Chapter 52: Chapter 52
“To kar ki je, idan Ahmad ɗin ya zo nan gidan bama nan duka ai kin huta” da sauri Amira ta tashi zaune tare da miƙewa tabi bayan Mummy dan zuwa ɗauko mayafinta, dan da gaskiyar mummy da ya zo ya same ta a gidan ita kaɗai gwara a gaban mummynta.
Tare suka sauƙo mummy na riƙe da key ɗin mota suka fito suka nufi parking space, mummy na miƙawa Amira wayarta tace
“Dinga duba min location ɗin as am driving zai faɗa min uban abinda yake yi a wajennan for 3 days without coming home”
Amira ta karɓi wayar tare da shiga motar itama mummy ta shiga mazaunin driver tana ajiye gyalenta akan cinyarta ta tada motar suka bar gidan Amira kuma na ƙoƙarin duba location ɗin inda zasu.
Zuba ma location ɗin idanu tayi tana ta kallon dot ɗin map ɗin kamar wawuya, can ta kalli mummy kamar zata yi magana sai kuma ta fasa, a zuciyarta tana ayyana me daddynta ke yi a unguwar gidan Nuwaira?, mummy da ta hau titi sosai ta juyo tana kallon Amira tace
“Where is he?” Ɗan sake kallon Screen ɗin tayi a hankali tace
“Ba nisa” Mummy ta ja tsaki tare da saka hannu ta ƙwace wayarta tana duba inda zasu, Amira ta mayar da kanta ta kwantar a seat, she wish tana tare da wayarta da ta kira Nuwaira taji ko tana gida since unguwar zasu.
Ita dai mummy bata sake kulata ba ta cigaba da driving ɗinta tana bin direction ɗin map ɗin.
Parking tayi a layin ta kashe motar tare da sake buɗe saƙon detective ɗin ta duba house number da ya bata kafin ta kalli Amira tace
“Sauƙa muje” ita kam Amira kallon layin kawai take, ganin har mummy ta sauƙa ya sa itama ta sauƙo a motar tana gyara gyalen da ta yafo akan gashinta ta bi bayan mummy walking slowly saboda ganin gate ɗin gidan da mummy ta nufa,
Mummy na isowa gate ta shiga knocking gate man ya leƙo yana kallonta yace
“Yes, wa kike nema?”
Zuwaira ta buɗe baki da niyyar masa masifa Amira ta rigata magana tare da riƙe hannunta alamun tayi shiru, muryarta a hankali tace
“Open up ni ce” sai a lokacin ya kula da Amira, ya ƙarasa fitowa yana faɗin
“Ina wuni hajiya, sannu da zuwa” ta ɗan masa murmushi kawai ya koma ciki da sauri tare da buɗe musu ƙaramar ƙofar suka shigo suma, ya sake kallon Amira yace
“Ai ban san tare da ke bane hajiya ayi haƙuri dan Allah” murmushin yaƙe kawai ta masa tana ƙarema ƙaramar space na compound ɗin kallo, gidan da ta zo shi babu adadi, idanunta ya sauƙa akan motar Nuwaira da ta daddynta dake tsakar gidan,
kama hannunta Mummy tayi ta nufi ƙofar palourn tana tambayarta a inda mai gadi ya santa yake gaisheta, jin bata amsa ba ta koma zancen motar daddy dake compound ɗin
“Ba na faɗa miki ba? Ba dai kin gani da idanunki ba abinda babanki yake yi Amira, duk abinda zan masa yau babu ruwanki”
itakam bin mummy kawai take yi kamar mutum mutumi har lokacin calculating take acikin kanta abinda Daddynta yake yi a gidan Nuwaira? Its not like suna shiri shima sosai da Nuwairar, ya ɗauki many of her responsibilities back then amma duka saboda ita yayi kuma yanzu baya ɗaukar komai na Nuwaira ita take ma kanta komai da kanta, to ko dai mijin da ta aura ya san daddynta ne? To ko motar mijinnata ne ma she mistook for na daddynta? Ta juya ta sake kallon motar, its definitely na daddy, dawo da idanunta tayi kan mummynta da ta fara knocking ɗin ƙofar palourn babu ƙaƙƙautawa ta jingina jikinta da bangon wajen tana kallon ƙofar ƙuri waiting for Nuwaira to open ta san she’s misunderstanding something kuma Nuwaira na buɗewa zata mata bayani ta cire ta a cikin duhu.
Nuwaira dake kwance jikin daddy tana game a wayarta jin knocking ɗin yaƙi ci yaƙi cinyewa ta tashi zaune tana faɗin
“Wani isashshe ne kuma da yammar nan?” Ta faɗa tana sauƙa a gadon ta saka takalmanta ta nufi ƙofa tana haɗe ranta dan ta san bazai wuce an dawo da laundry bane ake mata wannan uban bugun, kuma zata ci uwar lawisa da ta bari har ake wannan shegen bugun ƙofar bazata je ta buɗe ƙofa ba, Daddy ya miƙe ya biyo bayanta daga shi sai wando shima iya gwuiwa da singlet dan in dai tana gidan to ko jela anan ya gansa ya barsa, duk inda tayi haka yake binta sai dai in ita tace ya bar binta.
Tana fitowa palour yayi daidai da fitowar mai aikinta daga kitchen zata je ta buɗe ƙofar dan ta tsaya kwashe abin da ke wuta ne itama Allah Allah take ta zo ta buɗe kar Nuwaira ta taso, Nuwaira ta zabga mata wani kallon banza tace
“Dan ubanki lawisa baki ji ana buga ƙofa bane har sai da na taso dan tsabar raini da iskanci da wulaƙanci?”
Lawisa ta yi saurin tsugunawa a inda take tana faɗin
“Kiyi haƙuri anty na kwashe abin kan wuta ne kar ya ƙone tunda jira kike yanzu zani in buɗe”
Nuwaira ta tsaya tana kallonta wani mugun kallo har ta kai aya kafin ta daka mata wani mugun tsawa da yasa daddy dake bayanta ya ɗan matsa gefe ya tsaya,
tana nuna lawisa da hannu tace
“Tashi ki ɓace min da gani kar in zo in zauna a ruwan cikinki in sa kiyi kashin hanjinci ta baki, in kuma ci ubanki shegiya ƙazama mara jin magana kawai, wallahi garinku zaki koma shegiya mummuna kije can ki cigaba da surfen da kike tunda ni zaki dinga ɓata wa rai jakar banza”
tuni itakam lawisa ta ɓace a palourn, dan indan irin waɗannan ne ta saba, Nuwaira har dukanta take akan abu kaɗan sai ta lakaɗa mata tsinannen duka har da muciya.
Nuwaira ta ja tsaki tare da Kallon Daddy dake tsaye yana kallonta, ta ɗan masa murmushi, matsowa yayi kusa da ita yana faɗin
“kina bari ranki yana ɓaci a banza princess” ta sake jan ƙaramar tsaki ta juya ta kalli ƙofa jin sai bugun ake har lokacin ta nufi ƙofa tana faɗin
“Amma duk ɗan shegiyar da ke min wannan bugun zanci uwarsa, wani irin tsinannen bugu ne wannnan? ku karya ƙofar ku huta mana bana son iskanci” daddy ya bi bayanta yana kai hannunsa waist ɗinta tare da faɗin
“Sorry princess” ta buɗe key ɗin ƙofar da niyyar surfa ma duk ma waye a bakin ƙofar kwandon bala’in da har abada bazai sake mata irin wannan arnen buga ƙofar ba idan ta kama ma ta fyaffyalla masa mari, turus ta tsaya tana kallon Mummy da ta kawo hannu zata sake bugawa duk da tana jiyo masifar Nuwaira daga ciki aka buɗe ƙofar.
Ba iya Amira ba Mummy kanta maƙalewa hannunta yayi a iska tana kallon Nuwaira dake sanye da gajeren wando da top, attach ɗin kanta ta dawo da shi ta gaban ƙirjinta, ga daddy a bayanta da farar singlet da ya nuna girman tumbinsa shima da gajeren wando hannunsa a waist ɗinta.
dama ita Amira tunda ta jiyo muryar Nuwaira da masifar da take a ciki ta tashi ta tsaya da kyau ko blinking bata sake ba ta zubawa ƙofar idanu tana jira ta buɗe, tana buɗewa kuwa duniyar gabaɗaya ta tsaya mata cak, idanun Amira ya shige cikin Na nuwaira, her best friend, her sister, her everything, tare da babanta a tsaye a ƙofar gidan Aminiyartata da hannun daddynnata a waist ɗin Aminiyar tata, brain ɗinta ɗinta refused to accept abinda idanunta ke screaming, guiwowinta taji sun sage kamar an tsoma ta a ƙanƙara, kallon kallo kawai suke yi gabaki ɗayansu a bakin ƙofar babu mai ƙarfin halin ƙwaƙƙwarar motsi, wani irin shock ne da dukkaninsu basu tsammaci shi a yau ba, Yadda Amira ke kallon Nuwaira idanu waje haka itama take kallonta fuskarta expressionless kamar ba Nuwairarta ba, Daddy dake tsaye a bayan Nuwaira ya cire hannunsa a waist ɗinta yana kallon Zuwaira da itama ba shi take kallo ba Nuwaira kawai take kallo cike da abinda yafi al’ajabi, bakin mummy na rawa tace
“Nuwaira!” Sai a lokacin Nuwaira ta sake kallonta na daƙiƙa ɗaya ta wani irin ɗaure fuskarta kamar bata taɓa dariya ba sai kuma ta ja tsaki ta mayar da ƙofar ta rufe in their face tare da murza key, kamar irin bata taɓa saninsu ko ganinsu ɗinnan ba.
mummy jikinta rawa kawai yake irin na confusion da rashin sanin abinyi dan ba abinda tayi tsammanin tararwa ba kenan at all, ta juya ta kalli Amira irin kallon kin gani koh? Amma dukkansu babu wanda ya iya ƙwaƙƙwaran motsi har lokacin Amira kallon ƙofar take idanunta a ƙaƙƙafe kamar bata duniyarda mummynta take, ita wata duniyar take gabaɗaya, suna ta kallon ƙofar in ultimate disblieve kawai dukansu,
mummy ce ta tattaro ƙarfinta duka tayi cilli da gyalenta ta shiga buga ƙofar da ƙarfi kamar mahaukaciya tana jijjigasa tana faɗin
“Nuwaira! Nuwaira! Shegiya karuwa, ʼyar balaja’u, idan kin isa cikin uwarki da ubanki ki zo ki buɗe ƙofarnan, idan kin haifu cikin uwarki da ubanki nace, shegiya haihuwar asara, annamimiya, asararriya, da haihuwarki gwara ɓarinki, ʼyar iska kafira la’ananniya, kai kuma jaki, tambaɗaɗɗe ƙawar ʼyarka Musa, goat kawai dukanku la’anannu yan bura’ub….” Ji tayi numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa ta fashe da kuka tana dukan ƙofar da duka ƙarfinta kafin ta juyo da nufin komawa kan Amira da ita ce ta ja musu, itace ta yarda da Nuwaira ɗari bisa ɗari amma sai gani tayi Amirar ta tafi baya luuu zata faɗi, is like tun ɗazu da take tsaye ƙwaƙwalwarta assimilating abinda ke faruwa yake, all of a sudden ƙwaƙwalwarta komawa tayi tana tafiya slow a gane abubuwa sai yanzu ne ta gama fahimtar abinda ke faruwa a wajen, gani tayi idanunta ya mata duhu gabaɗaya bata ganin komai duk da yadda yake wide open, zuciyarta tayi wani irin mummunar bugawa guda ɗaya da ya sa ta tafi baya gabaɗaya zata zube, mummy ta taho da gudu ta riƙeta ta hanata buga kanta da ƙasan wajen tana rungumota jikinta da faɗin
“Amira! Amira! Amira!” Tana tapping fuskarta amma inaa babu ko ɗigon numfashi a tare da ita, mummy ta zunduma ihu tare da faɗin
“Amira miye haka? Kashe kanki zakiyi? Amira!” Ta faɗa da ihu da kururuwa da yasa mai gadi tahowa wajen da sauri yana faɗin
“Subhanallah hajiya me ya faru” Mummy da duk ta daburce tana kuka tace
“Bawan Allah ka taimake ni Amira ta mutu na shiga uku ka taimaka min motata na waje ka kaimin ita mota muje asibiti dan soyayyarka da Ma’aiki”
ai ko ƙarasawa bata yi na ya sunkuya tare da cicciɓar amira da ta sanƙare kamar block, jikinta ya sassandare ya nufi gate da ita da gudu, mummy ta miƙe tabi bayansa da gudu leaving mayafansu duka a bakin ƙofar tana cigaba da kuka da ihu kamar taɓaɓɓiya, a bayan motarta ya shinfiɗe mata Amira yana faɗin
“Allah ya bata lafiya hajiya..” mummy da majina ke zuba a hancinta tsabar kuka bata damu da ta goge ba ta buɗe gaba ta shiga tare da tada motar ta jata da gudun fanfalaƙi ta bar layin tana cigaba da kiran sunan Amira.
Mai gadi na dawowa ciki ya nufi ƙofar palourn ya tattare mayafan ya ƙarasa ya buga ƙofar tare da sallama, Nuwaira da ke zaune a palour tana cin dankalin da lawisa ta kwaso mata a plate tana jiyo duk iface ifacen mummy a tsakar gida ta juya ta kalli ƙofa jin sallamar mai gadi, kallon Daddy dake kwance shima a kujera yayi shiru yana kallonta tayi tace
“Buɗe ƙofar ina jin sun tafi” ya amsa da
“Toh” tare da miƙewa ya nufi ƙofa ya buɗe yana kallon mai gadi kafin yace
“Ya akayi?” Miƙa masa gyalen yayi yace
“hajiya ce tayi baƙi amma ina jin ƙawartata bata da lafiya ne kafin su kaiga shigowa gidan ta sume yanzu sun tafi asibiti da ita shine nace bari in sanar da hajiya halin da ake ciki”
nuwaira ta ajiye fork ɗin hannunta dan tana jiyo abinda suke faɗa ta miƙe ta nufo ƙofar tana kallon mai gadin tace
“To sannu munafuki, ɗan iska, mai kaɗa ma kashi kuka, ni zaka ma munafurci iliya? Uwata ce ta suma zaka kwaso mayafai ka kawo min wai wata ta suma a ƙofata? Ko ce maka aka yi bani da kunnuwan jin duk abinda ke faruwa?”
Shiru iliya yayi yana kallonta shima cike da mamaki saboda shi dai ya san alaƙarsu sosai tunda ya fara gadin gidannan, like Nuwaira tana da ƙawaye amma ko a cikin ƙawayenta Amira ta fita daban. Ya ɗan sunkuyar da kansa yace
“Ayi haƙuri” daga haka ya juya da nufin komawa gate da mayafan a hannunsa har ya ɗanyi nisa Nuwaira ta fito a palournta a yadda take da gajeren wandon ta biyoshi tsakar gidan tana faɗin
“Kai wuce kaje ka tattara tarkacenka ka barmin gida tunda ba na iyayenka bane, je ka na sallameka munafukin banza”
shi dai bai sake juyowa ba ya cigaba da tafiya towards ɗakinsa dan ya san bata haƙuri ma ɓata baki ne da ƙara ma kai wulaƙanci, gwara kawai ya rufa ma kansa asiri yaje ya tattara ya tafi inda aka san darajarsa dama me yake tsinana a gidan banda takaici? Masifar yau daban ta gobe daban, albashi bazata biya ba sai ta ga dama babu kyautatawa babu komai.
Nuwaira ta dinga huci tana kallonsa kafin ta juya ta dawo palourn tana kallon daddy tace
“A samo sabon gate man before tomorrow” amsa mata yayi da “to”
kafin ya rufe ƙofar ya biyota yana faɗin
“but haka yau za’a kwana babu gateman?”
“Eh” kawai ta faɗa tana ɗaukar kwanon dankalinta tana sake haɗe ranta ta nufi ɗaki shima ya bita a baya yana cigaba da mata magana.
Daf da magriba Nuwaira na zaune a palour tana cin cake daddy kuma na ɗaki saboda ta ce ta gaji ya daina binta up and down aka ƙwanƙwasa ƙofa, ta juya ta kalli ƙofar kafin tayi magana lawisa ta fito da sauri ta nufi ƙofa dan buɗewa, nuwaira ta cigaba da cin cake ɗinta dan yunwa take ji gashi yar banzar lawisa bata gama girkin dare ba.
Lawisa na buɗe ƙofar ta koma baya da sauri ganin sojoji in uniforms da ke bakin ƙofar, Nuwaira ta kalli ƙofa da niyyar tambayar lawisa su waye sai gani tayi sojoji sun shigo palourn kusan su 6 da boots a ƙafafunsu kuma da alama sunfi haka yawa a waje, Nuwaira ta miƙe tsaye tana kallonsu tuni zuciyarta ta tsinke ta tsaya tana kallonsu, kar dai Amira ce ta ɗebo mata sojoji amma tabbass da zata ci uwar Amira iya cin uwa,
tayi ƙarfin hali riƙe kunkumi tana kallonsu tace
“Miye haka?who gave u permission na shigo min cikin gida?” Ɗaya daga cikinsu ya mata wani banzan kallo fuskarsa babu alamun rahama yace
“Madam wuce mu tafi, idan kina son lafiyarki dont argue we need to deliver u kamar yadda aka bada umarni”
Nuwaira tayi wani dariya na ƙarfin hali tana kallonsa kafin tace
“Wa ya baku umarni? Ku kaini ina?for what? Ita wacce ta aikoku ɗin ku koma ku ce mata baku ganni ba nafi ƙarfinta wallah..…” ko rufe baki batayi ba ta ji jinta ya ɗauke ɗum sakamakon wani haɗaɗɗen mari da ya kife ta da shi, tayi baya baya kamar zata faɗi tana dafe kuncinta, ɗayan ne ya kalli ɗayan yace
“I dont think zata tafi da kanta ɗauko min ita”
ganin sun dunfarota ta taƙarƙare ta ƙwallo ma daddy kira
“sugar!” Daddy ya fito sanye da jallabiya yana ganin abinda ke faruwa a palourn ya ƙaraso da sauri yana faɗin
“Whats going on here?” Nuwaira ta tafi da gudu ta koma bayansa ta laɓe tana tattare doguwar rigar da ta saka not long ago.
Ko kulashi basu yi ba ɗayan ya kamo Nuwaira daga bayansa dan order da aka basu shine su kawo Nuwaira, in ma ta tako da ƙafarta ko a su kawota karairaye.
Nuwaira ta fara ihu tana riƙe daddy ta fara zage zage tana faɗin basu isa ba da ƙoƙarin dambe da soldier hakan yasa soldier lanƙwasa hannunta ya tsugunar da ita akan guiwarta yana ɗauke fuskarta da tafi.
Daddy ya matso da sauri yana faɗin
“What nonsense? Akan me zaku shigo har gida kuce zaku tafi min da mata babu warrant babu komai? This is unprofessional and i can sue u for that” ko kulashi basu yi ba, dan su ba peace ne ya kawosu violence ne ya kaeo su, da peace ne ya kawosu da sun taho da female soldier dan ɗaukar Nuwairar, ƙafa soldier yasa dake cikin booth ya naushi bakin Nuwaira da ta buɗe ta lailayo zagi jin daddy na tsaya mata, tayi baya ta faɗi a wajen bakinta ya fashe tare da hayewa lokaci guda ta saka ihu, ya sa ƙafa yayi pinning ɗinta da ƙasa ɗayan yazo ya ɗaure hannayenta da wani strap mai ƙarfi kafin su ɗagata dragging her out of the palour, itadai lawisa na gefe ta toshe bakinta hankali tashe tana kallon abinda ke faruwa, suna isa daf da ƙofa daddy ya taho ya tare ƙofar dan ji yake kamar da rayuwarsa zasu tafi hankalinsa duk ya gama tashi duk ya gigice ya shiga faɗin
“Ku rabu da ita, ko nawa suka biyaku zan baku ninkinsa ku saketa dan Alllah”
ɗayan wanda kamar shine shugabansu a ɗakin ya ma daddy wani banzan kallo kafin yace
“Step aside” Cike da taurin kai yace
“Ba fa inda zaku da ita” ɗauke sa da mari guy ɗin yayi yana sa ƙafa yayi ball da shi da dole ya matsa a ƙofar, dan as far as he’s concerned he dont care shi waye bare ma bai sanshi ba, Nuwaira ta saka ihu tana faɗin
“Sugarrrr!” Daddy ya miƙe yana huci da kallonsu yace
“Ull pay dukanku wallahi you will pay, princess go with dem ill come and bail u out, ill make dem regret taɓaki”
tasa ƙeyarta sukayi dragging her out of the house tana kuka da kiran daddy dan yanayin sojoji is not friendly at all at all, haka suka cusa ta a mota cikin biyu da suka zo da shi suka ja suka bar unguwar.
daddy da ya biyosu har waje ya bisu da kallo kafin ya koma cikin gidan kamar zai tashi sama dan ɗauko wayarsa ya fara neman hanyan fitar da princess ɗinsa daga inda zasu kaita yanzu.
Tunda suka iso asibitin aka shige da Amira ɗakin mummy ke tsaye a waje tana rawar jiki banda kuka da tsinewa nuwaira babu abinda take yi, damuwa ya haɗu mata goma da ashirin ji take kamar itama zata iya sumewa a halin da take ciki na tashin hankali a asibitin, duk likitan da ya fito sai ta bishi tana
“Please save my daughter, dan Allah ina bata mutu ba” ba ƙaramin ɗaga mata hankali halin da Amira ta shiga yayi ba. Babu wanda ke kulata cikinsu dole ya sa ta koma ta zauna a kujera tana share hancinta da Addu’ar Allah ya bar mata Amirarta a raye Allah ya ba ma Amirarta lafiya dan itakam ta tsorata ba ɗan kaɗan ba at the same time ta ɗauki alwashin saka Nuwaira da daddy dana sani, ta ma kanta alƙawarin sai Nuwaira ta yi dana sanin haifota da uwarta tayi duniya.
A cikin ɗakin likitoci biyu dake kan Amira ɗayan ya kalli Nurse yana frowning deeply bayan duba pulse ɗinta yace
“Her pulse is weak, get me oxygen immediately” da Sauri Nurse ɗin ta ɗauko oxygen ɗin aka fara mata fixing a fuskarta dan ya taimakawa numfashinta da ke ƙin bada haɗin kai , sauran kuma suka shiga preparing iv line.
ɗan motsi kaɗan Amira tayi hannunta yayi sanyi kamar ta sa a ƙanƙara.
Ganin Bp ɗinta yana dropping fast yasa suka fara ƙoƙarin stabilzing ɗinta ba ji ba gani ana pushing fluids, duk a ƙoƙarin daidaita pressure ɗinta, babu abinda kake ji a ɗakin sai ƙarar monitor, yadda beat ɗin ke fita kamar zai tsaya, kamar ko wani beat zai iya zama na ƙarshenta.
Ba ƙaramin wahala likitocin suka sha ba dan da ƙyar take responding to abubuwan da suke mata, ɗayan likitan ya kalli ɗayan yace
“She’s still in hypovolemic shock, idan bamu stabilizing ɗinta ba nan da few minutes zamu iya rasa ta, jikinta is shutting down..” ko ƙarasawa baiyi ba monitors ɗin suka fara beeping zuciyarta is crashing, hankalinsu ya sake tashi tuni likitan ya buƙaci defibrillator, haka aka dinga pressing ɗinsa against ƙirjinta ana aika mata shock dan ceto numfashinta, da ƙyar da suɗin goshi aka ƙwato numfashinta, line ɗin jikin screen ɗin ya dawo weakly.
Ajiyar zuciya suka sauƙe a tare “she’s back!” Dukansu kallonta kawai suke holding their breath har sai da lines ɗin jikin screen ɗin suka dawo steadied alamar she’s stabilized amma har lokacin bata motsin komai, from minutes har zuwa hours amma har sannan babu alamun motsi a tattare da Amira, doctor ɗin ya zare mask ɗinsa yana sauƙe ajiyar zuciya yace
“Ta dawo! Tana raye, amma…” sai kuma yayi shiru kawai ya kalli nurse yace
“Sedate her, a barta under oxygen support, a sanar da family ɗinta”
Mummy na zaune a kujera a waje aka buɗe ƙofar ta miƙe da sauri tana ƙarasowa dan jin yadda ake ciki idanunta jajir kamar gauta, ba tare da ɓata mata lokaci ba ya fara mata bayanin halin da ake ciki, ya kalli mummy tare da sauƙe ajiyar zuciya yace
“Madam, yarki suffered severe shock, munyi managing daidaita Bugun zuciyarta amma her body have shut down into a coma, tana raye amma she’s unconcious, bazan iya ce miki ga sanda zata tashi ba, zai iya ɗaukan kwanaki” wani kalan ihu Mummy ta zunduma da yasa likitan ja baya kaɗan yana kallonta ta zube a ƙasa tana kuka iya ranta, tana faɗin Nuwaira da daddy sun cuceta zasu kashe mata yarinya, kafin ta miƙe da sauri tana kallon likitan da ke kallonta shima cikeda tausayi tace
“Likita ka faɗamin kwanaki nawa zatayi a haka, dan Allah ka faɗa min, in ta mutu ne ma ka faɗa min” ya girgiza kansa yace
“Bata mutu ba she’s very much Alive, zata farfaɗo soon in sha Allah ki kwantar da hankalinki ki mata addu’a cause awannin da zasu biyo baya are critical for her” daga haka ya wuce ta yana sake jin tausayinsu.
Mummy ta ƙarasa tana leƙa Amira ta glass dake kwance motionless akan gado, zagaye da Na’urori wai sune suke taimaka mata numfashi kamar ba ita bace da safiya lafiyarta lau har da rana zuwanta gidan duk lafiyarta lau, me ya sa ma ta ɗauke ta ta tafi da ita? She wish ta barta a gida wayyo Allahnta dama sai da tace bazata je ba.



