Chapter 7: Chapter 7
Kwanan Safah uku a daki ba ta fitowa don kar su hadu da Yaya Imam din, ko yunwa take ji sai dai ta yi waya kichin a kai mata abinda take so. Shi ma Imam din ya share ta baya shiga sabgarta, ga shi ga dukkan alamu a yanzu kam ya fara amincewa da gaske Safah ta ke ba ta son shi. Idan a da yana yi mata uzuri da kuruciya a yanzu fa? Shekarunta goma sha tara, ta isa ta bambance abinda take so da wanda ba ta so. Wato dai ta isa ta yiwa rayuwarta ZABI ba tare da an tursasa ta ba.
Shi kuma ya amince ba zai aure ta bisa tursasawar iyaye ba. Zai yi mata yadda take so muddin ta furta da bakinta cewa ba ta son shi.
A dakin Hajiya Mama yake a safiyar yau suna hira, ta ce, “Ban da abin kuruciya irin na Safah ga dan’uwanki jinin jikinki, wanda ya san ciwo da darajarki, amma ki nace sai wani can da bai san zafin ki ba?”
Sai kuma ta tuna da wa take magana, ta yi hanzarin gyara subutar bakinta, ta ce, “Au, wanda yake son Safah shi Alhaji zai baiwa Marwah”.
Imam ya yi tsai da ranshi yana duban ta a tsanake. Ji yayi tamkar aradu ta rikito kansa. Amma ya nuna maganarta ba ta taba zuciyarshi ba.
Ta hanyar cewa
“Shi wanda take so din a ina yake?’
Hajiya Mama ta ga babu amfanin yiwa jikan nata rufa-rufa, kallo daya ta yi mishi ta karanci matsanancin KISHI a kwayar idanunshi.
Duk sai ta ji babu dadi, ta kuma yi Allah wadai da surutun ta. Koda yake dole kuma ta gaya mishi yadda abun yake, tunda kuma Daddy ya kashe maganar.
Ta ce, “Ma’aikacin Alhaji ne, wa yake da suna? Ni sunan wuyar fada yake mini”.
Ya ce a nitse, “Kutama ko Peter ko Maitama?”
Ta ce, “Kai, ba haka na ji sunan ba”.
Ya mike ya zura takalmin shi yana cewa, “Idan kin tuna ki kira ni, kin san baki san sunanshi ba kika fara gaya mini?”
Ta ce, “Dawo ka zauna zan tuna a hankali”.
Ya ce, “Kada ma ki tuna, bana son ji”.
Karfe sha biyu na rana Zahraddeen ya shigo gidan, cikin shadda edcelcior maroon colour, kanshi babu hula wanda hakan ya bayyanar da kwantacciyar sumar kanshi ta Mallawan usli, sai sheki shaddarshi take tana maiko tana nuna tsadarta.
Kiris ya rage suyi karo da Imam dake fitowa daga kofar cikin gida. Dukkansu basu san juna ba sai a suna.
Imam ya kan ji sunan ZAHRADDEEN MAITAMA a bakin Daddy ba tun yanzu ba, ta yadda yawan ambaton Zahraddeen din da Daddy ke yi Imam ya fahimci shi din wani hadimi ne mai muhimmanci ga Daddyn, domin adadin kaunarka da mutum adadin yawan ambaton sa a bakin ka, Zahraddeen kan ji dana ALMUSTAPHA a bakin Daddy, amma basu taba ganin juna ba.
A take Zahraddeen ya yankewa zuciyarshi wannan ne Almustapha, tunda ga kamannin Safah nan a kyakkyawar fuskarsa, ta wani fannin kuma da Daddy yake kama.
A take ya ce, “Imam…..”
Shi kuma ya ce, “Maitama….”
Suka yi hannu suna murmushi. Amma fa zuciyar kowanne na zabalbala da kishin dan uwan ansa, amma fa tsabtataccen kishi na masu aiki da hankali da tunani, ba kallon juna suke don son hango aibu ko nakasun junan su ba ko makamancin hakan a’ah, kallo ne na son hango how much lucky are you??? Kowannensu ganin dan uwansa yake a matsayin wanda yafi kowa sa’a a duniya. Imam ya fasa fita ya yiwa Zahraddeen jagora har main parlour.
Yau kadaran-kadahan Mami ta yiwa Zahraddeen karba ta mutuntawa. Tunda ya zama dolenta.
Ta ce, “Zahraddeen ga Almustapha fa”.
Ya ce, “ai na canka Mami, from the first glance…” (daga kallo na farko)
Ta ce, “Imam. Ga Zahraddeen din Daddy”.
Ya ce, “Nima na canka Mami, ko daga tsagin Mallawan”.
Duka suka yi dariya. Suka zauna tare cikin kujera, daga nan kuma sai hira rai-rai-rai kamar sun dade da sanin juna.
Cikin dan lokacin Mami ta soma fahimtar Zahraddeen mutum ne mai dadin mu’amala, kuma dole mutumin da ke alaka da shi ya so shi, saboda saukin kansa. Nutsuwarsa da yadda yake fidda kalamansa a ilmance, duk wata kalma data fito daga bakinsa mai ma’ana ce, daga yadda yake Magana zaka fahimci zurfin ilminsa, ga kyau da kwarjini, gashi mai wayayyen kai. Safah bata yi laifi ba don tayiwa kanta sha’awar auren Zahraddeeen domin ta ko’ina yayi a rayuwa.
Ta tabbatar Daddy na da hujjar shi na son Zahraddeen, kuma bai yiwa diyarta zaben tumun dare ba. Auren gata yake so yayi mata.
Sai ta russunar da kwayar idonta kasa ahankali cikin saduda. Sai azahar Daddy ya shigo yana baiwa Zahraddeen hakurin bata mishi lokaci da ya yi.
Zahraddeen ya ce babu komi. Saima halayen Alhajin dake kara masa ganin kimarsa. Bai dauki kanshi a bakin komi ba. Suka nufi masallacin Daddy dake wajen gidan suka gabatar da sallar azuhur.
Kamin su dawo Mami da Marwah sun shirya dining, ita ‘yar mulkin tana daki ko fitowa ba ta yi ba. Tana jiyo muryar Zahraddeeeeeeeen dinta……, cikin tausasan lafuzzansa. Ya na yiwa Imam bayanin nasarorin da ‘Dan-Kasa Holdings’ ta cimma a wannan shekarar. Bata san cewa hawaye ke zuba tarara daga idanunta ba. Saida ta ji su cikin kunnuwanta, da yake a kwance take.
Bayan sun kammala cin abincin Imam ya yi musu sallama zai je Rabah Road. Zahraddeen ke jan Daddyn cikin motarshi ‘buick’ da Imam ya kawo mishi, a kan hanyarsu ta zuwa ofishin Daddy.
Suna tattauna al’amura masu muhimmanci a garesu. Kamar Uba da dan sa, da yake matukar so. Kamin su gangaro kan muhimmiyar maganar dake cin zuciyar kowannensu.
Daddy ya ce, “Kai nake saurare Zahraddeen, ya ya ka yi shawara da Inna?’
Yana tukin, amma hakan bai hana shi sunkuyar da kai ba, ya ce, “Na karbi Marwah Daddy, na karbi musayan ka da hannu bibbiyu, ka yi min addu’a Allah Ya sa ta so ni……….???”
Dariya ta kama Daddy saboda yadda Zahraddeen ya yi maganar cikin sanyi? Kamar mai tambaya, kamar kuma mai hasashe. Ya mika hannu ya dafa kafadar Zahraddeen yana bubbugawa ya ce,
“Ta ina Allah ya rage ka da diya mace ba za ta so ka ba?”
Ya cira kyawawan idanunsa ya dubi Daddy. Ya daga mishi kai yana murmushi cikin bada karfin gwiwa, ya ce,
“Kada ka yi haufi kuma kada ka karaya Zahraddeen, you are a genius……
Allah Ya yi maka duk wata falala ta rayuwa, da dan adam ke burin samu.
Ba Marwah ba, duk ‘yar wanda kake so za ka aura Zahraddeeni, idan fa har za ka cire inferiority compled din daka sanyawa zuciyarka na kasncewar ka karkashi na. Tunda har Safah ta so ka, duk da akidunta da baudaddun dabi’unta, a gabana take kuka saboda son da take yi maka. Wanda na tabbata har yau bata daina ba, don tanada karfin zuciya ne da sadaukarwa.
Don haka count yourself among the luckiest, wanda ake so fiye da Imam dina. (yayi murmushi) Ni na gaya maka Marwah zata so ka fiye da son da Safah take yi maka. Ba duk abinda muke so a rayuwa lallai shi zamu samu ba.
Muna barin wani abu duk son da muke mishi don wani abu muhimmi, wanda ya fi son zuciyar mu muhimmanci. Ba duka mafarkanmu ne suke zama gaskiya ba. Su, (mafarkan) kamar ‘ya’ya suke; abin nufi, muna daukar cikinsu, amma ba kowadanne muke yin sa’ar haifewa ba.
Wasu tun suna ciki suke zubewa. Wasu kuma kuma a haife su a mace. (Zaynab Alkali). Irin wannan auren albarkatacce ne Zahraddeeni, kuma ba’a ganin fa’idarsa sai an zauna da juna, an fahimci juna ciki da waje. Soyayyah ta gaskiya ba lokaci daya take faruwa ba, sai a hankali, idan an zauna tare.
Ni dai fatana da kai shine ka zamo tsayayyen namiji wanda zai fi karfin gidansa, kada ka yi la’akari da kasancewar Marwa diya a gare ni ka kasa lankwasa ta.
Ka lankwasata da duk irin tarbiyyar da kake so ta mike da ita. Sannan auren ka da Marwah, baya nufin shi kenan ba za ka kara aure ba, ka auro duk wadanda kake so ka kara, in har za ka iya yin adalci a tsakanin su, nine kuma mai biyan sadakin kowaccensu”.
Zahraddeen sai ya yi murmushi yana mamakin halayyar GIRMA irin ta Alhaji Aliko. Ko da baya son Marwah, ya yiwa zuciyarshi alkawarin rike ta da amana saboda mahaifinta.
Sai dai yana shakkar Marwah dinnan, a yadda ya ga takunta da tsarin rayuwarta da kyar in za su daidaita, kwata-kwata halayenta da dabi’unta opposite na ‘yar’uwarta ne, ko ma ya take, ko yaya ne, ya yi alkawarin zai rike ta amana tare da dora ta kan turba sahihiya. Anya???
****
R
anar alhamis 9/9 na shekarar alif dari tara da casa’in da tara (1999) Baffannin Zahraddeen da kannen mahaifiyarshi suka gabatar da komai na auren dansu da Daddy ya ce sadaki kawai yake so.
Domin shine mai alhakin yiwa Zahraddeen aure, ko da ba diyarshi zai aura ba. Amma Baffan Zahraddeen ya ce tunda yaro yana da halin yi a barshi ya yi daidai karfinsa. TUWON GIRMA……miyar sa nama.
Duk wata dukiya da ake bukata kafin aure da al’ada ta gadar sun gabatar tare da sadakinsu, sama da yadda Alhajin ya nema. Da lefe saitin jakunkunan lefen zamani shidda, dankare da sittiru na masu rufin asiri, don dai shi Zahraddeen baisan wasu kayan adon mata ba, Rabi’a bata sani ba, balle kuma Inna. Umma kuwa ai ba’a zancenta, bakauya ce ta a bada labari ko Rabi’a tafita sanin kwalliya, don haka matar Peter ce abokin aikinsa Kafilat ta hado lefen ya biya komai bayan ta ci riba yadda taga dama, don bayerabe baya aikin banza.
Itama da taimakon makociyar ta Maryam da yake ita bahaushiya ce kuma mata ga ma’aikacin Zenith ta san yadda ake hada lefe a al’adar hausa. Sun tsaida ranar daurin aure asabar mai zuwa, saboda su Marwah za su koma makaranta litinin, wato kwana biyu bayan daurin aure.
Marwah ba ta san bikin da ake yi ba, ta dai ga Zahraddeen ya daina zuwa wajen Safah, sai ta dauka cewa Daddy ya ja masa birki ne tunda ga Imam ya dawo.
A satin duk kafafen yada labarai na radio, talabijin da jarida na jihar Kaduna, basu da muhimmin kanu sai na yada labaran gayyatar daurin auren ‘ya’yan tsohon Gwamnan, Alh. Aliko Dan Kasa, wanda al’ummar Jihar basu taba mantawa dashi ba. Har gobe cewa suke “baza’a taba yin Gwamnati irin ta Dan-Kasa a Kaduna ba!!!”.
Yana tuna musu da gwamnatin Janar Murtala Ramat Mohammed ta dan lokaci a kasarmu Najeriya, amma kuma ‘rebolutionary’ a zuciyar al’ummah duk da ta dan takaitaccen lokaci ce; considering his zero tolerance for corruption……, for ladity….., maladministration and nepotism…..
A kuma ranar ne Alh. Aliko ya tara iyalinshi baki daya, ga mahaifiyarshi da kanin mahaifinshi Malam Safiyanu a gefe, ya umarci Hajiya Mama da ta bude taron, da addu’a.
Bayan an shafa ya dubi ‘ya’yan nashi baki daya tsayin mintuna goma bai ce komi ba, yana son kowannensu ya samu nutsuwa.
Sannan ya ce, “To ‘yan biyu wannan taron kusan nace naku ne, Safah ke ce babba zan fara dake. Ba sai na tsaya ina yi miki bayanin wane ne mijin auren ki ba kin san shi, tun baki san kanki ba.
Amma kika ture kika kawo maganar Zahraddeen, kuma mun yi alkawari kin bar wannan magana har abada.
A kokarina na rashin son Zahraddeen ya kubucewa zuri’a ta, na yanke shawarar bashi MARWAH…..”
A razane suka cira kai dukkaninsu banda Mami da Safah wadanda tuntuni sun san da zancen. Ba tare da ya damu da razanar su ba ya ce.
“Hajiya Maama ki zama shaida, Baffa Sufyan kai ma ka zama shaida, ko bayan raina wani a nan ya tada wannan auren da zan daura a gobe Allah Ya isa ban yafe masa ba………!”
Marwah ta rushe da kuka ta ce, “Ni Daddy ya ya za ai min haka? A rasa wanda za a hada ni da shi sai yaron babana…… bana so…..wallahi bana son shi…..na wuce da ajinshi!”
Kalaman da suka shiga kunnen Zahraddeen kenan, a lokacin da ya sawo kai zai shigo falon, domin amsa kiran Daddy, wanda bai samu ya zo a kan lokaci ba, sakamakon ayyuka masu yawa da suka tsare shi a ofis.
Sai ya ja ya tsaya ya kasa shiga ciki, nan ya jiyo Daddy na zabgawa Marwah mari tare da fizgo wayar t.b ya shiga tsula mata yana cewa.
“Yaron nawa za ki aura, in yaso ki kashe kanki saboda bakin ciki. Shashasha wadda bata san Annabi ya faku ba. Ban san inda kika debo bakin hali ba, na girman kai da son duniya, ba haka ‘yar’uwarki take ba.
Ko mutuwa na yi na fada na kara ban amince a daura miki aure da kowa ba sai Zahraddeen. Ke ko mutuwa ki kai kafin gobe sai na fara kai gawarki gidan Zahraddeen kafin in kai ki kushewa…..”
Safah ce ta mike da gudu ta kifu a kan ‘yar’uwarta ganin irin dukan da Daddy ke mata, tana kuka ta ce.
“Daddy doke ni a madadinta, fatar jikina ta fi tata kwari…..” Imam baisan sanda yayi dariya ba,
Daddy ya ce “Ko ki kauce ko in hada da ke….”
Ba ta kauce ba ya hadasu ya dinga tsula musu wayar Imam na rikewa yana bashi hakuri. Da sauri Mami ta mike ta ce, “Za ka kashe min ‘ya’ya ne saboda Zahraddeen?”
Ta sha gabansa ta rike wayar da Imam ya kasa kwacewa. Hajiya Maama ta ce cikin mamaki, “Zainabu? Yau gaya mana kike ke kika haifi ‘ya’yan? Ai mun kwana da sanin wannan, ba sai kin maimaita ba”.
Daddy kuwa wanke ta ya yi da mari abinda bai taba yi ba a tsayin shekarunsu talatin da biyar da aure.
Ta kama kuncinta ta rike ta ce, “Ka mare ni, duk akan Zahraddeen?”
Ya ce, “Na mare ki, don Allah ki rama……”
Ba ta rama din ba ta juya ta fice daga falon, ya daga murya yana cewa, “Ki zo ki sa ‘yar taki a gaba ku tafi duk inda za ku in har ba za ta zauna da mijin da na zaba mata ba, to nima ba za ku zauna min a gida ba”.
Zahraddeen dake bakin kofa idanunshi suka yi jajir, jikinshi na rawa ya juya zai fita. Daidai lokacin Mami ta fito cikin sauri-sauri gudu-gudu, ta yi mishi wani irin kallo wanda har abada ba zai goge daga zuciyar shi ba. Sannan ta karasa da gudu ta bi matattakalar bene.
Haka taron ya tashi, jikin ‘ya’yan hutu Safah da Marwah ya yi rudu-rudu, har dai Marwah da take fara sol!
Shi kam Imam kamar mutum-mutumi ya koma. Sai dai fa jin bulalar Daddy dake sauka a bayan Safah yake kamar a jikinsa, amma kawaici, kunya da kau da kai ya danne komi.
Dakin nasu ya biyo su, a lokacin Safah ta cikawa Marwah ruwan dumi a baf ta zuba dettol, ta dawo ta ce, “Je ki gasa jikin ko kya ji dadi”.
Marwah wadda har zuwa lokacin kuka take yi, ta mike ta nufi bandakin. Kafin ta fito Safah ta fiddo mata doguwar rigar barci mara nauyi.
Ta dade a kwamin dumin ruwan na ratsa jikinta, yana rage zogi da radadin da jikinta ke yi. Sannan ta bude ruwan ya tafi, ta sake tara wani ta yi wanka da sabulu sannan ta fito, ta sanya rigar da Safah ta ajiye mata.
Safah na murza mata manthaleta a kafafunta da gadon bayanta inda bulalar Daddy ta kwanta rada-rada.
Ya daga labulen yana kallon su, sai suka ba shi dariya. Abu kadan yana amusing din Imam, a bery jobial and lobing personality. Ya saki labulen ya yi mai isarsa tukunna, ya shigo hannayenshi biyu sarke a baya, ya tsaya jikin kofar yana kallon su kowacce idonnan kamar an zuba dakakken barkono.
Ya ce a tausashe, “Haka kawai kin sa Daddy ya zabgar min ke???”
Hararar shi ta yi, ta ci gaba da shafawa ‘yar’uwarta manthaletan a dogayen yatsunta na kafa, inda wajen ya tashi sosai ya nuna shatin kwanciyar tsabga, ya toshe baki kada dariyar da yake yi ta fito ya ce,
“biyu kyautar Allah….!!!
Hadin kanku kan birge ni, but not all the time, (ba ko yaushe ba).
Kamar dai yau din nan da babu ruwanki amma kin kai kanki kin sha bulala adalilin mai bakin rashin kunya, ita mai cewa ba ta son Zahraddeen din me za ta nuna mishi? Da wani hacinta kamar tumatiri. Banda Allah Ya kashe Ya baki ai Zahraddeen sai BABBAR YARINYA….”
Haka ya yi ta tsokanar su uffan basu ce masa ba. Kulawa ma yabawa ce in ji ‘yan magana. Cikin zuciyar Safah cewa take yi sai an kula kashi yake yin doyi. Ni din da banyi bakin rashin kunyar ba son naka nakeyi? Bai yi aune ba ya ji saukar carbi a gadon bayanshi, ya juya Hajiya Maama ce, carbin ya shige shi sosai.
Ya ce, “Kai-kai! Kin taba jin mata ta doki mijinta?”
Ta ce, “Idan mijin ya zamo babban kwabo wani lokacin sai matar ta doke shi, ina ruwanka dasu? Tunda ka kasa kwatarsu sai bayan an gama tafkarsu zaka zo ka dame su? Kuma ba ka ce ka sake ni ba yaushe ka kara mai dani matar taka?”
Ta sa shi a gaba suka fita suna ta yi tana yankarshi yana ramawa.
A tsayin daren baki daya Zahraddeen bai runtsa ba. Maimakon daren ya zamo jajibiren ranar farin cikinsa, sai ya zamo jajibiren ranar bakin cikinsa.
Kalaman Marwah yake tunawa….. “A rasa wanda za a bani sai YARON BABANA….bana so, wallahi bana son shi….na wuce da ajin shi”.
Shikadai kamar zautacce, bai san sanda yace da karfi
“’yammata nima ba son ki nake yi ba!”.
Da kuma kallon da Mami ta yi mishi, wato kallon raini tsagwaro. Ya tambayi kanshi me ya yi zafi ne? Ko dai ya kira Daddy ya ce mishi ya hakura? Tunda shi ma ba son yarinyar nan yake yi ba?
Wata zuciyar ta kwabe shi da cewa
“Daddy ya fi karfin haka!!!”.
Shin yaya zai ji idan ya ce ya fasa auren diyarshi, a wannan lokacin da ya riga ya gayyato duniya? Yake ta narkar da aljihunsa domin shirye-shirye?
Hatta katin daurin auren a Leceister aka bugo shi. Ya shiga tausar kanshi da kanshi har ya amincewa zuciyarshi auren diyar Aliko Dan Kasa da zuciya daya, amma fa sai ya daidaita mata sahu.
Asabar din karshen watan Maris, dubban jama’a cikin garin Kaduna da wajenta suka shaida daurin auren Engr. Imam Zubair Dan Kasa da Safah Aliko Dan Kasa, sannan na Engr. Zahraddeen Aminu Maitama da Marwah Aliko Dan Kasa, a Kaduna State Central Moskue, a kan sadaki mafi kankanta.
Daga nan angwayen suka zarce da walima a gidan saukar bakin Alh. Aliko dake unguwar Jabi Road.
Mami na fama da jama’a, kawayenta, ‘yan’uwanta, ‘yan’uwan Hajiya Mama da ‘yan cin arziki, makota da abokan arziki, don haka ko tana cikin bacin ran abinda ya faru jiya ba za ka gane ba.
Hidima ta sha kanta, gidanta a cike yake taf ba masaka tsinke, musamman lokacin da ‘yan uwanta suka iso daga Yola, Bus biyu suka ciko.
A cikin akwai ‘ya’yan wanta Rahima da Badriyyah da ake kira Badar, tsaran Safah da Marwah ne.
Sannan akwai kawayen Marwah ‘ya’yan kawayenta su Fadila, Fatee, Maimuna da Yasmin duk sun zo, duk da ba Marwan ce ta gayyato su ba.
Mami ta yi musu waya sun biyo iyayensu sun zo, su suka takurawa ‘yan biyun suka yi wanka amma juyin duniya sun ce ba za su yi kwalliya ba.
Marwah ta ce, “Saboda boyi-boyin Baban nawa zan yi kwalliya? Sai ku sa ni inyi kwalliyar in gani.”
Safah ta juyo ta kalle ta da idanuwa masu kaifi…, (sharp-eyes). Jikinta ya yi sanyi da ta tuno da alakar Safah da Zahraddeen. Ta yi shiru ta yi lakwas. Tun daga lokacin bakin ta ya mutu. (abincin wani gubar wani)
Badar da yake abokan wasa suke wato ‘yar mace da ‘yar namiji, ta ce, “Wallahi ko ki tashi ko mu danne ki mu tube ki mu sa miki”.
Ta ga dukkaninsu sun mike suna shirin danne tan, ga Badar masha Allah da ita (lukuta ce) ta ce, “Ku dakata, mai yasa kuka damu sai ni? Ita Safah ba za ku danne ta ba?”
Suka ce, “Ai ke kin fita baki ne, bakin tsiwa da rashin kunya. Ita ba za ta bamu matsala ba kamar yadda kike bamu, Allah Ya sa dan kanzo ne angon mu bai dame mu ba, muna bisa umarnin Mami ne”.
Ta ga dai da gaske tube ta zasu yi, kuma an ce sarkin yawa….. ba girma ba arziki ta karbi kayan ta saka tana kunkuni tana cewa,
“Yo ba gara dan kanzon ba da wannan sumumu-kasau din? Yana tafe yana zukar iska da kyar kamar dole ake yi mishi sai ya shaketa, bayan da ganin shi ka ga dan talakawa, yaushe ya shigo garin da shaddar shi za ta burge ni?’
Suka sa dariyar data kara kular da ita suka ce, “Eh, hakan dai zamu wanke ki mu kai mishi Zaria. Arziki kuma na Allah ne, babu wanda aka haifa da shi kowa a nan duniya ya samu”.
Da wannan suka kashe bakinta. Badar ta fiddo robar kayan lalle ta ce, “Ni bani kafa ki gani in rangadawa bawan Allah lalle”.
Ita kuma Rahima kan Safah ta koma ta zame mata dankwali ta ce, “Wannan tufkar za a kwance, relader zan shafa miki”.
Haka suka rufe su, mai yin kunshi na yi, mai dilka na yi, mai gyaran gashi na yi. Kamin ka ce meye wannana sai ga ‘ya’yan Mami sun fito ragas.
Karfe takwas motocin diban jama’a zuwa wajen Dinner sun iso. Nan ma sai da aka tafka rigima da Safah da Marwah, domin sun ce ba inda za su.
Imam da Zahraddeen suna waje tare da zugar abokansu. Badar ta fito ta shaida musu cewa sunyi iya yinsu, amaren sun ce baza su je ba.
Hutu na musamman Alh. Aliko ya bai ma dukkanin ma’aikatan DAN KASA HOLDINGS, don haka kwansu da kwarkwatarsu suna cikin tawagar Engineer Zahraddeen Maitama.
Ga Peter da Ahmad Kutama manyan manajojin Daddy a hagu da daman shi. Peter ya sha shadda kai ka ce Bahaushe ne, har da hular zanna-bukar.
Yayin da angon ke sanye cikin wani lallausan yadi mai shara-shara fari sol har kana iya hango best dinshi da manyan damatsanshi masu nuni da alamun karfi da cikakkiyar lafiya da mazantaka ta ko’ina.
Kallon yadin kadai ya ishe ka kimanta tsadarshi, domin a kalla ya ba naira dubu tamanin baya. Anko ne suka yi ko in ce Daddy ya yi musu shi da Imam, wanda haske da kwarjininsa ya dushe hasken duk wani matashi mai ji da kansa dake harabar gidan.
Idan aka ce ka bambance wanda ya fi dan’uwansa tsakanin Zahraddeen da Imam Almustapha, an sanya ka cikin rudu.
Dukkanninsu bakake ne amma ba can ba, sannan ba za ka hada wanda ya rayu cikin arzikin tun haihuwarshi da wanda a rana daya ne Allah ya yi mishi arzikin ba, wannan shine kawai bambancinsu, shima cikin kwayar ido da yanayin fatar jiki yake ba a halittar su ba. Shi Zahraddeen din ya zarta Imam a kyawun fuska shikuma ya zartashi a kyawun fata da wayewar cikin kwayar ido. Wato ya fishi edposure.
Duk rabin jama’ar Imam jar fata ne daga garuruwa daban-daban na yankunan Birtaniya, inda ya zauna ko yayi wani aiki ko karatu ko yake da abokai.
Ya dubi Badar ya ce, “Suna ina?” Hausarshi kanta bata fita sosai.
Ta ce, “Suna dakin su”.
Ya ce, “Mami fa?”



