⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 7: Chapter 7

ta? To ni ban sakin matata ba idan burinki kenan.” ayed sb fetsw stem iyey isd st Bol Sai Nasrin ta yi kasake ta kasa gane kan wannan matsala. Ta kashe wayarta ta koma ga Dr. Jalo ta iske ya sauka baya kusa. Nasrin tá sulale ta kwanta tana mai tsananin damuwalda shiga rudani. Mafita daya itace ta fita daga harkar Malaika da Shamaki kawai. Daman bata sansu ba balle matsalarsu ta zame mata matsale. Bata da hawan jini samma da nalama agog et ab oluⱭ.iswi aid exsy swayed by

Shamaki da da Malaika zasu saka mata. Toh wai me ya yi zafi ido zai ci wuta?
*** *** ***
Da daddare misalin karfe goma da rabi na dare taga Dr.Jalo a facebook ta gaishe shi ya amsa amma sai ta ji ya ambace ta dawani suna wanda ya bata mamaki.
Nasrin Abdul Nasir (kueen), bata yi mamaki mai yawa ba dan dai bata rubuta wannan sunan akan Username dinta ba. Ta tabbatar ya yi bincike akanta, yau ya gano kowacece Nasrin kuma me yasa take ta bibiyar rubutunsa tana so su saba. Sai yanzu ya gane da wa yake magana ashe da cikakiyar ‘yar jarida yake magana, wacce take daya daga cikin mata ‘yan jaridar da suke burge shi wadanda suka san makamar aiki. Dr.Jalo ya jero mata waɗannan manyan
kalamai na jinjina. Sai ta ji tamkar a mafarki take ganin wadannan kalamai nasa, ta tabbatar yanzu ta zama mutum sosai a wajensa tun da andzadad ng joint enou

har ya damu ya bincika ya san ko ita wacece, lallai ta sami shiga. Ta yi masa godiya, sun kai karfe sha biyu na dare suna ta magana a facebook, . sannan suka yi sallma kowa ya sauka, bata damu da kwanciya da wuri ba saboda gobe lahadi babu aiki.
Tana duba wayarta ashe Malaika ta kikkira ta da yawa, bata ji ba saboda ta saka wayar a silent tun da yamma da suka ɓata mata rai. Tana gani ta yi tsaki ta turo baki kafin ta ankara Malaika ta sake kiranta. Nasrin ta danna a fusace tana jira ta ji abinda Malaika zata ce,sannan ta yi mata wankin babban bargo. Malaika tana ta kuka har yanzu ta ce “Nasrin! Ki taimake ni ina cikin wani hali. Shamaki ya kore ni kuma ya bani kwana daya in kwashe kayana, na je gidanmu ana ta zagi ana cewa basu da inda zasu saka ni da kayana, sai dai in san na yi. Ki taimake ni ki bani adireshinki in taho a Abuja wajenki tunda bani goyo kuma ya kwace ‘ya’yansa.’ da ” Nasrin ta ji tamkar Malaika ta caka mata wuka a kahon zuci na takaici, ga hausshin

DA MA NI CE…
Shamaki gami da tausayin Malaika, ga haushin jin danyen hukunci da Malaika ta yanke na zuwa wajenta.
“Ta zo wajena Abuja ta zauna akan me? Meye hadinna da ita?” Nasrin ta faɗa a cikin zuciyarta.
Nasrin ta dakatar da ita, ta ce, “in takaice miki mijinki yana zargina da kashe muku aure gani yake ni nake zuga ki saboda ina turo miki katin waya, dan haka Malaika kada ki sake nemana a waya balle kice za ki zo gidanmu.Ki je iyayenki da iyayansa su yi muku sulhu ku zauna lafiya, babu in da zaki je ki zauna ki yi daraja wanda ya wuce gidan mijinki, ki rungumi ‘ya’yanki dan babu mai rike miki su ki ga daidai idan bake da kanki ba. Dan Allah Malaika ki cire ni daga cikin mutanen da kika taɓa sani a rayuwa, matsalar gidanki ta dame ni ta tsaye min a rai, gashi ta jawo min zargi da wulakanci daga Shamaki.’ ”
Nasrin ta tsiyayo da hawaye ta katse wayar, tana katsewa ta yi sauri ta goge lambar Malaika daga cikin wayarta. Ta kashe wayar

DA MA NI CE…
gaba ɗaya ma dan taga Malaika tana ta sake
kiranta.
Ta rubutawa Dr.Jalo sako ta ce, “daga karshe wannan auren da muke kokarin ceto rayuwarsa Allah ya yi masa cikawa a yau da yamma. ”
Ta rufe computer ta, ta kwanta cikin gagarumin ɓacin rai.

BABINA TAKWAS
RANAR TALATA ABUJA •
au Dr. Jalo da Nasrin sun daɗe suna a facebook kasancewar ta ga
wadansu sakonninda abokansa su na
tura masa suna yi masasannu da jiki. Ta tabbatar bashi da lafiya, dan haka ta damu tana ta tura masa sakonninfatan samun lafya cikin gaggawa. Ya yi mata godiya saboda kulawarta ya nuna ya ji dadi. Amma ta matsa ya faɗa mata abinda ya ke damunsa, sai bai ce mata komai ba ya ma canja hirar. Gudun kada ta ɓata masa rai sai ta bar zancen, dan taga alamar baya son yawan tambaya.
Daga nan ta shaida masa tana yawan zazzaɓi da ciwon kai kwanan nan. Ta tambaye shi wanne irin magani ya kamata ta sha dan ta warke?
Ya jima bai ba ta amsa ba, daga baya yace ta je asibiti mana. Ta ce tana so ta je amma aiki ke hanata zuwa, kasancewar
Jamila Untar Tanko (JUT)
.
zazzabin dare ne kafin safe ya sauka sai ta
manta ta fita ofis. ХАТ АЙШАЯ Sai yau ya tabbatar mata shi ba likitan yau asibiti ba ne likitan karatu ne kawai. Nasrin ta yi mamaki matuka dan ya yi mata kama da cikakken likita mai farɗe mutum ya dinke. Sai ta ji ta rage mamakin yadda ya zama kwararren marubuči, rubutu masu ma’ masu ma’ana ashe likitan karatu nesanlods sbainnolsa p ebsw
ST Yashaida mata ya karanci English Litraturëb yana koyarwa a jami ar Lagos. Nasrin ta ji dadi kwarai da ta fara sanin wani abu nasa bodsa syibog stem by Y swaggsy
SY BUGSY sbstas y mamaki da ta ji yace ta bashi : bride sisu karanta FT sted tarihiin rayuwarta yana so ya sani.Ta sakon nan daya tura, ya daya tura, ya fi sau biyar dan ta tabbatar haka din yake nufi yake nufi dan kada ta fara zuba alhali bai ce ba. Ta newer sys gasgata haka yake nufis sai ta gyára zama. Ta rubuta ta tura masa ta ce idan bazai damu bazata is bidsvess kira shi su yı new ida magana a waya, zai fi dadiidan suka yi magana baki da baki, ta shaida masa kada ya damu bata biyan kudin katin waya.Nan da nan y nan ya bata izinin, żata iya kira ba damuwa. Farin ciki ya woman swusstened

rufe ta kafin ta kira shi sai da ta kira Dinah ta bata labarin yadda suka yi da Dr.Jalo, ta tabbatar mata yanzu ma zata.kira shi su yi labari.
Dinah ta yi mamaki ta kuma ta taya ta murna ta tabbatar mata ita ma ba zata yi bacci ba har sai sun gama wayar, tana jiran ta kira ta fada mata yadda suka yi, Nasrin ta yi mata alkawari zata kira ta f zata kira ta fada mata komai.
Dinah ta yi mata alkawarin zata dauki jarbi mai dubu ta taya ta da addu’a Allah Ya sa atattauna abubuwa masu alkhairi.
Maganar Dina ta bawa Nasrin dariya kwarai, dan haka ta yi ta dariya ta kashe waya. Ta fada abayyane “Dina shakiyiyar
yarinya ce wallahi.” Ayaw Gab Nasrin ta tashi ta buce firij ta dauko lemon kwali da kofi ta dawo kan gado ta zauna ta nutsu sannan ta kira lambar Jalo, bayan da ta b karanto kula’uzai ta tottofa a kowacce kusurwa ta dakin, ta na neman Allah ya tsare ta da ɓata masa rai ko ta faɗamasa abinda zai sa ya janye daga gare ta.

Data buga bai dauka ba har ta katse sai a karo na biyu aka dauka, maimakon ta ji muryarsa sai ta ji muryar matar nan data dauka ran nan, wacce yace mahaifiyarsa ce.
Nasrin ta zabura ta dukar da kai ta gaishe ta, cikin fara’a ta amsa gami da cewa ki kira nan da mintina goma idan yagama abinda yake yi. Nasrin ta amsa cikin ladabi sannan suka kashe wayar. Sai mamaki ya hana Nasrin rufe bakinta, ta duba agogo taga karfe goma shaɗaya da minti goma sha daya na dare amma Jalo yana tare da mahaifiyarsa.
“Ina matarsa ne? Ko irin mutanen nan ne masu son uwa, har yanzu yana nanike da ita? Daga gani baya ɓoyewa Mahaifiyarsa komai dan wayarsa ma yawanci a wajenta ta ke.’ Nasrin ta ke tambayar zuciyarta. ”
Tana cikin mamaki sai ta ji kira, tana dubawa ta ga shine ta ki amsawa, sai bayan data katse sannan ta kira saboda bata so ta ci masa kudin waya. Tana kira sai ta ga ya katse kiranta, sannan ya kira ta. Ta amsa cikin ladabi ta gaishe shi.

Yace “me yasa za ki kira ni? Ai ni ya kamata in kona katin wayata ba ke ba. Kada ki damu nima katin wayar zai isa mu kwana, mu yini muna hira bai kare ba.”
likita.'” ” Nasrin ta yi dariya ta ce, “na gode kwarai
Ya yi dariya ya girgiza kai yace, “kada ki gode min ki godewa Allah da Ya hada mu, gashi muna ta zumunci muna karuwa da juna. Yau ma na ga rahotanninki a gidan shugaban kasa (Billa), a labarai aka nuna, sannu kina kokari fa har kin fi wasu tsofaffin maʼaikatan sanin makamar aiki.”
Nasrin ta yi dariya ta sosa goshi ta ce, “haba dai muna ta koyo dai, ai ku ne gwanayen magana. Da ma zan iya ganinka in yi hira da kai ka wanke mana ‘yan kudu da suke yiwa ‘yan arewa gani-gani.”
Ya yi dariya yace, “rufa min asiri ni asu wa?”
Ta yi dariya ta ce, “kai kuwa kai ne komai,
amma sannu a hankali zan sanka, na yi alkawari sai na haska ka a duniya, gaba daya

sai an sanka. Kuna da amfani a cikin al’umma.” Ya yi murmushi ya canja hira,yace, “Nasrin, ba ni labarinki. Ina so in san ko ke wacece?” Ta gyara zama ta yi farfari da ido ta yi
gyaran murya.
LABARIN NASRIN:
Ta ce “Sunana Nasrin Mahaifina kuma sunansa Abdul Nasir, sunan mahaifiayata kuma Hajja Khadija. Gaba dayansu daga tsatso daya suka fito ‘yan uwan juna ne kakanninsu ɗaya, jikokin wani shahararren sarki ne mai karfin mulki a arewacin Najeriya. Dan haka jinin sarauta ne.
A daki daya aka rike su, da suka kammala karatun sakandire sai aka daura musu aure daman su na son junansu, aka tura su karatu America, acan suka zauna. Bayan sun kammala karatun jami’a ma basu dawo ba suka fara aiki acan. Haihuwarsu ta farko aka
haifi yayata Zainab wacce nake gidanta anan Abuja,nice ta

DA MA NI CE
biyu sannan aka haifi dan autanmu Nafi’u yana can tare da su shima ya shiga Jami’a. In takaice maka dai Mahaifina shine ambasadan Amerika da yake wakiltar Nigeriya.”
Dr.Jalo ya yi ajiyar zuciya yace, “da kyau. An daɗe ana neman ilimi a duniya ashe?”
Nasrin ta yi dariya, ta ce “gidansu gaba daya ‘yan boko ne abin mamaki kuma duk sai da suka sauke ku’rani tun kafin a saka su a makarantar firamare ma, dan haka hafizai ne, mu ma haka suka yi mana. Akwai wasu ustazan larabawa a Amerika su suka koyar da mu tun muna kanana.”
Jalo yace, ni kwarai.” “masha Allah amma sun birge
Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta sa hannu ta jawo kofi ta tsiyayi lemo ta kora ta ci gaba da cewa, “A Amerika muka yi firamare, muka yi sakandire da jami’a. Amma ni ina yawan zuwa Najeriya akai-akaiduk hutu, wajen kakannina.Amma na fi zuwa a lokacin da Zainab ta yi aure a Najeriya. Yanzu haka bautar kasa ce ta kawo ni. Idan na kammala

zan koma Amerika sai in yi masters da PHDdina, dan ina so in zama Dakta a fanni jarida. La so in zama kamar ka. Suka yi dariya su dukka. ”
Ya ce “in sha Allah Nasrin sai kin fi ni ma dan irin karatuna da naki ma ba daya ba ne, mu da mu ka gama karatu a Najeriya kasar da ake yawan yin yajin aiki, ga wahala. Ku kuwa karatunku babu wata damuwa, kun yi kun kare cikin nutsuwa.
Nasrin ta yi dariya ta ce,”abin ai a kwakwalwa ne, ga shi kuwa a wajenka mu ke koyo.”
Ya ce “kin gama zayyano min karatu amma ban ji kin ambaci aure ba. Ina labarin Fu’ad?”
Nasrin ta yi dariya ta rufe ido da hannunta ta ce “Fu’ad dan gidan Yayan Babana ne, A gidanmu aka rike shi, dan haka gidanmu daya, yana can tare da Baba a Amerika, yana aiki a karkashinsa.
Ta ji muryar mace tana yi masa magana cikin yaren fulatanci, shima ya bada amsa cikin harshen Fulatanci, sanna ya dawo kan Nasrin.

DA MA NI CE
S ” Ya yi dariya yace, “sorry! Muna magana da ke na juya ina magana da Mamata. Ta ce min in je in kwanta haka dare ya yi.”be iam os Nasrin ta yi mamaki ta juya da sauri ta kalli agogo, karfe goma sha biyu saura mintina biyar. end men ofbud
d stTa ce “Allah sarki da gaskiyar Mama
dare ya yi.” new Jalo yace, “to za gobe.” ayaw sismios ad cams iguaz et ab cust mu yi magana sosai que fabi at six stas Nasrin ta yi dariya ta ce, “na gode, Allah Ya tashe mu lafiya.” To adeown) sy loosd
Su ka kashe waya. Gaba dayansu suka kwanta cikin farin ciki da tunani muryoyin juna, da alama muryar Nasrin ta yi matukar tafiya da hankalinsa, haka itama
muryarsa tana burge ta matuka. st husYana ta nanata labarinta yana juya shi a ransa. Ya tabbatar Nasrin ba karamar ‘yar hutu bace, ko ba’a faɗa maka ba daga ganin suffarta da maganarta ba tashin nan bace. imen st danis st Ita kuma tana tamamakin yadda Mahaifiyarsa take tare da shia koda yaushenA”
“saspason nojsw s saitisl
on muslims SI

“Ina matarsa da yaransa ne? Ban taɓa jin muryar yara a cikin gidan ba. Ko irin uwar nan ce mai saka ido akan ‘yayansu su hana su zaman lafiya da matansu? Ko kuwa matar ce ta yi tafiya kasar waje kasancewar ‘ya’yan masu kudin nan haka suke basa kula da mazansu? Oho!” Nasrin na ta tambayar kanta da kanta ba tare da ta sami amsa ba.
Ta ma manta ta yiwa Dinahalkawarin zata kira ta idan sun kammala waya da Jalo, haka ita ma Dina tuni ta yar da carbi gefe, bacci ya kwashe ta.
Asuba ta gari!
Nasrin ta dan makaraam mata yi sauri ta shirya ta fito falo, ta iske Salis ya riga ta fita.Zainab kaɗai ta iske a falo, bayan sun gaisa Zainab ta nemi da Nasrin ta zauna ta ci abinci. Nasrin ta duba agogo ta girgiza kai ta ce “Antimi,yau na makara sosai na san saina amsa laifina a wajen manajana.”

DA MA NI CE T Zainab ta harare ta ce, “kin kwana kina hira da kawaye ko in ce da Mutanen ɓoye su Jalo ko?”
Nasrin bata amsa mataba, ta fice da sauri tana saɓa jakar Lap-top a kafaɗa.
Zainab ta bita da kallo cike da tausayi, saboda wahalar da take sha akan aikin nan data ɗorawa kanta, dan ba dan kudi take yi ba saidan sha’awa da neman suna.
***
***
Nasrin bata dawo gida ba sai da yamma likis karfe biyar na yamma. Tafiya take tana jefa kafa dakyar saboda gajiya ga yunwa. Banda lemon kwalba guda daya babu abinda ta saka a cikin cikinta yau.
Burinta ta ganta a kwance akan gadonta kawai, amma yau ta kudiri niyyar cin abinci da yawa dan har bata gani sosai saboda yunwa.
Ta isa kofar shiga falo, gami da yin sallama sannan ta daga labulen falon ta shiga. Maimakon ta ji muryar Zainab sai ta ji wata murya ta amsa mata. Muryar ta yi mata kama

da muryar da ta taɓa sani amma bata gasgata ba har sai da ta shigo tsakiyar falon ta kalli mai maganar sosai ta gasgata ba gezau ba ne gaskiya ne, ita din ce kuwa.
Malaika Shamaki. ta gani zaune akan luntsumemiyar kujera ta dora kafa daya kan daya tana shan AC ga remote din talabijin a hannunta tana canja tasha yadda take so, ta na karawa kuma tana rage murya. Ta cokalo daurin dankwali gaban goshi, gami da saka wani kwaftareren gilashi baki a fuskarta.
Nasrin ta ji wata gagarimar fargaba ta dira a cikin zuciyarta, ta ji tamkar aradu ce ta sauko a kahon kalbinta. Ta ji rugugin takaici ya taso mata. Ta yi kamar ta dora hannu akai ta rafsa ihu. Sai ta tuna da cewa duk sanda bala’i diro maka ka lakanci karanta ya
“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un.’ ” Ta fada a lokacin da take kokarin sulalewa, ta sulale ta zauna akan kujera dan kafafuwanta ba zasu iya daukarta ba. Malaika ta taso da sauri cinkin murna zata rungume ta tana fadin “oyoyo ga kawata ta dawo.”

Jakarlap-top din Nasrin ta sulmiyo daga kafadarta zata fadi kasa. Malaika ta yi sauri ta kama mata. Nasrin ta daga mata hannu alamar kada ta matso kusa da ita.
Nasrin ta zauna ta dafe kai tana ta jujjuyawa, sabbabin ciwuka ne suka taso mata, zazzaɓi da ciwon kai suka hadu da yunwa, gajiya da bakin ciki suka cakuɗe mata.
Malaika na tsaye akanta tana kallo tana fada a ranta “Tunda na zo bazan tafi ba, ko zaki mutu wallahi, irin wannan daula da na shigo kuma in tafi. Ashe ma na zama sarauniyar wawaye ta shekara. Sai dai idan an raba ni da raina sannan za’a iya raba ni da gidan nan, zama a Abuja daram ba zan koma Kano.” ”
Nasrin ta ci gaba da mamakin ta in da Malaika ta diro, ta shigo gidansu alhali ita bata taɓa faɗa mata sunan unguwar da take a Abuja ba. Ta ma daina amsa wayarta ko ta kira ta, tun ranar da ta goge lambobinsu. Shin Malaika mutum ce ko aljana?Hakika na ɗauko ruwan dafa kaina. Lallai na jajiɓowa kaina masifa. Watakila ma na dauko ajalina da hannuna.

Yaya zan yi da wannan natacciyar matar, data nace min? Ina zan kai hakkin auren da ta kaso a dalilina? Ta yaya zan wanke kaina a wajen Shamaki ya yarda ba ni na ce ta fito ta biyo ni Abuja ba? Allah Ka ga zuciyata Ka fitar da ni daga cikin wannan kangin da na shiga. Ka shiga tsakanin na gari da mugu. Ya Allah kada Ka bari Malaika ta cutar da mu tunda da kyakykyawar niyya na karɓe ta.” Nasrin take tambayar zuciyarta kuma tana ta addu’a.
Suna cikin wannan hali sai ga Zainab ta fito daga kicin da sauri dauke da faranti ta jero abinci kala-kala wanda ta shirya shi na musamman domin bakuwarsu Malaika.
Ta sankare a tsaye da ta ga yanayin da Nasrin ta shiga, ta tambaya a gigice, “Nasrin! Lafiya ko jikin ne?”
Nasrin ta dago da jajayen idanuwanta, ta dubi Zainaba cikin sanyin jiki ta ce, “ta ina matar nan zo mana gida? Ta yaya ta san gidan nan ta zo, dan ni ban gayyace ta ba?”
ce, Zainab ta cika da mamaki ta “Malaikarki ce fa wacce kike ba ni labarinta kullum. Ko ba ki gane ta ba ne? Kin manta

wayarki a cikin daki, kina fita na ji ana ta kira na je na dauka, ta ce gata nan zata zo Abuja kun yi za’a bawa direwa waya a fadi kwatance ya kawo ta har gida,na rike waya a hannuna muna ta waya har ta karaso. Da ta isa tasha ta kira, na yiwa direba kwatance ya kawo ta.”,
Nasrin ta ja dogon tsaki ta harari Zainab ta juya ta harari Malaika sama da kasa, ta tashi ta shige daki a fusace gami da bugo kofa da karfi ta datse, yayin data yi arangama da wata dankareriyar tsohuwar akwatin Malaika a tsakiyar dakinta wato kaurowa ma ta yi gaba daya, babu ranar tafiya tunda ta hankaro kaya haka.
Nasrin ta ji wani ɗaci ya taso daga cikin makoshinta har zuwa bakinta, ta fara zaton ɗacin ajali ne ya tunkaro ta gadan-gadan. Sai ta dau salati ta sulale ta zauna a gefen gado ta dafe kai.
Malaika ta langwaɓe kai,wai nan ita abar tausayi, ta zare bakin gilashin da yake makare a fuskarta, sai hawaye ya sirnano daga idanuwanta, ta sulale ta zauna akan hannun kujera ta yi tagumi.

matukar yi Hankalin Zainab ya tashi,kunya ta kamata, ta tafi kan tebur din cin abinci ta ajiye farantin abinci. Ta taho da sauri ta dafa kafaɗar Malaika tana lallashi, ta kamo hannunta ta kaita kan tebur din cin abinci ta zaunar, tana bata baki akan ta daure ta ci abinci ko kaɗan ne kada ta sa abinda Nasrin ta yi mata a rai ya dame ta.
Sai Malaika ta kyallare ido ta hango dankareriyar kaza guda sukutun, bayan kayan ciki, kai da kafafuwan da aka cire ba’a cire komai a jikinta ba, a haka aka gasa ta a gashe tana kamshi. Malaika ta sake kanne daya idon ta kyallaro shinkafa, ta zama koriya ga karas, wake gwangwani, gami da hanta da koda duk an jere a ciki, gefe kuma salad haɗɗade ya ji kwai. Ga lemuna kala-kala da kofi a kusa gaba daya nata ne.
Nan da nan ta ji ta fara fita daga cikin hayyacin dan dadi, ta fara tunanin ko jirgin tunanin nan nata da ya saba daukar ta ya kaita duniyar karya ne ya danno.
Zainab ta juya baya za ta shiga ɗakinta, sai Malaika ta yi mata gwalo, ta saita masun

yatsunta ta kaiwa kazar nan hari ‘CAK’ ta kafa mata hannu. Ta raba cinyar nan da gangar jikin, ba tare da ɓata lokaci ba ta kai mata sara ta cake ta da hakora, ta yaga ta ci gaba da taunawa.
Kan kace kwabo dadi ya kaiwa kunnuwanta hari, nan da nansuka dauki zugin dadi ‘zuuuu’ dan tunda take bata taɓa cin abinci mai dadi irin wannan ba.
Ta na ci tana fada tana nanatawa a bayyane tamkar karatu, ta ce, “Nasrin! ko za ki mutu ba zan bar gidan nan ba, sai dai ayi duk wacce za’a yi wallahi. Karen hauka ne ya cije ni da zan koma Dorayi?”
Kash!
Anan zan dakata.
Mu hadu a ‘DA MA NI CE. . . .’ littafi kashi na
Mu ji yadda zata kaya: *Tsakani Malaika da Nasrin

DA MA NI CE..
*Tsakanin Dr.Jalo da Nasrin. *Tsakanin Fu’ad da Nasrin. *Tsakani Shamaki da Nasrin. *Tsakanin Shamaki da Malaika
Ta ku
JAMILA UMAR TANKO

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved