Chapter 6: Chapter 6
sha’awar masu kudi take yi a zuciyar Malaika. Ya fara tunanin yadda zai raba alakar Nasrin da Malaika.
Bayan magruba Kanwarsa ta zo daga Muntsira Sadiyalle, sai Malaika ta bar Ahmad da Sadiyalle ta fito kan baranda inda Shamaki ya sami lungu ya takure yana ta damunta da waya.
Ta zo ta tsaya a gabansa kerere ta ce, “meye wai?”
Ya langwabar da kai yace, “Malaika!
zauna mu yi magana dan Allah, ta fahimta.” Ta zauna a fusace tana turo baki, Shamaki ya yi gyaran murya yana mammatsa hannu kamar marar gaskiya yayin da zuciyarsa ke dukan uku-uku.
Ya ce, “Malaika! Na san na ɓata miki rai amma ki yi min uzuri. Wallahi ban tashi dą ko sisi ba ciki da waje, haka na fita na duba gabas da yamma, kudu da arewa na rasa in da zan nufa, na so in je Bichi wajen aikina in samu a ranta min in an yi albashi a dauka na tuna yau asabar babu kowa a sakateriyar. Na juya zan shiga B.U.K na tuna bamu da Lacca yau sai
karfe hudu babu wandazan samu, in takaice miki har kantin kwari na je na yi bara, ina nuna katin asibiti, basu bani ba suka zage ni wai an sami sabuwar danfara kato da ni mutuwar zuciya ce in je in yi dako ko faskare mana. Na gasgata sun fadi gaskiya.
Na je kasuwar singa zanyi dako, na ji kudin da za’a biya ni a yini ma ba zai isa ko rabin kudin maganin ba. Na so in siyar da wayata ma na ji anyi min tayin wulakanci, kudin ba zai sayi magani ba.
Daga karshe naga bani da mafita sai na je na sami Fatima Giwa wata attajirar matace, daya daga cikin matan ajinmu a gidanta. Na yi mata bayani ita ta taimaka min da kudin magani, ta bani naira dubu goma. ”
Malaika ta harare shi ta ce, “Fatima Giwa ‘yar ajinku ko bazawararka?”
Ya girgiza kai yace, “matar aure ce ma tana auren wani attajiri a Nassarawa GRA, ban taɓa sanin gidan ba sai yau da ta kama,da naga bani da mafita, direbanta ma na kira ya bani shawara in zo zata taimaka min dan mun saba
DA MA NI CE…
da shi. Daman itace take siya min handout ni kuma nake bata amsa.” ”
Malaika ta taɓe baki ta ce, “in tayi tsami za mu ji, in an yi magana ace ni nake makalewa masu kudi. Kai yanzu me yasa baka makalewa talakawan ajin na ku ba su ‘yar shila amma ka Makalewa Giwar, saboda tafi maiko, da tsoka ko?”
Shamaki ya tabbatar Malaika bata da tausayi ta juya maganar gaba ɗaya zuwa wani sashi, sai ya yi shiru bai bata amsa ba.
Aka jima ya ɗago ya dube ta yace, “a ina kika sami kuɗi kika sayi magunguna da kayan shayi?”
Ta harare shi ta ce, “a wajen ‘yar ajinmu nima na samu Nasrin Giwa.’ ”
Ya daɗe yana kallonta kallo na takaici ya rasa amsar da zai bata.
Ya ce “rokarta kika yi kika ce na kasa?” Malaika ta zabura ta mike tsaye ta kama kugu ta ce “ba ka kasa din ba ne? Da ka fitaka dawo da wuri ne? Sai in bar dan nawa ya mutu? Daga yau na sami abin gori nima dagaka ce na
makalewa Nasrin zan ce kai ma ka makalewa Fatima Giwa.”
Ta juya ta tafi a fusace ta bar shi anan a zaune yana kallonta, kwalla ta cika masa ido. Ya girgiza kai ya sunkuyar da idanuwansa kasa sai hawaye ya surnano. Yana ta girgiza kai yana tausayin kansa da kansa yana mai takaicinjarabawar (test) din da ya rasa yau a makaranta. Yana kuma fargabar ko dansa zai tashi ko zai rasu, saboda jikin ya tsananta, yana tunanin halin da ya bar yaransa guda biyu a gidan makwabta. Ko ana kula da su ko kuwa an bar su da yunwa? Ya shiga tunanin kudin da za’a bukata nan gaba a asibiti dan bashi da su, bai san in da zai tafi nema ba kuma. tsaye akansa tana
Sadiyalle ya gani a kallonsa cike da tausayi ta ce, “Shamaki kuka kake yi? Ka yi hakuri komai yana da iyaka. Allah Yana tare da makurci. .
Sai ta rushe da kuka, shima ya fara kuka har zuwa lokaci mai tsawo babu wanda ya iya magana a cikinsu.
DA MA NI CE…
Shamaki ya mike tsaye ya kalle ta da jajayen idanuwansa yace “mu je gidan dare ya dan ki kula da su Aliyu.”
Su ka isa wajen Babur dinsa suka hau, suka tafi. A hanya sadiyalle take bashi labarin zamanta a gidan mijita. Itace mata ta uku, bata taɓa haihuwa ba amma tana ganin masifa a gidan nan, mijin baya tsinana masu komai sai dai kowacce ta nemo. Ta kara da cewa tana mamakin yadda Malaika bata godewa Allah da duk irin kokarin da mijinta yake yi mataba.
Shamaki ya yiwa kanwarsa nasihohi akan ta ci gaba da hakuri kuma idan ya gama karatu albashinsa zai karu zai dinga taimaka mata.
Su ka isa gida yace ta shiga Makwabta ta ɗauko yaran, tana shiga sai ta iske yaran a kwance a zaure cikin akuyoyi, matar gidan ta turo su ta rufe dakinta da yaranta, da alama suñ sha kuka sannan suka gaji suka yi bacci, yunwa ce a cikinsu daga gani dan cikin da doron bayan sun haɗe. Sadiyalle bata ji dadi ba ta kamo hannunsu ranta a ɓace suka fito suka iske shamaki a kofar gidan.
DÀ MA NI CE… ↑ Yana ganinsu ya tambaya “ba dai a zaure kika dauko su ba, dan na ga daga shigar ki kin fito.”
Ta fada masa a halin da ta gansu, sai ya ji ransa ya ɓaci ya kudiri a niyyar ba zai sake barin yaransa a gidan makwabta ba. Ya bawa Sadiyalle Mukullin gidan, yace bari ya je ya suyo musu abinci, ya hau babur ya tafi. Ita kuma ta bude gida suka shiga tsakar gida ta shinfida musu tabarma suka zauna. Ba jimawa sai ga Shamaki ya siyo musu dafafiyar indomie da kwai a cikin ledoji. Su ka yi ta ci hannu baka hannu kwarya, da alama ko abincin safe ba ‘a basu ba balle na rana da na dare. Shaniaki fada “daman
ya a bayyane Uwale bata da mutunci, dan rashin imani ta bar min yara da yunwa?”
Sadiyalle ta ce “wallahi wani abun ma saboda kai ake yin kara ake yi, amma ba dan Malaika ba. Aka bibiya ita ma Malaika tana yiwa ‘ya’yanta rashin mutunci. Kai a ganinka Malaika zata rike wa Uwale yaranta ta ciyar da su na yini guda?”
Shamaki ya gyada kai yace, “da wannan dan wannan.”
Sadiyalle ta ce, “yanzun ma saboda nauyin kai ka tura su ya sa ta karɓa. Sau nawa nake jin Malaika tana zagin Uwale ta ce sun yi zage-zage. Ai rashin kirkinta ne ya jawo aka yiwa nata haka.’ ”
Bayan sun gama ci Sadiyalle da yara suka shiga ɗaki suka kwanta, Shamaki ya shiga falo ya kwanta akan doguwar kujera, baccin gajiya ya kwashe su su dukka basu farka ba sai da assalatu.
*** *** ***
RANAR LAHADI.. .KANO ° Tun bayan da suka idar da Sallah Sadiyalle da Shamaki suka yi ta hidimar gida, Shara, wanke wanke, dafa abinci da wankin kayan fitsari.
Sadiyalle ta yi tsaki ta fada a bayyane “gaskiya Malaika kazama ce, Shamaki kalli yadda yana da kura su ka yanyame ko ina, datti kamar babu bil’adama a gidan. Wai me Malaika take yi ta bar gidanta a haka?”
DA MA NICE…
Shamaki ya yi tsaki ya harare ta, ya ce, “dalla Malama ki gyara in da zaki gyara, bana son yawan magana da cin naman mutum dan baya kusa. A gabanta za ki iya fadar haka?”
Da alama ya ji haushi dan an caccaki rabin ransa Malaika. Sai Sadiyalle ta zunɓuro baki bata kara magana ba, ta turo baki gaba.
Da misalin karfe tara na safe suka gama shiryawa tsaf, Sadiyalle ta dauko leda ta zubo kayan sakawar Malaika da na Ahmad, brush, makilin, soso da sabulu, suka jifgu akan babur su dukka ga kaya ga yara suka tafi.
Suka isa cikin asibitin, bayan ya nemi waje a wata inuwa ya tsaya sai suka dunguma cikin dakin su dukka dauke da filasanabinci a hannunsu.
Tun daga nesa suka hango Malaika cikin tashinhankali, ta tsaya a tsakiyar ɗakin ta ɗora hannu aka kamar maishirin kurma ihu.Sai suka tsaya cak sannan suka ci gaba da tahowa amma fa suna karanto
“Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un.’
☐
DA MA NI CE Tun Shamaki bai karaso ba ya gama fahimtar abinda ya afku, sai ya saki kayan da yake hannunsa ya kwaɗa salati a bayyane.
Malaika na ganinsa ta tahoda gudu ta rirrike shi ta na kururuwa, kukan da yake tafe da dinbun hawaye ta ce, “Shamaki! Ahmad ya rasu da asuba.’ ”
Sai hawaye ya surnano daga idanuwansa ya zame hula ya rike a hannu yana tafe yana sanɗa har ya karasa wajen gawar, ya buɗe a hankali, ya yin da kirjinsa yake ta faman dukan uku-uku. Ya dubi Ahmad yaro a mimmike daga kashi sai fata.
Ya shafa kansa ya fada a bayyane “Kulli Nafsin za’ikatil maut. Ahand! Allah ya jikanka ya baka uwar goyo a Aljanna. Mu ma muna nan tafe, ba mu yi jinkiri ba, haka kai da ka tafi yanzu baka yi gaggawa ba.” ”
Ba Malaika kadai ba, gaba daya ‘yan dakin da ma’aikatan sai da Shamaki ya basu tausayi, hawaye kawai zaka dinga gani a idanuwan manya maza da mata. Sun tausayawa Shamaki da Malaika sun tausayawa Ahmad yaron ya sha wuya, suna kuma masu tausayin
kansu da kansu, suma wataran zasu zama gawa tabbas.
Nan dai Shamaki ya yi ta maza ya nufi wajen Ma’aikatan lafiya suka ci gaba da tattaunawa akan fom din da zai cike da kuma yadda zai dauki gawar. An ɓata lokaci, daga karshe ya samo mota tasi aka saka gawar, Malaika, yara da Sadiyalle suka shiga suka tafi, bayan an saka ganye a bayan motar shaidar motar da gawa, duk wanda ya gani sai ya kauce ya basu waje.
Shamaki ya tsaya a jikin babur dinsa yana ta bugawa Makwabta da ‘yan uwa na can garin su, ‘yan uwansa da ‘yan uwan Malaika waya ya sanar da su anyi rasuwa duk mai hali ya zo jana’inza. Daga karshe ya hau Babur dinsa ya biyo su gida. Kafin ya karaso Mata sun cika gidan ana ta kuka. Malaika kam har rirrike ta ake yi tana ta kururuwa, mutuwar nan ta s shige ta an tausaya mata, ta sha jigila da yaron nan tunda ta haife shi bata hutaba. Daidai lokacin Nasrin ta kira wayar Malaika dan ta tambayi mai jiki, wayar a
hannu Sadiyalle sai ta shaida mata Malaika ba
NI CE… zata iya amsa wayaba saboda danta ya rasu ko binne shi ba’ayi ba. Kafin ma Sadiyalle ta fadawa Nasrin haka kuruwar kukan Malaika ta tabbatar mata da haka. Nasrin mai tausayi sai ta ji hankalinta ya tashi, tausayi ya lullɓe ta ta fara zubar da hawaye, ta kashe wayaba tare da ta ce wa Sadiyalle komai ba.
DA MA
Ta shaidawa Zainab yayarta halin da Malaika ta ke ciki sai jikin Zainab ya yi sanyi dan ita neman haihuwar ma take bata samu ba, sai yanzu ne take da karamin ciki.
Nasrin ta bugawa kawar Dinah waya ta shaida mata abinda ya sami Malaika, duk da Dinah bata sansu ba amma ta ji tausayinta, ta yiwa Nasrin gaisuwa ta ce ta yiwa Malaika idan sun yi waya. Haka Nasrin ta kasance yini guda cikin sanyin jiki mutuwar ta shige ta.
Aka binne Ahmad aka ci gaba da zaman makoki, Sai da daddare bayan komai ya lafa sannan Nasrin ta sake kiran Malaika ta yi mata gaisuwa gami da yi mata wa’azi akan dangana. Malaika tana ta kuka abin tausayi har sai da Nasrin ta yi kamar itama ta barke da kuka.
Da yake Malaika ‘yar dangice jama’a daga Muntsira suka yi ta diddikowa suna zuwa gaisuwa, haka dangin Shamaki da abokansa na Bichi da na BUK suka yi ta zuwa matansu da Mazansu.
Anan ne Malaika ta ga Fatima Giwa. Duk da an yi mata mutuwa amma sai da ta jinjina kyau da kudi irin na Fatima, farar shuwa kal. Ta kawo musu buhunhunan shinakafa biyu da Kudi naira dubu goma. Malaika ta dauko kwaraɓɓiyar wayarta ta karɓi lambar Fatima Giwa abin takaici kowa ya gane, bata karɓi lambar wayar kowa ba sai ta mai kudi..
***
***
***
Bayan kwanaki bakwai sannan kowa ya watse aka bar Malaika da Shamaki sai sauran yaransu guda biyu, su kaɗai jugum, sai a lokacin mutuwar ta dawo musu sabuwa fil. Malaika bata da aiki sai kuka Shamaki yana ta lallashinta. Yana ta lallaɓata duk wani abu da zai kwantar mata da hankali shi yake yi. Sun sassami kudi amma duk ya tattara ya damka
mata dan ta ji sanyi a ranta dan ya san ita
masoyiyarsu ce.
Va yayi
sanyi kalau da alama ta fara saduda da kyalkyalin duniya. Ba’ataɓa yi mata mutuwar da ta ji a jikinta ba sai wannan karon, kasancewar Uwa da uba da wasu kakaninta duk suna raye haka ‘yan gidansu wajen su talatin suna nan da rai, da wayonta babu wanda ya taɓa mutuwa. Haka shima Shamaki bayan Mahaifinsa da ya mutu yana karami bai san shi ba. Kakansa da ‘yan uwansa duk suna raye dan haka sai yanzu aka fara yi masa mutuwa. Sun yi kuka sun gaji Ahmad ya tafi ba zai dawo ba. Allah ya kyautata karshenmu. shi ba. Mahaifiyarsa, vidid net
Malaika jikinta
mullum Nasrin ta yi kokarinzumunci dan sai ta kira Malaika ta yi mata ta’aziyya kala jumata taʼaziva idan Shamaki na kusa ta ce a bashi shima. Malaik ta mika masa shima ta yi masa taʼaziyya. Ta yi mata alkawarin idan aiki ya yi sauki zata shigo Kano ta yi mata ta’azivya melicu sist azıyya. UCH IV:
Malaika ta ji dadi kwarai da wannan kulawa ta sharariyar mai kudi da take yi mata.
s at out a omum
stop det oM Schuede ennem a ovadonat Us
DA MA NI CE…
BABI NA BAKWAI
RANAR ASABAR. .ABUJA
au asabar ce, da misalin karfe goma sha daya na safe, Nasrin
tana zaune a falo da kofin shayi a hannunta. Dakyar take kurɓar shayin saboda yanayin zazzaɓin da take ciki. Ita kadai ce a gidan daga ita sai wayarta da take karancekarance a facebook.
Ta ci karo da sababbin rubutun Dr.Jalo tana ta bibiya amma bata yi niyyar tofa albarkacin bakinta ba. Kamar daga sama ta gan shi ya hau (online) bata yi masa magana ba dan bata shirya kwasar takaicin shariya ba, ta kanta take yi yau.
Sai ta zaci mafarki take da taga ya yi mata sallam. Ta amsa, ya sake gaishe ta. Nan da nan ta gyara zama ta ji sanyin da take ji ya fara gushewa dan har zufa ta fara feso mata. Ta cika da murna a take ta amsa masa. Ya tambaye ta menene tambayarta? Me take so ta
koya daga gare shi da take cewa tana so ta zama kamar sa?
Nasrin ta kaikaice ta yabe shi, ta koɗa shi, ta jinjina masa, sannan ta ce yana birge ta ne haka kawai.
Da alama ya ji dadin kalamanta shima sai ya yi mata godiya data sami dama takebiye da shi.
Ta nemi ya fada mata mafita game da wata matsalar aure dan taga rannan ya yi magana akantaɓarɓarewar auren Bahaushe. A takaice ta bashi labarin Malaika, sannan ta bashi labarin Shamaki kamar yadda suka bata. Ta shaida masa ta yi hira da mijin ba tare da matar ta sani ba haka ta yi hira da matar ba tare da mijin ya sani ba, kowannensu abinda ya faɗa daban ne ta rasa mai gaskiya a cikinsu.
Dr.Jalo ya yi murmushi ya rubuto mata bayanai a tsare daki-daki, ya jero matsaloli ya jero mafita. Daga bayanansa ta fara samun mafitar matsalolin auren Shamaki da Malaika. Ta ji dadi sosai ta yiwa Dakta godiya daya bata dama da lokacinsa yau. Shima ya yi godiya ya sauka.
CE… Sai Nasrin ta nemi zazzaɓi ta rasa, ta ware ragas, ta yi tsalle ta dire tana ta rawar murna ita kadai a cikin falo.Hakika mahakurci shine mawadaci. Ta jwo wayarta da karfin gwiwarta ta kira
DA MA NI
wayar Malaika.
Malaika ta amsa amma tana ta magana kasa-kasa cikin rada, da alama ba ita kaɗai bace a in da take tana tare da mutane Malaika ta shaida mata ta fito unguwa ne sai ta koma gida zata kira ta.
Nasrin ta kashe waya tana kashewa ta kira wayar Shamaki da karfin guiwarta tana, murna ta samo masa mafita, Shamaki na ganin kiran Nasrin sai ya ji ransa ya ɓaci, yayi jagejage da garin fulawa yana kicin yana kwaɓin danwake, yara suna ta kuka suna jin yunwa. Malaika ta fita unguwa bada izininsa ba. Gaba daya yana zargin Nasrin dasake ɓata masa Mata, dan ta turo mata katin dubu uku jiya shi ta siyar ta sami kudin hawa A-daidai-ta-sahu ta shiga gari.
Ya na kallon wayar ya ki dauka sai a karo biyu data sake kira, ya dauka a fusace
yana huci, Nasrin ta yi sallama sai ta ji ya ja dogon tsaki ya katse.
Ta cika da mamaki bata tunanin hakan yake nufi dan haka ta sake kira, ya dauka tana gaishe shi sai ya yi mata tsawa “Menene kuma? Kawar ta ki bata nan.
Ya kashe wayarsa ma gaba ɗaya. Nasrin ta sankare a zaune tana ta mamaki da takaicin abinda Shamaki ya yi mata, lallai ya wulakanta ta, ba’a taɓa yi mata irin abinda ya yi mataba a yau, ta fuskanci haushinta yake ji. Ta shiga zulumi shin ko dan bata zo musu gaisuwar mutuwa bane? To su a suwa da za zasu kullace ta dan bata zo gaisuwa ba? Yaushe suka santa ma da zai zama laifi? Gaisuwar data yi musu a waya ma ai ta isa. Kai! Ba wannan ba ne. Anya Shamaki bai fara kishi badan ya gaMalaika tana yawan zancenta da nemanta a waya?Dole da daya daga cikin wadannan abubuwan da ta zaiyano a ranta. . Nasrin ta damu da wannan yankwanawa
da Shamaki ya yi mata, gashi shi ba kowan kowa ba. Amma ta kudiri niyyar ko ya kira ta ba zata sake ɗauka ba, itama har abada ba zata
DA MA NI CE…
sake kiransa ba. A fusace ta goge lambarsa tana ta faman hucin takaici, ta rasa wanda zata faɗawa wannan mummunan labarin, ta ji sanyi a ranta.
Ta jawo wayarta a sanyaye ta kira lambar Jalo, cike da fargaba kada ta sake haduwa da wulakanci irin wanda Shamaki ya yi mata. Tana kira ta ji Mace kamila ta amsa, sai gabanta ya fadi ta yi kamar ta katse wayar sai ta daure, ta san dai matarsa ce tabbas.
Cikin ladabi Nasrin ta gaishe ta sannan ta shiga in-ina wajen gabatar da kanta.
Matar ta yi murmushi ta ce, “bari akai masa wayar. Ga Jalon can.” ”
Tana jin karar tafiyar matar har ta isa in da yake ta mika masa wayar, sai Nasrin ta shiga kogin mamaki gami da jinjina ga wannan mace ta gari marar kishi. Hakika ilimi ya yi a rayuwa rashin ilimi ke sa mata yin taɓargaza da sunan wai kishi. Haka kawai sai su binciki lambar mace a wayar mijinsu su kira suna zaginta, shima miji a tutsiye shi ayi ta rigima. Dr.Jalo ya karɓi waya bayan ya duba sunan mai kiran. Ta ji kamar a dakile baya
walwala a yadda yake amsa gaisuwar, dan haka sai ta shiga damuwa.
Nasrin ta ce, “na kira in gaishe ka ne kawai, sorry ban san kana gida ba ina fatan banyi laifi ba, uban gidana?”
Ya yi dan murmushi ya girgiza kai ‘ yace “ko kaɗan bakiyi laifiba, za ki iya kira kowanne lokaci.’ ”
Nasrin ta lumshe ido ta ce, “haba dai kowanne lokaci, ai ko Madam bata damuwa idan taga kiran ya yi yawa zata zargi wani abu.’ ”
Ya girgiza kai yace, “Madam babu ruwanta. ”
Nasrin ta gyada kai ta ce, “amma ina jinjina ga wannan gwarzuwar Mace ta gari, ta fahimci mijinta yadda ya kainata.”
Ya yi murmushi ya ce, “da Mamata kika yi magana yanzu ba da Madam ba.” وو
Sai Nasrin ta sake tsunduma cikin sabon kogin mamaki tana linkaya.
Ta tambaya a cikin zuciyarta “Me yasa mahaifiyarsa ta dauki wayarsa ta amsa sannan
kuma bashi ya zo ya karɓa ita ta tafi ta kai masa? Lallai dan gata ne, ya cika sarauta.” ”
Nasrin ta yi ajiayar zuciya ta ce “daman maganar ma’auratan nan ne nake so in baka labarin yadda muka yi, na kira su ɗazu zan basu shawara kamar yadda kace in basu sai aka sami matsala.’ ”
Yace “mu koma online mu yi bayani na fi kaunar rubutu (chats).”
Sai ta amsa masa cikin ladabi, suka kashe waya
. Nasrin da Jalo sun dauki awanni biyu cur suna hira a rubuce,idan ta fadi matsala sai ya faca mata mafita. Har ta gangaro matsalarta da wanda zata aura Fu’ad, ta fada masa halayɩnsa wanda take ganin aure da shi ba zai yiwu ba, yana da yawan fushi sai ya yi wata guda cur yana yi mata gaba. Jalo ya bata shawarwarin yadda zata bi ta gyara shi.
Tabbas ya shaida mata Shamaki ya fara jin haushinta yana zargin kudin da take bawa matarsa yana kara jawowa ta raina shi. “Meye mafita?” Nasrin ta tambaya
Jalo ya bata karfin guiwa ta ci gaba da jajaircewa zata sami lada. Kada ta yi fushi kuma kada ta gajiya.
Wayar Nasrin ceke ta ruri tana dubawa taga Malaika ce ta tabbatar ta dawo daga unguwa sai ta amsa da sauri. Da yake da computer take hirar da Jalo, tana waya tana bashi amsa.
“Innalillahi wa’inna ilaihi rajun.” Nasrin ta faɗa a lokacin da ta ji Malaika na kuka kamar ranta zai fita.
Nasrin ta tambaya “yaya aka yi?”
Malaika ta shaida mata Shamaki ya sake ta har yayi mata watsi da kaya.
Sai ta ji jiri ya fara daukarta ga Jalo a Computer yana ta jero zancen mafita, nan kuma aure ya taɓarbare.Sai ta kurawa rubutun Jalo ido babu abinda zata iya yi a yanzu.
Nasrin ta katse waya tana ta huci ta sake gasgatawa Shamaki mugun bawa ne shi yake cutar da Malaika, tabbas shine makaryaci, labarin duk da ya bata karya ne. Yana da kudi yake ɓoyewa yake bin karuwai.Duk da ta goge
DA MA NICE
lambarsa dazu, amma ta na da ita ala ‘dailledcalls’ da ta kira shi dazun. woorisjej
Nasrin ta kira wayarsa a fusace daman da haushin wulakancin da yayi mata ɗazu sai ta hada ta cashe masa.assislaM syst
☐ yana tashuciny Shima ya amsa a fusace ace “menene kuma? Ai ta faru ta kare, sai ta kaura Abuja wajenki ta zauna, saboda ke ta ki zaman aure ta raina mijinta. ;
aires Nasrin ta fusata ta ce, “baka da adalci, baka san darajar aure ba.. Me ya kawo maganar saki?” siit is inT TEMES
Yace “au har ta kira ta fada miki na sake



