⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 14: Chapter 14

“Anty Naeeeemmaaaa” juya wa tayi tana kallon Saif da ya fito daga motar bayan Ahmad ya buɗe masa child lock da ya saka, da matuƙar mamaki take kallonsa, “Saif?” Ta faɗa a hankali tana kallon yadda ya taho da gudu, tsugunawa tayi yana ƙarasowa ya shige jikinta yana ƙyalƙyala dariya, itama dariya tayi tana ɗago shi daga jikinta, sake koma wa jikinta yayi tana dariya tace “kai da waye Saif?” “Ni da papa, nace masa i promised u shine ya kawo ni, he said promise is a debt right?” Gyaɗa mishi kai tayi tana dariya “yes it is” “Anty Naeeema zamu iya ƙarasa cartoon ɗin da kika saka min rannan” kallon jakarta tayi kafin ta gyaɗa mai kai “ofcourse my love, amma sai in munje gida” daga haka ta ɗagashi daga jikinta tana kallon Yusuf dake jiranta ta masa alamu da tana zuwa, ta nufi Motar da taga Saif ɗin ya fito, duka glasses ɗin a ɗage suke bata ganinshi kwata kwata, ta ɗan saka hannu tayi knocking glass ɗin tana riƙe da hannun Saif, jin shiru ta sake knocking, Sauƙe glass ɗin yayi yana kallonta, ta cikin shades ɗin da ya saka a idanunsa just now, “how can i help u?” “Dariya abin ya so bata ta fuske “ina wuni Sir” can ƙasa ƙasa ya amsa da “lfy” “pls zan iya tafiya da Saif?” Kallonta kawai yake yi sai can yace “ki tafi da shi ina?” Tana kallonsa a hankali kamar mai contemplating tace “Gida?” Shiru yayi yana kallonta kafin ya ɗauke kansa daga kanta yana kallon farfajiyar makarantar, can kuma yace “come in” kallonsa tayi jin yace ta shigo motar, ta juya ta kalli yusuf, sai kuma a hankali ba tare da ta shiga ba tace “thank you but driver ɗina is here” “okay.. then drop Saif” tsayawa kawai tayi tana kallonsa da mamaki “kina ɓata min lokaci” ya faɗa yana kallonta, juyawa tayi ta bar wajen a hankali ta nufi Yusuf, da idanu ya bita yana kallon yadda take rike da hannun Saif har lokacin, bata jima ba ta juyo tana dawowa bayan yusuf ya shiga motarsa zai bar wajen, ya ɗauke kansa ya jingina kansa da Seat ɗin ya lumshe idanunsa.

Ganin ƙofar a buɗe yasa bata jira yace mata ta shiga ba ta buɗe gaba ta shiga da Saif akan ƙafarta ta kullo motar, sai da ya ɗan ɗauki seconds kafin ya buɗe idanunsa ya tada motar ba tare da yace musu komai ba, har suka isa gida bai ce musu komai ba banda shirme babu abinda suke tattaunawa da ita da Saif ɗin, ta gefen idanu yake kallonsu yadda abu kaɗan ke basu dariya daga ita har Saif ɗin, no wonder ya dame shi da batunta, yarintarsu ce iri ɗaya.

A gate yayi parking ba tare da ya shiga ba duk da mai gadi ya buɗe masa, “ill come pick him at night” ya faɗa yana kallonsu “okay, thank you for the ride” ta faɗa tana buɗe motar ta sauƙa, saifa ma ya sauƙo ta riƙe hannunsa suka nufi cikin gida, yana ta mata rigimar ta bashi jakarta tana ce masa da nauyi, har suka shige yana kallonsu kafin ya tada motar ya bar unguwar.

“Mr Sadiq Bulama” wata Nurse cikin scrubs ɗinta ta faɗa tana kallon sadiq dake zaune ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idanunsa a reception ɗin.

Buɗe idanun yayi yana kallonta, kafin a hankali ya miƙe tsaye, gaba tayi ya bita a baya, wani ƙofa ta isa da aka saka 302 kaɗai a jiki, ta ƙwanƙwasa ɗaya kafin ta tura ƙofar ta buɗe “come in” aka ce daga ciki ta shiga yana biye da ita a baya.

Ɗakin ba wani tarkacen haske, just a dim yellow light, sai doctor dake zaune akan kujerarsa da wani file a gabansa, ɗago kansa yayi yana kallon Sadiq kafin ya ɗan gyaɗa kai “Sadiq” ya faɗa yana kallonsa.

Ƙarasowa ciki Sadiq yayi hannunsa hannunsa ɗaya a aljihunsa, ba tare da ya amsa ba, ya zauna a kan kujera, juyawa Nurse ɗin tayi ta fita a ɗakin tare da janyo musu ƙofa, kusan mintuna arba’in da huɗu kafin sadiq ya fito a ɗakin, kwata kwata bazaka iya karantar fuskarsa ba, ba wanda ya kula ya fice daga asibitin, ko da ya shiga motarsa ya jima bai tada ita ba, ya jingina kansa kawai da kujera ya lumshe idanunsa, sai kuma yayi murmushi a hankali ya tada motar ya fice a harabar asibitin.

Sosai ran Amira ya ɓaci da shanyata da Ahmad yayi yau a gidansu, bayan yasan ba wai wani jituwa ke tsakaninsu ba, sanann kuma ya ɗauke Saif ya tafi sa shi, to ma ina ya kaisa?, a ɗakin Ammi ta wuni ko abinci su Yasmeen suke kai mata, tana kwance akan sofa tana Game, dama bata fara faɗa ma Nuwaira abinda ya faru ba duk da yanxu ma da ita suke magana, saboda tasan ran Nuwaira sai yafi nata ɓaci idan ta faɗa mata, tunda ba tun yau ba ta faɗa mata ta dawo daga rakiyar dangin mijinta ba sonta suke ba, jin ƙarar wayarta ta kalli mai kiran ɗan shiru tagi kafin tayi picking ta kai kunne “Mummy…” “dont mummy me, Gobe ina son Ganinki a gida, sannan babanki ma yana son yayi magana da ke, Amira ba dai duk abinda ba zamu huta ba shi kike so ke a rayuwarki koh? Kin fi son kiyi ta ɗaga min hankali kullum ko Amira?” Tura baki tayi tana ciro wayar daga kunnenta ta kalla ta sake mayarwa kunnenta “To ni me nayi?” Ta tambaya tana haɗe rai, “tambayata kike yi?, na faɗa miki i should see u a gidannan gobe gobe kinji na faɗa miki, kuma kinji na rantse miki idan kika kuskura kika ɗauko mini wata Nuwaira kika taho da ita wallahi sai ranki ya ɓaci, ko babanki bai isa ya hanani ci miki mutunci ba, tun farko ai shi ya janyo komai, amma ba komai.” Sake haɗa fuska Amira tayi “haba Mummy, wai me Nuwaira ta miki?” “Ubanki ta min, dama ban rabaki da yarinyar nan ba? Ko da yake ina zaki rabu da ita, tunda baku rabu tun Primary ba ai bazaku rabu yanzu ba koh?” Mummy ta faɗa cike da takaici.

“Nikam kawai shikenan ba dai kince in zo kuma kar na zo da ita ba Naji” “Hmm” kawai Mummy tace ta kashe wayarta.

Amira ta tura baki, ita da Nuwaira haɗin Allah ne, ita kanta ta san rabuwarta da Nuwaira zaiyi wuya, dama tun farko Mummynta ba son ƙawancensu take ba wadda ita bata kallon Nuwaira a matsayin ƙawa yanzu kamar yadda Mummy ke kallo, ba kamr Daddynta ba da yake taya ta son Nuwairan, Nuwaira tafi gaban ƙawarta ʼyar uwarta ce, da idan abu ya same ta takan fita shiga damuwa, kuma sai tayi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sama mata mafita, ƙawancenta da Nuwaira ba tun yau bane, dan tun suna ƙananu kasancewar iyayen Nuwaira ba masu ƙarfi bane yasa Dad da kanshi ya ɗauki Nauyin karatun Nuwairan ganin irin son da take ma Amira kuma itama Amirar take mata, wanda Amirar ce ma ta sa dole Dad ɗin ya sakata a makaranta saboda Kullum in za’a kaita makaranta Nuwairar sai dai ta zauna a bakin ƙofar gidansu tana kallonta.

A lokacin duk unguwar ba wanda ya kai Daddynta kuɗi ba kuma waɗanda suka kai Gidansu Nuwaira talauci a unguwar. Tun daga wannan ƙawancen suka zama aminai, dan har jiranta Amira tayi, wato ta faɗi jarabawa dan kawai Nuwaira ta iso ta su zauna a aji ɗaya, tun Farkon alaƙar mummy bata so ba, amma Dad yace its a good thing dole tayi shiru amma gut ɗinta is not telling her something possitive akan alaƙar Nuwaira da ʼyarta.

Suna gama waya da Mom ta ajiye wayar a gefenta tana jan wani guntun tsaki, ita fa shiyasa kwata kwata ta tsani zuwa gidannan jinta take duk a takure, in fact ba nan kaɗai ba she hates staying in anyones house talkless of gidan mother in law ɗinta, gashi har yanzu bai dawo ba, miƙewa tayi ta wuce toilet dan tun ɗazu aka yi magrib kuma bata yi ba har ana ƙoƙarin kiran isha.

Dama daga gidan Nasir office ya wuce to wrap up wani brief meeting, yana gamawa ya tsaya yayi sallah magrib da isha kafin ya nufi gidan Nasir dan ɗauko Saif, tunda ya bar su ɗazu yake tunanin yaron or yace yake tunaninsu shi da ƙawar tasa, duk da ba wani magana yayi da ita ba, but he cant get yadda tayi reacting towards Saif off his mind, sai da ma ya iso gidan ya fara tunanin yadda zai mata magana ta kawo masa Saif, akan dole yayi horn, mai gadi ya leƙo sannan ya buɗe masa gate ɗin, sai da yayi parking da kusan 3 minutes kafin ya fito a motar ya jingina da motar yana kallon entrance ɗin gidan, ganin haka mai gadi ya ƙaraso yana gaishe shi,

“Lafiya lau Jameel, ka ɗan kira min Saif a ciki” ya faɗa yana kallonsa.

“To ranka ya daɗe yanzu kuwa” ya faɗa yana nufar cikin gidan, Ahmad ya bishi da kallo kafin ya mayar da kansa kan wayarsa yana latsawa, danna door bell Jamilu yayi, mai aikin Faɗila ta buɗe ƙofa, yana washe baki yace “Alhaji yace Saif yazo” maida ƙofar tayi ta kulle ta koma ciki ya tsaya a bakin ƙofar kamar mai jira kafin kuma ya juya ya nufi Ahmad “Na isar da Saƙo Alhaji yana fitowa”. “Thank you” Ahmad ya faɗa yana maida idanunsa kan entrance ɗin. Jamilu ya koma bakin gate.

Suna palour da ita da Saif ɗin yana bata labari Mai aikin ta dawo “wai anzo ɗaukan Saif “ duk kallonta sukayi kafin Na’ima tace “okay” miƙewa tsaye yayi, itama ta miƙe tana kallonsa kafin tace “muje kace ma anty faɗila bye” a baya ya bita har sama, faɗila dake kwance a palourn sama tana kallo ta dube su “wai zai tafi gida” Na’ima ta faɗa tana zama da shi a jikinta, Faɗila ta miƙe zaune, “an zo ɗaukarsa ne ?” Gyaɗa mata kai tayi, Faɗila na kallonta tace “driver?” Shiru Na’ima tayi kafin tace “nima dai ban sani ba, Maybe, cause jamilu ne ya ƙwanƙwasa yace wai Saif ɗin yazo” “okay” faɗila ta faɗa tana mayarda dubanta kan Saif dake riƙe da hannun Na’ima “lallai Saif, to sai yaushe kuma kuma?” kafin ya amsa Naima ta riga shi “ai zai dawo soon ko champ” ta faɗa tana kallonsa, gyaɗa mata kai yayi, faɗila tayi dariya “to ka gaida Maminka” “toh” yace, Na’ima ta miƙe ta kama hannunsa suka sauƙa ƙasa, ɗakinta ta kaishi ta ɗauko wani ƙaramin jaka tana kallonsa tace “ina crown picture ɗin da mukayi drawing?” Ta faɗa tana ƙoƙarin saka masa ƙaramin backpack ɗin a bayansa, “i kept it in the backpack, just like u said!” Kissing goshinsa tayi ta Shafa gashinsa “Good boy” ta faɗa tana kama hannunsa suka nufi ƙofa, gabaɗaya ji tayi bata so ya tafi, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa yayi ba, hijab ne har ƙasa a jikinta wanda ta saka bayan ta shiga ɗakinta, ta buɗe ƙofar palourn suka fito tana riƙe da hannunsa, ɗago kansa yayi jin an buɗe ƙofar ya zuba musu idanunsa, a hankali take tahowa inda yake tana riƙe da hannun Saif, hango babansa da saif yayi yasa ya zare hannunsa a nata ya nufeshi da gudu yana nuna masa backpack ɗin da Anty Naeema ta bashi with all abubuwan da ke ciki, murmushi kaɗan yayi “kaji dadi, kace thank u?” “Yes i said Thank you ko anty Naeema?” Ya faɗa yana kallon Na’ima da ta ƙaraso wajen ta tsaya tana kallonsu, shiru tayi bata ce komai ba, Ahmad na kallonta yace “wai anty Naeema?” Ya faɗa yana cigaba da kallonta, saurin Gyaɗa masa kai tayi tana ƙaƙalo murmushi, dan ji tayi kamar tace ya bar mata saif ɗin ya sake tafiya ya barsu.

Buɗe ma Saif motar yayi ya shiga kafin ya rufe Saif ya ɗaga mata hannu “bye anty Naeema” itama ɗaga masa hannu tayi “bye my champ” rufe motar yayi kafin ya juyo yana kallonta, “Thank you anty Naeema” ya faɗa yana kallonta, kanta kawai ta iya gyaɗa mishi wani kunya na kamata wai anty naeema, ya zaga ya shiga motar, tana kallonsu har suka fice a gidan kafin ta koma ciki.

Sama Wajen faɗila ta wuce straight, faɗila ta ɗago kanta tana kallonta, “mutumin naki ya wuce kenan, shiyasa kika wani taho min nan” faɗila ta faɗa tana ɗan harararta na wasa, zama tayi tana kallon cikin faɗila da yayi ƙato, tace “Mummyn unborn” faɗila tayi dariya tana shafa cikinta bata ce komai ba.

Har suka isa gidan Ammi kunnensa bai huta ba, Magana ɗaya biyu ana ukun sai Saif yace “Anty Naeeeema ɗis, anty Naeema dat, har suka iso.

Amira na ganinsu ta sauƙe wani ajiyar zuciya kamar wacce ke kan ƙaya, tuni har ta miƙe tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta, bai ce mata komai ba yace taje tayi ma Ammi sallama ta zo su tafi gida, sama ta haura ta buɗe ɗaya ɗakin da Ammi ke ciki ta ƙarasa ciki a hankali tana kallon Ammi tace “Ammi zamu wuce gida dare nayi” kallonta kawai Ammi tayi daga kan Sallayar da take tace “to madallah, ku gaida gida” “amin” Amira ta faɗa tana nufar ƙofa, Ammi ta bita da kallo kawai,

ko da ta sauƙo ganin shi da su Yasmeen a palour ta sake haɗe rai ta nufi ƙofa, sama ya haura dan yi ma Ammi sallama shima Saif na biye da shi, suna shiga ɗakin ta ɗago kai ta kallesu, “daga ina? Tunda kuka tafi abinku sai yanzu kuke dawowa? Saif yau kam ba wajena kazo ba dama yawonka ka tafi da babanka” da Sauri Saif yace “No wajen Anty Naeema naje” ɗan kallonsa kaɗan Ahmad yayi kafin ya maida kallonsa ga Ammi dake kallonsa itama da alamar tambaya akan fuskarta, “Sai da safe Ammi” ya faɗa yana kawar da waccar maganar, itama ɗauke kanta tayi daga kallonsa “Allah ya bamu alkairi, kunci abinci kam?” “Amin, eh munci” ya faɗa a hankali yana nufar ƙofa, ya fice yana riƙe da hannun Saif ɗin, Ammi ta bisu da kallo kawai sai kuma tayi murmushi.

Yasmeen da Maryam suka rako su har mota, suna ma Saif wasa, ita dai Amira ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ta buɗe front seat ta shige ta rufe motar, buɗe baya yasmin tayi ta saka Saif suna ɗaga masa hannu suka rufe motar, Maryam na kallon Ahmad tace “yaya dan Allah kar ka manta” gyaɗa mata kai yayi, “text me idan na manta” “to yaya thank you so much” zagawa yayi ya shiga motar ya tada suka nufi gida.

Tun a hanya Saif yayi bacci, ko da suka iso gidan, yana gama
Parking Amira ta sauƙo ta buɗe backseat ta ɗauki Saif da ipad ɗinsa ta buɗe sabon backpack da ta gani a motar a tunaninta shi ya saya masa, ganin tarkacen wasa da kayan ciye ciye ne a ciki ta rufe ta ɗauki jakan kafin ta ɗaga Saif ɗin ta wuce cikin gida.

Sai da har suka shige kafin ya sauƙo a motar shima ya nufi cikin gida, sama ya haura ya wuce ɗakin da yake anfani da shi yanzu a matsayin nasa, dama tun bayan da Nuwaira ta kwana masa a ɗaki bai sake anfani da ɗakin ba, ya faɗa wanka, bayan ya fito yana shiryawa Amira ta shigo sanye da kayan bacci, ta ajiye tray ɗin hannunta dake ɗauke da flask ƙarami mai kyau a gefen bedside ta haura saman gadon tana kallonsa, ɗauke kansa yayi, ya ƙarasa shiryawa da yake yi ya feshe jikinsa da turaruka.

Ɗaya side ɗin bed ɗin ya ƙarasawa ya haura ya kwanta tare da kashe switch ɗin ɗakin ya bar dim one kaɗai dake gefen bed ɗin, ya juya mata baya, lumshe idanunsa yayi dan sosai turaren da ta saka yake kashe masa jiki, a hankali ya buɗe idanun jinta a jikinsa ta baya, ta saka hannyenta duka biyu ta zagayo su a ƙirjinsa, ta kwantar da kanta a bayansa, ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali, jin abinda take masa ya kasa daurewa ya juyo gabaɗaya yana janyota jikinsa ya haɗe bakinsu……

A hankali yake shafa gashinta tana kwance lamo a kirjinsa tana bacci, wanda shi sam ya gagara baccin, saman ɗakin ya zubawa idanunsa yayi nisa acikin tunanin da yake yi, a duk sanda wani abu zai shiga tsakaninsa da Amira yakan tsinci kansa a irin wannan yanayin wanda Allah ma ya sani yana iya ƙoƙarinsa duk wanann shekarun ganin wani abu ya canza a zuciyarsa game da ita amma ya kasa, more especially with her giving him more reasons everyday to feel same, lumshe idanunsa yayi yana cigaba da tunanin da yake yi da sauri ya buɗe idanunsa jin abinda ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa a daidai wannan lokacin, ya ɗan ja tsaki yana zareta a jikinsa jin yadda ta ƙanƙamesa kamar zata koma cikinsa, sauƙa yayi a gadon, ya wuce toilet yana sake kawar da tunanin da zuciyarsa ke bijiro masa da ita da ke sake birkita masa lissafinsa.

Har Asuba idanunsa biyu, ya ɗaga kansa daga kan sallayar da yake ya dubi Amira da ke sake dunƙulewa a cikin bargo kamar mage, jin kiran Sallah ya sa ya miƙe ya ƙarasa gefen gadon, hannu yasa yayi tapping ƙafarta “Amira, Amira…” “uhmmmm” ta faɗa ba tare da ta buɗe idanunta ba “ki tashi kiyi Sallah” “toh…” ta faɗa cikin muryar bacci tana buɗe idanunta ta kallesa, ganin yana tsaye still yasa ta miƙe zaune tana jan bargon ta rufe jikinta, “Na tashi…” juyawa yayi ya nufi ƙofa dan tafiya masalllaci, tana jin rufe ƙofarsa ta sake komawa ta kwanta tare da jan bargon ta rufe har kanta.

Bai dawo gidan ba sainda gari yayi haske, Yana shigowa ɗakin Saif ya shiga ganin yana bacci ya shafa fuskarsa, a hankali ya buɗe idanunsa “salat” ya faɗa yana kallonsa ganin idanunsa cike yake da bacci, juyawa yaron yayi cikin plenty pillows ɗin da suke kan gadon ya cigaba da baccinsa, bai sake tashinsa ba ya miƙe ya fice a ɗakin.

Jin ƙarar ruwa a toilet alamun wanka yasa ya ɗan ja tsaki, ya zare jallabiyarsa ya bar dogon wando ya ƙarasa ya hau gadon bayan ya kakkaɓe, ya zauna yana janyo laptop ɗinsa dake gefen side ɗin gadon ya kunna, dan sam baya jin baccin though kwata kwata baiyi baccin ba daren jiya, ɗaure da towel ɗinsa ta fito kanta na ɗigan ruwa ta ƙarasa gaban madubi tana goge gashinta.

Kallo ɗaya ya mata ya cigaba da abinda yake yi ta gama abinda zatayi a gaban madubi ta zura jallabiyarsa da hijab ta tada sallah.

Minti uku har ta idar ta cire hijab ɗin ta ajiye akan daddumar tana kallonsa.

“Albi, na manta ban faɗa maka ba, mom tace yau inje wai she wants to talk to me bout something”

dakatawa yayi da abinda ya ke ya ɗago ya kalleta
Ta miƙe tana naɗe sallayar “tun jiya nake so in faɗa maka mantawa nayi” maida kansa yayi ya cigaba da abinda yake yi ba tare da yace mata komai ba, ƙofa ta nufa ta fita a ɗakin sai alokacin ya kalli ƙofar kafin ya mayar da hankalinsa kan aikin da yake yi, jin ya fara jin bacci yasa ya kashe laptop ɗin tare da kashe wutan ɗakin ya bar dim one ɗin ya shige bargo ya lumshe idanunsa.

Kusan ƙarfe 10 na safe ya buɗe idanunsa a hankali yana bin room ɗin da kallo kafin ya miƙe zaune a hankali, sauƙar da ƙafarsa yayi kan floor ɗin ya miƙe tsaye ya wuce toilet.

Sai kusan ƙarfe 11:30 ya fito daga ɗakinsa, a hankali yake sauƙa ƙasa, Mary dake bama Saif abinci a baki ta gaishe sa ya amsa a taƙaice, saif ya ture abincin ya nufe sa “papa Mami taƙi taje dani..” sai a lokacin ya tuno Amira tace masa zata fita and he didnt remember telling her taje, kallon Saif ɗin yake kamar shine zai tambaya inda Amirar taje kafin ya juya ya koma sama da wayarsa a hannunsa.

“Wato Amira duk abinda nake faɗa miki a rayuwarki shiga suke ta kunnen hagu suna fita ta kunnen dama koh?, ban raba ki da Nuwaira ba dan ubanki”

Amira dake kwance a kujera a gefen babanta cikin katafaren palourn gidansu ta ɓata rai tana tura baki, Daddynta ya dubi Mom

“haba madam, meyasa kike irin haka ne?”

“Bangane meyasa nake irin haka ba, Nuwaira fa ba ƙawar arziƙin Amira bace, an faɗamin abinnan ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, ance min in har Amira bata rabu da Nuwaira ba wallahi zatayi dana sani amma ina magana sai ku dinga mayar ni kamar bansan me nake yi ba, sau nawa dan ubanki zance miki kar ki sake yawo da yarinyarcan, ina ni kike so ki dinga ɗagawa hankali?”

Shiru Amira tayi bata amsa ba, Dad dake kallon Mummy ya wani ja dogon tsaki “Da Nuwaira zata cuci Amira ai da ta jima da cutarta shekara nawa suna tare bata cuceta ba sai yanzu ne xata cuceta, wanda ya faɗa miki bai faɗa miki gaskiya ba, my daughter loves Nuwaira and she loves her too, ban ga meyasa kike son rabasu ba”

“Au wanda ya faɗa min ya faɗamin ƙarya ma kake cewa? Sanin kanka ne ai baya ƙarya wallahi, dan da yana ƙarya da ʼyar taka bata auri zaɓin ran nata da kayi iya ƙoƙarinka including blackmailing ubansa ya aureta ba yaƙi”

“Dama nasan sai kin ɗauko wannan maganar” ya faɗa yana miƙewa tsaye, ya saɓa babban rigarsa yana kallon Amira

“Dont mind ur mother, duk wanda kike so muna tayaki sonsa”

“Eh ina taya ta son wanda take so mana, shiyasa har na yarda ta auri wancan yaron da ba wani girmama mu na kirki yake yi ba, sai yaga dama yake zuwa ya gaishe mu, da naga dama ai da na raba aurennan tun ba yau ba, amma kaga Nuwaira bazan taɓa tayata sonta ba tunda har akace min ba alkhairi a tarayyarsu, kaga ƙarshe idan ta cuce ta ai ni xata bari da jinya da lallashi”

Tashi daga kwance da take Amira tayi tana kallon mummynnata

“wo, please oo, ni kar ki kira sunan mijina ko aurena wajen kowa bana so”

wani harara Mummy ta ɓalla mata kafin ta mayar da hankalinta kan mijinta da ya nufi matakala yana faɗin “sai na dawo, madam ki mata a hankali yarinya ce, please”

Ya faɗa yana sauƙa matakalan yana shafa cikinsa.

Sai da Mummy taga ya ɓace duka kafin ta juyo tana kallon Amira “kina ji na…?”

Kafin Mummy tayi magana wayar Amira ya fara ƙara, kallon wayar tayi ganin mai kiranta ta kalli Mummy, ɗauke kanta Mummy tayi bata ce mata komai ba, ɗaukar wayar tayi bayan tayi rolling idanunta ta kai wayar kunne a hankali tace

“albi.”

“When did i give u the permission to leave this house?” Ta jiyo deep muryarsa very steady and calm.

“Bangane ba, i told u zanje wajen Mummy” shiru yayi wanda ita tasan ma’anar shirun tasa, sai can yace

“I heard u ask, i didnt say yes” kallon Mummy tayi dake kallonta tana mata alama da hannu kan me yake cewa , ta tura baki

“Amma gidan Mummy ɗinne problem dan naje?” Nan da nan Mummy ta haɗe rai gane maganar da suke yi

“Pack and come home immediately!” Kafin ta amsa har ya katse wayar.

Ta tsaya da wayar a kunnenta shiru tana kallon Mummy kafin ta zare wayar a hankali,

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved