⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 5: Chapter 5

Kwananshi hudu a Kwatano ya yi ma Safah waya ya sanar da ita yana bisa hanya. Ashe Marwa ba ta gama shan mamaki ba, don yau Safah da kanta ta shiga kicin ta hada ‘dinner’ mai rai da motsi da taimakon Biola.
Sannan ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket na swiss lace ruwan zuma. Tana fesa turare kararrawar shigowa ta yi kara, sannan wayarta ta hau ruri tabbacin Zahraddeen ya iso.
A karo na farko gigicewa tayi. Kasancewar a yau ne zata taba fuskantar wani da namiji a rayuwar ta, da idanun soyayyah. Da kanta ta bude mishi kofa suka bi juna da kallo, wani irin sassanyan kallo mai kwantar da zuciya. Kafin kowannensu ya saki sassanyan murmushi mai dauke da boyayyar ajiyar zuciya.
Ta kauce ta ba shi hanya ya shigo cikin caftan na wagambari mai hasken sararin samaniya, gilashin idonshi na yau fari ne kal dan sirit, wanda ya fiddo da zahirin cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda rayuwa ke garawa tare da shi, ga bokon, ga opportunity, sannan ga mahadin su wato kyau.

Safah ta yi nisa sosai a kallon sa, ya yi murmushi ya soma karkada mata makullan mota a idanunta.
Ta ji kunya sosai, ta wuce ciki suka zauna cikin kananan leathers da suka yiwa karamin falon nasu kawanya.
Ta ce, “Ya hanya? Ya zirga-zirga?”
Ya ce, “Komai lafiya, ga motarku ta iso”. Ya mika mata mukullin karamar ‘Optima’, daidai lokacin Marwah ta fito daga daki tana rike da takardu zata shiga cikin makaranta.
Ta yi dan jim, tana kallon su, sannan ta saki fuska suka gaisa da Zahraddeen. Ta ce,
“Motar ta iso ne?”
Ya ce, “Tana waje, muje ku gani, in ba ta yi ba sai a sake”.
Dukkansu suka fito. Marwah na cewa “ballema nasan zata yi, Yaya Deen, bazaka zabo abu mara kyau ba”. Kwarai motar ta birge su, ta yi musu daidai. Kalarta fara sol!
Marwa ta bude ta zauna, ta tattaba gaban motar, ta kunna, ta bata wuta, ta ce, “Kai! Yaya na ka iya zabe”.
Ya ce, “Koh?”
Ta ce, “Wallahi”.
Ya ce, “To alhamdulillahi”.

Suka koma cikin gidan suna hira dukkansu. Marwah ba ta dade ba ta kwashi takardunta tayi daki ta bar musu falon, ko daukar laccar ta kasa zuwa, saboda yadda suka kasa boye soyayyar dake zuciyoyinsu a gabanta.
Ranta a jagule da mamaki, tausayin Imam da al’ajabi. Me Safah za ta yi da Zahraddeen yaron Babanta? Duk yadda Ya Imam ya kallafa rai a kanta tana nufin ba za ta aure shi ba ko me?
Ta kira Mami tana haki, Mami ta ce, “Ke lafiya kike numfarfashi?”
Ta ce, “Mami….”

Sai kuka ya kwace mata……..tausayin Imam take har ba ta san me za ta ce da Mamin ba.
Ta ce, “Ki yi min magana mana, ya za ki fasa min kuka alhalin ban san abin da ya faru daku ba. Wani abu ne ya faru? Ina Safah?”
Ta ja shessheka amma ta kasa magana, ba ta son ta hada Safah da iyayensu, don ta san muddin suka ji sai sunyi wani abu a kai. Ko dai su dakatar da karatun ko su tada maganar aure yanzu. Kuma ita Safah za ta blaming kan tana yi mata sa-ido, wanda a kullum Mami ke nuna musu rashin amfanin sa.
Bugu da kari tayiwa kanta alkawarin daina shiga zancen Safah da Ya Imam, tunda hakan rashin jituwa yake haifarwa a tsakaninsu. Don haka ta yi saurin alkawartawa ranta cewa babu ruwanta. Ta ce da Mami, “Bani da lafiya ne”
Ta ce, “Me ya same ki?”
Ta yi diri-diri na rashin gaskiya ta ce, “Ciwon marata ne har yau bai daina ba”.
Ta ce, “To ki nemi Zahraddeen ku je asibiti, Allah Ya sauwake, kuma ki samu Zam-Zam ki tofa ayatul-kursiyyu kafa bakwai ki sha, insha Allahu za ki samu sauki”.
Ta ce, “To Mami”.

Ta ce, “Daina kukan haka nan, wannan ciwon duk mata suna yinsa, sai dai na wata ya fi na wata. Nima da girmana har yau ban daina shi ba. Kira min Safah mu gaisa”.
Ta ce, “Tana falo ta yi barci ne”.
Ta ce, “To ki gaida ta, Hajiya Maama na gaishe ku, ga Shahidah ma tazo tana kewarku”. Ta yi dariya ta ce “Allah Mami aunty Shahida bata kewarmu da ta zo mana weekend ai”
Ta daga labule domin iska ta shigo, nan ta hango su bisa dining suna cin abinci. Ba abinda ya dame su sai junansu, sun dace, sun yiwa juna daidai, kamar don junansu aka halicce su. Kalar fatarsu iri daya. Ga kuma alamun kowannensu ba mai yawan magana bane. Fatar bakinsu kadai ke motsi ahankali.
Ta saki labulen ta koma ta kwanta tana cewa, “Ya Allah ka janyo hankalin ‘yar’uwata zuwa ga mai sonta tun ranar da ta zo duniya, tun tana tsumman goyon ta, koko tace tun tana ciki. Idan kuma babu alkhairi a ciki, Allah Ka zaba mata wanda ya fi alkhairi, ba tare da ran iyayenmu ya baci da ita ba”.

Soyayya tsakanin Zahraddeen da Safah ta ci gaba da mikawa cikin salo mai ban mamaki. Basu iya sati basu sanya junansu a ido ba. Ba shi Kaduna ba shi Zaria, kullum a tafe yake.
In kuwa bai zo ba, to suna makale a waya ana ta yiwa MTN da ‘Glo’ ciniki na fitar hankali. Sai da jarrabawar karshen zango ta matso sannan suka saurara, inda ya tattara ya koma Kaduna don ba zai so abinda zai shafi karatun ta ba.
Duk da haka su kan gaisa na ‘yan mintuna su kuma ji lafiyar juna.
Da suka kare jarrabawar suka sami hutu na watanni uku, suka tattaro suka dawo gida.
Sai dai kuma Safah cike take da taraddadin wannan hutu, don ta san babu wanda zai yi na’am da zabinta daga iyaye har ‘yan uwa da Kakarta.
Wannan bai sa ta ji ko dar a zuciyarta ba game da soyayyar da take yiwa Zahraddeen Maitama. Shi din, ya san mene ne SO? Ya san darajar abinda yake son, ya kuma iya tafiyar da shi ta hanyoyi daban-daban. Ta yadda duk wadda zata so shi, zata so shi ne da dukkan zuciya, ruhi da bargon jikinta ko da ta ki Allah, shi ba dan bariki ba. Amma ga matar da yake so, mugun dan soyayya ne kamar ba’indiyennan haifaffen Iran John Abraham. Irin kalaman da yake furta mata cikin waya, idan ka ganshi a zahiri rantsewa zakayi ba shi yake fadar su ba, sabida tsare gida, da rashin son raini.

Don haka ne bai sha wahalar yiwa zuciyar Safah kamun kazar kuku ba. Ba ta da wani tunani sai na Zahraddeen, ba ta da wani ra’ayi sai nasa bata da wani buri sai na mallakarsa, matsayin intimate –life-time partner (abokin rayuwa na har karshen rayuwa).
Gaba daya ta mance da Almustapha dake dake can wata uwa duniya yana fama da dakon soyayyar ta, wanda shima ke sonta da dukkan zuciya, ruhi da gangar jikinsa. Ta mance da wanda ya rayu cikin kaunarta, tun bata san kanta ba.
Ya yi hidima da soyayyarta, shekaru goma sha tara. Rana daya tasa kafa ta yi fatali da wannan, auren SO ko auren KAUNA bari muga wanda ke da tasiri.
Karfe takwas na dare Zahraddeen ya iso gidan uban gidansa, kasancewar ya zama dan gida tsakanin Mami da Daddy duk basu bawa zuwan nashi wata ma’ana ta daban ba.
Marwah da yake ta san dawar-garin ta zuba ido don ganin yadda za a karke. Duk da halin sa-idon, ba halinta bane, wannan dai confrontation ne like a chase-game da take son ganin yadda zai kare. Don haka take ganin bai kamata ta kira sa-idon nata da sunan sa-ido ba, saidai ta kira shi curiosity. Wanda hali ne na kowanne dan adam akan abinda ya bashi mamaki.

Bayan sun gaisa da Mami shi da Daddy suka shiga kasafce-kasafcen su cikin takardu da computer. Daga bisani Daddy ya hau sama ya barshi da Mami.
Itama bata jima ba suna ‘yar hirar Innarshi ta yi dakinta. Safah ta fito daga dakinsu, ta yi kyau kamar kullum cikin cotton-lace mai taushi fari sol da yarfin silver, riga, zani da kallabinsu, dinkin da bai kama jikinta ba. Domin Mami ta yiwa ‘ya’yanta tarbiyyar sanya sutura, don haka da wuya ka gansu cikin matsattsun kaya irin na ‘ya’ya ire-irensu.
Tun daga nesa suke sakarma juna murmushi mai sanyi. Kwanaki biyunnan da suka yi basu ga juna ba, jinsu suke kamar shekaru biyu. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, da karamin teburin gilashi a tsakaninsu, wanda aka dora faranti cike da kayan marmari uku; tuffaha, inab (grape) da pear. Shi kuma ya zame daga kujerar ya zauna a kilishi, ya rausayar da kai ya ce,

“Yan makaranta, barka da hutu!”.

Dariya ya bata sosai sabida yadda yayi maganar. Ta ce “Wane irin hutu an dankara mana uban assignment a cikin hutun?”.
Ya ce, “Babu damuwa, don na san you can make it, keep the flag flying….”. Sai ta sa dariya.
Ya yi shiru zuwa wani lokaci ya ce,
“Safah, na zauna na yi tunani mai yawa a kan al’amarinmu, ni talaka ne Safah, kuma sannan dan talakawa. Wadanda basu aje ba, basu kuma baiwa wani ajiya ba, sai abinda karfin jikinsu da lafiyarsu ya samo musu, wanda ke samun abinci a karkashin mahaifinki. Kina ganin za ki iya aurena a hakan in nemi Daddy alfamar neman auren ki?”
Maganganun shi sun mata ciwo. Ta ce, “Da ban san da hakan ba Zahraddeen na amsa ina sonka?”
Ya langabar da kai ya ce, “Za ki iya zama dani Safah cikin dan akurkin gidanmu a Zaria? Ba zan iya rabuwa da Innata inyi nisa da ita ba Safah a dalilin aure. Tayi min komai a rayuwa. Bayan kasancewarta Uwa, ta taka matsayin Uba ma. Za ki iya taimaka min in tallafi rayuwar ta, da marayun kannena?”

Ta lumshe ido cikin wata sabuwar kauna dake kara mamayarta, ta kuma lullube zuciyarta, ta ce,
“Kada ka yi haufi a kaina Zahraddeen, soyayyarmu hadin Allah ce, ba don wasu kyale-kyale na rayuwa ba. Continue be your natural-self Yaya Deen I like it, and I respect your balues too much……. Zahraddeen din nake so ta yadda har bana iya waiwayawa in hango hierarchy din da shi ya ke gani. Wanda so baya la’akari da su…….” sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta lullubeta don ganin irin yadda ya saki jiki sharaf ya zubawa fatar bakinta dake motsi ido kawai sai ta ke ganin kamar har ta zarme tayi subutar baki. Sai tayi sauran gyara zancenta da cewa
“Ni dai fatana da burina shine ka rike soyayyata cikin amana. Ka yarda dani, nima in yarda da kai, Allah Ya yarda damu bakidaya. Idan ka yi min wannan ni kuma na yi alkawarin zama da kai cikin kowanne hali, akwai ko babu, dadi ko akasin sa……”
Unconditionally ya mika mata hannu “Shake my hands, Safah….. na gode da soyayyarki……..ina rokon Allah Ya fidda ni kunyar soyayyar…. Ya bani ikon fita hakkokinta,…. Ya bani ikon muhimmantata fiye da duk wani al’amari da dan adam ke burin samu!!!.”
Suka hade hannunsu wuri guda kamar masu kulla alkawari.
***

Mami ta soma tsarguwa da yawan zuwan Zahraddeen cikin gidansu, da yawan kebewar da suke yi shi da Safah, ba dai wani waje suke tafiya ba anan ‘main’ falon su ne, don da sai ya yi wata guda bai zo gidan ba, amma tun dawowarsu hutu kullum ya taso ofis yana gidan, tare suke dinner da jama’ar gidan.

Ga wata sabuwar al’ada da Safah ta bullo da ita na yawan kwalliya wadda ta lura saboda Zahraddeen take yinta.
Ta shiga damuwa ainun tana neman bayani, ta san babu kuma inda za ta same shi sai a bakin Marwah. Sai dai kuma Marwah ba a jin ta bakinta in dai a kan ‘yar’uwarta ne, suna rufe sirrin junansu ta yadda ko su iyayensu basu san tsakaninsu ba.
Sannan Marwan ba ta taba fadin aibun ‘yar’uwarta sai dai alherinta. To haka ita ma Safah, duk da halayensu ba daya bane tana matukar kaunar ‘yar’uwarta, kashewa suke su rufe ba wanda ya ji ba wanda ya gani.
Ko fada su kai a junansu baya wuce kwana daya sun shirya sun manta komai. Don haka ta ga gara ta tunkari Safan kai tsaye ta yi mata bayanin abinda take zargi.
Karfe tara na daren ranar ta yiwa Zahraddeen rakiya ya tafi. Tana dawowa ta cimma Mami a gefen gadonta ta yi tagumi.
Ta zauna a gefenta ta sauke mata tagumin ta ce, “Maminmu, lafiya kika zuba wannan uban tagumi? Har na shigo baki san na shigo ba”.
Ta dube ta sosai da idanunta da ba sauki a cikinsu, ta ce,
“Safah”.
Ba ta amsa ba illa ta dube ta, sabida yadda ta kirayi sunan nata cikin kakkausan harshe.
Ta ce, “Me ke tsakaninki da Zahraddeen?”

Ta sunkuyar da kanta kasa. Ba ta yi magana ba, sai da Mami ta yi mata tsawa ta ce, “Ba magana nake yi dake ba?”
Cikin sarkewar murya ta ce, “Ki yi hakuri Mami….dama…..dama gobe ne Deen yake son ya sanar da Daddy, ni kuma dama yau zan sanar dake muna son junanmu……..mun yanke shawarar yin au….”
Ji kake kauu! Mami ta dauke ta da mari har sai da ta ga wuta, ta nemi ji da ganinta na wucin gadi ta rasa.
Mami ta ce, “Abinda za ki yi mana kenan? Tozarcin da zaki yi min kenan? Sabida kin je jami’a idon ki ya bude da maza. Kina nufin ba za ki auri dan’uwanki mai kaunar ki ba? Me Zahraddeen din yake da shi wanda Almustapha ba shi da shi?
Ke ko kunya ba ki ji a ce za ki auri yaron Baban ki? Boyi-boyin Babanki? Dube ki don Allah, kina kallon kanki a madubi kuwa? Amma ki rasa a inda za ki kare da zaman aure sai a cikin garin Zaria?
Me yake da shi? Me zai baki? Duk abin da zai baki daga aljihun ubanki zai fito. Wannan shine abin da kike ganin kin yiwa rayuwarki daidai?”
Tana share hawaye ga mamakin Hajiya Zainab sai ta bude baki muryarta na rawa ta ce, “Mami ni ba ruwana da kudi, matsayi ko mukami, face abin da zuciyata ta aminta da shi.
Ni ba kin Ya Imam nake yi ba, kawai dai ba zan iya auren shi ba, don ganin shi nake tamkar dan’uwana da muka fito ciki daya.
Ki yi hakuri Mami ki sanya min albarka, domin Deen nake so, shine zabina…..”.

Mami sai ta saka salati, kafin ta fashe da kuka. Yau tana fada Safah na mayar mata a kan da namiji da baya da tabbas.
Ta ce, “Da gaske Safah ba za ki auri Imam ba?”
Ta ce, “Ku yi hakuri Mami, wallahi bana son sa da aure!”.
Ta ce, “Ashe kuwa za ki sake wasu iyayen ba mu ba, muddin kika kafe a kan bakan ki. Yaron na dawainiya da son ki tun ranar da aka haife ki, amma da abin da za ki saka masa kenan?
To wallahi ba da ni ba, wannan cin fuska da cin amanar…..”.
Safah ta ja shessheka ta ce,
“Wallahi Mami ban taba yaudarar Ya Imam ba, balle in ci amanar shi. Ko mail da yake mini Marwa ce take amsa mishi bani ba, duk wani hannunka mai sanda da zai nuna bana ra’ayin auren shi na yi mishi tun ma kafin in hadu da Zahraddeen.
Me zai hana ya auri ‘yar’uwata tunda na lura ita tana son shi?”
Haushi ya kashe Mami. Ta ce, “Kin fi shi ido ne, ko kin fi shi sanin da wanzuwar Marwan ya ce ke yake so? Tashi ki bani wuri tun ban yi mugun kalami a kanki ba”.
Ta mike sum-sum-sum ta fice, a ranta tana cewa, “Ko duniya za ta taru a kanta ba za ta auri wanda zuciyarta ba ta so ba”.
****

Karfe goma na dare Mami ta cimma Daddy a dakin barcinsa yana sauraron rediyon BBC. Mami ta samu waje ta zauna ta yi jigum, ranta a jagule, zuciyarta a hargitse.
Kallo daya Daddy ya yi mata ya san yau wani abu ya sukurkuta mishi Zainabu-Abu. Ya rage rediyon ya taso daga mazauninsa ya zauna a gabanta.
Ya mika hannunshi ya kama nata ya ce,
“Wa ya tabo min Zaynabu-Abu, uwar-biyu, mai tagwayen suna, mai tagwayen ‘ya’ya?”
Duk da bacin ran data ke ciki, saida ya sata dariya. Ta yi murmushi, wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce,
“Daddy kenan, kada ka ce min baka san abin da ke faruwa cikin gidannan ba? Ka taba zama ka yi tunanin dalilin sintirin Zahraddeen a gidannan a ‘yan kwanakin nan?”
Cikin faduwar gaba Ya ce, “Me ya faru? Na ganshi dai yana zuwa, amma ba zan ce ga dalili ba”.
Ta yi kwafa ta yi huci mai zafi ta ce,

“Wai Zahraddeen da Safah son juna suke!”
Ya ce, “Gyara min kalaman ki Zainabu, ko dai Zahraddeen da Marwah?”
Ta girgiza kai ta ce, “Oh-oh! Yadda na fadi haka al’amarin yake. Baki da baki Safah ta gaya min nan duniya Zahraddeen take so”.
Daddy ya yi shiru, can kuma ya ce,
“Wannan ai shirme ne, ki kwantar da hankalinki, zan gansu dukkansu”.
Ran Mami ya baci ganin bai dauki abin da muhimmanci ba. Ta ce, “Ni dai ka ja mishi kunne, kada in kara ganin kafar shi cikin gidan nan da sunan wai ya zo wurin Safah yana hure mata kunne da wannan munafukar muryar tasa kamar ta ba-sarake, Safah da mijinta, kuma ko babu ban ga me za ta ci da Zahraddeen ba.
Bakin rijiya….ba wajen wasan yara bane. Ban da rashin hankali ya dubi Uwargijiyarshi ya ce yana so da aure? Saboda kankanba da neman wuce gona da iri ko saboda mene? Ai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,…… kuma Tuwon Girma…. Miyarsa nama”
Daddy ya yi murmushi yana kada kai ya ce,

“Wannan ba hujja ba ce, ku mata ban san irin ku ba wallahi. Ni a wajena Zahraddeen mutum ne har mutum, mai nagarta, daraja da sana’ar da za a bawa aure.
Ba don maganar Imam ba, babu abin da zai hanani wanke Safah in ba shi ba tare da na yi la’akari da hujjojinki ba. Mutum da karatunshi da usuli da lafiya da addini da aikin yinsa, me ake nema a nagartaccen miji da ya wuce wannan?
Jarumi haziki irin Zahraddeen, mai zuciyar neman na kansa, mai kwakwalwa, kyakkyawar zuciya da halaye na kwarai, gaskia da amana, wadanda suka yi karanci ga matasan zamanin nan, wallahi ba don Imam ba, zan baiwa Zahraddeen Safah ba tare da na ji ko da dar ba”.
Mami ta kama baki cikin mamaki. Cikin takaici ta ce,
“Kenan kana nufin babu matakin da za ka dauka? Idan aka yiwa Imam haka anyi adalci kenan?”
Ya ce, “Ni ban ce miki na amince ba, hujjarki kawai na soka (criticizing). Na ce dake zan gansu, ki bi komai a hankali, ki cire bacin rai, fushin fari ba naki bane, tunda ba ke za ki yi mata zaman auren ba”.

A wannan daren Mami ba ta yi barci ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare. Ita kam duk haushin Daddy ya rufe ta, me Safah take nufi? Da wacce fuska za ta dubi danta Almustapha idan Safah ta watsa musu kasa a ido?
A washegari Safah ba ta ga walwalar Mami ba, ta daure mata sosai. Da Marwa take sabgoginta, itama sai ta kama kanta, ta killace kanta a daki tana rubuce-rubucen ta.
Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, idan ta tuna marin da ta sha jiya. Ba ta taba ganin bacin ran Mamin irin jiya ba.
Har kullum ita cikin kauna take nuna musu komai, ba ta taba tunanin Mamin na da zafi har haka ba. Ta yarda ta amince akan Imam, Mami zata iya batawa da kowa hada dasu ‘ya’yan cikinta kuwa. Don har fadi musu take
“kafin in sameku shi na samu, a lokacinma dana riga na fidda rai da samun ‘ya’ya. Sai ya zamo wani irin nagartaccen Da, mai debe min kewar ‘ya’yan da bani da su. Don haka zuwanku bai rage komi daga kaunar dana ke yi masa ba. Sabida ya maye min gurbin ‘ya’ya goma, a lokacinda banida ko daya!!!

Balle ke kuma na haife ki ne kawai, amma bansan kashinki ba bansan fitsarinki ba, sai shayarwa ta dan lokaci, wadda ciyarwar dashi yayi miki da madara ta fita tsaho”.
Karfe takwas na dare Zahraddeen ya zo, Mami na falo cikin seater tana sauya tashar MBC zuwa Aljazeera.
Tun daga jin sallamar shi ta bi ta daure fuska irin yadda ba ta taba yi masa ba. Ya zube gwiwoyinsa a kasa yana gaishe ta, ta kafa mishi ido ba ta amsa ba. Karshe sai ta mike ta shige kafar benen da za ta sada ta da dakin barcinta, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Daga shi har Safah gwiwoyinsu suka yi sanyi, ita Safah ma kunya ce ta kama ta. Aka rasa mai fara yin magana a cikinsu.
Daga baya Zahraddeen yai ta maza, ya yi murmushi cikin basarwa ya ce,
“Mun yiwa Mami laifi halan?”
Ta yarfar da hannu, ta lumshe ido
“Tun jiya haka take, na kasa gane mata”.
Ya yi shiru cikin tunani, can kuma ya ce, “Mai yiwuwa ne ba ta yi na’am da al’amarin mu ba”.
Ta ce, “Babu komi, za ta huce a hankali”.

Daddy na saukowa daga matattakalar bene Mamin biye da shi rike da brief case dinsa ya yi tozali dasu a falon.
Ya yi murmushi yayin da Mami ta kara hade rai. Ya ce, “Dama ina son ganin ka”.
Ya mike cikin girmamawa ya bi bayansa suka nufi falon ganawa da bakinsa dake daga harabar gidan.

Daddy na bisa kujera, Zahraddeen na gefensa bisa kilishi.
Daddy ya ce, “Ya sakon da na baka na Wilcod din Abidjan?”
Ya ce, “Ya zo ya amsa tun shekaran jiya”.
Ya ce, “To madallah”.
Sai kuma ya yi shiru, shi ma Zahraddeen kanshi na kasa. Ko motsin kirki ya kasa.
Can Daddy ya ce,
“Zahraddeen”.
Ya dago da fararen idanunshi ya dube shi amma bai amsa ba.
Ya ce, “Meke tsakaninka da Safah ne?”
Zahraddeen ya rude, ya soma inda-inda, saboda kwarjinin da Daddy ya kara yi masa, har ya soma ganin wautar kansa, da wuce gona da irin sa.
Daddy ya yi murmushi ya ce,
“ Zahradden feel free with me. Ka amsa min mana, ni Babanka ne ba bakon ka bane”.
Ya yi ta maza ya ce, “Am Daddy, dama…..dama ina son mu samu lokaci ne, sannan in gabatar maka da kaina a matsayin mai neman auren Safah, mun daidaita kanmu”.
Daddy ya yi murmushi ya lumshe ido na ‘yan mintunsa sannan ya budesu a hankali akan Zahraddeen din ya ce,

“Zahraddeen zaka iya hakura da son da kake wa Safah, ka juyar dashi ga ‘yar uwar ta? Ina nufin, ka auri abokiyar tagwaitakarta MARWAH?”
A firgice ya dago ya dubi Daddy, kamin ya yi magana Daddy ya ce,
“Safah da mijinta, tun ranar da aka haife ta, amma idan kana ganin za ka iya auren ‘yar’uwarta sati mai zuwa ka kawo min sadakin naira dubu goma in daura muku aure rana ita yau. Lahadi kenan, zan daura auren Safah da Almustapha tare da naku. Tashi je ka ka yi shawara, ina sauraron ka”.
Ya bude baki zai yi magana Daddy ya ce, “Ka je ka yi shawara tukunna, ba zan yi hakan ba sai da amincewar ka. Ina sonka ne Zahraddeen, ina son hada jini da kai, saboda kai mutum ne na gari.
Banda shi wancan alkawari, ba abin da zai hanani baka wacce kake so cikin ‘ya’yana. Amma Safah da Marwah duk daya ne, abin da ya yi Safah shi ya yi Marwah, sai dai bambanci na akida da halayya wanda za ka iya lankwasawa cikin dan lokaci kalilan. Tunda har yanzu yara ne. Tashi jeka ka yi tunani sosai, ka kuma shawarci Innar ka, na baka kwanaki uku ka zo min da abin da ka yanke”.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *