⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 51: Chapter 51

“Sir pls ka bamu ita, if u hold her we cant save her, every second counts trust us pls”

kallonsu kawai yake kafin ya kalli fuskar Na’ima da tuni tayi pale jikinsa na rawa ya gyaɗa musu kai tare da ƙoƙarin sauƙeta a stretcher ɗin yana riƙe hannunta karɓarta sukayi suka kwantar da ita da kyau a akan stretcher ɗin da gudu aka nufi ciki da ita leaving him behind a tsaye a wajen almost frozen, kallon hannunsa yayi da ya ji shi empty reality na snapping cikin kansa,
ya ja ƙafafunsa ya ƙarasa nearest kujera dake haɗaɗɗen reception ɗin ya zauna yayi leaning forward tare da saka tafukan hannunsa a fuskarsa bugawar da zuciyarsa keyi har ya wuce misali, idanunsa da suka kaɗa suna tara wani ruwa da yake jin ɗacinsu har a cikin ransa da maƙoshinsa, the kind of bleeding da take yi ya sa zuciyarsa wani irin tsitstsinkewa dan baya son yarda da hasashen da zuciyarsa ke basa ko kaɗan.

Yasmeen ta zauna a gefensa tana share idanunta dai dai lokacin wata nurse ta ƙaraso tana riƙo yasmeen ganin itama jini kawai ke zuba a face ɗinta ta tafi da ita dan itama tana buƙatar dressing Aminu dake tsaye gefe ya bi bayanta yana riƙe da Saif kwata kwata shikam Ahmad ya gagara ko kallonsu.

Yana zaune a wajen har suka dawo bayan wasu lokaci an mata dressing a wajen an yi bandaging kanta, ta zauna a gefensa idanunta sun kumbura ta kwantar da kanta a hannunsa, sai a lokacin ya buɗe idanunsa ya kalleta idanunsa sunyi ja but dry, ya dinga kallonta for long kamar wanda muryarsa ta maƙale kafin ya janyo maganar muryarsa low and rough yace

“Me ya same ta? Tell me what happened to my wife yasmeen” yasmeen ta girgiza masa kai hawaye ya gangaro idanunta tana ƙoƙarin fashe masa da sabon kuka ya daka mata tsawa da yasa kowa na wajen ya dawo da kallonsu kansa yana kallonta

“Ce miki nayi me ya faru, tell me what happened?” Ya faɗa yana riƙo kafaɗar yasmeen, yasmeen ta fashe da kuka ta fara masa bayanin abinda ta sani daga farko har ƙarshe. Kallonta kawai yake yi tana masa bayani har ta kai ƙarshe baya ko ƙiftawa zuciyarsa na rising da falling a lokaci guda, maƙoshinsa yaji ya bushe kamar bai taɓa shan ruwa ba, yasmeen ta kulle fuskarta a hannunta tana cigaba da kuka, a dai dai lokacin Ammi da Aminu ya kira tuntuni ta iso asibitin hankali tashe, yasmeen na jin muryarta ta tashi da gudu ta nufeta tare da rungume ta tana fashewa da sabon kuka. Shikam Ahmad tashi kawai yayi ya nufi ƙofar fita a asibitin Ammi ta bishi da kallo ganin yadda ya fita a wani irin zuciye kamar zai tashi sama kafin ta ɗago Yasmeen daga jikinta tana tambayarta abinda ya faru.

Tunda suka baro part ɗin Na’ima jikin Amira ke rawa, sai yanzu ne reality yayi hitting ɗinta na abinda suka aikata, ko zama basu yi a palourn ba ta fara safa da marwa itama tana kallon Nuwaira tace

“Nuwa kar fa mun kashe ta” Nuwaira da itama gabanta ke faɗuwa amma sam fuskarta bata nuna ba dan ita damuwarta kawai kar Ahmad ya zo ya same ta a gidan tace

“Wani irin kashe ta? Haka aka ce miki ana mutuwa? Dan ɗan wannan abin sai ta mutu?” Amira tayi shiru tana kallonta tace

“Kamar fa bleeding ma take” Nuwaira tayi ƙwafa tana ƙarasawa jikin windown palourn ta leƙa conpound ta hango Yasmeen na magana da masu gadi kafin ta juyo ta kalli Amira tace

“To sai ki godewa Allah da take bleeding, saboda ita gata balbela uwar soyayya, ayu, daga shigowa har tayi ciki, duk yadda akayi cikinne ya ɓare take bleeding kar ki wani damu”

Amira da ta kasa zama tana kallon Nuwaira tace

“Kar in damu fa kika ce Nuwa? Me Albi zai ce na shiga uku” wani banzan tsaki Nuwaira ta ja ta ƙarasa ta ɗauki makullin motarta tana faɗin

“Dan Allah ni kinga tafiya ta ba ni zaki ɓata ma rai ba, ba albi ba albo, ke da gidanki har yana da bakin magana dan kin daki kishiyarki? Ai shima yasan bai sama ma kanshi zaman lafiya ba abinda yayi da ya ƙaro miki kishiya kuma har yana da ƙarfin halin ɗaukar ɗanki ya kai mata” tana faɗin haka ta saka takalmanta da ke bakin ƙofa ta kai hannunta ƙofa da sauri tana faɗin

“Komai zai ce miki just stand on ur ground cewa kin daka ɗin abin duka tayi shiyasa kika dake ta kika cire raini dan uwatta” Amira ta biyo ta da sauri tana faɗin

“Nuwa tafiya zaki yi ki barni? Dan Allah ki tsaya ni kam tsoro nake ji wallahi”

ko kulata Nuwaira bata yi ba ta buɗe password ɗin ƙofar dan Allah Allah take ta ganta a motarta ta bar gidan, Amira ta sa kuka tare da biyota dan sosai tsoro taji take ji ba na wasa ba, Nuwaira na buɗe ƙofar palourn ta sako kai waje yayi daidai da buɗe ma Ahmad gate da akayi ya shigo da motarsa ai da gudu ta koma ciki ita da Amira har suna rige rige suka kulle ƙofar, Amira ta saka kuka tana faɗin

“Mun shiga uku” zare idanu kawai Nuwaira keyi kafin ta miƙe ta sauri ta nufi window ta sake matsar da curtains ɗin tana leƙawa, Amira ma ta biyota suka tsaya suna kallo yadda Ahmad ya karɓi Na’ima daga Hannun Aminu ga yasmeen ma a wajen tana kuka da jini a fuskarta, Amira tace

“Amma Nuwa Me yasa kika hankaɗa yasmeen ɗin dan Allah mun shiga uku wallahi baki san halin Albi ni na san halinshi mun shiga uku mun lalace”

Nuwaira ma kallo kawai take amma ta gagara cewa komai, ai tana ganin motarsu ta bar gidan ta nufi ƙofa da sauri har tana tuntuɓe ta buɗe ta fito, Amira ta ɗauko mayafinta da ta shigo da shi a hannu ta biyo ta tana faɗin

“muje ki sauƙe ni a gida ni wallahi bazaki barni ni kaɗai anan ba”

ko kulata Nuwaira bata yi ba ta nufi motar ta kamar zata tashi sama ta buɗe motar ta shiga ba tare da ta jira Amira dake sauri ba ta ja motar a ɗari ta nufi gate, ko ƙarasa rufe gate basu yi ba bayan fitar su Ahmad ganin yadda ta doso gate ya sa suka buɗe mata ta fice a gidan a ɗari.

Tsayawa turus Amira tayi tana bin motar Nuwa da kallo kafin itama ta juya da gudu ta koma part ɗinta, ta haura sama da gudu ta ɗauko makullin motarta ta sauƙo ta fice a gidan itama kamar zata tashi sama, gudu gudu ta ƙarasa parking space na part ɗinta ta shige motarta tayi reverse hannunta na rawa zuciyarta na bugawa dan gani take kafin ta fita a gidan Ahmad zai iya dawowa ya rutsata, suka sake buɗe mata gate itama ta fice a gidan a 360 ta nufi gidansu.

Yana fitowa a asibitin aka fara yayyafi, ya ƙarasa ya buɗe motarsa ya shiga ya ja ta da mahaukacin gudu ya bar asibitin, maimaita maganar da yasmeen ta faɗa masa kawai yake a kansa, yadda wipers ɗin motar suke aiki steady kamar suna matching da bugun da ƙirjinsa keyi ya sa ya runtse idanunsa ya buɗe yana furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa, fuskar Na’ima kawai ke dawo masa cikin idanunsa, yadda yatsunsu ke kwance a fuskarta alamun marukan da suka kikkifa mata ne yana sa yana jin idan bai halaka Nuwaira da Amira ba zuciyarsa bazata taɓa masa sassauci ba, ya daki steering da ƙarfi, wani irin guilt yake ji, ji yake kamar shine ya ja mata komai, saboda shi aka mata duk ma abinda aka mata, tunda ta aureshi ta rasa peace, the only peaceful days da ta samu shine kafin a kawota gidansa? He couldnt keep her safe like he promised, meyasa ma ya dawo da ita gidan? Meyasa baiyi insisting on roƙon Mami ta barsu a gida daban ba? Ya ƙara gudun motar, its not just anger kaɗai its a new animal in him that rise, the one that wants nothing but revenge. Nuwaira da Amira ya rantse da Allahn da ya haliccesa they’ll pay, so yake duniya ta shaida abinda suka aikata duk da after dealing with them baya tunanin duniya zata shaida kamanninsu.

A cikin ruwan aka buɗe masa gate ko aknowledging dinsu bai yi ba ya shige da motarsa yayi parking da kyau ya buɗe ya sauƙo ya nufi part ɗin Amira, ruwan da baiyi ƙarfi sosai ba na jiƙa rigarsa da har lokacin ke da jinin Na’ima a jiki, not just rigarsa har wandonsa a ɓace yake da stains na jinin cause of yadda ya ɗaurata a jikinsa gabaɗaya.

Gidan tsit kamar anyi mutuwa, Mary ta buɗe masa ƙofar dan itama duk ta gagara zaune ta gagara tsaye, dan ta tabbata gidan babu lafiya, tun daga ƙasa yake kiran Amira a zuciye ya nufi stairs yana haurasu bibbiyu uku uku, jikin Mary kama rawa yayi sanin Amira bata nan gashi bata san yadda zata ce masa bata nan ba, a yadda ta gansa da yanayinsa kaɗai bazama ta fara ce masa kanzil ba, jikinsa da ke da stains na jini ya sake tabbatar mata babu lafiya, kuma ba ƙaramin abu bane yake faruwa a gidan, ita dama tunda Nuwaira ta zo gidan ta san baza’a yi abin kai ba yau kam, tana ta tsaye a palourn ya shiga sauƙowa, ta koma ƙofar kitchen ta tsaya a wajen a tsorace, har ya nufi ƙofa ya dawo yana kallonta yace

“Where’s she?” Ta shiga in ina tace

“She left, she’s…not in the house”

“Come and get out!” Ya faɗa yana kallon Mary dake tsaye a bakin ƙofar ta gyaɗa masa kai da gudu ta nufi ƙofa da niyyar shiga ruwan kawai ta bar gidan ya fi mata kwanciyar hankali, har ta isa ƙofar zata buɗe taji muryarsa kuma yace

“Wait! a ɗauke ruwa then u leave, banson ganin kowa a gidannan”

ta gyaɗa masa kai da sauri, ya laluba wandonsa ya kwashe duka kuɗin ciki ya ajiye mata a kan center table, dawowa tayi cikin palourn tana masa godiya ya juya ya nufi ƙofa ya fita, bai damu da ruwan da ya fara ƙara yawa ba ya nufi gate, walking like the Man dat he’s, Ɗaya daga cikinsu da ya hangosa ya fito daga ɗakinsu sauran ma duk suka fito a ruwan dukansu sanye da uniforms suka tsaya suna jiran ya ƙaraso. Har gate ɗin ya ƙaraso yana kallonsu fuskarsa a mugun ɗaure ransa a mugun ɓace yace

“Wa yace ku barsu su fita a gidannan?” Duk suka tsaya suna kallonsa confused, dan su basu san me ke faruwa ba takamaimai a gidan, Ɗaya ne yayi ƙarfin halin cewa

“Wallahi bamu san ba ka so su fita ba we’re so…”

“Shut the hell up?” Ya faɗa yana juyawa ya fuskancesa kamar dama jira yake yayi maganar

“Where is u guys common sense? After what happened ina buƙatar faɗa muku dont let anybody out?” Haƙuri suka shiga bayarwa, ya runtse idanunsa yana ƙoƙarin calming kansa down dan ya san ba laifinsu bane suma basu da hurumin hana Amira fita a gidan tunda bai bada wannan dokar ba, kuma basu san me details ɗin abinda ke faruwa ba, ya buɗe idanun a hankali ya kallesu ɗaya bayan ɗayan kafin yace

“Mary is leaving! Idan ta fita bana buƙatar kowa ya shigo min gida ko wanene shi without my permission” gyaɗa masa kai suka yi a tare suna haɗa baki wajen faɗin

“Okay sir” ya juya ba tare da ya amsa ba ya nufi part ɗin Na’ima duk suka bisa da kallo hankalinsu duk ya gama tashi.

Tsayawa kawai yayi yana bin palourn da kallo, from plate ɗin noodles ɗin da Na’ima take ci dake ajiye akan tray, plate ɗin Saif da ke kife a gefe ga noodles ɗin duk a zube a ƙasa sun bushe zuwa wayarta dake yashe shima a gefe sai kuma jininta dake malale a ƙasan tiles kusa da stairs wanda ganin jinin kaɗai shattered his mind, ya ɗaura tafukan hannunsa a fuskarsa ruwa masu zafi suka cika idanunsa, ya kai kusan minti 10 a haka yana sauƙe ajiyar zuciya mai zafi kafin ya cire hannunsa a fuskarsa, gwara da bai samu Amira a gidannan ba dan he might kill her shi ya sani, wani irin tsanarta yake ji da bai taɓa jin irinsa ba, ya sunkaya ya ɗaga cushion dake kan carpet ya ajiye shi akan kujera mazauninsa ya fara shirya cushions ɗin wajen duka, ya sunkuya ya ɗauki plate ɗin Saif ya saka hannu yana kwashe noodles ɗin yana zubawa a kwanan kafin ya haɗa da tray ɗin da nata plate ɗin ya wuce kitchen, ya tsaya yana kallon kitchen ɗin da yake nan tsaf da shi kafin ya ƙarasa ya ajiye tray ɗin a sink, ya buɗe inda take ajiye kayan gyaran gidan ya kwaso su duka ya zo ya fara gyaran palourn ba ji ba gani, yana yi yana sauƙe ajiyar zuciya, so kawai yake ya samu sassaucin zafin da ransa ke masa kar ya aikata abinda zaiyi dana sani, ya gama goge palourn tass, yayi vocuming ko ina kafin ya haura sama riƙe da wayarsa da wayar Na’ima da ya ɗauko a ƙasan, tun a stairs ya zare shirt ɗinshi ya bar iya wando yana shigowa yayi cilli da wayoyin kan gado ya wuce banɗaki, a ƙasan bathroom ɗin ya yarda rigar ya ƙarasa ya sakar ma kansa ruwan shower tun daga tsakiyar kansa yana sauƙa a jikinsa yana jiƙa har wandon jikinsa, ya saka hannayensa ya dafe bango yana sauƙe ajiyar zuciya a jejjere.

Ya daɗe a tsaye a wajen amma har lokacin zafin da zuciyarsa ke masa babu abinda ya ragu, replaying image ɗin kawai ƙwaƙwalwarsa ke masa, bai san iya lokacin da ya ɗauka a bayinba kafin ya kashe shower ɗin ya zare jiƙaƙƙen wandon tare da drying kansa mechanically ya ɗauro alwala dan azahar tayi, ya ɗauro towel a waist ɗinsa ya fito a banɗakin, plain shirt fara kawai ya ɗauko ya saka a jikinsa da trouser ya shinfiɗa dadduma ya fara sallah, a sujjadar ƙarshe ya daɗe kansa a ƙasa yana roƙar sassaucin abinda yake ji daga wajen Allah kafin ya ɗago kansa, yana sallame sallar wayarsa dake kan gado tare da na Na’ima ya fara ringing, ya tsaya daga inda yake yana kallon wayar har sai da kiran ya katse aka sake kira ya sake katsewa aka sake fara kira a karo na uku kafin ya miƙe ya nufi wayar, ya tsaya a gaban gadon yana kallon wayar dake kan gadon ganin Ammi ke kira ya ɗan shafa kansa kaɗan tare da kai hannu ya ɗauki wayar ya ɗaga kiran ya saka a speaker ya mayar ya ajiye tare da zama a gefen bed ɗin ya dafe kansa.

“Ahmad” muryar Ammi ya karaɗe ɗakin babu komai a cikin muryarta sai zallar lallashi. Muryarsa a ɗan shaqe yace

“Ammi..”

“Kana ina ne?” Shiru ya ɗanyi kafin yace

“Gida” Ammi ma tayi shiru kafin can tace

“To ka taho asibiti yanzu, the doctors wants to see u, tun ɗazu ake kiranka baka ɗauka”

“Ok” kawai yace yayi shiru, itama rasa abin ce masa ya sa ta kashe wayar cike da tausayinsa.

Ya miƙe ya ɗauki wayarsa da na Na’ima ya nufi ƙofa ya fito dan a motarsa ma ya bar key ɗin tun ɗazu bai zare ba.

Ɗakin Na’ima ya shiga ya janyo bedside ɗinta ya ɗauko key ɗin motarta tare da fitowa ya nufi ƙasa, yana sauƙowa bai ko sake kallon palourn ba ya nufi ƙofa ya fice a gidan ya tafi parking space ɗinta ya buɗe motarta ya shiga ya ja aka buɗe masa gate ya bar gidan dan lokacin har ruwa ya ɗauke sai sanyi da garin yayi kamar ba da rana bane lokacin.

Asibiti ya nufa straight duk da yadda zuciyarsa ke cike da fargabar abinda zai je can ya tarar, driving yake cike da concentration ba kamar ɗazu ba, dan zuwa yanzu ya gama yanke hukuncin da zai ɗauka akan Nuwaira da Amira but yanzu ba ta su yake ba zai juyo gare su bari ya tabbatar Na’ima is in safe spot first, kiran Nasir da ke ta shigowa wayarsa ma ƙin ɗauka yayi, yayi ignoring kawai dan ya san labari ya iskesu ne kuma shi a halin yanzu baya son explaining anything to anyone, yana parking ya sauƙo ya nufi cikin asibitin, a reception yaci karo da Nasir dake tsaye riƙe da wayarsa ya sauƙe ajiyar zuciya kawai tare da ƙarasowa yana kallon Fadila dake zaune idanunta kumbure dan kuka ga inaaya a hannun Yasmeen, Nasir ya miƙa masa hannu, kallon hannun kawai yayi kafin ya bashi shima suka gaisa ya ƙarasa inda Ammi ke zaune ya zauna a gefenta a hankali, Ammi ta dinga kallonsa dan Awanni kacal amma gani tayi kamar har ya faɗa mata a idanu, tayi ƙasa da muryarta ta kira sunansa ya juyo ya kalleta yace

“Na’am” shiru tayi bata ce masa komai ba tana kallonsa ya sunkuyar da kansa tare da miƙewa dan zuwa office ɗin doctor ɗin, Nasir ya bi bayansa suka wuce tare dan Shi Nasir ɗinne ma suka yi magana da Doctor ɗin yanzu shiyasa yake ta kiransa Dr yace he needs to see Na’ima’s husband.

Kallon doctor ɗin kawai Ahmad ke yi baya ko ƙiftawa bayan ya gama masu bayanin Na’ima had a miscarriage wai sunyi all they could but coulnd save the babies saboda basu yi ƙwari ba, zaune kawai yayi a kujerar yana kallon likitan kamar shine mai laifin, zai iya cewa yau is the worst day of his life, babu wani rana da zai iya zuwa masa as black as wannan, idanunsa suka kaɗa suka yi ja, Nasir dake tsaye gefensa ya dafa kafaɗarsa tare da ɗan bubbugawa a hankali alamun rarrashi amma shi kansa yayi baƙin cikin rasa cikin da Na’ima tayi, shi shaida ne na yadda Ahmad ke son haihuwa bare kuma cikin na Na’ima ya san dole abin ya dake sa fiye da misali, the fact that yaran ma ba ɗaya bane makes everything worse. Lumshe idanunsa Ahmad yayi ya buɗe a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallon likitan yace

“When? How many babies are there?” Likitan ya sauƙe ajiyar zuciya dan he could sense pain ɗin dake cikin muryar Ahmad ɗin yace

“2 babies ne but Before arrival already tayi miscarrieing ɗaya, one of the sacs ya riga ya collapsing before ma ku kawota, after ultra sound there’s still one a lokacin there’s still a heartbeat but bleeding da take yi heavily yasa duk ƙoƙarinmu na stablizing ɗayan it didnt survive either, munyi duk yadda zamu iya i’m sorry, amma ita yanzu munyi stablizing ɗinta she’s out of danger she’s sedated yanzu tana buƙatar hutu sosai, we’ll monitor her closely in sha Allah”

gyaɗa masa kai kawai Ahmad yayi bakinsa dry, idanunsa yayi ja not from hawaye but from abinda ya fi su zafi, ya miƙe daga kujerar tare da nufar ƙofa, Nasir ya kalli doctor ɗin yace

“Thank you” kafin ya bi bayan Ahmad ɗin, yana fitowa bai tsaya ma a inda su Ammi suke ba hakan yasa duk suka bishi da kallo har ya sake ficewa, Nasir da ya biyo bayansa Ammi ta kira tana tambayarsa what happened hakan ya sa ya bar binsa ya tsaya yana musu bayani, duk gabaɗaya jikinsu sake sanyi yayi tausayin Na’ima da Ahmad ɗin duk ya cikasu, fadila ta komar da kanta ta kwantar jikin bango tana tunanin yadda su Mami zasu ji news ɗinnan suma, dan tuni ta kirasu ta faɗa musu abinda ya faru na dukan da kuma asibitin da Na’ima take yanzu, har suna hanyar juyowa lagos duk da a jiya suka koma Abuja, this time around har da Fahad duk zasu taho, sosai hankalin Mami ke tashe guilt yaƙi barinta gani take ita ta jawa Na’ima da ta sa ta koma gidan, me ma yasa bata barta ya canza mata gidan ba? Yanzu kuma ko ya zata ji idan taji Na’ima ta rasa babies ɗinta? Big Daddy da shi faɗila ta fara kira ta faɗawa ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba, and he promise basu daki banza ba, bazasu daki yar sa su tafi a ɓagas ba yanzu shima idan yaji batun miscarriage ɗin ya zaiyi? dama fahad Fadila na faɗa masa yace he’s coming to lagos with su Mami.

Ahmad na shiga motarsa ya rufe kansa tare da buɗe wayarsa ya shiga neman number abokinsa Yusuf, the soldier dat helped him aka kama sadiq sanda yayi kidnapping Na’ima. Cause what he’s about to do yanzu baya son kowa yayi inteferring kuma ya san tabbass Yusuf bazai bari ayi inteferring ba.

Tunda Amira ta iso gida ta ma mummynta bayanin abinda ya faru mummy ke bala’i da tsinewa Nuwaira ita dai Amira har lokacin jininta a ƙumba yake tunda tasan gidan ba baƙon Ahmad bane in har yayi niyyar zuwa ɗin.

Sai yanzu take dana sanin biyewa Nuwaira su aikata abinda suka aikata amma still jin irin tsinuwar da zagin da mummy ke wa Nuwaira tace

“Mummy dan Allah ki bar zaginta haka, she did dat saboda taga halin da nake ciki a gidan, kin san halinta idan aka min abu she use to take it personal more than me, nima ina dana sanin abinda mukayi cause na san Albi wallahi sai ya ɗauki mataki, amma in sha Allah komai zai zo da sauƙi in Allah ya yarda”

mummy ta zabga mata wani harara tana neman layin mijinta a karo na ba adadi har lokacin user busy wayarsa ke nuna mata, rabonta da shi tun shekaran jiya, jiransa take ya dawo gidan ta sauƙe masa kwandon bala’i sai kuma ga Amira ta kawo mata wani sabon tashin hankali, kamar dai bata san halin Ahmad ba da zuciyar babansa ya ɗibo ai wallahi ita ta san he wont let dis slide.

Ganin wayar taƙi connecting ta cillar da wayar tana faɗin

“Amira call ur father for me ta wayarki kar ku haukatani daga ke har shi ku barni dan zatin Allah in ji da guda ɗaya”

Amira dake zaune a kujera tace

“ai na baro wayar a gida, dan Allah keep on trying mummy yadda ke da shi zaku haɗu ku bawa Albi haƙuri dan Allah ya yafe min”

Janyo wayar Mummy tayi tana hamdala ganin call din detective din da ta saka shi ya dubo mata komai akan daddy din tana faɗin

“in ya san wata bai san wata ba yanzu zan san a inda yake kuma wallahi ba ƙaramin hauka zan masa ba zai faɗa min dalilinsa na ƙin ɗaukar wayarsa da zuwa gidannan tun shekaran jiya bayan yana ƙasarnan”.

Mummy na daga kiran ta dinga masifa tanama detective din fada coz tun jiya take jiran call dinshi be kiraba kuma yace kada a kirashi he will call her himself

daga daya bangaren mutumin babu abunda yake se bata hakuri tare da fada mata ya tura mata aikin via watsapp ta duba ta gani komai da komai,sannan ya kara da cewa

“for the past week dat ive been following him baya zuwa ko ina sai waje ɗaya, and he’s currently there yanzu haka ma” Mummy ta kalli Amira da ke zaune tare da faɗin

“Good, send me the address right away” tana faɗa ta kashe wayar tare da miƙewa tace

“Tashi ki ɗauko mayafinki ki raka ni” Amira ta kwanta a kujera tare da girgiza mata kai

“Kije ki dawo kawai mummy tsoron fita nake wallahi”

Wucewa sama mummy tayi tana faɗin

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved