⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 1: Chapter 1

BABBAN GORO 1…
(Sai Magogin Karfe)

Dreams are conceibed, but not all dreams are born alibe. Some are aborted. Others are stillborn.
-Zaynab Alkali

Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
Copy write: Sumayyah Abdulkadir
hakkin mallaka: Sumayyah Abdulkadir
shekarar rubutu: 2014

SADAUKARWA
A yau sadaukarwar ta ‘ya ta ce, surukata, uwata, babbar Yaya makwafin Uwa ga daukacinmu iyalin Dr. Shehu Kabara. Malama Bintu Dr. Shehu Kabara (YAYA BINTU) Allah Ya kara nisan kwana Yaya Bintu!!!

GODIYA
Godiya ta musamman ga kawata kuma abokiyar karatuna Rukayyah Dr. Yusuf Ali, Allah Ya baku zaman lafiya mai dorewa da angonki Muhammad, Ya yi miki tukuici da Aljannar Firdausi ameen.

GAISUWAR GIRMAMAWA
Ga Uwarmu Uwar kowa a Kabara, Hajiya Safiya Ibrahim S.N.K (Hajiyan Kaura) Hajiyarmu Allah Ya kara girma!!!

SAKON GAISUWA
Sakon gaisuwata da ta’aziyya ga Aunty Zulaiha Zubair (Zulai) abisa rashin maigidanta data yi Tafidan Kano (Hakimin Kura), ina mika ta’aziyyata gareki da iyalanki bakidaya. Allah Ya ji kan Tafidah.

FATAN ALKHAIRI
Fatan alkhairi ga duk makaranta littattafan TAKORI, wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah Ya hadamu cikin ALHERIn Sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.

TAYA MURNA
A madadin Al-Fatih da iyalinsa, Sumayyah da iyalanta, Amiru da Abubakar bakidaya muna taya murnar auren kanwarmu MAIMUNA MUHAMMAD GAMBO (UMMI) da angonta IBRAHIM AHMAD MUHAMMAD, fatan alherin auren ga iyalan MAL. GAMBO ADO (former Director-General, Youth, Kano, Allah Ya bada zaman lafiya da zuri’a dayyiba.

SAYYiDAH is 15 years, (AISHA ABDULKADIR) daliba a fggc minjibir wishing u long life and prosperity
(yayarki Sumayyah)

Fatan alkhairi ga
manyan gobe
Marwah Dr. Shehu Kabara Ukbah
Ahmad (Khazrajy) Dr. Shehu Kabara
Muhammad, Saudatu da Zaliha Maghili Shehu Kabara
Aarif Ghazali Shehu Kabara
Nasira Abdulkadir
Fateema Abdulkadir
Mustapha (Baraki) Abdulkadir

(‘ya’ya na da kannena Allah Ya baku ilmi mai amfani Ameen).

Daga marubuciyar….
Rubutu wata hanya ce ta isar da sako daga mai rubutawa zuwa ga mai karantawa. A hanyoyin sadarwa babu hanya mai tsohon tushe irin rubutu, a dalilin rubutu ne muke samun ilmummukan addini dana zamani da muke amfani dasu ayanzu, babu hanya mafi saukin isar da sako da ajiyeshi a fahimta sosai kamar rubutu.
Mutum yana ganin majiginsa ne kamar a idonsa, wato kamar agabansa ake yi fiye da talbijin, tunda zuciya ke bada hotonsa ba ido ba. Sako ta talbijin yana zama ne na dan lokaci ko kuma a lokacinda ake bukatar isar dashi kawai, sako ta waya ba madawwami bane tunda sake waya muke kullum kamar yadda muke sake tufafi, sako ta radio ba kowa yake samu ba sai wanda ke tareda radiyon, wani bai ji ma wani bai da radiyon. Kai jama’a da yawa yanzu birni da kauye basu da lokacin sauraron radiyo. Sako na a tara mutane ayi musu ido-da ido (lacca) abune na mutane kalilan, kuma ba kowa ne zai zo yasaurareka ba, sako ta na’ura mai kwakwalwa ma rashin ingancinsa yawa ne dashi…… Don haka sakon alkalami shine babbar hanya mafi sauki ta isar da sako daga zuciya da kwakwalwar marubuci ga duniya bakidayanta.
Yana kurdawa lungu-lungu sako-sako ya tadda mutane iri daban-daban masu amfani da harshe daya, har inda suke, koda birnin Sin ne batareda wahala ba. Za kuma a iya kiranshi sako mafi lasting wato mafi karko from generation to generation, don hakane na zabeshi a matsayin tawa hanyar ta isar da sako akan dan hangena a fanni daban-daban na rayuwa ba soyayya kadai ba.
Asali ma bana so ta zamo itace jigon rubutuna, sai don kasancewar ta wani bangare na halitta da rayuwar dan adam. Ita din halittace. Wato dai itama halittar Allah ce (physical and biological), da ya halicceta ya sanyata tsakanin Adamu da Hawwa’u, su kuma suka haife mu.
ABRAHAM MASLOW (1970), an American psychologist, wanda ya samar da theory of self-actualization, tareda Hierarchy of Need Theory of Motibation, ya sanyata cikin rukunin bukatun dan adam na halitta kamar cin abinci, shan ruwa da sauransu.
Nakan zauna ne in zabi matsala guda daya dake yawo a cikin al’umma inyi dan rubutu akai, in sanya nishadi, in fadi illa, sannan in kawo magani ta hanyar shawarwari wadanda ba lallai su zama daidai da ra’ayinki/ka ba. Fahimta daban-dabance kuma ta fuska-fuskace. Don haka ban taba rubutu don in dadada ko in bakantawa wani ba. Ban taba daukar rayuwar kowa ko rubutun kowa ba. Don haka har kullum suka da gyara ababen maraba ne har a shimfida musu tabarma, a kawo musu ruwa mai sanyi daga Randa su sha. In ma aljihun Takori da albarka a hado musu da zobarodo ko kunun Aya. Makasudin sanya sunan Safah da Marwah ayau a matsayin jaruman BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE ba rayuwarsu bace, ba kuma rayuwace dana ke musu fata ba. Nayi ne kawai domin tunawa da marigayiyar da bazan taba mantawa da ita ba SAFAH in kuma tunawa masoyana da ita suyi mata addu’a, su kara yi min nima Allah Ya kara min danganar rashinta, Ya bani lafiyar data yi min karanci.Ya bani wata mai albarka. Ya raya Marwah da Khazrajy cikin Islama da doguwar rayuwa mai amfani. Itakuma Ya sanyata cikin daliban Annabin Allah Ibrahimu Alaihissalat wassalam. Ya sa ta cecemu da duk makaranta littafin Takori.
-Fatan ALHERI.
TAKORI
Maris/2014

BUDEWA
Shekara ta 1980
Gida ne na gani a bada labari cikin unguwar Gwamna Road dake cikin garin Kaduna, kafatanin harabar gidan an kakkafa ‘canopies’ (rumfuna) da kujeru na alfarma. Gidan cike yake da gawurtattu kuma tsofaffin ‘yan siyasar Najeriya wadanda suka dade ana damawa dasu a siyasar kasar, na jiya dana yau, har ma da na shekaranjiya duk ba’a barsu a baya ba, musamman yankin Arewa.
Daga cikin gida Najeriya da wajenta ma abokan huldar sa na siyasa duka sun halarta, manyan jifa-jifai (Jeep) kadai ke ta neman wajen adana motocin su, to haka kekuna da Baburan ‘yan achaba, keke-napeps, hade da kananan motoci na talakawa ma duk ba’a bar su a baya ba. Sun taru ne musamman domin taya Alh. Aliko Dan Kasa murnar hayewa kujerar Gwamnatin garin Kaduna, a sanarwar da aka yi yanzun nan a kafafen yada labarai, ciki har da gidan rediyon BBC da gidan talabijin na CNN da dukkan jaridu da mujallun da suka fita a safiyar yau, karkashin jami’iyyar NPC (Northern People Congress) jam’iyya mai farin jini a wajen talakawa.
Kowa ka gani cikin farin ciki da nishadi yake, ana ta shige da fice domin fitar da kabakin abinci iri-iri, tun daga namu na Hausawa, Igbo, Yoruba, Arabian har na Turai babu irin wadanda ba a fito dasu ba.
Sai da kowa ya cika tumbinsa aka soma gabatar da makasudin taron cikin tsari na ‘yan siyasar da suka wadatu da ilmin zamani suka kuma san ciwon kansu; (ba mahandama ba), suke kuma aiki da iliminsu wajen gudanar da siyasarsu.

Cikin wannan halin ne mai girma Gwamna ya fito cikin rakiyar jama’a masu dimbin yawa, ya fara da gabatar da jawabin godiya ga mahalarta taron, sannan aka ci gaba da gudanar da taron kamar yadda aka tsara.
Mai girma Gwamna Alh. Aliko Dan Kasa, ya yi maganganu masu zafi a kan yadda gwamnatinsa za ta bambanta da sauran gwamnatocin da suka shude. Ya yi alkawarurruka masu ma’ana da yake fatan Allah Ya bashi ikon saukewa.
Ba shi ya samu kansa ba sai karfe goma na dare, ya shigo gida a gajiye matuka, mai dakinsa Hajiya Zainab ta tare shi cikin murmushi mai nuna tsantsar farin cikin da itama take ciki a yau.
Suka tari juna da runguma cikin nuna godiyarsu ga Allah, kamin ta taimaka mishi ya cire babbar rigarsa, safa da takalmi, sannan ta gabatar masa da abin sha mai sanyi, kafin su zauna a tebir tayi ‘serbing’ din shi wainar masa, sinasir da miyar agushi data ji tsokar naman tolo-tolo, wannan shine nau’in abincin da Alh. Aliko ya fi so a rayuwarsa.
Saidai bai kai ga yin loma hudu ba, wayarshi dake gefe ta soma kurarin neman agaji. Yayi wa Haj. Zainab alamar ta amsa, sai ta amsa a ‘hands-free’ cikin yin sallama.
“Kwamishinan ‘yan sanda ne, Ibrahim Rigasa. Muna son yin magana da mai wannan wayar, saboda shine ‘last call’ (kira na karshe) da muka gani a wayar Alh. Zubair Dan Kasa, wadanda suka taso daga Abuja shi da iyalinsa a safiyar yau”.
Kasancewar a handsfree (murya waje) suke maganar, don haka yayi azamar amsawa da cewa,
“Da mai wayar kuke magana”.
Kwamishina ya ce,
“To ku gaggauta kuzo nan asibitin ABU sun samu hadarin mota da shi da matarsa da ‘ya’yansu biyu mace da namiji”.
Alh. Aliko ya tsame hannu daga abinci ya soma salati yana fadin “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!”
Itama Haj. Zainab salatin take yi. Suka mike a tare suka fito harabar gidan. Direba da masu tsaron lafiyarsa suka fito da mota suka shiga, a daren suka dauki hanyar Zaria.
Da suka iso basu sha wahalar samun kwamishinan ‘yan sanda ba. Nan da nan ya yi musu jagora zuwa dakin da suke. Ya dubi tilon dan uwansa Ministan FCT Zubairu Dan Kasa, ko’ina a jikinsa jini ne, bandeji ne plasta ce, yana numfashi da taimakon abin janyo numfashi.
Daga shi har matarsa Haj. Kaltume cikin yanayi daya suke. A gefe yaransu Al-mustapha da ake kira (Imam) da kanwarshi Shahidah ne suke ta kuka.
Al-mustapha da plasta a kansa da karaya a hannun dama, ita kuwa Shahidah abin mamaki ko kwarzane ba ta yi ba, amma hakan bai hana ta kuka ba, musamman ganin iyayenta duk a kwance cikin wani hali duk da kankantar shekarun ta.
Suna shiga Alh. Aliko ya karasa ga dan’uwansa hawaye na zuba a idonsa, yayin da Hajiya Zainab ta nufi su Al-mustapha tana rarrashin su. Ta kama Shahidah ta rungume tare da shafa kan Imam tana rarrashinsa.
Ko minti goma basu yi da shigowa ba Haj. Kaltume ta cika. Washegari da asuba shima Alh. Zubair ya ce ga garinku nan.

Tashin hankalin da mai girma Gwamna Aliko Dan Kasa ya samu kansa a ciki, ya mantar da shi farin cikin da yake ciki bakidaya.
Dan’uwansa tilo da ya rage masa duk fadin duniya, yau ya tafi ya barshi. Abokin shawararsa kwaya daya rak, a duniya, su fadi tare, su tashi tare, yau babu shi. Kai shi da za’a kwace mulkin a dawo masa da Yayan sa Zubairu, da yafi farin ciki. Kuka yake wiwi da shi da mai dakinsa.
Gari na wayewa aka shiga watsa mutuwar FCT Minister Zubairu Dan-Kasa a kafafen yada labarai. Da motar asibiti aka dauko gawarwakin zuwa ainahin gidan mahaifinsu, inda mahaifiyarsu take zaune a Unguwar Rimi.
Jama’a suka shiga tittudowa domin halartar jana’izar mazan jiya, wadanda tarihin Najeriya bazai taba mantawa dasu ba, tun bayan rushewar mulkin soja (return to cibil rule), wadanda suka taimakawa Najeriya ta kawo matsayin da take kai a yau: (from agrarian to industrial) irin su Minista Zubair Dan Kasa. Nan mai girma Gwamna ya zauna karbar gaisuwa, yayin da Haj. Zainab ke tare da su Imam a asibiti.

Haj. Maama, tsohuwa ba tukuf ba, wadda ta kasance mahaifiya ga Alh. Aliko da Alh. Zubairu, wadda samun kulawar ‘ya’ya nagari ya boye zahirin shekarun ta, ta sha kuka har ta gode Allah. Sai dai da yake mace ce ma’abociyar imani da rikon addini, cikin kwanaki uku da rasuwar babban dan nata da mai dakinsa ta dawo cikin nutsuwarta. Tana amsa gaisuwar kowa. Saidai bata umh bata umh-umh, sai jan carbin dake hannun ta, sai kuma in an yi mata ta’aziyyah ta amsa.
Da ganin mai girma Gwamna Alh. Aliko Dan-Kasa, ka san mutuwar ta buge shi yadda ba a zato. Ya rame ya yi duhu, ya manta da wata baiwa da Allah yai mishi na ba shi shugabancin al’ummar jihar su ko rantsar dasu ba a yi ba.
A ranar da aka yi sadakar bakwai ya hattama komai na marigayan ya adana a babban bankin Iloyds TSB na kasar Ingila. Sannan suka taho Kaduna, inda aka rantsar da shi a washegari.
Suka tattara shi da mai dakinsa da ‘ya’yansu Al-mustapha da Shahida, suka koma Gobt. House Kaduna State. Mulki ya soma kankama.

Awashegarin komawarsu gidan gwamnati, ya shiryawa gyatumar shi tafiya da Imam wani asibitin kashi a kasar India, garin Punjabi. Bayan ya yi magana da hukumar asibitin ta yanar gizo (Internet). Suka tashi ranar asabar, inda Imam (Al-mustapha), ya soma karbar treatment daga kwararrun likitocin kashi.
Cikin sati biyu ya warke ragas suka dawo gida Najeriya, kowa na murna da samun lafiyar Imam, kasancewarsa yaro mai shiga rai, babu wanda zai kalli Al-mustapha bai ce yana son sa ba.
Bayan kyau tsurar sa, da Allah Ya halicce shi dashi. Wani irin hazikin yaro ne mai kwarjini da kuzari hade da nutsuwa ta ban-mamaki. Haj. Zainab ta dauki kaunar duniya ta dora a kan marayun nan da maigidanta ya damka mata amanarsu. Bata taba haihuwa ba, a tsayin shekarunsu ashirin da aure. In har suna da matsala a rayuwarsu, to wannan ce.
Anyi jelen asibitin, anyi na gargajiyar shiru har yau. Don haka suka dauki komai suka mikawa Allah. Wanda ba’a sa Shi, kuma ba’a hanaShi. Shine mai bayarwa da hanawa ga wanda Ya so. Don likitoci sun tabbatar musu kowannensu lafiyarshi lau, lokaci ne Allah bai kawo ba.
Akwai aminci na hakika tsakanin Haj. Zainab da marigayiya Haj. Kaltume. Basu san wata kalma wai ita ‘faccalanci’ ba da matan hausawa ke yi, musamman idan mijin wannan ya fi na waccan, duk da ratar arziki mai yawa dake tsakanin Zubairu da Aliko a lokacin da suka aure su.
Don haka su Imam tuni sun saba da Haj. Zainab da Kawunsu Alh. Aliko, don a kan kawo su hutu wajensu lokacin da iyayensu na raye.
Don haka ne da Imam da Shahida suka bude ido suka gansu a gaban Uncle dinsu da Haj. Zainab, sai basu damu sosai ba. Sai dai jefi-jefi Imam da yafi wayo kan tambayi Haj. Zainab Mummy da Daddy.
Ta kan ce sun je Kano sai hutu ya kare za su zo su dauke su. Ita Shahida da yake karama ce ko ambaton iyayen ba ta yi, wasanta kawai take da ‘toys’ da ‘teddies’ (‘yar tsana) da aka cika mata gadonta dasu ba abinda ya dame ta.
Alh. Aliko ya dauko gyatumarshi Haj. Mama daga Unguwar Rimi (gidanta da Alh. Zubair ya gina mata) ya dawo da ita Govt. House, sassa guda aka ware mata, babu abinda babu na jin dadin rayuwar duniya, babun ce kurum babu. Kun san dai tsari irin na gidan Gwamnati.

Mulkinshi mulki ne mai cike da takawa (wato tsoron Allah), tsantseni (da dukiyar al’ummah) da tausayin talakawa.
A shekara daya kacal da ya yi yana mulkin jihar Kaduna da local governments dinta (kananan hukumomi) guda ashirin da uku (23), ya kawo sauye-sauye na ci gaba da dama, musamman ta fuskar tsaro da kariyar lafiyar al’umma.
Ya tsayawa malaman makaranta ta hanyar kara inganta albashin su, da basu rancen motoci a dinga diba da kadan da kadan daga albashinsu.
Haka ya tsayawa iyayenmu ‘yan fansho (pension) tare da taimako ta hanyar bada kayan aiki ga makarantun firamare da sakandire na jihar Kaduna.
Bai tsaya a nan ba, gwamnatinsa ta tsaya-tsayin daka kan wutar lantarki da ruwan sha, wadanda sune manyan matsalolin da jihar ke fuskanta. Haka ya taka muhimmiyar rawa a kan harkar ilmin manya (adult education) a jihar bakidayanta, da karo karatun malamai na jami’a dana sakandire a kasashen ketare ta hanyar daukar nauyin karatun da ‘accommodation’, da baiwa mata sana’o’I da tirenin akan sana’ar, haka matasan da basu samu damar yin ilmin zamani ba.
Kan ka ce meye wannan? Ya zamo zakaran gwajin dafi cikin gwamnonin Najeriya tsararrakinsa, sannan abin koyi, kuma abin so a zukatan al’ummar jihar. Sunanshi ya yi tambari a jihar baki dayanta, babu abinda ke fita daga bakunan al’ummar jihar, sai fatan alheri ga gwamnatinsa.
Wadanda suka san matsalarshi ta cikin gida kuwa (wato rashin haihuwa) sai addu’a suke masa Allah Ya ba shi magajin kyawawan halayensa.
A wurin shi kuwa, bai tsanantawa kansa kan rashin haihuwa ba. ‘Ya’yan dan uwansa sun isheshi, har gaba da abada in akwai, ‘ya’ya ne a gareshi da yake so fiye da ‘ya’yan da zasu kasance shi ya haifesu. Wato Imam da Shahidah. Fatansa Allah Ya raya masa su cikin tarbiyyar Islam ameen.

***

Haj. Zainab ce zaune a katafaren falonta tana kallon tashar MBC da ‘remote’ a hannunta, Al’mustapha na ‘game’ cikin wata na’ura ta yara. Shahida ta lallaba ta zagaya ta kashe, ya dago a fusace ya yi kanta da duka, da kyar Hajiya ta kwace ta.
Ta ce, “Haba Imam, irin wannan duka kamar ka samu sa’an ka? Baka ganin Shahida yarinya ce ne?”
Ya zumbura baki,
“To wa ya ce ta kashe min ‘game’ dina?”
Ta ce, “Ka yi hakuri ba za ta sake ba. A bar ‘game’ din haka, aje ayi alwala ayi sallah, sannan ayi shirin fita lesson (darasi) kafin teacher (malam) ya zo”.
Duk suka amsa, suka fita. Ta bisu da kallo, tana jin kauna da tausayin yaran har cikin zuciyarta.
Ta tashi ta nufi sassan surukarta Hajiya Maama, ta tarar da ita tana sallar la’asar. Ta samu kujera ta zauna har Hajiyar ta idar ta yi addu’a ta shafa.
Ta juyo da murmushi ta ce, “Ya ya Maman Imam? Ina ‘yan rigimar naki sun dawo ne?’
Ta ce, “Sun dawo tun dazu, har anyi wanka an ci abinci an tafi daukar lesson, yanzu aka gama rigimar na sha rabon fada, kin san Imam din nawa ba dai karfi ba. Ai Shahida tana cin duka, wannan bai hanata gobe ma ta sake tsokanarsa kamar ba jikinta ake tika ba”.
Hajiya Mama ta yi dariya ta ce, “A kullum na dubi yaran nan suna tuna min da Kaltume. Da wata hira da muka taba yi da ita. Ta ce Allah Ka bawa Haj. Zainab ‘ya in aurawa Imam”.
Hajiya Zainab ta yi murmushi cikin jin kunya kuma mai ciwo a zuci. Suka ci gaba da hira da surukuwarta, duk da shimfidaddiyar damuwar da Hajiyan ta gani a fuskarta a dalilin zancen haihuwa data yi.
Wayar mai girma Gwamna ce ta tada ita daga hirar da suke yi mai ban tausayi a kan marigayi Minista Zubair da mai dakinsa Hajiya Kaltume. Cikin su babu wadda bata zubar da hawaye ba.

Imam na aji uku na sakandire, Shahida na aji shida na firamare. Tenure din Alh. Aliko ta cika, ya sauka daga gwamnatin jihar Kaduna.
Ba yadda jama’a basu yi da shi ba a kan ya sake tsayawa takara amma ya ki amincewa, ya ce tunda ya tsira da mutuncinshi da kaunar shi a zukatan al’umma, to Alhamdulillahi. Suka baro Gobt. House suka dawo katafaren gidan da ya gina a Jabi Road, dake cikin birnin Kaduna.

ASALINSU
Asalin mahaifin su Alh. Aliko mutumin Kaduna ne, a wani gari, CHIKUN. Cirani ne ya shigo da shi cikin garin Kaduna tare da mai dakinsa Salamatu (Hajiya Maama). Itama ‘yar Chikun ce kamar mijinta Malam Salihu.
Haihuwar Salamatu bakwai duk suna mutuwa (wabi), sai a kan Zubair na takwas Allah Ya bar mata. Ba dadewa ta sake samun wani cikin, ta haifi Alh. Aliko, wanda sunan shi na ainahi, Aliyu. Baban shi ke kiran shi Aliko, kuma sunan ya bishi har girma.
Zubairu da Aliko sun rayu tare da iyayensu har girmansu, kafin Allah Ya dau ran mahaifinsu Malam Salihu. A lokacin Zubairu yana da shekaru ashirin, yayin da Aliko ke da sha bakwai.
Duk da iyayensu basu yi karatun boko ba, Mal. Salihu bai bar ‘ya’yanshi haka ba, sai da ya ga kowannensu a jami’a sannan ya samu kwanciyar hankalinsa. Ya tsaya tsayin daka a kan karatun su, wanda shine tsani na duk wani mataki da suka taka yau a rayuwa.
Karatu mai suna karatu, sun yi shi har sun kure biro, idan har ana kurewa, dukkansu akan siyasa. Amincin dake tsakaninsu na shakikan juna, ba kasafai ake samun irin shi a wannan zamanin ba. Daya baya zartar da komai kan abinda ya shafeshi ko iyalinsa ba tareda yayi shawara da daya ba.
Matsayi iri-iri a siyasa Aliko ya rike, tun daga kan Kakaki (speaker house of representatibe), dan majalisa, kwamishina, sanata, shugaban karamar hukumar Chikun da wasu da dama, har kawo na yau, wato matsayin daya taka na Gwamnan jihar Kaduna.
To haka Zubair ya rike mukamai da dama kafin Allah Ya dau ransa. Har kawo na karshen, wato Ministan FCT. Inda ya gamu da ajalinsa a kan hanyarshi ta zuwa taya dan’uwanshi murnar hayewa kujerar Gwamna.
Mutuwar Zubair ta taba Aliko ba kadan ba, yadda har ta shafi lafiyarshi. Sai dai kullum ya dubi Imam da Shahida dake gabanshi, yana godewa Allah da bai barshi da kewa ba.
Kullum ya daga ido ya dubi Imam (Almustapha) fuskar dan’uwanshi Zubair yake gani a fuskarsa.
Don haka son da yake yiwa yaron ba kadan bane, ta yadda har yake mantawa da cewa ba shi ya haife shi ba.

Imam Zubair Dan Kasa, yaro ne mai hazaka tun yana kankaninsa, yana da wasu baiwarwaki da dama da ba duk ‘ya’ya Allah Ya mallakawa ba.
Yaro ne da ya lakanci wani darasi daga cikin darusan da ake koya mishi a makaranta wai shi introductory technology. Ga kyau ga kyan hali, ga nutsuwa da rashin son wasa, ta ko’ina Imam Almustapha, abin alfahari ne ga iyayenshi da ‘yan’uwan shi bakidaya.
Rashin iyayenshi da ya yi a lokacin kuruciya bai sa shi ya yi maraici ba ko kankani. Baffanshi da matarshi a tsaye suke a kansu, farin cikinsu da walwalarsu.
Sannan Hajiya Maama ba ta da abin so irin mijinta Imam, wanda take sawa a gaba tana koyar da shi dabarun zaman duniya, da yadda za a yi a ci ribarta.
A irin wadannan lokutan, Imam kan dauki dukkan hankalinsa ne kacokan ya likawa Hajiya Maama, yana kwankwadar ilmin manya na yadda za’a gina rayuwa a duk halin da aka samu kai, yana aunawa a ma’auni na hankali da tunaninsa, yana hadawa yana tarawa yana rarrabewa, sannan idan ta gama ya jefo mata tambaya wadda ta fi karfin shekarunsa.
Akwai ranar da ya tambaye ta “Me yasa Daddy ya ki ci gaba da takara duk da kaunar da jama’ar Kaduna ke mishi?”
Ta yi murmushi ta ce da shi,
“Don ya tsira da mutuncinsa ne, ka san an ce tsira da mutunci ya fi tsira da kudi”. (Wannan Magana ta zauna cikin ran Imam har girman sa)
Akwai kuma ranar da ya tambaye ta, “Ita Mami (Hajiya Zainab) mai yasa ba ta haihuwa?”
Ta ce, “Allah ne bai bata ba Imam, amma ka dinga yi mata addu’a”.
Tun daga wannan ranar Imam bai kara tashi daga inda ya yi sallar farilla ba, ba tare da ya rokawa Mami dinsa haihuwa ba.
***
****

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *