi mai ratsa ƙashi da take ji. Ta ɗan kalle shi ganin baccinsa yake hankali kwance, Yaye duvet ɗin jikinta ta yi ta sauka daga kan gadon, Ta zura slippers ɗin dake gaban gadon sannan ta nufi bayi a sanyaye. Bata jima ba ta dawo ta kwanta, Ta dinga juyi dan sam ta kasa baccin, Daga ƙarshe ta saka kuka tana rufe idanun ta. Shessheƙar kukanta ce ta tashe shi daga baccin, Ya tashi zaune ya kunna haske sosai yana kallon ta. Kuka take sosai idanunta a rufe, Ya jawota jikinsa da mamaki ya ce

“Nana mene ne?”

Bata bashi amsa ba sai ci gaba da kukanta da ta yi, Ya kai hannunsa wuyanta ya ji wani irin zafi. Sake kallon karamar fuskarta ya yi ya ce

“Wani abun ne ke miki ciwo?”

Girgiza masa kai ta yi a hankali ta ce

“Ni gida zan je, ka kai ni wajen Abbana”

Girgiza kansa ya yi dan ya san so take kawai ta daga masa hankali, Ya kwantar da muryarsa ya ce

“To zan kai ki, yanzu kwanta anan”

Ya ƙare maganar yana nuna mata gefen gadon, Maƙale kafaɗa ta yi tana sake sakin wani sabon kukan, Ya yi shiru yana kallon ta. Sun fi 20mins a haka kafin ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya fice daga ɗakin, Bai jima ba ya dawo hannunsa riƙe da injection, Ya ajiye kan drawer sannan ya hau kan gadon yana kallon ta ganin yanda ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka, Ya girgiza kansa kafin ya ce

“Nana”

Kallon sa ta yi sai kuma ta ci gaba da kukanta, Ya jawota jikinsa ya ɗorata kan cinyarsa a sanyaye ya ce

“Abba ki ke so ki gani?”

Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ce

“To me zai yi miki?”

Cikin shassheƙar kuka ta ce“Magani zai bani, Bayana ciwo yake min, kuma…”

“Kuma me?”

Ya ce yana janyo syringe ɗin, Kwaɓe fuska ta yi ta ce

“Kuma yunwa nake ji, Cikina ciwo yake min sosai.”

Jinjina kansa ya yi ya ce

“To haa bakin ki na ga”

Ya yi maganar yana kallon ta, Tura baki ta yi ta ce

“Ni bana so Allah..”

Murmushi kawai ya yi ya ce

“Babu abin da zan miki fa”.

Shiru ta yi tana kallon sa, Can kuma ta buɗe bakin nata. A hankali ya ɗora nasa bakin ta yi saurin rufe idanunta, Da dabara ya janye rigar jikinta ya sai ta syringe ɗin sannan ya ya yi mata allurar, Kuka ta saki ta janye bakinta, Ya yi saurin rungumeta yana murmushi.

“Uncle zafi.”

Ta faɗa cikin kuka, Shafa bayanta ya yi ya ce

“Sorry Yar albarka.”

Ci gaba ta yi da kukanta can kuma bacci ya ɗauketa, Girgiza kansa ya yi sannan ya fara ƙoƙarin kwantar da ita, Ta riƙe gefen rigarsa idanunta a rufe ta ce

“Uncle ka bar ni”

Sam bai gane abin da take nufi ba dan haka ya ƙara ƙoƙarin kwantar da ita, Ta saki kuka tana ƙanƙame shi.

“Na bar ki a jikina?”

Ya tambayeta a hankali, Gyaɗa masa kai ta yi har sannan idanunta a rufe, Ya girgiza kansa dan yasan halin rigimar ta, Ya mai da ta jikinsa ya kwantar da ita. Ya jingina da jikin gadon ya lumshe idanunsa, Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar asuba sannan ya kwantar da ita, Ya rufeta da duvet ya tashi ya shige toilet.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *