Chapter 2: Chapter 2
Allah ne ya kawo Daddy zai wuce cikin gida
ya ganta a nan durkushe tana kuka, cikin mamaki da tashin hankali ya cira ta, ta mike yana tambaya “Lafiya? Me ya faru? Ina Imam din?”
Ya jero tambayoyin a jere don duk hankalinsa ya gama bashi cewa wani abu ne ya faru d a Imam din, don Mami ta gaya masa sun fita tare asibiti.
Safah ba baki sai kuka take tana jujjuya kai, kawai tayi kundumbalar mika mishi takardar dake hannunta. Bai bude ba tukunna ya sata a gaba suka shiga cikin gidan juwa na hajijiya da ita tana dafa bango yayi azamar riko hannunta barin jikin shi.
Mami na zaune a falo tana waya, shigowarsu haka yasa ta katse wayar, itama tambayar da ta yi shine “Lafiya? Ina Imam din?”
Dukkansu babu wanda ya bata amsa.
Daddy ya zauna kusa da Mamin, ya ciro medicated dinsa cikin brief case dinshi ya sanya, ko kadan zuciyarshi bata kawo mishi wani abu makamancin wannan ba, sannan ya soma warware dukunkunanniyar takardar ya soma karantawa.
Mami sai gani ta yi Daddy ya sulale kasa, kamin ta yunkura ta mike ya sume. Da gudu ita da Safah suka isa gareshi.
Safah hannuwa ta daga ta dora aka tana ihun a zo a taimake su. Da gudu Hajiya Maama da ma’aikatan gidan dake kusa suka shigo, kowa kokarin shafa masa ruwa yake har aka samu ya farfado.
Ya shiga bin kowa da kallo a hankali, kamin ya dire idanunshi a kanta, tana gefe sai kuka da makyarkyata take yi, kamar wadda aka sanya cikin sanyin kankara.
Ya maido idon shi ga Mami wadda kansa ke bisa cinyarta, sannan ya maida idon shi ga mahaifiyarshi wadda ke ta faman yi mishi firfita da mayafinta.
Tana cewa, “Ni Salamatu me ya faru ne Aliko?”
Duk sauran ma’aikatan suka fita, ya rage sai su hudu.
Ya mike da kyar ya zauna, ya dauki takarda ya bawa Mami ya ce ta karanta kowa ya ji.
Mami ta bude takarda ta karanto. Itama sai ta fashe da kuka.
Ta ce, “Haka kika zaba ko Safah? Haka kike so kuma ya yi miki. Ai shi kenan ki je ga duniyar nan ta ishi kowa riga da wando…..”
Hajiya Maama ta katseta, “A’a, Zainabu yi hakuri kada ki yi mata baki, ku yi hakuri gaba daya ayi tunanin hanyar gyara, dukkan su kuruciya ke diban su.
Shima Imam mene ne na saurin saki, ko me za ta yi masa ai yarinya ce….”
Mami cikin kuka ta ce, “wane gyara za’ayi cikin saki ukku? ‘Yar shekaru 19-20 ce yarinya? Allah kadai ya san irin rashin mutuncin da ta yi masa….amma ni na san Imam sarai…..haka kawai ko giyar wake ya sha ba zai yi wannan aika-aikar ba.
Ga gidan nan ki zo ki zauna, mu jera kafada ni da ke….idan na yiwa mijina kwalliya ki bini da ido….wannan ce dai rayuwar da kika zaba ko? To zauna mu yi ta. Allah Ya baki sa’a”.
Shi kuwa Daddy tunda ya farfado neman Imam yake yi a waya, amma gaba daya layukan shi a rufe suke. Alamar yana cikin jirgi.
Tana rabe a bayan kujera sai kuka take, Daddy ya mike ya wuce ta gabanta ba tare da ya dubi inda take ba, bai ce mata komai ba, ya bi matattakala zuwa dakin sa. Mami ta mike ta bi bayansa tana ta sharbe hawaye da majina da gefen mayafinta.
Hajiya Maama ta zuba mata dundu da iya karfinta ganin yadda take kikkifta ido na rashin madafa, tace, “Yar banza, mai munafukan idanu, kukan me kuma za ki yiwa mutane tunda burinki ya cika? To Zahraddeen din mijin ‘yar’uwarki za ki aura ko Ubanki? Bace min da gani tun ban yi miki Allah Ya isa ba….” Ta fada tana nuna mata hanya.
Sum-sum-sum Safah ta wuce ta nufi dakinta, ta kwanta a lallausar gadonta, amma yau sai ta ji kamar ta kwanta a kan kaya.
Wata irin nadama ta sauka a zuciyarta a sannu, filla-filla take tariyo majigin rayuwarta tun haihuwarta, da kaunar da Almustapha ya wanzar da rayuwarshi a nuna mata.
Shin mene ne ya shiga kanta ne da ya makantar da idanunta ga soyayyar dan’uwanta? Me Almustapha ya yi mata? Mene ne aibunsa? Me take nema a da namiji da babu a Imam? Zuciya ta gama zaluntar ta, ta kaita ta baro, da ta yi mata hudubar banza ta yi mata silar kubucewar mai kaunar ta da gaskiya, kaunar da ta tabbatar har duniya ta nade, ba za ta samu makwafinta ba, indai daga da namiji ne ba daga iyayenta ba.
Me yasa ta fi baiwa soyayyah muhimmanci fiye da kauna? LOBE is not the only thing we are to go for in marriage..…. There are other important aspects; sacrifice and debotion. (Abin nufi anan, bamu zo duniya don muyi auren soyayya kadai ba. Akwai wasu abubuwa da yawa da suka fita muhimmanci cikin aure, kauna da sadaukarwa)……
Ta yi tumus cikin nadamar da AL-AMEEN BELLO MAKARFI ya kira NADAMA MARA AMFANI. (Duba SIRADIN RAYUWA, littafin Takori na farko, tare suka fito, an sake buga shi a karo na biyu ga wadanda basu karanta ba)
Ga shi ta bata goma daya bata gyaru ba. Ta yi asarar mijin kwarai irin ALMUSTAPHA ZUBAIR DAN-KASA. Bata ga tsuntsu bata ga tarko.
Ta bata da iyayenta da Kakarta da ke tattalin ta da so da kauna, amma ‘yar kankanuwar biyayya ta kasa yi musu a rayuwa sabida soyayya. Wace rana haihuwarta tayi wa iyayenta, tunda basu isa su zaba mata abinda suke ganin shine alkhairi a gareta ba. Ta sanya su cikin baki-ciki da takaicin da watakila har su mutu, bazasu yafe mata ba. Idan ba Imam ne ya dawo garesu ba.
Mene ne makomar rayuwarta a halin yanzu? Wa za ta aura? Ko zama za ta yi ta yi a gida gaban iyayenta tana sa musu ido kamar yadda Mami ke cewa?
Rashin sanin hakikanin wadannan amsoshin ya sanya ta rushewa da kuka mai cin rai, kuma mai cakude da NADAMA MARA AMFANI….
****
cikin kwanakin da suka biyo baya, rayuwa ta yi zafi ga Safah, wata irin rayuwa take agidan Ubanta tamkar ta wadda aka saki uwarta aka bawa kishiyar uwa mara mutunci rikonta. Mami ta daina kula ta, ta daina shiga sabgarta.
Ba’ a maganar Daddy, wanda ko inda take ba ya kallo, da ya kalleta gara ya ga bakin kumurci, da yana da karfin zuciyarma da korarta zaiyi daga gidansa taje ma duk inda zata, amma zuciyar iyaye data muslunci ta rinjayi komi.
Har zuwa yau din kuma bai taba ce mata komai akan al’amarin ba, hankalinsa ya tafi ga binciken inda Imam ya shiga a fadin duniyar nan, domin an tabbatar masa bai bi jirgin da yayi booking ba zuwa Glassgow, wani daban ya hau, wanda ba’a tantance na ko’ina ne ba a nahiyar Birtaniya, har assistant dinsa Mr. Kalakari mutumin India na waya yana tambayar Daddyn dalilin rashin isowarsa a washegarin ranar daya je daukoshi a filin jirgi..
Duk wannan tarairayar da Daddy yake yi mata ada ya daina, ido kawai yake binta da shi idan ta zube agabanshi wai tana gaisheshi.
Wajen Hajiya Maama kadai take samun sanyi wani lokacin, duk da kullum itama ta tuno Imam sai ta zage ta. Ta kukkunduma mata ashariya, ta kai mata hauri ta kai mata duka da mangara, sai kuma ta koma kuka tace
“annamimiya, wallahi kin yi asara, kuma sai kin nemo min Almustapha”. Tayi ta kuka.
Duk kokarin Daddy na neman layukan Imam ya kasa samun shi, don haka ya soma shirin tafiya Glasgow ya gani da idonsa da gaske Imam bai koma bakin aikinsa ba, don watakila sun hada baki ne da Mr. Kalakari ya bugo ya nemeshin don Daddyn ya debe tsammanin kasancewarsa a can, in ba haka ba ina Kalakarin ya samu lambar wayarsa? Shirinsa yake ba tare da ya gayawa kowa ba. Saidai kuma ya samu tsaikon tafiyar sakamakon tsohon pasport dinsa da ya nema ya rasa cikin takardunsa.
Mami na zaune a gefen gadonta tana sauraron muryar Ahmad Sulayman cikin Suratul-Tagabun daga cikin wayarta, ta idar da sallar la’asar kenan, a lokacin ma tunanin Imam take, da halin da yake ciki. Jikinta na bata amatsayinta na UWA, Imam baya cikin kwanciyar hankali, yana cikin wani hali da yake bukatar mai kaunarsa akusa dashi ya rage masa maraicin da baiyi a kuruciyarsa ba sai a girmansa, tasa gefen hijabinta tana tsane kwallar idonta, ta yi sallama dakinta ta amsa ciki-ciki. Tunda amsa sallama ya zama wajibi ga musulmi, da bazata amsa ba.
Ta samu gefen kafafunta ta zauna, ta dora kanta a cinyoyin Mamin tana rero kuka a hankali. Mamin bata katseta ba bata rarrasheta ba saida tayi iyakacin wanda take ganin zata iya ta samu sassaucin zuciyarta sannan cikin rishin kuka ta ce,
“Don Allah Mami ku yi hakuri ku yafe min, na yi nadama na gane na yi kuskure wanda bazan iya repenting ba, wallahi sharrin zuciya da sharrin shaidan ne.
Ban taba zaton ‘yar maganar da na gaya mishi zai sa shi furta saki ba. Ko kadan ban kawo haka ba, sakin ma har guda uku? Mami idan kowa ya juya min baya na jure, ba zan iya jure naki fushin ba, domin dafi ne mai barazana ga rayuwata”. Ta ci gaba da kuka.
Mami ba ta katse ta ba sai da ta yi mai isar ta. Abinki da da da mahaifi, a hankali ta ji zuciyarta na yin sanyi. Abinda take so ta ji, bazai yiwu ba idan bata saurareta ba.
Daga can karkashin zuciyarta ta ce,
“Ni me kika yi min Safah? Amma saboda Allah ki gaya min abin da kika yiwa Imam har ta kai ga saki? Saki ukku?? Wanda bazai gyaru ba, wanda Allah baya so???”
Ba ta iya karya ba, ta gaya mata dalla-dalla. Mami ta yi shiru tana nazari, ta ce, “Ai shi kenan, tunda hakan kike so…….” Sai hawaye sharrr! Data yi tunanin watakila sakamakon hakan Imam zuciyarshi ta buga ya mutu ne, ko ya haukace.
Hankalin Safah ya kara tashi, yau ga mahaifiyarta na kuka saboda bakin cikin ta. Ta ci gaba da rokon Mami ta yi hakuri, amma Mami kuka take haikan tun daga karkashin zuciyarta. Sai da ta share hawayenta da tafukanta ta ce.
“Haka Allah Ya so, na kuma yarda da kaddara, idan Allah Ya rubuta ke ba matar Imam ba ce a duniya yaya zan yi? Halin da yake ciki, a ina yake? Shine abinda ke damuna.
Ki tattara ki koma makaranta, don in ina ganin ki cikin gidan nan ba zan rabu da bakin ciki ba. Wanda zai iya zamowa barazana ga lafiya ta”.
Cikin kuka ta ce,
“Mami baki yafe min ba kenan?
“A’a, na yafe miki, Allah Ya yafe mana baki daya. Ki je ki nemi afuwar Daddy shi kika batawa ba ni ba. Cikin sha’aninki yanzu kam ni ‘yar kallo ce”.
Jikinta babu kwari ta taso ta fito daga dakin Mamin ta nufi sama sassan Daddy.
Kishingide yake da jaridar New Nigeria da medicated glass dinshi yana dubawa, ta yi sallama ya amsa ba tare da ya dubi hanyar da ta bullo ba.
Ta isa gabanshi ta kwantar da kai a kan kafafun shi tana kuka tana rokon shi da kalaman da ta roko Mami.
Shiru ya yi mata kamar ba da shi take ba. Da ya gaji da kukan ta ya ce, “Me kike so in ce miki Safah? Kin nuna min ban isa dake ba, na yi hukunci kin tozarta ni, na ce ga abinda nake so sabida kyautatuwar rayuwarku gabadaya ko bayan raina kin ce bakya so.
To ya bi umarnin ki ya rabu dake ba sai ki yi abin da kika ga dama ba?”
Ta ce, “Don Allah Daddy ka yi hakuri, na yarda na yi kuskure na yi nadama”.
Ya yi murmushi ya ce, “Nadama ko? Tukunna ma. Yanzu me kika yankewa rayuwar ki?”
Ta ce, “Makaranta zan koma gobe in Allah Ya kaimu”.
Ya sa ido yana kallon ta ya ce, “Aure kuma fa?”
Ta sunkuyar da kai ta ce, “Zan yi Daddy in Allah Ya kawo mijin”. Ya kyabe baki.
Ya ce, “Tashi ki je ki yi shirin tafiyar”.
Ya janyo brief case ya rubuta mata chekue din kudi masu yawa, ta karba ta yi godiya ta fito.
Safah na tuki a kan titin da zai kaita Zaria daga Kaduna, cikin kankanuwar motarnan kia-optima, wadda Zahradden ne ya zabar musu ita. Ba yadda Mami bata yi da Daddy a kan direba ya kaita, amma ya ce shi ya daina sangarta ‘ya’ya, motar ma daya barta ta dauka zai tura a dawo masa da ita. Ta shiga Adaidaita sahu ya daidaita mata sahu.
Yanzu zata san yaya dalibai suke neman ilmi a jami’a, a tsaye ba’a kwance ba irin wanda suka samu, ta shiga cikin hostel ta zauna tayi rayuwa daidai da dan kowa, a kyale ta ta fara koyon darasin rayuwa. Domin batasan Annabi ya faku ba”.
Gudu take sosai hawaye na sauka a kan kuncinta. Ta kan kalli gefenta mazaunin Marwah ne. Da tana cikin motar da yanzu ta kunna c.d na wakar India kabhi khushi kabhie gham, tana bin wakar tana rawa da daga inda take zaune. Allah sarki! Tuna Baya Shine Roko.
Wai yanzu ita da Marwah suna duniya daya, amma muhalli daban-daban saidai a ga juna da shauki lokaci-zuwa lokaci. Wani irin nutsatstsen al’amari game da IMAM na sauka a zuciyarta, wani irin ni’imtaccen feeling ne da ba za ta iya fassarawa ba.
Allah ne kadai ya kawo ta Zaria lafiya, cikin kiyayewarsa da alfarmarsa, amma fa ta sha zagi daga motocin gabanta da bayan ta.
Ba ta sha wahalar samun daki a hostel ba da taimakon wata ‘yar ajinsu Jamila Sarki. Su biyu ne a dakin ita da Jamila.
Ita Jamila ‘yar Kano ce, tana da aure amma ba ta haihu ba. Mijinta Mus’abu ma’aikacin M.T.N ne yana reshen Bauchi, ita kuma take karatu a nan Zaria.
Duk gayun Jamila sai ta ke raina kanta a duk lokacin da ta daga ido ta dubi Safah Dan-Kasa, ita ba ‘yar gayun bace (ba mai sa kyale-kyale ba), non-transparent (ba mai daukar ido ba), asali ma sai ka kura ido sosai sannan zakaga kyawun bakar fatar data mallaka da nata salon gayun na halitta, komai nata natural babu kari da na kanti ko daya, daga fata, gashi, kyawun sura duka Safah ta mallake su amma in an extraordinary manner.
Haka kawai Safah take burge Jamila, gata yarinya danya sharaf, don Jamila ta girme ta da wajen shekaru biyar. Sannan gata kwaruwa a fannin karatu, sam ba ta wasa oberall ce, abinda ya kawota kawai ta sanya a gaba.
Sai dai a dan zaman da suka yi na tsayin lokaci Jamila ta fahimci Safah Dan Kasa na cikin matsananciyar damuwa da ba ta san ko ta mece ce ba.
Tana so ta tambayi Safah abinda ke damun ta take yawan zama shiru silent sannan isolated, wato ta kebance kanta daga son shiga jama’a.
Ta rufe wayoyinta gaba daya ba ta amsa wayar kowa. Tun fil azal kuma dama bata cikin kowanne ‘social network’. Wayar ma data dan rike na dan lokaci soyayyace ta rinjayeta, ita kuma tayi biyayya a gareta. To tunda ta zama tarihi suma wayoyin su zama tarihi kawai. Sai dai kuma Jamila ba ta so ta zamo mai shisshigi cikin abinda bai shafe ta ba.
Don haka ta kawo ido ta zuba mata, cikin zuciyarta tana taya ta da addu’ar Allah Ya yaye mata duk irin matsalar da take ciki, sabida ita tsakanin ta da Allah take kaunar Safahn, ga Safahn kuma bata damu da kowa ba sai abinda ya kaita.
Saidai duk wani hakkin Jamilah dake kanta na makwabci mafi kusanci tana saukeshi. Lokacin a zauna ayi hira ne ko jin tarihin juna da ire-iren hakan bata dashi.
A zahiri damuwar itace, Safah ta fada wani hali na soyayya wanda ita kanta ba ta san cewa soyayyar ce ke dawainiya da zuciyarta ba, soyayyar tsohon mijinta dan uwanta Imam, wanda a halin yanzu ba ta san a halin da yake ciki ba, ba ta san inda yake ba. Yana raye ko baya raye?
Wani zubin kwana take tana kukan nadama ba tare da sanin Jamila ba. Tana ganin ta gama kashewa kanta rayuwa tunda ta rasa shi.
Soyayyarshi a zuciyarta a kullum kara karuwa take, kamar ana iza wuta. Kamar azal. A lokacin da ya riga ya zama haramiyar ta. Tunda daman babu iddarshi a kanta, kuma tuni lokaci ya mika.
Kuka take sosai a duk ranar da ta tuno rabuwarsu ta karshe…… “Na tabbata dan halak, ba shege bane ko….?”
Sautin da ke ta yi mata kuwwa a kunne kenan, a duk lokacin da ta zauna ita kadai, wanda ke kara ruruta wutar nadamar ta. Ita da bakinta tace da Imam idan shi dan halak ne cikin UWA da UBA ….to ya saketa….gashi ya sake tan kamar yadda ta bukata, to amma sakin ya zamar mata jafa’i….da dai wannan halin da ta tsinci zuciyarta da ruhinta a ciki na bege…. da so da kaunar ma gabadaya…… Harshe?
Ya Allah ka bamu linzamin shi a hannun mu, yana kaimu wuta, yana kaimu sa’ira, yana kuma kai mu Aljannah. Again, yana lalata mana rayuwa, mu dinga rikeshi ta hanyar tauna Magana kafin mu fade ta. Idan ya furta baya taba mayarda ita komai dadinta ko dacinta.
Harshe (da Hausa), tongue (da turanci), Lisan (da larabci). Wata tsoka ce mai amfani daban-daban da Allah Ya halitta a cikin bakinmu, wadda in muka iya controlling dinta, zamu iya controlling dukkannin al’amuran rayuwar mu.Ta kan ce,
“Ina ma ana maida hannun agogo baya?”
Me za ta yi ta yi repenting kuskuren da ta tafka a baya? Babu! Imam, foreber and eber (har Abadan) ya zama haramiyar ta. Ko da ace watarana ya dawo daga inda ya shiga. Domin dai ita kyakkyawan zaton yana lafiya take masa ba kamar Mami ba, kawai dai yayi hijira ne don ya raba duniyarsa da tata.
Ta tabbatar ba za ta kara samun soyayyar sa ba. Bazata kara samun damar da ta samu har tsayin shekaru ashirin ba. Kenan ya zama dole ta yi hakuri, ta fuskanci rayuwarta ta gaba, ta baiwa mazan dake rububin ta damar fitowa, mafi yawa daga ciki farfesoshinsu da manyan Dactocinsu, wadanda yawanci hazakarta ce take sayo mata soyayyar, kamewa da kamalarta, ba kamar sauran dalibai ‘yan uwanta ba, da yake a dan tsukin aka tura su TH, wato ‘teaching hospital’ suna koyar ayyuka a aikace, gara tayi maneji da dayansu duk da dukkannin su masu iyali ne.
To amma wa zata zaba wanda zai maye gurbin Imam a zuciyarta? Wa za ta samu ya so ta kamar yadda Imam ya so ta? Yaya za ta yi da dimbin soyayyar shi da a yanzu take dawainiya da zuciyarta???
***
Tana kicin tana gashin pizzawarma da french bread da take so za ta yi kalaci da shi, ta jiyo sallamar Rabi’a a bakin kofar shigowa sassanta.
Ta yi tsaki tsuww! Tana kunkuni, “Yaushe wadannan mutanen za su daina shiga sabgata ne? In abinci ne na ce bana cin jagwalgwalo a kyale ni mana?”.
A fusace ta fito ta bude kofar, Rabi’a ce dauke da food flasks guda biyu, ta raba ta gefen ta don ta shiga ta ajiye mata tunda bata bata hanya ba, ta yi mata wani banzan kallo ta ce.
“Ke, koma da abincin nan a koshe nake”.
Jiki babu laka Rabi’a ta fasa shiga ta juya, ta rufo kofarta ji kake garam! Har sai da Rabi’a ta tsorata. Ta karta a guje.
Ta maida flasks din kicin ta ajiye. Inna Binta dake kofar kicin din ta ce, “Ya kika dawo da shi? Ko bata tashi ba?”
A kufule Rabi’a ta ce,
“Inna ki yiwa Allah ki daina sa sanwa da matar nan, ba ci take ba asara ake, kullum sai dai in zubar yadda na kai mata haka nake daukowa.
Yau kuma kwata-kwata cewa ta yi in komo da shi ta koshi”.
Inna ta ce, “Ke kam kin fiya daukar zafi a kan abinda bai kai ya kawo ba, don ta ki ci ba cikinta ba? Hakkina ne in ba ta a matsayinta na diyata kuma makociya mafi kusanci dani”.
Haushi ya kashe Rabi’a ta ce,
“Inna ita ba ta dauke ki a matsayin Uwa ba, tunda ta zo gidan nan yau sati biyar ta taba zuwa inda kike ta gaishe ki?
Ni ban taba ganin inda ake haka ba, kawai an kwaso mana wadda ta fi karfinmu kuma ta raina mu, ko ‘yar Karuna ce ai sai haka.
Ni wallahi ba zan dauki raini ba, ba zan kuma zuwa kai mata abinci ba tana yi min kallon biyu-a-hu. Sai dai ki aika Nura amma ni wallahi ba zan kara zuwa dakinta ba”.
Inna ta yi murmushi tana danne nata bacin ran ta ce, “Bana son rashin arziki, ba gaba take dake ba? Ko ba matar Yayanki ba ce? Abinci ba zan fasa bata ba, ko ta zubar ko ta ci babu ruwan ki”.
Sallamar Zahraddeen ta katse su. Ya hade cikin bakaken suit kai ka ce bakin Ba-Amurke ne, inda duk ya gifta lallausan kamshin Dior-Addict ke tashi.
Inna ta daga kai a hankali tana kallon sa, cikin sati biyar da yin bikinsa ya rame kwarai. Kowanne ango yana yin kiba harda teba ya yi kyau bayan bikinsa, amma banda Zahraddeeninta. Wanda wuyansa ya koma uwa marikin lema, idanuwa wadanda dama a lumshe suke, suke kara shigewa ciki.
Ya samu kujera ‘yar tsugunne ya zauna yana murmushi ya ce, “Inna kun tashi lafiya?”
A sanyaye ta amsa “Lafiya kalau Deeni, ya ya amarya?”
Ya yarfar da hannu, ya dan juyar da kai ya ce, “Lafiyarta kalau”.
Duk sai suka yi shiru kowanne da abinda ke cikin ransa, amma kowanne baya so ya furta. Ba ya kuma son dan uwansa ya gane yana cikin damuwa.
A karshe Zahraddeen ya ce, “Inna ko zan samu kalaci? Kaduna zan wuce yanzun nan”.
Ta ce, “Ina matarka da kullum za ka zo ka ce in baka abinci?”
Ya rausayar da kai ya ce, “Naki nake so Inna, babu inda zan ci abinci in ji na gamsu Inna sai naki”.
Ta yi murmushi ta jawo kulolin da Rabi’a ta dawo dasu ta tura masa, yana cin funkason alkama da miyar alayyahun data ji kaji zukuzuku suna hira.
Cikin hirar yake tambayar Inna
“Wai Inna ina wannan Yayar taki ta rugar Ardo Lamido?’
Ta ce, “Yaya Badijo? Tana nan lafiya, sai dai fushi take dani don na kwan biyu ban je ba. Amma insha Allahu karshen watan nan zan yi kokari na je. Nura nake jira ya samu hutu don shikadai zai iya shiga wannan jejin mai kayoyi da kwazazzabo da mota ba tareda yayimin korafi ba.
Bikin ka ma ban samu na aika mata ba saboda yadda abin ya zo a kurace, laifi kan laifi kam na yiwa Yaya Badijo, sai dai ta dubi Allah ta dubi zumunci ta yafe mini.
To abu ne irin na jeji ko irin wayar zamanin nan basu da ita balle a samu saukin sadarwa. Sannan babu yadda ban yi da ita ba kan ta dawo nan mu zauna tare bayan rasuwar maigidanta ta ki. Ita ba da ba sai ‘yar jikallen ta Anisa wadda danta Iro ya mutu ya bar mata”.
Ya ce, “Ita ce wadda kike gaya min kin sa ta makarantar su Rabi’a?”



