⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 3: Chapter 3

Inna ta ce, “Ita ce, yanzu ajinta uku kenan a karamar sakandire, tare suke da Rabi’an, abinda yasa baka ganinta nan in sunyi hutu can ruga take komawa ta yi hutun ta. Ko tazo min nan ana I gobe zata koma ne, yawanci kuma baka nan kana Kaduna.
Amma gashi tun ba’a je ko’ina ba Yaya Badijo ta fara fadan karatun ya isa haka aure take so ayi mata, wai ta samu miji a can rugar su.

Ita kuma yarinyar bata so tafi son ta yi karatu, sai dai kwakwalwarta bata ja, gashi tana son karatun kamar me, amma Allah bai bata kwakwalwa ba.
Rabi’a ta ce ita ke daukar na karshe a ajinsu, sai dai hakan baya damuna don tun farko ba a dora ta akan turbar karatun ba, banda ma n adage na kafe aid a ko firamare bazata bar tat a je ba, sai kiwo da tatsar nono”.
Zahraddeen ya yi dariya ya ce, “Duk sanda za ki Inna ki yi min magana zan kai ki nima in sada zumunci, bazan taba mancewa da kaunar da Badijo ta nuna min ina yaro ba, ita ta yaye ni, a wajenta nayi jinyar shayi (kaciya)”. Inna tayi dariya tace “ashe baka manta ba”.
Ya mike ya zuba hannun shi cikin aljihu ya zaro mukullin motarshi ya nufi hanyar fita yana cewa, “Ni na yi nan Inna, Kaduna za ni hutun da Alhaji ya diba min ya cika, yau zan koma ofis ayi mana addu’a”.
Inna ta ce, “Addu’a kullum ina yi maka Dini, Allah Ya ji kan mahaifinka, ya baka ‘ya’yan da za su share ma hawaye kamar yadda kake share min. Ya kare min kai daga sharrin makiya da mahassada, ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya”.
Har ranshi ya ji dadin addu’ar Inna, ta wanke bacin ran da ya kwana da shi. Cikin sukuni yake tukinsa a kan titin da zai sada shi da garin Kaduna.

Isarsa ofis ya tadda jibgin ayyuka na jiransa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya. Sai da ya gama dukkan ayyukan shi sannan ya rubuta (resignation letter) wato takardar ajiye aiki da ‘Dan Kasa Holdings’ da hujjar tafiya karo karatu, ya tura ofishin Daddy.
Alh. Aliko ya dade yana juya takardar Zahraddeen a hannunsa, wadda sakatariyarshi ta shigo mai da ita. Wadda ta ciro yanzunnan a kwamfuta.
Kafin ya ce wani abu Zahraddeen ya yi sallama a ofishin cikin sallama, daga mishi kai kawai Daddy ya yi, amma ya kasa amsa sallamar shi.
Binsa kawai yake da kallo kamar yau ya fara ganinsa. Zahraddeen ya zauna ya sunkuyar da kai shima ranshi babu dadi.
Shiru ta ratsa a ofishin na tsayin mintuna biyu, sannan Zahraddeen ya yi ta maza ya gaida Daddy ya amsa, sannan ya sassauta mamakin sa ya ce.
“Da gaske kai ka aiko da wannan takardar?”
Cikin matsanancin ladabi ya ce, “Na’am Daddy ni na aiko da ita”.
Ya ce, “Kuma don za ka je karo karatu sai ka ajiye aikin gaba daya?”

Idanuwanshi na son zubo da hawaye yana kokarin maida su da karfin gaske, ba kuma na komai bane na ‘sabo’ ne da kaunar da yake yi ma Alh. Aliko, Uba mai cin tudu biyu a yanzu; siriki/ubangida.
Ya ce, “Hakan na ga zai fiye min kwanciyar hankali Daddy, ka yi hakuri kada ka kullace ni, ko ka yi min wata fahimta sabanin kyakkyawan kudirin dake zuciyata.
Daddy ban yi haka don raini ko don na bata maka rai ba, ko don ka yi min wani laifi ba, ina da sha’awar zurfafa karatuna ne kawai”.
Alh. Aliko sai ya yi murmushi don shi babba ne, tuni ya hasko abinda yasa Zahraddeen yin wannan zuciya.
Ba shakka ya fahimci rainashin da Marwah ta yi shine dalilinsa na yin hakan. Sai ya ji yaron ya kara burge shi, ya kara shiga ransa.
Ya ce, “Ina bayanka Zahraddeen, Allah Ya shige mana gaba. But I’ll miss u so much…..(zan yi kewarka da yawa). Ina za ka je karatun?”
Ya ce, “Ba wani waje bane, a nan ABU ne zan yi PhD dina tsayin shekaru uku, zan yi karatu ne full time shine dalilina na ajiye aikindon bana son in bata shekaru masu yawa wurin kammalawa”.
Daddy ya girgiza kai ya ce, “Ina yi maka fatan ALHERI, amma ba zan iya soke sunanka daga cikin ma’aikata na ba.
Duk ranar da ka gama karatun, ka ga kuma kana sha’awar ci gaba da aiki tare dani, to kofa a bude take. Yanzun dai zan baka (leabe without pay), hakan ya yi maka?”
Bashi da zabi banda ya daga mishi kai. Duk da ba haka yake so ba, so yake ya yi sallama kwata-kwata da aikin ‘Dan Kasa Holdings’ ya bude sabuwar rayuwa wadda babu raini a cikin ta.
Ya manta cewa babu wani aiki a gwamnatin ma da babu bin na gaba a duniya. Kafin mu hau sama, dole mu taka matattakala.
Daddy ya bude jakarshi ya fiddo chekue ya yi rubutu na minti guda ya tura mishi. Ya kuma kara da cewa.

“Duk sanda kake neman wata shawara kan wani al’amarinka ka neme ni, haka duk wata matsala da ta shafi karatun ma.
Game da iyalinka kuwa Zahraddeen sai in ce ka kara hakuri, watarana sai labari. Sannan komai na duniya mai canjawa ne, musamman al’amarin yara mata, wanda kuruciya ta yi yawa a cikinsa. Kana da ra’ayin Marwah ta koma makaranta ko baka ra’ayi?”
Ya dago ya dubi Daddy hawaye taf a idanun shi, hawaye ne na kauna, sabo da kewa. Domin ji yake kamar zai kara rabuwa da mahaifinshi ne a karo na biyu.
Kaunar dake tsakaninshi da Alh. Aliko kauna ce tabbatacciya daga Allah!.
Shima Daddy kokarin mai da nashi hawayen yake yi cikin dabara, don baya son Zahraddeen ya ga karyewar zuciyarshi.
Ya soma kalubalantar kanshi da auren diyarshi da ya lakabawa Zahraddeen ba da son ranshi ba. Sai don nashi amfanin.
A yanzu kam yana nadamar hada wannan auren, wanda babu so da kauna ko yaya daga kowanne bangare, duk shi ya jawo wannan, shi ya jawo a yau Zahraddeen ya zabi ya barshi don ya tsira da martabar sa a idon diyarsa da ‘society in general…….’
“Yaya zan aure ta tana karatun ta sannan in hana ta Daddy?” Muryar Zahraddeen dake sassarfa da karkarwa ta katse shi daga tunaninsa.
Daddy ya ce, “Shi kenan Zahraddeen Allah Ya yi jagora”.
Hannu biyu yasa ya karbi chekue din ya yi godiya ya mike ya doshi kofar fita.

“Zahraddeen”. Daddy ya kara kiransa.
Ya juyo ya dawo, sai kuma tari ya sarke shi, ya yi ta tari ba kakkautawa.
Da sauri Zahraddeen ya bude dan karamin firjin dake gefe ya dauko gorar ruwan Ragolis ya cika tambulan ya mika masa, amma ya kasa karba, tari yake ba kakkautawa kamar mai ‘tuberclosis’.
Gaba daya Zahraddeen ya rude ya rasa irin taimakon da zai bawa Daddyn, sai ya tsuguna a gabansa yana ta faman jera mishi sannu.
Da kyar tarin ya lafa, ya karbi ruwan ya sha, ya koma ya kwanta a kujerar shi. Har zuwa lokacin Zahraddeen bai daina yi mishi sannu ba.
Ya dafa mishi hannu sannan ya rufe takardun dake gabanshi ya tura su gefe ya mike.
Ya ce, “Muje ka sauke ni a gida, ba zan iya aikin ba, bana jin dadin jikina”.
Jikin Zahradden ya yi sanyi sosai, ya soma zargin kansa da rashin yiwa Alh. Aliko adalci. Mene laifinsa don yana kaunar ka? Ya dauki ‘yarshi da yake so ya baka ba don kwandalar ka ba, sai don kaunar da yake yi maka.
Amma a kan shirmen diya mace ka ce ka rabu da shi duk da yakinin da kake da shi na cewa ba shi da mai taimakonsa tamkar ka.
Ya soma girgiza kai da sauri ya ce, “Ka yi hakuri Daddy, na janye, wallahi na fasa tafiya karatun….baka yi min laifin komai ba Daddy…”

Hawaye suka balle a idanunsa. Daddy ya rungume shi ya ce, “A’a, Zahraddeen ina bayanka, ka koma karatun ka, ka kuma zabi duk yarinyar da kake so ka aura don Marwah ta shiga hankalinta. Yaran yanzu ne ka haife su amma halinsu a duniya suke daukar abinsu. Itama dayar abinda tayi min bazaka so ka ji ba, har gara ita wannan din inada kyakkyawan zato akanta tunda har ta yarda ta zauna zuwa wannan lokacin. Ko yau ta fito nasan na taba yi mata aure da miji nagari bani da wannan tambayar wajen Ubangiji. Tana bukatar lokaci kafin tasan menene rayuwa. Nayi kuskure babba wajen nunawa yarannan soyayya mai yawa”
“babu kuskure acikin tarbiyyar daka yi musu Daddy. Ka basu tarbiyyah wadda ta dace baka barsu kara zube ba. Ka sa ido akan addini da tarbiyyarsu ni shaida ne akan hakan. A ko’ina kuma suna nuna su jakadu ne na mahaifinsu. Lamarin bai kai yadda ka zace shi ba”. Zahraddeen ya fada cikin kokarinsa na Daddy ya kwantar da haankalinsa.
“Za ka yi min wannan alfamar dana nema din Zahraddeen ko ba za ka yi ba?”
Da sauri ya ce, “Zan yi maka Daddy, wallahi zan yi maka”.
Ya ce, “To na gode Zahraddeen muje gida, bana jin dadin jikina ko kadan”.
Mami na kicin a lokacin da suka shigo. Zahraddeen rike da Daddy, ya taimaka mishi ya kwanta cikin doguwar kujera.
Daidai lokacin da Mami ke fitowa ita da Shahida wadda ta sakko daga matattakalar bene.
Mami ta ce, “Subhanallahi, lafiya? Me ya samu Daddy Zahraddeen?’
Zahraddeen wanda ya fisu shiga tashin hankali ya ce, “Cewa ya yi baya jin dadin in kawo shi gida”.
Mami duk ta rikice, Alh. Aliko ya maida idanunshi ya rufe.

Mami ta soma kokarin kiran wayar Dr. Mathew da wayar hannunta, ta yi sa’a bugu daya ya dauka. Ta gaya mishi ya zo cikin gaggawa Daddy ba shi da lafiya.
Zahraddeen bai bar gidan ba sai bayan tafiyar Dr. Mathew, wanda ya yiwa Alhajin gwaje-gwaje, ya kuma yi mishi allurar barci.
Ya ce da Mami da Hajiya kada su damu, in ya farka barcin shi da safe insha Allahu zai warware, hawan jinin shi ne ya motsa.
Ya roke su su daina gayawa Alhajin duk abin da zai tayar mishi da hankali.
Zahraddeen ya dauki laifin duk ya dora a kansa, da ya san abin da zai faru kenan da ko kusa bai zo ya ce da shi zai barshi ba.
Don haka barcinshi a wannan daren kalilan ne. Da safe shine mutum na farko da ya danna musu kararrawa karfe takwas na safe.
Shahida ta bude suka gaisa, sannan ta bashi hanya ya wuce cikin falon.
A lokacin Daddyn ko farkawa bai yi ba. Mami na gefe ta zuba mishi ido ta rasa abin da ke mata dadi. Bai farka ba sai karfe tara na safe. Mami ta taimaka mishi ya yi wanka ya yi alwala ya gabatar da sallar asubahi da ta kubuce mishi, tare da jero istigfari.
Bayan ya yi sallama abin da ya fara ce da Mami shine, “Ina Zahraddeen? Ta kara gwada layin Imam ko za ta same shi”.
Cikin hanzari Mami take latsa wayar hannunta, kamar ko yaushe kwamfuta ta sanar da ita an daina amfani da wannan layin.
Ta kira ta Zahraddeen nan ya ce da ita ai yana cikin gidan. Ta ce to ya karaso Daddy na kiransa.

Hajiya Mama da Shahida duk tare suka shigo da Zahraddeen. Ya durkusa ya gurfana gaban Alhajin, shi kuma ya kama hannun shi ya rike tamau ya ce.
“Zahraddeen na san ban kyauta maka ba da na baka auren diyata alhalin dukkanku bakwa so…”
“Ka daina cewa haka Daddy, har abada jininka ya fi karfin rashin so a gare ni. Marwah kanwa ta ce ko da bata sona, ban taba tunanin akwai wata rana da za ta zo in ji bana kaunar ta ba, ko da kuwa ita bata son nawa.
Aure da jininka Daddy yanzu na fara har ranar da na daina numfashi”. (Har abada hoton wannan ranar ba zai gushe daga zuciyoyin su ba).
Daddy ya yi murmushi ya ce, “To na gode Zahraddeen, ina kuma shi wancan alkawarin da ka yi min?”
A nutse ya ce, “Wane alkawari ne Daddy? Wallahi na manta”.
Ya ce, “Alkawarin da ka yi min jiya na alfarmar da na nema cewa ka yi aure na soyayya da duk yarinyar da kake so?”
Ya ce, “Na tuno Daddy, amma ka yi mana afuwa ba yanzu ba, sai lokacin da Allah Ya nufa, wato lokacin da na samu wadda zuciyar tawa ta kwanta da ita, in ka janye zancen ma Daddy zan fi yin farin ciki, Marwah zata so ni, jiki na na bani Daddy WATARANA na zuwa da zuciyoyinmu zasu hadu, cikin yardar wanda ya nufe mu da zama karkashin inuwar aure, bada jimawa ba. Insha Allahu!!!.”
“Ban janye ba, ba kuma zan janye ba”. Ya fadi a hankali. Hawayen da suka cika idon Zahradddeen suka gangaro, ya ce, “Na yi wannan alkawarin Daddy…”
Ya sake yin tari ya ce, “Sai alfarma ta biyu, kuma ta karshe.”

Gaban Zahraddeen in banda faduwa ba abinda yake, cike da tsoron wadannan alkawarirrika masu nauyi da Alh. Aliko ke sa shi yana yi. Ya ce, “Wace irin alfarma ce kuma Daddy?’
Ya ce, “Abin da baka so ne, nake son ka yi min. Ka yi min alfarmar kulawa iyalina da dukiyata bayan raina, ina nufin ‘Dan Kasa Holdings, Dan Kasa Inbestment, Dan Kasa Electronics, Dan Kasa……..duk suna cikin AMANAR KA”
Ya kasa karasawa saboda yadda tari da shakuwa suka taru suka sarke shi. Gaba daya falon kuka suke, in ka cire Hajia, kada Zahraddeen ya ji labari. Babu shakka kukan da Zahraddeen ke yi a yau bai taba yin irinsa a rayuwarsa ba.
Cikin karkarwar murya Hajiya Maama ta ce, “Aliko ka daina fidda rai da rayuwa saboda ciwo…..”
Ya dubi mahaifiyarshi yana murmushi, sannan ya ci gaba da tari, da ya lafa ya ce,
“Ban fidda rai da rayuwa ba Hajiya, (mutanen kirki Allah kan nuna musu karshen rayuwarsu. Takori ) na yarda rayuwa da mutuwa duk na Allah ne.
Wai hasashe nake, ko da ta Allah za ta kasance a gare ni. Na yafewa Safah da Marwah, ku gaya musu na yafe musu duniya da lahira.
Duk ranar da Allah ya juyo da Almustapha gida, ku roka min shi alfarmar ya yafewa Safah ko ma me tayi mishi, koda Allah bai kaddari aure a tsakaninsu ba, domin hakika ta yi nadama, ku gaya mishi na so in yi tattaki har can Glasgow in isar mishi da wannan sakon Allah Bai bani iko ba.
Hajiya ki yafe ni idan na taba yi miki ba dai-dai ba…”

Ta taso ta kama hannunshi, a lokacinne hawaye suka zubo a idonta.
Ta ce, “Na yafe ka Aliyu, na yafe maka. Na yafe maka…..Kai dan albarka ne, daidai da rana daya baka taba bata min ba, ban taba aje kara ka tsallake ba.
Allah Ya yi maka albarka, kuma Allah Ya baka lafiya….”
Mami ta kunshe fuska cikin mayafi sai kuka take. Don dai ita bata ga dalilin wadannan maganganun masu kama da wasiyya ba, ciwo ai ba mutuwa bane. Daddy ya juya gare ta zai yi magana shakuwar ta kara sarke shi.
Da kyar ya samu ya ce, “To mene ne abun kukan? Ke ma ki yafe ni Zainabu, tunda na yiwa ‘yarki aure ba tare da son ranki ba. Ki yarda dani gata na yi mata. Ba kowadanne mutane ne irin Zahraddeen ba!
Ba kowadanne mutane ne ke da irin nagartarshi ba, ba kowadanne mutane ne a wannan zamanin ke da irin kyakkyawar zuciyarshi da Amanar shi ba…”
Shakuwar ta kara sarke shi. Da sauri Mami ke kiran wayar Dr. Mathew, Hajiya Mama ta mike ta fita don ta samu ruwa ta yi mishi tawaida.
Ko kafin ta dawo shakuwar ta ci karfinsa, har gudu ake tsakanin Mami, Zahraddeen da Shahida don a kawowa Daddy ruwa, ko kamin su dawo rai bakon duniya ya yi halinsa.
****

Babu wanda bai zo da ruwan ba a cikin su, kuma daidai da isowar Dr. Mathew. Mami ta isa gare shi ta tallafo shi don ta ba shi ruwan ba tare da ta fahimci abin da ya faru ba.
Dr. Mathew ya karbi ruwan daga hannunta ya sa hannu ya rufe mishi kwayar idanunsa. Ya kwantar dashi a kasa. A lokacin ne duk suka gane abinda ya faru.
Ganin Dr. Mathew ya ja zanin gado ya rufe shi, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!…” Abinda Zahraddeen ke fada kenan yana kuka riris a kasa kamar karamin yaro.
Yayin da Dr. Mathew ke basu hakuri amma dukkansu kuka suke ba ji ba gani.
“Allah Ka ji kan MAZAN JIYA…..” Abinda Shahida ke fadi kenan a zuciyarta. Tana sharbe nata hawayen da habar zaninta.
****

Daruruwan jama’a ne suka halarci jana’izar tsohon Gwamnan, wadanda suka hada da ‘yan siyasa, ‘yan boko, talakawa da al’ummar garin Kaduna baki dayan ta.
Sai dai wanda bai samu jin sanarwa a kafafen yada labarai ba, kamar Safah da Marwah, wadanda basa sauraron rediyo ko talabijin.
Ita Marwah wayar ta babu caji, domin kwanansu biyu kenan basu da wutar NEPA, ga shi masu gidan (su Inna kenan) babu wanda ya damu da wata wutar NEPA, duk sun kunna fitilar kwai duk da cewa akwai inji cike taf da petir a gidan.
Ita kadai cikin duhu don bakar zuciya ta fi karfin ta ce da Nura ya tayar mata injin ko Rabi’a ta sayo mata kyandir.

Haka nan take kwance cikin bargo a lallausar gadonta da yake tana hutun sallah, haka nan take fama da faduwar gaba akai-akai, da rashin jin dadin zuciyarta. Tana tuna irin abubuwanda take yi a cikin gidannan wanda ba halinta bane ba, bana iyayenta ba, ba wani ya koya mata ba, shaidan ke ta koya mata launi-launi da nau’i-nau’I na rashin mutunci don a koreta. Amma bayin Allahnnan kamar basu san tana yi ba. Shin idan Mami ake yiwa abinda take yiwa uwar Zahraddeeen da kannensa yaya zata ji a zuciyarta?
Ko Rabi’a tayi fushi ta daina dosar flat din, idan taji ta kunna kira’a sai ta shigo ta zauna koda bazata kulata ba, sabida itadai bata da waya bata da radiyo kuma tanason kira’ar Khusairi da Marwahn ke sawa. Kasancewar da kira’ar warshu yake yi ba hafsu ba.
Malamansu na islamiyyah sun sha gaya musu kira’ar warshu itace kira’ar ‘yan aljannah. Rabi’ah hafiza ce tanada haddar hizfi arba’in akanta. Don haka duk inda ma’abocin sauraron Alkur’ani yake, Rabi’a abin so da girmamawa ne agareta.
Sai tace a ranta ita wannan dai rashin arzikin (rashin mutuncin) a fatar bakinta yake, ba’a zuciyar ta ba. Gata da sallah, goshinta ya nuna, kafafunta sun nuna, kuma kusan kullum ta shigo sallah take ko girki mai shegen kamshi irinna turawa. Wani abin dariya ma in Rabi’an na zaune ko bata kulata ba in tagama dafe-dafenta da gashe-gashenta sai ta zubo ta ajiye mata ta shige daki.
Wani lokacin ta ci kadan, in bakinta ya ki karba ta bar mata abinta. Idan nama ne sai ta nikashi, har bakin Rabi’a ya kasa tantance ko menene. Don haka ita wannan cakude-cakuden da ganyayyakin kayan lambu dana gongoni da Marwan ke ci ta aje mata agabanta bata iya cinsu, sai ta dauka ta mayar mata cikin firjinta.

Idan kuma taga dama sai tasa wakar India, nan ma Rabi’a na so. To haka a can dakin daliban Medicine na asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello, Safah Dan Kasa ke kwance da tulin takardu da litattafai a gabanta, amma ta kasa kammala thesis din da aka bata.
Wata irin kasala ce ta sauka a zuciyarta, sannan gabanta ya yanke ya fadi, ta kai hannu ta dafe kirjinta, hankalinta ta ji ya yo gida. A lokacin karfe hudu na yamma.
Ta aje biro ta mike a sanyaye, ta juya ta dubi Jamila wadda ke ta sharar barci a gadonta. Ta bar mata dan ‘note’ a saitin kanta inda take sanar da ita ta tafi Kaduna.
Gudu kawai take shararawa a kan titin da zai sada ta da garin Kaduna daga Zaria. Allah ne kawai ya kawo ta lafiya amma ba nutsuwar tuki ba.
Cincirindon mutane ta gani fal a layin su, wanda ya tabbatar mata lallai wani abu ya faru. Ga canopies (rumfuna) an saka, tun daga farkon layin har zuwa karshen sa.
Ko gurin da za ta yi parking babu, haka ta aje motar a farkon layin ta karaso da kafafunta. Domin daga baya da Daddy ya huce ya maida mata motar.
Cikar al’ummar dake cikin gidansu ya sanya ba za ta iya gane ko su wane ne ba, haka ta rika cira kafa idanunta a rufe ba tare da ta damu da kallon da jama’a ke binta da shi ba, ko inda take cilla kafartata.
A babban falonsu ta cimma Shahida ta ci kuka har ta gode Allah, Mami da Hajiya Maama na daga cikin daki cikin jama’a.
Ta kukkutsa ta shiga, ta fada jikin kakarta ta fara kukan itama, tana tambayar abinda ya faru.
Hajiya Maama ta ce,
“Ki yi hakuri Safah, Allah da Ya bamu Alhaji ya karbe shi…..”
Iyakar abin da ta ji kenan sai farfadowa ta yi ta ganta kwance a cinyar Mami tana kuka itama.

Gudu sosai Zahraddeen ke yi a kan hanyar Zaria, domin ya dauko Marwah, ta halarci makokin mahaifinta.
Zai iya kwatanta mutuwar Alh. Aliko da mutuwar mahaifinsa a zuciyarsa. Har zuwa wannan lokacin hawayensa basu bar ambaliya ba.
Karfe hudu na yamma a Zaria ta yi mishi, yadda ya shigowa Inna ta tabbatar ba lafiya ba, ba ta taba ganin Zahraddeen yana kuka ba tun tasowar shi.
Ta ambaci “Innalillahi…!” A zuciyarta.
Shi kuma ya zauna a gefenta yana zubar da hawaye. Inna ta soma nasiha tum ma bata ji makasudi ba, tana cewa,
“Duk abinda ya faru ga bawa mukaddari ne daga Allah, kuma Allah yana sane da shi, sai ake so bawa ya karbi wannan kaddara da hannu bibbiyu. Ya godewa ni’imomin Ubangiji a gare shi, amma ba ya yi ta kuka ba”.
Zahraddeen ya daga jajayen idanunshi yana kallon Inna, nitsatstsiyar dattijiya mai kyautatawa ‘ya’yanta, tare da yin duk wani kokari don ta faranta musu, a cikin halin bakin ciki ko tashin hankali.
Ya ce,

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *