Chapter 15: Chapter 15
“Miye wai?” Mummy ta tambaya tana kallonta
“babu komai, kawai zan wuce gida yanxu Mummy if thats all maganar da dama kika saka naxo saboda shi” Mummy na mata wani kallo tace “cewa yayi ki dawo yanzu ko me?”
“Ah ah kawai ni naga daman tafiya yanzu”
“Hmm, ke kike sani, bazaki tafi da wancan turaren ba dai saboda azababben taurin kai koh?”
“Mummyyy” ta faɗa tana miƙewa ta wuce bedroom dan ɗauko jakarta, Mummy ta bita da kallo.
Tana shigowa da motarta gidan tayi parking tana kallon space ɗin taga babu motarsa alamun ya fita a gidan, haɗe rai tayi ta sauƙo a motar da jakarta a hannu ta nufi cikin gida, sai da ta ƙare ma palourn kallo kafin ta kalli hanyar kitchen jin muryar Mary dake can tana aiki tana waƙa, tsaki tayi ta wuce sama, ta jefa jakarta a kujera, to ma miye anfanin wani ɗaga jijiyoyin wuya ta dawo gida bayan ya fita shi? Uban me zata masa a gidan, ta ɗauka zata dawo ta same sa waiting for her sai tazo taga wayam, ta ja tsaki ta wuce bedroom ɗinta.
Parking Ahmad yayi kafin ya sauƙo a motar yana saka sunglasses a idanunsa ya nufi cikin building ɗin, a hankali yake amsa gaisuwar da Ma’aikata ke miƙo masa, elevator ya shiga ya danna third floor, ƙofar na buɗewa ya fito yana tafiya a hankali har ya isa office ɗin Nasir, secratary ɗinsa ta gaishe shi ya amsa a taƙaice tare da buɗe ƙofar office ɗin ya shiga, Nasir dake zaune a kujerar office ɗin ya ɗago kansa daga files ɗin gabansa yana kallon Ahmad har ya ƙaraso cikin office ɗin da sallama ciki ciki, kujera ya wuce ya zauna ya jinginar da kansa ba tare da yace masa komai ba, shima Nasir ɗin bayan amsa sallamar maida hankalinsa yayi kan abinda yake yi, har ya ƙarasa kafin ya miƙe yana zare rigar Suit ɗinsa dake jikin kujera ya riƙe a hannu ya ƙaraso kan kujerar yana kallon Ahmad ɗin “how far?” Buɗe idanunsa yayi ya kalleshi, yana zare sunglasses ɗin idanunsa da gyara zamansa “gud” ya faɗa yana ƙare ma office ɗin kallo, shima Nasir kallon office ɗin yayi ganin shi Ahmad ɗin ke kallo kafin ya dawo da hankalinsa kan Ahmad “before u ask, yeap nayi renovation, ni fa na manta rabonka da office ɗinnan, yau ma dai nayi mamaki wallahi” ya faɗa yana ajiye rigar hannunsa ya miƙe tsaye
“eh kai yaushe rabonka da nawa office ɗin?”
Dariya Nasir yayi yana ƙarasawa coffee machine dake cikin office ɗin ya fara making coffee, “okay kawai a bar maganar, amma kaima kasan wa ya fara”
Bai amsa masa ba har ya gama haɗa coffee ɗin yazo ya miƙa masa ɗaya, shima ya ƙarasa kan kujerarsa yana riƙe da ɗaya ya zauna yana kallonsa “so whats up” ya faɗa yana kurɓan coffee ɗin yana kallon Ahmad dake riƙe da mug ɗin ba tare da ya kai baki ba.
“Wifey told me about kaima Naeema Saif da kayi, is there something i should know?” Sai lokacin ya wani kallesa ya kafesa da idanu.
“Something like?” Ya tambaya yana kallonsa tare da sake haɗe rai, dan dariya Nasir yayi yana ajiye mug ɗin
“nothing mana, kawai nayi mamaki ne, dan ban taɓa tunanin zaka yi hakan ba”
“Yes i did, saboda Saif insisted, ba yadda zanyi da shi ne shiyasa na kai shi”
“Oh i see, Allah sarki, har ya saba da ita haka kenan, Allah sarki” ya faɗa yana kallonsa harda tagumi
“Eh, nima nayi mamakin sabon nasu”
“To ai ba abin mamaki bane, kawai jininsu ne ya zo ɗaya”
“I thought as much”
Wani murmushi Nasir yayi bai sake cewa komai ba, ganin Ahmad ɗin ya miƙe yasa yace “wai har zaka wuce?”
“Eh” ya faɗa yana ajiye cup ɗin coffee ɗin a kan table ɗin dake wajen,
“Ba na taka maka toh” Nasir ya faɗa yana miƙewa tsaye shima.
“Dont bother, na san hanya” daga haka ya nufi ƙofa, Nasir ya bishi da kallo har ya rufe ƙofar kafin ya koma ya zauna yana juya kujararsa da murmushi kwance akan fuskarsa.
Sadiq na kwance akan gadon ɗakinsa lulluɓe da bargo, a hankali ac ɗin ɗakin ke aiki though ba’a ƙure yake ba, message ɗin da ya shigo wayarsa ya sa ya janyo wayar a hankali yana kallon sunan Na’ima dake kan screen ɗin “kaci abincin?” Kallon message ɗin yayi tayi kafin a hankali ya mata reply “yes na ci kaɗan, but am still weak.” Kiranta ne ya shigo, ya ɗaga ka kai kunnensa yayi shiru “Sadiq..” lumshe idanunsa yayi for almost 30 seconds kafin ya buɗe a hankali, “jikin ne har yanzu?” Ta tambaya jin yayi shiru.
“I dont want to bother u” ya faɗa a hankali kamar ba shi ba.
“Kaima ai kasan ban sani bane sadiq, u didnt tell me”
“Ta yaya zan faɗa miki when u dont pick ur calls”
“Karatu nake yi ne bangani ba ai, to kayi hakuri” ta faɗa a hankali more like lallashi.
“Hmm” kawai yace yana komawa ya kwanta rub da ciki a kan gadon ya saka wayar a speaker, yana kallon hotonta dake fuskar wayar.
“Na’ima pls tell me u love me” ya faɗa yana saka yatsansa ya shafa fuskarta dake kan screen ɗin, ya ƙurama ƙaramin bakinta idanu, jin tayi shiru ya ɗan dakata da abinda yake yi.
“Kaje ka ga likitan? I want u to get better”
“Naje jiya” ya faɗa yana cigaba da kallon fuskarta akan screen ɗin
“Okay.., Allah ya baka lafiya” ta faɗa a hankali, ta so ta tambaya me likitan yace amma kuma sai ta fasa kawai
“Amin, i miss u” ya faɗa kamar mai raɗa
“I know, get well soon” itama ta faɗa tana miƙewa ta zura takalmanta masu taushi da take yawo da shi a gidan ta nufi ƙofa
“Zan kira anjima inji ya jikin, ka daure ka dinga cin abincin kaji?”
Gyaɗa mata kai kawai yayi kamar yana gabanta “okay bye” daga haka ta katse wayar tana fita a ɗakin dan xuwa duba abinda ta ɗaura a kitchen dan yau ita ke girki da kanta dan bata je school yau ba, though tana da lecture amma da yake ɗaya ne she decides to rest at home.
Bayan kwana 2
Ƙarfe goma da rabi na dare Na’ima na zaune akan gadonta ta naɗe ƙafanunta tana flipping through pages, ga textbook a gefenta da ke buɗe half-highlighted, da glasses masu haske a idanunta da highlighter a hannunta, ga laptop ɗinta a buɗe akan gadon, spreadsheets ko ina akan gadon. jin knocking ta ɗaga idanunta tana kallon ƙofar, faɗila ce ta turo ƙofar ta leƙo ciki tana kallonta “Na’i” murmushi ta mata “Na’am anty” ƙarasa shigowa tayi baby bump ɗinta daya turo sakekken shirt ɗin jikinta Na’ima ta kalla kafin tayi murmushi “mummyn unborn” ƙarasowa Faɗila tayi hannunta a aljihun maternity wando dake jikinta, “tunda baki ce mana sai da safe ba mu munzo mu ce miki” ta faɗa tana zama da ƙyar a gefen bed ɗin.
Dariya Na’ima tayi tana ajiye highligher ɗin hannunta “Ai na ɗauka kin kwanta already, more especially da yake gobe is ur day, by the way happy Anniversary in advance anty Faɗila” Dariya faɗila tayi tana gyɗa kai “yeah 1 sweet year already” duk sukayi dariya.
“Nasir is taken me out tomorrow, ki shirya muje tare”
Da mamaki take kallon faɗila kafin ta ƙyafta idanu “Ni kuma?”
“Eh mana ya kamata, its our happy day, ke kuma ure part of our home, at least zaki samu ki sha iska ki huta wannan irin karatu da kike ba dare ba rana, Monday to friday”
Murmushi Na’ima tayi tana mayar da kanta tayi resting da jikin gadon,
“Anty Faɗila i’d love to, but bazan iya bin ku ba, kinga nace miki ina da accounting ethics presentation ranan monday, kuma har yanzu bamu gama organising case study group slides ba”
Faɗila na kallonta tace “ ɗan hour 2 ko uku dai wont kill u”
“Na sani, but kinga breakdown fa zamuyi na financial malpractice in nigerian firms, idan ban maida hankali ba ill look unserious” ta faɗa tana kwaɓe fuska.
Murmushi faɗila tayi cike da alfahari da ita tace
“always the serious one, naji, idan mun dawo sai muyi celebrating a gida tare, dan dole ki bar karatunnan ko kuma dan dole in cusa miki cake”
Dariya sosai Na’ima tayi “deal kuma kar ku manta ku taho min da chocolate”
Miƙewa faɗila tayi “naji, sai da safe accountant of the year”
“Goodnight” ta faɗa tana mayar da kanta kan screen ɗinta amma har lokacin da murmushi kwance a fuskarta.
Washegari asabar da ya kama ranar anniversary ɗin su Faɗila, tun sassafe ta tashi tayi wanka ta shirya cikin atampa riga da skirt dai dai jikinta, ta ɗauko principle notes ɗinta ta dawo palour ta zauna tana revising, sai wajen ƙarfe 12:30 faɗila da Nasir suka sauƙo daga sama, ta ɗaga kai tana kallonsu ganin yadda suka yi kyau sosai, faɗila na sanye da flowing dogon riga peach colour da bai hana baby bump ɗinta nunawa ba, tayi light make up a fuskarta tayi kyau sosai, Nasir na riƙe da hannunta suna sauƙowa a hankali, yana sanye da kaftan fari ƙal da ya masa kyau shima, murmushi ne yaƙi ɓacewa a fuskarta ta janyo wayarta tana musu hoto da video, “aww” ta faɗa tana dariya har suka ƙaraso palourn, Nasir na murmushi yace “kema ki kawo saurayinki mu miki aure” ɓata fuska tayi “Ni bani da saurayi” Faɗila ta harareta “shi kuma sadiq ɗin fa?” Ƙin amsawa tayi Nasir yayi dariya “wato denying saurayinki kikeyi?” Shiru tayi taƙi amsawa tana kallon Faɗila, Faɗila ta ɗanyi dariya “to naji ba saurayinki bane, ina dai har yanzu bazaki bi mu ba koh?”
Murmushi tayi tana ɗaura ƙafafunta akan kujera “Sai kun dawo” dariya suka yi duka, Nasir yace “munji, amma just know that u arent touching our cake too, are u even sure Naima ba so kike mu tafi ki kalli netflix ɗinki in peace ba?”
Tana dariya itama tace “baza’a yi haka ba ko anty faɗila, kuma Allah yaya Nasir karatu zanyi”
Dariya kawai faɗila tayi bata ce komai ba, suka nufi ƙofa, miƙewa tayi tabi bayansu, har suka shiga mota kafin ta ɗaga musu hannu ta koma ciki, tana jin kaɗaici, yau ita kaɗai zata wuni fa kenan a gidan, amma kuma ita bazata iya binsu ba, they should have their moment tunda anniversary ɗinsu ne, kitchen ta wuce jin yunwa ya far damunta.
Ahmad na zaune a mota a parking space ɗin gidansa yana danna wayarsa ya kwantar da kujeran, Saif kuma na backseat yana kwance yana kallon kids youtube a ipad ɗinshi, tun ɗazu suka dawo daga gidan Ammi, kawai he wasnt in the mood na shiga cikin gidanne, Saif ya ajiye ipad ɗin ya tashi tsaye akan seat ɗin ya tsallako tsakanin kujerun front seat yana kallon Ahmad ɗin “Papa” “uhm” “pls zamuje wajen anty Naeema?” Ba tare da ya kalleshi ba yana cigaba da danna wayarsa his face expressionless yace
“No”
“Please” ya faɗa yana kwaɓe fuskarsa, dakatawa da abinda yake yi yayi ya ɗago ya kalli yaron, sometimes Saif idan yayi abu ji yake kamar yafi ƙarfin shekarunsa, yana kallon Saif ɗin yace
“i Said No!” Shiru yayi yana kallonsa kafin ya koma back seat ɗin ya kwanta baice masa komai ba, mayar da hankalinsa kan wayarsa yayi yana cigaba da dubawa, kusan 5 minutes Saif ya sake tashi ya dawo yana kallonsa yace
“to papa can u call her?, ina son in ce mata wani abu”
Kallonsa Ahmad yayi na few seconds kafin ya sauƙe ajiyar zuciya “okay”
Call log ɗinsa ya shiga, sai kuma yayi shiru yana tunanin to da yace masa okay ai shi bashi da ma lambar yarinyar.
Number Nasir yayi Dialing, yana resting kansa da kujera, sai da ya kusa katsewa Nasir ya ɗauka
“Assalamu alaikum” Nasir ya faɗa daga ɗaya ɓangaren
Amsawa Ahmad yayi, kafin ya ɗanyi shiru, sai can kuma yace “kana gida ne?”
“Nope, out with wifey, ko ka manta yau anniversary ɗinmu”
“Ohhh” ya faɗa a hankali yana kallon Saif dake kallonsa.
“So whatsup?” Nasir ya faɗa dan dai yasan kiran da dalili shiyasa ma ya ɗaga dan da wani daban ne ya kira sa ma ba ɗauka zaiyi ba.
Sai da ya ɗan yi shiru kafin yace “um that girl..”
Nasir ya katse sa “which?”
“Wanda take gidanka mana, Saif wants to talk to her wai, sai damuna yake yi, nayi zaton ko kana gida ne”
Nasir ya jingina bayansa da kujera yana kallon Faɗila dake sanye da spa robe wanda aka rubuta orchid blu a jiki, dan yanzu haka suna spa session ne na orchid blu, wato private luxury spa da garden restaurant dake ikoyi, daga nan kuma zasu je for thier anniversary lunch, sannan sai anniversary potrait da Faɗila ta shirya musu, and many more, lumshe idanunsa yayi ya buɗe kafin yace “Na’ima?”
“Is that her name?” Ya tambaya yana ɗauke idanunsa daga Saif ya Mayar window
“No its urs, zaka ce baka san sunanta bane ko iskanci” shiru ya masa
“So kake a bata wayar?” Nasir ya sake tambaya
“No dont worry ka barshi kawai.”
Ɗan dariya Kaɗan Nasir yayi,
“Muma bama gida anyway, she didnt come with us kuma, sai dai in number ɗinta zan tura maka sai ka kirata direct”
“Dont bother, sai anjima” daga haka ya katse kiran, Ya dubi Saif dake kallonsa, yana shirin magana text ya shigo wayarsa, dubawa yayi yaga Nasir ne ya tura masa number, shiru yayi ya ƙurawa ma lambobin ido kamar mai contemplating sai kuma yayi dialing ɗin lambar.
Har sai da wayar ya kusa katsewa kafin aka yi picking, ya zuba ma screen ɗin idanunsa rasa abin da zaice.
Naeema dake kwance saman kujera a palour ta gaji da karatun dama tun ɗazu, ta kwanta kenan sai ga kira daga special numbers dake yawo a screen ɗinta, sai da ta gama ƙare ma number ɗin kallo tana tunanin wa zai kirata da Number, a irin wannan lokacin, ganin zai yanke ta sa hannu tayi picking ta kai kunne tayi shiru, jin shiru sai a little hum na mota ya sa ta ciro wayar a kunnenta ta kalla ta sake mayarwa a hankali tace “Asslm alaikum” kafin ta tambayi whos on the line pls ta jiyo Muryar Saif “Anty Naeeeema” buɗa idanunta tayi bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, “My champ” “yes Anty Naeema its me, na ce papa ya kiraki i want to tell u something” tana dariya da gyara kwanciyarta tace “haba?, to tell me ya akayi?” Shiru yayi yana kallon Ahmad da ke kallonsa ya jingina da kujera kuma yana jin duk convwrsations ɗin nasu kasancewar a handsfree wayar take, “ban san abinda zan ce miki ba anty Naeema” murmushi ne ya kufce ma Ahmad, ya juyar da kansa window cause he knew it already babu abinda Saif zai faɗamata dama he just wants to talk to her, yana mamakin sosai irin son da Saif ke mata cause ko su Ammi baya matsawa haka yace sai ya musu magana ko a kaisa wajensu. ƙaramar dariya tayi daga cikin wayar “i miss you Saif” ta faɗa a hankali da murmushi akan fuskarta “zaka iya ce ma Papa ya kawo ka pls?” Ta sake faɗa not knowing shes on speaker” ɗan juyowa yayi ya kalli wayar, Saif ya tashi tsaye a kujera da wayar a Hannunsa “ai yace barai kawo ni ba” “haka yace? But why?” Ta faɗa tana marairaicewa kamar zata ma Saif ɗin kuka “kaga Saif am alone at home, kuma na gaji da karatu, kazo sai muyi wasa da drawing” kallon Ahmad Saif yayi, Ahmad ya ɗauke kansa kamar bai san me suke yi ba, a zuciyarsa kuma murmushi yake yi, now ya gane me yasa Saif ya maƙale mata, shes his play mate, wai kazo muyi wasa, baisan me yasa ba but he finds hirar tasu interesting “Papa pls zaka iya kaini?” Muryar Saif ta katse shi, shiru Na’ima tayi jin ya ambaci papa dan bata yi zaton ma yana wajen ba, ko da yake Maybe wayarsa Champ ɗin ke using, shiru itama tayi tana jiran amsarsa da Addu’ar Allah ya sa ya yarda, “No!” Ta jiyo Muryarsa deep and steady, Naima ta sauƙe ajiyar zuciya bata ce komai ba, kukan Saif da taji a kunnenta ya sata buɗa ido da sauri, sai kuma ta hau faɗin “Champ! Saif!” Amma ina ko amsata baya yi tana ji yana kuka ta rasa me zatayi.
Da mamaki Ahmad ke kallonsa ganin ya jefa wayar kan kujera ya kama kuka, “what is it?” Ya tambaya yana kallon Saif ɗin “Anty Naeema…”. “U said u want me to call her i called, Saif idan kana haka bazan sake kira maka ita ba, and bazan sake kaika wajenta kuyi wasa ba if ure been stubborn u hear me?” Kukanshi ya cigaba da yi, ya shafa kansa, “Now shhh” ya faɗa yana ɗaura hannunsa akan lips ɗinsa, shiru yayi yana kallonsa ya goge masa fuskarsa da babu hawaye yana kallonsa yace “come here” ɗaga shi yayi ya ɗaura a ƙirjinsa yana shafa gashinsa ba tare da yace masa komai ba, kusan 3 minutes yaji yayi bacci a jikinsa, murmushi yayi, ya miƙa hannunsa ya ɗau wayarsa dake gefen kujera da Saif ya wulla can, da mamaki sosai yake kallon screen ɗin ganin har lokacin tana kan wayan, kallon wayar yayi ta yi kafin ya katse kiran ba tare da yace mata komai ba.
Kallon wayar ita ma dinga yi ganin an katse kiran, ta sauƙe ajiyar zuciya, since Saif yayi shiru ai shikenan.
Haka ta wuni ita kaɗai a gidan da takaddunta, idan ta gaji da ɗakinta ta dawo palour, idan ta gaji da nan ma ta koma ɗaki, Har ta shiga ta kwanta wajen 9 su Nasir bata dawo ba, itama kuma bata kirasu ba, let them enjoy! Tayi murmushi tana jan bargo. Wayarta ta janyo ta buɗe, ganin missed calls ɗin Sadiq har 6 tayi ɗan jim kafin ta danna kiransa, har ya katse bai ɗauka ba, kallon wayar tayi tayi kafin kamar mai kokonto ta danna lambarsa har yayi ringing ya katse shima ba’a ɗauka ba, ɗan shiru tayi, is kiran da tayi wrong? Maybe yana tare da matarsa yanzu, since shes sure wayar Papa ne, but she wants to ask if Saif is alright, tun ɗazu take so ta kira ta kasa, kallon lambar ta cigaba da yi har zata sake kira ta fasa, feeling dissapointed in her self na kiran da tayi ma in the first place, ta ajiye wayar a gefenta ta ɗauko starnley cup ɗinta dake gefen gado ta zuƙi abin ciki ta mayar ta ajiye tana gyara net ɗin da ta saka gashinta a ciki.
Ringing ɗin wayarta yasa ta dubi wayar, a zatonta ko Sadiq ne, lambobin da ta gani ya sa tayi shiru tana kallon wayar, ganin zai katse tayi saurin ɗaukar wayar tayi picking ta kai kunne, shiru duk sukayi kafin a hankali tayi Sallama, amsawa yayi a taƙaice, ta ɗan yi shiru tana tunanin me zata ce kuma
“u called.” ya faɗa jin tayi shiru
“umm Naeema ce”
ta faɗa dan ta rasa ta ina zata fara,
“i know”
ya amsa ƙasa ƙasa
“umm dama, i didnt mean to bother u, kawai ina so ne dama in tambaya, is Saif alright?,naji yana kuka ɗazu ive been worried”
“he’s fyn”
ya amsa can ƙasan maƙoshinsa yana kallon Saif dake kwance a gefensa yana bacci,
“okay to, thank u Papa” ɗan shiru yayi kafin yace
“ke who is ur Papa?”
buɗa idanu tayi tana hana kanta murmushi
“Sorry Sir, ai naji haka Champ yake cewa ne”
“umm i see”
ya faɗa yana gyara kwanciyarsa akan gado.
“ okay thank you Sir good night?”
“Good night, but dont call me Sir pls”
ɗan Murmushi tayi tana mamakin yadda yake magana yau, cikin ƙaramar muryarta tace
“okay Yaya Ahmad” shiru yayi bai amsa ba kafin can a hankali yace
“Night Anty Naeema” tura baki tayi
“No pls” ta faɗa a shagwaɓe wanda bata san ma tayi ba, ɗan shiru yayi for seconds kafin yace
“No what?”
“I’m not Anty Naeema”
“okay but Saif calls u that”
ɗan murmushi tayi wato ya rama tunda tace Saif calls him papa shine shima ya kirata sunan da Saif yake kiranta
“yes ai saboda na girmeshi ne” sosai hirar ke masa daɗi ya gyara kwanciyarsa
“haba? To ai nima kin girmeni” ta buɗa idanunta kafin tace
“taɓ na girmeka kuma?” He can hear how childish she sounds, Murmushi yayi
“yes, how old are u?” Ɗan shiru tayi feeling a bit awkward “18” ta faɗa a hankali kamar mai jin kunyar faɗa, “really?” “Um” ta faɗa a hankali
“hm okay, night” “okay goodnight” ta faɗa tana zare wayar a kunnenta jin ya katse. Juyawa tayi ta kwanta da murmushi akan fuskarta, sai kuma ta sake tashi zaune, shiru tayi ta jingina da gado tana sake tunano maganganunsu da shi, ashe ma he can be dis nice? Hes always grumpy she thought baya magana ashe yana yi, Murmushi tayi ta ja duvet ta rufe har kanta.
Kallon screen ɗin laptop ɗinsa da ya ɗauke tuntuni kawai sadiq keyi, ƙirjinsa na wani irin heaving, ya kalli wayar da ke ajiye akan table ɗin gabansa karo na ba adadi, and whos dis that called her? No itace ma ta fara kiransa kafin shi ya kirata, ɗaukar wayar yayi ya shiga bincikawa yaga ko ɗazu Sunyi waya na almost 30minutes, wani zafi zuciyarsa ke masa, yayi replaying wayarsu na ɗazu wanda duk shirmenta da Saif ne kafin ya sake replaying na yanzu, yayi replaying wannan ɗin yafi sau 20, ji yadda take murmushi happily take waya da shi, ko a wayarsu da Saif ɗazu yana jin yadda take dariya genuinely, wanda shi yaushe rabon da ta masa? Ya daɗe a zaune a wajen bai motsa ba, duk da sanyin ac dake ɗakin zufa ke yanko masa, kalaman doctor suka shiga dawo masa, something about detachment da controlling ɗin kansa, gyaɗa kanshi ya shiga yi, ya saka hannayensa guda biyu ya rufe fuskarsa, shi ya san bashi ne matsalar ba, kowa so yake ya gwada patience ɗinsa, mutane ke ingiza shi ko da yaushe, the world kept testing him.
Cire hannunsa yayi daga fuskarsa ya jingina bayansa da kujeran ya lumshe idanunsa da har sunyi ja, buɗe idanun yayi, ya janyo wayarsa da yake anfani da ita, ya fara duba available flight to Lagos, jin fever ɗinshi kamar na shirin dawowa ya sa ya ajiye wayar akan table bayan yayi booking flight to lagos in two days.
Ya ƙarasa kan gadonsa ya shige bargo yana sauƙe ajiyar zuciya.



