⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 48: Chapter 48

It’s been a while da rabuwar su da Zahra, Gaba ɗaya ya tattara lamarinta ya mayar gefe, Duk da tana yawan fado masa a rai amma sam baya bari tunanin ta ya yi tasiri cikin zuciyarsa, A yanzu babu wadda yake son ganin fara’arta sama da Nana, Indai yana gida to tana maƙale dashi, Baya taɓa barinta ta huta sai dai idan ya fita, Sannan ita ma take zuwa wajen Amma. Gaba ɗaya gidan ya dawo kamar yanda yake da, kowa sai harkokin sa yake, Siyama da Haule ne kawai har sannan basu saki ran su ba. A bangaren Zahra ma ta fawallawa Allah komai, tun bayan ciwon da ta yi wanda har sai da ta kwanta da Asibiti, Umma ta dinga yi mata addu’o’i a ruwa tana bata tana sha, A hankali ta fara rage damuwar da take. Har zama take hira tare da ƴan uwanta, Ban da Anty Khadijah wadda ko kallon in da take bata yi, ita ma ba shiga harkar ta take ba. Dan gaba ɗaya hankalinta na kan auren da zata yi da Malam Garba, Sai ta fara daina son sa, Sai rana ɗaya ta birkice ko bacci taƙi yi har sai an kira shi. Duk yanda Umma ke ƙiƙiyar auren nan haka ta haƙura ta rabu dasu aka gama magana.

****
Ranar wata Juma’a misalin ƙarfe 10:00 na safe ya shigo ɗakin, Sanye yake da dakkakiyar shadda Madam gezner Nude colour, Ɗinkin Jampa da Babbar riga sai zuba ƙamshi yake. Gaba daya ya zama kamar bashi ba, Ya ƙara girma da haiba kana ganinsa kaga babban mutum. Girgiza kansa ya yi ganin har sannan tana kwance tana bacci, Ya ƙarasa ciki ya taɓa ta a hankali ya ce

“Nana”

Kasancewar bata da nauyin bacci ya sanyata buɗe idanunta, Ta tashi zaune tana murza idanun ta. Ta zama wata babba da ita kamar ba Nana ba, Ta yi ƙiba ta ƙara haske har wani jaa fatar ta take.

“Ba zaki tashi haka nan ba?”

Abdusammad ya tambayeta yana murmushi, Langwaɓar da kai ta yi ta ce

“Uncle ina zaka je to?”

Murmushi ya yi dan daman ya san sai ta tambayeshi, Ya ja dogon hancinta kafin ya ce

“Zan je Abuja ne, amma an jima zan dawo kin ji”

Shiru ta yi kamar me tunani, Ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta ya ce

“I promise fa yau zan dawo”

Gyada kanta ta yi a sanyaye ta ce

“To nima zan je wajen Amma.”

Murmushi ya yi ya ce“Naji amma bana son yawo, Ki zauna waje ɗaya.”

To kawai ta ce, Ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet, Yana zaune har ta fito daga wankan. Ta buɗe press ɗinta ta zaro wata Shayla Abaya sea green ta saka, Kasancewar yadin yana da santsi ya sanya duk motsin da ta yi sai jikinta ya amsa. Ta ƙarasa gaban madubi ta fara shafa mai, Ji ta yi an rungumeta ta baya, Ta sauke numfashi tana kallon sa ta madubi ta ce

“Uncle…”

Bai ce komai ba ya fara ƙoƙarin juyo da ita, Saurin girgiza masa kai ta yi ta ce

“Uncle ba fita zaka yi ba?”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh ai sai an jima Flight ɗin zai tashi, Zo ki ji”

Shiru ta yi tana kallon sa, Ya ɗan haɗe fuska ya ce

“Baki ji ba?”

Sauke idanun ta kasa ta yi, kamar zata yi kuka ta ce

“Dan Allah uncle ka yi haƙuri, wallahi bani da lafiya..”

Ta ƙare maganar tana rau-rau da idanu, Shiru ya yi yana kallonta, Can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“Okay sai na dawo.”

“A dawo lafiya, Allah ya tsare.”

Ta ce a sanyaye. Da Amin ya amsa sannan ya fice daga ɗakin, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta, a yan kwanakin nan har tsoro lamarin sa yake bata, Ta ƙarasa shiryawa a gurguje ta bar gidan ita ma.

Tana zuwa ta samu Amma zaune a parlon ita da Haule, Ta zauna bayan ta gaida su,

“Amma me ku ka dafa?”

Harararta Amma ta yi sannan ta ce“Me zaki yi da abin da muka dafa?”

Langwaɓar da kai Nana ta yi ta ce“Yunwa nake ji Amma!”

“Ke baki yi girki ba?”

“Nayi bana ci”

Ta amsa tana ƙoƙarin kwanciya. Ɗauke kai Amma ta yi ta ce

“Ki je kitchen akwai abinci”

Ƙarasa kwanciya ta yi sannan ta ce“to bari na tashi”

Ita dai Amma bata sake bi ta kanta ba suka ci gaba da maganar su da Haule. Bayan an sakko daga sallar juma’a suka je apartment ɗin Hajiya Babba, Gaba ɗayan su suka haɗu, Amrah, Haule, Hamida, Maimoon, Sai kuma Nanar. Su duka da ciki Nana ce kawai babu, Duk wanda ta kalla a cikin su sai ta fara dariya. Maimoon da Amrah ne kawai ke biye mata, Su ko sauran sai kallo da ido. Wajejen ƙarfe 3:00 na rana Atta ta fito parlourn ta zauna suna hira duka. Koda aka kawo abinci Maimoon ce ta zubawa kowa, Nana ta dinga kallon abincin sai kuma ta ajiye, Tun safen babu abin da taci. Atta ta dinga kallon ta sai kuma ta ce

“Ke ba zaki ci abincin ba?”

“Na ƙoshi?”

Ta amsa tana ɗauke kai. Taɓe baki Atta ta yi ta ce“To kar ki ci ɗin, Shi mijin naki idan ya dawo sai na faɗa masa, Ni babu ruwana ba zai zo ya ce na bar ki da yunwa ba!”

Tura baki Nana ta yi, Hajiya Babba da ta zo parlourn sannan ta kalle su ta ce

“Mene ne?”

“Wai ba zata ci abinci ba, Salon mijinta ya zo yana yi mana rashin ɗa’a”

Da ɗan mamaki Hajiya Babba ta dinga kallon ta, Can kuma ta ce

“Nana ɗauki abinci ki ci”

Kasa cewa komai ta yi. Ta ɗauki plate ɗin jallof rice ɗin wadda ta sha kayan haɗi ta fara ci a hankali. Ko loma huɗu bata yi ba ta ajiye spoon ɗin tana yamutse fuska. Hajiya Babba da ke lura da ita tun ɗazu ta ce

“Mene ne?”

Girgiza kanta ta yi ta buɗe bakin ta da niyyar yin magana sai ta fara ga amai, Durƙushewa ta yi a wajen tana kwarara aman kamar zata amayar da kayan cikinta. Hajiya Babba ta taso ta riƙeta, Atta ki tsayawa ta yi a wajen tana kallon ta, Duk suka yi shiru. Sai da ta gama aman sannan Hajiya Babba ta sanya ta tashi ta rakata ciki, Mai aiki ta gyara wajen, Koda ta shiga ɗakin banɗaki ta wuce ta zare kayan jikinta ta yi wanka. Bayan ta fito ta zauna gefen gadon tana jiran Hajiya Babba ta dawo, Koda Hajiya Babba ta dawo samunta ta yi ta yi bacci a wajen, Ta girgiza kanta sannan ta ƙarasa ta rufeta da duvet ta ƙaro gudun ac sannan ta ajiye rigar ta juya ta fice daga ɗakin.

Koda Hajiya Babba ta dawo ƙasan zaune ta same su sun yi shiru suna sauraren Atta da ke faman magana, Tana ganinta ta ce“Khadijah me ya sami yarinyar ne?” Sai da Hajiya Babba ta zauna sannan ta ce“Ba komai Atta, Maybe ta ci abin da bata so ne, tana sama.” Shiru Atta ta yi kamar me nazari, Can kuma ta ce“To ni dai kada mijinta ya dawo ya ganta a kwance, Yanzu sai ya ce na bar ta da yunwa. Gwara ta zo ta faɗi abin da take so a dafa mata taci ko dan Allah?” Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“A’a Atta, kawai rabu da ita.” Taɓe baki Atta ta yi sannan ta mai da idanun ta kan su Maimoon ta ce

“Ina faɗa muku…”

****
Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha’i, Kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya shiga, Ya yi wanka sannan ya fito ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba. Koda ya shiga zaune ya same su a parlour suna hira, Ya ƙarasa ciki bayan ya yi sallama ƙasa-ƙasa ya zauna kan sofa, Murmushi Aliyu ya yi ya ce

“Buddy sai yanzu?”

Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya ce

“Na gaji wallahi, Da kwana zan yi to ina son gobe naje gurin can da wuri, Cause nan da 2 days nake son komawa.”

“A haba dai 2days? Bai yi wuri ba?”

Wani kallon sheƙeke Abdusammad ya yi masa sai kuma ya ɗauke kansa ya ce“Da yake baka san abubuwan da ke gabana ba. Ina Hajiya?”

Kafin ya yi magana ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da ƙaramin bowl, Ta ƙaraso parlourn ta zauna kan sofa sannan ta ce“Kiran me ka ke min?” Langwaɓar da kansa ya yi yana murmushi ya ce“Kawai na zo na gaishe ki ne, kuma sai naga ban gan ki ba.”

Jinjina kanta kawai ta yi sai kuma ta kalli Maimoon da ke gyangyaɗi ta ce

“Aliyu ka raka yarinyar nan gida ko ta shiga ciki ta kwanta.”

Sai a sannan Aliyun ya kalleta, Baccinta take a zaune hankali kwance, Ya girgiza kansa sannan ya ce

“To Hajiya.”

Daga haka ya tashi ya ƙarasa kan kujerar da take, Tashin ta ya yi sannan ya riƙe hannun ta, Ya yi musu sallama sannan ya fice daga parlon, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga ficewa. Ya rage sai Abdusammad kawai zaune, Hajiya Babba ta kalle shi ta ce

“Yaushe zaka tafi?”

“Nan da Sunday nake so”

Shiru ta yi tana tunani kafin ta ce“Har da Nana zaka tafi?”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh in sha Allah, Kin ga tana zuwa school ai.”

“To Allah ya kaimu lafiya”

Ta ce tana ɗaukan spoon ɗin da ke cikin naman, da Amin ya amsa sannan ya tashi ya ce“Sai da safe.”

“Ita yarinyar fa?”

Da ɗan mamaki ya ce“Tana nan ne?” Kallon hanyar sama ta yi ta ce“Tana can tana kwance” Toh kawai ya ce sannan ya nufi saman, Ɗakin Hajiya ya buɗe ya shiga, ya sameta kwance kan gadon ta rufe idanun ta amma ba bacci take ba. Kamar ba zai magana sai kuma ya ce

“Taso mu tafi”

Yanda ya yi maganar a shaƙe ya sanyata tashi zaune tana murza idanun ta. Ya juya ya fice daga ɗakin, Jiki a sanyaye Nana ta sauka daga kan gadon, Ta ɗauki mayafin rigar da Hajiya Babba ta bata ta ɗan yafa kanta sannan ta fara tafiya a hankali. A tsaye ta same shi a parlourn yana yi wa Hajiya Babba magana, Ta ƙaraso ta tsaya a gefe tana kallon su, Sai da suka gama sannan ya nufi waje, ta yiwa Hajiya Babba sallama sannan tabi bayansa. Koda ta fita samu ta yi har ya yi nisa abin sa, Ita dai ta ci gaba da tafiyarta a hankali har suka ƙarasa gidan. Ɗakinsa ya shige ita ma ta nufi nata ɗakin, Tana shiga ta faɗa toilet ta yi wanka sannan ta shirya cikin wata sleeping dress doguwar riga wadda ta tsaya mata iya gwuiwarta, Ta ɗaure gashinta da ribbon sannan ta fito daga ɗakin. Koda ta shiga ɗakin sa zaune ta same shi gefen gado yana danna system ɗinsa gefensa kuma wani ɗan madaidaicin tray ne mai ɗauki da kayan fruits, Ta ƙarasa ciki ta zauna gefen gadon ta yi shiru tana kallon sa. Har bayan mintuna goma babu wanda ya ce da wani ƙala a cikin su, Daga ƙarshe dai ta numfasa ta ce

“Uncle..”

“Uhm.”

Ya amsa ba tare da ya ɗago kansa ba, Sanyi jikin Nana ya yi, Dan indai taga ya yi mata haka ta san wani laifin ta yi, To amma ita bata san me ta yi masan ba. Dan haka ta yi ƙasa da muryarta ta ce

“Uncle ba zaka ci abinci ba?”

Girgiza kansa ya yi yana ci gaba da abin da yake, Ta dinga kallon sa amma bata sake cewa komai ba. After 5mins ya rufe system ɗin ya tashi hannunsa rike da plate ɗin ya fice daga dakin, Tana nan zaune har ya dawo ya nufi toilet, wanka ya sake yi sannan ya fito, Wani boxer kawai ya saka a jikinsa ya nufi kan gadon ya yi kwanciyarsa can tsakiyar gadon ba tare da ya kalli inda take ba. Tuni hawaye suka fara zubowa kan fuskarta, Ta jima zaune a wajen kafin ta tashi ta hau kan gadon ta ɗora kanta akan bayansa cikin shessheƙar kuka ta ce

“Uncle me nayi maka to?”

Bai yi magana ba, Duk da idanun sa a buɗe suke, Jin bai ce komai ba ya sanyata sake cewa

“Dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba wallahi! Ba zan kuma ba uncle.”

Har sannan bai ce komai ba, Ta leƙo fuskarsa taga idanunsa a rufe. Ta jima tana kallon kyakkyawar fuskarsa kafin ta tashi daga jkinsa, ta share hawayenta sannan sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin. Sai da yaji ƙarar rufe ƙofa sannan ya buɗe idanun sa, Ya tashi zaune yana kallon ƙofar. Can kuma ya koma ya yi kwanciyarsa.

Nana na shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da wani sabon kukan, Ita bata san laifin da ta yi masa ba, Gashi a rayuwarta ta tsani a shareta. Shi kuma sararsa kenan duk sanda ta yi masa wani laifi to ba zai kulata ba ranar, Gajiya ta yi da kukan bacci ya ɗauketa a wajen, Around 11pm ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta kwanta akan hannunta sai numfashi take sauketa a jere a jere alamun baccin baya yi mata daɗi. Ƙarasawa kan gadon ya yi ya gyara mata kwanciyar, Ta sauke ajiyar zuciya tana motsa bakinta, Ɗan murmushi ya yi sannan ya shafa dogon gashinta. Ya rufeta da duvet, Ya jima zaune yana kallon ta kafin ya kwanta shima, Ya jawota jikinsa ya rungumeta, Kamar jira take ta sake shigewa jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Ya kashe hasken ɗakin sannan ya lulluɓe su a tare nan da nan bacci ya ɗauke shi. Kiran sallar farko ya tashi ya bar ɗakin, Ya koma nasa ya ɗauro alwala sannan ya wuce masallaci, Koda ya dawo bai shiga daƙinta ba ya shige nasa ya yi kwanciyarsa. Sai ƙarfe 11:00 na safe sannan ta tashi daga bacci, Ta shiga banɗaki ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata atampa glitter ɗinkin A-shape, Ta ɗaura ɗankwalin akanta sannan ta fito parlour. Neman waje ta yi ta zauna duk da yunwar da take ji, Bata fi 5mins da zama ba ya shigo parlourn, Ganin yana shirin wucewa ya sanyata tashi tsaye, Ta ƙarasa ta tare gabansa tana kallon sa a sanyaye ta ce

“Dan Allah uncle…”

Kallon ta ya dinga yi fuska a ɗaure,Kafin ya ce“Matsa min hanya.” Madadin ta yi abin da ya ce sai kawai ya ga ta faɗa jikinsa tana kuka, Shiru ya yi yana saurarenta, Ta dinga rera kukanta kafin daga bisani ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce

“Dan Allah uncle ka yi hakuri, Wallahi ba zan sake ba kaji.”

Janye jikinsa ya fara ƙoƙarin yi, Ta sake ƙanƙameshi tana sakin wani sabon kukan, Ya ɗauke kansa saboda dariyar da ke neman kwace masa, Sai da ya yi clearing throat ɗinsa sannan ya kalleta fuska ɗaure ya ce

“Me ki ka min?”

Girgiza kanta ta yi cikin kuka ta ce

“Wallahi ban sani ba, Ban san me nayi maka ba”

“Ko?”

Ya tambayeta yana kafeta da idanu, Gyaɗa masa kai kawai ta yi. Ya janyeta daga jikinsa ya ce

“Idan ki ka tuna abin da ki ka yi min sai ki zo ki bani haƙuri”

Daga haka ya ratsa ta gefenta ya haye sama abin sa, Tsayawa ta yi a wajen tana nazarin maganar da ya faɗa, To me ta yi masa? Ta buga ƙafafunta a ƙasa kafin ta bi bayansa a hankali. Zaune ta same shi gefen gado yana danna wayarsa, Ta ƙarasa ciki ta zauna gefensa ta ce

“To ai ban san me nayi ba Uncle.”

Kallon ta ya yi kamar ba zai magana sai kuma ya ce“To tun da baki sani ba tashi ki ban waje”

Langwaɓar da kanta ta yi, Ta kwanta akan cinyarsa sannan ta ce“To ai na ce ka yi haƙuri kuma”

“Ba zan haƙura ba!”

Ya yi maganar yana ajiye wayar hannunsa, Shiru Nana ta yi tana kallon sa. Can kuma ta ce“To idan baka haƙura ba ya zan yi?”

Yanda ta yi maganar kamar zata fashe da kuka ya kusa bashi dariya, Ya tsuke fuska ya ce“Ina ruwana da yanda zaki yi?”

Tura baki ta yi, Ta sauka daga jikinsa ta kwanta a kan gadon ta rufe idanunta. Bai ce komai ba ya tashi ya fice daga ɗakin, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da wata leda, Ya ajiye a ƙasan gadon yana kallon ta ya ce

“Tashi ki dafa min abinci”

Jiki a sanyaye ta tashi ta fice daga ɗakin, Ya girgiza kansa sannan ya nemi waje ya zauna. Sai da ta ɗan yi jim a wajen tana ƙarewa kitchen ɗin kallo kafin ta ɗauko wuƙa. Doya ta ɗauka ta feraye sannan ta wanke ta zuba a tukunya ta ɗora akan wuta, Ta nemi kujera ta zauna tana jiranta, Bayan ta dahu ta kwashe sannan ta fasa kwai ta saka albasa da kayan ƙamshi, Ta saka maggi sannan ta ɗora mai akan kasko ta fara soyawa. Bayan ta gama ta dauko wani flask mai kyau ta zuba a ciki, Sannan ta ɗora farfesun kayan ciki a wata tukunyar, Ta gama shima ta zuba a flask sannan ta ɗiba ta ɗora akan tray ta nufi saman, A parlour ta ajiye ta koma ta dauko tea flask da cups ta dawo ta ajiye. Sannan ta shiga ɗakin, Zaune ta same shi ya sauya kaya zuwa wasu English wears riga armless da cargon 3-quater gashin kansa ya zubo gefen kafaɗarsa gwanin ban sha’awa.

“Uncle na gama”

Ta ce tana kallon sa, Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ajiye wayar hannunsa ya ce

“Okay I’m coming”

To kawai ta ce sannan ta juya ta fice daga ɗakin, Zama ta yi kan kujera ta kunna tv ta fara kallon wata drama da ake haskawa a Netflix, After some minutes ya fito hannunsa riƙe da ledar ɗazu, Ya nemi waje a ƙasa ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa. Kafin ya yi magana ta taso ta tsuguna a gabansa, Plate ta ɗauka ta zuba masa abincin sannan ta haɗa masa tea ɗin ta miƙa masa. Ta koma ta zauna tana ci gaba da kallon ta,

“Kefa?”

Taji ya tambaya, Kallon sa ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“Na ƙoshi”

Wani banzan kallo ya watsa mata kafin ya ce

“Kin taso anan ko sai na ɓata miki rai?”

Tura baki ta yi sannan ta tashi, Ta koma ƙasa kusa dashi ta zauna. Wani empty cup ɗin ya dauka ya zuba mata tea ɗin, Ya miƙa mata sannan ya saka plate ɗin a tsakiyar su ya ce

“Ohya eat!”

Kamar zata yi kuka haka ta ɗauki shayin ta kai baki, Ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye, Haɗe rai taga ya sake yi ya ce

“Ba zaki ci ba?”

Girgiza kanta ta yi sannan ta saka hannu ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki, Dakyar ta tauna tana yamutse fuska. Ya gyara zamansa yana kallon ta har sannan, Ganin ta jingina da jikin kujerar ya sanya ya ce

“Nana yaushe na fara wasa dake?”

Kamar zata yi kuka ta ce“wallahi uncle na ƙoshi”

“Idan na sake miki magana sai kin gwammace baki sanni ba Nana!”

Ganin how serious he’s ya sanya ta sake ɗaukan ɗaya ta kai baki,Dakyar ta dinga taunawa, Tana dira cikinta ta tashi da gudu ta bar wajen, Da idanu ya bita sai kuma ya miƙe bayan ya ajiye cup ɗin hannunsa, Bayanta ya bi, Ya sameta durƙushe cikin banɗaki sai kwarara amai take. Da mamaki ya ce

“Subhanallahi”

Ya ɗagota yana kallonta ya ce

“Mene ne?”

Bata iya cewa komai ba sai numfashi take saukewa, Ya girgiza kansa sannan ya janyeta daga wajen. Sai da ta wanke bakinta sannan ya sanya ta fito, Ya gyara wajen ya biyo bayanta. Zaune ya sameta kan sofa sai numfarfashi take, Ya ƙarasa ya zauna gefenta sannan ya jawota jikinsa, Sosai yaji zafi a jikinta, Ya ɗago kanta ya ce

“Baki da lafiya ne?”

Girgiza kanta ta yi kawai, Ya rungumeta ya ce

“Sannu to”

Kwace jikinta ta yi ta tashi da gudu ta koma toilet ɗin, wani aman ta sake yi, Ya dinga kallon ta ganin yanda take aman kamar zata amayar da kayan cikinta, Sai da ta gama ta wanke bakinta sannan ya kalleta ya ce

“Zo nan”

Jiki a sanyaye ta ƙarasa gabansa, Ya ɗauketa kamar ƴar baby suka fita daga toilet ɗin, Ɗakinsa ya kai ta ya kwantar da ita sannan ya zauna kusa da ita ya kai hannunsa goshinta ya ce

“Sannu, Bari na shirya mu je asibiti”

Ita dai bata ce komai ba sai lumshe idanunta da ta yi, Ya tashi ya fice daga ɗakin. Koda ya dawo samu ya yi ta yi bacci, Dan haka ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa, Shi kaɗai ya dinga murmushi yana shafa kanta, Can kuma ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga gidan.

Yinin ranar a kwance ta yi sa, Sai wajen ƙarfe 6:30 na yamma sannan ta tashi ta yi wanka, Ta shirya cikin wata doguwar riga brown colour, Ta saka ɗan ƙaramin hijabi sannan ta sakko ƙasa, Yunwa sosai take ji, kuma bata jin zata iya cin abin da ta dafa, dan haka kawai ta tafi apartment ɗin Hajiya Babba. Koda ta shiga zaune ta samu Atta da Mama suna magana, Sai Hajiya Babba da ke zaune tana karanta azkar, Sallama Nana ta yi sannan ta gaishe su, Suka amsa a tare, Kallon ta Hajiya Babba ta yi ganin ta tsaya ta ce

“Nana lafiya dai?”

Gyaɗa kanta ta yi a hankali ta ce“Ba komai Hajiya.”

“Nana zo nan”

Mama ta yi maganar idanunta na kanta, Ƙarasawa ta yi ta zauna gefenta, Mama ta taɓa wuyanta sannan ta ce

“Baki da lafiya ne? Me ke damun ki?”

Ta jera mata tambayoyin, Sunkuyar da kai Nana ta yi ta ce“Zazzabi nake Mama”

“Shi Abdusammad ɗin bai kai ki asibiti ba?”

Cewar Hajiya Babba tana kallon su, Gyaɗa mata kai Nana ta yi tana hawaye. Hajiya Babba ta ɗauki wayarta da ke gefenta ta yi dialing numbern sa, Ringing ɗaya ya ɗauka murya babu walwala ta ce

“Abdusammad kana ina?”

Daga can ɓangaren Abdusammad da ke zaune parlon Aliyu ya ce

“Ina gidan Aliyu Mama”

“Ka zo ina neman ka yanzu”

Toh kawai ya ce sannan ta kashe wayar, Ta mayar da idanun ta kan Nana wadda ta sunkuyar da kanta tana hawaye ta ce

“Kin ci abinci?”

Girgiza kanta ta yi, Hajiya Babba ta ce

“To me zaki ci?”

“Ni bana cin komai”

Ta bata amsa cikin shessheƙar kuka. Haɗe rai Hajiya Babba ta yi, Kafin ta yi magana Atta ta ce

“Mene ne haka ne ke faruwa? Me ya sameta? Ke zo nan”

Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ƙarasa gaban Atta, ta zauna akan kujerar, Ƙare mata kallo Atta ta yi sannan ta shiga jinjina kanta ta ce

“Eh lallai! Arɗo ya yi ƙokari, Ji yarinya ta ɗashe ta yi fari, Duk jiki ya circiko, Ba dai ciki ya mata ba? Wannan ƴar taliliyar ƴar”

Babu wanda ya ce komai a cikin su, Dan haka Atta ta sake riƙe Nana ta ce“Ke kina jin tashin zuciya?”

Ita dai Nana bata amsa ba, Ba kuma ta daina hawayenta ba. After some minutes aka buɗe ƙofar parlourn, Shigowa ya yi shi da Aliyu, Ya gaishesu idanunsa na kan Nana ganin sai shessheƙar kuka ta ke. Hajiya Babba ce ta kalle shi fuska a ɗaure ta ce

“Abdusammad mene haka?”

Da rashin fahimta ya ce

“Wani abun ya faru Hajiya?”

Kallon Nana ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce

“Idanun ka basu gane maka abin da ke damunta ba? Ko baka sani ba?”

Sunkuyar da kansa ya yi, Duk da ba wai kunyar Hajiya Babban yake ba amma sai da yaji jikinsa ya yi sanyi. Ganin ya yi shiru ya sanya ta sake cewa

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *