Chapter 6: Chapter 6
Shiru tayi hawaye har ya ciko idanunta, tana kallonsa
“To bazaka sha fruits ɗin bane?”
Ɗan kallon plate ɗin that is messy yayi, sai kuma ya raɓa kawai ta gefenta ya fice a kitchen ɗin ta bishi a baya kamar chewing gum, har ya haura sama, ɗakinsa ya wuce ya ɗauko makullin motarsa ya fito a bakin ƙofa ya ganta tsaye, ya wuce ya buɗe ƙofar palournsa ya fita, har ya fara sauƙa bene yaji tace
“In dai wata zaka je wajenta wallahi ban yafe ba “
Dakatawa yayi ya juyo gabaki ɗayansa yana kallonta, sai kuma ya dawo muryarsa da alamun ɓacin rai, amma still a nutse yake kallonta kafin ya fara magana
“ i didnt ask for love from you Amira, i asked for peace, amma kin gagara bani, i dont owe u proof of where i go every hour, instead of u to focus on kula da kanki da ɗanki yadda ya kamata, kin mayarda hankalinki kan neman abinda babu shi, its almost 12 amma har yanzu kina yawo a pyjamas, for once baki taɓa shirya Saif da kanki ba, but ure here asking ina zanje, da wa kuma zan haɗu, shi wannan abin da kike nema ɗin ina mai tabbatar miki kin kusa samunshi”
Daga haka ya juya abinsa ya barta baki sake tana binsa da kallo har ya gama sauƙa, da sauri ta wuce ɗakinta tana son hana kanta kuka ta shiga kiran Nuwaira…
Yana sauƙowa yaga Saif a tsaye bakin steps an canza masa kaya, hannu ya miƙa masa, yaron ya riƙe da sauri yana murna ganin fita zasuyi, har compound yana riƙe da hannun Saif, few Ma’aikata dake compound suna gaishe shi, a hankali ya amsa musu, ya ƙarasa ɗaya daga cikin motocinsa, sai da ya zaunar da Saif ya saka masa seatbelt, sannan ya rufe motar ya zaga ya shiga shima ya tada motar ya bar gidan…
A zaune a kan kujera a wani babban palour da ya gaji da tsaruwa, babbar mace ce da bazata wuce shekaru 54 ba, sanyin Ac da ƙamshin turaren wuta mai daɗi kawai ke tashi a palourn, ta ɗago kanta daga hisnul muslim da take karantawa ta dube shi, har yanzu yana zaune ya jinginar da kansa da kujeran da yake zaune ya lumshe idanunsa..
“Wani abun ya sake faruwa ne?”
Buɗe idanunsa yayi ya miƙe zaune a hankali yana kallonta bai ce komai ba
“Tambayarka nake, ka zo min gida kuma ka zauna kamin shiru akwai abinda ya faru ne?”
“Babu komai Ammi”
Ya faɗa yana mayarda kansa ya jinginar amma wannan karan bai lumshe idanun ba ya zuba ma Ammi da ta cigaba da buɗe hisnul muslim ɗinta idanun lost in his own world, sai da ta gama tsaff kafin ta rufe ta ajiye shi a kan centre table dake wajen, ta gyara zamanta tana kallonsa
“Ya maganar da mukayi da kai Last week ? Har yanzu kayi shiru, u know u can’t avoid this discussion forever.”
Shafa kanshi yayi yana maida dubanshi tv dake aiki amma muryar a rage har ƙarshe, “i havent forgotten” ya faɗa a hankali
“U gave me ur word, ill not allow u break it” ta sake faɗa tana kallonsa wannan karan cikin muryarta da tabbatuwar she mean abinda take faɗa
Juyowa yayi ya kalleta, sai kuma ya gyaɗa mata kai kawai bai ce komai ba, ganin ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta ya sa ya sauƙe ajiyar zuciya
“Ammi, zan bar Saif anan har na dawo daga cape town”
“Why? Mamarsa bata nan ne?”
Shiru yayi baice komai ba, sai da tayi ɗan jim kafin ta dawo ta zauna tana kallonsa,
“Tell me”
Lumshe idanunsa yayi ya buɗe kafin a hankali ya ce “Shes just insecure, gani take kamar am seeing other girls”
“And so?” Ta faɗa tana kallonsa fuskarta a tamke
“Saboda miye Bazaka ga other girls ɗin ba? Ko ta manta dalilin aurenku ne? Yarinyar da respects Nobody cikin danginka, ta mayar damu abokan gabanta?…Shirun da nake yi doesnt mean am happy at all da aurenka, amma Allah ya riga ya rubuta hakan babu wanda ya isa ya ja, kannenka sam sun daina zuwa gidanka, ko hakan yana maka daɗi ne kai”
Shiru yayi bai ce komai ba
“Allah ya kyauta, ka barshi a nan ɗin toh ba damuwa, yaushe zaka yi tafiyan?”
“Gobe in sha Allah”
“Allah ya kaimu..”
Daga haka ta miƙe ta wuce ɗakinta, da kallo ya bita kafin ya miƙe ya fita a palourn…hannunsa ɗaya a cikin aljihunsa kamar yadda yake sarar sa yake sauƙowa benen yana kallon Rahama da Yasmeen da suke kwance a kan sofa, suna sharing blanket ga popcorn a gefensu, suna dariya ƙasa ƙasa, idanunsu akan screen ɗin tv da suke kallo….
A hankali ya cigaba da sauƙowa footsteps ɗinshi calm and steady.
Haɗa idanu da Yasmeen tayi da shi ya sa ta gyara zamanta da sauri tana matso da hular kanta, Rahama ma juyowa tayi tana kallonsa kafin ta tashi zaune itama sosai tana kallonsa har ya ƙaraso palourn ya zauna a kan kujera ɗan nesa da su yana kallonsu, Yasmeen ta saka hannu ta janyo remote ta rage tv, a tare suka gaishe sa
“Ina wuni Yaya”
“Fyn” ya faɗa yana jinginar da kansa da kujera, suma komawa sukayi suka jingina suna kallon sa, kusan 10 minutes kafin ya miƙe yana kallon Yasmeen yace
“Saif?”
“Yayi bacci”
Juyawa yayi ya nufi ƙofa duk suka bishi da kallo, sai da suka tabbatar ya fita gabaɗaya kafin rahama tace
“is he okay?”
“Ko zaki bisa ki tambaye sa?”
“Ji wani iskanci dan na tambayeki sai ki wani ce in tambayesa? Nawa a wanne zan wani tambayesa?” Rahama ta faɗa tana hararar yasmeen
Yasmeen ta koma ta kwanta tana ƙara volume ɗin tv
“Ni dai na san ba zai wuce shi da matarsa ba, im not being typical dangin miji amma koh hmmm”
Rahama tayi dariya kaɗan itama tana faɗin
“Ku da kuke zuwa gidansa kenan, tun da muka je da anty hafsa ta mayarda mu yan iska ban sake zuwa ba, ni rabona da gidansu ya kai shekara ɗaya da rabi”
Yasmeen ta mata wani kallo sai kuma tayi ƙwafa
“Ai wlh sai naje, haka kawai ni da gidan yayana ace bazan je ba saboda matarsa can wai batada mutunci, da zai barni ma tattara kayana zanyi in koma can har na gama school wallahi”
“Kinsan me ya fi bani haushi? Rashin zuwa gaida Ammi da takeyi, lokacin da Abbu ke raye ai tana zuwa saboda munafurci tunda ta san shi ya haɗa auren, amma tunda ya rasu ni dai i can count so nawa tazo gidannan”
“Allah ya sa ya ƙaro aure” yasmeen ta faɗa tana ƙyalƙyakewa da dariya, Rahama na tayata
“Tabb da zuciyar wata yayi bindiga, ke matarnan fa bata da man kai, ko da yake yaya Ahmerdyn ne ma zai yarda yayi wani Auren, yaushe yaji daɗin na farko ma bare ya ƙaro ta biyu, su kashe mana shi mu shiga uku”
Yasmeen tayi tsaki bata ce komai ba, suka cigaba da kallon da sukeyi..
WAZIRI ALIYU CRESCENT, OFF ISA KAITA ROAD, UNGUWAR RIMI, KADUNA STATE.
“ Rahilaaaa, Rahilaaaa! Wannan yarinyar idan na miƙe na same ki a kitchen ɗinnan wallahi ill slap ur destiny back to ur primary school”
Rahila ce ta fito da gudu daga kitchen tana share hannunta a zaninta
“Hajiya gani”
Hajiya Zainab Bulama ta dube ta tace
“wani irin mopping kika yi wannan kamar wanda kika yi shi da Mangyaɗa ko so kike in zame in mutu ace tsatsauyi ne hajiya ta faɗi”
“Wlh hajiya…”
“Tafi dan Allah nikam ki sake bana son dogon zance” ta faɗa tana ƙarasawa cikin palourn ta zauna tana ci gaba da mita
“Kowa sai shegen musun tsiya, idan an faɗa muku abu miye anfanin kare kai bayan ƙiri ƙiri kunsan baku da gaskiya “
Rahila ta amsa da “toh hajiya, kiyi hakuri hajiya” ta juya ta koma kitchen
Maryam ce ta shigo palorn daga waje da wayarta a hannunta ta ƙaraso ta zauna kusa da Mama jin har lokacin sababi take yi
“Mamanmu calm down, kinsan pressure fa bashi da kyau”
“Im angry not sick, ni rabu da ni dan Allah”
Umar ne ya shigo shima da Can ɗin maltina a hannunsa da earphone a kunnensa, yana kallon Mama ganin yadda ta haɗe rai tana jan carbi ya juya ya ɗan kalli Maryam, ta ɗauke kan ta ta mayar wayarta bata ce komai ba, zama yayi a kujera yana shan malt ɗin hannunsa
Maryam ta ɗaga kai ta kallesa a hankali tace
“Yaya Umar ka bata haƙuri”
“Me zance? You want me to collect stray slap”
Dariya Maryam ta fashe da shi tana kallon Salima da ta fito daga ɗaki da zumbulelen hijabi akan jeans ɗinta jin Mama tana sababi, tazo ta samu waje ta zauna a falon kamar mutuniyar kwarai.
Mama ta kalli Salima “ina wayarki?”
“Tana ɗaki”
“Je ki ɗauko ki kiramin yayanki”
“Mama…”
Umar ya harareta ta miƙe da sauri ta wuce ɗaki sai gata ta dawo da waya, dialing lambarsa tayi tana Addu’a Allah ya sa ma kar ya ɗaga
“Helloo” ta jiyo muryarsa bayan wayar tayi ringing for a while
“Assalamu alaikum yaya Sadiq Mama ce take son Magana da kai”
Shirun da yayi ya saka ta miƙawa Mama wayar ta koma ta zauna
“Assalamu alaikum” mama ta faɗa tana miƙewa ta nufi ɗakinta duk suka bita da kallo
Sai da ta zauna a kan Gado kafin ta amsa gaisuwarsa, shiru ne ya gifta cikin sanyin murya kamar ba ita ba tace
“Sadiq yanzu bazaka dawo gida ba? Kana kyautawa kenan kai a tunaninka? One week, two weeks not a single call?”
Ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali
“Im busy sosai ne Mama”
“Busy with what exactly? Mata kake da shi ko aikin me kake yi a can ɗin?”
“Im working” ya faɗa a hankali
“Okay, naji, yaushe zaka dawo gida ?”
Shiru yayi bai amsa ba
“Meyasa bazaka manta da abinda ya faru ba already? Ba laifinka bane, meyasa bazaka Manta Mimi and move on ka dawo gida ba, abinda ya same ta uve nothing to do with it, shekarunka gaba suke yi fa ba baya ba, so kake jini na ya hau ne kam sadiq?”
“Why are u bringing her up i didnt hurt her, she hurt me” Ya faɗa a hankali
“Saɗiq yaushe zaka zo gida ka amsamin”
Ta faɗa tana share waccar maganan
“Zanzo, Soon”
“Haka kake cewa kullum, shekara ɗaya fa kenan Sadiq”
“Da gaske nake this time zan zo soon”
“Allah ya sa, Allah ya maka albarka”
“Ameen”
Basu jima sosai ba bayan wannan sukayi sallama, bai ce ta bama su Umar ba itama kuma bata bukaci ya gaisa da su ɗinba dan tasan yana ƙiransu once in a blue moon ya ji yaya suke”
Ajiye wayar yayi bayan sun yi sallama da Mama ya lumshe idanunsa, sai kuma ya buɗe ya janyo wayarsa, hotunan Na’ima ya shiga dubawa masu yawa dake wayarsa, wasu ma sam bata san an ɗauke su ba, yayi zooming fuskarta yana kallon hoton da ya ɗauke shi ranan fundraising na makarantarsu
“Mimi hurt me, shiyasa abinda ya faru da ita happened, nasan u wont hurt me, ure Mine Ni’ima, ure Mineee, haduwa da ke is not a coincidence, ni na zaɓeki”
Am so sorry for not posting yesterday, my phone had issues amma Alhamdulillah yanzu na gyara tnk u for bearing with me ❤️
Sake labulen window tayi bayan ta gama kare Musu kallo, ta juyo ta kalli Suhaila da ke Zaune fuskarta a haɗe kamar zata fashe, Mummy Salma ta dawo ta zauna a gefen gado ita ma fuskarta a murtuƙe tace
“Shi ne wanann ɗin da kika ce kin ganta da shi rannan ya kawo mata flowers?”
“Wlh Mummy shine, like shes not even his level, hes too perfect for that Naive girl”
Mummy dai shiru tayi kamar mai nazari sai kuma tayi wani murmushi tana jijjiga kai tana kallon Suhaila tace
“Ure angry right?”
“Eh mana” suhaila ta amsa almost immediately dan har ranta take ji inaaaa bazata taba bari wani abu yayi nisa tsakanun sadiq da Na’ima tana ji tana gani ba.
“ then use it! Ki saurare ni da kyau Suhaila, mutane irinta, simple and modest girls, they shine toi brightly when u ignore them”
Sai kuma ta taso ta dafa kafaɗan Suhaila “the only way da zaki haska is by dimming her light first, kece kika cancanci ɗaukaka da haskakawa tunda ai kin girme ta”
Suhaila ta ɗaga idanunta tana kallon mamanta kafin ta gyaɗa mata kai a hankali tana sauƙe ajiyar zuciya.
Da daddaren Ranan Mummy na zaune saman King size bed na ɗakin Dad, ta jingina da allon gadon tana kallon walk in closet da Dad ɗin ke ciki yana shiryawa for bed
Buɗe ƙofar closet ɗin yayi ya fito sanye da dark grey pyjamas ƙamshin turarensa mai ƙamshi da tsada ya mata sallama, sai da ya hau gadon kafin ya ɗau glasses ɗinsa dake gefen bed ya saka a idanunsa ya ɗauki remote dake gefen wajen yana ƙoƙarin canza channel.
Sauƙa Salma tayi ta ƙarasa wajen Fridge dake ɗakin ta buɗe, sai da ta ɗan saci kallonsa kafin ta ɗauko wata brown kwalba mai sanyi, wani dogon farin glass cup dake kusa da wajen ta ɗauka ta tsiyaya content ɗin a ciki, ta ɗan saka few cubes na ƙanƙara kamar yadda ta san yana so, ɗauko wa tayi a hankali ta juyo ta nufo sa ta ajiye a gefensa tana kallonsa, ƙaran ajiyewanne ya sa ya ɗago kansa ya dubi class cup ɗin da yana iya ganin content ɗin ciki sai kuma ya dube ta, murmushi ta masa
Ya ɗauke kansa
“Im not drinking today”
Ya faɗa yana mayarda kansa kan abinda yake yi
“Why?”
“Haka kawai” ya faɗa yana ba tare da ya kalleta ba
“Okay.. are u sure? In mayar kenan?”
“Eh” ya faɗa bayan ya juya ya ɗan kalli cup ɗin cike da temptation.
Ɗaukan cup ɗin tayi kamar zata mayar sai kuma ta kama hannunsa ta saka masa a ciki
“I insist” ta faɗa tana kallon cikin idanunsa.
Yana riƙe da cup ɗin reluctantly at first sai kuma ya kai bakinsa ya kurba, ya sake miyarwa ya ƙara sha, Salma ta gyara zamanta tana murmushi tare da gyara kayan baccin jikinta.
Sai ta ya kai kusan shanye content ɗin cikin cup ɗin kafin ya jingina bayansa da gado ya ɗan lumshe idanunsa wanda ya riga ya cire glasses ɗin tun da yayi second sip.
Mummy Salma ta gyara zamanta da serious face and tone tana kallonshi tace
“Daddyn Suhaila da Na’ima can i say something?”
Ya ɗan buɗe idanunsa ya kalleta
“Yaushe kika fara tambayan permission kafin kiyi magana?”
Ɗan murmushi tayi sai kuma tace “its about Na’ima” sosai ya maida duka attention ɗinsa kanta harda gyara zamansa
“What about her?” Ya tambaya yana ƙarasa shanye abinda ya rage a cup ɗin ya ajiye a gefen bed.
Wani ajiyar zuciya ta sauƙe kamar mai tunanin ta inda zata fara “ bana son ina cika magana ne wallahi amma kuma abin ya dame ni ne, wallahi im littled concerned lately”
“Concerned how?” Ya faɗa fuskarsa ɗauke da mamaki
“Kaga shes growing fast, kuma yarinya kamarta, fresh out of high school a irin garinnan, ka dai san yadda abubuwan suke..”
Shi dai kallonta kawai yake, ta cigaba
“The other day Salma tace min ta ganta da wani guy, though i didnt believe, amma sai gashi yau ma da kaina na ganta da shi, duk da ba wai wani abu suka yi dats inapprpriate ba but still they seemed close, irin wanda ban taɓa ganin tayi da wani ba, am just afraid kar ta haɗu da wrong people…”
Ɗage girarsa yayi fuskarsa tana canza wa zuwa ɓacin rai
“waye wannan?”
“Gaskiya dai ban san waye ba, bansan sunansa ba”
“Na ɗauka ma ka sani ai..” ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa
“No she didnt mention any boy to me”
Mummy ta gyaɗa kai “shes a good girl, am sure tana ganin kamar tana making friends ne, but dai kai kasan how men can be”
Shiru yayi kamar mai tunani
“But why are u telling me now? Meyasa baki tsawatar mata ba?”
Salma ta zaro ido sai kuma ta ɗanyi ƙaramar dariya
“Ai kai kasan how this children can be, bana so taga kamar ina shiga mata rayuwa ne, kuma kaga dama ita ba wani magana ma take yi ba, ko salma bata kulawa abin na damuna ban san meyasa dai take haka ba”
Ta ɗan kalleshi ganin yayi shiru, “maybe, just maybe Nigeria might be better for her, kaga a can ga mamanta, ko ba wai duka zata koma can ba, ko University ta gama kaga sai ta dawo sannan ta san kanta she wont fall for abubuwa irin wadannan”
Shiru yayi bai ce komai ba, itama sai kawai tayi shiru
Miƙewa taga yayi ya ɗauki glass ɗin ya ƙarasa fridge ya buɗe ya ƙara cika cup ɗin
“Shes a smart girl, bazatayi anything reckless ba ni na sani”
No, ofcourse not ai kam nima na san bazata taɓa ba, kawai dai kaga ai rigakafi yafi magani koh?”
Shiru yayi bai amsa ba, itama sai ta miƙe ta ƙarasa saman gadon ta kwanta tana sauƙe ajiyar zuciya da addu’ar Allah ya sa yayi considering.
“You know zaka iya yin business ɗinka a Abuja, or Lagos?.. but No, its always London or paris yau kuma Cape town zaka koh?”
Amira ta faɗa tana kallonsa bayan ya gama shirya wa tsaf, his suitcase na gefe packed already
Ajiye kwalbar turaren da ya gama fesawa yayi,
“Saif na wajen Ammi, hell stay there har na dawo”
Zaro idanunta tayi dan bata ma lura Saif ɗin baya nan ba sai yanzu da ya faɗa ta ɗauka yana gurin Mary.
“A saboda miye toh?”
“Saboda she’ll take good care of My Son har na dawo wanda ke bazaki iya ba, Sai na dawo”
Ya faɗa yana wuce ta ya fice daga ɗakin ta bishi da kallo kamar zata fashe..
Tana jin rufe ƙofarsa ta wuce ɗakinta ta hau kiran Nuwaira, tana ɗagawa ta saka a handsfree ta ajiye a gefen gado tare da fashe mata da kuka
Nuwaira daga ɗaya bangaren tace
“kar kice min Ahmad kike ma wannan kukan kar kisa raina ya ɓaci a banza “
Cikin kukan Amira ta soma faɗa mata yadda suka yi jiya da tafiyar da yayi yau
“Kinga yasan raina zai ɓaci shiyasa ya ɗauki Saif ya kai musu, saboda ya nuna musu bani da daraja, kuma tafiyar nan ma ni ban yarda business trip bace, jiya fa har ce min yayi abinda nake nema zan samu, me yake nufi kenan?”
Ta cikin wayar Nuwaira tace “shey Ahmad dey Mad ni? Akan miye zai ɗau yaronki ya kai miki gidansu ba da yardar ki ba, babe ke kika ƙyale mutummin ma, da kika zauna kina kuka akan yayi tafiyarsa ya barki to sai me? He should kuku travel to hell, see babe ki kwantar da hankalinki okay i dey come ur house like dis yanzu, ki kwantar da hankalinki ki bar kuka”
Ajiyar zuciya Amira ta sauƙe “Nuwaira pleasee dont talk about him like dis, kawai toh sai kinzo”
“Ai kinga irinta ni kam in kin san baƙin ciki zaki ƙunsa min idan na zo nayi zamana gidan Ubana”
“Ah ah pls ki zo zuciyata zafi take min”
“To gani nan zuwa”….
“Yanzu wanke fridge ɗinne haka Rahilaa? Miyesa kam bakya tsoron Allah”
Rahilaa da ke tsaye gefe tana kallon Hajiya Zainab ta yi ƙasa da kanta, dan ta san tana buɗe baki da nufin kare kanta zata janyo wa kanta masifar da tafi wannan, bayan kuma wlh ta wanke yanda ya kamata, Salima da Maryam ne suka saka yi kunun aya da daddare suka ajiye sauran a fridge basu rufe ba ya zube duk ya ɓata ko ina.
“Wai kam ba magana nake miki ba, kika koma gefe kika ƙi cewa komai? Baza’a faɗa miki kinyi ba dai dai ba ki buɗe baki ki bada haƙuri sai dai kiyi ta abu kamar ni ce azzaluma ina zaluntarki ke abar tausayi koh?”
“Kiyi hakuri hajiya zan sake wanke wa yanzu”
“ u better! Kuma dis time use ur brain”
Daga haka ta fice q kitchen ɗin, Rahilaa ta bita da kallo, sai kuma ta ƙarasa ta fara ƙoƙarin wanke frideg ɗin tun kafin ta dawo ta fara mata kwarmato.
Bata gama wankin fridge ɗinba Maryam ta shigo tana kallonta,
“rahilaa ki soya min ƙwai gudu biyu ki kawo min falour”
Ta faɗa tana ɗaukan bottle water guda ɗaya ta fita a kitchen ɗin, a falour ta samu Salima dake game a waya tayi matashin kai da ƙafar Umar dake video game a tv, ta zauna tana ɗaka ma Salimar duka a cinya,
“dillah can ɗaga masa ƙafa”
“Ina ruwanki?” Umar ya faɗa ba tare da ya ɗauke kansa daga abinda yake yi ba, Salima ta miƙe zaune
“Mtsw akan me zaki dokeni?”
“Ko zaki rama ne?”
“Allah ya isa” ta faɗa tana miƙewa, Ganin Maryam ma zata yo kanta, ta koma bayan kujera ta tsaya, dai-dai Rahilaa ta kawo ma Maryam ƙwai ta duƙa ta ajiye mata, Maryam ta koma ta zauna, ta ɗauki ƙwan ta soma cj bata sake bi ta kan Salima da ke tsaye ba.
Ko dai nima zaki soya min ƙwannan ne? Umar ya faɗa bayan ya ɗan saci kallon ƙwan da Maryam ke ci.
Rahilaa tace “toh”
Tana dab da shiga kitchen Salima tace
“Rahilaa in kin bashi ƙwan ki je sama ɗakin anty Maryam akwai Kayana zaki ɗauko min, ki haɗa da waɗanda na nuna miki ɗazu ki goge min”
Rahilaa tace “toh”
Kafin ta shige kitchen sai da ta rufe ƙofar kafin ta tura baki
“sai kace kutare komai Rahilaa, Rahilaa,Rahilaaa”
Da sassafe Na’ima ta fito daga ɗakinta sanye dogon rigan material mai kyau, fuskarta fess alamun har wanka tayi, sai baƙin hula a kanta da ya mata kaɗan saboda yawan gashinta dats coiled, ƙafarta babu takalmi take taka marbles ɗin, har ta fara sauƙa taji Suhaila ta buɗe ƙofar ɗakinta in a sleeping dress riga da wando, Na’ima bata tsaya ba ta cigaba da sauƙa ƙasa abinta.
Itama Suhailar ƙasan ta sauƙo tana tafiya kamar ʼyar shugaban ƙasa, ta wuce Na’ima zuwa Kitchen inda su Mariam ke aikin abincin safe, bata jima ba ta fito bayan ta gama balbale su da bala’in da basu san dalilinsa ba, ita kam Na’ima dama tunda ta ga ta nufi kitchen ɗin ta samu waje a falour tayi zamanta.
Ƙarasowa falourn Suhaila tayi ta zauna tana kallon Na’ima daga sama har ƙasa
“Flower girl ina flower boy ɗin naki?”
Shiru Na’ima ta mata, Suhaila ta miƙe ta dawo kujeran da Na’ima take ta zauna ta sa hannu ta juyo da fuskarta
“Magana nake miki, nace ina guy ɗin da ke zuwa wajennaki yake?”
Hannu ta sa ta buge hannun Suhaila daga fuskarta
“Baki da google ne? If ure that pressed maybe ask Google, or like pull a tarrot card or something, im not his GPS”
Cike da neman bala’i Suhaila tace
“sai dai in tambayi uwarki ko ubanki”
Wani irin kallo Na’ima ta mata na kusan two minutes dead in d eyes, kafin tace
“dont try dat again”



