Chapter 1: CINNAKA ????????????
CINNAKA????????(BAI SAN NA GIDA BA)Story
&
Written by
F&F
(PERFECT PAIR)
DEDICATED TO ALL NURSING AND MIDWIFERY STUDENTS
بسم الله الرحمن الرحيم…….Dukkan yabo da godiya sun ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bamu ikon fara rubuta first novel ɗin mu yadda muka fara shi lpy Allah ka bamu ikon kammala shi lpy.
Allah ya sa mu rubuta abunda zae amfani mutane ka karemu daga rubutu ɓanar da kuskure Ameen thumma Ameen ????????????
Chapter 001
True life story
Zuciya mai juyawa rayuwa mai ban tsoro, al’ajabi,alhini da sarkakiya labari mai cike da tausayi hargitsi, cakwakiyya, makirci,nishadi shin soyayya ce ko son zuciya ??????
Wadannan kalaman masu ɗauke da ɗinbin hikima sune mabuɗin da suka buɗa mana ƙofar wnn tafiyar da ayanzunne mafarin ta..
Jikina wata kalar tsuma yake yayin da zuciya ???? ta ke kara kaimi wajen bugu na fara buɗe pages ɗin littafin dake hannuna da sauri ina karanta each heading da ke jikin kowacce chapter sai dai bazan iya kawo maku rahoto a wnn gaɓar ba saboda ni kaina ba fahimta nake ba bani kaɗai ba har ta bestyy na dake kusa da Ni muna bin juna da ido ???? hakan ce itama a ɓangaren ta saboda atare muka tsinci diary n da wasu manyan shahararrun mutane ɗaya daga cikinsu ta Yar a rashin sani wanda aka yi ma take da JAY’S RELATIVE (AB’S FAMILY) shahararrun mutane ne wadanda duniya ke damawa dasu a wnn lokacin ga kuɗi ga mulki da shahara da nasaba..
Kar in cika ku da surutu mu tafi kai tsaye mintina goma da suka shuɗe (10 mins ago) Ni Nur da bestyy na hooda (qawata, Aminiya ta abokiyar shawarata kuma’yar uwata) ɗalibai ne a jami’ar dake garin Abuja excursion ya kaimu ziyarar gidan marayu mallakin JAY’S RELATIVE (AB’S FAMILY) wanda Makarantar mu kanyi a irin wannan lokaci na karshen shekara ba makarantar mu kaɗai ba hatta sauran Makarantu dake fadin kasar mu Najeriya saboda shi mamallakin gidan marayun kan kawo ziyara da kanshi. Wnn excursion ya kasance na musamman ga duk wanda ya tsinci kansa a wnn wurin harda mu ɗin nan abun ba’a cewa komai sai san Barka ???? abunda ya fi jan hankalinmu nida hooda shine familyn shi sun samu damar halartar taron ahali ne masu tsananin kama da junansu kamala, tattali kulawa da soyayya kamar zasu haɗe junansu duk da cewa idon duniya akansu yake bai sa sunji shayinsu ba
Kai!! Ranar na shaida garin daɗi na nesa ???? in Allah ya baka ka huta watau duniya akwai kyawawa snn akwai kudi (suna dae inda suke ????) shigowar su kadae abin kallo ce tsayayyun maza guda hudu lafiyayyu gwaraxa Duk da shekarun girma ya kama su amma jin dadin rayuwa da hutu ya boye girman nasu sae wasu samari dake cikin tawagar tasu ko wannensu na makale da matarsa da ‘ya’yansu masu kama da su sae escort dake take masu baya gwanin sha’awa ko makiyansu suka gani sae sun yaba Sai dai masu mummunar manufa a cikin zuciyar su tafasa take tana xaɓarɓaka kmr zata kama da wuta sun sani sun shaida BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE NAN GANI NAN BARI SADAKIN AGALAWA wannan shine karo na biyu da suka bayyanar da kansu a zahiri kamar haka..
An gudanar da taron ckn tsari da wayewa don ba wuri ne daza a nuna locality ba ba’a bukatar illiterate Hmmm… wllh kudi ke mgn a duniyar nan in kana dasu zaka baza capacity yadda ranka ke so bestyy na ke maganar yayin da Ni kuma nake gyaɗa mata kai alamar gamsuwa na ɗaura da cewa amma kinsan mi bestyy da ace zamu bibbiyi rayuwar su da nasan zamu sha mamaki dan nasan they face alots of challenges kafin su kai matakin nan ” ke dae bari bestyy ae zakiga da wuya mutum yaci nasara a rayuwarsa bae sha wahala ba amma zan so jin labarin su” cewar hooda ban samu damar bata amsa bah naji MC na shelar tafiyar JAY’S FAMILY batare da mun an kara ba sun gama gabatarwa, photo da duk abin da ya dace
Tsananin cunkoso da hall din nan yayi kamar zai tsage gida 2 tsabagen cika saboda haka muka ja gefe Ni da bestyy duk da yawaitar Ac dake wurin amma hakan bai tasiri ba saboda tsananin zafin da ke wurin ,bamu fi 5mins da tsayuwa bah na kalli bestyy na sakamakon kalmar danaji ta furta”wow” bata wani bi ta kaina ba ta taka stairs ta nufi makeken table da ke gaban kujerun da gwaraxan na ku suka zauna abinda ke sama ta dauko ta dawo wurin da nake tsaye tana nuna min Ni kaina haɗuwar littafin ta tafi dani da kyar muka gane yadda ake buɗeshi bayan mun gama santin shi (cox it’s unique) TRUE LIFE STORY Shine abunda ke rubuce a First page ɗin littafin abunda ya qara jan hankalinmu ga littafin shine family status na JAY’S RELATIVE (AB’S FAMILY) wnn shine dalilin da yasa muka bar hall ɗin a sace da niyyar mayar masu da littafin sai dai kash ???? mun makaro zuwanmu tafiyar su…..
Shishigi zan kira shi ko sa ido da karfin hali yasa na buɗe na fara kawo maku chapter 1 shine zancen mu na farko wannan shi ya sa mu shiga halin da kuka tarar damu. Wata uwar harara bestyy ta watsu man lkcin da na ke kaiwa zaune akan jerin kujerun da ke jere a qayataccen wurin shan iska an yi shi musamman don hutawa dariya nayi nace bazan baki littafin nan ba sai na karanta kaf abinda ke cikinsa snn zamu mayar dashi ae wnn faɗuwa ce tazo dai dai da zama yo Omo nasha in mayar da littafin nan ban karanta abinda ke cikinsa ba ,hmmm kawae bestyy tace. Nasan takaici ne ya hana ta magana cikin nusarwa tace”wllhy nur suke ki ayi tsiren mu a tsakiyar kasar nan kin san match ɗin da kike son taro mana gashi bamu da ‘yan wasan bugata balle fili”baki na taɓe na ce daga baya knn banason rashin M nasan kina so kina kaiwa kasuwa ne bata ce man komai ba nasan bazata yi magana ba shysa na tashi ina cewa zo mutafi kar su tafi su barmu sae na koma hostel zan karanta shi harara ta sake antayo min a karo na biyu tace”wllhy baki isa ba tunda ke kika tsince shi ba anan zamu fara karantashi dariya rainin hankali nayi ina kaiwa zaune kusa da ita, ta taɓe baki tace “nasan dole laifin ki sai ya shafe Ni to da ace nayi kuma banyi ba gwara kawae nayi banason surutu oya start………..
Ku biyo mu sannu a hankali zamu warware maku lauje cikin naɗi da sarkakiya da ke cikin wnn duniyar tasu da fahimtar komai a bayyane sai ku kasance damu F&F (PERFECT PAIR) don jin yadda salon da tsari, harmutsi da tsilla-tsilla zae kaya kudi kuyi mana share,vote and comment snn ku cigaba da bibiyarmu akai akai don sanin manufar labarin mu da kuma salon takun mu tare da kamo maku bakin zaren muje zuwa……….,
????????????????



