Chapter 32: Chapter 32
“Lets talk” ya sake faɗa yana sliding hannunsa ƙasa ya riƙo nata, ɗumi da taushin hannunsa ya gauraya da nata, binsa kawai take yi a hankali tana taka lallausan carpet ɗin har suka isa sofa, ya zaunar da ita kafin shima ya zauna a hankali yana gyara hular kansa, ta ɗan saci kallonsa dan ita kam bata taɓa ganinsa ma da manyan kaya ba sai yau, though ba wai babbar riga ya saka ba but yau Native wear ne a jikinsa harda hula, gashin kansa luff a ƙasar hular, ya jingina bayansa da kujera yana kallon kyakkyawar fuskarta, sussune kai da take wai kunya burgesa yake sosai, a hankali ta zare fingers ɗinta daga cikin nasa tana gyara zamanta da ɗan bada distance kaɗan tsakaninsu tayi folding hannunta akan ƙafafunta sannan ta ɗan saci kallonsa ganin ya lumshe idanunsa ya sa ta ɗan zuba masa idanu, rasa abin cewa yasa muryarta ƙasa ƙasa tace
“Ya hanya ”
Ya buɗe idanun a hankali ya kalleta “Alhamdulillah, lafiya ƙalau, and u? How have u been?” Ya faɗa yana gyara zamansa da kyau ta ɗanyi murmushi kaɗan ta gyaɗa masa kai tace
“Fyn” ta faɗa tana janyo gyalen ta rufe gaban rigarta da shi da kyau wanda hakan yasa ya kalli wajen kafin ya mayarda idanunsa kan fuskarta ya sake mayarda kansa ya jinginar da kujera yana kallonta kawai, ganin kallon da yake mata ya sa ta ɗan tura baki, yayi murmushi yana miƙewa zaune da kyau ya nuna mata kusa da shi sosai alamun ta matso, maƙe masa kafaɗa tayi, bai sake kulata ba shi ya matso kusa da ita sosai ta matsa ta haɗu da hannun kujeran shima ya sake matsowa daf da ita har ƙafarsa na brushing nata, ya harareta kaɗan
“yanzu ma sake matsawa” riƙe murmushinta tayi taƙi kallonsa, ya zuba ma hannunta idanu kafin ya kai hannunsa kansu ya kamo ya rike yana ɗan murza hannun a hankali da thump ɗinsa yace
“Baby” ita bata san whats with idan ya kirata haka ba, is it voice ɗinsa ko me amma wani azabar daɗi sunan yake mata a kunnuwanta idan ya kira ta haka, ganin bata amsa ba yace
“Are u still angry?” Ɗagowa tayi ta kalleshi bata ce komai ba, ya ɗanyi shiru,
“Okay kiyi haƙuri, ban kyauta ba, i shouldve ask them su jirani in kira in faɗa ma sarauniya am sorry, now lets pretend ba’a ɗaura ba if i should call u now in faɗa miki za’a ɗaura would u say yes?”
“Nima ban sani ba” ta faɗa a hankali tana kallon hannunsu dake haɗe waje guda, yayi murmushi ya kai hannun bakinsa ya sumbata a hankali, kafin ya juya tafin hannun yana kallon cikin ƙaramin tafin hannun nata mai kyau da taushi.
“All that matters is that yanzu ure mine, and am urs isnt it what we both want? Uhmmmm?” Gyaɗa masa kai tayi a hankali.
“Are u still angry?” Girgiza masa kai tayi a hankali dan tuntuni ta manta da wani fushin da take da shi, shine dai yake ta sake emphasising ko ta haƙura ko bata haƙura ba.
“I love u baby okay, my love for u is a huge endless circle babu escape and as long as ina raye it will never end, ina sonki Na’ima, ure my east ure my west ure my south and ure my west kinji?” Kallon idanunsa tayi, all she sees a ciki is truth, all she sees is soyayyarta she thought he’s nonchalant farkon haɗuwarta da shi, bata taɓa zaton he can express himself so much ba har sai da yace yana sonta, babu ranar da baya ce mata he loves her and she so much love dis version of him that makes her feel special, seen and loved, ta gyaɗa masa kai a hankali tace
“i love u too” sake hannunta yayi ya ɗago fuskarta da ta sunkuyar bayan ta faɗi haka yace
“No ai banji ba” ta karɓe fuskarta tace
“to shikenan tunda baka ji ba ya wuce ka”
“Repeat it” ta maƙale kafaɗa tace
“Zan faɗa maka gobe”
“Tell me now” ya faɗa yana kallonta looking serious, ta shagwaɓe fuska tace
“to ai na faɗa kace baka ji ba”
“Eh banji ba tell me again” ta langaɓe kanta a hankali tace
“Cewa nayi Nima ina sonka papanmu ni da Saif” murmushi yayi a hankali yana ƙoƙarin kai hannunsa kan cikinta yace
“No papan Saif, kema amma soon zaki ɗauki naki Saif ɗin” saurin ture hannunsa tayi ta riƙe hannun a cikin nata gudun kar ya ce zai maida, to distract him and herself yasa ta sake hannunsa ta janyo tray ɗin kan center table ta turashi a hankali saitin sa sosai tace
“Baka ci komai ba ” ta faɗa ne kawai bawai dan tana tunanin zai ci ɗinba, ya kalli tray ɗin sannan ya kalleta,
“Ke kika yi?” girgixa masa kai a hankali tace “Mami” ya ɗan gyara zamansa da kyau ya janyo tray ɗin small chops ɗin da orange juice da ke kan tray ɗin, sai kuma ya ɗan kalleta,
“Ko zaki bani” wani murmushi tayi ta ɗauke kanta taƙi tace komai, shima murmushi yayi har set na haƙoransa na bayyana, kafin ya sa hannu ya ɗauki spring roll guda ɗaya ya kai bakinsa ta zuba masa idanu tana kallonsa kawai zuciyarta na melting gabaɗaya a kansa, guda ɗaya kawai yaci ya ɗan sha orange juice ɗin ma kaɗan ya ajiye, ya juyo ya kalleta tayi saurin ɗauke kanta, pretending ba kallonsa take ba, ganin kamar iya abinda zaici kenan ta kalleshi kafin ta sake kallon tray ɗin ta marairaice ta langaɓar da kanta tace
“Wai har kaci kenan” shiru yayi yana kallonta kafin ya sake ɗaukar sandwich ɗaya yace
“Not really my thing ne, dama dai abinci ne” ya faɗa yana kai sandwich ɗin bakinsa yana kallonta, kafin ta amsa masa maganarsa suka ji an ƙwanƙwasa ƙofar, ta ɗan kalleshi tayi murmushi tace
“yanzu kuwa zaka ci abinci, and i wont accept any excuse” daga haka ta miƙe ta nufi ƙofa ya bita da kallo, yana ajiye sandwich ɗin hannunsa saman tray ɗin.
Buɗe ƙofar tayi tana kallon 3 daga masu aikin gidan dake tsaye bakin ƙofa, tun ɗazu take expecting ɗinsu shine sai yanxu, hannu tasa ta karɓi gleaming silver tray dake hannun ɗayan da dish ɗin ciki is covered ta juya ta koma ciki, kallonta kawai yake da mamaki, ta matsar da wancan tray ɗin ta ajiye wannan kafin ta juya ta koma bakin ƙofa, har ta gama shigo da duka dishes ɗin da suka kawo kafin ta koma ta rufe ƙofar shi dai kallo kawai yake binta da shi har ta gama kai da komowan, ta dawo ta zauna ɗan nesa da shi ta tallafi kumatunta tana kallonsa tace
“To ga abinci kaci” ɗan ɗage mata girarsa yayi iya kallonta yace
“Banda wancan? Ko shi appetizer ne kawai” ya faɗa yana making serious face da nuna mata first tray da ta kawo masa
“Ni dai kaci kar yayi sanyi, ai kai kace kana jin yunwa”
Ya ɗan buɗa ido yana kallonta cause he didnt remember him sayin dat.
Kafin yayi magana ta kwaɓe fuska
“Sai fa kaci” ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya kaɗan yana kallonta fukarsa a sake sosai though ba murmushi yake ba
“Unless ull serve me”
“Okay” ta faɗa tana sauƙa dan serving ɗinsa.
Mummyn Amira ce a tsaye, Amira na Zaune akan carpet tana kuka Daddynta na zaune akan kujera dukansu ransu in yayi dubu ya ɓaci duka banda huci babu abinda Mummy take yi cause kwata kwata bata kawo abinda Amira zata zo ta faɗa mata ba kenan, kamar ya wai Ahmad ya ƙara aure. Miƙewa Dad yayi yace
“To wallahi bazai yiwu ba, yaronnan yayi ƙarya, yata zai ma kishiya? Dan yana hauka ko ya fara shaye shaye ne? Dan wallahi babu dalilin da ya isa ya saka ya mata kishiya muna kallo, zuwairah kiji fa” Yadda yake masifa duk muryarsa ta cika palorn, Mummy ta katse sa da sauri da faɗin
“kai dai kayi shirunka mana, ai wallahi abu ne da bazai saɓu ɓa wallahi tallahi, in dai ni ce na haifi Amira yadda ban zauna da kishiya ba wallahi bazata zauna da ita ba itama, babu namijin da ya isa na rantse da Allah, yadda baka isa ka min kishiya a gidannan ba itama ba’a isa a mata ba wallahi ka koma gefe kawai kayi kallo”
Ran Daddy a ɓace yace “bari inje office zuwairah sai na dawo am already late waiting for yar ki ta zo ta faɗa mana abinda aka mata ashe wannan baƙar labarin zata kawo mana” Mummy ta ja tsaki
“Kuma wai har take da idon baccin safe ta bar mu muna jiranta ashe ma kishinki na hofi ne Amira!” Shi dai daddy Ƙwafa kawai yayi ya baza babbar rigarsa yayi waje.
Sai a lokacin Mummy ta mayarda kallonta kan Amira da har lokacin kuka take
“To kukan uwar me kika saka ni a gaba kike mini yanzu? Amira kina jin magana ne? Tun farko me na faɗa miki akan Ahmad? Da na zo nace ki zo in kai ki inda wallahi Ahmad uwarsa tayi kaɗan ya ɗaga miki yatsa ba ƙi kika yi ba, ko kinfini ilimin addini ne? A tunaninki kin fini hankali koh, To yanxu kuma zaki sakani a gaba da kukan banza kukan hofi ai ke kika saya da kuɗinki wallahi, ba don ke yata bace wallahi ko kulaki bazanyi ba duk wulaƙancin da ya ga damar miki ya miki”
Ita dai Amira kuka kawai take yi, dan maganganun mummy ƙara mata zafi suke a ranta,
“Kin raina ni Amira, kin raina ni, amma wallahi gobe ko kin ƙi ko kinso sai kin bini munje dan ubanki, dan ba ni zaki kashe ba, idan namiji ya kumsa miki ciwo ai bashi da asara ni nake da shi, Niger zamu tafi gobe gobe don ubanki, ko ance miki ba don malamina na niger mutumin amana ba da Shi Ahmad ɗin zai taɓa aurenki ne? Ko balaraben ubansa mai tsinannen taurin kai an ce miki zai amince da aurenne bayan abinda ke tsakaninsa da ubanki? Duk da abubuwa da suka faru a lokacin bari kiji sai da na kai sunansa har niger aka fara tankwara sa shi dan shi yaron taurin kansa ya wuce misali, kafin uban ya ƙarasa mana aikin ya sa shi ya aure ki, kuma kinsan da wannan amma kika yi burus, ko ubanki da kike ganin business ɗinsa na tafiya yadda ya kamata kinsan adadin zuwa na niger saboda shi? Ai shi ya sani wallahi, saboda haka idan zaki buɗe idanunki ki buɗe ki saurareni da kyau, ba dai kince an ɗaura ba to wallahi da ƙafarta zata fita ta bar miki gidanki wallahi kinji rantsuwar musulmi dan Malam na niger ba imani ne da shi ba.”
Ganin Amira na ta kukanta tace “ko yanzu ma bazaki je bani kike min kukan banza da hofi” cikin shesheqa tace “zanje mummy” “kar ma kije, mutum dama idan yaƙi ji ai baya ƙi gani ba, sau nawa ina karɓo miki taimako ki mayar da ni ʼyar banza ki ƙi anfani da shi ? Yarinya sai shegen girman kai kin raina malamai, Shiyasa na daina wahalar da kaina da kuɗaɗena akanki da aurenki Ameera amma tunda yanzu duniya ta koya miki hankali yanzu ne zaki san anfanin masu taimako a rayuwarki” daga haka ta miƙe ta wuce sama ta bar Amira a zaune a ƙasa tana sauƙe ajiyar zuciya, ji take zata iya zuwa ko wani extent na ganin ta raba Ahmad da Na’ima ko da hakan na nufin bin Mummynta da Nuwaira ne inda ba wai ta gama yarda da wajajen bane.
Haka ta wuni sukuku a gidan, duk da yadda Mummy ta dinga janta jiki tana nuna kamar komai bai faru ba, dan ita ta riga ta saka a ranta fa suna zuwa can ƙarshen labarin kenan wallahi, amma sam Ameera ta gagara sake jiki, har sannan she’s heartbroken she couldnt even fake a smile.
Ko da daddy ya dawo daga office ma haka suka haɗu suka dinga nuna mata ta fa kawo kukanta inda za’a share mata shi tass, dan Mummy har ta faɗa masa gobe zasu tafi Niger wajen malam.
Da daddare duk yadda Amira ta so tayi bacci gagara yi tayi banda juye juye babu abinda take yi, Tunanin Ahmad ya mata yawa a cikin kirjinta ko me yake yi yanzu? Kar dai yana wajen Na’ima, innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ɗazu tana ganin kiransa dama taƙi ɗauka sai shima bai sake kira ba ya rabu da ita, tayi kuka har ta ƙoshi, ta kira Nuwaira a waya, Nuwaira na fara mata complain ɗin rashin zuwa tace mata tayi haƙuri zasuyi tafiya da Mummy gobe idan sun dawo zata zo ta faɗa mata yadda ake ciki, da sauri ta katse wayar ta tura ƙasan pillow tayi ruff da ciki ta rufe idanunta kamar mai bacci jin an buɗe ƙofar ɗakin, dan sarai ta san mummy will not be happy with her idan taji ta da Nuwaira da darennan, ganin tayi bacci suka juya suka tafi.
Har kusan asuba idanunta biyu tana juye juye, idanun har sun kumbure dan kuka, sai daf da asuba bacci ya ɗauke ta, ƙarfe bakwai Mummy ta shigo ta tashe ta wai ta shirya dan da wuri zasu wuce niger ɗin, tana ganin idanunta ta san bata yi bacci ba amma ta share bata kulata ba dan ta rasa irin son da Amira ke ma yaronnanan.
Daddy ne ya kaisu har airport, kafin ya juyo ya dawo gidan, tun a hanya ya janyo wayarsa yayi dialing wata number ya ajiye a gefe bayan ya sa a speaker yana driving da hannu ɗaya, ɗayan kuma yana shafa tumbinsa.
Ana ɗagawa daga ɗayan side ɗin muryar mace tace
“Alhajina” yayi wani dariyar manya yace
“yan matan Alhaji, kai yarinyar nan i miss u so much” ya faɗa da dariya yana shafa cikinsa a hankali, itama dariya tayi tace
“ah ah baka yi kewata ba tunda kana tsoron matarka” ya wani ja tsaki
“ke dillah matsa ce miki nayi tsoronta nake ji, yanzu dai me ya tashe ki da sassafe haka gimbiya”
“wallahi yunwa” ta faɗa tana wani kakkashe murya
“hahahaha, to yayi yanzu ki taho gidana mana sai muci abincin tare nima yunwar nake ji”
“wani gidannaka?matarka ta baka abincin mana, matar da ta tsane ni so kake na zo ta kashe ni?” Wani dariya ya kuma yi,
“ta kashe ki kuma? To bata ƙasar ma tayi tafiya yanzu na sauƙe ta filin jirgi on my way home now ki zo pls”.
“Ah ah sai dai kai kazo tunda yau saturday baka da office, ka zo gida in jiraka”
“kaiii to gani zuwa bari amma inje gida inyi wanka in shirya miki yan matan alhaji”
“ah ah ka taho kawai yanzu sai kayi wankan anan”
“haka za’a yi” ya faɗa yana juya akalar motar zuwa gidan kishiyar mummy ta waje Lol.
Yana isa madaidaicin gidan mai gadi ya buɗe masa gate da hanzari ya ƙarasa yayi parking a harabar gidan da zai ci mota biyu yana kallon motarta dake parke a wajen ya fito ya nufi ƙofae shiga gidan, ya tsaya ya ƙwanƙwasa yana riƙe jallabiyar jikinsa, buɗe ƙofar akayi, ya tsaya yana kallonta tana sanye da bomshort da tshirt ta riƙe ƙofar tana masa wani kallon tace “Alhajin Nuwaira” shigowa ciki yayi yana dariya shima da faɗin “Nuwairiri yan matan Alhaji”
Sati biyu da suka biyo baya Sosai biki ya kankama, the entire house anyi transforming ɗinsa sai wani haske na musamman yake, atmosphere ya canza bikin ʼyar gata, gidan Mami a cike da mutane yan biki, banda raha da dariya babu abinda ke tashi agidan, already mai gyaran jiki ta jima da zuwa private ɗaki guda aka ware mata da take gyara da sulle amarya Na’ima, ɗakin da dim golden lights banda uban ƙamshi babu abinda ɗakin keyi, da wani gado mai shegen taushi inda take scrubbing mata jikinta da perfume pastes, da herbal mixtures kala kala masu azababben ƙamshi, ga massage da take mata da oils masu shegen kyau, bayan nan ta tsuma ta da kyau dan steaming pots kala kala ke ɗakin, zuwa yanzu ba ta yadda zaka iya mata kallo ɗaya ka ɗauke kai duk kuwa kauda kanka, beauty specialist ce matar hakan yasa duk wani natural kyau da Ni’ima na Na’ima sai da ta ƙwaƙulosa, jikinta glowing kawai yake kamar wani silk.
Ba sosai take samun magana da Ahmad ba these days saboda how busy take, kuma its like shima on his part he’s busy da shirye shirye, but still ko sau ɗaya ne kullum zai kirata wanda hakan yasa cousins da Sisters ɗinta da suka zo ahead of bikin kasancewar bata da friends suka sakata a gaba da tsokana, ita kam sai dai tayi murmushi ta rufe fuskarta da pillow dan kunya ma suke bata, sosai ake pamparing ɗinta a gidan ba su fadila ba ba su Mami ba, har sometimes abin ya sakata kuka ganin irin gata da take da shi, Mami da fadila su suke supervising usual elegance ɗinta, akwatina na kayan fitar amarya duk suna ɗakin Mami, dan tuni aka gama final fittings har fashion designers ɗin sunyi delivering kayayyakinta.
Bridesmaids ɗinta sun gama karɓo ɗinkunansu na emerald green lace da aka raba musu kyauta tuni, gabaɗayansu ɗinkin fitted gown sukayi banda gwada kayayyaki babu abinda suke aukinyi anticipating ranar event ɗin. Ɗakinta a yanzu ya cika da gift boxes kala kala da basu fara buɗewa ba, zuwa yanzu duk wani bookings an gama confirming, make up artists da sauransu, yan uwa ke ta yiwa Mami da big Daddy kara, ga dangin baban Na’ima suma da suka taho biki sosai, kowa da irin shawarar da yake bata bayan lots of hugs da wishes da ake ta mata.
Kamar yadda Mami da big Daddy suka sake bakin aljihunsu haka daddyn Na’ima shima ya sake, hakan bai hana Ahmad sake nasa ba, komai excess ake yinsa gwanin sha’awa, komai well planned and coordinated.
Back in lagos sosai su ma suke preparation na biki daga gidan Ammi, yan uwa sosai suka zo duk da ance babu ɗaurin aure an riga an ɗaura, event planners sai aikinsu suke, Gidan da Na’ima zata zauna da ke cikin lekki an gama komai duk da yace ba’a buƙatar komai sai Amarya but inaaa Big daddy da daddyn Na’ima suka ce basu san zancen ba, su da kansu zasu ma yarsu komai, Salma baƙin cikin wannan biki take ji kamar ta haɗiye ranta ta mutu ta huta, dan tuni kowa ya san relationship ɗinta da Amarya da ango, tsabar haushin Ammi da take ji ya sa bata shiga bikin ba ta ɓangaren Ammi baka bata je Abuja ba tace idan an kawo Na’imar lagos su zasu karɓa daga nan, Suhaila dama tuni tayi flying outside country da wani friend ɗinta wanda Salma hakan ya ma fi mata kar azo a samu matsala.
2 days to ranar da za’a yi ma Na’ima jere a gidanta Amira tazo har gida ta samu Ammi tana kuka, sosai Ammi tayi mamaki dan shes never seen her this broken, Ammi ta ja ta ɗaki a sama kaucewa mutane da maganganu ya zaunar da ita a gado tana kallon yadda take share hawaye duk jikinta sai yayi sanyi dan ta san kishi halak ne, kuma kishiya bata da daɗi sam.
Cikin kwantar da hankali tace “What happened Amira” Amira ta zamo daga saman gadon ta haɗa kanta tana kuka, Ammi ta dafa ta tace
“kiyi haƙuri, ki saka ma ranki salama Amira, ki ɗauka hakan shine alkhairi a rayuwarku duka..” bata bari Ammi ta ƙarasa ba ta fara magana
“Ammi Baya sona, tunda ya ɗauko abin bikinsa baya ko bi ta kaina, kinga tunda nayi tafiya na dawo Ammi har yanzu baya wani kulani, kuma duk saboda Na’ima ne Ammi, yanzu kuma yace wai baza mu zauna gida ɗaya ba wai raba mana gida zaiyi gidanta daban, kuma zai kai mata Saif” Ammi tayi shiru tana kallonta dan bata ga itakam problem a raba musu gida ba, can tace
“To miye ne damuwar in an raba muku gida Amira? I think duk zaku fi samun kwanciyar hankali batun Saif kuma babu inda za’a kai Saif, infact Saif ya dawo wajena gabaɗaya” ta ɗago idanunta da ke cike da hawaye tana kallon Ammi, amma sai ta share batun Saif da taji Ammi tayi, dan rabonta da ganin Saif ta kusa wata ɗaya, amma da dai ya kai wa Na’ima wallahi gwara a bar shi a nan ɗin in yaso daga baya in komai ya lafa ta zo ta ƙwace abinta.
“Ammi wallahi idan ya raba mana gida cutata zasuyi, na faɗa masa ban yarda ba yace baya buƙatar amincewata, Ammi ko ce min zaiyi aure baiyi ba kawai yai aurensa yanzu kuma yana so ya raba mana gida saboda su dinga cutata bayan kamta yayi ya haɗa kanmu waje ɗaya” Ammi ta rasa me zata ce mata, ta san kishi ke ɗawainiya da ita, hakan yasa tace
“Kin fi so ku zauna gida ɗaya kenan?” Ta gyaɗa ma Ammi kai tana share hawayenta,
“Shikenan i’ll talk to him ku zauna gida ɗaya since his house is big enough amma only idan kin min alƙawari, babu tashin hankali Amira, zaku haɗu ku kwantar masa da hankali” gyaɗa ma Ammi kai kawai take, tace
“wallahi Ammi ni bazanyi tashin hankali da ita ba, na miki alƙawari”
“Shikenan Allah ya sa mu dace ya sa hakan yafi alkhairi” ta amsa da Amin a hankali. Bata jima ba bayan hakan ta bar gidan, a daren ranan Ammi ta zaunar da Ahmad a ɗakinta bayan ya zo mata sai da safe, tun da ta fara maganar Amira ya haɗe rai, tana kallonsa tace
“Kaga kai zaka fara jawo matsala kenan a gidanka tun kafin ma ɗayar ta shigo, tace baka shiga sabgarta tunda kayi aure, kana abubuwanka da yake nuna ka fi son amaryarka which is very wrong on ur path” kallon Ammi kawai yake baki sake, dan he cant recall yaushe sukayi haka da Amira, ko maganr banzq bai shiga tsakaninsu ba, in fact da ta ɗauki ƙafa tayi tafiya without his knowledge ma for almost a week bai ce mata komai ba dan baya son unnecessary drama, jin yayi shiru tace
“Kuma tace wai zaka raba musu gida ta maka magana kace bazaka fasa ba” ya ɗan gyara zamansa a hankali yana kallon Ammi yace
“Ammi abinda yasa nace mata haka its for my peace of mind, theres no way zan haɗa Na’ima da Amira gida ɗaya without Amira trying something stupid, na san Amira much enough in san cewa shirun da tayi yanzu da accepting ɗin auren ba ra’ayin kanta bane Ammi, sai dai in na ƙawarta, suna jira ne a kawo Na’imar sannan suyi making move ɗinsu ko su mata wani abin tunda ba ko da yaushe xan zauna a gidan tare da su duka ba, ita kuma kinga ƙarama ce bazata iya faɗa da su ba” kallonsa kawai Ammi take yi har ya kai aya kafin tace
“What if duk hasashennaka kuma ba haka bane? Tsoron kar ka ƙi yin adalci tsakaninsu yasa ta fi so su zauna gida ɗaya wannan tana da gaskiya cause ure already showing side ɗin da ka fi karkata Ahmad” ya lumshe idanunsa a hankali ya buɗe dan Ammi bazata fahimci all this thing da Amira ta zo ta mata drama bane,



