⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 11: Chapter 11

Na’ima ta share hawaye amma ta gagara magana, anan suka zauna a waiting room ɗin wanda sanyin ac ɗin ya fara saka ta jin kamar zatayi zazzaɓi itama, ta haɗe hannunta waje ɗaya tana jijjiga ƙafarta da addu’a a zuciyarta.
sai gabanin asuba likitoci suka fito, Nasir ya miƙe da Sauri likitan yace ya same sa a office ɗinsa, da sauri Nasir ya bi bayanshi, ita dai komawa tayi ta zauna tana binsu da kallo, after mintuna Nasir ya dawo yana kallonta ganin expression ɗin fuskarsa ya sa ta sauƙe ajiyar zuciya tun kafin ma taji me zai ce “Alhamdulillah, both the baby and my wife are safe Na’ima” “Alhamdulillah” itama ta faɗa tana murmushi, “amma baza su discharging ɗinmu ba sai nan da 2 days, bari in yi sallah sai in kaiki gida ki huta, thank you Na’ima” ya faɗa yana wuceta ya fita daga gurin ta bishi da kallo tana murmushi kamar ba shine ya daburce ba jiya, Alhamdulillah ta sake maimaitawa tana kallon ƙofar.

Wajen ƙarfe 12 Na’ima na zaune a kujera a gefen gadon faɗila da bata jima da bacci ba, a hankali take ɓare ayaban da ke hannunta tana kallon machines ɗin da ke aiki a ɗakin kafin ta mayarda dubanta ga faɗeela da ke bacci hannunta dafe da cikinta, stress ɗin last night har ya saka ta faɗa lokaci guda Naima tayi murmushi kawai ta kai ayaban bakinta ta gutsura tana kallon wayarta da ta ɗauko ɗazu da Nasir ya maida ta gida jin yayi ƙara

“ why wont u just talk to me?” Ita fa zuwa yanzu abin sadiq ya fara bata tsoro, dan ko da ta dauko wayar ta tararda missed calls ɗinsa da messages ɗinsa sunfi a ƙirga, is he even okay? Ta tambayi kanta tana ƙara kallon message ɗinsa da ya sake shigowa “Navy colour yana miki kyau sosai” ta kalli navy colour abaya dake jikinta ta sake kallon wayar baki sake” dai-dai nan aka buɗe ƙofar ɗakin da sallama ta ɗago kanta tana amsawa, Nasir ne ya shigo first kafin shima ya shigo da sallama can ƙasa ƙasa, da mamaki take kallonsa har ya ƙaraso cikin ɗakin same posture, same authority. Ta ɗauke kanta a hankali ta mayar kan Nasir da ya zauna gefen bed ɗin faɗila wacce ta buɗe idanunta just now “how are u?” Nasir ya faɗa yana taɓa forehead ɗinta, ta masa murmushi “naji sauƙi but am weak” ta faɗa tana ƙoƙarin tashi zaune ya taimaka mata ya saka mata pilow ta zauna, sai lokacin ta lura da Ahmad dake tsaye a bayansa, cikin muryar marasa lafiya tace “ina wuni yaya Ahmad” ajiye abin hannunsa yayi a bedside yana kallonta “u scared us ai faɗeela” ta ɗanyi dariya kaɗan, “ya su Madam?” “Lafiya lau” ɗago kanta Na’ima ta yi ta dube sa jin faɗeela ta tambayeshi madam ashe ma yana da mata, Nasir ya dubi Na’ima yana murmushi “Na’ima ya jinya?” murmushinta mai kyau tayi masa “Alhamdulillah ina wuni yaya Nasir” sai kuma ta ɗan dubi Ahmad “ina wuni” Nasir ne kaɗai ya amsa, ko kuma Ahmad ɗin ya amsa bata ji ba oho bata sani ba, Nasir na kallon faɗeela yace “jiya fa kuka ta dinga yi, ƙarshe ni na haƙura da nawa tashin hankalin ina bata haƙuri” Faɗeela tayi dariya kaɗan tana dafa cikinta “u alright?” Ta gyaɗa masa kai kawai.

Nasir ya dubi Ahmad da ya koma jikin window ya tsaya ɗan nesa kaɗan sai kuma ya kalli Na’ima da ke danna wayarta, maida kallonsa yayi ga Ahmad yace

“dude, meet Na’ima my wifes cousin sis”

“Na’ima, this is Ahmad”

Ɗago kanta tayi suka haɗa ido, a hankali ta Sake gaishe shi bayan ta ajiye wayarta duk da bata yi niyya ba dan sarai ƙin amsa na farko da yayi ya mata zafi bata yi niyyar sake shiga harkarsa ba, amma rasa abin cewa bayan abinda Nasir yace ya sata gaishe shi “Lfy” ya faɗa a taƙaice yana maida dubansa ga Faɗeela “Allah ya ƙara sauƙi” ya faɗa yana ƙarasawa ya ajiye mata bandir ɗin kuɗi kusa da ledan da ya ajiye da farko faɗeela na murmushi tace “thanks for coming a gaishe min da anty Amira pls” “Zataji in sha Allah” ya faɗa yana nufar ƙofa, Na’ima tabi bayansa da kallo har ya fita, ita sai taga ma kamar ko bai gane ta bane? Ko is he still holding grudges tun rannan ne? Amma ai ta bashi haƙuri ai koh? Sai yanzu ma ta ƙara gane fuskarsa ashe ba sau biyu ƙadai suka haɗu a jirgi ba ashe shine ta buge a kamun faɗeela sannan ta sake haɗuwa da shi wajen dinner before ta haɗu da shi a airport, thats why his face looks familiar from day one.

Nasir yayi kissing hannun faɗeela yana faɗin “ill be right back baby” ya shafa cikinta sannan kafin yabi bayan Ahmad da sauri.

Ruwan goran gefenta Na’ima ta ɗauka ta buɗe tana ƙoƙarin kurɓa wani message ɗin ya sake shigowa wayarta, sai kuma wani again wani ya biyo bayansa.

“Baza ki amsa ba?”

“Tell me what i did wrong”

“I thought u miss me kamar yadda nayi naki”

“Talk to me pls”

Kallon saƙwannin kawai take yadda suke shigowa ɗaya bayan ɗaya, mamaki yaƙi barin fuskarta

“Answer ur damn phone”

Why are u doing this, it hurts”

“Ni’eema”

“Pls”

Wai miye hakan ke nufi ne? When did friendship ɗinsu ya kai har haka? A iya saninta weeks ago sadiq was someone da zata iya kira her bestfriend, wanda zata iya faɗa ma komai ba tare da ɗar ɗar ba, wanda babu wani abu mai kama da soyayya tsakaninsu sai ma zallar relating da each other, he relate da duk wani abu da take going through, yana sa taji damuwarta is his, yana sa ta manta damuwarta yayi boosting confidence ɗinta, amma ko kaɗan abu mai kama da soyayya baya tsakaninta da shi, ita sai yanzu take sake tunanin meyasa yaƙi bari ta sansa kamar yadda shi ya santa? Me yasa bata san komai game da shi ba even the smallest of things banda sunan siblings ɗinsa da adadinsu? ta ƙurawa wayarta idanu kafin ta ɗago idanunta ta kalli faɗeela da ta koma ta kwanta ta lumshe idanunta, kamar amsar tambayarta wani saƙonne ya sake shigowa

“I Love you Ni’eema, i always have, u owe me something, and i swear by my life ull be mine only mine Ni’eema, babu mai sonki duk duniya bayan ni, ill protect you, i promise u, dont ignore me, i can do anything!”

Afwan lovelies ???? kaina bisa wuya, ko wuya bisa ƙafa ne? How una dey talk am sef???????? gabaɗaya kun gigita ni ????

Jumu’at kareem my discussion board gang, sonku nake fisabilillahi, my day one’s, u guys are always in my Du’a, Allah ya muku albarka ya raya muku zuri’a, yan matan cikinku Allah ya baku mazaje na gari❤️

Chapter 19: Meant to heal

Washegari ƙarfe bakwai na safe, Na’ima na zaune gefen gadon faɗila tana sanye da loose wando da shirt kanta da gyale amma bata yafashi da kyau ba loosely ta sake shi, ta naɗe ƙafarta a kujeran tana sipping black tea da aka kawo mata daga kitchen ɗin asibitin, kwata kwata bata wani samu bacci ba jiya, sosai al’amarin sadiq ya tsaya mata a rai fiye da zatonta, a hankali take kurɓan tea ɗin tana kallon yadda machines ɗin cikin ɗakin ke beeping amma sam hankalinta ba a wajensu yake ba.

Ringing ɗin wayarta ya dawo da ita daga tunani tayi saurin kashe ƙaran kar ya tashi faɗila dake bacci kafin ta duba mai kiranta, ganin Mami ce ya sa ta miƙe a hankali ta fita a ɗakin tana gyara yafin jersey veil dake kanta.

“Whats wrong baby? Are u okay? Jiya kwata kwata baki kirani ba” Mami ta faɗa bayan ta amsa gaisuwar da Na’iman ke mata

“Lafiya lau Mami wallahi. Anty faɗeela ce bata da lafiya tun shekaran jiya da daddare, yanzu haka ma muna asibiti”

“Subhanallah, me ya same ta? Is she alright? Shine kuma baku faɗa ba kwata kwata? Hows she? And the baby?”

Ajiyar zuciya Na’ima ta sauƙe tana zama akan ɗaya daga cikin kujerun dake wajen,

“Taji sauƙi fa sosai Mami kawai dai basu sallame mu bane, amma da sauƙi jikinnata both she and the baby are perfectly fine”

“To Allah ya raba lafiya”

“Amin Mami ina su Aryan”

“Gasu nan suna ƙiriniya, yanzu kam ai sun haƙura sun bar nemanki”

“Allah sarki” ɗan shiru sukayi duka sai can kuma Mami ta fara magana

“Kamar yadda nake faɗa miki kullum, Nasan Faɗila na da ƙoƙari, i trust her, but be careful Na’ima pls, zaki haɗu da mutane kala kala dan Allah ki dinga kiyaye wa kinji?”

“In shaa Allah Mamina”

“Allah ya miki albarka”

A hankali ta amsa da “Amín” tana jin wani irin kewar Mami

Sun ɗan jima suna magana kafin Suyi sallama ta koma ɗakin, tararda faɗila tayi tana waya da mummynta ta ajiye wayarta a kan kujera ta wuce toilet.

Ƙarfe 12:30 na ranar aka sallami faɗila daga asibiti ganin babu wata matsala, duk da haka sai da likitar ta jaddada musu duk wani slight abdominal pain kar suyi ignoring su taho asibiti, sannnan ta huta na weeks though baby ɗin is stable. Faɗila gyaɗa kai kawai tayi tayi Nasir kuma na saurare shima.

Likitar ta dubi Nasir “ill write prescriptions before discharge ɗin, Allah ya tsare gaba and pls be more careful, no lifting, no stress, no driving”

Duk amsa mata sukayi tare da mata godiya, ko da aka sallamesu Na’ima ce ta riƙe jakan faɗila, Nasir kuma na riƙe da hannunta tana tafiya a hankali har mota, ya buɗe ya taimaka ta shiga, itama Na’ima ta zagaya ta shiga tana tunanin 2 days kenan bata je school ba, sai yanzu hankalinta ya karkarta can.

Ko da suka dawo gida sama Nasir ya haura da faɗila bayan yace da Na’ima ta huta itama cause kwana biyunnan shima ya san how stressed she was, hakan ya sa ta wuce ɗakinta, sai da tayi wanka ta shirya kafin ta janyo takardunta ta shiga karatu cause gobe definitely zata shiga school.

Zuwa dare ta je ta duba faɗila yafi a ƙirga, wacce ta warware sosai sai abinda baza’a rasa ba, bata jima sosai da kwanciya ba bayan ta kaima faɗila mint tea da ta mata da kanta bacci ya ɗauke ta kasancewar da wuri take son shiga makaranta washegari.

Washegari da wuri Yusuf ya sauƙe ta a school, ta wuce lecture building ɗin tana rataye da designer tote bag ɗinta kamar kullum. Bayan angama lecture cafe ɗin makarantar taje ta nemi abinda zata ci kafin next lecture ɗinta.

Zuwa yamma sosai ta gaji, ko da yusuf ya zo ɗaukarta ma da ƙyar ta amsa masa gaisuwar da yake mata ta shige motar tana sauƙe ajiyar zuciya.

Tunda aka buɗe musu gate yusuf ya shigo da motar Na’ima ke bin Mercendes maybach Gls 600 da akayi parking wanda bata san da shi ba a gidan da kallo, da tunanin motar wayece cause bata taɓa ganin motarba a gidan. ba tare da damuwa ba ta sauƙo a motar, ta nufi cikin gida, a hankali take tafiya har ta ƙarasa ƙofar palourn ta tura ƙofar ta shiga da sallama ƙasa ƙasa, takalmanta ta cire, tana gyara gyalen abayan jikinta ta nufi cikin palourn, tana jiyo muryar Nasir sama sama ta ƙarasa bakin palorn, ɗan dakatawa tayi daga bakin ƙofa na yan seconds tana kallon living room ɗin da mutanen cikinsa,

Ahmad na zaune a kan sofa ƙafarsa ɗaya akan ɗaya ya jingina bayansa da kujera yana sauraren Nasir dake sake masa bayanin yadda abin ya faru wanda zuwa yanzu ya faɗa masa yafi a ƙirga, beside him wata mata ce wacce ita dai Na’ima bata santa ba, kyakkyawa sosai black beauty, doguwa sosai saidai bata da wani aukin kirki, fuskarta ba kwalliya amma sosai fuskar ke glowing tana sanye da silk ɗin doguwar riga da ya mata kyau sosai da scarve ɗinsa, tana zaune very close to him tana danna wayarta kamar zancen da ake a ɗakin bai dame ta ba sai ma chewing gum da take taunawa fuskarta a haɗe.

Faɗila dake zaune kusa da nasir ta naɗe ƙafarta a hankali tana saurarar hirar da Nasir ke ma Ahmad dan tun bayan gaisuwa da kawo musu kayan motsa baki babu abinda ya sake haɗa ta da Madam ɗin ta dubi Na’ima da ke tsaye bakin ƙofa “kin dawo?” Hakan yasa duk suka ɗaga kai suka kalleta including Ahmad da Amira.

“Assalamu alaikum” ta faɗa daga bakin ƙofar tana ƙarasowa ciki duk suka amsa mata ta ƙaraso ta zauna a kan kujera opposite Amira tana ajiye jakarta akan kujerar a hankali, gaishe su tayi a hankali tana kallon Saif dake ɗaya gefen na babansa, wanda Nasir da faɗila ne kaɗai suka amsa mata gaisuwar suna tambayarta school, Amira kam sake ma haɗe rai tayi fiye da da ta mayar da kanta wayarta dan nan take kawai taji Na’imar bata mata ba babu dalili babu mafari, zuba ma Saif idanunta Na’ima tayi ganin yadda sosai yake kama da Ahmad kamar yayi kaki ya tofar ta mayarda idonta kan Ahmad karaf suka haɗa idanu dan shima ita yake kallo, sake gaishe sa tayi tana ɗauke idanunta daga cikin nasa da ƙoƙarin miƙewa

“Lafiya lau, how’s chool?” Ya tambaya yana kallonta still, fasa tashi tayi dan bata yi tunanin ma zai amsa ba, “Alhamdulillah” ta faɗa tana ƙaƙalo murmushi, ya gyara zamansa yana kallonta “wani course kike yi?” Nan take Amira ta ajiye wayar da take dannawa ta mayar da hankalinta kansa tana sake haɗe rai kamar zata yi bindiga “Accounting” Na’ima ta faɗa tana kallonsa ba tare da ta lura da irin kallon da Amira ke mata ba, “Good choice” ya faɗa a hankali, ta zata shikenan sai kuma taji muryarsa “wani makaranta?” Kafin ta amsa muryar Amira ta katse su “wow, so ure asking about her school now? Me zaka yi to da sunan makarantarsu?” Daga Na’ima har Ahmad da ma su faɗilar kallon Amira suka yi, Faɗila ta buɗe baki da niyyar Magana Na’ima ta miƙe tsaye a hankali dan ta gane matarsa ce ta ɗauki jakarta tana kallon Saif dake jikin Ahmad da baice komai ba amma daga dukkan alamu ransa ya ɓaci da abinda Amira ta faɗa
“Do u want to come with me?” Na’ima ta faɗa tana miƙa ma Saif hannu dan zuwa yanzu kwata kwata ji tayi zaman palourn ya isheta ɗakinta take so ta wuce, Saif ya kalli Ahmad gyaɗa mishi kai yayi ya sauƙa da sauri yayi wajenta Na’ima ta miƙa masa hannu ya riƙe hannunta suka wuce hanyar da ɗakinta yake, Amira ta bisu da harara amma ta gagara magana ganin yadda ya haɗe rai kuma bai kulata ba ita ta san ransa a ɓace yake in ba haka ba wallahi da ba zata bari ta tafi mata da ɗanta ba. Itafa haka kawai taji Na’imar bata mata ba sam, kafin su kai ga ɓacewa Faɗila tace “Abinci fa?” “Im not hungry naci abinci a makaranta”daga haka ta wuce tana riƙe da hannun Saif.

Tana buɗe ƙofar ɗakinta ta sauƙe ajiyar zuciya tana kallon Saif da har yayi cikin ɗakin,

“Wow is dis ur room?” Ƙarasawa tayi ta ajiye jakarta akan kujera tana kallon kyakkyawan yaron, sosai ya mata kyau, ta sunkuya tana kallonsa “yes dis is my room, miye sunanka?” “Saifuddeen Ahmad Yarwa, but everyone calls me Saif kema Saif zaki ce” dariya tayi tana kallonsa “are those ur mom and Dad?” Ta faɗa tana nuna masa ƙofa, bin ƙofar yayi da kallo sai ya girgiza mata kai alamun ah ah, da mamaki take kallonsa dan dai sosai take ganin kamannin Ahmad akan tasa fuskar “ba Mom and Dad bane Papa da Mami ne sunansu anty” dariya tayi tana cigaba da kallonsa harda durƙusawa “haba?” “Yes” ya faɗa yana ƙarasawa kan gadonta ya hau sama yana rarrafawa tsakiyar gadon “is dis ur bed?” Miƙewa tayi daga durƙuson da ya barta tana yi tana kallonsa tace “No its Saif’s” tashi yayi tsaye a kan gadon “No ba na Saif bane, na Saif is at home” tayi murmushi kawai tana zare gyalen kanta ta ajiye ta ƙarasa ta janyo bedside drawer ɗinta ta ɗauko chocolate guda biyu ta miƙa masa, sauƙowa yayi daga gadon ya zo ya karɓa, ta ɗaga shi ta zaunar kan gadonta ta sunkuya ta cire masa designer takalman yara dake ƙafarsa “kaga ka taka min gado da takalmi kuma babu kyau” ta faɗa tana tura baki, ƙyalƙyalewa yayi da dariya ta tsaya tana kallonsa yadda yake ta dariya kamar ta masa cakulkuli sai kawai tayi murmushi ta miƙe daga wajen ta wuce toilet ta barsa yana cin chocolate ɗin da ta basa.

Bayan awa ɗaya lokacin har tayi wanka ta canza kayanta ta kunna musu cartoon a laptop suna kallo suna cin cookies a ƙasan ɗakinta faɗila ta buɗe ƙofar ta leƙo ciki “to laifin daɗi ƙarewa Saif zo ur mum is calling u zaku tafi gida” miƙewa yayi da sauri Na’ima ma ta miƙe tana kallonsa “ɗauko shoes ɗinka in saka maka, ɗaɗi ma kake ji zaka tafi ka barni” wucewa yayi ya ɗauko takalman nasa ya kawo mata yana dafa kafaɗan ta while tana saka masa takalmin “ ill tell papa to bring me tomorrow ai” tana saka masa ɗayan takalmin tace “pinky promise?” “Pinky promise” ya faɗa yana yin waje da gudu, Naima ta miƙe tsaye tana binsa da kallo da murmushi akan fuskarta, Faɗila ta nufi ƙofa tana faɗin “ki zo kuyi sallama Na’ima zasu wuce” “toh” tace ta ƙarasa ta ɗauko hijab ɗinta ta saka ta biyo bayan faɗila har palourn, Ahmad da Nasir kaɗai suka tarar a tsaye a palourn Ahmad yayi gaba Nasir na biye da shi a baya suma sai suka bisu a baya “a bakin ƙofa Na’ima ta tsaya ta riƙe ƙofa tana kallon Faɗila da Nasir da suka rakashi har jikin motarsa wanda tuni Amira ta shige da Saif, Nasir ya bashi hannu “thank you so much dude” bashi hannun yayi suka gaisa ya dubi Faɗila “Allah ya ƙara sauƙi” “Amin mun gode yaya Ahmad, Allah ya kiyaye hanya” da Amin ya amsa yana zagawa dan shiga motarsa, Na’ima dai kallonsa kawai take yi, gani tayi ya ɗago kansa ya kalli inda take suka haɗa idanu da sauri ta saki hannun ƙofar ta koma ciki, buɗe motarsa yayi ya shige su faɗila suka ɗaga musu hannu har suka fita daga gidan kafin su dawo cikin gida.

A palour suka tarar da ita, Nasir na kallonta yace “Naima ya akayi” ya faɗa yana ƙoƙarin haurawa sama, “babu komai yaya Nasir” ta faɗa tana kallon Faɗila da ta zauna a saman kujera “Gobe ai bazaki je school ba koh?” Gyaɗa kai tayi tana ƙarasawa ta zauna akan kujera itama, “Eh gobe saturday ba zan shiga school ba, this week fa sau uku kaɗai naje school” faɗila tace “imam ɗinki amma zaizo gobe” “eh zaizo, kin tuna min ma ban iya inda ya koya min ba” “zaki sani ai” faɗila ta faɗa tana harararta, dariya kaɗan tayi, “ai zan koya”

“kar ma ki koya ɗazu muna waya da su Mami nace musu ai kina dagewa both school da arabic classes ɗinki, idan naga dugu dugu ai kiransu kawai zanyi ince musu fa accounting kaɗai kika saka a gaba banda fiƙhu da hadisi kar kije su miki tambaya su ɗauke ni maƙaryaciya” Naima ta dinga dariya “kema ai kinsan ina yi anty Faɗila, just that i cant pronounce some arabic alphabets well but im trying, kuma ai ko a newyork ina online classes so almost duk abinda imam ke koya min ma fa na iya su” “oshey” faɗila ta faɗa tana dariya, miƙewa Na’ima tayi ta wuce kitchen dan ɗibo abinci tana cigaba da dariya.

Tun a mota take kumbure kumbure ganin bai kulata ba har suka iso gidan, buɗe motarsa yayi ya fita ya wuce cikin gida ba tare da ya bi ta kanta ba, ta bi shi da kallo har ya shige kafin ta fara tashin Saif dake bacci a jikinta, sauƙo da shi tayi a motar ta wuce cikin gida yaron na biye da ita yana gyangyaɗi da ƙoƙarin faɗuwa, tana shiga palourn ta jira Saif ya shigo kafin ta wuce sama tana faɗa ma Saif ya tafi wajen Mary.

Ɗakinsa ta wuce ta murɗa ta jishi a kulle da makulli, ta ƙwanƙwasa a hankali jin bai buɗe ba ta tura baki ta wuce ɗakinta. Jakarta kawai ta ajiye ta zaro wayarta, missed calls ɗin Nuwaira da ta gani yasa ta shiga ƙoƙarin kiranta bata kai ga kira ba wani kiran Nuwairan ya sake shigowa “wai ina kika shiga ne nake ta kiranki kina ƙin ɗauka wannan ma ai iskanci ne” Amira tayi tsaki tana cilli da takalmanta “ƙawata ki bari kawai, kinsan bawan Allahn nan sai da ya sa naje?” Nuwaira tayi wani ashar “yasa kika je ina? Gidan wannan munafukin Nasir ɗin? Ba sai da nace miki kar kije ba?” Amira ta zare ɗankwalinta ta ajiye kan gado itama tana zaunawa akan gadon “ke kinsan jaraban da ya dinga min ne a gidannan? Bayan kece kika saka naƙi zuwa asibiti, ba yadda na iya dole na bishi muka je, dan munafunci ni ban ga ma alamar wani rashin lafiya ba da matar Nasir ɗin sai ma baƙin ciki da na kwaso a gidan yanzu haka ya wuce ɗakinsa ya rufe ƙofa kuma nasan ransa ne ya ɓaci”
“To fah, bayan kin bisa ɗin kuma me yake so?”
“Wai fa kawai dan nace akan me yasa zai tambayi wata banzar cousin ɗin matar Nasir ɗin makarantarta, to haka kawai me ya haɗa da ita da zai tambayeta wai wani course take yi kuma ina ne makarantarsu?” Nuwaira dake kwance ta miƙe xaune
“Bangane ba, cousin ɗin matar Nasir? Kuma a gidan take ko me?”
“Yo a gidan take mana tunda muna gidan ma ta dawo daga makaranta, banza ta wani zo tana lanƙwasa harshe da wani forced accent ɗinta harda ɗaukan Saif ta kai ɗakinta”

“Shine shi Ahmad ɗin yake fushi dan kin hana ya tambayi makarantarsu?”

“Ohon masa nima ban sani ba ya dai kulle ƙofarsa da makulli daga dawowarmu”

“Taɓdi to ai ƙawata wannan ba maganar waya bace, zanzo gidanki gobe..”

Da sauri Amira ta tare ta “Ah ah mu haɗu a gidan Mummyna ko kuma mu haɗu a eatry ni bana son fitina wallahi”

“Amma dai ke banza ce Amira wai yaushe kika fara jin tsoronsa ne?”

“Ni dai kawai mu haɗu a inda nace miki kawai”

“Ai shikenan, tunda haka kika ce” Nuwaira ta faɗa daga ɗayan ɓangaren bayan ta ja tsaki.

Na’ima na kwance akan gadonta da dare bayan faɗila taje ta kwanta tana karanta texts ɗin sadiq da ya mata throughout the day a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya ta buɗe whatsapp ɗinta ta shiga dm ɗinsa, nan ɗinma messages ɗinsa ta tarar har da voice notes bata bi ta kansu ba ta shiga masa reply “sadiq we need to talk” sai da ta ɗan dakata kaɗan kafin ta tura masa saƙon, kamar dama yana cikin dm ɗinta dan instantly taga ya ga saƙon nata, typing taga yana yi ta lumshe idanunta a hankali

“Why Ni’eema?” Saƙonsa ya shigo
“Meyasa kike min haka, u have no idea me nake ji Ni’eema”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved