⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 38: Chapter 38

How many days zaka raba mana toh?” Tashi yayi zaune ya dawo da ita jikinsa ya zaunar da ita a ƙafarsa yace

“How many days kike so?” Ta langaɓe kai tace

“One one” ɗan dariya yayi yace “why?”

“So that u wont take long before coming back to me”

“I see, kuma bazan daɗe anan ɗin bama again ill go back to her too”. Wani kallo kawai take masa bata amsa ba, sai kuma can ta sauƙe ajiyar zuciya tana ƙoƙarin sauƙa a jikinsa tace

“zan ɗaura girki” riƙo hannunta yayi ya dawo da ita kan ƙafartasa yace

“yanzu da baki ce Ammi ta bar kawo mana ba da kinga u wont have to stress urself”

ta ɗan haɗe rai tace

“bari inje in ɗaura girkin”

“ah ah i dont want the food”

ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaura bakinsa a nata, ta juya fuskarta tace

“ni to yunwa nake ji” ajiyar zuciya ya sauƙe yace

“Okay!” Ta miƙe daga jikinsa ta nufi ƙitchen ya bi jikinta da kallo har ta shige kitchen ɗin, kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya miƙe ya bi bayanta zuwa kitchen ɗin, shi kanshi mamakin kansa yake yadda yake maƙale mata yake binta ko ina a gidan kamar yana binta bashin ƙoda, tana tsaye a gaban gas tana ƙoƙarin kunnawa ya tsaya bakin ƙofa yana kallon ƙafafunta zuwa cinyoyinta dats open dan farar shirt ɗin ya ɗan sauƙa amma bai wuce rabin cinyarta ba, gashinta data kama a sama roughly sai wanda ya kwanta luff a bayan wuyarta, ya ƙaraso ciki a hankali ya rungumeta ta baya pulling her ya haɗata da ƙirjinsa, ya kai hannunshi ya kashe gas ɗin a hankali yace

“lets eat out” mitan da ta tashi yi ne ya maƙale ta juyo ta sauri tana kallonsa tace

“really?” Ya gyaɗa mata kai tare da kissing forehead ɗinta yace

“Kina so ki fita ne?”

“Eh” ta faɗa a hankali tana washe masa teeth, yayi murmushi ya lakace hancinta

“To muje ki shirya!”

“A motata zamu je?” Ta tambaya tana bin bayansa bayan ya riƙe hannunta ya nufi ƙofa da ita

“Ur porsche?” ya tambaya yana nufar stairs da ita, ta gyaɗa masa kai tana binsa kamar wata ƙaramar yarinya

“Yes pls”. Ya tsaya a jikin steps ɗin ya juyo yana kallonta yace “toh” kafin ya ƙarasa haurawa da ita stairs ɗin

excitedly ta shiga shiryawa cikin wata flowing tsadaddiyar abaya, ta ɗaura gyalen a kan hular kanta bayan ta gyara ɗaurin gashinta sai gyalen yayi kamar yayi highlighting skin ɗinta da glow ɗin fuskarta, she looks effortlessly regal.

Dai dai shima ya gama shiryawa tsaf cikin ƙanunun kaya yayi madarar kyau da har satan kallonsa ta dinga yi, ko da yaushe yayi dressing sai taga kamar ita she’s underdressed.

Hannunsa ya miƙa mata, ta saka nata a ciki ɗayan hannunsa na riƙe da makullin motarta suka sauko ƙasa, shi ya rufe ƙofar part ɗinta kafin suka jero beautifully zuwa wajen motarta, ya buɗe mata passenger seat ta shiga, ya tsuguna ya gyara mata rigarta kafin ya miƙe ya rufe motar ya zaga ya shiga, ya tada suka bar gidan, kallonsa kawai take yana driving ɗin tana tunanin yadda gobe he wont be with her, she’s definitely going to miss him so much, a wani kyakkyawar restaurant suka tsaya suka yi lunch kana ganinsu kaga couples carved out of love itself.

Afterwards suka tsaya a wani Babban shopping mall that he wants to get something, duk da yadda bata yi niyyar shiga ba ya matsa dole ta biyo sa cikin mall ɗin dan ya ce bazata rasa abinda take so ba.

Shopping ɗin da he ends up doing all of it, sai dai idan ya ɗauka mata wani abin ta ɗan kalleshi ko ta sake riƙe hannunsa da ke cikin nata tace “isnt it too much hubby?” Sometimes ko kulata baya yi ko kuma idan ya ga dama ya ɗan harareta.

Few things ya saya ma kansa, zuwa lokacin duk ta gaji da binsa a cikin mall ɗin, suna zuwa wajen biyan kuɗi, ta kwaɓe fuska ya ɗan kalleta yace

“kin gaji?” Ta gyaɗa masa kai a hankali tana pouting tare da leaning kaɗan a jikinsa ,

“lazy girl” kawai ya faɗa ƙasa ƙasa yana matsawa dan biyan kuɗin, dai dai lokacin wayarta ya fara ringing ta kalli wayar dan har yanzu da tsohon wayarta take anfani batayi setting up new gadgets ɗin nata ba, ganin number da ke kiranta ta ɗan yi shiru, dis number has been calling her but she kept missing the call saboda yadda Ahmad is clingy kullum yana maƙale da ita bata ma sanin inda wayarta yake atimes, ta ɗan kallesa yana biyan kuɗin kafin tayi hanyar fita a mall ɗin ta ɗaga wayar ta kai kunnenta tare da sallama tana fitowa wajen mall ɗin sosai, shiru taji daga ɗaya side ɗin, ta ciro wayar taga har sannan the person is on the line tana shirin mayarwa kunne ta tambayi waye ne aka katse kiran, ta ɗanyi jim, sai kuma ta taɓe baki, har ta juya da niyyar komawa ciki sai kuma ta fasa, gwara kawai taje ta jirasa jikin mota since hes coming out now, just before ta isa inda suka yi parking taji an ɗaura hannu roughly a waste ɗinta an riƙota da ƙarfi, ta buɗa idanu tare ta ƙoƙarin fasa ihu amma kafin tayi aka toshe bakinta kirif.

Zuciyarta tayi wata tsinanniyar bugawa ta fara ƙoƙarin dambe da koma wanene ganin wajen shiru babu mutane bare wani ya taimake ta, wani dim corner dake gefen mall ɗin aka jata inda mutane ma rarely pass wajen, gyalenta dake kanta ya sabule ya dawo wuyarta sauran gyalen iska ya fara fifitashi a wajen, ya jingina ta da ginin wajen yana kallon yadda ta zaro duka idanunta banda “mmmmmh, Mmmh” babu abunda take yi tana ƙoƙarin magana amma ya toshe mata baki sosai.

Ɗaya Hannunsa ya kai ya cire face cap ɗin kansa ya sauƙe mask ɗin fuskarsa yana kallon cikin idanunta breathing harshly on her face, muryarsa na rawa yace

“Ni’ima! Ni’eemata” sake zaro idanunta tayi ta fara ƙoƙarin fizge jikinta amma ta kasa tana kallon sadiq da ya rame soaai yayi duhu dake gabanta yana kallonta yayi pressing ɗinta da bango forcefully,

“Kiyi shiru! Please keep quiet pls i beg u Ni’ima ki tsaya ki ji”

Tuni har idanunta ya ciko da ruwa ta dinga juya masa kanta ta saka ƙafa tana tattaka ƙafarsa da ke daf da tata, tana fara ƙoƙarin dambe dashi, ƙarfi ya sake saka mata ya murɗa hannunta ya juya ta ya manna face ɗinta da bangon jin bazata tsaya ta saurare sa ba, ya matso daf da ita muryarsa na breaking kamr mai shirin kuka yace

“Pls Ni’ima just 1 minute, wallahi i’m not here to hurt u, dan Allah ki tsaya ki saurareni Na’ima zan mutu ne kinji” bakinta da ya sake mata ta buɗe ta kurma ihu, yayi saurin toshe bakin yana pressing kansa against her ajikin bangon muryarsa na rawa yace

“Dont provoke me! Nace ki saurareni, Dont be like Mimi dat doesnt listen”

Muryarta can cikin wuyarta tace “Sadiq,…. ure hurting me”

“Its because bazaki tsaya muyi magana ba” ya faɗa yana kallon hannunta daya ke riƙe da shi da ƙarfi da har ya soma yin ja kafin muryarsa na rawa yace

“i’m sorry, i’m so sorry ni’ima kiji tausayi na dan Allah, kintsaya ki ji me zance ”…..

Tunda ya fito bai ga Na’ima awajen ba mamaki ya kamasa he thought zai ganta a jikin motarta, ya fara kalle kalle around but babu ko mai kama da ita, to ko ta koma ciki? Just as he’s about to go back in idanunsa ya sauƙa akan veil ɗinta da kaɗan iska ke kaɗowa from edge na wani dark passage.

Nufar wajen yayi wondering what she’s doing there, har ya ƙaraso wajen, and then he saw them, yadda sadiq yayi pinning ɗinta da gini and she’s struggling ta ƙwaci kanta ta kasa, wani dum idanunsa suka masa yana musu wani irin kallo, da sauri sadiq ya sake ta ya ja da baya da sauri yana kallonsa shima, ai tana ganin Ya sake ta taho wajen Ahmd da gudu ta riƙe gefen rigarsa har sannnan jikinta rawa yake sosai tana kuka sosai, ledojin hannunsa ya zubar a wajen idanunsa gabaɗaya ya gama rufewa da ɓacin rai har ya canza colour ya nufi sadiq dan ji yake idan bai halakasa ba bazai taɓa jin daɗin rayuwarsa ba, ya cakumo kwalarsa ya fito da shi daga wajen yana kwashe fuskarsa da wani shahararren marin da yayi resetting brain ɗinsa, tuni itama ta fito a wajen ta tsaya tana kallonsu, Sadiq ya kalleta idanunsa ya ciko da ruwa

“Dis is the person u chose over me?” Ya faɗa hawaye na gangaro masa daga idanunsa, cakume kwalarsa da kyau Ahmad yayi yana kallon idanunsa

“You Bastard” Ahmad ya faɗa yana fara kikkifa masa mari hagu da dama kamar zai halakasa da mari wanda sam sadiq ɗin bai yi ƙoƙarin dambe da shi ba amma har gefen bakinsa ya fara jini, sai hannu kawai da yake saka wa yana tare fuskarsa da hakan ke sake provoking Ahmad ɗin, ya rufe shi da duka kamar zai yi ajalinsa, babu wanda yayi yunƙurin rabasu sai few da suka tsaya suna kallonsu ita kam tuni Na’ima jikinta ya fara wani shegen rawa, ganin kirɓansa kawai da Ahmad ke yi yana ball da shi a harabar wajen ya sa hankalinta yayi masifar tashi dan abin ya fara yawa, ya saka hannu ya cakumo kwalarsa yana huci sosai yace “how dare u? How dare u touch her?” Yana faɗa ya sake kife sa da mari, zuwa yanzu Na’ima couldnt take ita banda kuka babu abinda take yi, ta nufe sa da sauri jikinta na mazari ta riƙo hannunsa tana kuka sosai tace

“dan Allah ka ƙyale sa, ka bar shi haka bashi fa da lafiya dan Allah mana am begging u”

But Ahmad didnt stop kamar ma maganarta tunzurasa yayi, ya sa ƙafa ya fara ball da shi, yana sake sauƙe masa tafi

“Ahmad!!!, Ahmad please” ta faɗa tana jijjiga hannunsa

“Kashe shi zaka yi ne wai?” Ta faɗa tana rushe wa da sabon kuka.

Ko kulata baiyi ba ya cakumoshi ya buga shi da gini, Ya riƙo kwalarsa zuciyarsa banda boiling babu abinda take yana huci yace

“touch her again, i’ll bury with with my hands”

Tari Sadiq ya fara yi sosai jini a gefen bakinsa, kyakkawar fuskarsa har ta kumbure, Muryarsa desperate yana kallonta yace

“just 1 minute pls Ni’ima”

Ahmad bai san sanda ya dunƙule hannunsa ba ya ɗuma masa a ciki tuni ya fara kilarsa kamar abinda aka aiko sa yayi kenan duniya, Na’ima kam ta birkice ta fara kallon waɗanda ke wajen ganin abin ya fara wuce hankali tana faɗin

“Pls ku hana shi mana sai ya kashe shi ne?” Ɗaya daga cikinsu yace

“police are on their way”

Inaaa bazata iya jira har su zo ba, cause Ahmad ɗin da take gani ba Ahmad ɗinta bane, bata taɓa sanin haka yake da zafin rai ba sai yau, Hannunta da jikinta na trembling ta ƙarasa da gudu inda wayarta ke yashe a ƙasa ta ɗauka tana kuka kamar ranta zai fita ta soma dialing lambar Nasir, yana ringing biyu kuwa ya ɗaga, kafin ma yayi magana ta fashe masa da kuka

“Yaya Nasir zai kashe shi!” Ta faɗa cikin matsanancin kuka, dan wani irin azababben tausayin sadiq take ji, Nasir yace

“Wa zai kashe wa? Where are u at?”

Ta kalli Mall ɗin ta faɗa masa sunan Mall ɗin tace “Yaya Ahmad ne zai kashe Sadiq”

“Sadiq?” Ya faɗa da hanzari! Ta dinga jijjiga masa kai, yace

“hold on gani nan zuwa am not far da inda kuke, in less than 10 minutes i’ll be there” gyaɗa masa kai kawai take yi kamar ƙadangaruwa kafin ta cillar da wayar ta nufi Ahmad da har lokacin ƙwallo kawai yake da sadiq kamar ya samu ball.

Ganin bazata iya jiran har Nasir yazo ba in 10minutes da yace ta sa hannu biyu ta riƙe hannun Ahmad jikinta duka rawa yake tace

“dan girman Allah Ahmad stop… for my sake. Leave him pls ure hurting him”

Dakatawa yayi da naushin da ya dunƙule hannu zai kaiwa sadiq jin abinda tace, shi dai sadiq na dunƙule a ƙasa fuskarsa gabaɗaya ta canza kamanni, ya juyo a fusace yana kallonta yace

“I shouldnt hurt him? Ure begging me for him?” Ya faɗa yana nuna sadiq da ya ɗan miƙe ya tsuguna a wajen kamar kneel down yana kallonsu da kumburarren fuskarsa da jini ya ɓata, ta haɗiye miyau ganin ya dawo kanta ta girgiza masa kai a hankali amma ta gagara magana sai kuka kawai take, wanda kukanne ke ma ɓata masa rai fiye da komai, like is she crying all this cry saboda Sadiq? This son of a bitch ?hannu biyu ya sa ya riƙo kafaɗarta ya jijjigata yana kallon idanunta da idanunsa da sun kaɗa sunyi jajir yace

“He pressed u to the wall! Kinsan me hakan ke nufi? He touched my wife!”

Hawayen idanunta na gangarowa tace “amma ure going too far”

“Too far kika ce?” Ta gyaɗa masa kai tana kai bayan hannunta ta goge idanunta

“Bashi da lfy, kuma.. kuma He’s not an animal, ka kalleshi ka ga abinda ka masa” juyawa yayi ya kalli sadiq ɗin kafin ya dawo da idanunsa kanta, sake kafaɗunta yayi a hankali ya ja da baya, wani azababben zafi ƙirjinsa ke masa na bala’i yana kallonta sannan ya kalli sadiq dake tsugunne a wajen har sannan yana kallon Na’imar, idan ya cigaba da tsayuwa a wajen tabbass zai kashe Sadiq har lahira, dai dai lokacin motar yan sanda suka shigo wajen a tare lokaci ɗaya da Nasir, ko jiransu Ahmad baiyi ba ya juya tare da tsugunawa ya ɗauki makullin motarta a ƙasa kawai ya wuce ya buɗe motar ya shiga, Nasir da yayi parking ya bishi da ido ganin yadda ya figi motar ya bar harabar wajen leaving Na’ima behind tare da Nasir ɗin da kuma sadiq da ko attempting guduwa bayayi dan sosai ya daku, sai yan sanda da Nasir ya ƙarasa wajensu dan suyi magana, itakam banda wata irin rawa babu abinda jikinta keyi gyalenta a hannunta ƙafafunta ma ba takalmi.

Kallon hanyar da ya bi da motar kawai take yi hawaye na cigaba da sintiri a idanunta cause bata ma san tunanin me zata yi ba, she didnt mean to hurt him ko kaɗan thats the least thing da zatayi a rayuwarta amma at the same time tana tausayin sadiq bata so ya masa lahani, tears ɗinta suka gagara tsayuwa, duka jikinta is trembling dan ko sake kallon inda sadiq ma yake bata yi ba ta kai hannunta dake shaking ta ɗaura gyalenta a kanta she just couldnt think straight.

Nasir da ya gama magana da yan sandan, dan shima waɗanda ya kira kafin ya taho wato asalin masu handling case ɗin sadiq are on their way, dan wancan karan da yayi kidnapping ɗinta dama friend ɗin Ahmad wani Soldier kamal shine ya taimaka aka kamasa before a mayar da case ɗinsa wajen waɗanda ya kamata, ya ƙarasa inda take amma ya gagara ce mata komai dan already yayi sensing akwai matsala, ganin ƙafafunta ba takalmi ya juya ya fara kalle kallen wajen, a can kusa da lungun ya ga takalman ya wuce ya ɗauko su ya ajiye su a gabanta yace

“Saka takalmanki” tana cigaba da tsiyayar da hawaye ta zura ƙafafunta cikin flat shows ɗin, ganin ta saka takalman ya sa ya wuce inda sadiq ke tsugune har lokacin kamar wanda aka saka kneel down, ya ɗan tsuguna shima yana kallonsa, ganin yadda fuskarsa ta kumbure sosai ba kaɗan ba idanunsa suka yi ƙananu, ga jini a gefen bakinsa da ya fashe da kuma goshinsa inda Ahmad ɗin ya buga sa da gini, gagara magana yayi kawai ya miƙe yana zaro wayarsa a aljihu yayi dialing wata Number ya koma gefe yana magana a wayar bai jima yana magana da su ba yace “alright” ya kashe wayar cause dis time around ba zai bar guy ɗin ya sake suɓuce masa ba, he’ll try his best ganin ya sama masa lafiya ko dan albarkacin mamarsa da kullum cikin kiransa take da roƙo duk da yanzu ba kasafai ma ya cika ɗaukar wayar ba but he’s taking Sadiq to a psychiatric ayi retaining ɗinsa a can he really needs the help, Sadiq dake kallon Na’ima har sannan ganin Nasir ya tafi waya ya fara jan gwuiwarsa yana matsowa gabanta muryarsa bata fita sosai yace

“Ni’ima” ai kamar ya tsikareta da allura ta koma baya da sauri, ya haɗe hannayensa yana kallonta wasu hawaye masu zafi na bin kuncinsa yace

“Kar ki manta old times Ni’ima, ure my life, kar ki bari a rabamu dan Allah, he doesnt deserve u, ke watarana zai daka i promise u this Ni’ima ” yana faɗan haka ya fashe da kuka ya saka fuskarsa a tafukan hannunsa yana kuka sosai jikinsa har na jijjiga, ganin abinda ke faruwa gashi Na’imar ma sai kuka take yasa Nasir ya taho wajen, ya kalli Sadiq kafin ya kalli Na’ima ganin duk kuka suke sosai yace

“Je mota ki jira ni Na’ima” ta kalleshi ya gyaɗa mata kai a hankali ta juya ta nufi motar har sannan hawaye ke bin fuskarta ta rasa me take ji a ranta, lokaci ɗaya damuwa ya mata yawa har ji take kamar zata faɗi ta nufi motar Nasir, buɗe motar tayi ta shiga ta rufe ta kifa kanta da gwuiwarta ta cigaba da kuka, har police officers da doctors ɗin da Nasir ya kira suka iso tana cikin motar, ɗaga saɗiq sukayi da jikinsa yayi tsami sosai carefully taking him away, Nasir ya bisu da kallo har suka saka shi a mota suka bar harabar wajen suma police ɗin farko suka wuce abinsu bayan Nasir ya sallame su tare da nuna musu medical report ɗin Sadiq ɗin da kuma tabbatar musu from here za’a wuce da shi asibiti ne, kafin ya wuce motarsa leaving few mutanen da suka ga dramar har ƙarshe a wajen, ya buɗe mazaunin driver ya shiga yana kallon Na’ima da ta kwantar da kanta a jikin ƙofa tayi shiru dis time around ba kuka take ba sai hawaye kawai da ke zubowa a idanunta, bai ce mata komai ba har dai ya tada motar, sai da suka hau titi sosai kafin ya ɗan kalleta kaɗan yayi ɗan gyaran murya yana mayarda hankalinsa titi yace

“Tell me what happened, ya aka yi sadiq ya san inda kike” wasu hawayen ne suka gangaro mata ta kai bayan hannunta ta share tace

“Nima ban sani ba kawai munje munci abinci ne shine.. shine yace zai siya abu and he insist i go in with him…….” Tiryan tiryan ta faɗa masa duk abinda ya faru tana yi tana goge idanu

“Ni ban ce masa haka to hurt him or anything ba, amma yaya Nasir ai kaga yadda ya masa, where’s his humanity? I only tried stopping him kar yayi abinda zaiyi regretting amma shine yayi fushi ya tafi ya barni” tana kaiwa nan hawayenta suka ƙaru ta rufe fuskarta da hannu tana kuka a hankali. Nasir ya ɗan yi shiru kamar ba zai ce komai ba kafin a nutse yace

“U shouldnt have said that to him though, ko miye zai faru nan gaba bama fata amma koma miye ne u should side with ur husband ba wani daban ba, zaki iya hana shi in other ways ba tare da kin faɗi abinda kika faɗa ba, amma dai kar ki wani damu, haka yake fa shi dama iya da zuciya sosai, he’ll calm down later kaɗan, its normal” gyaɗa Masa kawai tayi a hankali ta mayar da kanta tana kallon taga, yadda suka tashi yau har zuwa fitowarsu bata taɓa tunanin haka ranar xai ƙare musu ba, bata taɓa tunanin zasu koma gida seperately ba, har cikin compound ɗin Nasir ya sauƙe ta, muryarta ciki ciki tace “thank you” tare da buɗe motar ta sauƙa ya miƙa mata wayarta da ya ɗauko mata ta amsa ta juya tana kallon motarta dake parke a compound ɗin ta nufi part ɗinta tana tafiya kamar ƙwai ya fashe mata, juya kan motar Nasir yayi ya bar gidan ya bi bayansu sadiq cause so yake ayi komai a gama a yau.

A buɗe ta samu ƙofar palournta ta ɗan tsaya a bakin ƙofar jim kafin ta nufi ciki zuciyarta na bugawa kamar yaron da ya san yayi laifi ya dawo gida za’a hukuntasa, ta mayarda ƙofar ta rufe a hankali tana kallon palourn ganin babu kowa.

Sama ta nufa jikinta duk a sake dan sai yanzu take sake jin rashin daɗin fushin da yayi da ita, ta shiga bedroom ɗinta ta ƙarasa kan gadonta ta faɗa ta ɗaura fuskarta a pillow ta cigaba da kukanta abinta.

Tun tana kukan har bacci ya ɗauke ta tana sauƙe ajiyar zuciya, kiran Sallar la’asar ya sa ta miƙe zaune a hankali tana jin kanta na ciwo sosai, ta sauƙa a gadon ta wuce toilet tana sake jin yadda kanta ke sara mata duk ta motsa, kayanta ta cire ta watsa ruwa ta ɗauro alwala ta fito ta shirya cikin simple egyptian gown tayi sallah, tana idarwa ta zauna akan sallayar ta juya tana kallon ƙofa, to ko ya shigo tana bacci ne? Miƙewa tayi a hankali da hijab ɗin da tayi sallah a jikinta ta nufi ƙofa ta buɗe ta fito,
duk da bata saka ran ganinsa a ɗakin ba dan tunda suke gidan bai taɓa ko zama na 1 hour a ɗakinsa ba sai dai nata amma still ta nufi can, ta murɗa ƙofar ɗakin a hankali ta tsaya a bakin ƙofa tana kallon cikin tamfatsetsen ɗakinnasa ganin baya ciki ta ƙarasa ciki a hankali ta zauna a gefen bed ɗinsa tana jin kamar zai iya shigowa maybe anytime sai da ta kwashe kusan 1 hour da kaɗan ganin ba shigowa zaiyi ba ta miƙe ta koma ɗakinta ta rufe ta kwanta idanunta na sake cikowa da sabon hawaye, ta janyo wayarta ta shiga kiran layinsa amma har ya katse bai ɗauka ba ta sake kira nan ma bai ɗauka ba, ta tura masa text tana share idanunta amma no reply haka ta haƙura ta cire hijab ɗinta ta hau kan gadon ta kwanta tayi shiru tana tunane tunane wanda duk nasa ne ta rasa yadda zata yi da ranta.

Har aka kira magrib tana kwance ji take kamar zazzaɓi ma zata yi ta daure ta sauƙa a gadon ta wuce toilet tayi alwala ta zo tayi sallah tana idarwa wayarta dake kan gado ya fara ringing ta miƙe da sauri da tunanin ko shi ne amma sai taga Fadila ce ke kiranta ta san maybe Nasir ya faɗa mata abinda ya faru hakan yasa ta ɗaga wayar, a hankali tayi sallama, aikuwa ta canka dai dai dan straight Fadila ta soma tambayarta what happened, ta fashe mata da kuka tana labarta mata yadda ta faɗawa Nasir ɗin ma, fadila ta sauƙe ajiyar zuciya tace

“Babe yace min Yaya Ahmad left u there shi ya dawo da ke gida, kin same shi a gidan da kika dawo?”

Ta share idanunta tace “ban same sa ba, da na dawo ban duba ba na zo na kwanta da na tashi kuma baya gidan”

“Meyasa baki dubasa ba sanda kika dawo Na’ima”

“Babu” ta faɗa a hankali, fadila tayi shiru tace

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved