Chapter 51: Chapter 51
Yinin ranar Nana a ɗaki ta yi shi ko parlourn ƙasa bata sakko ba, Shi ma bai sake shiga harkarta ba har dare. Around 9pm ya shigo ɗakin cikin shigarsa ta ƙananun kaya hannunsa na dama riƙe da wayarsa yana dannawa, Tana kwance kan gado ta yi nisa cikin tunanin da take. Ya tsaya gefen gadon ya zura wayar a aljihu yana kallon ta ya ce
“Ki tashi ki ci abinci”
Ko daga kanta bata yi ba ballantana ya saka ran zata kula shi, Ya ɗan yi jim kafin ya sake cewa
“Nana baki ji bane? Tashi nace!”
A fusace ta tashi zaune tana kallon sa tana huci ta ce
“To ba zan ci ba ɗin, Ina ruwanka dani ko dole sai na…”
Saukar marin da taji ya sanyata haɗiye ragowar maganar tata, Ta sanya hannunta na hagu ta dafe kuncin daya mara tana kallon sa, Kuka take son yi amma ta kasa. Fuskarsa a haɗe babu alamar wasa ya ce
“Duk ranar da bakin ki ya sake kuskuren ɗaga min murya sai kin gwammace baki sanni ba!”
Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama. Sai da ta ga ya rufe kofar sannan ta kece da wani kukan baƙin ciki, Ta koma ta kwanta tana kuka kamar ranta zai fita. Abincin da bata ci ba kenan har bacci ɓarawo ya saceta, Cikin dare ta farka saboda ciwon da cikinta ke mata, Ta tashi zaune tana dafe da cikin nata. Ta jima zaune a wajen tana kuka kafin ta tashi ta shige toilet, Fitsari kawai ta yi ta dawo ta kwanta, After 5mins ta tashi da gudu ta koma toilet ɗin, Amai ta yi ta tsaya a wajen tana sauke numfashi. Sai da ta ɗan ji sauƙin cikin sannan ta fito daga toilet ɗin ta kwanta akan gadon, Ta jima kafin wani baccin ɗauketa. Da asuba ya shigo ɗakin yana sanye da jallabiya mai taushi hannunsa riƙe da counter da alama masallaci zai je, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta cure jikinta waje guda, Daga jin yanayin yanda take numfashi ka san ba daɗi kwanciyar take ji ba. Ya ƙarasa ciki ya gyara mata kwanciyar sannan ya ja duvet ya rufeta, Ya ɗan yi jim yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta kwaɓe ta kamar zata fashe da kuka, Girgiza kansa ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Sai ƙarfe 8:00 na safe ta farka, Tana tashi ta shige toilet ta yi wanka, Ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando marasa nauyi, Ta koma gefen gado ta zauna ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru jiya. Kenan har yanzu yana sonta? Har yanzu bai rabu da ita ba? Har yake iya yi mata tsawa akanta. Shar haka taji hawaye na zubowa kan farar fuskarta, Babu abin da ya fado mata a rai sai Junaid, Allah sarki, Duk da ya aikata mata ba daidai ba amma ta san da shi ne ba zai taɓa yi mata haka ba. Domin shi ne wanda ya nuna yana sonta, Wannan kuwa kowa ya san auren alfarma ne a tsakanin su, Da wannan tunanin ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana fashewa da wani sabon kukan. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta tashi ta shige bayi, wanke Fuskarta ta yi ta fito ta zura hijabi kan kayan jikinta sannan ta ɗauki wayarta da jakar makarantar ta ta fice daga ɗakin.
Bata same shi ba ko a ƙasa duk da kasancewar ranar Sunday ne, Kawai ta samu driver ta ce ya kaita schl ɗin. Koda ya sauketa shiga ta yi, Babu wasu mutane sosai domin ba kowa ke da lecture Sunday ba, Suma wani lecturer ne ya kira su. Dan haka kai tsaye department ɗinsu ta nufa, Tana zuwa ta samu har an fara lecturen. Haka dai ta nemi waje ɗaya ta zauna tana saurara duk da ba fahimta take ba, Bayan sun gama tana shirin fitowa taga Amani. Kallon ta kawai ta yi sai kuma ta ɗan yi murmushi ta ce
“Ina Mu’ash?”
“Bata zo ba”
Amani ta bata amsa kai tsaye, Jinjina kai Nana ta yi sai kuma ta ɗauki jakarta tana ƙoƙarin ratayawa ta ce
“Zan tafi sai jibi.”
“Nana me ya faru ne? Naga duk kin yi wani iri, Me ya samu fuskar ki?”
Sai a sannan Nana ta kai hannunta kan fuskarta saitin daya mareta.
“Wa ya dake ki?”
Amani ta sake mata tambayar, Girgiza kanta ta yi hawaye na taruwa cikin idanun ta ta ce
“Babu kowa.”
Ɗan murmushi Amani ta yi sai kawai taja hannunta suka fice daga class ɗin. Can wajen wata coconut tree ta kai ta suka tsaya, Ta ɗan yi murmushi ta ce
“Nana idan baki faɗa mana abin da ya dame ki ba wa zaki faɗawa? Kin san dai baki da kowa a ƙasar nan idan ba mu ba ko? To akan me zaki ɓoye mana abin da ya dame ki”
Ai kamar jira Nana take ta fashe da kuka, Ta fara murza idanunta da hannunta na hagu, Amani ta ɗan yi shiru tana kallon ta can kuma ta riƙe hannunta ta ce
“Ki yi haƙuri ki daina kuka, Ki faɗa min abin da aka yi miki”
“Uncle ya tsaneni, Baya sona. Uncle bani yake so ba matarsa yake so, Nima bana son shi, Tafiya gidanmu zan yi, Ba zan koma gidan sa ba. Ƙasar mu zan tafi, Sai dai ya sakeni, Ba zan zauna dashi ba wallahi!”
Amani da bata gama fahimtar abin da ya faru ba ta ce
“Wai me ya yi miki? Me ya sake haɗa ki dashi? Shi ne ya mareki?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi cikin kuka ta ce
“Saboda na zagi tsohuwar matarsa shi ne ya ke min bala’i, Kuma ya mareni, ai baya sona. Ita yake so har yanzu, Nima ai gara na bar gidan kawai”
Girgiza kai Amani ta yi ta ce
“Akan me zaki bar gidan Nana? Gidan mijin ki ai, Kin san me ya sa yake miki haka?”
Shiru Nana ta yi lokaci ɗaya ta shiga girgiza kanta. Amani ta gyara tsaiwarta sannan ta ce
“Saboda wannan cikin ne! Shi ne abin da ya saka yake nuna baya sonki. Mazan yanzu haka suke, Zasu nuna suna sonki, Su dinga taraiyarki, Su saka ki farin ciki da nishaɗi, Amma daga sanda ya fahimci akwai ciki a jikin ki sai ya watsar. Sai ya daina ɗaukan al’amuran ki da girma, Ya mayar da ke kamar wata mara amfani, Sai ki yini bai shiga harkar ki ba. Wanda da a sanda ki ke lafiya ne yake morarki baya miki haka”
Shiru Nana ta yi tana nazarin kalaman Amani.
Amani ta sake cewa “Ke yanzu da haka yake miki? Sanda ya aure ki haka yake miki? Ko farkon zuwan ki ƙasar nan haka ya dinga miki?”
Girgiza kai Nana ta yi, Amani ta ɗora da faɗin
“To me ya sa yanzu ya sauya miki? Me yasa ya daina kulawa da ke? Me yasa yake iya dukan ki? Amsar guda ɗaya ce, Saboda yanda yana ganin ciki a jikin ki. Yana ganin kin gama masa amfani idan bana haihuwa ba, Wannan shi ne ya sanya sanda ya aure ki ya dinga yiwa Zahra haka ita ma. Ki nutsu ki fahimci komai Nana”
Kusan mutuwar tsaye Nana ta yi a wajen saboda mamaki, Tunanin bai taɓa kawo wa nan ba, Sai yanzu da Amani ke faɗa ta fara tabbatar da hakan. Da gaske sanda bata da ciki ba haka yake mata, Daga samun cikinta zuwa yanzu basa kwana biyu basu yi faɗa ba, Kusan kullum sai ya mata tsawa. Kenan wannan shi ne dalili? Amani ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar faɗin
“Kin gane abin da nake nufi?”
Nana ta gyada mata kai hawaye na zubowa kan fuskarta. Jinjina kai Amani ta yi kafin ta ce
“Yanzu shawara ta rage naki, Idan har kina son zama cikin gidanki hankali kwance cike da soyyayar mijin ki to sai dai ki rabu da wannan cikin da ke jikin ki!”
Shiru Nana ta yi, Ta rasa wace makama zata kama, Ta yarda ta zubar da cikin ko kuwa ta bar shi? Idan ta bar shi haka zata ci gaba da zama gidan Uncle cikin baƙin ciki daga nan har ta haihu? Ta girgiza kanta a fili ta ce
“To ya zan yi na zubar?”
Murmushi Amani ta yi ta ce“Yauwa kin zaɓi abin da zai fissheki. Kina ji yanzu ki zo muje na sauke ki sai mu biya da pharmacy ɗin da muke siyan magani na karɓa miki tablet ɗin.”
Jiki a sanyaye Nana ta ce “To kuma zai zube ɗin?”
Wani kallon sheƙeke Amani ta yi mata sai kuma ta ce“a’a ƙarya zan miki!”
Daga haka ta yi gaba abin ta, Sauke numfashi Nana ta yi sannan tabi bayanta. Kamar yanda Amani ta faɗa haka ce ta faru, Ta barta a motar ta tsallaka ɗaya side ɗin inda babban Medcare pharmacy ɗin yake. Ta shiga bata jima ba ta dawo hannun ta riƙe da leda, Akan cinyar Nana ta ajiye ledar sannan ta yiwa motar key suka ci gaba da tafiya. Nana ta dinga kallon ledar ba tare da ta yi gigin taɓawa ba, A bakin mansion ɗin nasu ta yi parking sannan ta juyo tana kallon ta ta ce
“To gashi nan, Guda ɗaya kawai zaki sha, Kada ki sha sama da haka. Sannan ki bari sai baya nan, Kamar kin san ya kusa dawowa ko kuma zai fita sai ki sha, Ki yi komai a nutse, kar ki bari ya gani”
Ban da gyada kai babu abin da Nana ke yi, Ta sauke numfashi kafin a sanyaye ta ce
“To babu matsala dai ko? Idan na sha kuma wani abun ya sameni fa?”
Ɗan tsaki Amani ta yi ta ce
“Ke wai yaushe zaki fara fahimtar abubuwa ne? Cewa nayi fa ki sha idan ya kusa dawowa, Ko kuma ya kusa fita, Yanda ba zai yi nisa ba. Sai ki ce ko faɗuwa ki ka yi ko wani abun, Kada ki bar ya gani! Kada ki kuskura ki bari ya gani”
To kawai ta ce sannan ta ɗauki ledar ta mata sallama ta buɗe motar ta fita. Amani ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kanta, Ita har cikin zuciyarta tausayi take bata. Sai da taga ta shiga gidan sannan taja motar ta ta yi gaba, Nana kuwa a compound ɗin farko ta tsaya ta zare maganin daga ledar ta yar a dustbin sannan ta saka maganin cikin ɗan ƙaramin aljihun jakarta sannan ta ci gaba da tafiya. A sanyaye ta buɗe ƙofar parlourn ta shiga, Zaune ta hange shi yana magana a system da alama vidcall yake yi, Ta ƙarasa ciki ba tare da ta ce komai ba. Tsayawa ta yi a bayansa dan ganin da wanda yake wayar, Sai dai fuskar wadda ta gani ya sanyata sunkuyar da kanta. Murmushi Zahra ta yi ta daga mata hannu ta ce
“Hi Nana!”
Sai a sannan Abdusammad ya juya yana kallon ta dan sam bai lura da shigowar tata ba, Bata ce komai ba ta juya ta nufi hanyar sama a sanyaye. Sai da ta bar wajen sannan Zahra ta ce
“Dan Allah doctor ka tayani bata hakuri, Ta daina jin haushina”
“Just leave her”
Ya ce a takaice, Shiru Zahra ta yi duk sai taji bata ji daɗi ba, Ita yanzu bata da niyyar ganin wani abu mara kyau ya samu Nana dan haka ta numfasa ta ce
“Sai an jima.”
“Mu jima da yawa”
Ya ce yana ƙoƙarin rufe system ɗin. Tashi ya yi ya nufi saman shima, Kai tsaye daƙinta ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, Tana zaune gefen gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take. Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ƙarasa ciki, A gefen gadon ya zauna yana kallon ta still bai ce komai ba, Can dai ya numfasa ya ce
“Nana!”
Bata amsa ba haka kuma bata ɗago kanta ba, Ko kaɗan bata son jin muryarsa, Baƙin ciki isarta yake, Ji take kamar ta mutu ta huta da zama dashi. Ya jawo hannunta a sanyaye ya ce
“Me akayi miki kuma?”
Ya yi maganar yana ƙoƙarin matso da ita jikinsa, Janye jikinta ta yi ta sauka daga kan gadon ta shige toilet ba tare da ta yarda sun haɗa ido dashi ba, Ya yi shiru yana kallon ƙofar bayin, Can kuma ya tashi ya fice kawai.
****
Yola, Nigeria.
Zahra ta dinga kallon Umma jiki a sanyaye, Can dai ta ce
“Umma Ya Bashir kuma?”
Gyaɗa mata kai Umma ta yi kafin ta ce
“Eh Zahra’u, Bashir, Yana son ki ya ce. Kuma zai aure ki, Dan haka kawai ki bashi dama, Da zarar iddar ki ta ƙare sai a ɗaura muku aure.”
Shiru ta yi tana sauraren Ummar, Ita gaba ɗaya sai taji jikinta ya mata sanyi, Bashir ɗin da bata yi tunani ba shi ne zai zama mijinta na biyu, Shi ɗin ɗan yayar Umma ne, A Kaduna suke, Yana aiki a Saudiyya. Tun tana ƴar ƙarama ya taɓa cewa yana sonta, amma bayan tafiyarsa sai ta gamu da Abdusammad ta kuma ce shi take so, Har zuwa wannan lokacin bai yi aure ba, Gashi ƙaddara na neman sake hada su a matsayin mata da miji.
“Zahra’u”
Umma ta kira sunanta a nutse, Ɗaga kanta ta yi ta kalleta a sanyaye ta ce
“Na’am Umma…”
“Kin yarda? Bana son nayi miki abin da ba zai miki daɗi ba, Idan kin ce bakya son sa shikenan domin a yanzu kina da damar zaɓar mijin da ki ke so. Amma ki sani ba zan ji daɗi ba idan ki zama kamar yanda Khadijah ta zama, Kin ga dai yanzu halin data saka kanta”
Zahra da hawaye ya fara sakkowa kan fuskarta ta ce
“Ba zan sake ƙin biyayya ba Umma. Na yarda zan aure shi, Na yarda wallahi”
Ajiyar zuciya Umma ta sauke dan daman ta san halin Zahra ba zata bata matsala ba, Ta dafata fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce
“Allah ya yi miki albarka, In sha Allah Alkhairi zaki gani a rayuwar ki Zahra’u, In sha Allah ba zaki sake samun matsala ba. Ki dinga yawan addu’a kin ji, Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa.”
Jiki a sanyaye Zahra ta ce
“Amin Umma, Na gode sosai.”
Murmushi kawai ta yi, Ta miƙe tana ƙoƙarin barin ɗakin ta tuna, dan haka ta tsaya ta ce
“Na manta, Ki samu ki je ki duba Khadijah, Ina son ki manta da komai dan Allah.”
Ba zata iya yiwa Umma musu ba, Duk da daman ita bata riƙe ta ba, Ta kalleta ta ce
“To Umma zan je in sha Allahu.”
“Allah ya yarda”
Cewar Umma, Sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana jin wani iri a ranta, Kaddara ta rabata da mijinta, Ta kuma rabata da ƴarta, sannan take shirin haɗata da wani sabon mutumin a matsayin abokin rayuwa. Tabbas Allah abun tsoro ne, Komai nasa akwai hikima da dalilin faruwa.
Bayan sallar la’asar ta shirya suka je gidan Anty Khadijah ita da Safeena da Amal. Sanda suka je tana zaune a ɗaki ta zuba uban tagumi, Gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Ta yi wata irin rama ta tashin hankali, Babu abin da ka ke gani a jikinta sai ƙashi da idanu, Ga wata irin yamushewa da fatarta ta yi. Sai kace wadda take fama da cutar ƙanjamau, Tun ranar data faɗi a soro bata sake takawa ba, Gaba ɗaya kafafun sun nannaɗe sannan Malam Garba ya hana akai ta asibiti ballantana a san abin da ke damunta. Sai ƙarewa take a banza, Babu ci babu sha, Sai kuka kawai, Babu abin da ke ɓata mata rai sama da abin da Kaddu ta yi mata, Ashe ƙawar da take ɗauka fiye da kowa nata ita ce take cutar da ita, Tabbas duk wanda ya bar Allah sai Allah ya bar shi, Kuma duk harkar da babu Allah kana zaune zata wargatse aji kunya. Zahra da ke zaune gefen gado ta kalleta ta ce
“Sannu Anty, Allah ya baki lafiya”
Anty Khadijah bata iya cewa komai ba sai hawaye dake zubowa kan yamusasshen fuskarta, Safeena da ke hawaye ita ma ta ce
“Kin gani ko Anty? Abin da nake ta faɗa miki kenan amma ki ka ƙi ji, Yanzu kalli halin da ki ke ciki. Kin zama abar tausayi, Kin raba mata da mijinta, Kin yi silar mutuwar ƴarta, Ina zaki je da wannan haƙƙin?”
Girgiza kai Zahra ta yi muryarta a sanyaye ta ce
“Ki bar cewa haka Safeena, Ni wallahi na yafe mata, Na yafe har abada. Duk da naji zafinta a da amma yanzu ya huce, Na gane kuma ƙaddara ce ta sanya hakan ta faru, Dan haka ni na yafe kome ta yi min, Ina mata fatan Allah ya yafe mata.”
Wani irin raunataccen kuka ne ya kwacewa Anty Khadijah, Ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana rera shi, Tabbas ta yi dana sani, Ta ji kunya, Ta yi nadama. Nadamar da baza ta amfanar da ita komai ba, Domin komai ya ƙare mata. Tashi Zahra ta yi ta koma gefenta ta ɗagota ta fara share hawayenta ta ce
“Ki yi haƙuri Anty, Dan Allah ki daina kuka kada wata cutar ta same ki bayan wadda ki ke ciki”
Gyaɗa mata kai Anty Khadijah ta yi sai a sannan ta ce
“Na gode Zahra.”
Zahra ta yi shiru hawaye na zubowa kan fuskarta, Ɗan uwa rabin jiki, Sai taji ina ma ita ce ciwon ya sameta ba Anty Khadijahn ba. Suna nan zaune har kusan magriba sannan suka tafi gida, Ko awa biyu basu yi da zuwa gida ba aka kira wayar Umma, Bayan ta ɗaga matar gidan ta sanar da ita halin da Anty Khadijahn ke ciki, Umma da ta gama ruɗewa ta faɗawa su Zahra haka suka sake ɗungumar jiki suka koma gidan, Koda suka je basu sameta ba, Dan an yi asibiti da ita. Dan haka suka wuce can, A asibitin suke samun labarin irin dukan da Malam Garba ya yi mata bayan tafiyar su Zahra, Ya kuma ce ya saketa, Akan ta tambaye shi gwala-gwalanta da ke hannun sa. Umma ta jingina da jikin bango hawaye na zubowa kan fuskarta. Su kansu su Zahra kuka suke, Duk da basu san halin da take ciki ba, Suka bugawa Siyama waya suka sanar da ita. Kasancewar gobe zata gama takaba yasa ta ce goben tana hanya zata zo, Suna nan zaune har kusan ƙarfe 10 na dare kafin likita ya fito, Da sauri suka ƙarasa inda yake, Zahra ce ta yi ƙarfin halin cewa
“Doctor ya jikin nata?”
“Ki sameni a office!”
Shi ne kawai abin da ya ce sannan ya yi gaba, Zahra ta sauke numfashi ta bi bayansa. Koda ta shiga office ɗin a tsaye ta same shi, Ya yi alama data zauna ta zauna sannan shi ma ya zauna, Zare glasses ɗin idanunsa ya yi yana kallon ta ya ce
“Ke ƴar uwarta ce?”
Gyaɗa masa kai Zahra ta yi ta ce
“Eh Yayata ce uwar mu ɗaya uban mu ɗaya”
Shiru likitan ya yi can kuma ya ce“Me yasa baku kawota asibiti ba tun wuri? Sannan wa take aure? Ina yake?”
Sosai gaban Zahra ya fadi, Ta ce“Tana gidan mijinta ne kuma malami ne baya bari ta fita”
Da mamaki ya ce
“Malamin ya yi mata wannan illar? I’m sorry to say ya gaba lalata mata jiki, Na ɗaya ba zata sake haihuwa ba, Na biyu tana da cutar Hiv. Na uku ƙafafunta ba lallai bane su sake takawa, Sakamakon faɗuwar da ta yi!”
Zahra bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba, HIV? Kenan ita ta shafawa Siyama? Siyama kuma ta shafawa Safwan? Innalil lahi wa ina ilayhi raji’una. Shi ne abin da kawai take iya maimaitawa cikin ranta, A fili kuwa ban da kuka babu abin da take. Tashi likitan ya yi ya fice daga ɗakin baki ɗaya.
****
Washegari da safe Nana na tashi ta yi wanka, Ta fito parlour, Kitchen ta shiga ta haɗa breakfast sannan ta fito ta zauna anan kan sofa, Bayan ta gama ci ta tashi ta koma ɗakin da niyyar ɗaukan maganin da Amani ta bata, Dan ta san yanzu duk inda yake to ya gama shirin fita. Sai dai me? Duk irin duban da ta yi wa jakar bata ga maganin ba, Babu shi babu dalilinsa. Sai da ta zazzage gaba ɗaya takarcen da ke ciki duk da ta san a pocket ɗin jakar ta ajiye, amma aka ce idan raƙumin ka ya ɓata to har kafar allura ga duba. Tana cikin dube-dube aka buɗe ƙofar ɗakin, A ɗan zabure ta juya tana kallon sa, Sanye yake da suit black colour da alama fita zai yi. Hannayensa zube cikin aljihun trousern dake jikinsa, Kallon kallo suka dinga yi, Can dai ta ɗauke nata idanun tana ƙoƙarin kwashe kayan data zubar
“What are you looking for Nana?”
Ta tsinkayi muryarsa a sama, Girgiza kanta ta yi a ɗan rarrabe ta ce
“Babb…Nothing”
“Are you sure?”
Ya sake tambayarta. Juyawa ta yi ta kalle shi, Ta ga ya sakar mata murmushi. Ya zaro tablet ɗin daga hannunsa ya daga shi yana faɗin
“Ko dai wannan ki ke nema? Are you looking for ur abortion pill ko?”
Bata san sanda ta tashi tsaye ba a mugun firgice, Ta fara girgiza kanta da hannayenta ganin yana murmushi har sannan. Ja da baya ta fara yi hankali tashe ta ce
“Wallahi wallahi uncle ban sha ba, Na rantse ban sha ba, Sai da nace bana so. Wallahi ba zan ƙara ba!”
Bai ce komai ba ya mai da maganin aljihun sa ya juya ya fice daga ɗakin. Nana ta yi zaman daɓaro a gefen gadon tana jin wani irin tashin hankali. Yaushe ya gani? Me yasa bai yi mata duka ba? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru wajen azahar. Ta tashi ta shige toilet ta wanke fuskarta sannan ta ɗauro alwala, Bayan ta fito ta gabatar da sallah sannan ta zauna a wajen, Har dare bata samu sukuni ba. Shirun da ya yi mata ta matuƙar ɗaga mata hankali, Haka ta koma balcony ta tsaya tana jiran dawowar sa, Bai dawo gidan ba har wajen ƙarfe 12:00 ta gaji da jiransa ta kwanta a wajen. Ba ita ta farka ba sai washegari wajen ƙarfe 9:00 na safe. Ta tashi ta shige toilet ta yi wanka sannan ta ɗauro alwala, Sallah ta yi sannan ta fice daga ɗakin ta nufi nasa, amma koda ta murɗa sai taji a rufe take. Ta kasa knocking haka kuma ta kasa barin wajen, Tana nan tsaye har bayan mintuna biyar taga wata maid ta hauro saman, Ta kalleta ta ce
“Excuse me pls.”
Tsayawa matar ta yi cike da girmamawa ta gaisheta, Nana ta amsa a sanyaye sannan ta ce
“Ina doctor yake?”
“He already gone”



