⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 9: Chapter 9

“Kada ka yi haka Zahraddeen, Alh. Alhaji Aliko bai cancanci wannan sakayyar daga gareka ba……”
Lumsassun idanun shi ya sauke ahankali akan Kutama…. “Kutama sai in zauna in zama mijin hotiho da lafiyata, da kuruciya ta, da ilimina, da martaba ta da komai? Ko ko sai in zauna in zama mijin Hajiya don kawai a ce ina auren diyarsa?
Dama a ce yarinyar ta san mutuncin mutane ne kamar ‘yar uwarta da da sauki, to ba ta san wannan ba”.
Kutama ya ce, “Wai me ta yi maka ne?”

Ya ce, “Ban sani ba, tunda duk bayanin nan da na bata lokaci na nayi maka baka fahimci komai ba”.
Ya ce, “Na fahimce ka mana, sai dai bana bayan ra’ayinka.
KUDI! Sune mutuncin da martabar my friend. Ya fada yana bubbuga kafadunsa.
Kada zuciya da shirmen mace yasa ka yi saki-na-dafe, ka san dai yadda yanayin kasar tamu yake a yanzu. Takamar ka shine kana da kwalayen ilimi, to akwai wadanda suka fi ka fal a kasar nan amma suna nan zube ‘unemployed (babu aikin yi). Zahraddeen wulakancin da rainin yana tsiro ne? Ko yana toho a jikin dan Adam?
Balle nawa yarinyar take? Da ka dora mata nauyin kirjinka ka kalallame ta da kalaman soyayya shi kenan za ka mantar da ita shirmen ta. Kai fa ‘giant’ ne Zahraddeen. Irin mazan da baku da yawa a duniya. Wallahi ba irin ku ne mace ke cewa bata so ba, duk abinda take takama dashi kuwa; kyau, ilmi ko arziki.

To kai matsalata da kai ‘fadin rai’ da ‘ji da kai’. Ko da yake YEEESSS…..! Kana da abubuwan da za ka yiwa diya mace yanga dasu ko ‘yar shugaban kasa ce ba ‘yar Aliko ba.
To ka yi amfani da wadannan makaman da Allah ya baka, ka yi yakin neman soyayyarta dasu ku zauna lafiya.
Amma fa ra’ayina ne wannan nake gaya maka, don gaba nake da kai na fi ka edperience a kan rayuwar yau. Ban ce lallai ka yarda dani ba, amma ka yi tunani”.
Ya tada injin motar suka hau kwalta suka ci gaba da tafiya.

Zahraddeen kallon sa kawai yake, yana mamakin matacciyar zuciya irin ta al’umma, sabida kudi sai su sarayar da martabarsu da mutuncin da Allah Yayi musu, Ubangiji (SWA) da kanSa Yace “Na girmama bani – Adam!” sai bai ga amfanin ci gaba da magana da mutum mai karamin tunani da kwadayi irin sa ba.
Don haka ya ja bakinshi ya yi shiru. Har suka shigo Kaduna bai bari sun kara yin maganar ba.

Nan suka hadu da sauran abokansu suka je wa Daddy Ta-sani. Daddy ya yi murna sosai har ‘yar kwarya-kwaryar walima yasa aka hada musu. Zahraddeen ya tambayi Imam Daddy ya ce ya je Abuja kan shirye-shiryen komawar shi, don gobe zai tafi.
Suka shiga suka gaida Mami, fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa musu, sannan ta kawo atamfofin English masu dauke da hoton Safah da Marwah da angwayen nasu da aka bugo daga Ghana na taya murnar aure ta ce su kai wa matansu, da botikai cike da kayan gara su alkaki, nakiya, dubulan, cin-cin, bakilawa ta basu.
Duk da ranta bai son Zahraddeen da auren diyarta, amma ya ya za ta yi? Alhaji Aliko ya fi karfin gidansa. Zahraddeen ya riga ya zamo bangaren iyalin ta. Basu bar gidan ba sai bayan la’asar, motocin kayan gara suka mara musu baya.
Inna Binta na alwalar sallar magariba aka soma shigo mata da buhunhuna da katon-katon da bokitai tare da jarkokin mai iyakar ganinta.

Duk fadin tsakar gidansu cika ya yi taf, tun tana salati har ta yo lullubi ta fito tana ce da masu saukewa “Ina zan kai wadannan kayan? Ku barsu haka nan”.
Basu bari ba sai da suka gama saukewa tsaf sannan suka kada kan motocinsu suka tafi, ko tukuicinta basu tsaya karba ba.
Zahraddeen na shigowa ta soma fada ta ce, “Lallai yasa a maidawa Alh. Aliko wadannan buhunhunan ita ba ta da yadda za ta yi dasu, sai ka ce siyar musu da ‘yar ya yi?”
Zahraddeen shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi, don ya san halin Alhajin nasu, yanzu idan ya ce a mayar zai yiwa al’amarin wata fassara ta daban ne.
A nan ne yake gayawa Inna kyautar gidan da ya yi masa, da ya ce ba zai karba ranshi ne ya baci, kuma bai fasa kyautar da ya yin ba.
Har karfe sha biyun dare yana tare da mahaifiyarshi suna ta hirarsu irin ta da da mahaifi. Sai da Rabi’a ta shigo za ta kwanta ne Inna ta ce ya tafi haka dare ya yi, ita ma barci take ji.
Sannan ne ya yi mata sallama ya tafi. Ya yi amfani da makullanshi ya bude kofar glass (sliding- door) ta falon sassanshi ya shiga falon.

Babu kowa babu motsin komai sai hucin split wadda ta ni’imta falon sosai kamar babu wani mahaluki a cikin sassan saboda yadda falon ya yi shiru. Ya shiga wara idanu a hankali yana kallon yadda aka tsara falon kamar kana falon Alh. Aliko sabida tsari ba tarkace ba.
Dakinshi ya nufa kai tsaye ya sunce ya shiga toilet ya sakarwa kanshi shower na ruwa mai sanyi. Ya fito yana tsane kai da karamin tawul yayin da babban ke daure a kugun shi.
Ya dubi kanshi cikin madubi, ya yarda cewa shi namiji ne mai surar MAZA irin wadanda basu da yawa a cikin al’umma. Kamar yadda Kutama ya fada.
Ga koshin lafiya da kuzari, sannan da dakakkiyar zuciya. Kwakwalwar da kullum a shirye take da daukar duk abinda aka koyar da ita. Idan har yana da wadannan ilhamomin, mai zai hana ya ci gaba da yunkurin neman ilimi da fafutukar rayuwa? He has to applaud the idea that, Indibidual is an actor seeking for goal……
(and these goals are endless/limitless) wato basu da karshe.
In haka ne mai zai sa ya zauna diya mace na yi mishi kallon raini saboda kawai yana ma’aikacin Babanta? Namijin da ya san ciwon kansa, ba mace ce kawai a gabanshi ba, bai dauketa a matsayin jigon rayuwa ba, sai dai wani bangare na rayuwar namiji, wanda amfanin nata bangaren bai zuwa ma sai ana cikin kwanciyar hankali (when the goals are achiebed).

Ba ta san cewa shima ba sonta yake yi ba, ya aure ta ne kawai don ya darajja kaunar mahaifinta gareshi? Gaskiya ne da ‘yan magana ke cewa ‘Allah daya gari bam-bam’, kuma ‘kowa da halinsa’, sannan ‘kama da wane bata wane’ halinta ba daya bane da na ‘yar’uwarta ba! Ta kowanne bangare basu yi tarayyah ba, to ya zaiyi? Sai hakuri da kaddara. Domin cikar imani.
Har ya yi shirin kwanciya ya yi light off ya tuna cewa duk rashin mutuncinta hakkinsa ne ya dinga bincikar lafiyar ta.
Ya ja dogon tsaki ya safko daga lallausar gadonshi ya zura ‘bed shoe’ ya zura farar jallabiyyarsa, ya murda kofa ya fito ya nufi dakin nata.
Sallama ya yi tare da murda kofar ya shiga. Dakin duhu didim, sai dai hasken fitilar barci koriya. Ya dauka zai samu ta yi barci a makeken gadon ta, sai ya samu akasin abin da ya yi zato.

Tana bisa darduma daga can kuryar dakin ta yi nisa cikin sujjadarta, cikin yalwataccen hijabin sallah. Ya rufe kofar ya koma ya jingina da kofar a hankali, idanunshi a runtse.
Sai kuma ya bude ya dubi kulolin dake gefensa wadanda ya san na Inna ne. Na rana ya tadda na safe, na dare ya tadda na rana.
Ya sunkuya yana bubbudewa yana haskawa da wayarshi, ko cokali daya ba a diba ba, wanda ke nufin, har zuwa yanzun ba ta sa komai a cikinta ba, saboda tana kyankyamin mahaifiyarshi.
Da kanshi ya kwashe filas-filas din ya kai kicin. Ya samu leda ya juye duk abincin. Ba zai so Inna ta gani ba don ranta za ya sosu.
Ya yankewa ranshi gobe zai yo mata cefanen, kada ta kashe kanta da yunwa a daura mishi jakar tsaba, kaji su bishi.
Dakinshi ya koma ya sauya riga. Ya dauki makullin mota ya fita.

‘Yahuza Soya Spot’ ya nufa ya sayo gasassun kaji biyu da robobin ‘fresh milk’ din ‘Oldenburger’ masu sanyi, ya zuba a gaban motar ya dawo gida.
Yadda ya barta haka ya dawo ya same ta, wato deep in sujjadah. Ya tambayi kansa me take roka ne haka? Bai yi zaton ‘ya’yan gata irin ta masu ji da kansu da takama da iyayensu suna da bukata ba”.
A gefen ta ya ajiye ledojin ya juya ya fita. Sai da ya koma daki duk haushin kansa ya kama shi. Me yasa ya sayo mata? Me yasa zai biye mata ta raina abincin gidan su? Wanda kuma hakan raini ne ga mahaifiyar shi karara. Nan zuciyar shi ta tunatar da shi cewa
“hakkin ka ne ka ciyar da ita, ba hakkin mahaifiyar ka bane ciyar da matar ka”.
Da wannan ya kwanta ya lumshe ido, yana kukkullawa yana kwakkwancewa, game da future din rayuwarshi ta gaba, da kuma matakan da zai dauka wajen daidaita sahun Marwah Aliko Dan Kasa, ta san wane ne talaka? Ba abin wulakantawa bane.
Kowa da ka gani a duniya ba wulakantacce bane duk yadda yake, saidai in shi ya wulakanta kansa. Cikin darajojin da Allah Ya yiwa dan adam, babu zancen kudi a cikinsu. Wulakantaccen dan adam shine wanda ya dogara da wani, ba da Allah ba. Wanda yake ganin in ba wannan dan adam din da ya dogara dashi ba, to bashi da madogara. (Allah Ka bamu wadatar zuci irinta Zahraddeen ameen, Takori)

Almustapha Zubair Dan Kasa (Imam), ke sharara gudu a kan titin da zai dawo da kai Kaduna daga garin Abuja, yana daidai ‘zuma rock’ cikin motarshi banguish tun farkon shigowarta, a wannan lokacin banguish bata zo Najeriya ba, zai iya kiran kansa mutum na farko, dake yawo a cikin ta a Abuja gabadaya.
Yana gab da shiga garin Minna wayar Mami ta shigo, ya yi amfani da hannun daman shi wajen amsa wayar yayin da yake tuki da na hagun cikin kwarewa da gwaninta.
Mami ta ce, “Ka taso ne?”
“Har na kusa isowa Minna Mami, nan da ‘two hours’ insha Allah zan iso”.
Ya kashe wayar tare da kara taka totur din motar sosai, gudu yake kamar zai tashi sama. (Tukin Mota), na daya daga cikin abubuwan da ke sanya shi nishadi. Har dai ace motar mai budadden sama ce.
Sanye yake da shadda coffee kala kanshi babu hula, wanda hakan ya bayyanar da tulin kwantacciyar sumar kanshi baka sidik mai santsi da sheki.
Yana jin kansa cikin wasu mutane kalilan masu sa’ar samun duk abinda suke so a rayuwa, tunda Allah Ya mallaka mishi abin da rai da zuciyarshi ke so, tsayin shekaru goma sha tara. At last, ya samu. Don haka ba shi da abin da zai ce da mahaliccin shi sai godiya, da neman dadin falalarsa da ni’imarsa.

Karfe shida da rabi ya shigo garin Gwamna, don haka kai tsaye alwala ya yi a harabar gidan ya wuce masallaci don samun jam’in maghariba.
Mami ta kwankwasa kofar dakin da ta ji an kulle da makulli, Safah ta zo ta bude, sanye take da ‘shirt’ da wando samfurin polo kalar ruwan zuma, ta matse gashin kanta daga tsakiya.
Mami sai ta ga ‘yarta ta kara kyau na ban mamaki. Ko da yake hasken amarci daban ne, ta yi murmushi ta ce, “Mene ne na sanya mukulli a kofar?”
Ta ce, “Haka nan”.
Mami ta sake yin murmushi, ta san don wanda ake kulle kofar. Tunda aka tafi kai Marwah Zaria tun shekaranjiya ko falo ba ta kara lekowa ba.
A dakinsu take hidimominta ta kulle kanta ba ta son yin mu’amala da kowa. Daga Mami har angon babu wanda ke shiga sabgarta, shi ba ya garin ma tun wayewar garin litinin ya wuce Abuja, inda yake fafutukar bisar ta da passport dinta da ya amsa wurin Mami.
Ta ce, “Fito maza ki tayani aiki, ai tunda Marwah ta tafi na san na yi rashin mai taimaka min a kichin”.
Ta yi rau-rau da ido kamar za ta yi kuka ta ce, “Kai Mami ni bana tayaki?”

Ta ce, “Da yaushe da yaushe kike taya nin? Kin ga bana son dogon turanci wuce muje”.
Haka tasa ta a gaba har kicin tana cewa, “In ban da Imam din wa zai iya zama dake? Ga kiwa ga son jiki, ga yawan kwanciya kamar mage, bakya um bakya um-um kamar wata jikakkiyar tsumma.
Ayi mace sai ka ce namiji, daga takarda sai biro? Ko huda-huda yana samun lokaci ya shiga cikin ‘yan’uwansa ya yi mu’amala mai dadi dasu.
In bakya hutar da idanuwanki in kin tsufa za ki samu matsala dasu kin ji na gaya miki”.
Ta rausayar da kai ta ce, “Nice zan tsufa Mami?”
Ta ce, “A’a, ba za ki tsufa ba tunda hurul-eeni ce?”
Ta yi smiling har wushiryarta da jerarrun hakoran suka fito. Ta taimakawa Mami suka hada abincin dare mai rai da motsi suka jera a dining, sauri take a gama ta gudu kada Imam ya zo ya same ta wanda take Allah-Allah ranar tafiyar shi ta zo ya bar gidan ta huta, don bata da masaniyar yaushe zai tafin.

Dan halak din kuma dan gatan Mamin sai ga shi ya shigo cikin takunshi na sassarfa ya shigo kicin din.
Daga bakin kofa ya tsaya yana kare mata kallo kamar bai san ta ba. Daga Mami har ita babu wanda ya san da shigowar sa, hirar su suke suna dariya.
Sai da ya kalle ta son ransa sannan ya yi gyaran murya ya ce, “Mami wane delicious ake shirya mana ne? Irin wannan ‘aroma’ haka tun daga bakin get?”
Tana murmushi ta ce, “Duk naka ne, na san ka tunda ka bar gida ba za ka tsaya ka ci wani kwakkwaran abinci ba sai shirme wanda baya rike hanji”.
Ya yi dariya kadan ya ce, “Mami kina sangarta ni, sai na tafi inda bani da gata in yi ta ragaita…..”
Ta ce, “Ga shi kuma Allah ya baka makiwaciyar mata, ya ya za a yi kenan?”
Ya kai duban shi ga sashen da take, idanunshi a sanyaye, ta hade fuska ta yi murtuk kamar hadari, kai ka ce tunda aka halicceta ba ta taba dariya ba sai hura hanci take.
Ya girgiza kai ya ce, “A haka zan yi maneji Mami, an ce “da babu…..”
Ta karasa mishi “…..Gara babu dadi!”.

Ita dai ba ta tanka musu ba, karewa ma ko inda yake ba ta kalla ba ta tsallake su za ta wuce. Muryarshi ta yi kasa so cool ya ce, “Kin gani ko Mami za ta tafi ta kulle kofa saboda ga dodonta ya zo….”
Ita ma Mamin ranta babu dadi, tausayin Imam take ji sosai. Ciwon kana so ba a sonka matukar ciwo ne da shi.
Ta ce, “To ya zan yi muku ne Almustapha? Ita taurin kai, kai kuma baka iya lallashi ba”.
Ya ce, “Wallahi Mami ba zan zauna ina lallasarta ba, ai sai ta raina ni”.
Ta yi dariya ta ce, “Ka daina cika baki IMAMU-ALMUSTAPHA, ranar rarrashin ba ta zo bane, amma tana nan tafe”.
Ya ce, “To Mami ke ki lallasar min ita man ko ‘yar hira ce ta bari mu yi kafin in tafi? Kin san halin rai……”
Mami ta katse shi da cewa, “Ni nake maka auren da zan je ina maka bambadanci? Tunda ka ce ba za ka yi ba, to ku yi ta zama a yadda kuke, ruwan ku.
Lafiya za ka je ka dawo insha Allahu, ka zo ka same mu cikin alheri da koshin lafiya kamar yadda ka barmu”.
Ya tayata da daukar warmers suka fito. Masallaci ya koma don yin sallar isha’i, inda ya tarar da Daddy suka yi sallar tare sannan suka shigo cikin gidan suka nufi tebir din cin abinci.
Daddy ya dago yana kallon su ya ce, “Wai ina Safah ne?”
Shahida ta ce, “Tana dakinsu”.
Ya ce, “Kirawo ta”.

Har ta yi shirin barci cikin wasu tausasan nighties bakake wuluk, tana tufke gashin kanta yadda zata ji dadin kwanciya. Shahida ta kwankwasa kofar, daga ciki ta ce, “Waye?”
“Idon matambayi ne”. Shahida tace a kufule.
Ta bude kofar tana dariya ta ce, “Ki zo Daddy ke kiran ki”.
Ta yafa mayafi ta bi bayanta tana kunkuni, ita an dame ta.
Shahida ta ce, “Ki ce ba za ki je ba mana short and simple….”
Ta tura baki ta ce, “To ban ce ba”.

Daddy ya bita da kallo har ta zauna a jikin Mami, gaba daya ta rame ta yi sanyi, tausayin ta ya kama shi.
Sai dai ta wani fannin ya fi jin tausayin Imam din da ya kallafa burin rayuwarshi da soyayyar shi a kanta tun haihuwarta. Ya rasa mene ne aibun dan shi da ta kasa son shi. Shi kuma ya rantse har bayan ransa ba zai ta da wannan aure ba.
Cikin kulawa ya ce, “Baki da lafiya ne?’
Ta girgiza kai, “Lafiya ta kalau”.
Daddy ya ce, “Gobe ne za ki koma makarantar?”
Ta daga mishi kai.
Ya ce, “Ki yi min magana mana, sai daga min kai kike kamar kadangaruwa…”
Ta ce, “Eh, amma ‘hostel’ zan koma, ba zan iya zama ni kadai a gidan ba”.
Ya dube ta yana kiyasi ya ce, “To mene ne fa’idar komawar taki tunda barin makarantar za ki yi gaba daya?”
Hawayen da take tattali suka kwace, tsoronta Allah, tsoronta kada ace ta bi Imam, ta ce, “Don Allah Daddy a barni in yi karatuna, na yi nisa kuma ina jin dadin sa….”
Ya ce, “To, mene ne abin kuka a nan? Kin san dai yanzu ba mu da iko dake sai yadda mijin ki ke so”.
Ya juya ga Imam wanda kanshi ke kan wayarshi yana danne-danne kamar bai jin su, ya ce, “Yaushe za ka tashi?”
Ba tareda ya dago daga abinda yake yi cikin wayar ba Ya ce,
“Gobe da asubah insha Allahu”.

Ya ce, “To in zai yiwu ka kara kwana daya don ku samu lokaci ku yi shawara a junanku”.
Ya ce, “Ni Daddy duk yadda ka yi daidai ne”.
Ya yi murmushi ya ce, “Saboda kana tsoron ta? To in gaya maka ba a sakarwa mace ragamar kanta, ka zama namijin duniya ma’abocin gwagwarmaya da rayuwa kala-kala. Kada ka bari soyayyar da ke zuciyarka tasa ka kasa tankwara iyalin ka.
Ku tashi ku je ku yi shawara a tsakanin ku abin da kuka yanke gobe ku sanar dani”.
Da haka taron ya tashi kowa ya nufi dakin sa. Sai dai har zuwa washegari babu wanda ya nemi dan’uwansa tsakanin Safah da Imam.
Ita taurin kai da rashin son duk wata alaka da za ta hada ta da Imam din. Sai ta hadu da wanda ya dame ta ya shanye wajen rashin son wargi da miskilanci.
Imam irin mazan nan ne da duk soyayyar da suke yiwa mace, ba za su lamunci ta raina su ba. Sannan bai taba barin ka gane ‘weakness’ dinsa akan soyayyah. Shi Imam ko yana matukar son abu, da wuya ka gane sabida rashin son raini ya ratsa. Sai a inda yasan za’a yi maraba dashi, da abinda zuciyarsa ta zo dashi ko ta ke kunshe dashi. Mami kadai yake iya gayawa cikinsa. Kamar ba ita ta haifi Safan ba.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *