Chapter 4: Chapter 4
Murmushi tayi, ta miƙe ta dauƙo gyalenta ta yafa ta saka flat shoes ɗin tana kallon Mami da ke ta binta da ido duk inda tayi.
“Ki same ni a falo,” Mami ta faɗa tana juyawa ta fita a ɗakin, wayarta da ta ajiye gaban mirror da zata saka kayan ta ɗauka tayi selfie mai kyau.
Sadiq ta tura ma da taga yana online with the caption
“feeling cute, feeling home, guess whos blending in already”
A take ya mata reply, murmushi tayi tana kashe datan ta bayan ta karanta reply ɗin nasa
“u didn’t just blend in…. U stole the whole show,.. u look stunning”
Falo ta fito, ganin basa falon ya sa ta sauƙa ƙasa da sauri almost running jin Muryar big Daddy da twins a ƙasan, yana ganinta ya buɗe mata hannunsa yana murmushi ganin how pretty she looks da gudu ta shige jikinsa ta ƙanƙameshi tana dariya, apart from being mijin mamanta he’s her favourite uncle tun kafin suyi aure da Mami, kamar yanda yake favourite cousin ɗin Mami tun da can, yana shafa kanta yace
“Ya naga ba kya ƙara auki sai tsawo Na’ima, are u sure u don’t dodge rice over there”
Dariya tayi tana ɗagowa daga jikinsa
“Ina wuni big Daddy and welcome”
Amsawa yayi yana kallon Mami dake ta murmushi tana kallonsu.
Da daddare bayan dinner, Big Daddy ya wuce sama, Mami tana kallonta tace
“Kinsan faɗila?”
Na’ima ta ɗago daga wayanta ta kalli Mami
“Faɗilan uncle Aminu?”
“Eh ita, aurenta is in a week, gobe zamuje gidansu maybe ill leave u there, cause tun kafin kizo take ta roƙona she wants u to be her bridesmade, already jibi za’a fara events ɗinma, zaku kaita lagos”
Tashi zaune da kyau tayi
“fr?”
Mami ta kalleta bata ce mata komai ba
Tashi tayi ta dawo kusa da Mami, tana kwaɓe fuska
“Ni dai bazaki barni a can ba sai dai muje mu dawo”
Hararanta Mami tayi tana miƙewa ta nufi sama
“Idan na kaiki nabar ki a can ki dawo, da nace ma bazaki Lagos ɗin ba kai amarya amma yanzu na fasa, idan baki saba da yʼan uwanki yanzu ba sai yaushe?”
Bin Mami tayi da kallo har ta haura kafin ta tura baki ta miƙe itama ta wuce ɗakinta.
Washegari kamar yadda Mami tace after breakfast tare suka fita da ita zuwa gidan uncle Aminu wanda shima cousin ɗin Mami ɗinne.
Sosai suke ta jan Na’ima a jiki musamman faɗila da ta jata ɗaki tana faɗa mata yadda shirye shiryen biki yake tafiya, gidan akwai mutane sosai wanda duk yawanci yan uwa ne dan har an fara zuwa biki, already Gobe za’ayi traditional kamu da sakun lalle, jibi kuma ɗaurin aure sai kuma dinner da zasuyi a Lagos bayan an kai amarya.
” look ull have to help me” fadila ta faɗa tana kallonta a marairaice
“Ill do my best” Na’ima ta faɗa tana dariya ganin how serious faɗila seems, duk ƙawayenta da ke ɗakin suma dariya kawai sukeyi.
Har yamma suna gidan ana ta shirye-shiryen kamu da za’a yi gobe. Na’ima bata ga Mami ba, da ke can part ɗin Mummyn Faɗila, sai da ta tashi tafiya almost Magrib, har bakin mota ta rakota inda driver ɗinta ke jiranta. Mami ta shiga baya tana kallon Na’ima da ta jingina da motan.
“Ko mu tafi ne sai ki dawo gobe?”
Girgiza ma Mami kai tayi tana ƙirƙiro murmushi.
“Noo Mami, I’ll stay!”
“Okay then, sai na zo gobe. Be a good girl.”
Gyaɗa ma Mami kai tayi tana ɗaga mata hannu har suka ɓace ma ganinta kafin ta juya da nufin komawa cikin gidan.
“Wai Na’ima ce wannan?” ta ji muryar wani daga bayanta tana dab da shiga ƙofar falon.
Juyowa tayi tana kallonshi, ya naɗe hannunshi a ƙirji yana kallonta.
“Tell me baki gane ni ba tukunna, kiga me zan miki?”
Tura baki tayi dan dai da gasken bata gane shi ba. Yayi murmushi yana kallon yadda ta tura baki, yace
“Lallai ma Na’ima, ni ɗinne baki gane ba. Ai kawai Mami yanzu kam kar ta barki ki koma waccar ƙasar ta bar mana ke tun kafin ki daina ganeta itama.”
Murmushi tayi tana ƙarasawa cikin falon, ganin shima shiga falon yake ƙoƙarin yi. Ya zauna saman kujera yana jan ta da hirar da she’s not really interested. Ita dai sai dai tayi murmushi, ko idan ya mata tambaya ta bashi amsa a taƙaice da accent ɗinta, that’s so sweet.
Ƙanwar Faɗila mai suna Yusrah, dake zaune a dining tana jinsu, ta ɗauko plate ɗin abincin gabanta tana tahowa falon tace
“Yaya Fahad, ba fa wani gane me kake cewa take ba?”
Fahad ya harare ta
“Haka tace miki? Kuma ina ba a falon zaki dawo kici abincin ba tsabar gulma?”
Tsayawa tayi da plate ɗin a hannunta, ba tare da ta ƙaraso cikin falon ba sai kuma ta tura baki ta koma dining ɗin, amma rabin hankalinta na kan hiran da Fahad ɗin ke yi da Na’iman
Ƙawar Faɗila, Siyama, da ke gidan ahead of the wedding, ce ta sauƙo tana kallon Na’ima, tace
“Ai mun ɗauka kin bi Mami, daga bari ki rakata, shiru.”
Girgiza kai Na’ima tayi, tana miƙewa ta nufi sama tana faɗin
“Yanzu dama nake son komawa.”
Siyama ta dubi Fahad da ya miƙe shima, gaishe shi tayi, ya amsa da murmushi kafin ya fice daga falon, Yusrah ta bishi da harara.
Ita dai Na’ima har ta haura abinta. Ɗakin Faɗila ta shiga, suka kusa cin karo, ta ɗan koma baya Faɗilan ta fito tana faɗin
“Na’ima, ina kika tsaya? Wai ai na ɗauka kun wuce da Mami.”
Tana kallonta ta girgiza mata kai
“No, I was downstairs na tsaya…”
Bata bari ta ƙarasa ba ta ja hannunta
“Muje ɗakin Mummy. Kayan da Siyama ta amso ɗazu suna can na Kamun Gobe. Though I went for fittings, but I need to be sure ba wani prob. Kema ankonki duk yana wajen Mummy. Wai ina Siyamar ne?”
Ita dai binta kawai tayi a baya har ɗakin Mummy. Siyama ma can ta same su bayan ta ɗebo ma Faɗilar abinci da bata samu ta ci ba.
Mummy ta ba wa Na’ima duka ankonta da ke wajenta, wanda mummy ɗince da kanta ta mata, ba Ammi ba. Ta kai ɗaki, jakar da ta taho da shi da Mami ta sa ta haɗa kayanta kala 3 ta saka kayan a ciki sannan ta koma ɗakin Mummy wajen Faɗila.
Kiran sallar Magrib ya sa suka bar ɗakin dan yin sallah.
Har ƙarfe goma na daren ranar, idanunsu biyu anticipating for tomorrow’s event, da ƙyar Na’ima tayi bacci saboda hira da suke tayi a ɗakin.
Washegari, bayan sunyi sallah da Asuba, duk komawa suka yi bacci. Ganin ta kasa komawa ta janyo wayarta bayan ta rufe har kanta da bargo, messages ta gani from Sadiƙ har guda 3 asking how she’s wanda ya mata tun jiya, amma sam bata lura ba saboda how busy she was jiya, sai da tayi replying kafin ta fita. Morning greetings ta tura ma Dad da Ammi da big Daddy kafin ta kashe wayar ta rufe idanunta.
Ƙarfe tara, hayaniyarsu ya sake tashin ta. Miƙewa tayi zaune tana kallonsu kafin ta sauƙa daga kan gadon ta wuce toilet.
Bata jima sosai ba ta fito bayan ta wanke fuskarta. Faɗila da ke chatting da make-up artist ɗinta ta ɗago tana kallon Na’iman da ta jingina da mirror tana kallonsu.
“Kin tashi?”
Gyaɗa mata kai tayi kafin a hankali tace
“Good morning.”
“Morning, Na’ima.”
Ta faɗa tana gyara zamanta a tsakiyan gadon.
Sai da Na’ima tayi wanka, sannan ta sauƙa ƙasa bayan tayi breakfast da aka kawo musu tuntuni.
Ta gaishe da Mummy da wasu baƙi dake falon kafin ta fita compound. Already har an fara shirya inda za’a yi kamu, event planners suna ta aikinsu.
Kujeru da ke compound ɗin ta janyo ta zauna tana kallon ma’aikatan na aikinsu.
Ta ɗan jima a wajen ganin ta gaji da zaman wajen ya sa ta miƙewa ta shige cikin gida.
Komawa tayi ɗaki tana kallon Faɗila da few friends ɗinta da ke ɗakin. Lokacin ƙarfe 12:40.
Banɗaki ta wuce tayi alwala kafin ta koma falon Mummy. Ganin nan ma da mutane ta wuce cikin ɗakin, sai da tayi sallah kafin ta fito a falon Mummy ta haɗu da Maminta da isowarta kenan.
Da sauri ta rungumeta kafin ta sake ta tana ma su Aryan wasa.
Ɗakin Faɗila ta koma. Zuwa lokacin har sun fara shiryawa da shirya Amarya da Siyama ta tursasa taci abinci kafin su fara make-up da make-up artist ɗinta.
Zuwa ƙarfe huɗu, duk sun shirya cikin atampa royal blue colour wanda shine ankon kamun. sosai fitted gown ɗin yayi ma Na’ima kyau sosai. Fuskarta babu kwalliya ko kaɗan, dan duk yadda Faɗila tayi da ita ta bari ko simple makeup a mata, ƙi tayi. Fresh skin ɗin fuskarta sai glowing yake yi, kanta ɗaure da ɗankwalin atamfar da makeup artist ɗin ta ɗaura mata shi yayi kyau sosai. Ta ɗan matsar mata baya kwantaccen gashin kanta a kwance lubb. Duk ƙawayen Faɗilar kallonta kawai suke.
Faɗila da tayi kyau sosai, kana ganinta ka ga amarya, ta dube ta tace
“Yasmeen, ɗan ce ma Mummy, pls I want to talk to her.”
Miƙewa tayi ta ɗauki gyalenta daga kan gadon ta fita. Wata ƙawar Faɗilata dubi fadila
“This ur sister is cute, amma dai kin ɗauko ƙaramar yarinya kin saka cikin bridesmade ɗinki.”
Faɗila da ke scrolling a wayarta tace
“She’s my fav cousin, kuma duka duka 3 years na bata. She’s 17 fa kawai bata da girma ne.”
Shiru ƙawar tayi, bata kuma cewa komai ba.
A falon Mummy ta same su da Mami da friends ɗin Mummy da few relatives. Ta ƙarasa kusa da Mami ƙasa ƙasa, more like whispering in her ears, ta faɗa mata saƙon Faɗilan.
Mummy ta miƙe tana faɗin
“Okay,” kafin ta fita a ɗakin zuwa ɗakin Faɗila.
Mami da ke kallon Na’iman ta miƙe, hannunta ta ja zuwa ɗakin Mummy, tana kallonta tace
“Are u comfortable?”
Murmushi tayi tana kallon Mami tace
“Eh Mami.”
“Sure?”
Gyaɗa mata kai tayi, Mami tace
“Okay, am very happy kina connecting with ur family. Ina addu’a Allah ya sa Dad ɗinki ya yarda this time around. I don’t want u ki koma kwata-kwata, na fi son ki jona university a nan.”
Gyaɗa kai tayi bata ce komai ba. Mami ta gyara mata ɗankunnen gold dake kunnenta
“U look so beautiful.”
“U too,” ta faɗa tana dariya.
Sosai wajen kamun ya haɗu. Yamma lis aka fara kamu inda ya ƙayatar ba dan kaɗan ba. Na’ima na zaune a inda aka tanadar dan ƙawayen amarya gefen amarya, akan carpet mai kyau ga kilisa a jejjere a gun gwanin sha’awa. Professional videographers da photographers suna ta aikin covering komai.
Amarya da ango na zaune inda aka tanadar musu, few friends ɗin ango ba su fi uku ba a wajen, looking elegant and rich, suna matsa wayoyinsu very unbothered.
dangin ango sun yi bajinta ba kaɗan ba.
Ana tsaka da gudanar da kamun Na’ima, ta miƙe gaba ɗaya ji tayi ta gaji, Gashi tana so ta yi sallah, dan har an kira magrib. Ga wani fitsari da take ji, kutsawa tayi tana ƙoƙarin fita a wajen. A dai dai entrance ɗin wajen ta ci karo da mutum da shima fita yake ƙoƙarin yi a wajen, hannunsa riƙe da wayarsa kaɗai.
Saura kaɗan ta faɗi, tayi saurin dafe bangon wajen tana kallon shi, dai-dai Shima ya ɗago, those lazy hazel eyes ɗin nashi ya zuba mata su yana kallonta.
Gyara tsayuwarta tayi da sauri tana kallonsa. Very smooth fabric ne a jikinsa, wine colour ɗinkin kaftan, da babban rigan that is stiched with gold thread, hular kanshi ta dace ƙwarai da kayan jikinsa. Nan take ta gane yana cikin waɗannan unbothered abokan angon da suka yi kama da they were forced su zo wajen kamun.
Daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo sai dai bai ce komai ba, ya juya ya ci gaba da tafiya towards masallacin da ke cikin gidan. Binsa tayi da kallo, ganin yadda ya wuce abinsa without saying a word, ta so ta bashi hakuri, amma ganin irin kallon da ya mata yasa ta ji ta kasa bashi hakurin da tayi niyya. Ta bi tall figure ɗinshi da kallo kafin ta ja tsaki ta wuce cikin gida da sauri, jin fitsarin ya matseta sosai.
Har aka tashi a kamun bata sake komawa ba, tayi kwanciyarta a cikin gida, tana jin dawowansu tayi kamar tayi bacci.
Washegari aka saka amarya a lalle, wanda itama Na’ima a ranar sukayi henna mai kyau da aka kawo henna artist ɗin har gida ta musu.
Ranar jumma’a ana sauƙowa masallaci aka ɗaura auren Faɗila da angon ta Nasir, wanda a ranar jirgin dare zasu bi zuwa Lagos inda gidan Amarya yake kuma acan za’ayi dinner washegari.
Suna isa Lagos direct gidan Amarya aka wuce da su, few friends ɗinta da relatives da suka rakata, kowa wajen kwanciya kawai ya nema a makeken gidanta dake Lekki.
Na’ima dama tun da tayi sallah itama tabi lafiyar gado a ɗakin da aka sauƙesu ita da just 2 friends na Faɗila da suka taho daga Abuja.
Washegari sai bayan isha’i suka isa wajen dinner a wani private lounge a Lagos, wanda ya gaji da tsaruwa sosai, dinner ɗin ya ƙayatar. Ita dai Na’ima tunda ta zauna a inda aka tanadar musu ƙawayen amarya bata sake tashi ba, sau ɗaya suka haɗa ido da shi da yake zaune cikin abokan ango, shima by mistake bata sake bari ta kalli sashin da yake ba.
Sufyan da yake zaune kusa da Ahmad da ke danna wayarsa very unbothered da abinda ake yi a wajen yace,
“Guy.”
Ɗan kallonshi Ahmad yayi ta gefen ido.
“U see that girl?”
Ba tare da Ahmad ya kalli inda yake ƙoƙarin nuna masa ba ya maida kanshi kan wayarsa.
“Which?” ya faɗa yana ci gaba da abinda yake yi a wayarsa.
“The one i told u about a wajen kamu, wannan da bata dariyannan,” Sufyan ya faɗa yana ɗan murmushi.
Shiru Ahmad yayi baice komai ba.
Ganin Sufyan is still talking about her ya sa ya ɗago ya dube shi.
“Ka santa daga wani wajene?”
“Nope, kawai dai…” sai kuma yayi shiru ganin kallon da Ahmad ɗin ke masa.
“Guy chill ba fa wani abu bane, shes just cute, that’s all.”
Tsaki yayi ya maida kansa kan wayarsa.
“Ure just easily impressed, banga miye cute a wajen ba.”
Kallonsa kawai Sufyan yake kafin yayi dariya yana sipping mocktail a glass cup ɗin hannunsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Sanin halin Ahmad ɗin ba zai sake cewa komai ba akan batun ba.
Har kusan sha ɗaya kafin aka tashi a dinner ɗin, gaba ɗaya ba ƙaramin gajiya Na’ima tayi ba, ita kam da ta san yadda zata koma gida, da for sure ta gudu gida. Ganin basu da niyyar tashi yasa ta miƙe ta fita wajen hall ɗin. Silk fabrik ɗin jikinta ba ƙaramin kyau ya mata ba, champagne colour ne wanda aka yi mata hand beading, an mata ɗinkin fitted gown da ya sauƙa ƙasa sosai, ɗaurinta mai kyau sosai a kanta, unlike yesterday yau akwai simple make up a fuskarta, very light one ta sanya tayi matuƙar kyau, ƙafafunta sanye da heels looking very elegant and classic.
Sai da ta fito waje sai kuma ta tsaya a harabar da ke cike da expensive motoci tana bin ko ina da kallo, kamar zatayi kuka. Ta ɗan ɗage gown ɗinta ta ƙarasa wajen, a jikin wata matte black Maybach ta jingina tana ƙoƙarin ciro wayarta daga ɗan ƙaramin jakarta. Da yake glass ɗin motar tinted ne kwata-kwata bata san da mutum a ciki ba.
Yana zaune a bayan motan, yana riƙe da ruwan gora a hannunsa da ya gama sha, ɗayan hannun yana riƙe da wayarsa, shima bai jima da fitowa ba, away from the loud music and useless small talks.
Yana kallo ta jingina da motar sai dai baya ganin fuskarta saboda ta bashi baya, gani yayi ta ɗan sunkuya tana duba fuskarta da ɗaurinta a side mirror ɗin motar, sai a sannan ya ga fuskarta.
ɗan murmushi yaga tayi.
“I look like I need rescue,”
ta faɗa tana gyara masa mirror ɗin sai kuma ta soma tafiya ta koma cikin wajen. Binta yayi da kallo har ta shige sai kuma ya ja tsaki ya mayar da kansa ya jinginar ignoring kiran Amira dake ta shigowa ba ƙaƙƙautawa a wayarsa.
Ganin ba zata daina kira ba ne yasa ya buɗe idanunsa a hankali yana kallon wayar. Ya ɗago kansa daga inda ya jingina da kujera, ya sa hannu yayi swiping ya ɗaga wayar zuwa kunnen shi, ya yi shiru.
A can ɓangaren Amira, da ta gama cika tayi fam, ta soma magana.
“Albi, why aren’t you picking up your calls? Kuma dinner dînne har yanzu ba a gama ba ko me?”
Shiru ya yi, bai ce komai ba. Sai ma lumshe idanunsa da ya yi yana sauraron ta.
“Kayi shiru,” ta ce, tana jan numfashi. Sai lokacin ne ya yi clearing throat dinsa, sannan ya buɗe idanunsa yana kallon entrance ɗin wajen.
“Look Amira, am not in the mood for all this. Zan dawo yanzu. Ina Saif?”
“Yayi bacci,”
“Okay,” ya faɗa yana buɗe ƙofar motar. Ya sauka ya ƙarasa driver’s seat, ya kunna motar ya bar harabar wajen. tuƙi kawai yakeyi amma zuciyarsa cike take da tunani iri-iri har ya isa gida.
A main parlour ya tarar da Madam ɗin tana jiransa. Kallo ɗaya ya mata , ya wuce matakala. Da sauri ta biyo bayansa. Yana jin takun ta, amma bai ce komai ba har suka isa sama. Sai da ya fara duba Saif wanda har ya jima da bacci kafin ya nufi bedroom ɗinsa.
A tsakiyar ɗakin ya tsaya yana kallonta Ganin har nan ta biyoshi kuma bata da niyyar yin magana sai ma tsayuwa da tayi ta yi folding hannunta ta jingina da ƙofa tana kallonsa ya ɗauke kansa. Ya cire rigar saman ya ajiye a gefen gadon, sannan ya fara ɓalle cufflinks ɗinsa.
“Amma kasan ƙarfe nawa yanzu?” ta tambaya tana cigaba da kallonsa.
Sai da Ya ajiye cufflinks ɗin kafin ya juyo gaba ɗaya yana kallonta, ba tare da ya ce uffan ba. Irin Kallon da ya sa ta kasa ƙarasa abinda ta ke shirin faɗa.
Ƙwafa ya yi ya wuce toilet ya rufo ƙofar. Ta bi ƙofar banɗakin da kallo kafin ta ƙarasa ta zauna gefen gadon. Rigarsa ta ɗauka ta kai hancinta tana sniffing ko zata ji ƙamshin wani turare daban da ba nasa ba, Jin ƙamshin turarensa ne kaɗai a jikin rigar ya sa ta lumshe idanu. Ta ajiye rigar a kan gado, ta juya ta fita daga ɗakin.
Sam bata son ganin ya jima a waje. Ji take kamar yana tare da wata. Ko dinner ɗin ma taso yaje da ita amma ya ƙi. Shiyasa ta sake yarda cewa akwai wata da zai haɗu da ita, ba iya dinner ba. Duk da ta san ba halinsa bane, amma zuciyarta sam akansa bata da yarda.
Yawan business trips da yakeyi suna daga mata hankali, dan har ya dawo bata da nutsuwa, Tana jin kamar watarana zai haɗu da wacce zuciyarsa zata So bayan ita. For the past 5 years da suka yi aure, bai taɓa bata ƙofa da zai wulaƙanta ta ba. Yana iya ƙoƙarinsa wajen sauƙe haƙƙoƙinta dake kansa, amma hakan ba yana nufin zata mance dalilin aurensu bane. Ba zata bashi ƙofa da zai so wata ba, ba zata taɓa bari idanunta ya rufe kanta yayi murfi ba.
Tana isa ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta shiga kiran ƙawarta Nuwaira…
Tun da suka dawo daga dinner, wanka kawai tayi ta kwanta, dan da ciwon kai sosai ma ta dawo. Washegari bayan breakfast suka fita buɗe ido a Lagos. Duk da yadda ta so ƙin zuwa, basu barta ba.
Sun zagaya Lagos: daga Nike Art Gallery, Landmark Beach inda ta cire takalmanta tana tafiya barefoot a kan ƙasan wajen mai tsananin laushi. Suka ci boli—abinda bata taɓa ci ba, amma dole ta yarda it’s amazing, more than any grilled food she’s had in New York.
Sosai suka yi nishaɗi. Idan ta tuna cewa na lokaci ƙanƙani ne kafin ta koma New York to her boring life, sai ta ji jikinta yayi sanyi.
Washegari suka bi jirgin yamma zuwa Abuja. Faɗila da Nasir suka rakasu har Airport. Nasir na tsokanar Na’ima wai itama ta zo Lagos ta yi aure, sai Faɗilarsa ta samu relative a Lagos. Na’ima ta ɓata rai taƙi ce masa komai, a ranta kuwa cewa take “Ni da Lagos sai dai ziyara!”
Haka suka rabu da Faɗila cike da kewa. Nasir ya rungume abarsa tana kuka a hankali a jikinsa, tana ɗaga musu hannu.
A Abuja, Big Daddy da kansa ya ɗauko ta daga gidan Uncle Aminu zuwa gida, tana ta ba shi labarin Lagos, yana ta biye mata yana mata dariya.
Kwanakin da suka biyo baya are her happiest, warmest, and most peaceful days. Mamy ta koya mata girke-girke na gida, tana sa ta ɗanɗana abubuwan da ta dade bata ci ba. Suka je spa, aka musu gyaran jiki tare. Aka wanke musu hannaye da ƙafafu. Aka gyara musu gashi. Da yake lallenta na biki bai goge ba, Mamy ce kaɗai ta yi jan lalle.
Wani sa’in idan ta kalli Mamy, sai taji idanunta ya ciko da hawaye. Tasan tayi iya bakin ƙoƙarinta, amma Dad bazai bari ta zauna ba. Ko dan irin soyayyar da Big Daddy ke mata wanda ta jima da fahimtar baya so.
But zata yi iya ƙoƙarinta wajen convincing Daddy ya bar ta ta dawo gurin Mamynta. Amma sai ta koma New York tukun.
Sosai ta zaga dangin Mamynta har da na Daddy. Sunyi matuƙar murna da ganinta. Da zata tafi, suka haɗa mata goma na arziki, suna mitan rashin zuwan Dad wanda har sun gaji sun hakura.
Sosai su Aryan suka saba da ita. Duk inda ta je suna biye da ita. Tana magana da Sadiq kusan kullum. Babu wani labarin Nigeria da bata ba shi ba. Wanda har mamakin yadda ta yarda da shi ta kuma shaƙu da shi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci take yi.
Duk da haka, ba komai ta sani game da shi ba, Banda cewa shima dan Nigeria ne, yana da brother ɗaya da two sisters, waɗanda baya magana sosai akansu. Idan ta ɗauko maganar ma , sai ya san yadda zai sauya topic ɗin. Shiyasa itama kawai ta hakura ta watsar.



